RAWANIN TSIYA CHAPTER 1 BY FADEELAH
MALLAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT-KANO STATE
Zaune yake a cikin motar shi qirar BMW M340 baqa wuluk sannan sabuwa gal wadda ya faka a parking lot na airport din.
Babu abinda yake tashi a cikin motar sai wani asirtaccen qamshin da humidifier take fesowa wanda ya gauraye da sanyin AC ya bada wani yanayi mai dadin gaske.
Maganar gaskiya ita ce mamallakin motar nan ya kwana biyu yana hawan ta don haka ba wani abu ya janyo ake yi mata kallon sabunta ba, bala’in tsabta ne na mai ita. A yanzu haka da nake kallon interior na motar babu datti ko alama.. infact the car is spotlessly clean.
Magana yake yi a waya through CarPlay. It’s exactly 10:30am.
“…Yes Sir yanzu na karbi saqon” ya fada cikin muryar shi mai dadin ji wadda ga dukkan alamu zata yi tsada domin kuwa yadda yayi maganar zaka tabbatar ba mai yawan yin magana bane.
On the other side of the call ne na ji yace “toh ko dai zaka tafi gida ne abinka tunda na ga yau Saturday kana buqatar hutu plus bazaka rasa one or two things da kake son yi ba.. in yaso sai driver ya je ya dauko ta”
“No sir, it wont be necessary ai. Tunda ina nan din I can wait. Ba kace flight din su zai sauka by 11:00am ba?”
“Yes Son, 11:00am tace”
“it’s just a thirty minutes wait.. uhm, amma baka fadi mun sunan ta ba”
Dariya na ji mutumin yayi sannan yace “ban fadi maka ba ko kuma ka manta??”
“Sorry Sir na manta ne.. My bad”
“it’s okay Son.. Hanifa Aliyu Bugaje, shine full name dinta. Nima insha Allah zan biyo flight na gobe in dawo.. I am practically done here kuma ma garin ya ishe ni”
murmushi yayi yace “amma Sir, Milan is a great City fa”
“Yes it is but there is no place like home Son”
“Yes I agree with you Sir.. Allah ya dawo da kai lafiya”
“Ameen”
Bayan sunyi sallama ne yayi disconnecting call din sannan na ga ya shiga Note din wayar shi yayi rubutu kamar haka:
Hanifa Aliyu Bugaje..
Ni kuwa nace like seriously?? kenan ya rubuta sunan don kar ya manta??? is the name that hard to recall??? babbar magana!!
Yana disconnecting call din karatun Al-qur’ani cikin muryar Abdurrahman Sudais ya cigaba automatically… da alama abinda yake ji kenan before the call.
Gani nayi ya kwantar da seat dinshi yayinda ya kishingida yana jiran 11:00am.
***********
Wuraren qarfe Goma sha daya ne da minti uku jirgin su ya sauka. Yana zaune a cikin motar shi ya ji saukowar jirgin amma bai fita ba domin kuwa ya san ko ya fita sai ya jira saboda formalities da ake yi kafin arrivals din su fara shigowa don haka he chose to sit in the car and wait a little more..
Exactly 11:20am ina tsaye na ga ya bude qofar motar ya fito..
“Hasbuballabu wa ni’mal wakeel” abinda na fada kenan.
Wani kyakyawan gaske na gani. Dogo ne ba mai jiki ba. shi ba fari ba sannan ba baqi ba amma da ka kalli fatar shi babu abinda kake gani sai tsabar hutu… irin hutun nan da ake haifan mutum da shi. Gashin kan shi da fuskar shi baqi wuluk sun sha gyara sai qyalli suke yi.. in all dai wannan gayen ya hadu iya haduwa, tun daga gashin kanshi har zuwa yatsar qafar shi babu abin kushewa.. asali ma irin mazan nan ne wadanda idan ka kalle su zaka kasa dauke idanuwan ka daga kansu saboda kyau da kwarjini.
STORY CONTINUES BELOW
Sanye yake cikin wandon sweatpant black color da wata white Polo-shirt. Qafafuwan shi sanye cikin wani black designer slippers. Yana riqe da wayar shi sai wallet da makullin motar shi. Babu abinda yake bazawa sai qamshi na designer turare.. irin qamshin nan mai sanyi da dadin gaske.. Mai karatu the guy is dope because he is handsome, charming, good looking, classy and elegant.
Dayake ana cikin yanayi na Zafi ne tun da sassafe rana ta fito ta haske ko’ina qal.. yanzu haka tuni gari yayi zafi
Gani nayi yayi squeezing fuskar shi yayinda ya sa hannu ya kare ranar da ta daki gefen fuskar shi… da alama dai baya shiri da zafi.
Makullin motar ya danna yayinda motar tayi ‘yar qara sannan ya nufi bangaren arrivals na airport din.
Aikuwa tunda ya fito ‘yan matan da suke giftawa suka sa mishi idanuwa.. ba don komai ba sai don kyau da haduwa. Kai abin mamaki hatta wasu mazan ma sun bi shi da idanuwa saboda dai gayen ya hadu babu qarya…
Ko da ya shiga ya tarar babu mutane dayawa domin kuwa Yawancin mutane duk sun kama gaban su.. infact there are more people outside than on the inside.
At first tsayawa yayi yana kalle-kalle kamar wanda ya San wadda yake jira.
Sai kuma na ga ya dan girgiza kai yayinda ya nufi wurin masu rubuta sunan mutane suna dagawa saboda matafiyan su gane wanda ya zo daukar su.. it’s mostly done akan wadanda basu san wanda suka zo dauka ba.
Gani nayi sun gaisa da daya daga cikin mutanen sannan ya shiga Note na wayar shi ya duba inda yayi saving sunan ta sannan ya fadi mishi.
Nan da nan mutumin ya rubuta sannan ya daga board din sama.
Wayar shi ce tayi ringing yayinda yayi saurin dubawa.. Gani nayi yayi murmushi ya amsa tare da matsawa gefe yace “Good morning my dearest Naana.. how are you today???”
From his expression alone zaka gane cewar koma wacece ‘Naana’ she means alot to him..
********
Zaune take a kan daya daga cikin kujerun da suke arrivals din yayinda take latsa wayarta tana cika tana batsewa…
It’s been like twenty minutes da take zaune tana jiran wanda Paapa yace zai zo daukan ta.. da alama ta gaji da jiran already domin kuwa yanayin ta ya nuna hakan. Dukda tana cikin bacin rai bai hana ni ganin kyanta ba domin kuwa duk ‘yan matan da nake ta gani suna giftawa cikin airport din babu wadda ta kamo ta a wurin kyau.
Fara ce sol kamar tsaada.. dukda a zaune take na kula doguwa ce amma siririya. Kyakyawa ce sossai.. Babu make up a fuskarta, just her natural beauty which is breathtaking.
Sanye take cikin wandon blue Jean da white top daidai dan jikin nata.. Qafafuwan ta sanye cikin takalamin sneakers na mata mai masifar kyau. Hula ce a kanta yayinda na ga sweater da kuma wata qaramar jaka a gefen ta bisa kujerar.
Da alama dai qasar da ta baro sanyi akeyi sabanin nan din da ake zafi.
Dago kai da tayi ne ta ga mutumin riqe da board mai dauke da sunan ta.
Zaraf ta miqe tsaye… hakan ya qara bani damar ganin ta sossai. Tabbas ban yi qarya ba domin kuwa dukda tana sanye ne cikin kayan yahudawa ta bala’in yin kyau..
Gani nayi ta dauki jakarta ta rataya a bayan ta sannan ta dauki sweater dinta ta nufi wurin wanda yake riqe da board mai dauke da sunan ta din.
“Hey I am Hanifa.. who is here for me?” ta fada rai a bace.
Sauke board din yayi sannan ya nuna mata shi tsaye few inches away yana ta magana a waya.
Zaro idanuwa Hanifa tayi ganin wanda aka ce ya zo daukarta.. Gaba daya ma freezing tayi yayinda ta qura mishi idanuwa babu qyaftawa.
STORY CONTINUES BELOW
Da alama dai wannan gayen ya tafi da imanin Hanifa kamar yadda yake tafiya da na sauran Mata…
“how can this guy be a driver??? like how????” ta fada muryar ta qasa-qasa cike da mamaki.
Hanifa dai tayi spending a great part of her life a turai.. dukda bata associating kanta da mutane
bata taba ganin kyakyawa ba kamar mutumin da take kallo a yanzu a cikin dukkanin mutanen da ta taba haduwa dasu.
Bata san minti nawa ta kashe ba a tsaye tana checking din shi out har sai da wani official na airport din yace “Ma’am where are we taking your luggage??”
Ajiyar zuciya ta saki sannan tayi composing kanta tace mishi “wait” a wulaqance.
Gani nayi ta murtuke fuska ta qarasa wurin shi tace “how dare you keep me waiting??”
Cike da mamaki ya dago kai ya kalle ta tare da fadin “excuse me??”
Tsaki ta ja sannan tace “don wulaqanci an aiko ka don ka dauke ni sai ka koma gefe kana waya?? what nonsense…”
Ji nayi yace “Naana zan kira ki anjima.. I gotta go. I love you bye”
Bayan ya kashe wayan ne na ga ya ratsa ta gefen ta ya nufi wurin mutumin da ya daga board mai dauke da sunan Hanifa yayi mishi magana sannan na ga ya bude wallet dinshi ya ciro kudi ya bashi.. mutumin kuwa sai washe baki yake yi yana yi mishi magana shima.. da alama dai godiya yake yi mishi.
Hanifa wadda take tsaye bata ankara ba ta ga gayen ya juya ya fita ba tare da yayi sparing dinta a second glance ba… hakan kuwa ya bata mata rai sossai.
A duniyan nan babu wanda ya isa ya wulaqanta ta.. how dare he walk out on her yana matsayin driver. Don yana da kyau ya iya gayu?? he is still a driver and he has to respect her..
“I hate this guy, he has to go..” na ji ta fada yayinda ta bi bayan shi. shima mai riqe da trolley din nata ya bi bayanta.
*************
Zaune yake cikin motar shi yayinda ranshi yake a bace. Sossai yarinyar ta bata mishi rai.. shin ta san precious time dinshi da ya bata yana zaman jiranta?? how dare she talk to him like that??? banda don mutuncin da ke tsakanin shi da mahaifinta da ba qaramin gyara mata zama zai yi ba for what she did to him back there a cikin airport din domin kuwa a duniya babu abinda ya tsana irin ayi disrespecting dinshi a wulaqanta shi. tabbas a ganin shi na farko da ita ya tsane ta and God knows baya qaunar ya qara bude idanuwa ya ganta… he hopes this will be the last time he sees her..
Toh fa…
Hanifa ce ta qaraso wurin motar yayinda mutumin ya qarasa wurin boot zai sa trolley dinta. A bude kuwa ya tarar da boot din.. da alama dai an bude mishi ne. Bayan ya sa trolley din ne ya rufe sannan ya juya yayi tafiyar shi ba tare da ya bi ta kan Hanifa ba.. da alama shima ya kula marassa mutunci ce balle ma ya sa ran zata yi mishi ihsani.
Gani nayi ta tsaya kusa da motar kamar tana jiran wani abu.. can kuma sai ta bude baya ta gefen owner’s corner ta shiga.
Ulalaaaaaa… wani qamshi mai dadi ne ya daki hancin ta wanda har sai da ta lumshe idanuwa.
Da sauri tayi composing kanta sannan ta danna mishi harara tace “shine don ka raina ni bazaka iya bude mun qofa ba?? what does my dad pay you for?? is it not to serve us?? I swear I will make sure you go”
from his expression I could swear bai ma ji abinda take fadi ba domin kuwa gaba daya hankalin shi baya kanta.. all he wants is to drop her off and to never see her again.
***********
Suna tafe a kan hanya yayinda karatun Al-qur’ani mai girma yake tashi.. Hanifa sai satar kallon shi take yi ta front mirror yayinda take zabga mishi harara. Shi kuwa ko a jikin shi don bai ma san tana yi ba.
Tsaki ta ja sannan tace “don Allah Malam ka taka mota da kyau ka kai ni gida.. ka tsaya kana ta wani tafiya in slow motion. Baka san irin gajiyar da nayi bane???”
Ba tare da yace komai ba na ga yayi pulling off a gefen titi ya faka motar ya dauki wayar shi da wallet dinshi da kuma wani qaramin package wanda ya tabbatar mun da cewar saqon da ya je karba ne ya bude qofa ya fito.
Hanifa wadda ta cika da mamaki sai gani tayi ya tsaya a gefen titi kamar mai neman Taxi… aikuwa dai ba wai kama ba, Taxi din ya tsayar ya duqa yayi ma driver din magana sannan ya bude qofar baya ya shiga.
Gani nayi Hanifa ta saki baki galala tana kallon ikon Allah. Did he just leave her in the middle of nowhere???
Kallon gaban seat tayi ta ga makullin motar.. wato bar mata yayi ta kai kanta gida da kanta kenan???
“me wannan gayen yake nufi ne?? I swear to God he will pay for what he did to me” ta fada yayinda zuciyarta ke tafasa.
Washegari!!+
ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA- KANO
Wuraren qarfe takwas da rabi na dare Alhaji Aliyu Bugaje wanda aka fi sani da Paapa shine yake zaune a danqareren falon shi tare da matar shi Hajiya Binta wadda aka fi sani da Mamy.
A yau lahadi ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa qasar Italy har tsawon kwana bakwai- he actually went on a business trip.
Kusan awa hudu kenan da dawowar shi amma bai ga ‘yar lelen shi ba.
Dayake a gajiye ya dawo sai da yayi wanka yayi salloli ya ci abinci sannan ya huta.
A yanzu haka yana zaune da matar tashi ne suna kallon News yayinda suke hira..
“wai ina Baby ne ban ganta ba tunda na dawo?? ko bata gida ne??” ya tambayi Mamy.
Mamy dai tunda Hanifa ta dawo jiya suka hadu sau daya bata qara ganin ta ba.. a yadda ta gan ta ma ta tabbatar akwai matsala don kuwa tun da ta shigo gidan take ta yi ma masu aiki masifa da fada na babu gaida babu dalili. Toh kuma dama dai idan har tana gidan haka zaman nasu yake, babu mai shiga sabgar wani… saboda dai Hanifa ba yarinya bace mai mutunci.. idan baka riqe girman ka ba duk shekarun ka sai ta karta maka rashin mutunci ta wulaqanta ka a banza don haka ne ma Mamy bata shiga harkar ta ko alama.2
Tabe fuska tayi sannan tace “tana nan.. tun da ta shigo jiya ban qara ganin ta ba”
Murmushi yayi sannan ya dauki wayar shi yana dialing lambar ta yayinda yace “Ni na rasa yaushe zan gan ki tare da Hanifa zaune a wuri daya kuna hira kamar yadda kowacce uwa take yi da ‘yarta”
Murmushi kawai Mamy tayi bata ce komai ba domin kuwa ta sani cewar hakan ba abu bane mai yiwuwa.
“Hello Babyna where are you ga Paapa ya dawo bai gan ki ba??”
Shiru ya dan yi sannan yayi murmushi yace “Yes I am back my Baby, ina falona”
Daga nan ya kashe waya yana murmushi yace “gata nan zuwa amma fa daga jin muryar ta na tabbatar an taba mun ita… bari dai ta zo mu ji”
Mamy dai tana mamakin yadda Paapa ya sangarta Hanifa haka.. Gaba daya yarinyar bata ganin kowa da daraja dukda yawancin iya shegen da take yi ba a gaban shi bane don haka baya sani amma ai still akwai wasu abubuwan da take yi a gaban shi wadanda yakamata ya dinga tsawata mata but sai kawai yayi over looking…3
Hanifa ce ta shigo falon sanye cikin wata rigar bacci in and out pink color. Ta cikin dai gajera ce wadda ta tsaya a gwiwarta sai kuma ta saman wadda take kamar robe doguwa ce har tana jan qasa.. tana sanye da takalmi mai laushin gaske shima pink.. da alama hade yake da rigar baccin. Fuskar ta fayau.. Gashin kanta dogo baqi qirin ya kwanta a kafadarta da bayan ta gwanin ban sha’awa.
In all she looked very beautiful.
Cike da shagwaba ta qarasa wurin Paa
pan nata ta zauna a gefen shi in between shi da Mamy ta kwanta slightly a jikin shi tayi hugging dinshi very tight tace “Oyoyo Paapa… I missed you very much”
Yana rungume da ita yana shafa kanta yace “I missed you too Baby.. how have you been?? ya examz?? yanzu dai finally kin gama da Oxford ko??”
“Yes Paapa.. Na gama da Oxford”
“toh masha Allah Baby.. welcome back”
“thank you Paapa”
“so tell me ya kike.. what have you been doing tunda kika dawo??”
STORY CONTINUES BELOW
“I am fine Paapa.. I’m kinda bored but I am sure I will find something to keep me going..”
Gani nayi ta gyara zama tana kallon shi tace “amma fa Paapa ina da complain akan driver din da ka aiko jiya ya dauke ni daga airport. Wallahi Paapa he is rude and very disrespectful.. Ni kawai ka kore shi don bana son shi..”
“Cike da mamaki Paapa yace “what?? me yayi miki??”
Mamy dai shiru tayi tana sauraron ikon Allah.
Daga nan dai Hanifa ta bashi labarin dukkanin abinda ya faru jiya tun daga lokacin da tayi arriving har zuwa lokacin da ya bar ta a kan hanya yayi tafiyar shi..
“Wallahi Paapa haka ya bar ni a hanyar Airport yayi tafiyar shi.. you know how much I hate to drive… I had no choice but to drive myself all the way.. sai ma ka gan shi yadda yake controlling motar kamar tashi.. meyasa ka bashi babbar mota yana driving dinta Paapa?? the guy is just so full of himself.. I hate him please just fire him”
Bata ankara ba ta ji Paapa ya fashe da dariya sossai wanda hatta Mamy sai da tayi murmushi tunda dai ta gane wanda Hanifa take qorafi a kai.3
“Paapa what’s funny???”
“Nothing Baby.. well, da farko dai ina so ki sani cewar ABUBAKAR SADIQ ba driver na bane.. infact he is a very special employee of the company and also, the very best.. He is the General and Finance Manager. Motar da ya bar miki ba tawa bace.. tashi ce, don haka gobe da safe sai kiyi qoqari ki sa a mayar mishi da motar shi..”
Hanifa dai tunda Paapa ya fara yi mata bayani ta cika da mamaki.. Kenan Paapa har ya samu someone he trusts da har ya bashi babban matsayi yake biyan shi salary that he is able to buy the damn car and dress so classy and elegant??? how??? kenan alot has changed and she isn’t aware???
“…actually Sadiq ya je Airport karban wani saqon shi ne shine na roqe shi alfarma akan ya dauko mun ke since your plane was to land within the time da yake airport din.. that was how it all happened”
Jikin Hanifa yayi sanyi sossai jin bayanin Paapa.. from the way da yake maganar Sadiq din da alama yana respecting gayen kenan..
“dukda haka Paapa, it doesn’t give him the right na ya wulaqanta ni.. he is your employee for crying out loud and I am your daughter. Gaskiya ni bana son shi”
“Baby listen to me.. i am sure abinda ya faru was just a misunderstanding.. na tabbatar when you get to know him better zaki fahimci cewar yaron bayada problem ko kadan.. infact he is one of the most down to earth people I have ever met in my life… so please ki kwantar da hankalin ki kin ji??”
Turo baki tayi tace “babu wani fahimtar shi da zanyi Paapa.. ni kawai bana son shi”1
Ta miqe tsaye tace “let me go and sleep.. na gaji sossai wallahi” ta duqo tayi mishi kiss a kumatu tace “Good night Paapa”
Yana murmushi yace “Good night Baby, try and get enough sleep”
“thank you Paapa” daga nan ta juya zata tafi yayinda ta jiyo muryar Paapa yace “baki ce ma Mamy good night ba.. that’s very bad”
Juyowa tayi tace “Good night Mamy”
Mamy wadda ta bi ta da idanuwa ce tace “Allah ya tashe mu lafiya Hanifa”
☆☆☆☆☆☆☆
Washegari!!
BUGAJE INDUSTRIES
KANO- CENTRAL
A yau Monday wuraren qarfe tara da rabi na safe Paapa yana zaune a executive ofis dinshi yana duba wasu reports a laptop dinshi.
Qwanqwaso qofar shi akayi sannan aka bude. Yana dago kai na ga yayi murmushi yace “Son”
STORY CONTINUES BELOW
Ko da na kalli wanda ya kira ‘Son’ din sai da nayi freezing a tsaye.. Lallai Allah ya zuba kyau a wurin wannan gayen.
Ba wani bane banda Sadiq!!
A yanzu ma da na gan shi sai na ga kamar ya qara kyau. Sanye yake cikin wani yadi fari sol mai laushin gaske wanda aka yi ma dinkin zamani irin wanda samari suke yayi a yanzu.. da ganin wannan yadin ka san ya ja kudi don kuwa dukkan alamu sun nuna hakan.. Kan shi babu hula wanda hakan ya bani damar ganin wannan gashin nashi mai kyan gani. In all the guy looked super handsome.
“Ina kwana Sir” ya fada tare da russunawa.
“Lafiya lau.. Zo ka zauna mana”
Sadiq ya qarasa ya zauna a daya daga cikin kujerun ofis din yayinda yace “ka dawo lafiya??”
“lafiya lau.. Ya fama da ofis?? na ga reports dinka ai, I am so much impressed… I am sure we will make something out of that Korean deal”
“Insha Allah Sir”
“driver ya kawo maka motar ka da safen nan?”
“Yes sir, he did”
“Uhm yes, na ji abinda ya faru tsakanin ka da Baby.. please kayi haquri da abubuwan da tayi maka”
Sadiq wanda bai fahimce shi bane yace “uhm sorry Sir, wa kake nufi??”
Paapa yayi murmushi sannan yace “my daughter Hanifa.. I call her Baby”
Gani nayi Sadiq ya dan bata rai sannan yace “it’s okay sir”
“ya maganar clients dinnan namu?? are they still interested in the deal??”
“Yes Sir, munyi meeting da su ranar Friday, sun ce zasu dawo jibi sai muyi finalizing deal din…”
“that’s good news Son.. Well done”
“thank you Sir”
Qofar ofis din suka ji an bude yayinda ta shigo tana fadin “Paapa wallahi ma’aikatan kamfanin nan naka sun raina ni sossai. Could you believe that security sai da ya bata mun lokaci sannan ya bude gate?? again, one of the receptionist had to look at me from head to toe sannan ta gaishe ni.. da zan shigo lift ma…”4
“Ssshhhh.. it’s okay my Baby, I will talk to them” Paapa ya fada yana murmushi. As usual duk lokacin da Hanifa ta fara yi mishi complains irin wadannan he always try to cut her off saboda ya san halinta na qoqarin neman fault akan duk wani abinda wani yayi.
Turo baki tayi ta qaraso wurin shi ta rungume shi btiefly tare da yi mishi kiss a kumatu tace “Paapa Good morning, yau ka tafi ofis baka neme ni ba.. not fair”
“kiyi haquri baby.. nayi tunanin kina ta bacci kina hutawa ne.. remember jiya kin ce kin gaji? I didn’t want to bother you”
“it’s okay Paapa.. kayi kyau as usual”
“kema kin yi kyau baby na amma baki rufe gashin ki gaba daya ba..”
Sanye take cikin wani pencil wando wanda bai qarasa kai qasa ba da wata farar top ‘yar qarama sai wata Kimono mai kyan gaske da ta dora a sama. Akwai light makeup a fuskarta wanda ya qara mata kyau sossai.. ta fito dai a first class babe dinta!
Turo baki ta dan yi sannan tace “na fa rufe Paapa.. ya kwance ne” Daga nan ta cire gyalen da ta yafa ta zare hair band din wanda yayi revealing dogon gashin ta mai bala’in kyau tana qoqarin daure shi da kyau.
Sadiq wanda yake zaune tunda ta shigo bai daga kai ya kalle ta ba.. kai gaba daya ma baya sauraron conversation din nasu.. asali ma wayar shi ya dauka yana latsawa.
Gani nayi ya miqe tsaye tare da fadin “Sir.. bari in koma office, akwai aikin da zan yi”
“Baby baki ga Sadiq bane??? won’t you greet him??” Paapa ya fada
STORY CONTINUES BELOW
Hanifa wadda take ta qoqarin daure gashin ta tace “Paapa na gan shi toh amma shima bai gaishe ni ba ai”1
For the first t
ime Sadiq ya daga kai ya kalle ta wanda yayi daidai da itama shi din take kallo..
Lallai yarinyar nan bata da hankali.. ya gaishe ta?? is she mad??? who the hell does she think she is da har ta cancanci ya gaishe ta???
Zuciyarta ce ta buga a dalilin kyan nan nashi da ya ruda ta.. toh amma kuma irin kallon da ta ga yayi mata ne ya bata mata rai.. wato dai ta ga alama Sadiq mugun dan rainin wayau ne.. babu wanda ya taba wulaqanta ta ya zauna lafiya don haka bazata taba bari ya zauna lafiya ba..
“da ke da shi waye babba?? come on greet him”
Ranta a bace tace “ina kwana”
Sadiq dai shiru yayi ba tare da yace komai ba… da alama dai gaisuwar ce bazai amsa ba.
Wayar shi ce tayi ringing.. da sauri ya duba wayar ya ga sunan qanwar shi Asma’u.
“excuse me sir” ya fada yayinda Paapa yace “Go ahead Sadiq”
Kafin ya fita daga ofis din ya amsa wayar yana fadin “Hey Mini-Me… how are you??”
Hanifa wadda ta bi shi da harara ce ta kalli Paapa tace “wallahi Paapa bana son gayen nan… don wulaqanci na gaishe shi bai amsa ba??”
“baki ga call yayi receiving ba??” Paapa ya fada yayinda ya cigaba da kallon reports dinshi.
“Wallahi Paapa ko da bai yi receiving call ba he didn’t intend to answer.. I just dont like him”
“kiyi mishi uzuri Baby.. I really want you to get along with him well because he is a nice person”
Gyalenta ta dauka ta yafa a kai sannan tace “kai kadai kake ganin shi a matsayin nice Paapa”
“Toh Baby Zauna ki fadi mun.. to what do I owe this visit?”
Hanifa ta zauna tare da fadin “dama zan je Shoprite ne shine nace bari in zo in gan ka..”
Gani nayi ya ture laptop dinshi gefe sannan ya kalle ta yace “nagode sossai Baby na.. thank God you are here.. Ya maganar fara aikin ki a kamfanin nan??”
Murmushi tayi tace “Paapa I really cant wait.. Babban buri na shine inyi aiki a kamfanin nan.. when do I start?”
“ina farin cikin jin haka daga gare ki Baby na.. zaki iya farawa anytime.. na tabbatar you will make a good manager kafin kiyi aure wanda idan mijin ki ya amince ki cigaba da aikin sai ki cigaba”
Turo baki tayi tace “Paapa ba yanzu zanyi aure ba…”
“what??? why??”
Cikin shagwaba tace “toh Paapa ni fa bani da saurayi kuma ka sani kuma ma fa I am just 22”
Murmushi yayi yace “yes na sani you are just 22 kuma na sani cewar baki da saurayi but I am sure Allah zai kawo miki na arziki kwanan nan…”
“still dai ba yanzu ba Paapa”
“toh shikenan Baby, Allah ya kai mu lokacin. Zan sa a buga maki offer letter dinki, zuwa Monday sai ki fara zuwa”
“Okay Paapa.. but I have a condition”
“What condition Baby??”
“Gaskiya bazan yi aiki under thesame roof da wannan gayen dan wulaqanci ba.. sai dai ka kore shi idan har kana so inyi aiki a kamfanin nan Paapa”1
“what??” Paapa ya fada confusedly.
“toh Paapa ni bana son shi”
Paapa ya saki ajiyar zuciya sannan ya tashi ya koma kujerar da take gefen wadda Hanifa take zaune ya zauna.. Gani nayi ya juyo da kujerar ta tana fuskantar shi sannan ya janyo hannun ta ya riqe tare da fadin “Baby saurare ni da kyau.. bazan iya korar Sadiq daga kamfanin nan ba..”
“what.. Paapa why??”
“Because he is very important to me, he is very good, he is a genius and trust me tunda nake ban taba haduwa da mutum mai qwalwa irin tashi ba.. Haquri zakiyi don kuwa a department dinshi nake so kiyi aiki, I need you to work closely with him saboda ki koyi wasu business tactics wanda ina mai tabbatar miki cewar zasuyi miki amfani nan gaba”
Hanifa dai shiru tayi tana tunani.. Ya za’ayi tayi aiki tare da mutumin da bata so?? does Paapa understand the level of hatred she has for the guy?? Ga dukkan alamu Paapa bazai kori Sadiq ba, haka kuma itama bazata yi forfeiting long term burin ta ba saboda shi don haka batada zabin da ya wuce ta amince in yaso idan ta fara aiki she will find a way to send him out.
“Shikenan Paapa” ta fada ranta a bace
Paapa ya fahimci bata so haka ba but how does he make her understand that Sadiq is untouchable a kamfanin?? For now, ya sa a ranshi when she gets to know him better zasu zama best of friends..!2