RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 18 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 18 BY HALIMA K/MASHI

 

 

ce kullum tana gida kowa ya fice ba. Cikin haka

kwatsam sai ga Nafisa ta soma jinya.

Suna zuwa asibiti aka ce ciki, Nafisa ta daka

tsalle ta ce,Saidai a zubar, Shatima kuma ya ce,

wallahi in ta sake ta zubar masa da ciki zai mata hauka, za ta sha mamaki. Rikicin da sai da ya kai su gaban

Mamanta, inda Mama ta yi mata tas, ta kuma cc kar ta sake jin makamanciyar irin wannan maganar. Dole

Nafisa ta zo ta dangana, amma sai da Shatima ya nemo mata mai aiki

saboda kula

da Ashrat, tunda ita

laulayinta ba ya mata da wasa.

Wani abu da ya sa Shatima cikin wani mugun

Bacin rai,

Amna ta saka Jafar a

makaranta mai

matsanancin tada. Ajin wasan yara, kuma sai da ta kaishi ta yi komai ba tare da ta sanar da shi ba. Sun yi

rigima sosai ba tare da kowa ya sani ba. Kinyarda da

ka^idojin da ya saka. mata ne na cewa, lallai ta ciro yaron daga makarantar domin dan ikonsa ne ba nata

ba. Abin da ya sake bata masa rai da ya kira mahaifinta

ya sanar da shi, sai ya nuna cewa, ai shi ta taimaka

kasancewar ba ta ce ya bada kudinshi ba. Haka kuma

ita ma tana da ikon yi wa dan komai tunda ita ta haife

shi. Rikicin bai

Kare ba, sai da ta kai kara gurin

Hajiyarsa.

Hajiyarsa ta hada su ta yi musu nasiha inda ta

nuna ma Amna cewa ba wai laifi ba ne don ta saka

dansu a makaranta, amma komai ya zama cewa za su

ke yin shawara. Shi kuwa Hajiya ta ce ya yi hakuri

komai ya wuce. Da ma Aliya ita ce ta yi ta kara

tunzura shi. tana

nuna masa cewa kan ya yan zai

bambanta in har ba makaranta daya suke zuwa ba

Sannan yaran Amna za su raina shi a nan gaba matsawar suka gano cewar uwarsu ce ta ke yin dawainiya da su, shi za su ga kasawarshi. Irin wannan

zantukan na Aliya suke saka shi jin tsanar Amna da jin

zafinta. Bugu da Kari, Amna ta je ta saka maganin hana

daukar ciki don tace masa baza ta iya haihuwa duk

bayan shekara biyu ba. Nan ma sun sha rigima da jin zafin juna.

Ranar wata litinin Salma sun je makaranta, sai

aka ba su hutu domin mataimakin shugabar makarantar

ya rasu, Salma Dankasa ta ce bari ta je gidan su Salma Bash sai ta yi waya a z0 a dauke su tunda direbansu ya

wuce. Su Amina Hamza da su Jamila A Ramalan sukace suma za su je. Salma kuwa ta ja su suka je, ta yi

musu girki suka ci, suka sha hirarsu har suna

tambayarta wai nan sashenta ne ita daya sai ka ce wata matar aure?

Salma ta ce, ai yayanta yana ji da ita,

“Ni yayan

nata ne ma wallahi ya yi min, akwai aji

Salma dai ta bi su a haka, kowa ta nufi gidansu,

Salma kuwa direbar,u ya zo ya dibe su da kannanta.

Aliya aikin rana gare ta, tana gida lokacin, nan

ko ta kira Shatima a waya ta ce, ga Salma nan ta debo

zugar ” yan makarantarsu sunzo suna ta yi wa mutane

hauka. Nan ko Shatima ya cika dam, don in har Aliya

ta fada mishi magana tamkar wahayi ba ya bincike. Ya

kira lambar Salma a kashe, bai san ta yi wata ba ta da

waya ba. Domin wayarta da Baban Nafisa ya sai mata ce kuma ta samu matsala.

Yana dawowa dakin Salma ya nuta, tana zaune

tana yanke farce. Ya fado tare da sallama. Cikin tsoro

Salma ta dube shi, tareda amsa sallamar.

Yace, “Wane zugar yaran ki ka debo min zuwa

gida yau?”

Ta zaro ido, cikin rawar baki tace

“Salma ce fa da Kannenta.

Ya katse ta,

“Wace Salma? Na lura rawar kai

yana damunki, in kin yi wasa zan cire ki daga

makarantar nan. Ina son ki sani kar ki sake ki sake janyo min wani tarkace gidan nan”

-Jikin Salma a sanyaye, cikin sanyin murya ta

ce,Ka yi hakuri, insha Allahu ba zan sake ba”

Tsaki ya ja, sannan ya juya ya fita.

Sannu a hankali su Salma suka yi jarabawar

shiga S.S 2 suna gida suna hutu, sai dai islamiyya,Lokacin Shatima ya samu karin girma a gurin aikinshi

inda aka maida shi ofishinsu da ke Abuja. Hakan ya sa

sai bayan sati daya yake zuwa Kaduna, Nafisa ya fi tafiya da ita don ita ce ba ta zuwa ko’ina, Aliya ba ta so

hakan ba, amma babu yanda za ta yi tunda ga aikinta.

Cikin haka Nafisa ta haihu, danta namiji.

Wannan karon a gidan Shatima aka sha suna, inda yaro

ya ci sunan Alhajin su Shatima. Tunda ta haihu ta lashi

takobin cewa fa sai ta yi tsarin iyali, kuma sai ta koma makaranta.

Lokacin ne Shatima ya samu damar biya musu

kudin aikin hajji shi da Aliya. Da lokacin tafiya ya yì

suka tafi, Aliya ta tsananta rokon Allah a kan haihuwa.Ta yi roko sosai, ita dai Allah ya ba ta haihuwar ya’ya

maza ita ma. Da aka gama aiki ta  hakuri, kuma ta

Kara kyau da yar Kiba.Lokacin tafiyar ne dai kansu tafi har aka yi dan

rikici, Nafisa ta nuna damuwarta, tare da koratin yanda

yake nuna Aliya ta fi kowa, shi ya sa ma zai je makka

da ita. Ya ce, ba haka ba ne, duk yana sonsu don dai ita

babba ce, kar ta damu duk za su je. Amna kuwa ko a

jikinta don Saudiyya ba bakuwarta ba ce. Salma kuwa

ba ta ji batun tafiyar ba har sai da suka z0 mata sallama, har Aliyar tana fadin a yafi juna.

Sun yo tsaraba, ko da Aliya ce ta yo tsarabar,

don shi bai siyo komai ba tunda ba zuwanshi ne nafarko ba. Ana ta rabon tsaraba, Salma dai an ba ta wata

“yar yaloluwar riga kamar ta bacci, ita dai ta yi godiya ta amsa.

Cikin ikon Ubangiji ko wata ba a yi ba sai ga

Aliya da ciki, murna gurinta da shi kanshi Shatima ba a

magana. Nan ko ta shiga kaudi da salo, Shatima kuma

ya kama biye mata.

Ita Salma yanzun damuwarta daya, duk yan

ajinsu mafi yawa za su yi SSCE, ita ma ta so a biya mata, amma tana tunanin tunkarar Shatima, ga shi an

kusa bikin Badi’atu da su Hamida, da Mami kannen Nafisa. Ta sani duk harkar kudi ce shi ya sa ta kasa

tunkararshi da zancen. Zuciyarta tana yawan fada mata

cewa, ta same shi kawai ta ji abin da zai ce, amma ta

yanke shawarar sai in ya dawo dakinta za su yi

maganar.

anar da ya dawo dakin nata tana jinshi yana

kallon labarai amma ta kasa yi masa magana. Sai ta yi

kamar ta tashi, sai kuma ta koma ta sauna. A karo na

uku ne ta yi ta-maza ta tunkari dakin. Sanye ta ke da

kayan bacci masu dan kauri, don yanayin sanyi ne

lokacin. Duk da cewa, ba wannan ne karo na farko ba

da ta shiga dakin, amma bai hanata diriricewa ba,

kamar dai kowane lokaci in ta shiga.

Yana kwance tsakiyar katifar ya ware A.C duk

da sayin da ake yi, amma ya rufa da bargo.

Hankalinsa kaf yana kan talabijin da yake kallo. Ya maido da kallonsa ga kofar da aka turo, ya kalli fuskar

Salma sosai, kaman mai yin nazari a kan abin da ta z0

da shi. Sannan ya sake maida kallonshi ga labaran da

yake kallo. Ta rusuna gwiwa biyu a gaban katifar,

sannan tace, “Ina yini Yaya?”

Ya amsa ba tare da ya sake kallonta ba. Hakan

ya sa ta ji dan karfin gwiwar da ta shigo da shi ta rasa.

Jin shirun ya yi yawa yace

“Lafiya?”

Ta dago ta dube shi, har lokacin idanunsa suna kan talabijin, tace *•Yaya dama na z0 ne.

Sai kuma ta yi shiru.Ya dube ta, “Kinzo me?”

Cikin sauri

ta dube shi. Ya tsare ta da

idanunshi ta sake sunkuyar da kai,

“Yaya a ajinmu ne

aka ce duk wanda yake son ya zana jarrabawar fita, to ya biya

sake yin shiru, ga sanyin A.C din ya soma

ratsa ta, har ta soma kaduwa

Ya ce, -Ke kina ajin fita ne?”

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *