RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Tana jin Titarshi ta taho sadaf! Sadaf!! Ta

leka ta windo, sashen Salma ya nufa. Tamkar ta fita ta bi shi, amma tana tsoron kada ta fita shi kuma ya juyo. Dole ta daure taci

gaba da tsayuwa a gurin. Yana shiga ba ta falon, ya shiga dakin ta bata,nan karshe dai ya duba ko’ina amma ba ta babu dalilinta, cikin sauri ya fito ya nufi gurin maigadi. Ya ce,

“Baba, Salma ta fita ne?”Ya ce, “Gaskiya ban ga fitar kowa ba

Shatima cikin mamaki ya sake shiga ya

duba ko’ina, sai lokacin ya lura babu akwatin daya ga ta dauko, kuma babu jakar hannunta. Ya fito ya nufi dakin Aliya, cikin sauri ta juya da

gudu ta koma gurin danta da yake ta kuka, amma saboda leken gulma ta kasa zuwa gurinsa. Ya dauki wayarsa a caji ya zauna a falo layin yayan Salma Auwal ya kira, suka gaisa, yaCE,

“Ka yi hakuri na kira ka da daddare

Auwal ya ce,Ai daren ma bai yi ba”.

Shatima ya ce,Salma ta zo?”

Auwal ya ce, Yanzun nan na zo na samu

gida a rufe, na zo Inna ke fada min zuwanta tun dazu, amma dai ta kore ta. Ina zaton tana hanyar dawowa Shatima ya ce,

ya yi mata kyau” Auwal ya ce,

“Ai na so in same ta, da sai

na mata dukan tsiya, don Allah ka yi hakuri”

Shatima ya ce, Sai da safe ka ce, ina

gaida Inna Aliya ta yi murmushi,

“An kai ga yaji kenan, bari ya zo mu ji, ai sai naji kan zancen

Shatima ya kasa shiga daki, ya zauna

zaman jiran dawowar Salma. Har ya soma

gyangyada karfe dayan dare ta buga, Shatima ya tsorata kar dai yarinyar nan ta fada mugun hannu garin rashin jinta. Aliya ta fito ta same shi yana kai-kawo. Tace Wai lafiya?”Ya ce,

“Salma ce wallahi, ta kama ta tafi

Zaria da daren nan”. ilAliya ta ce,

“To ba sai ka yi kwanciyarka

‘ ba? Ai na san tuni ta je”Ya ce,

“Na kira an ce ta taho”Aliya ta zaro ido,

“To ita me ya kai ta Zaria da daren nan? Yarinyar nan kuwa ba ta da

aljanu?”Shatima ya ce,

“Nima na soma tunanin haka, tunda na zo na ga ta shirge kaya guri guda

a falo. Yanzu ko ina kuma ta yi? Oho!”Aliya ta ce, “Allah ya sa ba aljanun ba ne

suka yi wani gurin da ita. Sai dai kuma in dai sune ba za su bari wani ya cutar da ita ba”

Shatima ya kalli Aliya da son jin karin bayani

. Aliya ta ce,Za su tsare ta, ai suna

haka” Shatima ya ce, In ko haka ne na cutar da ita, don na dake ta Dariya ta so kwace wa Aliya, ta yi saurin maida dariyar hamma, sannan ta ce,« Amma ba ka kyauta ba Ta kama shi, “Mu je ciki ka dan kwanta,

insha Allah tana cikin kulawa. Kuma Allah ya bata lafiya’Dalilin jimawar da ya yi a daren ya sa yana yin sallar asubahi bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.Karfe shida daidai Hajiya Kaka ta ce da Maryama ta kira mata Hajiyan Shatima a waya.Hajiyar tana lazimi kiran ya shigo, cikin sauri ta dauka tana fadin,

“Ba dai ba ce da jikin?”

Sai ko ga Hajiya Kaka, da sauri ta daga

“‘a Maryama ta gaida ta, sannan ta mika ma Hajiya Abu Kaka. Suka gaisa, sannan ta ce,

“Ina son ku zo ke da mijinki da safen nan”

Hajiya ta ce,Lafiya, ba dai jikin ba?” Kaka tace, Ba jiki ba ne, in kun zo za kuji’ Bakwai da mintuna Alhaji suka shigo. Sun samu su Hajiyan a falo tana sauraron radiyo. Sun

zauna duk sun gaida ta cikin girmamawa, sannan ta ce,

“Maryama turo min Salamatu’ Ta ce,

“To”Su dai sun yi shiru suna son su ji me yake

faruwa? Salma ta fito ta zo ta durkusa gabansu sannan ta gaida su. Suka amsa duk da Hajiyan Shatima can Kasan makoshi ta amsa. Hajiya ta ce,Salma, dago kanki”

Ta dago, Kaka ta ce, Ku kalli fuskar yarinyar nan’A lhaji cikin sauri ya ce,

“Subhanallah! Me ya same ta haka?”Kaka ta ce,Shatima ne wai ya ware Karfi

babu ko kunya ya daki ‘yar wannan yarinyar, har ya kai ga mata wannan raunin. Su kuma iyayenta da yake mutanen da ne sai suka kora ta wai ta koma gidansa da dare fa jiya ta zo nan kusan goma. Ai ni na ga shirmensu, ai ba a haka sam. Mazan yanzun ne za su koro min

*ya sannan nima in kora ta, bare ta zo da wannan fuska suntum”Alhaji cikin takaici yace,

“To shi Shatima shaye-shaye ya fara da zai mata wannan duka babu wani dalili?”

Kaka ta ce,Ai ko da dalili dukan mace,

ba tsarin tarbiyyar gidan nan ba ce. Amma bansan bangaren Hajiyarsa ba Hajiya ta ce,

“A’a, mu ma dai kaf din mazan gidanmu ba dai a ce wani ya daki matarsa ba. Amma an binciki dalili kuwa?”Kaka ta ce,Ban bincika ba, yanzu dai sai ku bincika ku tunda iyayensa ne Alhaji ya dubi Salma,Me ya hada ku?”Salma cikin zubar hawaye, ta ce,Shi ne

yake ta fada wa mutane wai ba ya sona. Ni kuma na ce kawai ya sake ni tunda ba ya sona, shi ne ya kama ni da duka, ya mare ni har a baki”Alhaji yace,Wannan zance haka ne

babu karya a cikinsa Hajiya ta ce,

“Ni kuma zan so a ji ta bakinsa tukunna,

domin ko don haka aka yi alkali’ Alhaji ya ce, “Ai in ba ki manta ba ya taba

fadi a gabanmu cewa taimakon yarinyar nan yayi, ba sonta yake ba. Ni ma ban ga laifinta ba don ta ce ya sake ta”Hajiya ta ce,

**Aikin asiri ne, kuma in ya karye dole a ga ba daidai ba. Ai gara ma ya saketa, ni na fi son hakan ma’Kaka ta ce, Da kanki Hajiya Amina ki ke wannan maganar? Da kanki?” Hajiya ta ce,To gani na yi ita ma ta nemi sakin ko?” Kaka ta ce,Amma dai kin san wannan maganar bata dace ga maida ita a wani guri ba ko?

Ina miki kashedi ku ne dai iyayensu mu namu

shawara ce, amma game da zancen wannan

yarinya ina son kai Alhaji ka kira Shatima yazo,

dalilin wannan duka nike son sani. Daga baya ayi sauran zance, kuma sai ka dauke ta ku kai ta asibiti” Nan fa fuskar ta sace a bisa jiya da tazo suntum har da busasshen jini. Alhaji yace,

“Insha Allahu zan kira shi, ke kuma tashi mu je a duba ki Hajiya tace,Kaka, Allah ya huci zuciyarki, nima zan masa fada Kaka ta ce,

“Ya dai kamata”A cikin mota, Salma tana baya zaune, Hajiya tana gaba tana ta surutu, ita gara Shatima

ya saki Salma, ban da ma Salmar butulu ce duk hidimar da yake musu don ya dake ta har ta wani zo kawo Kara? Alhaji ya katse ta da cewa,Hajiya Amina in ba ki yi min shiru ba gaskiya zan tsaya a nan ki sauka”

Dolenta ta yi shiru don ta san Karamin aikinsane.An duba Salma, an ba ta magunguna,sannan suka maida ta gida. Har ciki Alhaji ya kai ta, ya kuma yi wa Hajiya alkawarin kiran Shatima.

Ya fito wanka daidai lokacin sha daya da

wani abu kiran Alhajinsa ya shigo. Ya gaida su

cikin girmamawa, sannan Alhaji ya ce,

“Lallai yana son ganinshi da azahar. Shatima ya ce,Dama yanzun nike shirin zuwa Zaria din

Suka yi sallama akan cewa sai ya zo.Shatima ya kalli Aliya wadda ta gama shirin

tafiya gurin aiki, tana jiran ya sauke ta.

Ya ce,Ko dai Salma ta je gurin su Alhaji

ne? ya ce wai yana nemana yanzun nan”

Aliya ta ce,Ko kuma aljanun sun ingiza

ta can ba”Ya ce,To bari in je dai in ji”.

Ta Ce,Kyau kafin ka kai can ka samu

mai rukiyya Shatima ya ce,Ina zan samu wani mai rukiyya kuma?”Ta ce,

“Munnir za kai ma bayani kan ka

zo zai sama maka, idan an yi mata karatu sai su fita in Allah ya taimake ta Shatima bai Ki ba, ya kira Munnir suka gaisa. Ya ce,

“Abokina an samu matsala ne, jiya

Salma ta taho gida. Ashe kuma aljanu ne daga

baya muka gane hakan, shine zan shigo Zari’ yanzun na ce ko za ka binkita mana wanda zai

mata karatu kafin na shigo?”Munir yace,

“Subhanallahi, Allah ya kyauta. Zan yi wa Fatima magana kaninsu yana

yi domin har shagon islami yana da shi”

Shatima ya ce,Yauwa, to sai na iso”.

Bayan tafiyar Shatima Aliya ta yi ta

kwasan dariya, wai ta jona ma Salma hauka.

Shatima ya samu Alhajinsu gida, bayan

sun gaisa ne kafin Alhajin ya soma maganar

Hajiya ta tashi ta yi dakinta.

Alhaji ya dubi Shatima ya ce,

“Yanzun saboda Allah abin da kayi daidai ka yi kenan? Ka ware karfi ka jibgi yarinya karama, duk ka ji mata ciwo haka sai kace hatsarin

mota? Ni da naganta na yi tsammanin

mota ce ta fadi da ita. Gaskiya Babana ka bani kunya, ko da wasa ban zaci haka daga gare ka ba”Shatima ya ce,Alhaji, yanda ta yi min ne

ban san lokacin da na kai mata mari ba. Sai daga baya ma Aliya ta ke fada min cewa, aljanu ne suke damunta. Munnir zai zo da wanda zai mata karatu”Alhaji ya ce,

“Ban gane aljanu ba?” Shatima ya ce,

“Zage-zage ta ke yi tun

kwanaki uku da suka wuce, kuma ta hada duk

kayan dakinta a falo. Alamu dai ga su nan”.

Alhaji ya ce,Aj tana can gidan Kaka”.

Shatima ya ce, to bari su je su tafi da mai

karatun. Alhaji ya yi masa fada sosai tare da

gargadin kar ya kuma jin haka.Hajiya tana jiran ya same ta a nata dakin

ne ta bayyanar masa da nata ra’ayin, sai kawai ta ji tashin motarsa, Yana daukan su Munnir din ya ji  wayarsa na ruri, Hajiya ce take kira. Ya daga, Tace,

“Waton ban isa ka shigo gurina mu gaisa ba

ko? Yace Ba haka ba ne, yanzun zan dawo,

Munnir suna jirana ne”Salma tana bacci lokacin da suka shiga,

Hajiya Kaka ta yi gum da fuska tamkar ba ta taba dariya ba. Hakan ya tabbatar ma Shatima lallai tayi matukar fushi. A ciki ta amsa gaisuwar tasu,Shatima ya soma yi mata

bayani,ya nuna Khamis mai rukiya,

Malami ne zai yi wa Salma karatu”

Kaka ta dube shi, “Karatu? Aljani ne a

kanta?”Shatima ya ce,

“E Kaka, aljanu ne”. Ta ce,

“Lallai kuwa, ka kai karshe a rashin

son yarinyar nan tunda har hauka kake son

dora mata Malamin yace,Hajiya, aljanu ai

ba hauka bane, cire.Ta daga mishi hannu,

“Dakata kai yaro,kai ne mai karatun?”

Ya ce, “Ni ne”.Hajiya ta ce,

“Tashi ka je abinka, ba ta da

koma• Ta kalli Shatima,Ka ba ta takardarta

Shatima ya dubi Hajiya,Ban gane in bata takardarta ba?”Hajiya ta ce,

“To, tashi ka je ubanka zai

maka bayani yanda za ka gane”.Munnir ya ce,

“Hajiya, a yi haQuri da kin

bari an fara yi mata karatun tukunna”

Hajiya ta ce Muniru ya fada maka abin

da ya faru?”Munnir ya ce,

“Ba mu yi cikakken bayaniba” Ta Ce,

«To shi kenan ku je ya yi maka

bayani kawai”Munnir ya ce,Ina Salmar ta ke?”‘Hajiya ta ce,

“Alhaji nasa ya zo ya kai ta

asibiti sun mata allura tana bacci. Dukan daya

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *