RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 12 BY Fateeyzah mbs✍️
Www.bankinhausanovels.com.ng
Bangaren mummy kuwa, irin matan nan ne wad’anda basu damu da kowa ba sai kansu, ciki kuwa har da ‘ya’yan da suka haifa, sannan kuma tana da wani hali, na bata iya taimakawa miji da ko k’wandala a harkar da ta shafi gida, don acewarta duk wannan hakk’in namiji ne, wannan yana d’aya daga cikin abunda yasa bata kula damu, duk abunda zamu tambayeta zata ce muje wurin Daddynmu ai ba hakk’inta bane ta mana, a rayuwarta bata son kowa ba sai kanta, zan iya ce muku da wayau na ban tab’a cij k’wandalar mummy ba.
Sannan suna da wata ak’ida ta fad’a a tsakaninsu, a gaban kowa zaku ji suna maida ma junansu da magana, saboda dukkansu babu mai hak’uri, wani halin nasu baxan iya fad’anshi ba don kasancewarsu iyayena.
Haka muka taso a wannan rayuwar, wannan yasa daga ni har Alameen muka tsiro ma kanmu wata irin rayuwa, da farko muna d’aura ma kanmu dogon buri, da kuma d’aura ma kai wahala wanda ya samo asaline ga irin makarantar da muke zuwa, wanda gaba d’aya yaran masu kud’ine, muna ganin yanda suke fachaka da dukiyar iyayensu tare da saka suturu na alfarma, waya mai tsada, hadda wad’anda suke hawa motocin kansu, daga nan nima na saka ma kaina sai nayi haka, wanda ashe shima Alameen halin daya d’auka kenan, da farko munyi shawarar fara ma Daddy da mummy sata, mu ringa d’iban kud’i muna biyan buk’atunmu, sai dai duk wayonmu da dabarun mu sun tashi a banza, don idanunsu kar yake indai akan kud’ine, a haka dai muka rasa madafa, muka ci gaba da rayuwa a yanda muke, sai dai ba wai mun janye k’udurunmu na canza rayuwarmu bane.
Ina gama j.s.s 3 zan shiga s.s 3 Daddy ya canza mun makaranta daga *therbow* zuwa *zaria academy* , duk wanda yasan zaria academy yasan makaranta ce ta yaran masu k’udi, wanda a makarantar zaka ga yaran masu manyan muk’amai na gwamnati, manyan ‘yan kasuwa, manyan ‘yan siyasa da kuma manyan celebrities daga 36 states of nigerian, makaranta ce ta ‘yan karya sosai, sai dai ni naji dad’in makarantar, don abincin danake ci a nan ban ci a gidanmu, domin kuwa kowa serving din kansa yake a dinning, gashi ba a mana abincu babu kifi ko nama ko kuma kwai, kuma ni dama ko da za a kaini ba had’a min wani provisions aka yiba, shiyasa duk damuwar dana tafi da ita ta yaye, nan danan na k’ara haske had’e da kyau, ga wani kyau dana k’ara.
Matsalar dana fara fuskanta a makarantar shine tsangwama daga wurin d’alibai, suna ganina low class, wasu ma cewa suke hala ma scholarship na samu na zuwa makarantar, duba da yanda komai nawa na nuna ni talakace, daga provisions, uniform, dasu check dina, haka kuma ga rashin k’udin kashewa wanda kowani d’alibi iyayensa ke siyan masa ticket wanda ke mazaunin kud’in da zaka ringa kashewa a shagon makaranta, duk da raina yana b’aci in suka min haka, bana ganin laifinsu face na iyayena, saboda yanda suka kasa tsare mana komai tare da biya mana buk’atu, wannan ya kuma sani d’aura d’amara don ganin na shiga sawun yaran masu k’udi.
Ban kuma tozarta ba sai da lokacin visiting yaxo, ta yanda naga manyan motoci da suke ta fakawa tare da manyan mutane da suke zuwa da manyan kulolin abinci na alfarma wanda zaki d’auka biki ake yi, sai dai ni banga wani da yazo min ba, da alama iyayena sun ma manta dani,ranar nayi bak’in ciki tare da zubar da hawaye, gashi kuma banda wata k’awa da zata tausani, don na zama mujiya a cikinsu.
Lalacewar rayuwata ya fara ne lokacin da muka dawo hutun first time, yadda abun ya faru shine…….
_Toh yaya ta kasance ne da meena?_ _, kumin hakuri ku biyoni zuwa gobe, don yau I am busy, bazan iya dogon typing ba._
*Laifin dadi, karewa*
_Saura k’iris in kammala part one((1) na wannan littafin mai suna *RAYUWAR CAMPUS* don son jin labarin har k’arshe sai ku biyoni a part two(2), wanda ya kasance na kudi, biya don ki karanta._
_Zaku iya fara biya don kar a fara badda ku, zaki iya biya ta katin waya ko kuma account number_
*Domin shiga paid group* 👇
*_Single #200_*
*_VIP #300_*
*_Document #400_*
_Zaku biya ta wannan hanyar👇_
*08161734851(katin waya) tare da turo da shaidan turawa.*
*Account number*
*0796627818*
*Fatima sani Muhammad*
*Access bank*
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*_Fateeyzah mbs ce✍️_*