RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 1 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA-3
ALhaji Isa ya shiga cikin Falon yana kiran,
“Hajiya!”
‘ Badi”atu ta fito daga dakinta tana yi
wa Alhajin sannu da zuwa,
sannan ta ce,
“Yaya Mustapha ya kai ta Kaduna”.
Ya kalli agogon bangon falon tare da fadin,
*Nan da Kaduna shine har yanzu sai ka ce wadanda http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
suka tafi Abuja?
Badi’atu ta ce,
“Sai da suka yi sallar azahar
sannan suka tafi”
Ya ce,
“Kai Hajiya tana da shiririta sosai. Ni da
muka yi da ita za su tafi tun safe?”
” Ya ja tsaki tare da
fadin,
“Yanzu dubi fa shida saura, kuma ta san ina
azumi”
Badi’atu ta ce,
*Ga shayinka can yanzu na
gama dafawa, na sa a flask”
Ya ce
“*Shayin ne kadai matsala ta kenan?
Tana sani na tsani in dawo ba ta gida. To wai su nawa
suka yi tafiyar ne?”
Badi’atu ta ce,
“Su da Mama
Ya nufi dakinshi yana fadin,
*Bari in kira ta”
Daidai wannan lokacin Shatima yana tsakiyar
falon cikin tsansnin damuwa, da tashin hankali. Minti
daya tak din da Hajiya ta ba shine ya yi mugun tsorata
shi. Sam ba ta ba shi isasshen lokacin da zai yi tunani
ba. Ya nufi kujera da nufin zama ko zai samu basirar
shawo kan matsalar. Don rudewa sai ya kai zaman
kafin ya isa kujerar. Hakan ya sa shi zubewa a kasa http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Salatin da ya ji dakin ya dauka gaba daya ne ya
sa shi lunshe ido, tare da fatan Allah ya sa mafita ce
wannan Ya saki jikinshi tamkar wanda hankalinsa ba
ya tare da shi Nan duk suka yi kansa suna kiran
sunansa. Hajiya tana fadin, “Na shiga ukuna! Shatima
don allah ka tashi! Ku debo min ruwa
Mama ta ce, “Tsaya mu gani ko dai juwa ce ba
suma ba ne?”
Aliya da su Amna sai nanata sannu suke yi.
Hajiya ta dibi ruwa ta wanke mishi fuksa tare
da fadin,
“Sannu Shatima, ka tashi don Allah
Duk yana jinsu, ko babu komai sanyin ruwan
ya rage masa zufar da take tsiyaya a jikinsa. Sannan ya
sauke wata irin ajiyar zuciya.
Mustapha cikin bacin rai ya ce, “Ban ga dalilin
yin wannan zantukan ba tunda ba su ne suka kawo mu
ba”
Shatima kuwa addu’a yake a cikin zuciyarsa,
yana kiran sunayen Allah tsarkaka. Fatanshi Allah ya http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
fidda shi cikin wanna fitina. Miyan bakinshi ya tsaya
cak! Lokacin da ya ji muryar Hajiya tana maimaita ya
wartsake a yi ta ta kare, don ba zan bar wannan damarba.
Mama tace, “Haba Hajiya! Don Allah ki bar
wannan maganar, a bi komai sannu
Alhaji ya yi ta duba wayarshi a daki, sai ya tuna
tana mota inda ya jona ta a caji. Ya cire kayanshi ya
maida jallabiya mai gajeran hannu, sannan ya fita.
Missed calls ashirin na Mustapha ya gani, Tsoro ya kama
shi, tare da fargaba suka darsu a zuciyarshi. Tuni ya
Raya cewa sun yi hatsari ne. Cikin rawar hannu ya bi
kiran.
Da sauri ya daya,
*Alhaji don Allah ka kira
Hajiya yanzun tazo tana ta fada da abubuwa a gidan
ga shi nan har Ya Shatima ya fadi!*
“Faduwa?” Alhaji ya tambaya da karfi.
Mustapha ya ce,
“Faduwa kuwa, yanzun haka
ba ya cikin hankalinshi
Alhaji ya ce, “Ai babu batun kira, bari kawai in
kira Babanku Musa muzo gidan
Mota ya fada a hakanshi, sannan ya kira layin
dan uwansa Alhaji Musa. Lokacin da Alhaji Musa ya http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
daga wayar Alhaji ya kusa fitowa daga layinsu. Alhaji
Musa ya ce, ga shi a Jaji sun z0 duba jikin Alhaji
Yakuba abokinsu, wanda ya hadu da ciwon mutuwar
Barin jiki.
Alhaji ya ce, “Gani a hanya, jira ni a titi zan
dauke ka mu wuce”
Alhaji Musa ya ce, “Ina zamu Wuce!?”
Alhaji ya ce,
“Kaduna gidan Shatima, Hajiya
Amina da suka je dubiyar jikin Nafisa ta tada musu
wata fitinar. Ga shi can an ce jikin Shatima ya tashi har
ya fadi yana da rai ko ya mutu ma? Ni ban sani ba”
Gudu sosai Alhaji ke yi, cikin mintuna ya iso
Jaji, ya dauki Alhaji Musa ya kuma daukar hanya
Cikin lokaci kalilan Shatima yana jingine da kujera
kanshi yana cinyar Aliya wadda wadda idanu suka yima jajir don kuka.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.DAILYNOVELS.COM.NG