RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
ya gaji da yadda ake sa Meeting ana dagawa duk saboda tsoron Sultan yasan komai. Duban Sultan ya yi a lokacin da ya zare farin gilashinsa, wanda ke sake Kawata fuskarsa, “Sultan zauna mu yi magana.”
Babu musu ya zauna, tare da kafe idanunsa akan na Al-ameen, da alamun shi kadai yake saurare, yana son sanin dalilin hadin sunan Baba Mu’azzam, da irin maganar nan. Da alama dai basu san wanene suke alaKanta shi da wannan barnar ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Al-ameen ya sake duban Sultan ya ce, “Sultan Baba Mu’azzam Yayan Umma, wanda yake zaune a garin Kaduna, kuma mai Karya da addini, ina nufin ya shiga rigar addini yana abinda ya gadama, shi ne mutumin da muke ta nema akan matsalar Nasreen, ina nufin shi ne mahaifin Nasreen da Sultan. Shi ne mutumin da ya boye kansa yake ta bamu wahala wajen nemansa.”
Sultan ya mike yana duban Al-ameen. Tabbas da a kusa suke da juna da babu abinda zai hana shi shake shi, a kan Kazafin da yake son yi wa Baba Mu’azzam. Sultan ya sake dubansu ya tabbatar da dukkansu sun san da wannan maganar kuma sunyi na’am. Cikjn tashin hankali sultan
ZAMU TASHI
Sultan ya girgiza kansa ya ce, “Ku fada min sunan wani amma ba Baba Mu’azzam ba. Babu yadda za ayi Baba Mu’azzam ya aikata abinda ake zargi. Me yasa zaku zarge shi? Mene ne hujjarku? Kumaaa..”
Cak ya dakata a lokacin da ya tuna kamannin Naufal da Haidar, haka suna kama da ‘yan gidan su Umma. Can kuma ya tuna ai Baba Sani Kanin Umma yana can Kasar waje da iyalansa. Baba Sani biyu ne, akwai a Www.bankinhausanovels.com.ng dangin Abba, akwai kuma a dangin Umma. Na kan titi a gabansa wani abokin Alhaji Mu’azzam ya kira shi da sunan. Amma ta yaya Malami kamar Alhaji Mu’azzam zai iya aikata wannan rashin imanin? Kai bai yarda ba, ba zai taba yarda ba, babu hujja mai Karfi a cikin wadannan hasashen. Kansa a daure ya ce, “Amma mene ne hujjarku na cewa Baba Mu’azzam shi ne mahaifin Nasreen?”
Barrister Tajjud ya watso masa hotuna, sai a lokacin ya dubi hotunan da suke watse a gabansa. Ga mamakinsa, hoton Baba Sani ne, sai hoton Alhaji Mu’azzam wanda tare da Baba Sani aka dauka, abin mamaki har da shi a cikin hoton yana Karami. Ba zai taba mance lokacin da aka dauki hoton ba, a wata ziyara da Baba Sani ya dauke shi suka kaiwa Baba Mu’azzam, kasancewar Baba Sani shi ne dan gaban goshin Baba Mu’azzam. Hotunan Saudat ya kafe da idanu yana jin zafin rabuwa da ita. Kafin ya samu ya dawo hayyacinsa, Alameen ya mika masa littafin da Saudat ta yi ta rubuce-rubuce da turanci. Shafukan ya dinga budewa duk labaran soyayyarta ce da Baba Sani, sai kuma shafin da ya dauke masa hankali, shi ne shafin da ta rubuta sunan Alhaji Mu’azzam da manyan haruffa. Ya kasa dagowa saboda tashin hankalin da ya tsinci kansa.
Wannan karon Ashmaan ne ya ci gaba da magana, “Mun ki bude littafin nan da ka bamu ne, saboda muna son mu yi amfani da Karfin KwdKwalwarmu, domin wannan wani abu ne mai rikitarwa. Dukkan mu =mun_ yarda_ da Kwarewarmu shi yasa muka hada kai babu dare babu rana sai mun gano wanene Www.bankinhausanovels.com.ng mahaifin Nasreen. Alhaji Kabir ya bamu wahala, mun kasa gane komai akansa, har sai da muka hada masa tarko kuma ya fada. A lokacin da ya kiran domin ya ci gaba da yi min barazana sai na gaya masa, muna da masaniyar tare da Alhaji Sulaiman suke aiki, don haka zamu zayyano sunan su, sai hakan ya daga masa hankali, wanda a zahiri bamu san suna da alaKa ba, kawai Case din su Alhaji Sulaiman ya yi kama da irin Case din su Nasreen. Da haka muka samu suka yi ta bin mu, Suna son mu gana, sai na yarda da ganawar, ta hanyar hada tafiya a tsakaninmu mu dukka, kuma kowa ya tafi da shirinsa. Cikin ikon -Allah bayan mun hadu mun tattauna, ashe sun bi bayan Mahbub, wanda babu wanda ya ankare sai saukar bindiga a dantsen hannunsa.”Sulta ya dubi Mahbub kansa a daure yadda babu wanda ya taba gaya masa, haka kuma bai taba sani ba. Tajjudeen ya ci gaba da cewa, “Abubuwa sun faru mas’ yawa, a dalilin neman shaidar wanda , ya yiwa Anti Saudat fyade. Abin burgewa a ranar Khamis ya bi bayan Alhaji Kabir ya kuma ga ina ne mazaunin su a duk lokacin da suka kwaso yara, domin zuwa yi masu fyade.” Sultan ya riKe kansa da Karfi daga bisani ya dubi Tajjud cike da tashin hankali ya ce, “Kana nufin fyaden Kananan yara? Har da Baba ake yi wa yara Kanana fyade?”
Ashmaan ya amshe maganar, “Kwarai kuwa. Baba Mu’azzam shi ne babban wanda ke
turawa a samo yara ‘yan shekaru biyar ko sama da hakan. Haka a kowacce rana yana aikata fyade ga Kananan yara sau biyar ko sama da hakan. A ranar da muka gane Baba Mu’azzam ne, mun shiga rudu da tashin hankalin, ta hanyar da zamu iya sanar maka. Haka mun bude littafin mun samu dukkan bayanan da muke nema. Yaran aikinka da ka watsa su anan Kawo, sun samo amsa dai-dai da irin namu, mu muka hana su gaya maka komai. Haka na sami Nora na nuna mata hoton Alhaji Mu’azzam ta tabbatar min da shi ne. Don haka kamannin da kake gani a tare da Haidar da Naufal, da gaske ne, jini daya ne, haduwar jininku shi yasa ka dage sai ka taimaka wa Anti Saudat. Mun yi ta kauce maka ne dan bamu son ka san abinda ke Www.bankinhausanovels.com.ng faruwa da wuri. Da fatan a yanzu zaka sami Umma domin ta amshi ‘ya’yan dan uwanta hannu bibbiyu?” Sultan ya koma ya zauna shiru.. Bai samu ya iya magana ba, sai da ya dauki wasu ‘yan mintuna, sannan ya ce, “Mahbub ka tafi Kaduna ‘ gobe, ka shirya min motar ‘yan sanda, zan Karaso gidan mu insha Allahu, akwai abinda zan yi.” Gaba daya suka dube shi, ba su taba tunanin zai amince da hukunta Baba Mu’azzam da wuri haka ba. Sultan ya dube su yace, “Za ku iya biyo ni mu je mu Karasa aikin nan tare. Zan kama Baba Mu’azzam zan kuma tabbatar da kotu ta hukunta shi, ko da kuwa hakan yana nufin rabuwar shi da gidan duniya ce.”
Sultan ya dubi abokansa da yake jin su tamkar jininsa. Yana son ya yi masu godiya, sai dai ya san babu wanda zai so hakan. Don haka suka yi Sallama kowa ya shiga motarsa suka kama hanyar gida, a bisa sharadin goben a Kaduna kawai za su hadu. Sultan ya dai-daita muryarsa sannan ya daga waya ya kira Baba Mu’azzam a waya, ya tabbatar masa ya kashe maganar, amma kuma yana son gobe ya je gidansu ya roki mahaifiyarsa ta Kyale shi da matarsa Nasreen kada ta raba su. Babu musu Baba Mu’azzam ya amince da abinda Sultan ya roKa domin yana ganin ya gama rufa masa asiri tunda ya kashe Karar da ake son danganta shi da ita.
A ranar Sultan ya kasa barci, ya kasa zaune ya kasa tsaye, a bakin windo ya tsaya yana dogon tunani. Umma ta tsine masu yafi a Kirga, ta ce zuri’arta tsaftatattu ne, na wasu ne banza. Ta ce ta tsani mara addini, bayan mara addinin
tafi dan uwanta kamun kai. ‘tace ta tsani mazinaci, sai ga nata mazinacin da yara Kanana yake aikata irin nasa zinan. Umma ta tsananta tsanarta ga zina, ta yi tirr ta yi Allah wadai da mazinaci. Ta Kyamaci Saudat da abinda ta Haifa. Ji yayi an tabashi shi, bai waiwayo ba, ba shi da alamun kuma waiwayowan.
Nasreen ta goge hawayenta ta saita muryarta ta ce, “Dee me ya hanaka barci? Ko nice na bata maka?”
Juyowa ya yi gaba daya yana jin kunyar hada idanu da ita, kasancewar zuri’arsa ce ta ci mutuncin mahaifiyarta, dukkan halin wahalar da mahaifiyarsu ta shiga, a dalilin dangin Sultan ne, yana duba Www.bankinhausanovels.com.ng girman laifin fyade, da kuma kisa. A lokaci guda kuma idan ya tuna Karshen Kiyayyar Nasreen da Umma ya zo Karshe, duk lokacin da za ta ci mutuncinta, za ta tuna da alaka mai girma da ke tsakanin su. —
Murmushi ya Kirkiro mata, “Ki je ki kwanta gobe insha Allahu, za mu je Kaduna.” Kwantar da kanta ta yi a Kirjinsa, dole suka shiga dakin tare, suka kwanta. Kowannen su da irin tunanin da yake yi, haka ko da barci yake barawo bai ci nasarar sace su ba. Da sassafe ya dauki Nasreen ba tare da yayi Sallama da Zakiyya ba, suka wuce Kaduna, da ‘yan sandansa. Umma suka samu tana ba masu_aiki umarmmin abubuwan da za su yi. A lokacin Naural yana zaune ya yi tagumi, idan ka Kura masa idanu zaka ga hawaye kwance a_ fuskarsa. Nasreen ta Karaso gabansa da sauri tana tambayarsa, “Me ya faru? Naufal kai da waye?”
Umma ta dube ta cike da bacin rai, “Shi da uwarki ce, dan ba zan ce ubanki ba, tunda babu uban. Ni ce nan nace ba zan iya zama da kato a cikin gidana ba, ya tattara ya koma Makaranta da zama, ban ga dalilin zama da ‘ya’yan shegu a wuri guda ba. Kai kuma Sultan ka tabbata. Nasreen ta dawo kenan zan san inda za a sama mata ta zauna. Wallahi na tsani yaran nan, ga su kamar mayu, sun Ki barin mu.”
Nasreen tasa kuka, Sultan ya dubeta a lokacin da Abba yake fitowa, domin duk ya ji furucinta. Sultan ya ce, “Ku daina kuka Nasreen, Umma bata tsaneku ba, hasalima ita ce wacce za ta fi son ku fiye da kowa, domin ku din ba dolen Abba ba ne, ba dole na bane, amma dolenta ne.” Umma ta bude baki cike da mamakin furucin Sultan, haka ma Abba ya tsura masa
idanu yana kallon damuwa cike da fuskar Sultan. A lokacinne kuma Hafsat ta fito da gudu tana sheKa amai. Duk suka bi ta da kallo. Tana gama aman, Sultan ya karaso kusa da ita yana mata sannu, ya ce Nasrcmeen ta zo su jesu kaita asibiti. Hakan yasa duk suka zauna cikin zulumi, ita dai Umma bata kawo komai a ranta ba, Sultan ya dauketa sai asibiti.
Suna nan zaune aka fito da sakamakonta tana dauke da ciki. Nasreen ta dora hannu a kai za ta fara kuka, Sultan ya Harare ta, dole ta ja bakinta, amma duk da hakan sai da hawaye suka wanzu a fuskarta. Hafsat kuwa hannu ta dora a baki tana ja da baya tana kuka. Sultan ya rike hannunta da Karfi ya wuce ya jefa ta a cikin mota. Ji yake kamar zuciyarsa za ta faso Kirji saboda azaban zafin da take masa. Kukan su kawai yake saurare ba tare da ya iya furta komai ba. Suna isa gida suka sami Abba Baba Mu’azzam, Baba Sani da Umma suna zaune suna karyawa. A falon ya watso da Hafsat yana yi mata wani duba. Umma ta dube shi cikin rikicewa ta ce. “Lafiya kuwa? Menene?”’ Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan bai yi magana ba, ya dubi Baba Sani, wanda bai ma san ya dawo Kasar ba. A lokacin Naufal ya shigo yana duban Nasreen da ke kuka. Shi kansa Baba Sani kafe su ya yi da idanunsa yana mamakin = irin’ wannan kama. Baba Mu’azzam ma yau dai ya Kare masu kallo ba tare da ya furta komai ba.
‘Umma ta dubi su Naufal tace “Yau naga masifa. Tunda nan babu ubanku ko danginsa, sai ku fice ku bar ‘ya’yan dangi muyi magana ko? Yaya ka dai ga abinda nake gaya maka ko? Da kake cewa in barsu tare, in dai Sultan ya zauna da ‘ya’yan mazinaciyar nan babu ko shakka watarana sai sun shafa mana masifa a cikin dangi.”
Abba yai yi magana, Sultan ya dakatar da shi da hannunsa. Yana jin yau zai gaya wa mahaifiyarsa gaskiya sai dai ta tsine masa. Ya waiwayo yana duban naufal da ya kamo.hannun Nasreen suka yi hanyar fita, dukkansu kuka suke yi yace, “Kai Naufal ku dawo, akwai danginku anan, kuma nan gidan gidanku ne, zaku iya sakin Jiki ku y? abinda ‘ya’yan Baba Mu‘azzam za su
Umma ta zabura ta ce, “Karya kake yi Abdullahi! Babu yadda zaka hada ‘ya’yan Kwarai da shegu. Na kula rashin kunyarka sake girma yake yi, ni kuma zan sauke maka.” Sultan ya Karaso gaban mahaifiyarsa ya ce, “Umma ki gafarceni, amma su Nasreen ba su da gidan da ya wuce nan. A yau kuma zagin da kike yi masu akan basu da uba, su je su nemi uban su, mun jajirce Kwarai mun nemo masu_uba. Nasreen, Naufal ku zo Baba Mu’azzam shi ne mahaifinku, shi ne wanda ya yi wa mahaifiyarku fyade, shi ne wanda ya tura a_ kashe mahaifiyarku saboda kada asirinsa ya tonu. Baba Sani shi ya so ya auri mahaifiyarku, saboda
Kaddara ta sameta ya gujeta a lokacin da ya kamata ya kusanceta, ya nuna mata kulawa, ko dan darajar addininmu da ta shiga. Umma kin jima kina tirr da mazinaci, kin jima kina aibata mazinaci, kina kasa yi masa addu’ar shiriya, saboda Baba Mu’azzam malami ne, shima ya tsani mazinaci. Sai ga ‘ya’yan shegu sun zama jininki, Hafsat kuma ta dauko maki abin kunyar da har mu mutu ba zai daina bin mu ba, Hafsat tana dauke da cikin shege a jikinta.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Baba Sani ya mike zumbur, Abba ma ya mike, haka Baba Mu’azzam shima ya mike. Nasreen da Naufal suka dubi wanda aka kira da mahaifin su duba na tsana, ba su taba jin tsanar mutum kamar mutumin da ke tsaye cikin shigar mutunci da sunan mahaifin su ba. Umma ta daga hannu ta wanke shi da mari, tana dubansa. “Kai har ka isa ka ci mutuncin Yayana uwa daya uba daya? Sultan ka cuceni, ba shi ka ci wa mutunci ba, ni mahaifiyarka ni ka wulaKanta.”
A jejjere su Ashmaan suka shigo, fuskarsu babu wata rahama. Sannu a hankali suka warware masu komai
Baba Sani ya dubi Baba Mu’azzam ya ce, “Yaya ka cuceni, har gobe da soyayyar Saudat nake rayuwa. Na rabota da kowa nata na kawota cikin addinina, shi ne ka zagaya ka wulaKantata, ni kuma na kasa yi mata uzuri. Sultan baka fadi Karya ba, haka dukkan bayananku ya gamsar da ni. Yanzu ‘ya’yan Saudat ne wadannan? Daman cikin jikinta jinina ya yi mata? Datun lokacin ta gaya min da ban barta ta wulakanta ba.” Abba ya dubi Umma cike da fushi ya ce, “Wallahi kin taba fuskar Sultan na Karshe, idan
kika sake Kofarin marinsa, zan nuna maki kuskurenki. Kin ji kunya Salma! Yanzu ne kike girban abubuwan da kika shuka. Mazinaci kika tsana? Ga ‘yarki nan manne da abin kunya. Kin tsani ‘ya’yan shegu? Yayanki ya Haifa maki, sai ki jira haihuwar Hafsaat, domin babu mai zubar da cikin nan. Nasreen da dan uwanta sun sha gori, ashe ke ce kike dauke da abin gorin. Kin wulakanta ‘ya’yanki ba tare da wani daga cikin mu ya tayaki ba. Kin jima kina neman ubansu, to ga uban su nan a gabanki. Malam Mu’azzam ka _bani mamaki. Ban taba tunanin hakan ba, anan har da kai ake haduwa ana zagin mazinaci, a maimakon addu’a da fatan Allah ya shirya. Kun “tsani wadanda suka tuba suka koma addininku, amma baku tsani wanda ya keta haddin wacce ba addininku daya ba. Duniyar nan ina za ki damu? Yau wacce irin rayuwa muke ciki ne?
Sultan da ke jin bakin ciki yana cinsa ya duKar da kai yana magana, “Babu yadda ban yi da Umma ba, akan su Nasreen amma taKi saurarena. Akan ‘ya’yanta ta wargaza gidan, ta ce ba zamu zauna lafiya ba. Bansan su Nasreen jinina bane, na damu sai an taimaka masu. Umma kullum maganganun da kike fada akan su
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG