RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 19 BY HALIMA K/MASHI
Shatuma yace Kaka, wallahi bakin
zuwa nayi ba koda, Hajiya ce ta ce lallai sai dai
kar inzo Kaka ta dube shi cikin sauri Hajiya
Amina da kanta tace kar kazo? Ya yi shiru kamar yana daya sanin fadi Ta kalli Maryama,
“Tashi ki je ciki”Maryama tana fita kaka ta kalli Shatima,Amina dama ta hana ka zuwa ko? To babu laifi ban tsammaci haka ba Amma ban yi
mamaki ba, don ita ma ta dauke tata kafar.
Yanzun sai ka tashi kaje har sai ranar da ita da
kanta taCe kazo sai kazo In matarka ta aminta
ya ce.Kaka na san yanzun ko ta ji nazo
ba za ta ce komai ba. Kaka ina son matata
Kaka ta ce,Ni dai ga abin da nace
Shatima ya mike,Zan je in same ta yanzu, kuma zan dawo Bayan fitar Shatima kaka ta kira Salma, tace, Saura da yazo ya ce ki yi hakuri, ba
kamewa babu komai ki ce kin hakura”Salma ta ce
“‘Shi ya sa ma da ya shigo” ban ko zauna a falon ba Kaka ta Ce,Amma kin kafe shi da ido
ai Salma ta yi yar dariya tare da fadin,Banma san ina kallonshi ba Kaka ta ce,Madalla, shi ya sa na ce da yazo ki yi kamar sakarya”Bayan magariba
Salma tana juya hannunta a cikin tuwon gabanta ta kasa ci. Duk kuwa da tun safiyar ranar take fadin, yau tuwo miyar Kuka za su yi, tunda ga manshanu an kawo musu, kuma ga yajin jego na Badi’atu da ta haihu, an aiko da shi
Maryama ta ce,Har kin sa yawuna ya
tsinke”Amma ga tuwon a gabanta ita ta yi shi,
amma ta kasa ci. Kaka ta dube ta a karo na uku,
sannan ta ce,Kin ga in kin koshi dauke tuwon
nan, haka da rana ina kallonki ki ka kasa cin
abinci. Mijinki ya zo kin ganshi duk kin rasa
nutsuwarki Salma ta ce,Haba dai Kaka, cikina ne
babu dadi, amma ba don shi ba ne”Kaka ta ce,
“Oho, ke ki ka sani, Ko dai komawa ki ka yi in jikinki babu kumari kin rame na ga da me za ki burge shi. Don dai shi namiji lafiyar mace ce mai amfani a gurinsa Salma ta soma tura tuwon ba don tana jin dadinsa ba. Ga mamakinsu sai suka ji sallamar Shatima. Da sauri ta tashi ta bar tuwon ta shige daki, a ranta ta ce, Yau lahadi gobe fa litinin, ko da safe zai wuce Abuja?” Shatima ya zauna inda Salma ta tashi, ya kalli Kaka,
“Don Allah kaka ki yi hakuri ki min duk hukuncin da ya dace da ni, amma ki bari in
tafí da matata Ta ce,Ban hanaka matarka ba, ai ga ta can.Amma cewa na yi uwarka ba ta sani ba”Ya ce,Kaka ta sani yanzun gurinta na
dawo, duk ta yi nadama”Hajiya Kaka ta yi
‘yar dariya tare da fadin,A’a ba ta gane ba tunda bata tako zuwa nan ba” Shatima ya tashi ya koma gaban tuwon Salma,Kaka ki min izini in je in yi magana da ita” Kaka ta ce, Ka ga bana son in sake jin ka kira ni a kan tsakaninka da matarka. Komawa ne dai na ce, sai in uwarka ta zo na ji dalilinta. Inko ya zama babu hujja shi ke nan sai ka ba yarinya takardarta”Ya mike,Bari in yi magana da ita to”Kafin ya ji amsar Kaka har ya mike da tuwonta a hannunshi. Ta bi shi da kallo tana fadin,To da ka dauki tuwo ka bi ta da shi, dure za ka yi mata?”Bai dai tanka ba ya shiga dakin Kaka. Salma tana ganinshi ta fada bandaki ta kulle kofa. Ya aje tuwon ya je bakin kofa yana
fadin, “Don Allah Salma ki bude mu yi magana.
Ina sonki Salma, ke kadai ce matsala ta yanzu
bana bacci”Salma ba ta tanka ba, kuma ba ta bude ba.Kaka kuwa tana can ta cika dam tana jiran Shatima ya wuce su kwashe ta da Salma, don zatonta Salmar ta shantake ne suna hira, shi ya sa ma ta ji shi shiru.Ta ce,Maryama zo ki kama ni mu je daki, ita kuma ta fito ta bi shi”
Suna shiga ta ganshi tsaye kofar bandaki,
ya ce, “Kaka ki sa baki don Allah, duk tsawon
zaman nan ta shige bandaki
Kaka ta Ce,Maryama kai tuwon nan
kicin Ta dube shi,Don Allah ka tafi, mu
kwanciya za mu yi Ya ce, In dai ba ta fito ba sai dai in kwana nan Kaka dai ta ga da gaske yake yi, ta ce,To fita ka kwanta a falo” Ya ce,
“Kaka don Allah ki mata magana”Kaka ta Ce,
“Ka je dare na yi, sai in ka sake dawowa
Da kyar Kaka ta lallaba shi ya tafi, Salma
ta fito ta ci kuka, Kaka ta ce,Kukan na mene
ne? in sonsa ki ke me ya hana ki bi shi?”
Salma ta ce,Ni ya rabu da nine kawai”*
Kaka ta ce,Babu batun rabuwa, amma ki
tabbatar yana sonki da gaske Salma ta share hawaye,Ni ban san yazan yi in gane yana sona da gaske ba Kaka tace,Zauna ki bani aron
hankalinki nan”. Ta zauna tare da lankwashe kafafu kamar mai zaman cin tuwo, ta ce,
“‘Salamatu, ke fa mace ce kuma yar zamani, har sai ni tsohuwa zan koya miki yanda za ki fahimci mijinki na sonki?” Salma ta ce, “Kaka ba ga shi ba duk da ina yar zamanin sai ke ki ka koya min zama da kunshi, zama da kamshi, girki na musamman a ranar juma°a kitso akan kari, yin girkin gargajiya da sauransu?” Kaka ta ce,
“Ai mu duk juma’a za ka yi lalle da kitso. Abinci na musamman maigida in yazo sai kawo ma matarshi turare, har da
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe