RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

tun a jiya ta gano matsayin waccan Mahaukaciyar yarinyar, don ita minti shidda ya dauka a gurinta.
Sai dai har karfe takwas bai shigo ba, gashi ta kasa tashi ta nemi koda abin kari, sai wani bakin ciki da taji yana yi mata tukuki a zuciya.
Amna ya soma kira don layin Aliya ya ki shiga. Ta dauka da fadin “Hello honey!” Ya ce, “My honey na makara office yau, ban shigo ba ina fatan kina lafiya?”
Ta ce, “Ina lafiya zumana.” Ya ce, “Kin ci abinci ko?” Ta ce, “Yanzun na tashi, zan sha tea ne da Indomie yau.” Ya ce, “To ki sha da yawa. Ta ce, “Jiya mun yi waya da Mom dinmu, ta ce za a kawo min mai aiki yau ko gobe.”
Ya dan yi jim, me hakan ke nufi, shi zai biya ‘yar aikin? Ta ce, “Hello kana ji na kuwa?” Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce “Kaga na huta.” Ya ce, “Haka ne, to sai na dawo.” Yayi shiru yana juya wayar hannunshi.
Kenan ana nufin sai ya dauki ‘yan aiki hudu ko
ko me? Ya juya ya shiga kiran layin Nafisa. A cikin dakinta ta jiyo karar wayar, ta mike tana dauka wayar tana tsinkewa, kiran ya sake

shigowa. Ta daga cikin daure fuska tamkar tana gabanshi.
Ta ce, “An tashi lafiya?” Ya ce, “Lafiya lau, kin karya kuwa?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Kan me sweety?” Ta ce, “Ba ka ki zuwa ba, kila ma kaje ka duba kowa ni ce ban da matsayin da za a zo a duba ni.” Muryarta ta soma rawa alamun kuka.
Ya ce, “Haba Nafisa! Ki min kyakkyawan zato mana, tun yanzun za ki soma dora zargi a tsakaninmu? Gaskiya ban ji dadi ba. Na makara ne shi ne dalilin da yasa na tafi office na ce zan kira ku in ji lafiyarku.”
Ta ce, “To kayi hakuri.” Ya ce, “Ya wuce, amma kar ki sake. Sannan ki nemi abinci ki ci.” Ta ce, “Zan yi yanzun.” Ya ce, “To babu kuma wata matsala?”
Ta ce, “Babu komai, sai ka dawo. Kayi tunanina.” Ya ce, “Zan yi, kema kiyi tunanina.” Ta ce, “Kullum kana raina.”
Aliya tana ta kai-kawo a cikin dakinta tsakanin kicin da dakunanta, abin karinta take dafawa. Taliya ta ke son ci dafa-duka ta manja, sai dafaffen kwai.


Www.bankinhausanovels.com.ng
Sannan tana son hada shayi, zuciyarta kuwa cike da son sanin abin da yasa har ita da take ganin ta kai a zuciyarsa bai iya zuwa ya dubata ba.
Sannan tana son jin shin me ya faru jiya da ta ga rufe kofar Shatima bayan ya fito daga dakinta ya dau kaya, ta zaga gurin windown Salma ta baya, taji kukan Salma tana fadin “Don Allah Yaya kayi hakuri..” amma bata ji muryar Shatima ba duk da tasa kunne sosai.
Kuma kukan na Salma yafi yi mata kama da kukan shagwaba fiye da kukan laifi. Karar wayarta da ke jone a chaji ne ya sa ta fitowa da sauri, don tasan Shatima ne, domin ta ware masa ringing dinsa na musamman.
Tana dagawa ta ce, “Masoyina!” Ya ce, “Kin tashi lafiya abar sona?” Ta ce, “Lafiya lau.” Ta sauke ajiyar zuciya. “Na zuba idanu ban ji ka ba. Ya ce”Yau nayi latti ne my love, shi yasa na ce bari in ji ya ki ke, cikin bai kara ciwo ba ko?”
Ta ce, “Bai kara ba, dama yana min haka ko a gida, wani lokacin cikin dare zai tashi.” Ya ce, “Kuma ba ki taba ganin Likita ba?” Ta ce, “Na gani sosai ma aka ce wai ba komai, zan daina lokaci ne.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce cikin muryar tausayi, “Allah Ya baki lafiya.” Ta ce”To Salma ta sha’afa ne bata tashe ka da wuri ba?” Tayi maganar cikin son ta ji kurilla.
Ya ce, “Wannan baby din kin san sai dai ni in tashe ta, kuma kin san tayi kokari gurin bani abin kari da wuri, ni kaina ban san me yasa ni yin latti ba.
Ta ce, “Soyayya ce tayi dadi.” Ya ce, “To, soyayyar ce gata nan kala-kala, kowacan ku da irin wadda take bani. Yau dai kina fes-fes ko? Don ke yau ne amarcin naki, kyalli na koya cika cif.”
Tayi ‘yar dariyar tsokana, “Ai ko har yanzun ban yi fes ba.” Ya ce, “Haba dai, har ina cewa ke yau in mun zo me tazarce ne, dan watanni mu dauki baby.”
Cikin jin kunya ta ce”Haba dai?” Yayi ‘yar dariya, “Sai na dawo ke dai ki sa mu cikin addu’a.” Ta ce, “To sai ka dawo.” Tana kashe wayar ta ce, “Allah Ameen. Allah Ka sa ni zan soma dire da a gidannan, kuma namiji yanda ni ke Yayarsu haka ma dana ya zama babbansu.”
Aliya ta kammala karin kumallonta tana zaune shiru ta kasa kwashe kayan, tunda bata ji abin da
Www.bankinhausanovels.com.ng
take son ji ba a gurin Shatima, ya kamata ta bigi cikin wannan wawiyar yarinyar cikin dabara.
Dan kwanan silba ta samu ta shake da taliyar, sannan ta saka kwai guda daya ta nufi sashen Salma.
Salmar tana wanke-wanke a cikin kicin ta jiyo
sallama hade da kwankwasa kofa. Ta dauraye
hannu ta fito. Ganin Aliya sai ta saki fara’a “Sannu da zuwa Anty.” Ta saki fara’a itama “yauwa sannu kanwata. Na ce tun da ke ba ki zuwa gaida ni ni bari in zo mu gaisa.” Salma ta ce, “Lah! Ba haka ba ne Anty, ki zauna mana.”
Aliya ta zauna a hannun kujera, tare da fadin “Ban sani ba ko an hana ki ne.” Ta ce, “Haba Anty, wa zai hana ni? An dai ce min ne kada na ke shiga dakunan kowa.”
Ta tsugunna tana gaida Aliya. Ta amsa tare da
fadin “Tashi ki zauna a kan kujera.” Ta mika
mata, “Ga taliya ko kema abinci ki ka dafa?”
Salma tasa hannu biyu ta amsa tare da fadin “Na gode, ba abinci na dafa ba, Biredi na ci.” Ta ce, “Ai bani iya cin biredi kullum.”
Salma ta ce, “Ni ai duk abin da na samu bana tara.” Aliya tayi dan murmushi, “Kin huta.” Tayi
Www.bankinhausanovels.com.ng
dan kalle-kalle a dakin. Salma ta ce, “Kin ga nawa dakin bai kai naku kyau ba ko?”
Aliya ta ce, “Ai wannan duk ba wata matsala ba ce, sannu a hankali za ki sai duk abin da ki ke so ko?” Salma ta zaro ido. “Ina zan samu kudi, ni dai na gode ma Allah Anty tunda na samu mijin daba irin gama-garin maza din nan ba.”
Aliya taji mamakin kalamin Salma, har ma ta kasa boyewa. Ta ce, “Har kin san namiji me inganci?” Salma ta rufe fuska cikin kunya. Aliya ta ce, “Ashe kin iya soyayya shi yasa ki ka sa Angon naki ya makara?”
Salma tayi yar dariya, “Ni ban san wata soyayya ba Anty, shima ya sani.” Ta ce, “To ai jiya ina jiyo ki daga dakina kina kuka.” Salma ta zaro ido tana kallon Aliya.
Aliya tayi ‘yar dariya, “Ai ina ji kina kukan shagwaba, Yaya kayi hakuri.” Salma ta rufe fuska. Aliya ta harare ta, lallai abin da take zato haka ne. Ta ci gaba da fadin “Har zan shigo ceto na zaci
laifi ki ka masa.” Salma dai tayi shiru. Aliya ta ce.
“Ko wani abin ki ka yi masa?” Salma ta sake rufe fuska tare da fadin “Babu ruwana, ya ce kada in fada ma kowa.” Gaban Aliya ya fadi, tayi shiru. Can ta ce, “To ai ba zan
Www.bankinhausanovels.com.ng
fada mishi ba, ni na dauke ki kamar kanwata ne, duk abin da ki ka yi ba daidai ba zan nuna miki. Kuma shima ya bamu amanarki.”
Salma ta ce, “Ni dai kiyi hakuri Anty, tun da ya ce kar in fada ma kowa.” Aliya ta ce, “Shi kenan. Juye ki bani kwanon.” Salma ta ce, “Ki bari in na wanke zan kawo miki, dama naga dakin kowa naki ne ba
n gani ba.
Aliya ta mike, “To sai kin zo. Bayan ta koma sashenta, tana zaune a cikin dakinta tana ta nazari. Yanzu Shatima saboda rashin hakuri ga su su nawa sai da ya kula wannan ‘yar yarinyar saboda ja musu raini?
Duk da ta ki fada alamu sun nuna akwai abin da ya faru tsakaninsu. Sai dai zata gwada kishin yarinyar ta gani kowane irin so take yi wa Shatima.
Ba ta ki ace ita kadai ba ce da Shatima, kuma
sannu a hankali da siyasa burinta duk sauran su
zama a karkashinta, sai yanda tayi, sai kuma yanda ta ce. Salma ta gama komai, sannan ta janyo kofarta,
ta dauki kwanon Aliya ta tafi kai mata.
Ta same ta tana zaune tana kallon TV, don rana daya yasa aka saita musu TV nan su, aka kuma saka musu Tauraron Dan Adam.
Salma ta shiga da sallama, Aliya ta amsa tare da cewa “Salma kanwar Anty.” Salma tayi murmushi, sannan ta tsugunna.
“Sannu Anty.” Aliya ta ce, “Yauwa. Tashi ki zauna muyi kallo.” Ta kalli TV kasar Indiya take kallo. Sannan ta hau kujerar ta zauna.
Salma ta dinga kallon falon, ta dubi Aliya wadda tana hankalce da duk motsin Salma da inda take kallo. Salma ta kalle ta.
“Anty ashe kema haka dakinki yayi kyau?” Aliya ta ce, “A hakan? Ai ban kai su Amna ba nima.” Salma ta ce, “To ai kema babu laifi.” Aliyar ta mike “Zo ki ga dakunan kwanan.” Daki biyu da gado, daya kuma da kafet da katifa.
Salma ta ce,”Wai duk dakunan da aka sa gado sauran wa ke kwana?” Aliya ta ce, “Babu kowa, amma in kayi baki ka huta sai su kwana, ko kuma yau in kun kwana a nan, gobe ku kwana a can.”
Salma tayi dariya, “Ni in bakin nayi sai in shimfida musu Tabarma.” Aliya ta ce, “Kokari dai zaki yi kamar yanda na fada miki, ki dage ki sai
Www.bankinhausanovels.com.ng
duk abin da ba ki da shi, kiyi gado me kyau, sai ki cire wancan ki kai shi daya daga cikin dakin.”
Salma ta ce, “Anty ni da ba sana’a ba, yanzun haka bani da Naira daya.” Aliya ta ce, “A wanda yake bamu mana. Salma ta dubi Aliya cikin. mamaki, “Wane kudi kuma?” Aliya ta ce, “Dubu dai-dai na kashewa da ya ke ba mu, shekaran jiya da jiya ya bamu.”
Salma ta girgiza kai, “To kila ya manta ne, ko
kuma zai tara min.” Aliya ta ce, “Wai kina nufin ke bai ba ki ba?” Salma ta ce, “A’a.”
Aliya ta ce, “To amma kada fa ki tambaye shi.” Salma ta rike baki tare da fadin “Ni! Ba zan yi mishi magana ba, kila ku ya ga kuna da bukata ni ko me zan da kudi? Kuma nasan Yaya ba zai cutar da ni ba, da yaga ina da bukatarsu zai bani.”
Aliya bata so haka ba, ta so a ce Salma ta nuna rashin jin dadinta a fili. Suka dawo falo, Salma ta ce, “Bari in je in kwanta bacci ni ke ji.” Aliya ta ce, “Ai gara kije ki kwanta tunda jiya bai bar ki kin yi bacci ba.
Ta dan rufe fuska, “Kai Anty!” Sannan ta fice cikin kunya. Nan ta bar Aliya tsaye cikin takaici. Ta lura in ma ta tsaya bin ta Salmar nan haushi
Www.bankinhausanovels.com.ng
zata sha, gara ma ta koma yaki da manyan arnan. Amma zata bari ta kama Maigidan a hannunta.
Haka Shatima ya ci gaba da zagaye dakin matansa, tare da kokarin ganin ya yi adalci a tsakaninsu. An turo ma Amna ‘yar aiki, ‘yar babba ce haka bazawara, kakarta ita ce ke aiki a gidan su. Amna taji dadin ta domin tana yi mata aikin gida tare da girki. Har Shatima ya share bai
Tambayi albashin ‘yar aikin ba, sai kuma yaga rashin dacewar hakan.
Ya tambayi Amna “To a kan nawa suka yi za ake bata, sannan zata ke dan taimaka ma sauran mata?” Amna ta ce, “A’a wannan ba wanda zata
taimakawa, domin iyayena ne za su biyata. Za ka iya samo musu wasu babu matsala.”
Hajiyarshi ta kira shi wata safiya, lokacin kwananshi goma da auren. Ta ce “To ‘Yallabai, yanzun an yi aure za ayi mana kaura, ko waya rabonka da kiranmu yau kwana uku.
Na zaci ni daya ce, ashe har Babanku. To, in mun maka laifi ne tuba muke.” Cikin sauri ya ce. “A yafe min Hajiya, aiki ne kuma ga gidan har yanzu ban gama saita shi ba, amma zan shigo. Nayi kuskure, zan kira Alhaji yanzun nan.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “To ya batun zuwa gaisuwar Surukai? Sati daya ake zuwa bayan biki, kai kuma naji shiru, ko kun je?” Ya ce, “Tab! Wallahi Hajiya na manta, Munnir ma ya kira ni ya tuna min amma abin ya shige min. sai dai in Allah Yaso wannan satin da zai zo sai muje.”
Ta ce, “To shi kenan. Su kuma sai ka debo su su zo ku gaida iyayenka da Kakarka ko?” Ya ce, “Wayyo Allah! Hajiya wannan shi ma dole ne? in bai zama al’ada mai karfi ba amin hakuri.”
Ta ce, “Ba yanzun da sauri ba, a hankali ma sai ka zo da su.” Ya ce, “To shi kenan.
Shatima ya kalli agógonshi, sha dayan dare sam bai so ya kai wannan lokacin ba, alhali yana dakin Nafisa, domin shi ya san korafi ta da mita, har bai so ya mata wani kuskure, don baya son tun yanzun ya fara nuna fushinsa.
Kuma fita ce ta kama shi ta dole za su ga Gwamna. Daga can suka wuce bikin wani abokin aikinsu. Shatima ya mike tare da dafa na kusa da shi.
“Abubakar ba zan iya jira a gama wannan Dinner din ba. domin iyalaina suna zuba ido.” Shima ya mike, “To ai dole nima in tashi tun da

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *