RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA

soyayya tana matuKar riKe aure, musamman ma idan ladabi yana ciki. Domin ladabin aure shi ne magin cikin aure, soyayya kuma ya goya masa baya ya zama gishirin da ke cikin aure. Haka suka ci gaba da hira cike da annashuwa, haka kamar ba kudi ake cirewa ba. Ya ce mata ta riKe wayar zai dinga kiranta. Ta yi godiya ta ajiye wayar tana jin natsuwa tana shigarta. Jidda ce ta shigo tana murmushi, sai dai Nasreen ba ganinta take yi ba, don haka ta yi shiru.
Jidda ta ce, “Wallahi muna dawowa Najeriya zan ziyarci shagon Jafar dinnan da kaina ba sako ba. Kai amma dai Yumnah ta ci amanar zaman tare, shegiya sai shige-shige ka rasa wa yake gaya mata irin Www.bankinhausanovels.com.ng wadannan sirrikan.” Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Wa zai gaya mata idan banda ‘yar mutan Borno? Ita ta gaya mata komai. Shiyasa na gama kula kamar ta fi son Yumnah akan mu.”
Jidda ta girgiza kai, “Ke kike ganin hakan, amma ni nasan ta fi sona akan kowa.” Nasreen ta gyada kai “Zai iya yiwuwa. Yanzu na gama waya da Dee, ya ce yana gaida ku.”

 ZAMU TASHI 

Ta nufi bandaki tana cewa, “Shi ya sa na ga fuskarki fes babu damuwa, sai fara’a kike yi, ashe soyayya kika sha.” Nasreen ta dan muskuta ta ce, “Ke kuma ruwa kika je kika ba shi kenan.” Jidda ta KyalKyace da dariya ta shige abinta.
Cikin dare Sultan ya kasa barci, yana kallon yadda Zakiyya take shakan barcinta minshari yana biyo baya. Gaba daya idan tana barci sai muninta ya sake fitowa. A cikin natsuwarsa ya mike ya fito

falonsa yana kaiwa da komowa, gaba daya ya rasa meke masa dadi? Yana son sake jin kalaman Nasreen, wanda yake masa kama da wacce take busan sarewa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wayarsa ya zaro ya danna layin da ya gaya mata ta rike wayar, yana addu’ar Allah yasa ta amsa ko a cikin magagin barci ne. Tunda yasan awa daya ne a tsakanin su da London. Ita kanta bata yi barcin ba, ta kasa samun natsuwa. Jidda kuwa tuni ta gudu wurin mijinta, daga cewa tana zuwa. Nasreen ta Kosa idanunta su bude tana son ganin Sultan, tana da burin ganin yadda Naufal dinta ya koma. Farin ciki ya Kara kamata, ta y! juyi ta sake Kankame filonta. Karar wayar ya ankarar da ita, ba tare da dogon tunani ba, ta lalubi madannin wayar ta danna ta kara a kunne. Kafin ta yi magana ta ji saukan ajiyar zuciyarsa. Ita ma bayansa ta bi da ajiyar zuciyar tana jin tarin natsuwa yana sake ziyartarta. “Na yi kewar muryarka. Na Kosa inganka na kasa mance zaman mu a Lagos na kwana daya tak! Sai nake jin kamar shekara muka yi.” Lumshe idanunsa ya yi yana sake cusa kansa a windo yana Karewa tsakar gidansa kallo da ya wadatu da Kwayaye masu haske. “Na fi ki tunawa da kwanan mu a Lagos, domin kina ta guduna, hakan ya rage mana jin dadin mu. Kina zaton zan yi maki wani abu ne? Babu abinda zan maki, ina sane da Kasar da za ki je, idan nayi maki hakan waye zai taimaka ya lallaba min ke kina narkewa ina lallabaki? Nasan abinda nake yi Nasreen, ina tattalin lafiyarki fiye da nawa. Bani labarin yadda kuka sami London.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta dan shagwabe ta ce, “Ba na gani Dee, bana iya tantance fari da baki a cikin Kwayar idanun nan nawa. Amma naji Naufal da Jidda suna ta kururuta Kasar. Ka bani labarin Kasata Najeriya su Umma suna lafiya ko?” Idanunsa Kyar akan windo yana mamakin ganin kamar ‘yan sandan nan dukkan su barci suke yi. Kuma barci irin wanda ba Karamin nisa suka yi ba. Sai dai bai kawo komai a zuciyarsa ba ya ci gaba da cewa, “Kasarmu akwai dadi sai dai kwanciyar hankali da sakin jiki kayi barci sai turai. Gidan ya yi mana fadi saboda babu majidadin cikin gidan.”
Murmushi ya Kwace mata, “Irin sarautar da ka bani kenan? Zan fi kyau da sarauniyar zuciyar mijinta.” “Uhm! Babu sarautar da ban baki ba, ni da na baki sarautar Naufal gaba daya?”
Nasreen ta tuntsure da dariya, hakan ba Karamin faranta masa ya yi ba, ya jima bai ji dariyarta haka ba. Sultan ya shaki numfashi ya fesar a cikin wayar, wannan numfashi shi ya yi sanadiyyar mutuwar duk wani abu da ke jikinta, ya saukar mata da wani irin kasala. Itama ta sakar masa nata, a lokacin da bata zaci fitowarsa ba. Hakan yasa dukkansu suka yi shiru na wasu lokuta, wanda da ba dan saukar ajiyar zuciyarta ba, da zai iya cewa babu ita akan layin. A wannan lokacin ne kuma ya ware idanunsa masu tsananin haske ya watso a waje yana sake nazarin gidan. Motsi ya ji a in da bai kamata ba, hakan ya gane an shirya masa wani abu a cikin gidansa, cikin gaggawa ya koma ya dauko
bindigarsa ya fice a hankali. Shi kansa bai san bai kashe wayar ba, kawai mayar da wayar ya yi a cikin aljihu ya labe sosai, ta in da babu wanda ya isa ya ganshi. Ta nan ne yake hango mutane masu bakaken kaya, mamaki ya kama shi, ya kafe su da ido.
Yau lalacewa ta yi lalacewar da barayi za su tako su shigo har gidan AIG? Ta ya ya suka ci nasarar sanya masu gadinsa barci? Www.bankinhausanovels.com.ng
Baya buKatar kira a zo daga office shi kadai zai iya da su. Tuni zuciyarsa ta gaya masa daga inda suka fito, don haka ya sake samun Karfin guiwa. Kafafun daya daga cikin su ya saita a lokacin da suke KoKarin neman hanyar da za su shiga cikin gidan, ya danna masa harbi. Hakan ya gigita su, har suka yi zaton tabbas akwai wadanda maganin barcin bai yi masu amfani ba, sai dai idan suka tuna Karfin farin hodan da suka watsa suna da tabbacin ba tashin yanzu ba, sai dai idan akwai wasu a cikin gidansa. Amma kuma yawan ‘yan sandan da ke gidan an gaya masu ko su nawa ne, kuma gasu reras a kwance. Tunawa da Sultan din jan wuya ne ya sa duk suka sake gigicewa, suna KoKarin dauke wanda aka harba, suka sake jin harbi. Gashi ko ma waye
mai harbin ya Kware a saiti, indai ya harba sai ya sami mutum. Su Umma suka ji Karar bindiga don haka suka fito falon a gigice. Zakiyya ma jikinta yana rawa ta fito. Sultan ya dan waiwaya yaga Umma da Hafsat suna doso shi suna kuka, ya dan walwaya yana girgiza masu kai, “Umma ku koma ciki ku rufe Kofa insha Allahu babu abinda zai same ni.”
Hafsat ta fasa kuka ta yi bayan Sultan ta KanKame shi, Umma ma ta kama dayan hannunsa tana KoKarin jansa suna kuka, “Yaya ka taimake mu ka zo mu je mu Boye kada su kashe mana kai. Yaya ka zo mu je, ba zamu iya tafiya mu barka ba.”
Umma ta sake rike shi sosai tana fadin ‘‘Wallahi sai dai a kashe mu tare, ba zamu barka ka tafi ba, sai dai a kashemu.” .
Sultan yasan halin mata da gigicewa shiyasa bai so da suka tashi ba. Zakiyya kuwa tuni ta yi cikin daki da gudu ta rufe Kofa tana fadin  wani miji ba za ta kashe kanta ba, su dai da suka ga za su iya su tsaya. Sultan ya juya da su Umma suka shiga daki ya yi masu dabara ya rufe su ya fice tsakar gidan gaba daya. Nasreen ta fasa Kara tana Salati, fadi take yi “Shi kenan sun kashe min shi, ankashe Deeedi wayyo! Ashe turo ni kayi nan Kasar saboda akasheka? Naufal! Na shiga uku bani da idanu ina zan ga Naufal?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kuka take sha babu KakKautawa, ita Karan harbin da ta ji shi yake gaya mata ankashe Sultan. A can bangaran kuwa tuni sun ci nasarar guduwa sai suka bar wanda aka harba. Sultan ya fito yana duban mutumin idanunsa a rufe. Sai a lokacin ya tuna da wayarsa, haka kudin ciki bai Kare ba, ya daga ya mayar kunne yana fadin Hello! Sai dai baya jin komai sai sautin kukanta da irin kalaman da take yi tana fadin. “Ka san zaka mutu ne shiyasa ka turo ni nan? Wayyo rayuwata ta zama abar tausayi, waye zai sake zama gatana a gidan duniya?”
Kashe wayar ya yi tare da kiran Office din su, cikin gaggawa motar ‘yan sanda suka bayyana a gidansa. Yana nan tsaye aka tafi da shi, wasu suka tsaya a gidan, haka ya hana a taba ‘yan sandan ya ce a bar su har su tashi da kansu. Shi kuma ya koma ciki ya zauna a falon yana mayar da ajiyar zuciya. Sai da ya dan natsu sannan ya je ya bude Kofar su Umma da suka dami ko ina da ihu.
Yana budewa gaba daya suka fada jikinsa, ya ce, “Umma lafiyata Kalau don Allah ku daina kukan nan.” Umma ta ce, “Idan suka kashe min kai ba zan taba yafe jinin dana ba, Sultan duk tsaron da ke gidanka me yasa ‘yan fashi suka iya shiga cikin gidanka? Ina ‘yan sandan?”
Furzar da huci ya yi mai zafi sannan ya dawo falo ya zauna haka suka biyo bayansa kamar wanda zai sake bace masu. Wayarsa ya zaro ya kira Nasreen, tana jin kukan waya ta dauka hannunta na rawa, “Hello.” Yadda ya ji muryarta tana rawa yasa shi yin murmushi, ““Waye ya gaya maki an kashe ni? Kukan nan da kike yi kamar za a zare ranki na menene? Wa ya gaya maki har kin tabbata marainiya? Kina nan da gatanki insha Allahu, share hawayenki ki kwanta zamu yi magana gobe.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta kasa magana sai hawayen farin ciki da ke sauka a kumatunta. Ya katse wayar yana duban su Umma har yanzu hankalinsu baya cikin jikin su. “Umma turo su akayi akan wani Case da ake son dole sai na ci hanci. Ni kuwa ko rayuwata za su dauke ba zan bi su ba. Umma Case din fyade ne ‘ya’yanmu da Kannanmu ake Gatawa rayuwa. An yi wa babbar budurwa fyade
ta mutu bare Kananan yara wadanda basu wuce shekaru hudu ba? Umma a Kaduna a kowacce rana sai mun sami case din fyade idan yau mun sami na yara ‘yan shekaru hudu gobe zamu samu na ‘yan shekaru biyar, jibi za mu samu na ‘yan shekaru shida. Umma a haka za a yi ta bata rayuwarsu? Sannan ba za mu Kwato masu ‘yancin su ba, sai a nuna wa hukuma kudi ko kuma a dauki rayuwarsu? Bana jin ko mahaifina na kama da wannan abin zan iya barinsa, duk girman son da nake masa kuwa.”
Umma da tunda ya fara maganar idanunta suke bude saboda tsoro, ta gyada kai, “Na tsani mazinaci, mazinacin ma mai bata rayukan yara Kanana. Ina tare da kai Sultan ka Kwatowa – ‘ya’yanmu hakkin su. Ka tona asirin su duniya ta gansu. Mutanen nan-su suke bata mana Kasa. Na amince maka ka tafi ka Kwatowa bayin Allah hakkin su.” ;
Sultan ya sake samun Kwarin guiwa yanzu ya kula da babu Zakiyya, haka Hafsat tana Kudundune tana aikin kuka. Ya yi murmushi ya ce, “Hafsat zo nan kusa da ni. Ashe haka kike son Yayanki? Lallai yau na ji dadi tunda naga kulawar Hafsat akaina.”
Ba su san lokacin da suka yi murmushi ba, Anan falon suka yi barci shi kuma ya tashi yana Kwankwasa Kofar dakinsa da Zakiyya tasa key, Da Kyar ta bude sai da ya tabbatar mata da shine. Ko a yanzu ya gane su waye dolensa? Su waye suka shirya sadaukar da rayukansu akan tasa rayuwar. Bai yi barci ba, bai kuma yi mata magana ba. Kawai yana zama ta zauna ta hau taba shi. Tana cewa, “Wai kai ko irin wasa na ma auratan nan baka iya yi bane? Kullum fuskarka babu wani annuri.”
Sultan ya fizge jikinsa yana aikata mata wani irin kallo. “Ke wacce irin macece mara tunani? Ba ki iya bambance lokacin da mijinki ya ke cikin farin ciki da akasinsa? Ban iya wasan ba, idan za ki iya zama da ni a haka ki zauna idan ba za ki iya ba ga hanya Please! Kin ga ta inda Nasreen ta fi ki kenan, ita tana da natsuwar da take bambance lokacin wasa da_ lokacin lallashi. Duk da tana yarinya Karama amma ta fi ki hankali da sanin ciwon kai. Wasa kuma sai mace ta gyara kanta take samun yadda take so a wurin miji. Kada ki sake matsoni a lokacin da nake Kunshe da damuwa.” Yaja filo ya kwanta kawai. Karfin turarenta da ta yi amfani da shi
suka hade da warin jikinta suna bayar da wani irin tsami. Ji ya yi gaba daya ya tsani kansa, yana matukar kokari wajen yi mata kawaici. Dole ya yi alwala domin yin Sallah ya mika godiyarsa ga Allah, ya fice zuwa falo. Har asuba idanunsa biyu, yana karatun AlKur’ani domin ya sani yaKin da yake shirin tunkara ba abu bane mai sauki. Shiri yake na tonawa dukkan wanda yake da alhakin shigar masa gida asiri, ko waye shi. Ana kiran Sallar asuba ya fito zai je Masallaci ya sami ‘yan sandansa sun farka har
sauran sun yi masu bayanin komai. A nan suke cewa su ba su ji motsi ba, sai farin fauda da suka
gani ya bade ko’ina. Wasu ‘yan sandan suka yi masa jagora zuwa Masallaci, yana dawowa ya yi wanka a gurguje ya yi shirin zuwa office. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da isarsa ya kira Ashmaan a waya ya kira Mahbub da Khamis duk suka hadu a Office dinsa. Ya gaya masu dukkan abubuwan da suke faru ya Kara da cewa, “Akan case din nan ba zan bari rayuwata ta zama a cikin hatsari ba, bai – kamata in ci gaba da boye su bayan su rayuwata suke nema data iyayena ba. Don haka Ashmaan za ka iya zuwa ‘yan sanda su matse mutumin da na harba a Kafa, sai ya gaya mana wadanda suka turo su, ku buga a cikin Jaridarku daga ta hausar har ta turancin. Ba zan sake yin gangancin da nayi, har aka shigo gidana ana neman rayuwata ba. Na dauki hakKkin Umma da Hafsat, hatta Nasreen da ke can London sai da ta sha kuka har ta gode Allah, kalamanta sun bani tausayi, gani take yi na tura ta can ne saboda zan mutu. Don haka sai sun biya tashin hankalin da suka sa iyalina ta hanyar fanshe abinda suka shuka.”Khamis ya yi shiru can ya ce, “Sultan ka ba ni case din nan mana ya dawo hannun sojoji, ta yadda za mu kakkarya kayayyakin banza mu sake hade su.” . Ashmaan yace, “Ba za a yi haka ba, a dai tona masu asiri kawai.”
Mahbub ya saki ajiyar zuciya, “Wai kai ma kenan da kake sama da ni. Na tsani aikin dan sanda sosai, wasun mu‘su suke jawo mana zagi a duniya, ake hada mu ana cewa ba mu da mutunci. A yi yadda ya kamata din.” Cikin hukuncin Allah Ashmaan ya sami yin hira da mai laifin ya kuma samu abinda yake so, sunayen wasu manya ya kirawo daga ciki har da Alhaji Sulaiman da aka yi zaman meeting da shi, da kuma sunan Ogansa. Don haka kafin fitowar jarida Sultan ya kira Meeting da dukkan manyansu meeting din gaggawa. Ogansa yana ganin Sultan gabansa ya dinga faduwa.
Sultan ya tsaya a tsaye bayan ba su girma da ya yi ya fara magana cikin bacin rai, “Ku yi hakuri na kira wannan tattaunawan ne saboda in gaya maku abinda ke faruwa a tsakanina da Oga.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya kwashe komai ya gaya masu, ya Kara da cewa, “Kai ba ka isa ka hada baki da wasu a nemi rayuwata ba, baka isa ka sani inci hanci dole ba, idan kai za ka iya amsar kudi a kan rayukan ‘ya’yanmu da suke cikin matsala, ni . ba zan iya ba. Na kuma gaya maka a baya ba siyan kwalina na yi ba, a’a da Karfina.na shiga ‘ aikin.” Ya juya wajen babbansu ya sara masa ya ce, “Sir! Barin wadannan a cikin Kasa tare da kakin mu a jikin su tamkar Kara ruguza Kasar ce. Bayan Sultan ya gama jawabinsa ya zauna, a nan take aka yi ta tattaunawa cikin natsuwa babu wani kace nace aka ce a rufe shi, a cire masa kakin jikinsa, har sai an kammala bincike.” Sultan ya dawo gida cike da farin ciki, domin a ranar aka tura akamo su Alhaji

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *