RANA DAYA CHAPTER 15 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Ya ce “Iso mana, sauri nake yi.” Ta durkusa ta gaida shi, ya ce “Mike muyi magana.” tashi. Ya ciro katuna daga mota ya mika mata. “Ta
“Na daurin aure ne kawai babu na dinner. Sannan ya bata dubu talatin “Wannan koda za ki yi walima da kawayenki.”
Ta ce “Sun yi yawa Yaya.” Ya ce, “Haka na ba sauran.” Ta kalle shi zata sake magana ya ce, “Ki je gida ina sauri ne naga bakinki da magana, lokacin yinta yana zuwa amma ban da yau.

Bai saurari abin da zata ce ba ya shiga mota, ta juya ta shiga gida.
Biki saura sati daya aka je aka yi wa Nafisa jere itama. Aliya kuma washegari ana saura kwana shida. Duk kowace an yi mata bakin rabonta.
Nafisa itama dakunan nan an zuba gadaje, sannan kicin da falo suma an yi babu laifi, don yafi na Aliya tsada ita gado biyu ne, dayan dakin aka sa katifa.
Amma duk ba wadda ta kama kafar Amna. Ita ko Salma daidai wannan lokacin suna can Www.bankinhausanovels.com.ng
suna ta ganganda yanda za a sai kaya. Gidan Gaje Dillaliya suka je in da suka samu gado da kujeru na hannu aka sake musu feshi, sai suka sai sabuwar kati fa da zannuwan gado.
Sai kuma kayan girki abin da ba a rasa ba. Suna dan matsewa ne don su samu na siyan gara. Don ma Salma ta ba da kudinta na walima, ta ce ba zata yi walima ba tunda Babanta bai dade da rasuwa ba, babu wani taro da zata yi.


A son Amna tun Laraba yaje mata, amma ya bata uzirin nasa shirye-shiryen da abokansa, ya
ce tayi hakuri sai Alhamis zai zo ya kai har Asabar ya dawo saboda zata yi abubuwa da dama, ya dai halarci biyu. Ta ce, “To, babu komai.”
Ko’ina ya kacame da shirin biki ba sauki. Ana ta shirya Amare ban da Salma, wadda tsimi kawai Yaya Hadiza ta bata, sai ci da kaza wadda ba a kawo ba ma.
Su ko can Amna sai da tayi sati daya a gidan mai gyaran jiki. Haka- Nafisa har gida kullum mai gyara ke zuwa. Aliya ma dai ana ta dilka. Wata kawarta ke mata, saboda Amna aka maida daurin aure Lahadi, don su Kano sun fi daura aure ranar Lahadi.
Tun Laraba suka fara da bikin gargajiya. Amna tasha kyau da kawayenta, washegari Alhamis suka yi ranar Larabawa, sun sha kyau ita da shi cikin shigar Larabawa.
Haka abokansa sun je da yawa. Nan hotuna suka shiga zaga duniyar sama ana ta watsa su. Washegari Juma’a aka yi ranar Turawa.
Sun fi kullum kyau don kayan da yasa a gidan su Amna aka sai masa. Bai ma san da su ba sai da aka kawo masa. Motar da aka dauke su sabuwa ce dal, an ce kyauta Babanta ya basu an jera mata balan-balan, gata mai tsada. bashi.
Washegari Asabar yasa su taho da safe, amma ta roke shi ya bari sai da yamma saboda za suyi Kumbo. Can Zaria ma sun shirya kumbo din, kuma suna sa ran zai zo.
Sai dai ita Nafisa bata so wannan kumbon ba dan sam bata gayyaci kowa ba, sai sauran sa’anninta na cikin dangi su ne suka raba katin, kuma suke shirya komai. Ko kudin da ta ki amsa Hafsa ce ‘yar gidan Www.bankinhausanovels.com.ng
Anty Saude ta kira shi ya turo musu. Abin da ya
kara ma Nafisa takaici yanda hotunan shagalin
su da Amna yake ta ratsa wayoyin dangi ana ta labari.
Bai baro Kano ba sai taran dare shi da tawagarsa. Ya shiga yayi wanka lokacin sha daya daidai.
Yana kwanciya sako yana shigowa wayarsa. Shahida ce daya daga cikin ‘ya’yan kanin Alhajinshi, tana nuna mishi rashin jin dadinsu da yanda ya wofintar da nasu shagalin bai zo ba, ga kujerarshi nan babu kowa har aka tashi.
Bái tura mata amsa ba duk da yana da amsar maganar, kuma ko yana gari bai zuwa. Ya fasa kwanciya ya sakko zuwa falon Hajiya, yana son yayi magana da Alhaji don a kasa daurin auren domin Kano na safe suke yi.
Daidai kofar dakin Hajiya suna tsaye ita da Hajiya Azimi, tana cewa. “Babbar matsalata yanzun na ce miki wannan
yarinyar da ya kutsota daga karshe. Nayi-nayi
Alhaji ya daure masa gindi. Babu wani binciken asali ba komai, sai ka ce wani mara hankali. Kuma yanda na samu labari an ce matsiyata ne na karshe, kuma an ce kudi yake kashe musu na tsiya.
Don haka ina son gobe kafin auran tunda
unguwarku ce ki bincika min komai game da su,
ni kuma ina son duk yanda za’ayi in hana wannan daurin auran.
Yaron nan ba shi da hankali, an fada mishi da kowane gama-gari ka ke hada zuri’a, bare matsiyatan tilis.”
Hajiya Azumi ta ce, “In don wannanne kar ki damu, ni da naji kin ce komai dare in na dawo in zo har na tsorata, nayi zaton ko wata gagarimar matsala ce. Ki kwantar da hankalinki, gobe tun safe zan fita da kaina in samo miki komai kafin goman safiya labarinsu ya nuna a gurinki.”
Hajiya ta ce, “Ai ko kina da tukwici mai tsoka, na gode Allah Ya kara zumunci. Shi yasa na ce ki zo.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Shatima ya koma cikin mamaki, sam bai zaci Hajiyarshi tana da irin wannan mugun tunani ba, domin yaga suna kokari gurin taimakon na kasa da tausayin marashi.
Ya zaci zata fi kowa murna in taji irin taimakon da ya shirya yi. Dama saboda talauci Hajiya ke gudun Salma?
Shi kam ya sha alwashi in dai yana raye bai mutu ba, duk irin abin da zai faru goben nan sai ya zama mijin Salma. Allah bà zai ba su Hajiya ikon rusa raya sunnar Manzonsa ba.
Tun da ya shiga dakinsa yake safa-da-marwa tare da tunanin yanda zai yi. Katin da suka buga na daurin auren kowanne da lokacin da suka saka. Na Amna sha dayan safe, na Aliya karfe daya bayan sallar Azahar.
Na Nafisa Rarfe biyu da rabi, na Salma Karfe uku da rabi, sai walima karfe hudu. Lallai Hajiya tana da ishasshen lokacin da zata tarwatsa komai. Ya zari makullin motarsa ya fita. Kai-tsaye gidan su Salma ya nufa. Sha daya da rabi daidai
lokacin su sun rufe gidan ma.
Ya kwankwasa kofar, ya jima yana kwankwasawa kafin ya ji takun tafiya. Muryar Auwal ya ji yana tambayar. “Waye?” Ya ce, “Ni ne Shatima, wanda zai auri Salma.”
Tsoro ya kama Auwal, kar dai mutumin nan fa mugu ne ta bakin Innarsu…ya ce, “Lafiya?” Shatima ya ce, “Lafiya lau, ka bude.”
Auwal ya bude cikin faduwar gaba da
addu’o’i a cikin zuciya. Shatima ya ce, “Yanzun
zamu iya samun waliyin Salma?”
Auwal ya ce, “To ban dai sani ba Allah yasa lafiya?” Shatima ya ce, “Ba an ce kanin Babanku ya bar ma aminin Babanku waliccin ba?’ Auwal ya ce, “Eh haka ne.” Shatima ya ce, “To muje mu duba.”
Auwal ya ce, “Amma Alhaji lafiya?” Ya ce, “Muje za ka ji.” Sun kwankwasa Allah yasa shigarsa ke nan gidan ya fito.
Shatima ya gaida shi, sannan ya gabatar da kanshi. Ya ce, “Alhaji lafiya?” Shatima ya ce,”Dama nazo ne saboda maganar daurin auren nan gobe, za a dawo da shi da safe saboda akwai wani daurin auran a Kano wanda za su tafi.”
Waliyin Salma ya ce, “Wannan ba wata matsala, Allah Ya kai mu.” Shatima ya ce, “Amin. Karfe takwas na safe.” Waliyin ya ce, “Gashi dare ya yi bare aje a sanar da shi kanin Mahaifin nasu. Kai Auwal gobe da sassafe sai kaje ka zo da shi.” Auwal ya ce, “Babu komai, Allah Ya kai mu.”
Suka koma, ya sauke Auwal a kofar gida, suka yi sallama. Sha biyu daidai ya koma gidan kamar ya shiga gu
rin Alhajinsu, sai kuma ya fasa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya daga wayarshi ya kira layin Alhajin. Bai zaci za’a daga ba, nufinshi ya bar missed call da asubahi yasan Alhajin zai neme shi.
Alhajin ya katse mishi tunani da cewa, “Ya ya dai Babana?” gaban Shatima ya fadi, da wata zuciyar ta ce mishi in kuma suna tare da Hajiya fa?
Cikin sauri Shatıma ya ce, “Dama ina son zamu yi wata magana ne, tunda ka shiga mu bari sai da Asubahi. Alhaji ya ce, “Ka gani ba za ka hana ni bacci ba, in ta sake-sake, fada min kowace magana ce.”
Ya ce, “To ko in sakko ne kawai don tun dazu ni ke nemanka.” Ya ce, “Eh sauko, ina can tare da su Alhaji Amadi sun zo daga Sokoto, masaukin bakin Alhaji Nadabo muka kaisu, su da su Alhaji Na Allah duk sun iso.
Shatima ya ce, “To gani nan.” Suka hadu a falo. Yayi ta waige-waige Alhaji ya ce, “Lafiya?” Shatima ya ce, “Bana son Hajiyarmu taji ne, don zata-ce komai sai in ce yarinyar nan.
Dama mun canza lokacin da zamu yi walima ne da abokanmu saboda akwai wadanda za su koma garuruwansu a goben shi ne muka dawo da walimar baya, sai muka maida daurin auren Salman na safe karfe takwas.”
Alhaji ya ce, “Babu damuwa, zan kira iyayen naka in fada musu, ana gama daurin auren natan sai a wuce Kano din kawai, tunda kila sai an kai tara a gurin ko ma fi.”
Shatima ya ce, “Haka ne. na gode Alhaji, Allah Ya kara girma.” Ya ce, “Babu komai, kaje ka kwanta, zama ka iya bacci kuwa yau?” Alhajin ya zolaye shi.Shatima yayi ‘yar dariya. Ya ce “Shi yasa na
baro masaukin abokaina nazo gida ko zan runtsa.” Ya ce, “To sai da safe.” Ya zauna bakin gado yayi shiru, gobe kamar yanzu ya zama Angon mata hudu, A fili ya ce Www.bankinhausanovels.com.ng
“Allah Kasa wannan abin da na shirya ya yiwu,
don ban san me Hajiyana ke shiryawa ba.” Idanunshi sun kasa runtsawa har kusan biyun dare, sai kawai yaga bari ya tashi yayi Ibada. Ya roki Allah sosai ya albarkaci auren nashi, ya ba shi ikon cinye jarabawar da ke cikin auran nashi, ya dora shi a kan matan nashi, ya kuma ba shi ikon sarrafa su.
Ya dauki wayarshi bayan ya idar ya sake karanta sakon Shahida, yayi shiru yana tunanin kila ‘yan’uwansa suji haushinsa tunda ita Nafisa ‘yar dangi, daga ‘ya’yan yayin Alhajinsu sai na kannenshi sa’anninta.
To bari kawai ya warware ma Shahida yanda suka yi da Nafisa kar su ci gaba da ganin laifinsa. Ya tura mata sako kamar haka:
Ki tambayi ita Nafisa yanda muka yi da ita. Ta ce min ba za ta gayyaci kowa ba a ranar da nazo in ji tsarinta, don haka ban san kuna da wanı bikin da ku ke son in zo ba.Ya tura mata.
Bugun kofarshi ne ya farkar da shi daga bacci, gashi har ya makara sallar Asubahi. Shida ya gani da ya kalli agogo.
Cikin sauri ya nufi kofa. Badi’atu ta ce
“Hajiya tana kiranka.” Ya ce “Ki ce na makara in nayi sallah zan zo.’ Www.bankinhausanovels.com.ng
Wanka ya fada, da ya fito yayi sallah tun daga lokacin ya fara nuna shi ango ne. Gizna ce ya sha fara sol sai aikinta mai ruwan kasa da ratsin gwal.Aka soka hula kube
takalmi. Turare kuwa yanda ka san zai yi
magana. Ya sakko suka hadu a falo.
Hajiya tana aiken Direbansu, ta tsaya tana kallonshi. Yayi mata kyau sosai. Ya ce, “Hajiya sannu da fitowa.” Ta ce, “Kai ne da sannu Ango, wannan irin wanka haka?”
Ya ce, “Ai karamin wanka ne wannan sai ma anjima.” Ta ce, “To zo muyi magana mana.” Dakinta suka shiga ta ce, “Naji Alhaji yana cewa wai za a daura aure da safen nan?”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *