RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Yana gaida Hajiya, Mustapha ya shigo. Ya gaishe shi, Shatima ya ce “Don Allah Mustapha ka hada min duk kayana. Sannan kuma in an gama zirga-zirga ka dauki motar nan tawa ta da.”
Dadi ya rufe Mustapha, ya shiga godiya. Hajiya ta ce, “Kafar yawo ta karu, ai dole kayi murna.” Mustapha yace Ai na huta, in na ari motarki, ko ta Alhajinma, sai a kira ni a ce dawo min da motata yanzun nan.”

Ta ce, “Ai dai tayi maka amfani.” Ya ce, “Sai dai za ki dinga taimakawa da na mai ko Hajiyarmu?”
Ta ce, “A’a wanda ya baka motar sai ya hado maka da na mai, ko kuma duk lokacin da zaka fita sai ka kira shi ya turo maka da na man.” Suka sa dariya.
Bai baro Zariya ba sai da ya tabbata duk abokan shi na nesa sun wuce. Kusan karfe biyar ya shirya kayanshi a motocinsa guda biyu. Ya ce, Mustapha ya tuka masa motar suje, sai ya hau ta haya ya dawo.
Yana cikin tuki ya tuna ashe fa zai bada abincin rana a gidansa, gashi tun da ya fito bai koma ba. A fili ya ce, “Lallai akwai kalubale na ciyarwa.” Yayi murmushi, tare da addu’ar Allah Ya taya shi.
Gudu ya kara har Mustapha da ke biye da shi
ya soma tunanin ko lafiya?
Yana shiga gidan kai tsaye kofar Aliya ya tsaya. Bai bi ta kan Mustapha ba, bare kayan shi da ke cikin mota. Ya nufi falonta da sauri. Tazo ta bude tana yi masa sannu da zuwa, ya jiyo maganar mutane a ciki ya ce, “Kina da baki ne?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Yan unguwarmu ne.” Ya ce, “Me ku ka ci? Na manta fa wai zan ba da abincin rana.” Ta ce “Ni dai naci biredi. Salma ma na ce mata tazo ta amsa ta ce akwai a gurinta.”


Ya ce, “Ina zuwa, bari in ji sauran.” Daidai lokacin Mustapha ya karaso gurin su. Suka gaisa da Aliya, ta ce ya shigo. Ya shiga taje ta kawo masa cin-cin da ruwa, tana fadin gashi bani da komai, ni ko me zan baka? Tana ta haba-haba da shi.
Shatima yaje gurin Amna ya zaci ‘yan uwanta suna nan. Amma sai ya ji gurin tsit! Ya shiga kiranta “Honey!” daga dakin da ke rufe dazun ta amsa da cewa, “Honey!”
Ya shiga dakin a nan ya zama tamkar soko, domin dakin ya tsaru fiye da sauran dakunan. Ya kalleta a gaban madubi tana kwalliya, ya je ya
tsaya a bayanta suna kallon juna ta madubi. Ya isa ya dafa kafadunta
“My honey kin yi kyau matuka, wannan dakin ya dace da me kyau irinki.” Ta ce, “Honey wannan dakinka ne, shi yasa aka rufe shi.
Ya ce, “Wai sun tafi ne? me ku ka ci da rana?” Ta ce, “Sun dafa Indomie.” Ya ce, “Kin tabbata ba
Www.bankinhausanovels.com.ng
su tafi da yunwa ba ko?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “To ke me ki ka ci?”
Lokacin ne ya dora yatsun shi a kan lebunanta. Tayi dan fari “Ban ci komai ba, amma tunaninka ya kosar dani.” Ya kwanto a kan kafadarta fuskarsu suka daidaita.
“Ina son ki Amna.” Ya fada cikin murya tattausa. Ta lumshe ido “Ina tsananin sonka mijina.” Yayi mata wata magana a kunne, tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta.
Ya saketa yana dariya tare da fadin “Da gaske ni ke yi, bari in je in dawo.” Tabi kofar da kallo bayan ya fita, sannan ta sauke ajiyar zuciya. Tayi imani da gaske Shatima yafi sonta.
Yana shiga gurin Nafisa, tana zaune a falo ta
mike a kan kujera tana danna waya. Ta dago ta
kalle shi tare da amsa sallamar kasa-kasa. ya zo ya
zauna a hannun kujerar, yasa hannu ya dago fuskarta.
“Haba Amaryata! Wai fushin me ki ke yi da Angonki?” Ta lumshe ido. “Bayan ba ka sona, don kaga su Alhaji ne suka hada mu.”
Ya koma kan kujerar ya zauna, sannan ya janyota jikinshi. “Wa ya fada miki cewa bana sonki? Haba sweetyna, wallahi ina sonki tun kina
Www.bankinhausanovels.com.ng
Karama, ban dai taba fada ba ne. Allah Ya taimake ni su Alhaji suka yi min gata.” Tayi murmushi, “Har naji dadi.” Ya ce, “Kina
jin yunwa ko?” Ta ce, “Ban ji yunwa ba, su
Shahida ma sunyi-sunyi in ci indomie da suka yi
na ce bana jin yunwa.” Ya kai hannu ya shafa cikinta, “A’a bari a samo miki wani abu. Me ki ke son ki ci?” Ta ce, “Abin da za ka ci.” Ya sumbaci kumatunta “To bari in je in nemo mana.
