RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Nasreen ta ce, “Kullum sai na yi maka  maganar ibada, amma sai kayi fatali da maganata, ka nesanta kanka da Allah shiyasa wannan abubuwan suke ta faruwa da kai. Kadage da addu’a ka yaki duk mai nufinka da ; sharri.” Ya ce, “Babu komai zan sake dagewa, idan zan je Masallacin sai in ji kamar ansa igtyoyi andaure ni.” Suka sake yin shiru, can yace “Barci nake ji ko za ki raka ni?” Bata karga mayana ba, wayarsa ta dauki kara. Ganin lambar Umma yasa ya dauka, “Gidan uban wa kaje? Ashe da kai za a tafi lagos din shi ne bani da mutuncin da zaka gaya min?” Sultan ya shafi kansa kamar tana ganinsa ya ce, “Umma ki yi hakuri don Allah, gobe insha Allahu zan dawo.” Umma ta ce, “Ya yi maka kyau Sallamammai. Saura ka takura mata tunda kana sane aiki za ayi mata.” Umma ta fada haka cike da damuwa da addu’ar kada Sultan ya aikata wani kuskure da zai hada jininta da shegu. Sultan ya dubi Nasreen yana sauke wayar, yasan ta ji dukkan abubuwan da Umma take gaya masa, sai ya share kawai Www.bankinhausanovels.com.ng 
Da daddare kowannen su suna dakin su, Nasreen tana kwance a Kafafun Sultan yana aika sako ta Email dinsa. Bayan ya gama ne ya daga ta ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito, itamia ta shiga tayi wanka da ruwan da ya tara mata ta nufi ‘yar Jakarta ta shafa man Kamshin da ya karbo mata daga shagon Jafar, ta shafe jikinta. Kamshin yasa ya dago yana dubanta da Katon Hijabi a jikinta. Murmushi ya Kwace masa, gaba daya ya fara mance sakon me yake aikawa

ZAMU TASHI 

cikin wayarsa? Da kansa ya tako ya jawo ta ‘ gabadaya jikinsa tayi luf’a Kirjinsa. “Babyna ina son Kamshin nan, idan naji rikitani yake yi.” Yana magana ne yuna aika mata sakonni. Ita kanta Wasu maganganu take yi wanda bata san kansu ba. Kai tsaye suka yi wa kansu makwanci a faffadan gadon suna jin wata natsuwa tana shigarsu. Da gaske sun yi kewar juna, Sultan ji yake kamar ya yi shekara rabonsa da ita. A hankali ya yi mata magana a kunne, “Baby kinyi kewata?” Ba ta yi magana ba, sai daga kanta da tayi yace, “Ok nuna min irin kewata da kika yi sai in yarda Kunya ta sa ta cusa kanta a Kirjinsa tana ‘yar dariya, a lokaci guda tana zakuda kafada alamun ba za ta iya ba. Washegari

bayan sun karya ne suka hau shiri babu ji babu gani. Ita dai Nusreen gani take yi kamar ma ba za ta sake dawowa ba,Www.bankinhausanovels.com.ng kamar ta tafi kenan. Da suka isa filin jirgi ne idanunta suka kawo hawaye, yasa hannu ya dauke su, ya kamo kafadanta, “Me yasaki kuka? Ko baki gaji
jiya bane insake mayar da ke gado in yi maki abinda yafi hakan? Kwanciya ta yi a jikinsa tana murmushi mai hade da hawaye, tana girgiza kai, sannan ta sa dan yatsanta ta ce, “A’a kai ne bana son intafi in barka. Ka kula min da amanar kanka, ka ci gaba da yi wa Umma biyayya. Daga Karshe ka kiyayi shiga hakkin Allah. Allah ya dafa maka a dukkan lamuranka na alkhairi, ya nesantaka da dukkan wani sharni. Addu‘ar iyaye tana tare da kai, bana tunanin ze ka tabe“Ina son ka Dee, na san kasan hakan kuma zaka ci gaba da riKe hakan a zuciyarka, ko bayan raina. Sai watarana.” Ta Karashe muryarta tana rawa. . Hannunta ya kama dukka biyun yana duban su masu kyau da haske. Ya manna masu kiss ‘ wanda har sassanyar yatsunsa suka sauka abisa hannun. Ta ji sanyi har cikin zuciyarta, hakan ya haifar mata da sakin ajiyar zuciya a bayyane. “I love you too, Baby Girl.” Bata iya sake yin magana ba, ta juya abinta, tana jin wasu hawaye sabbi suna sauka daga idanunta. Naufal ya Karaso ya rungume Sultan, ya ce “Ka cika dukkan sharuddan kasancewarka Uba. Allah ya biyaka da gidan Aljannah, ya sakawa dukkan mutanen da suka yi sanadin tafiyar ‘yar uwata.
Ba zan manta wannan abun ba. Mum gode Father.”
Ya sake rungume shi hawayensa suna ci gaba da sauka a jikin Sultan. Gaba daya jikin Sultan ya muta ya rasa meke masa dadi? Ya yi Karfin halin dago shi Www.bankinhausanovels.com.ng yana duba shi, tare da share masa hawayensa, “to maza azo a wuce saura kaje kana yi masu Kauyanci don nasa a daukar min dukkan abinda ke faruwa acan. Kai ga mai “yar uwa ko? Maza wuce kada a tafi a barka kukanka ya fara, dan wannan kukan ta gulma ce.” Naufal ya yi dariya shima. Alameen ya Karaso a jokacin da Jidda take rike da Nasreen. Suka mikawa juna hanno suka gaitsa tare da rungume yuna. Sultan’ ya fara magana cikin damuwa, “Prince ba ni da abinda zan ce sai Allah ya biyaka. Kayi min dukkan abinda wani dan uwanka ma ba zai iya yi maka ba. Kun nuna min Kauna tunda kuka nunawa Nasreen. Kasan komai ba sai na sake tunatar da kai ba, ka kula min da Nasreen. Na gode da wannan sadaukarwar.” Al-ameen ya yi murmushi, “Ba wannan ne a gabanmu ba, samun lafiyar idanunta sune babban matsalolin mu. Idan kana gode mana sai muga kamar bamu cika sharuddan zama ‘yan uwa ba. Ka dinga cin abinci sosai Abdullah, domin ka rame da yawa, ya kamata Nasreen ta bude idanunta ta ganka kafi da cika da kwanciyar ‘Rankali. Ka bar damuwa da Zakiyya idan ba haka ba, za ta iya kasheka ba tare da ta yi asara
ba.” Sakin juna suka yi yana tabbatar masa zai yi abinda ya ce masa. Ba ya son yin Sallama_ da Jidda don haka ya ce wa Al-amecn, “Ka fayawa ‘yar Kauyen matarka, saura ta je can ta ga turawa ta manne masu tana cewa, ‘yan uwan mamanta ne, ko kuma ta ga mutum ta yi zaton gunki ne tana shafa fuskarta.” Al-ameen ya yi murmushi yana ccwa, “Wallahi ka ci bashi za kuma ka biya shi.” Haka suka tafi jirginsu ya daga, Sultan kuma ya bi jirgin da ya yi booking ya koma Abuja cike da damuwar rashin Nasreen. A can gida bayan Umma ta gama waya da .Sultan Zakiyya ta fito tana waKe-waKe saboda ta ji lokacin da Umma take waya da Sultan, kuma ta kira shi yaKi dagawa, don haka ta fito da rashin mutuncinta. Kafar Umma ta take da Karfi Www.bankinhausanovels.com.ng
Umma tasa Kara, hakan yasa Hafsat fitowa da. tana duban Umman. Jin irin sayin da take yi wa Zakiyya ne ta fahimi abinda ke faruwa, don haka ta dora mata tafi a fuska tana huci. “Ke uwata ba sa’arki ba ce. Butulu kawai mun yi maki rana kin yi mana dare. Ki bar ganin ana Kyaleki wawuya wai idan an tambaye ta wai tana da ciki, bacin mun san komai babu komai a cikin. Ai shi ciki ba a Karyarsa domin nan da watanni uku dole ya bayyana kansa.” Zakiyya ta yi kukan kura za ta shako Hafsat
Hafsat ta nuna ta da yatsa, “Idan kika yi tsautsayin kwatanta hakan zan baki mamaki, don Wallahi sai kin koma gida kin yi jinyar kanki. Kada kuma ki ce ban gaya maki ba.” Dole Zakiyya ta dakata da abinda ta yi ninya, ta koma daki tana kuka ta gayawa uwarta, hakuri ta bata ta ce ta barsu tana nan tana sabon shiri akan su. Sultan yana isowa gida ya sami Umma ta gama shiryawa tsaf tana zaman jiran Sultan. Yana ganin abinda ke faruwa ya dubi Umma cike da mamaki ya ce, “Umma ina za ki je?” Umma ta fara hawaye ta ce, “Sultan ni zan tafi. Zakiyya ta ci mutuncina a gidan nan, haka
kaima baka dauke ni a matsayin uwa ba. Zan koma gun mijina na tabbata shi kadai yake sona ko da kuwa nayi wani mugun abu ne.”
Zakiyya ta fito tana taunar cingam, ta dubi Sultan ta mika masa takarda fara Kar da biro, “Ka sake ni ba zan iya ba. Kuma cikin nan zubar da shi zan yi. Ba zai yuwu wasu can su dake ni baka ce komai ba, haka Salamatu ta ce za ta kai hannu jikina. Dubi fuskata Hafsat ta mare ni.” Sultan ya dubi fuskokin kowa ya tabbatar da ba Karamin abu akayi ba. Ya riga yasan Zakiyya ‘yar dambe ce ta Karshe don haka kome za a ce ta yi ba zai musa ba. Yana son fara ba Umma hakuri domin zuwanta Kaduna wani tashin hankalin Www.bankinhausanovels.com.ng ne da zai hana shi samun natsuwa. Haka yasan Ummansa tana iya tsine masa akan dai kishiyar da za ta tarar. Don haka ya durKusa yana roKonta kada ta koma yanzu, ta bari ya sami natsuwa agun aiki a lokacin sai ta koma. Da Kyar ya shawo kan Umma, ita kuwa Zakiyya dubanta ya yi ya ce, “Wace ce kuma mai sunan da kika ambata?”
Ta dube shi sosai ta ce, “Wai Salamatu? Ga ta nan a gabanka.” Sultan ya mike cike da fusata zai yi kanta, Umma ta girgiza kai, “Kada ka taba ta ka barta da halinta, zan je Kadunan har gidan uwarta. Kuma ni ba ni ta kira kai tsaye ba, uwarta Ladidi ta kira. Shashasha wacce bata san ciwon kanta ba.” Zakiyya ta juya ta tafi tana taunan cingam da Karfi yana bada wani sauti. Shi dai Sultan yana gama lallaba Umma ya zayaya ya kira Abba ya kwashe komai ya gaya masa, Abba ya saki ajiyar zuciya yace“Sultan ka Kyale ta ta dawo nima ina son dawowar nata, – gara tasan komai ta yi abinda za ta yi kowa ya daina fargaba. Idan muka jure babu shakka zai zo ya wuce. Dole duk boye-boyenka watarana za ta sani. Zakiyya kuma kayi ta hakuri da ita ita kanta wataran sai ta yi danasani.”
Sultan ya amsa yana cewa, “Abba ko za ta zo ba zan bar ta ta dawo yanzu ba, ina cikin damuwa abubuwa duk sun Kwace min. Ga Office dina ina fuskantar barazana akan wani Case na fyade da aka yi wa wata ‘yar yarinya, so suke su bani kudi saboda kada sunansu ya baci, ni kuma naki karbar kudin, shi ne da su da Ogana suke aiko min da barazana. Kankat daga can sama gargadi ake yi min. Ni kuma na yi alkawarin ko wannan ne dalilin cire kakina sai na dau mataki a kansu.” Abba ya jinjina kai, “Hakane Babana Allah ya taimaka ya dafa maka. Ina Kara gargadinka da ko ni mahaifinka ka kama da aikata dokan da ta sabawa aikinka, ka kama ni ka hukunta ni daidai da laiifina. Allah ya yi maka albarka.” Sultan ya ji dadin furucin mahaifinsa haka yana samun natsuwa ne a duk lokacin da ya sanya masa albarka. Haka suka sauke wayar sannan ya nufi cikin gida wurin Zakiyya. Bai wani sha wahalar lallashinta ba, domin ya gaya mata ya daina lallashin mace, hakan yasa ta yi  tunanin ko asirin ya yi sanyi ne? Dama kuma asiri sai dai ka dora, amma Www.bankinhausanovels.com.ng aikinsa kwana arba’in ne kawai, ya tashi aiki. Tunda Zakiyya ta riKe shi a daki ta hana shi fita, hankalinsa yana kan su Nasreen, haka yana kallon kiran waya da lambar waje, mai dauke da +44 ya tabbatar da Code din London ne don haka ya ki dauka ta gagare shi. Tafiyar awa shida da minti kusan arba’in da uku ya kawo su Kasar London. Kai tsaye aka
nufi da su shahararren Hotel din Marriot Hotel wanda babu nisa a tsakaninsa da eye Centre din da za ayi mata aiki. Tana jin Naufal da Jidda suna santin wurin amma ita babu idanun da za ta gane haduwar wurin, sai dai ta shaki iskan Kasar. Kai tsaye suka nufi gun Abokinsa Dr. Sadiq da ya iso da kansa yana murmushi.
Bayan sun gaisa ne ya dubi Nasreen ya ce, “Ita ce patient din namu? Al-ameen ya amsa masa, sannan suka shiga ciki. Jidda tana tare da Nasreen, Bayan sun gama cin abinci Jidda ta ce, “Wai don Allah ina kika samu wannan Kamshin ne? Tun a Najefiya nake son tambayarki. Idan kin zo da shi dan sammin in je dakin Abban ~ Muhsin nasan zai ji dadinsa.
Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wallahi ~ Yumnah ta bani a lokacin da na je gidanta, shi ne Dee ya ji Kamshin ya matsa sai da.aka basa lambar Jafar din ya yi tattaki ya tafi har Zaria, yasa Kanwar Anti Fatima Dan Borno ta je ta siyo masa, da yake ance ita kanta Anti Dan Bornon acan take siyayyan duk wasu Kamshi da take amfani da su. Idan kika je ma za ki iya haduwa da ita taje nata siyayyan.” Jidda ta zaro idanu ta ce, “Ko dai agunsa ne Anti Bintu take siyan kayan Kamshin jiki da na gyaran fata? Ita ma daga Zaria ake sako mata a mota.”
Nasreen da hankalinta gaba daya yake gun Sultan ta ce, “Shi ne ma, shima a Sabon garin Zaria yake, wai kafin akai Police Station. Kuma ya riga ya yi sunan da kowa ya san shi. Yanzu haka Yumnah ta ce min idan na dawo za ta ba ni wani sirri da ta siya a wurinsa, wai ba kowa yasan sirrin ba. Karin abin burgewa talaka ma zai iya zuwa da kudinsa kadan ya mallaki abinda yake so. Bari in dibar maki ki je za ki ba ni labari.”” Jidda ta ce, ‘“‘Lallai ma Yumnah wato so sone son kai ya fi. Yanzu duk yadda nake da ita bata kawo min wannan na gwada ba?”
Nasreen ta miko mata, kai tsaye ta fada wanka ta fito ta goga man ta shafa dan humran ta fito tana tashin Kamshi. Babu kunya Jidda ta shige dakin mijinta, ta bar Nasreen da dogon tunani. A lokacin ne kuma Naufal ya shigo hannunsa dauke da waya ya miKawa Nasreen ya ce, “Ki yi magana Dee ne yake kan layi.” Shi ma ya fice abinsa harabar Hotel din yana kallon yadda tsarin su yake abin akwai sha’awa da sanya nishadi. Yana sanya masoya a cikin wani hali na samun natsuwa.
Nasreen ta lume akan gadonta tana jin sany1 yana ratsata, ta fara magana cikin sanyi da ruda dukkan wanda ya _ saurari wannan murya, “Amincin Allah ya tabbata a gareka uban marayu. Da fatan zuciyar da na bari a cikin shauki cike da soyayyata tana cikin kwanciyar hankali da natsuwa?”’ Www.bankinhausanovels.com.ng
Sassanyar murmushi ya saki sannan ya bata amsa cike da kewarta da ke nuKurKusansa, “Wannan zuciya da kika tafi kika bari, kin barta ne cikin sonki da kewarki hakan ya taimaka wajen Kuntatawa wannan zuciyar. Me yasa ma bature bai fitar mana da yadda zaka zama tsuntsu ka je dukkan garin da ka gadama a lokacin da ka. so ba? Ai da yanzu na iso bisa gadonki na tayaki barci irin na Lagos.”
Murmushi ya subuce mata, ta sake jawo filon ta KanKame. “Anan wurin haka tawa zuciyar take ciki. Sai dai jin muryarka ya kore dukkan wani Kishirwa da ke cikin maKoshina, hakan ke nuna min ruwan da yake nema ne aka kawo akan lokaci kuma aka shayar da makoshin har ya gamsu.”
Ya gamsu da bayanan matarsa akansa, ya gamsu soyayya tana matuKar riKe aure, musamman ma idan ladabi yana ciki. Domin ladabin aure shi ne magin cikin aure, soyayya kuma ya goya masa baya ya zama gishirin da ke cikin aure. Haka suka ci gaba da hira cike da annashuwa, haka kamar ba kudi ake cirewa ba. Ya ce mata ta riKe wayar zai dinga kiranta. Ta yi godiya ta ajiye wayar tana jin natsuwa tana shigarta. Jidda ce ta shigo tana murmushi, sai dai Nasreen ba ganinta take yi ba, don haka ta yi shiru.
Jidda ta ce, “Wallahi muna dawowa Najeriya zan ziyarci shagon Jafar dinnan da kaina ba sako ba. Kai amma dai Yumnah ta ci amanar zaman tare, shegiya sai shige-shige ka rasa wa yake gaya mata irin Www.bankinhausanovels.com.ng wadannan sirrikan.” Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wa zai gaya mata idan banda ‘yar mutan Borno? Ita ta gaya mata komai. Shiyasa na gama kula kamar ta fi son Yumnah akan mu.”
Jidda ta girgiza kai, “Ke kike ganin hakan, amma ni nasan ta fi sona akan kowa.” Nasreen ta gyada kai “Zai iya yiwuwa. Yanzu na gama waya da Dee, ya ce yana gaida ku.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *