RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 10 BY Fateeyzah mbs✍️
Www.bankinhausanovels.com.ng
*_Marubuciyar_*
*_Gidan nagoggo_*
*_Doctor zahrah_*
*_Yakin Mata (aure)_*
*_Kuda wurin kwadayi_*
_Tukwicine ga daukacin matan jami’a_
*_ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ_*
Kallon da nayi ma Anisa bayan haihuwarta shine kallona da ita na k’arshe, har yau ban kuma sakata a ido ba, domin a daren ranar Aunty Yakurah ta sa Bukar yamin saki biyu, tare da cilla mini dubu biyar inyi kud’in mota dashi, hankalina ba k’aramin tashi yayi ba saboda ganin k’iri² an raba ni da ‘yata da ban gama warkewa daga nak’udarta ba, haka Aunty yakurah tamin koran kare, ina tafe jini na bin k’afata har tashar mota, inda Allah ya taimakeni ina zuwa wata trailer ta gama lodin kifi, nan na biyasu suka karani a baya, ganin halin da nake ciki yasa drivern ya siyo mun pad ya bani domin in gyara jikina, samin wuri nayi na k’ebe na saka, tukunna motarmu ta tashi, mun dauki kusan kwana hud’u a hanya kafin mu isa, saboda tsaye tsayen da drivern keyi, tun ina zubar da hawaye, har hawayen idona ya kafe.
Da asuba muka isa, nan na samu taxi ta karasa dani gida, iyayena ba karamin tashin hankali suka shiga na ganina ba, nan mamana ta daura ruwan zafi ta min wanka tare da kintsa ni, ta bani abinci naci sannan na basu labarin ukubar da nasha tun daga tarewata har zuwa dawowata garesu, sunyi kukan bak’in ciki, kamma babana yaji, saboda bai tab’a tunanin hakan zata kasance ba, don Bukar na yawan kiransa a waya su gaisa, kuma yana tabbatar masa da ina lafiya.
A can maiduguri kuma, bayan tahowata haka Aunty yakurah ta had’a karya da gaskiya ta sanar ma baba shatima sa sauran dangi, hadda cewa tun dana sami cikin nake ta kokarin zubar dashi don nace ni bazan had’a jini dasu ba, hakan ne yasa ta dawo danu gidanta, bayan na haihu na ajiye mata jaririyar nace bazan shayar da ita, kuma nace in bukar ya cika d’an halas ya sakeni, shine ya sake ni, nan fa gaba d’aya dangi suka yadda da maganarta hakan yasa ba wanda ya nemi iyayena, ko da babana ya nemesu da maganar nan suka cimmasa mutunci tare da kwaso kayan d’akina suka aiko min dashi nan lagos, hakan yayi sanadiyyar tab’arb’arewar zumuncin mu, ya zamana an ware mu wuri guda.
Haka na ci gaba da jegon da babu jaririya, duk da kallo d’aya na mata, amma Allah ya d’aura mini masifar sonta don kullun sai nasha kukan rashinta, haka na rame, na fige, duk da kulawar da iyayena suke bani, amma duk a banza har sai da ya zamana kwakwalwata ta tab’u, ganin haka yasa iyayena tashi tsaye da nemo mini maganin dangana har Allah ya yayemin na dawo normal.
Haka naci gaba da zama kullun cikin bak’in ciki, ganin haka yasa mamana tuntub’en babana akan ko zan ci gaba da karatu ne, sai dai ya nuna mata bai da k’arfin maida ni makaranta, da naji haka, sai na basu shawara a siyar da kayan d’akina in koma makarantar, in yaso abunda ya rage a cikin kud’in zan ci gaba da juyawa saboda in samu in ringa d’aukan nauyin karatuna, nan suka yi na’am da shawarata, Allah ya taimakeni lokacin an fara biyan k’ud’in Jamb, nan nayi register tare da cike wannan jami’ar saboda samun sauk’i, don karatun kudu ya fi na arewa tsada, Allah ya bani sa’a kuma nayi passing dana rubuta, lokacin post utme shima nayi register, nazo na rubuta, wanda nayi planning din tafiyar saboda ban da kowa a garinnan, balle in sauka a gurinsu, sai na taho ana gobe exams din da la’asar, na iso ranar exams din da safe, ina rubutawa kuma na wuce tasha nabi motar dare, cikin yaddar ubangiji na sami admission , nan na fara shirin zuwa makaranta, inda na shiryo gaba d’aya na taho, na kama d’aki a nan school hotel, wanda sai dana yi kwana uku, tukanna na gama screening hade da registration, sannan na samu hostel nayi packing, daga nan sai mamana ta aiko min da flat shoes daga lagos wanda zan ringa saidawa.
Daki d’aya aka had’amu da meena, sai kuma ya kasance course d’inmu d’aya da ita, nan muka had’a kai, domin hatta abincin tare muke girkawa, sai dai na fahimci meena na da rawar kai, domin birthday ko school party, babu wanda take missing, ba yanda ba tayi ba ranar matriculation muje freshers party tare na k’i zuwa, hakan yasa ta tafi ita kad’ai wanda bata dawo ba sai washe gari da safe, raina ba k’aramin b’aci yayi ba, dalilin haka muka rabu, na dena mata magana itama ta dena mini magana.
Haka na maida hankalina wurin karatu, ga kuma sana’ta ta takalma ina yi kuma ina ciniki, ganin kawo takalma na biyu da kyar ya k’are yasa na shawarci mamanmu akan zan gwada siyo viel(mayafai) da inners inga ko za a siya, hakan ce ko ta kasance don ko dana sami wata tamin kwatancen kasuwa naje na siyo, ina kawowa cikin kwana biyu ya k’are har ana nema, hakan yasa na kuma nufan kasuwa domin k’arowa, wanda anan na had’u k’addarar sannan kuma silar rayuwar nan da nake ciki, wanda ko kad’an banjin dad’inta.
Ko dana isa shagon da na siya na farko, sai na tarad ba a kawo musu kaya ba, hakan yasa yamin kwatancan wani shago, wanda da naje na sami colours da design din da nake so, nan na zazzab’a ya min total had’e da fad’min kudin, ko dana zuge jaka don in dauko……….
_Hmmm, sai aka yi yaya, namsy kiyi hakuri kiyi managed, na gaji wallahi yau._
*Comment*
*Like*
*_Fateeyzah mbs ce✍️_*