RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 9 BY HALIMA K/MASHI

 

Haka ta yi ta bai wa Nafisa shawarwari, har dai Nafisar ta sauko, amma duk da haka dole

ta dauki mataki. Shatima kuwa yawo ya yi

ta yi da yaranshi, su shiga nan su fita can. Guraren shakatawa. Lokacin sallah suka je

masallaci, sannan suka je gidan cin abinci suka ci suka yi dam! Bai nufo gida ba sai sha daya lokacin yaran sun yi barci. A dakinshi ya kwantar da yaran  suka kwana. Da safe ya shiga shirin tafiya aiki, ta zo ta kwashi yaran don shirya su zuwa makaranta, kamar yanda suka saba tare suka karya amma ita ba ta zauna ba. Ya fita da yaran don kai su makaranta, sannan ya wuce nashi

gurin aikin.

Salma ta warke sarai, sai dai tana ji tana

gani aka yi bikin Auwal Inna ta ce karta ganta

matsawar ba ta koma gidanta ba. Hadiza ta aiko lokacin da Hadizar ta zo karbar kudin hannun Salma da ta ce ta zo ta amsa don hidimomin na bikin. Ta ci gaba da zuwa makarantarta daga gidan Kaka, a ranar da ta cika kwana biyar da zuwa gidan. Kaka ta ce, kar ta damu, ta kwantar da hankalinta ta ga yanda za su kwashe da Shatiman. Ranar asabar ya iso Kaduna, kwana daya

zai yi don ba ya son matsala. Ya ji dadin tarbar

da ya samu daga Aliya tare da kwantar masa da hankali, gami kuma da lallashinsa kan kar ya damu da tuhumar da matansa suke masa.

Ya shiga gurin Amna da safe, bai zaci zai

samu kallon mutunci ba, amma sai ya ga sun

gaisa cikin mutunci kamar yanda suka saba. Tare da shi suka fita kai Jaffar hadda.

Sun dawo ta ce,Baban Jafar ina son ka

fada min gaskiya, ba ka taba yi min zancen da ba gaskiya ba ne, kuma zan yarda da duk abin da ka fda min. haka kuma in ma ka aikata laifin zan iyayi maka uzuri sakamakon gaskiyarka da kuma kasancewarka sabo a cikin laifin Shatima ya kama hannun Amna ya matse cikin nashi tafin hannun, Na yi miki alkawarin cewa, zan fada miki gaskya a kan abin da na Sani Amna ta tsura mishi ido kamar mai son ta gane gaskiyarsa a cikin idanunsa, ta ce, Menene gaskiya game da yarinyar da Nafisa ta kira ni ta ce min kana nema da lalata, kuma wai ka yi alkawarin sakin daya daga cikinmu don ka maye

gurbnta? Shatima ya yi rantsuwa da girman Allah, har sau uku sannan ya ce bai san komai game da maganar ba. Bai san ina maganar ta fito ba. Amna ta ce,To ni dai Nafisa ta kira ni,

Aliya kuma ta sake tabbatar min da maganar har ta fada min cewa, Salma ka ke son ka saki don ka dake ta, kuma ka kore ta Shatima ya zaro ido,Aliya kuma? Ai ita da tace ba ta san wannan maganar ba Amna ta ce, “Gaskiya ta sani, don mun yi maganar da ita”Ran shatima ya baci amma zai mata magana, ya ce,

“To gaskiya matsala ta da Salma

daban ce, ita tuhumar da take min daban ce, bata, shafi wata ba. Rashin kunya kuma ta min na dake ta Amna taCe, To ita Nafisa ina ta ji

wannan maganar? Ya kamata ku zauna ta fada maka inda ta ji don ka gano bakin zaren”

Shatima ya ce; Gano bakin zaren kuwa

shine zai warware wannan kullin? Amna ta ce,

“Haka ne Shatima mamaki yake wai Aliya ta san da zancen nan? Me ya sa ta nuna ba ta sani ba? Me ya sa ta kafa ma Amna hujja da Salma? Gaskiya yana son ya san dalilinta. Ya samu Aliyar har kicin dinta tana shirya

“abincin rana, ya ce, Aliya ashe kin san maganar nan ki ka nuna min ba ki sani ba sam-sam?”In ji wa?” Aliyar ta tabamya cikin tsananin faduwar gaba.” ya ce,Amna ta fada min kin sani, harma ta fada min kin nuna mata dakin Salma tare da ba ta labarin matsalarmu, sai dai kin danganta matsalarmu da Salma a cikin wannan matsalar a kokarin gamsar da ita cewa na aikata”Aliya ta sóma kuka, “Yanzun ka yarda da abin da aka ce maka a kaina? Ina ce tsakaninmu akwai amincin da in ka ji abu za ka yarda kuma ka tantance na yi ko ban yi ba?Ta nufi falo,Yasha gabanta Ya riko ta zuwa jikinshi, *A a maganar bata kai haka ba. Ina mamaki ne musamman da yake na san Amna ba ta iya’ karya ba. Ba ta da rufa-rufa sak! Take Aliye ta ce,kenan ka yarda na fada?” Ta

kama kici-kici, “Mu je kawai? na tambayeta a inda na fada mata Ya ce, “*Amma dai na ce abar maganar ko?” Ya sake ta, «Tunda ke ma taurin kan za ki koya, je ki same ta” Aliya ta dawo ta ci gaba da aiki tana sharar kwalla. Shi ko Shatima wata alama ya dora yana ta auna zancen Amna da Aliya. Sam bai yi niyyar zuwa Zaria ba, haka nan ya kira Alhajinsa sun gaisa ya bada uzurin ba zai zuwa Zaria ba. Alhajin ya ce,Babu komai, ya ya batun matarka?”

-Shatima ya ce,Wai Salma?”Alhaji ya ce,

“Ita”Shatima ya ce,Na bari ne Hajiya Kaka ta

huce sannan inje mu yi magana Alhaji ya ce,

“‘Shikenan”Yana hanyar komawa Abuja Hajiyarsa ta kira shi, cikin faduwar gaba Shatima ya daga. Ta Ce,Tunda ka guje ni don nace ka saki wannan annobar yarinyar shine ka dauki gaba dani?’Ya ce,

“Hajiya, don Allah ki yi hakuri zan

kira ki, kwana biyu aiki sun min yawa ne

Ta ce,Aiki sun maka yawa ko kuwa

sharrin matanka? Ina son ka sani kuma matan

naka su sani zan sa kafar wando da kowaccensu.Ina sane da duk abin da ke faruwa a gidanka daga can Abujar har Kadunar, kuma ina son ka zama namiji tsayayye kamar yanda na sanka ba soko ba

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *