RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 13 BY Fateeyzah mbs✍️
Www.bankinhausanovels.com.ng
…Yadda abun ya faru shine, wata friend d’ita Lubna da muka yi junior tare ta gayyaceni birthday, ban yi nauyin baki ba data kawo mun Iv na sanar da ita banda kayan sawa, hakan yasa ta d’aukeni muka je shopping mall don ta siyanmu, anan muka had’u da wani had’adden guy Anwar wanda already ita lubna ta san shi, ko da suka tsaya gaisawa idonsa k’yar a kaina, nan yake tambayar Lubna wacece ni, ta sanar da shi friend d’inta ce, bai yi nauyin baki ba yace mata yana sona wallahi, ko da ya tambayi number wayata nace masa ban da waya, bai yi mamaki ba don tunda lubna ta fad’a masa mahaifina yasan za a rina, don yasan wanene Alhaji D’an k’warai sosai, haka yace mu jira shi, bai d’auki lokaci ba sai gashi da kwallin wayar ipone 7+, yana zuwa ya mik’amin tare da bud’e bayan k’aramar wayarsa k’irar nokia ya ciro sim card ya m’ikamin yace in naje gida in saka sai kirani, hmmm ranar na tsinci kaina cikin farin ciki, don ji nayi kamar an mini bushara da gidan aljanna.
Abunda zai baku mamaki ko da mummy taga wayar sai cemin tayi hala Daddynku ya siyan miki, banda amsar da yafi in amsa mata da eh, wai bud’ar bakinta sai cewa tayi ai dama tasan zai dawo kan hanya, wa ya fad’a masa barno gabas ce, da zata zama jakarshi tana ma ‘ya’yansa hidima, kamar Had’in baki shima da daddy ya yaga wayar tambayar da yamin kenan, shi kuma dana amsa dariya yayi yana fad’in yanxu ya fara ganin ya auro d’iyar mai dala, kai ni abun nasu ma mamaki ya bani, Alameen kad’ai na fad’a ma gaskiyar wanda ya siyan min wayar.
Ko da ranar birthdayn tazo can muka had’u da Anwar wanda zuwa lokacin mun saba ta waya, haka akayi birthday aka watse ya d’aukoni a motarsa, sai dai maimakon ya kaini gida kamar yanda yace sai kawai ya wuce dani *APPLE WHITE PALACE,* ko da muka shiga already ya kama d’aki, ganin a tsorace nake haka yayi ta jana da hira yana ta kwantar mun da hankali da yaudararrun kalamansa har na saki jiki dashi, nan ya fara romancing dina wanda ni kuma na ringa jin dad’i har takai na sakin masa jiki, a tak’aice a ranar Anwar ya rabani da virginity dina wanda a lokacin I am only 16 years, naji jiki sosai don ma ya bini a hankaline, ranar a hotel din muka kwana, sai washe gari ya fita dani ya mini shopping sosai , sannan yaje dani bank aka bud’emin account, Daga nan kuma muka wuce gida ya sauke ni ya wuce.
Ganina a k’ofar gida ya saka hankalina tashi domin bansan me zan tarar ba, sai dai ko dana shiga , Alameen kawai na tarad a gida, cikin sauri ya taho ya tareni yana mai tambayata inda na kwana jiya, don hankalinsa ya tashi daya ga ban dawo ba, gashi shi ba waya ba balle ya kirani ba, kasancewar bana b’oye masa komai yasa na sanar dashi, duk da ya nuna min bada kaina da nayi bai kamata ba, amma yayi murnar samun chanjin rayuwar da nayi, nan fa muka bubbud’e shopping d’in da Anwar ya min, ya d’auki abunda zai iya amfani dashi ya barmin sauran.
Abun da zai baku mamaki, wai fa su Daddy da Mummy saboda rashin kula basu san ba a gida na kwana ba, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yayin da Anwar ya maidani kamar matarsa don haka yake d’aukana muje hotel mu kwana, amma kuma ni da Alameen bamu nemi komai mun rasa ba, yanda yake kashe mana kud’i kamar bai son zafin nema ba, duk wata yake turamin kud’i ta account dina.
Ko dana koma hutun makaranta, student sunyi mamakin canzawata, haka zan samu ana gulamata amma ko a jikina, in aka tashi visiting kuma, Anwar da Alameen suke zuwa mini, haka suke yomin shopping sosai ga abinci kala² da suke mun order, haka muka ci gaba da rayuwa har na gama secondary, wanda a wannan lokacinne kuma Allah ya d’auki ran Anwar sakamakon hatsarin jirgin sama da yayi, nayi kukan rashin Anwar sosai don kukan da nayi ko iyayena suka mutu iyakarsu kenan.
Abunda zai baku mamaki, duk abunda muke ciki su mummy basu sani ba, domin kowannansu gani yake ‘yan uwansa ke mana wannan hidimar.
Rashin Anwar ya samu shiga wani hali, don kusan gaba d’aya abunda na tara daga wurinsa ya k’are, cikin k’ank’anin lokaci muka kuma komawa gidan jiya, da mummy ta fahimci haka ma sai cewa tayi ai dama tasan Daddy bazai daure d’aukar d’awainiyarmu ba, shi kuma daddy cewa yayi ta dawo da halintane, Allah ya kyauta ansan mace da tausayin ‘yayanta.
A haka na samu admission har nazo school dinnan, yayin da Anwar kuma aka kaishi Nigerian Navy School dake lagos, farkon zuwana school dinnan naso kame kaina, amma hakan bazai yiwu ba, saboda 3k daddy ke aikomin a wata, ganin haka yasa na koma gidan jiya, a haka nake biya ma kaina bukatuna.
“Wannna shine tak’aitaccen tarihina, kallonta suje cike” cewar meena tana mai share hawayenta.
Gaba d’aya kallonta suke yi cike da mamaki, don jin labarinta suke kamar a film ko novel, dama akwai iyaye haka.
Hibba ce ta gyara zamanta tare da cewa “Allah ya kyauta meena, sumy gareki, don yau ya kamata kowacce ta fad’a mana tarihin rayuwarta”.
Dogon numfashi ta saki, sannan ta fara.
*Wacece sumy?*
Ni rayuwata, rayuwace mai cike da k’azanta, kamar yanda kuka sani Sumayya Turaki ne sunana, babana d’an asalin jahar bauchi ne cikin garin Dass, amma yanxu muna zaune ne a Abuja, Daddy ya rik’e muk’amai da yawa a fad’in Nigeria, tun daga kan state har federal, yanxu shine ministern Kud’i, Mahaifiyata kuma banma santa ba, yayyina dai sun cemin buzuwace daga nijar, kasancewar mahaifinmu mai auri saki ne, duk yawan ‘ya’yanshi mu goma sha biyu(12), kowanne shi d’ayane gurin mahaifiyarsa,mu mata mu 4 ne kuma mune k’anana, maza kuma su 8.
Rayuwar gidanmu rayuwace ta ‘yanci, rayuwace muke yi ta turawa, kowa zaman kanshi yake yi cike da ‘yanci, babu mai takura ma wani, mu mata zamu iya kawo saurayi har bedroom d’inmu, mazan ma haka, don mu k’adai muke rayuwa a cikin gidan, don Daddy yana rayuwane shi da matarsa a wani gidan da ban…….
*_Chab di, wata irin rayuwace wannan?_*
*_Shin Meena nada laifi a irin rayuwar da ta tsinci kanta._*
*Laifin dadi, karewa*
_Saura k’iris in kammala part one((1) na wannan littafin mai suna *RAYUWAR CAMPUS* don son jin labarin har k’arshe sai ku biyoni a part two(2), wanda ya kasance na kudi, biya don ki karanta._
_Zaku iya fara biya don kar a fara badda ku, zaki iya biya ta katin waya ko kuma account number_
*Domin shiga paid group* 👇
*_Single #200_*
*_VIP #300_*
*_Document #400_*
_Zaku biya ta wannan hanyar👇_
*08161734851(katin waya) tare da turo da shaidan turawa.*
*Account number*
*0796627818*
*Fatima sani Muhammad*
*Access bank*
_Ina masoyana na asali ,ku garzayo ku biya, don kara samun damar karanta sabon littafina mai suna *MATAR BAHAUSHE*_
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*_Fateeyzah mbs ce✍️_*