Ya fito ya shiga gurin Salma. Bata ji shigowarshi ba, tana dayan dakinta wanda babu komai a ciki, tana kakkaɓe tsofaffin littafanta na Makaranta tun tana JS1 har zuwa 3.
Ya ce, “Ke kuma me ki ke yi a nan?” Ta ce,
“Ina duba takarduna ne ko da wanda zai min
amfani. Ya ce, “To ajiye ki zo.” Ta same shi
zaune a falo. Ta durkusa a gabanshi. Ya kama
hannunta.
“Zauna nan.” Zai dora ta a cinya ta ce, “Yaya bari in zauna a nan.” Ta nuna kujerar kusa da shi. Ya ce, “Nan za ki zauna.” Ta ce, “Wani abu ni ke ji.” Ta fada tare da rufe fuska. Ya kyalkyale da dariya. Cak! Ya daga ta ya dora ta kan cinyarshi tare da rungumeta.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Babyna kina jin yunwa ko?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Aliya ta ce ta ba ki biredi.” Ta ce, “Bata bani ba, dama ina da wani ragowa na safe.” Ya ce, “Me za ki ci da dare in kawo miki?”
Ta ce, “Ni fa komai ina ci, ko Rogo da dankali ne zan ci.” Yayi dariya, “Su ki ke marmari? Ta ce, “A’a wai naga su ne mutane basa so.” Ya dire ta sannan ya mike, “Bari in nemo mana abin da zamu ci.”
Da ya dawo gurin Aliya, ya samu tayo wa bakinta rakiya’ za su wuce. Ya ciro dubu biyu ya basu, ya ce su hau mota. Suna ta godiya. Ya ce ma Aliya ta turo mishi Mustapha.
Sun kwashe kayan cikin mota guda daya, ya ce “Hau muje.” Gidan abinci suka je suka siyo. Ya siyo har da su shawarma don ba lallai Amna ta ci abinci ba.
Suna zuwa ya sallami Mustapha don kada dare yayi masa. Yana ba Aliya abincin duka ya wuce Masallaci nan kusa da su. Sai da yayi Isha’i sannan ya shigo. Ya ce ma Aliya ta fito da abincin nan ta shirya su don nan zai kira su duka aci, sannan yayi amfani da wannan damar ya hada kansu.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Hakan yayi.” Ya fito ya ce da Maigadi ya rufe gidan kawai. Sannan ya nufi gurin Nafisa don yafi tunanin zata fi ba shi matsala. Ya ce, ta zo sashen Aliya. Ta ko bata rai, sai yayi kamar bai lura ba ya fita.
Yana shiga gurin Amna ta idar da sallah. Ya ce ta taso za suci abinci tare a gurin Aliya. Ta kalle shi “Mene ne?” Ya ce, “Gurin Aliya zamu je honey, saboda ina son in yi magana da ku.”
Ta tabe baki, “Yi hakuri honey ban raina ka ba, amma gaskiya ba zan iya zuwa gurin wata ba.” Ya isa gurinta ya kama hannunta. “Haba honey, Aliya ta girme ku fa!” Ta ce,
“Wannan ba matsalata ba ne, amma ba zan je
ko ina ba.” Zai kara magana ta ce, “Honey banason muna yin jayayya please.”
ya juya zai fita, ta ce “Yauwa honey, mene ne labarin yarinya ta hudu da muka je dinner da ita?” Nan take ya ji yawun bakinshi ya dauke. Ya dube ta.
“Labarin yarinyar yana da tsawo.” “Gajarce min don in fita a duhu.” Ya ce, “Ita ce mace ta hudu, na aure ta ne don in taimaki rayuwarta, in cece ta, amma ba don so ba.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta tsura mishi ido, sannan ta daure fuska, “Auranta shi ne taimako na Karshe da zaka iya mata in ba haka ba za ta mutu?” Ya ce, “Honey shi yasa na ce miki labarinta mai tsawo ne.” Don ya kauda zancen ya ce “Zamu iya zuwa dakinki mu ci abincin?” Ta daga kafadu, “In kun ga dama ina yin maraba da ku.”
Yana fita ya sauke ajiyar zuciya. Ya koma gurin Nafisa, ya ce “Tazo dakin Amna.” Salma ma ya same ta ta idar da sallah, ya kira ta. Ya je gurin Aliya, bai boye mata yanda suka yi ba, taji haushi… amma sai ta nuna ba taji ba.
Ta ce, “Muje, durkusa ma wada ba gajiyawa ba ne, sai ka tashi da tsawonka.” Duk sun gigita da ganin falon Amna, Salma kuwa kasa shiru tayi ta . kalli Amnar wadda ta kwaso cokula ta zuba a cikin tiren da ke kan dinning din da za su zauna ta ce, “Anty gaskiya dakinki yayi kyau. Zamu iya leka  sauran dakunan?”
Aliya da Nafisa suka kalleta da sauri, har Nafisa ta kasa. dannewa taja tsaki. Amna cikin maganarta.can kasa ta ce, “Sosai kuwa, ku shiga ko ina.” Har Salma ta mike Shatima ya ce, “Jira mana aci abincin dama ya soma hucewa.” Salma ta dube shi, tare da fadin “To.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tamkar Shatima ya sani Amna shawarma kadai ta ci sai madara. Nafisa ma kadan ta ci da alamu ita ba mai cin abinci ba ce. Duk da har da kishi da suka gama, ya ce su koma kan kujeru yana da magana da su.
Ya ce, “wa zai bude musu da addu’a.” Salma ta cafke, don sun saba yin addu’a in anje gidan gaisuwa ko taya mura daga Islamiyarsu. Sai dai shi ne ya karasa addu’ar da fatan Allah Ya basu zama lafiya, ya hada kansu.
Ya ce, To yana son sanar da su kamar yanda suka sani Aliya ce uwargida don ta dan girme su. Yana son su bata girmanta. Ita kuma yaja hankalinta da cewa tayi musu adalci, sannan ya ce dukkansu ga amanar Salma, yarinya ce kankanuwa yana son in tayi ba daidai ba su sa ta a hanya.
Ita kuma ya ce ta bi kowa sau-da-kafa. Ya bukaci jin ta bakinsu. Aliya.ta ce, “Insha Allahu zata yi fiye da yanda yake so.” Amna ta lumshe ido cikin isa ta ce, “Zan kula.” Nafisa ta ce, “Naji, amma da ka ce ga amantar,wannam yarinyar shi ne ban dauka ba, don ba a rainon kishiya ko jaririya ce.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Salma dai burinta a gama maganar ta kalli cikin dakunan gidannan, don haka da ya ce Salma ba ki ce komai ba? Ta ce, “Ni Yaya duk yanda ku ke so wallahi haka zan yi.” Kafin yayi magana ta ce, “An gama mu kalli dakunan?”
Tausayin Salma ya tsirga mishi, yarinyar babu komai a cikin zuciyarta. Daga shi har matan ba su gabanta. Ya ce “Za ku gani ki bari a gama magana.” Ta ce, “To.”
Ya ce, “Sai batun kwana, ni dai in sona ne in yi kwana daya a dakin kowaccen ku, amma ku ya ku ka gani?” Aliya ta ce, “Yayi.” Amna ma ta ce “Yayi.” Nafisa ta ce, “Ai dama sai hakan, don in ya wuce haka sai bayan wane lokaci za ka ga mijinka?”
Ya ce, “Ke wai fadin to ne matsala?” Ya dubi Aliya, “Yau nan ni ke kenan?” Ta ce, “Haka ne. Suna tashi Salma ta ce “Zaku tafi ba mu gani ba.` Nafisa ta ce, “Ke bakauyiya sai kiyi ta kallo.”
Aliya dai yi tayi kamar an kira wayarta, tasa a kunne ta fita tana fadin “Hello! Hello!! Salma kuwa sai da ta leka ko’ina, Shatima yayi mata jagora. Sai fadi take “Aljannar duniya!”
Suka dawo falo inda Amna ta harde a kan kujera ta ce, “Anty guri ya yi kyau Allah ya kara
Www.bankinhausanovels.com.ng
arziki.” Amna tayi dan murmushi, sannan ta ce “Amin.” Suna fitowa Salma ta ce “Tsorona daya fa Yaya zan kwana ni daya yau, in aka dauke wuta zan firgita.” Ya ce, “Ba za a dauke ba in Allah Ya yarda, to a haske ki ke kwanciya?” Ta ce, “Sosai ma. Jiya sun dauke wuta Allah yasa Anty Badi’atu tana nan, na kankameta.”
Ya ce, “Dama ke sarkin tsoro ce?” Ta ce, “Kai, Allah ko da ranar nan tsoro nayi ta ji.” Ya ce, “Muje in raka ki, kiyi addu’ar bacci babu abin da zai same ki.”
Bayan ya sa ta ta rufe kofa, ya nufi dakin Aliya yayi wanka yasha sabbin kaya, ya dauki makullin mota ya fita.
Kajin Amarci ya siyo da madara mai sanyi, da
sauran kayan zaki, don ya lura Amna tana son
shan zaki ko ya ce an saba musu da shan zaki.
Kai tsaye gurin da motocin ta suke ya wuce, ya saka tashi. Sannan ya fito da ledojin ya nufi falon Amna. Yana shiga ya kulle kofar, don yasan ba zai fito ba sai gobe.
Dakin da ta sanar da shi cewa nan ne nashi, nan ya nufa. Karan ruwan da ya ji daga cikin bandakin shi ne yasa shi tunanin tana ciki. Sai ma ya ga kayanta da ta cire a kan gado.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *