RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 4  CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

                Www.bankinhausanovels.com.ng 




MUN TSAYA 

Sultan ya tsaya a tsaye bayan ba su girma da ya yi ya fara magana cikin bacin rai, “Ku yi hakuri na kira wannan tattaunawan ne saboda in gaya maku abinda ke faruwa a tsakanina da Oga.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya kwashe komai ya gaya masu, ya Kara da cewa, “Kai ba ka isa ka hada baki da wasu a nemi rayuwata ba, baka isa ka sani inci hanci dole ba, idan kai za ka iya amsar kudi a kan rayukan ‘ya’yanmu da suke cikin matsala, ni . ba zan iya ba. Na kuma gaya maka a baya ba siyan kwalina na yi ba, a’a da Karfina.na shiga ‘ aikin.” Ya juya wajen babbansu ya sara masa ya ce, “Sir! Barin wadannan a cikin Kasa tare da kakin mu a jikin su tamkar Kara ruguza Kasar ce. Bayan Sultan ya gama jawabinsa ya zauna, a nan take aka yi ta tattaunawa cikin natsuwa babu wani kace nace aka ce a rufe shi, a cire masa kakin jikinsa, har sai an kammala bincike.” Sultan ya dawo gida cike da farin ciki, domin a ranar aka tura akamo su Alhaji

ZAMU TASHI 

Sulaiman. Talakawan da Sultan ya taimaka masu suna ta neman ‘Sultan domin su yi masa godiya, amma ganinsa ya zame masu wahala. Yana can kwanaki biyu ya zama sai a hankali baya zama, ita kuma Nasreen har an fara duba idanun, haka sun sanya ranar aikin. A lokacin ta yi Kokarin ganin ta yi waya da Sultan ya kirata yake lallashinta akan yana wani bincike ne.

Al-amcen ya karbi wayar suka tattauna, ya Kara yi masa godiya akan irin dawainiyar da yake yi da Nasreen da Naufal ya ce babu komai. A zaman Nasreen da Jidda Nasreen ta Karu da ilimi kala-kala ta ji dadin wannan zaman, haka hankalinta ya kara kwanciya tunda ta fahimei Jidda macece mai ban Www.bankinhausanovels.com.ng dariya da saukin kai, a lokaci guda ta shiga cikin jerin mutanen da take son ganin fuskarsu. Hankalin Sultan bai dawo jikinsa ba, sai da aka yanke masu hukunci, duk da Alhaji Sulaiman bai fada masu asalin wanda yake aikata wannan aikin ba. Yanzu yana jin kansa

kamar an sauke masa wani nauyi. Yau Umma ta dage tana son zuwa gida, tana yawan yin mugayen mafarkai. Dole ya shirya ‘yan sanda ya ce su kaita gida ya kuma, ce zai zo gobe. Su Umma suka Www.bankinhausanovels.com.ng
tafi, gidan ya sake yi masa fadi gabansa yana fadiwa akan abinda zai faru a garin Kaduna, gani yake kamar ya shirya ya bi su, sai dai idan ya bi su abin zai fi kwabcewa. Yana zaune Zakiyya ta fito ta zauna kusa da shi tace, “Ka yi hakuri idan nayi maka laifi.”
Sultan yana son mace mai bada hakuri a lokacin da ta san ta yi kuskure, sai dai bai taba zaton Zakiyya za ta kasance daga cikin ‘irin matan nan ba. Babu musu ya ce babu komai, a ranar dole ya biye mata, yana mai jin Kunci a zuciyarsa. Yanzu tunanin zuwa London kawai yake yi, domin Al-amcen ya tabbatar masa da anyi aikin idanun suna sa ran za a bude idonun ko wani irin lokaci. Don haka ya fara shiri kawai ba tare da ya gayawa Zakiyya ba. Da gaske yake jin gidansa ya yi masa girma ya saba da hayaniyar gidan. A gefe guda gabansa yana faduwa akan mahaifiyarsa. Umma tana isa Kaduna ta ce wa Driver ya wuce da ita gidan Hajiya Ladidi, babu musu ya wuce da ita. A gida ta sameta tana shirin fita
Umma ta zabga mata harara, “Kin bani mamaki butulu. Ba ni Salma za a yi wa haka ba. Kin kai sunan Sultan gidan malamai saboda baki da kirki, kika zugo ‘yarki ta yi min rashin kunya ko? Zan nuna maki baki isaba in dai da gaske ni na haifi Sultan zan nuna maki Karfin ikon a hannuna yake. Zakiyya kamar ta bar gidan dana ta gama. Ke Hafsat juya mu tafi.”
Hajiya Ladidi ta kamo hannunta ta marairaice, “Haba Hajiya idan aka gaya maki zan sa Zakiyya ta yi rashin kunya za ki yarda? Kuma ni ban kai sunan Www.bankinhausanovels.com.ng Sultan wurin boka ba, gani nayi yadda yake wulakantata yana maki ciwo shiyasa nace bari intaimaka maki inrage maki wahala kin san dan yau ka haife shi ne baka haifi hali ba. Ai ba zan mance karamcinki ba.”Umma ta yi Kwafa ta ce, ‘Me yasa ba ki daukar wayata?”Ta sake marairaicewa, “Wallahi saboda zancen mijinki da na fada maki ne na san ki da kishi shiyasa.”Umma ta saki ajiyar zuciya, “Shi kenan babu damuwa, yanzu zan je gida idan na huta zan leKo” Hajiya Ladidi tace, “Naso kuwa muyi maganar yadda ya kamata ayi da Nasreen dinnan naji ance har waje ya turata aikin idanu. Yarinyar nan tana neman ta zame mana masifa.” Umma ta dawo da baya, “Wannan maganar sai mun zauna, da bakin cikin hakan na dawo Duk da ita ma Zakiyya ta Bata min rai sosai.” Hajiya Ladidi ta ce, “Ai ba ta gaya min ba, ta san halina sai in yi tattaki inci mata mutunci.” Umma ta ji dadin kalaman Hajiya Ladidi don haka ta tafi tana murmushi. Tana wucewa Hajiya Ladidi ta harare ta tace, “An gaya maki bari zan yi ki rabo ‘yata da gidan mijinta? Sai dai ke in raba ki da danki rabuwa ta har abada, muje zuwa.” A mota Hafsat take cewa, “Umma ni ban yarda da matar nan ba, Karya take yi tace bata san abinda Zakiyya take aikatawa ba.”
Umma ta yi shiru, bata san dalilin da yasa gabanta ke faduwa ba. Suna isowa gidan aka shiga kwasan kaya ana kaiwa ciki. Ta sa kai ta shiga falon. Mairo ta samu tana matsawa Abba Kafafu shi kuma yana duba Jarida. Umma ta shigo tana zare idanu, ita kuwa Mairo tana ganin Hajiya ta mike jikinta yana Bari. A natse ya ajiye jaridar yana Karewa Hajiya Salma kallo babu wata damuwa a fuskarsa, shi kansa bai Www.bankinhausanovels.com.ng san zai iya irin wannan jarumtar ba. “Salma saukan yaushe?” Sa’a daya ya ci yana matsayin mijinta, da babu abinda zai hana ta liliyo ashar ta dura masa. Hawaye suka fara gudu a fuskarta, Hafsat ma ta fasa kuka tana cewa, “Mairo kin cuce mu kinci amanar mu. Yanzu Abbanmu kike irin wannan zaman da shi?” Umma ta saki jakar hannunta tana duban Abba, domin ya fi ba ta mamaki. Ta yi magana cikin sanyin jiki, “Yanzu wannan ne yardar da kake nema a wurina? Ka cuce ni ka cuce ni da har na hada zuri’a da kai. Mazinaci wanda baya tsoron Allah.” Jikinsa na rawa ya mike yana nunata da hannu, “Kada ki sake kirana da mazinaci. Matsayinku daya da Maryama don haka nake sake neman tsari da aikata zina. Ai nasan kin tafi kin bar ni ne saboda in aikata abinda kike fada, sai dai Allah ya nesanta zuciyata ma da wannan tunanin, domin mutuncin ‘ya’yana nake ji ba mutuncinki ba.” Hafsat ta yi cikin daki da gudu tana rusan kuka. Umma ta yi kukan kura ta yi kan Mairo tana cewa, “Yau sai kin bar duniyar nan, sai kin daina cin amana daga kaina. Ni Mairo? In maidoki mutum ki ci amanata? Mijina za ki aura kina Kazamarki da ke? har kin isa in hada miji da ke?”Abba ya samu ya raba ta da jikin Mairo da Kyar. Jikinta yana kyarma ta shako wuyan rigar Abba, “Kai kuma shugaban munafukai! Idan baka sake ni ba yau gidan nan babu mai yin barci. Ka sake ni ko kuma dukkanku indauki mafi munin mataki akanku. Ni za ka yi wa kishiya? Kishiyar ma mai aikina? Duk matan duniyar nan baka ga-mace bane sai Mairo? Ka sake ni nace bakin munafuki.” Tana maganar tana huci kamar zakanya.
Abba dai bai ce mata komai ba, ya dubi Mairo ya ce, “Ke Mairo wuce dakinki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Mairo ta raba gefenta za ta wuce ta saki wuyan rigar Abba ta koma ta fizgo Mairo ta hau duka babu ji babu gani, tana cewa “Babu inda za ki je makira, sai kin gaya min wanda ya baki shawarar aure min miji daga zuwa Unguwa indawo. Fada min dan ubanki, dama kuna neman juna ne? Ba za ki gaya min ba sai na kashe kayan banza?” Abba ya dago ta ya dora mata mahaukacin mari wanda ya yi sanadiyyar fashewan gefen bakinta, amma bakinta bai mutu ba, gaba daya ta zama mahaukaciya. Marin da ya yi mata ya tsaya masa a rai, danasani ya shige shi a lokaci guda. Sannan ya dubi Mairo da ke kuka kamar ranta zai fita ya ce, “Maryama zo ki wuce. Idan kin cika mahaukaciya ki sake taba min mata, za ki ga irin wulaKancin da zan yi maki. Na yi auren ‘nan ne don inbata maki kamar yadda kika bijirewa umarnina, kuma burina ya cika. Idan takardarki kike buKata ki je dakinki zan kawo maki yanzu, domin ni daman na gaji da halayyarki.” Umma ta fasa wani kuka mai ban tausayi a lokaci guda tasa hannu tana goge Www.bankinhausanovels.com.ng hawayenta, “Ban yi mamaki ba, sunanka namiji ne babu abinda ba zaka yi ba. Kaddarar namiji waccece bamu sani ba? Cin amana agun maza wannene bakon mu? Don haka ina son a yanzu ka furta da bakinka ka sake ni ba zan zauna a gidanka ba, na gama zama da kai, ba zan sake yarda da da namiji ba, tunda kai Lukman kayi min haka. Allah ya isa tsakanina da kai mugu azzalumi.” Abba ya ce, “Duk naji kuma na amince, nima ban ce maki zan ci gaba da zama da ke ba. A hakan kuma namiji ya yi maki rana don haka ki fice min a falo.” Yana son ya lallasheta zuciyarsa tana gaya masa kada ya kuskura, domin lallashin nan zai sake jawo wata matsalar ce Karshe ma tayi masa
Illa, Ta dube shi cikin bacin rai tace, “Me ka taba yi min? Juyo ka gaya min meka taba yi min?” (Ku yi haKuri ‘yan uwa mata, ina son jan hankalinku a kan wannan kalma ta me ka taba yi min? Namiji ya yi maki komai tunda ya raboki da gidan iyayenki, ya kuma dauki nauyin ci da sha dinki, ya hana duniya ta zage ki. Ashe kuwa baki da wata gata da ta wuce ta miyinki? Ashe mijinki ya yi maki abubuwa kala-kala. Baya yuwuwa ace ki zauna da namiji shekaru talatin da wani abu, rana guda ki ce me ya taba yi maki? Sai kace mana zamanin jahiliyya? Idan ran mu ya baci don Allah mu yi shiru kada mu yi magana, domin a yayin yin maganar bamu muke yin maganar ba, shaidan ke yi. Maza suna jin zafin Kalmar me ka taba yi min? Kai ba namiji ba, hatta ke dinnan mai fadin hakan idan watarana aka gaya maki ba za ki ji dadi ba. Ko me namiji ya yi maki ‘yar’uwa ki zauna ki yi tunani kafin furta masa mayana). Www.bankinhausanovels.com.ng
Abba ya zakuda kafada, “Babu abinda na taba yi maki Salma. Bana fatan ki tuna alkhairi daya da na taba yi maki.” Ya koma ya zauna yana jujjuya Kalmar nan, haka da alamun kalaman sun zauna masa a zuciya ta yadda goge su za su zama abu mai matukar wahala. Dakinta ta shiga da ninyar kwaso kayanta ya lallaba ya rufeta. Ta yi ta bugun Kofar tana kuka, gaba daya ta zama mahaukaciya. – Gabadaya “dabara ta Kare masa. Dakin Hafsat ya shiga ya dade yana lallashinta da bata baki, sannan ta tsagaita da kukan.Washegart da sassafe ya kamo_ hanyar Kaduna, saboda Abbansa ya gaya masa komai. Ga shi jibi jirginsa zai daga zuwa London. Yana hanya ya kira Al-ameen yake gaya masa akwai matsala a gida, da wahala ya sami zuwa ganin Nasreen. Al-ameen ya jinjina kai, “Lallai akwai rikici sosal, kafin a shiga da ita ta sake jaddada min innemeka ko me kake ka iso gareta.” Hankalin Sultan ya sake tashi, ya gaya masa halin da ake ciki a gida, don haka shima ya jajanta ya kuma yi addu’ar samun sassauci akan komaiTafiyar awa biyu ya iso da _ shi garin Kaduna. Yana isowa ya shigo cikin damuwa. Ya dubi Abbansa da duk ya rame a lokaci guda. “Abba ina Umman take?” Da hannu ya nuna masa dakinta, babu bata Www.bankinhausanovels.com.ng lokaci ya karbi makullin ya budeta. Tana jin alamun budewa ta mike. Ido hudu suka yi, duk ta rame ta zama abar tausayi. A lokaci guda tausayin mahaifiyarsa ya yi tasiri a zuciyarsa. Tunani yake yi da mata ne aka halartawa yi wa maza kishiya, da babu abinda zai hana mazajen duniya basu zama masu kisa ba. Mata suna haKuri matuKa.
Umma ta taso da wuri tana zuwa ta dauke Sultan da wani irin mari, kafin ya wartsake ta sake dauke shi da mari, sannan ta ci kwalarsa, “Ban taba ganin mara kishi irinka ba, da kai za a hada baki a cuceni? Har in turo ka ka duba min abinda ke faruwa amma ka gaya min babu komai? Ka fada min da saninka aka yi wannan auren kokuwa? Nayi alKawarin duk wanda ya tsaya tsayin daka aka yi min kishiya da ‘yar aikina sai na hukunta shi.” Abba da yake tsaye a bayansu ya ce, “Za ki dauki hakkinsa bai san da komai ba.” Umma ta juyo tana duban Sultan ido jajir, idan har da Www.bankinhausanovels.com.ng saninka akayi min kishiya Allah ya tsi..Sultan da yaji tsigan jikinsa yana tashi ya rike Umma da Karfi jikinsa yana rawa ya ce, “Umma kada ki tsine min, da ni aka je aka daura auren Abba. Umma Sunnar Ann…”
Bai Karasa ba ta sake dauke shi da mari, sai dai na wannan karon yafi sauran zafi. Saboda ta gigice jin da danta na cikinta aka hada baki aka yi mata kishiya da ‘yar aiki. “Ka cuci kanka, ka kawo abinda zai raba_ mahaifiyarka da mahaifinka rabuwa na har abada. Ba zan sake _~ zama kusa da ku ba, bana son watarana ka tuna a zuciyarka ni Salma ni na haife ka, na yafewa Mairo. Na jima da ji a zuciyata ba ni na haife ka ba, ban tabbatar da hakan ba, sai yanzu. Zan je duniya in fada da babban murya dan cikina ne ya sa ayi min kishiya da ‘yar aikina. Kai Sultan ba zan taba yafe maka ba, ka jima kana cutar da ni, ka kawo min mazinata gidana, ka kawo min ‘ya’yan arna gidana, ka kawo min _ kishiya gidana? Idan na ce na yafe maka kai kanka sai kayi shakkar kasancewata uwarka, wacce tasha wahala kafin ta haifeka. Da nasan wahalar da zaka jawo min kenan Sultan da na danne ka a lokacin da nake naKudanka ka mutu, da nasan tuggun da kake son ka girma ka hada min kenan, babu ko shakka da a lokacin da likita ya sanar da ni ina da ciki da na sha magani na watsoka kana matacce. Allah ya isa tsakanina da kai Sultan ban yafe maka ba.” Hankula fa sun Kara tashi, danasani ya sake shigarsa, bai taba tunanin abin zai kai haka zafi ba. Sultan ya riKe kansa da Karfi yana ganin Www.bankinhausanovels.com.ng mutanen wurin bibbiyu. Ya yi magana cikin dauriya da cijewa. “Na yi asara a rayuwata, nayi mugun asara tunda har mahaifiyata take danasanin haihuwata, na yi tirr da rayuwar da nayi. Yau ni ce uwar da ta haife ni take cewa ta yi danasanin tsawon rayuwata a matsayin dan cikinta. Umma saboda mahaifina  ya raya Sunnar ma’aiki shiyasa kike tsine min? Raboda mahaifina ya raba kansa da muguwar cutar nan da ke damun wasu ya kiyaye kansa  daga fadawa halaka shiyasa kike tsinewa danki? Yau da waje ya fita ya aikata ba dai-dai ba, na

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *