RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE END BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Abba Zaria zan je akwai shagon da zanje a Zaria din, wai shagon Jafar, zan yi wa Nasreen siyayya.” Abba ya saki fara’a, “Sai ka hada da Zakiyya.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Gabansa ya fadi ras! Jin an ambaci sunan Zakiyya, sosa kansa ya yi ya ce, “Eh amma ba zan karbar masu iri daya ba, ko kuma ita Zakiyya tunda tasan wurare sai inbata kudinta ta siyo nata, itama Nasreen din irin wanda take so zan siyo mata.” Abba ya jijjiga kai alamun ya fahimta. Sultan ya mike ya shiga gun Mairo yana kallon Kofar mahaifiyarsa a rufe, ya girgiza kai. A daki ya sami Mairo ya gaidata sannan ya ciro kudi masu yawa ya mika mata Da Kyar ta Www.bankinhausanovels.com.ng karba, ya fito ya tasa Naufal suka tafi Zaria tare. Www.bankinhausanovels.com.ng
A cikin mota Naufal yake bashi labarin yadda Abba yake kasancewa a cikin damuwa. Sultan ya dafa kafadarsa, ““Kada ka damu insha Allahu komai zai zo Karshe.” Kai tsaye wurin Hauwa’u Dan Borno suka tsaya daga can suka wuce Kasuwan sabon garin. Sai dai bai shiga ba, ya tura Hauwa’u ita ta siya masa komai, ya yi mamakin da ta dawo masa da canji. Kudi ya Kara mata yace itama ta siya
ZAMU TASHI
turarukan da Mumran. Cikin KanKanin lokaci Kamshi ya cika motar, yana da tabbacin Malam Jafar yana siyar da manyan turarukan maza, ya sha alwashin zai dawo ya sake siya.
Naufal ya ce, “Dee, wasu abubuwa ne masu Kamshi haka? Kamar na taba jin Nasreen da irin Ramshin, duk da wannan yafi nata dadi.” Sultan ya yi ,murmushi ya ce, “Dukka nata ne, ita ta aiko ni.” Naufal ya yi dariya yana jin dadi. Kai tsaye suka dawo Kaduna, a Kasan gada suka tsaya. Nan da nan fuskar Sultan ta sauya, shi dai . Naufal sai kallonsa yake yi kamar ya sami tv. Suna tsayawa, Sultan ya sauka, hakan yasa Naufal bin bayansa ba tare da yasan yana binsa ba.
A gaban dan sanda ya tsaya wanda yake tsaye da kayan aikin kanikanci. “Rankashidade muna ci gaba da bincike, sai dai ko waye makashin matar da ta haifi ‘yan biyu a KarKashin mota…” Sultan ya daka masa tsawa, “Wacece ta haifi ‘yan biyu a KarKashin mota?”
, Mutumin ya Kame masa ya ce, “Sorry sir! Ina nufin matar da ta yi rayuwa da ciki a wurin. Mutumin yana da wayo, bai yarda anyi magana da shi a wayar sadarwa ba, sai ya tura wani mai Www.bankinhausanovels.com.ng
suna Alhaji Kabir wanda yake KoKarin nuna cewa shi ne yake da case din, wanda a zahiri ba shi bane. Amma wannan takardun suna dauke da bayanan abubuwan da na samo a dalilin bincike na. Zamu ci gaba da yin bincike har inda Karfin mu ya Kare insha Allahu.”
Sultan ya amshi takardun ya bugi kafadarsa, “Aikinku yana kyau sosai. Ina fatan zaku ci gaba a yadda na sanku. Idan muka gano waye Alhaji Kabir babu shakka zamu gano sauran.” Sultan yana juyowa, suka yi ido hudu da Naufal da ke , duban kowa duba irin na mamaki. Sultan yaso ya yi masa fada sai kuma ya kasa. Suna shiga mota ya dinga dauke kansa baya son amsa tambayar da ya gani a cikin idanun Naufal yana sonyu masa. “Deedi wai” Kafin ya Karasa Sultan ya dubi gefen titi ya ce, “Naufal lokacin ina Karami babu abinda yake faranta min rai sama da kallon gefen titi, hakan yana sa ni nishadi.”Naufal ya dan yi dariya ya ce, “Ashe kai na biyo da kallon gefen titi Deedina.” Sultan ya yi murmushi, “Eh ni ka biyo mana. Driver tsaya mu siya kayan marmari.” Suka dan dakata, a lokacin ne idanun Naufal ya hasko masa Mansur, cikin gigicewa ya ce, “Dee ga mutuimin da ya sace mu Can ya ce zai auri Nasreen.” Sultan ya juyo cikin gaggawa, a lokaci guda ya ba ‘yan sanda daman zuwa su cafko shi, sai dai ihun da Naufal ya yi ya ci nasarar isowa cikin kunnuwan Mansur, haka kuma ya ji dukkan abinda yake gayawa Sultan, don haka ya Kara da gudu. Duk Kokarin da suka yi domin ganin sun kama shi, inaaa hakan bai yuwu ba. Hakan ya bata Www.bankinhausanovels.com.ng ran Sultan ya so ya kama shi, domin jin wanda ya sa su wannan aiki na * wahalar masa da Nasreen. Haka suka je suka ajiye Naufal wanda ya kasa yi masa tambayar da yake son yi, a dalilin fushi da ya gani a idanunsa. A matuKar gajiye Sultan ya dawo gida. sai dai yana shiga falan bai ci karo da kowa ba, hakan yasa ya nufi’sashen Nasreen tana nan a _kwance shiru. A hankali ya Karaso kusa da ita ya ajiye mata kayayyakin da ya siyo a shagon Jafar, bai yi mayana ba sai jin muryarta ya yi cikin rauni ta ce, “Sannu da zuwa.” Bai amsa ba, sai da ya bata Fake a goshi sannan ya ce, “Yauwa Nasreen. Ga saKon kayan Kamshin ki nan duk ya cika mana mota. Bari in je in gaida Umma.”
[Ta kai ta amsa, sannan ta dan tashi da girmamuawa ta ce, “Na gode Allah ya Kara maka budi yasa ka fi hakan. Ina na Anti Zakiyya da su Umma?” Murmushi ya kufce masa. Duk yadda yake cikin bacin rai, in har zai zauna a gaban Nasrren sai ya nemi damuwar ya rasa. “Ban siya masu ba, amma zan ba kowa kudi iya adadin abinda na siya maki din. sai su je su siya ko?” Ya bata amsa tare da sake cusa mata tambaya. Nasreen ta yi murmushi wanda iyakarsa fuska ta ce, “Hakan yana da kyau, amma idan da hali ka basu fiye da nawa, Kila abinda za su siya yafi nawa tsada. Kayi Sallah ko?” Ya miqe yana tafiya yana bata amsa, “Na yi Sallah Nasrcen, zan basu dubu talatin talatin kamar yadda kika roKa. Sai na fito zan sake dawowa.” Yana fita kai tsaye dakin Umma ya nufa ya
’ sameta tana gyangyadi, tausayinta ya kama shi ya Karaso yana duban ta, “Sannu da hutawa Umma.” Ya gaidata yana KoKarin sunkuyar da kai. Kamar za ta share shi sai kuma ta amsa babu yabo babu fallasa. Haka hafsat ta gaida shi itama babu wata fara’a a tare da ita. Shiru suka zauna babu wanda ya sake yin magana. Zuciyar Umma tana tafarfasa tana jin ashe haka Hajiya Gwayyo taji, a lokacin da ta hana Abba saurarenta? Ashe haka uwa take ji a zuciyarta?
Sunkuyar da kai ta yi babu alamun nadama ko Www.bankinhausanovels.com.ng danasani a zuciyarta, sai tsabar jin zafin Zakiyya da uwarta da ke sake nuKurKusanta. Ta kira Hajiya Ladidi yafi a Kirga amma ta ki dauka. Ganin shirun ya yi yawa yasa ya mike yana mata Allah ya Kara sauki amma ko uffan bata ce ba. Sultan ya ce, “Oh umarninku na bi na zauna da Zakiyya, wacce nake so kunsa min Katanga a tsakanin mu, ban san ya kike son in yi maki ba Umma. Ga shi yanzu wacce nake bin umarninku saboda ita ta sami abinda take so a wurina.” Ya wuce abinsa, ba tare da ya bari Umma ta ji maganganun da yake yi ba. Tunda ya shige babu wanda ya sake ganin Kyeyarsa, haka Sallar Isha’in ma bai yi ba, sai wajen asubahi da ya tashi ya hada gaba daya. Yana tashi ya wuce Office abinsa. Lamarin da suke ganinsa kamar da wasa abin ya fara yin nisan da kowa yake ji a jikinsa. Wannan lamari bai sa Umma ta sauko daga irin tsanar da take ji akan Nasreen ba. Don haka ne Nasreen ta fi kowa shan wahala, mutumin da shi kadai yake tausaya mata a yanzu bata ganinsa ma. ‘yar Kibar da ta yi duk sun tafi. Babu wanda take sha’awar ya dawo kusa da ita kamar Naufal, ta sani idan da yana nan ba zai taba barin hawayenta su zuba ba. Zaman gidan duk ya fita akanta. Zakiyya yanzu ita ke yin dukkan abinda ta gadama a lokacin da ta so. Umma duk masifarta ta kasa cewa komai ta zuba mata idanu. Addu’a take yi Kunan da ke Kafafunta su warke, za ta tattara ta koma Kaduna sai ta nunawa Hajiya Ladidi kuskurenta. Haka tana nan akan bakanta sai ta tafi da Nasreen, don ba za ta bar gurbatattu biyu a wuri guda ba. Ita kuwa Nasreen kwana biyu idanunta Kaikayi suke yi mata saboda yawan kuka. Yau da kanta ta fito, bayan tana da tabbacin baya cikin falon. Ta dinga lalube har ta iso waje, tana ci gaba da tafiya. Gate din gidan ta nufa da ninyar fita, “yan sandan suka tare ta da tambayar, “Hajiya ina za ki je?” Ta girgiza kai, “Ina son ganin gari ne.”
Suka hana ta fita, suna roKonta ta koma, ita kuma ta dage ba za ta koma ba, daga Karshe tasa kuka. Sultan ya fito hannunsa dauke da Kwallo ya hango su, don haka ya Karaso. Da idanu ya kalle su duk suka bar wurin. Jikinta ya bata yana wurin don haka ta sunkuyar da kanta. Ya Karaso ya tsareta da idanunsa, “Nasreen. Ina za ki je?” Ta kasa magana sai ruwan hawaye da suke sake kwaranya. Sultan ya juya yana dubawa ko Zakiyya tana nan, domin ya tsani dukkan abinda zai bata mata rai, haka Nasreen tana nan a zuciyarsa, kawai Zakiyya ce ta yi masu tsakani. Hannunta ya kamo suka zagaya baya, ya rungumeta tsam a Kirjinsa. Rabon da ya ji sanyi irin na yau tun ranar da ya rabu da jikinta. Shinshinarta yake yi da gaske kamar zai cinyeta danya. Ita kanta jikinta rawa yake yi Www.bankinhausanovels.com.ng
Da kanta ta yi Kasa tana kuka mai ban tausayi. Shima sunkuyawa ya yi kusa da ita yana , mata duban tausayi, “Nasreen kina fushi da Dee ko? Dee ya yi maki laifi ko? Gaya min irin horon da za ki yi min na shirya karba, amma don Allah kada ki horani da barin gidana.” Nasreen ta girgiza kai, “Baka yi min komai ba Deee. Kawai bana jin dadin yadda gidan ya koma ne, ina son ka mayar da ni gidan Yumnah Aminu, ko kuma ka kaini Kaduna in zauna da Abbana. Idanuna suna yi min zafi kamar za su fado.”
Sultan ya kafeta da ido yana jinjina irn wannan rama da ta yi. “Kin gaji da ni za ki ce –
Nasreen, kin gaji da halina ba wai kin gaji da gidan ba. Gaya min abinda kike so amma banda abubuwan da kika zayyano. Idan na kai ki gidan Abba zai yi fushi da ni, inhar ya ga irin ramar da kika yi. Abbana bai taba fushi da ni ba, sai a ranar da aka sace ku, kina ganin a yanzu idan na kai ki kina da damuwa ba zai tsine min ba? Nasan ba za ki so hakan ba. Haka ba zan iya kaiki gidan Yumnah ba. Idanunki kuma da suke zafi Nasreen kukan da kike yi ta yi yawa. Ya kamata ki ragewa kanki yawan kukan nan. Bari * inkira Al-ameen yanzu sai in ji yadda za ayi. Jibi zan sa dan sandana ya dauke ki ya kaiki a yi ~ maki komai da komai na fita waje.”
Nasreen dai ba ta ce komai ba, sai ajiyar zuciya take yi. Zama ya yi akan wani dan baranda ya jawota jikinsa ta kwantar da kai a bisa kafadar da take kewa. Hakan yasa sanyi ya dinga ratsata. Tana jin su suna waya da Alameen wanda yake tabbatar masa su zauna cikin shiri domin likitan ya dawo yana London, don haka a can za.ayi aikin idanun. Sun jima a wurin ba tare da sun dawo cikin gidan ba, har barci ya soma kwasar Nasreen, kasancewar ta dade bata Www.bankinhausanovels.com.ng barci sai tashin dare, tana yi wa mijinta addu’a.
Iska yake hura mata daga sassanyar bakinsa, tana shaKar iskar wacce take shiga har cikin maKoshinta tana cin nasarar kauda duk wani Kishin ruwa da ke danKare a makoshinta. Haka iska yana sake kadawa, yanayin dole yasa masoya a cikin nishadi kamar yadda ya ci nasarar sa Sultan da Nasreen. Tare suka shigo gidan yana rike da hannunta, sai aka ci sa’a Zakiyya tana falon. Idanu a waje take dubansu, “Yaya Sultan me zan gani haka? Ai na yi zaton ka ce min babu ruwanka da ita domin wari take yi maka, haka kai ka tsani ta matso kusa da kai. Ko dai halinku na maza za ka nuna min masu zama da mata fiye da daya?” ’
Sultan ya zaro idanu yana jin wani sabon sharri. Lallai idan bai nuna mata halin su na maza masu mata fiye da daya ba, ita za ta nuna masa halin makircin mata, masu son dole sai sun baKantawa ta kusa da su.
Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Da gaske ne ya ji wari a jikina, amma ya gaya min kuma na gyara, insha Allahu daga yanzu ba zan sake barin hancinsa ya shinshini wani abu ba Kamshi ba, domin na fahimci warin da na bari ya shaKka ya cutar da shi, har hakan yasa yake guduna.”
Zakiyya ta ware idanu tana jin dacin maganar Nasreen, gani take yi Sultan ya zagaya ya gaya mata tana wari shiyasa ma take gasa mata magana.
Ta dubi Sultan ta ce, “Au ashe gulmata kake yi kai da matarka? Har kake gaya mata ina wari.”
Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Au ashe warin kike yi? Me yasa kike zagin wani bayan ga abin zagi a jikinki?”Www.bankinhausanovels.com.ng
Zakiyya ta yi kukan kura ta fizgo Nasreen ta haye jikinta ta hau duka. Babu abinda zai baka
* mamaki Nasreen ko tari bata yi ba. Ran Sultan ya yi matuKar baci, har bai san lokacin da yasa hannu
ya fizgo Zakiyya ba, ya wawwanke mata fuska da mari yana huci. Tsananin azaban marin yasa ta shiga taitayinta ta koma gefe tana zare idanu. Sai da ta dawo hayyacinta ta dage ta kurma ihu, tana fadin yau sai ta karya Nasreen sai dai idan ba zai fita a gidan ba. Umma da Hafsat suna kallon duk abubuwan da ke faruwa, amma babu wanda ya tanka. Sultan ya jawo Nasreen yana dubawa ko ta ji mata ciwo. .
Zuciyar Nasreen cike da kuka, amma ta ci alwashin Zakiyya bata isa taga hawayenta ba. Sultan ya ce, “Idan kin cika mara kunya ki zo ki sake tabata ni kuma nayi maki alKawarin kakkarya Kafafunki. Karamar mara kunya, mahaukaciya za
ki mutu da hauka da sunan kishi. Idan kinsan kina da kishi bai kamata ki auri mijin wata ba, sai ki nemo mijinki ki kafa masa doka, ba wai mijin da tuni ya yi aurensa aka kawo masa ke a matsayin Kari ba. Aurenki ko auren Kaddara! Nasreen duk abinda za ta ce kada ki tanka mata, mahaukaciya ce take neman abokin da zai taya ta hauka.”
Umma ta dubi Hafsat duk suka ci gaba da zuba masa idanu. Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Albarkacinka Dee, Zakiyya za ta yi min abinda ta gadama. Kuma bambancin mai ilimi da jahili aiki da abinda ya sani. Dambe? Haushi? Ba su daga cikin dabi’un da na koyo, ka koya min hakuri da tausasa zuciya a yayin fushi, ba wai haushi da zage-zage ba, irin rayuwar dabbobi da karnuka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wayyo Nasreen tana caccaka mata magana, tana jin kowani harafi da Nasreen take yi tamkar tana soka mata mashi. Kalaman Nasreen basu da yawa, amma suna da kaifin da za su iya raba mutum da rayuwarsa gaba daya. Wato ita ce mahaukaciya?
Wani kukan kura ta yi ta sake yo kanta, Sultan yasa mata Kafa ta fadi Kasa. Umma ta dube shi, “Sultan amma kana cikin hayyacinka kuwa? Kana son mayar da gidanka dandalin ‘yan kokawa? Idan fada za su dinga yi maka a gida gara
duk ka sallame su su tafi. Kana sakin su jibi zan daura maka aure da tsala-tsalan ‘yan mata wadanda suka fi ku, ku kuwa sai ku yi shekaru goma kuna yawo babu mashinshini, da anzo neman aurenku ace ai fada suke yi da kishiyoyi, suna ya lalace. Shi namiji yake, ko me zai yi ado ne akan ku. Kananan ‘yan iska. Kada ka sake kula kowa ni zanji da su, zo ka wuce.” Www.bankinhausanovels.com.ng Zakiyya da ta ji maganar takarda sai kuma idanunta suka bude. Duk da haka sai da ta mike tana duban Umma sama da Kasa ta dubi Nasreen ta fara bata amsa, “Uwarki arniyar nan ita ce kare ba ni ba. Ke kuma da kike cewa ya sake mu, ai ni ko ya sake ni babu inda zanje domin naci gida Wallahi, saboda abinda ke cikina dole shi ne magajinsa. ”
Sultan ya ja ya tsaya cak! Daga barazanar dukan da yake shirin kai mata. Maganar ciki ya razana dukkan mutanen da ke cikin dakin daga ciki har da Umma.
* Mu hadu a littafi na 4, kuma na Karshe.