RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 7 BY HALIMA K/MASHI
ita. Ya rusuna yana gaida Inna, duk da cewa a zaune
yake don girmamawa.
Salma ta zuba idanu tana kallonshi, ya yi kyau
cikin yadi mara nauyi mai ruwan madara. Hular kansa
ta yi matukar dacewa da kayan. Ya kalle ta, ta lumshe
ido, tare da fadin, “Barka da zuwa”.
Ya ce,
“Yauwa. Na ga ko shiryawa ba ki yi
ba?”
Ta ce, “Wai har tafiyar ta tashi? Na zaci sai
dare”
Ya yi mata hararar wasa, tare da fadin, “Amma
na ce miki ki shira ba?”
Ta mike, “Bari in yi wanka”
Ya ce, “Wane wanka kuma? Tashi kawai mu
tafi ki yi shi a gida in mun koma”.
Inna ta ce, “Gaskiya kam, domin ba zama zai yi
yana jiranki ba”.
Salma ta tura baki don yin shagwaba ga Inna, tace, “Kuma hijabi kadai zan zira?”
Inna ta ce, “Oho! In ma a haka za ki babu
hijabin je ki”
Shatima cikin murmushi ya ce,
“Inna fada mata dai”.
Inna ta dubi Shatima tana ‘yar dariya, tare da
yin godiya da dawainiyar da ya kawo musu,
Ya ce Haba Inna, a yi hakuri da shi, garin ne
sai a hankali”
Salma ta hada kaya tana tura baki, ga su da dan yawa saboda dinkunanta da ta amsa. Shatima ne ya
kinkimar mata kayan. Ita kuma ta rataya hijabi a katada.Shatima ya ce, „Ba ki fa san gatse ba fa ke? Ki saka hijabin mana .Salma ta yi mamakin ganin Aliya a cikin mota,
ashe ya dauko ta. Salma ta yi ta maza ta dube ta, but ya zuba kayan Salma sannan ya shiga. Ita ma ta shiga
baya suka nufi gidan su Nafisa.
Suna isa Abin da ya bai wa Salma mamaki sal taga
Aliya ta fita ta nufi cikin gidan su Nafisa tare da Shatima,
ita ma saita Fito ta bIsu. A zuciyarta kuma tana
tambayar me ya sa ba ta shiga nasu gidan ta gaida Innarta ba?
Sun samu duk yan gidan a falo, Da alamu Nafisa
tuni ta shirya don jiran zuwan Shatima. Aliya cikin
kissa da irin salonta ta nufi Natisa.
Yar uwa ya ya dai?” Natisa ta yatsina, fuska, “Lafiya, ya ki ke?”. *”
Aliya ta ce, “Lafiya Ta rusuna tana gaida Mama,wadda Suke
magana da Shatima. Salma ma ta rusuna tana gaida
Maman. Hamida cikin fara’a ta dubi Salma,
“Za ku tafi?” Salma
taceEh. Yauwa Hamida ina
hotunanmu na wayarki?”Ta ce, “Bari in dauko in tura miki Aliya ta kalli Shatima, “Taso mu je Nafisa karmu yi tafiyar dare Tuni Salma ta fahimci Aliya tana fadin haka ne
don taji Hamida za ta tura mata abu a cikin waya. Sai
ta zauna tare da fadin, Dauko ki tura min, ni ban yi hotuna sosai da wayata ba, kin san ba ta da kyan hoto Ko da Aliya ta azalzala su tafi hakan bai saka
Salma ta tashi ba, sai da Hamida ta gama tura mata
sannan suka fito a tare zuwa gurin motar. Aliya ta kalli
Salma wadda ke rike da jakar Nafisa ta taya Hamida dauka. Ta ce,
*Ai na zaci ke ba yau ba
Salma ta yi tamkar ba ta ji ta ba, suka yi
sallama suka hau mota. Salma ta yi dan murmushi
ganin Aliya an dawo bayan mota, Nafisa ta hakimce a gaba. Nan suka nufi Kaduna.
Sun dawo da ‘yan kwanaki aka soma azumi.
Ranar farko dai Salma daure ta yi domin makara ta yi,
washegari ta yi Kudirin tashi nan ma daure ta yi har da
zuwa rana ta uku, a rana ta hudu Shatima a dakinta
yake, ya zaci za ta tada shi kamar yanda sauran suke yi,
amma sai shine ya tada ta. Ya ce,
“‘In don saboda ke ne
makara za mu yi
Ta ce,Ai ni ban taba yin sahur ba’
Ya ce,Saboda me?”Ta ce, “Makara nake yi”
Ya ce,
“Shirme kenan, bacci ki ke kwanciya ki
ta sharawa a wannan watan mai albarka?”
Ta yi shiru, ya ce,
“To daga yau ‘na kashe
baccin nan. A tashi a kai kuka gurin Ubangiji”
Salma ta ce, “To zan tashi, amma sai ka
taimaka gurin tashina Ya ce Shi kenan, zan dinga kiran wayarki, sai
ki dinga barinta a bude
Ran da ya koma gurin Aliya, sai da ta nuna
rashin jin dadinta da tashin Salmar duk da bai tahimci ta damu din ba. Cewa ya yi ta miko mishi wayarsa a caji, sai tace wa zai kira? Ko mutan Saudi zai kira?
Sai da ya soma kiran layin Salma din sannan ya ce,Salma zan tada daga barci
Ta yi ‘yar dariya, “Salmar yanzu don lalaci sai
an tashe ta! Ya kalle ta da dukkan gaskiyarsa, ” Salmar! Baki ganin yarinya ce, wai ashe duk azumin nan dore take yi, wai makara take Ta tabe baki daidai lokacin da yake sake
kiranta, bayan kiran farko ya katse. Cikin barci ta ji
” Karan wayar ta farka da sauri cikin mayen bacci tadaga wayar tana fadin, “Yaya na tassshhhi!’
Ya ce, “Kin tashi ko dai na tashe ki?”
Ta yi murmushi mai sauti, cikin amsar gyaranta
ta ce, “Yaya to ka tashe ni’
Ya ce, “To a yi maza kar a makara.
Ya dubi Aliya wadda takaici ya cika ta, yana
;yar dariya ya ce, “Kin ji ta wai na tashe ta amma tana
fadin ta tashi”
Aliya tace
“To wai ita bata sallar dare
kenan?”
Yace ai dole in matsa mata takeyi.
Aliya tace
“To kai ma kaci abincin kar kai
kuma ka makara.
Ta mika mishi kofin shayin da ta gama hadawa.
Haka kuma a dakin Nafisa randa ya je sai da tayi Korafi da zai tashi Salma, wai ita bai taba tashinta ba in ba ya dakinta.
Ya ce, “Kar wannan ya dame ki, ita ai yarinya
ce ke ki ke tashina wani lokacin ma fa
Ta ce, “Ba wani, don dai ta san za ka tashe ta
din ne shi ya sa take shantakewa
Azumi ya soma tafiya, har lokacin Amna ba su
dawo ba, a zatonshi sati biyu za su yi, “amma shiru!
Yana dai jira ya ga ikon Allah. Hankulan mutane ya
karkata kan sallah, Aliya ta matsu da son ta samu kudi
domin ta lura neman suna sai da kudi, ga shi ba ta nemi
komai ta rasa ba, amma ba ta da kudi a hannunta. Wata
dabara ta fado mata, bari Shatima ya zo ta kallallame
shi ko zai ba ta kwangilar siyan kayan jarirai don ta so
a ce ita ce da ciki domin da tayi tatsa sosal.
Suna kwance bayan idar da sallar asham wadda
yake jansu a falon Aliya. Salma da Nafisa sun tafi
lokacin, ta ce, “Wai masoyina sai yaushe za a sayi
kayan jarrai? Ka san fa ana yin sallah za su haihu.
Yanzun ya kamata kawai ka siya a wuce gurn in sallah tazo sai aji da hidimar sallah*.
Ya kai hannu ya janyo ta zuwa jikinshi tare da
fadin,
“‘Shawara mai kyau, amma kin san dole sai
Amna ta dawo sannan mu je a siya. Ban ma san ko me
da me za a siya ba .
Ta tashi zaune, “Haba dai, kar ka fara da haka,
ka zama namijin da kowane lokaci a gidansa shine mai
tsarawa, kuma shine mai zartarwa. Ni na san duk abin
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe