RIKICIN KAUNA CHAPTER 9 BY MARYAM SALISU MAI DALA

Babansu Nana ne da kansa ya zo da hakan babu wani abun da zai iya cewa, amma ya ji duk jikinsa ya sanyi sanyi mai yiwa ko don yana jin kamar auren ne ya fara zuwa masa bugu da karin abin shi gashi ko da yaushe cikin rikici suke da Dubu’ musamman a kwanan nan don ganin abinda take yi din, amma tunda abin ya zo dole ya ‘kauda fushinsa ya tsaya ya yi mata maganar dole ta nutsun ta bar abubuwan da take yin, yana ta raya hakan a ransa har a sanda kaka ta gama jero natan, tana kallonshi sai da ya ji ta kare ya mike kaka ta ce “Ban ji Tafida ya ce komai ba.”

Ya ce “Kaka Allah ya kaimu.” Ya sa kai ya fice tana maganar yazo ya karya din da abin da ta ajiye masa ya ce yana zuwa yana fita din kuwa gurin  mai kosai ya zauna zaunawarsa ke nan sai ga su Nana da Laure da kayan boko zasu wuce bokon, kamar ya kyalesu don yadda yaga suma sun share shi zuwa can ya ce “Laure idan hakan ya yiwa Nana kyau ke ba kyau zai miki ba.”

Laure ta waigo ta ce “Au Tafida ina gajiya?”

Ya ce “Lafiya Laure sannu Laure.” Don yadda yake fado sunan nata tamkar yadda Nane ke kiranta dole sai sautin ga ya fito a karshen sunan nata, to itama haka Nana ke fadar.

Nana ta gane da ita yake amma ko kula shi bata yi ba don ta riga ta camfa shi sai dai idan ba a hadun ba wai ma don babu su Da’°u da abin tasan sai ya fi haka, Tafida ya sa me kosan ta Gunsa musu ya bawa wani almajiri anan kusa ya bisu da gudu ya mikawa Laure ya ce “Wai ga shi ku biyu.” Laure ta karba don har tana dan waigowa ta kallo Tafidan ta dan daga masa hannun godiya sannanta juya tana murmushi tana cewa Nana “kuma fa a hakan da kike gani kirki ne da shi.” Nana ta ce “Dama, shi ai tsokana ceta cinye masa rai kullum idan bai yi ba ko a abokanai ne ba zai ji dadi ba.” Suka sa dariya duka.

Ranar Lahadin kuwa akayi baikon Tafida da dubu, don yadda Dubu ta hada dandali tarakar bikin ana wake Tafida, aka saka musu watani hudu, Dubu ta dinga jin tamkar duk tafi sauran matan kauyen sa’a tunda kuwa zata auri Tafida, don daren ranar bata shigo gidan da wuri ba saboda ana can dandali ana wake har kyauta tayi a ranar.

Tafida ya riske Dubu bayan kwanaki biyu da yin baikon nasu sanda yaro ya shiga ya fado

Tafida na sallama, Dubu na cin tuwo bata sam sa’adda ta ture kwanan tuwon ba ta zabura, rabon da taji hakan ta jima tun kafin su yi rikici,ta

mitsittsike hannunta a gefen zani ta mayar ta daura ta ja dan gyalenta ta sokeshi a kugu ta fice, ta samu Tafida jingine a bangon kofar gidansu ya aza hannuwa a kirji tamkar me wani tunani, amma ya farko sanda ya ji Dubu nai mishi magana, tace ya shigo daga zauren su mana.

Ya ce a’a ta barshi haka, tayi dashi ko ta shiga ta kawo masa ‘yar tsuguno ya ce a’a yana nan tsaye ya dubi Dubu ya ce “Dubu duk da al’ada ce daura mayafi anan.” Yana nuna mata inda ta ci

damara a kugu, “Amma ina ganin tamkar sai ya fi sirri ki rufe jikin ki musamman daga sama ke kan ki sai kin fi jin dadin jikinki.”

Ta kalleshi ta dubi saman kirjinta ta gano, yadda yake nufi, tace “To naji Tafida zan dinga gyarawa.” Amma bata gyara din ba.

A lokacin ya dan kau da kai ya ce “Dubu ko da

Da sauri ta kalleshi tana dan zaro ido tana dafe

Ya ce “Owo? Tadin so waccen maganar kuma a barta ko?” Yana kallonta, “Kin dauka na manta, to abin yana nan a raina 

kan haka don duk wani abu da aka kawo gidan ku zan barshi ne ni kuma in nemi wata in sake kai mata.”

Dubu ta sake zazzaro ido sosai wanna kalma ko a baki ta tsani taji an danganta Tafida da wata, a raunane ta ce “Tafida abin har ya kai haka, zaka dinga ambaton wata a gabana.” Tana nuna Kirjinta da yatsa.

Ya ce “A to ni dai na gaya miki don kada ki ceban sanar da ke ba.”

Dubu ta sake langwadar da murya ta ce “Tafida in dai don kan…

Ya ce “Ni ba wata magana nace ki tado da ita ba yanzu kin ga dai yanzu ga abinda na ce miki in kika kiyaye min haka ni babu wata matsala a tare da ni, ko aure mukayi in dai kin kiyaye Hakan to komin zan iya yi miki shi kenan ni zan tafi.” Ya juya.

Dubu ta ce “Haba Tafida yanzun har tafiya zaka yin?”

Ya ce “To me zan jira dama abinda na zo na gaya miki kenan.”

Ta ce “To shi kenan Tafida yaushe zake dawo tadin.”

Ya dan kalleta yace Sai anyi kwanaki.”

Cikin sanyin jiki ta ce “Shi kenan ni gobe zanzo na gaisar da kaka.” Kawai wucewa yayi ya barta nan tsaye tana ta kallonshi har ya bace.

Ranar kasuwa Tafida na cikin rumfar shi Balele ya shigo kenan ya fita ya hangi su Nana suna siyan kuka ita da Laure sun tsaya za a auna musu, da yake idan ranar kasuwa ne tun safen suke fita sai ko goshin magariba zasu dawo, to yau din ma haka Tafida ya yiwa wani yaro nunin su ya kirawo su, da yake ba duka ranar kasuwa Nana ke zuwa ba sai ta kama idan ma aike ne anfi aiken ila, Nana taji ana kiranta daga baya ta waigo yaron ya nuna mata ana kiranta tayi tunanin irin samaria da suke tararsu a hanya ne sai da ta dan ratso sosai ta ga. Tafida, ya sa hanou ya kara yafitar ta alamar tazi ta dan dakata tana son ta gano fuskarsa don bata son su raba abin fade a tsakiyar mutane shima ya fabinto haka yayi dan murmushi ya juya ciki bayan ya yi mata inkiyar su zo, itama ta dan yafito Laure suka biyoshi, kallo daya Nana tayi masan a ranta ta ce, daga kallonsa yinwa yake ji amma ba ta yi magana ba kuma ko a fuska bata muna ba ya de “Kaka tana gida?” Yana kallon Nana.

Ta amsa a hankali “Sanda dai muka fito tana

nan

Hmmm