RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Zan je duniya in fada da babban murya dan cikina ne ya sa ayi min kishiya da ‘yar aikina. Kai Sultan ba zan taba yafe maka ba, ka jima kana cutar da ni, ka kawo min mazinata gidana, ka kawo min ‘ya’yan arna gidana, ka kawo min _ kishiya gidana? Idan na ce na yafe maka kai kanka sai kayi shakkar kasancewata uwarka, wacce tasha wahala kafin ta haifeka. Da nasan wahalar da zaka jawo min kenan Sultan da na danne ka a lokacin da nake naKudanka ka mutu, da nasan tuggun da kake son ka girma ka hada min kenan, babu ko shakka da a lokacin da likita ya sanar da ni ina da ciki da na sha magani na watsoka kana matacce. Allah ya isa tsakanina da kai Sultan ban yafe maka ba.” Hankula fa sun Kara tashi, danasani ya sake shigarsa, bai taba tunanin abin zai kai haka zafi ba. Sultan ya riKe kansa da Karfi yana ganin Www.bankinhausanovels.com.ng mutanen wurin bibbiyu. Ya yi magana cikin dauriya da cijewa. “Na yi asara a rayuwata, nayi mugun asara tunda har mahaifiyata take danasanin haihuwata, na yi tirr da rayuwar da nayi. Yau ni ce uwar da ta haife ni take cewa ta yi danasanin tsawon rayuwata a matsayin dan cikinta. Umma saboda mahaifina ya raya Sunnar ma’aiki shiyasa kike tsine min? Raboda mahaifina ya raba kansa da muguwar cutar nan da ke damun wasu ya kiyaye kansa daga fadawa halaka shiyasa kike tsinewa danki? Yau da waje ya fita ya aikata ba dai-dai ba, na
ZAMU TASHI
tabbata ba za ki yi mana wannan kalaman ba. Kishiyar waje ita ce abar Kyama ba matar halak ba. Bana danasanin abinda nayi, amma ina danasanin isowa gareki a yau dinnan da naji kalaman da har in mutu ba zasu taba bace min ba. Umma na jima da sanin_ baki sona, kina rowan sa min albarka a dukkan abubuwan da . nayi, na alkhairi ko
akasinsa. Yau zan barku zan tafi, bana tunanin zan sake waiwayo gidan nan, domin ba zan mance ba, a cikin gidan nan mahaifiyata ta tsine min.Juyawa ya yi da ninyar tafiya, jirI ya kwashe shi ya zube Kasa. Abba ya rugo da sauri ya riKe shi yana jijjigawa. — Www.bankinhausanovels.com.ng
Umma ta Karaso cikin kuka mai tsanani tana danasanin furucin da ta jefi danta da mijinta akan abinda suka aikata wanda ba haramun bane, sai dai cin fuska ne. Za ta taba shi Abba ya daga mata hannu. “Kada ki kuskura ki taba min da. Kuma akan wannan abun da kika aikata ki tafi na sake ki saki daya. Kin lalata min rayuwar yaro, tun yana Karami yake fuskantar matsala a dalilinki. Ya kamata Sultan ya fi haka, amma saboda mugayen addu’ar da kike jifarsa da shi, yana nan adankwafe a wuri guda. Ina fatan za kije ki auri_mara mata, wanda ba zai taBa yi maki kishiya ba?Umma. ta girgiza da sakin da Abba ya yi mata ta sake sa kuka, tana fadin “Na shiga uku. Sultan ka tashi na yafe maka, na janye tsinuwar da nayi maka. Insha Allahu albarkata tana tare da kai, don Allah kada ka mutu ka barnI. Kada ka tafi ko ina. Lukman yau ni ka saka saboda wata? Ni ka wulaKanta saboda ‘yar aikina?”’
Abba ya dube ta cikin jajayen idanu ya ce, “Da zan sake ki saboda Ita, da tun jIya da kika rufeta da duka zan sallame ki, amma na cije. Haka kika babu zagin da baki yi min ba, amma na daure na Kyale ki a zatona za ki yi hankali daga jiya zuwa yau, sai dai zuciyar kafiran da ke manne da jikinki taki sakinki bare ta baki shawarar Kwarai. Kuma Wallahi idan dana ya rasa rayuwarsa babu shakka sai nayi shari’a da ke.”
Hafsat ya Kwalawa kira, ta kawo ruwa jikinta yana rawa, aka watsa masa. Abba ya dade da shi anan kwance sannan ya farfado, ba tare da ya iya furta komai ba. Idanunsa sun sauya. Ana hakane Alhaji Mu’azzam yayi sallama ya shigo. Kallo daya yayi wa Umma ta shiga taitayinta, suka kama Sultan suka kai dogon kujera a falo. Abba ya dubi Alhaji Mu’azzam ya mayar masa da komai.
Duban Umma yake yi yana ganin kamar ba za ta iya aikata hakan ba, ““Amma Salma kin bani mamaki. Wannan ba tarbiyyata bace, ki shake wuyan rigar mijinki? Mijinki fa?? Kinsan girman miji kuwa? Hauka da jahilci su suke aikatawa, ba aikin addini ba. Aure ba a aure ne aka aure ki? Iyayenmu kafin su bar Www.bankinhausanovels.com.ng gidan duniya matansu nawa? Kuma saboda rashin hankali a gaban ‘ya’yanki? Ki ji tsoron Allah Salma ki nemi afuwan mijinki tun kafin lokacin nadamar da babu amfani ta zo maki. Ki guji cin fuskar mijinki don yafi ni daraja a gunki nesa ba kusa ba. Kuma idan bai mayar da sakin da yayi maki ba, ki san gidan ubanda za ki koma ba gidana ba, ba kuma gidan dan da kika tsine masa ba. Kin lalata rayuwar danki da kanki, saboda son zuciya.” Kallo daya za ka yi wa Umma ka tabbatar ba wai ta hakura bane, amma sai ta nuna ita tayi nadama, ta roki Abba tana kuka. Abba ya yi ajiyar zuciya yace, “Idan har kin daina wannan abinda kikeyi ni na hakura. Kuma na mayar da ke dakinki, fatana ki hada kai da ‘yar uwar zamanki ki kuma kama girmanki.” Umma ta dube shi duba na tsanake ta sunkuyar da kai ba tare da ta iya furta komai ba.
********?
A can kasar London kuwa yau za a bude idanun Nasreen, dow haka tasa masu rigima ita sai Deedinta ya zo. Al-ameen ya Karaso yace, “Nastcon yace haba ki hakuri wani abu mai mahimmanci ya hana shi zuwa, ki yi hakuri ba zamu dade ba zamu koma Kasarmu har sai kin ji ya isheki.” Nasreen ta girgiza kai ta ce, “Uncle ba zan iya ba, shi nake so infara gani, shi nake mafarkin ya zama mutum na farko da zan dora idanuna akansa inhar Allah yasa sun bude. Don Allah Uncle ka taimaka min a fasa bude idanuna a tsaya a jira shi.”Dr Sadiq ya Karaso yana murmushi, ya yi mata magana cikin harshen turanci, “Ki yi hakuri dole zamu bude idanunki. Idan mun bude sai ki kalli Kasa idan kin tabbatar mana kina gani shikenan sai ki Www.bankinhausanovels.com.ng mayar da idanunki ki rufe har sai ya iso. Hakan ya yi maki?”Nasreen babu yadda za tayi dole ta amince. Ana warware bandejin gabanta yana tsananta
fadi. Sannu a hankali aka gama _ warware bandejin. Yana kallonta taki dago kan haka taki budewa. Dr din ya yi magana a hankali, “Bude idanunki ki kalli saitin Kofa a hankali idan kin tabbatar kina gani sai ki mayar da idanun ki rufe, bana son ki kalle ni.”
Nasreen ta ware idanunta tana duban Kofa, sai dai dishi-dishi take gani, don haka tace, “Dr, ina ganin dishi-dishi. Yauwa ina ganin wasu fararen abu kamar farar riga.” Dr ya yi murmushi, “Ci gaba da ware idanun a hankall1. Babu musu taci gaba kamar yadda yace. Fes ta dora idanunta masu girma a kan wanda take fatan fara gani kafin kowa.
Tsurawa juna idanu suka yi, ya Kara kyau da haske, sai dai da alamun rama a jikinsa, kamar wanda ya yi jinya ko kuma yake cikin halin rashin lafiya. Ta kasa kauda idanunta, ta kasa daina kallonsa, bata san akwai ranar da Allah zai amsa addu’arta ba, na sake kallon Dee dinta mai kyau da kwarjini. Shi kansa idanunta yake kallo yana jin wani farin ciki yana ratsa shi, ji yake kamar ba a taba halittar damuwa a zuciyarsa ba. Yana harde cikin fararen kayansa da suka sake haskaka fatarsa. Murmushi kawai yake . zubawa yana jin kamar ana sake sa masa soyayyarta. Tana son yin kuka ya girgiza mata kai, ya taka cikin tafiyarsa ta isa ya iso har gaban gadonta. Sai a sannan ta sake ganinsa da kyau. Waiwayawa ta yi kamar mai neman wani abu, sai Www.bankinhausanovels.com.ng kuwa ga Naufal. Ya zama Kato ya fita girma har da wani gemu. Farin ciki ya sa ta bude hakora tana dariya. “Deena, Naufal Allah na.gode maka da ka amsa addu’ata.” Dukkan su suka zauna akan gadonta suka ‘ kamo hannaeyanta suna ci gaba da kallonta. Sultan yace, -“Alhamdulillahi. Al-ameen shigo ka ga idanun Nasreen dita fes da su.” Ya kai hannu kamar zai tsokane idanun, ta rike yatsan tana dariya. Jidda da Al-ameen suka shigo a tare. Farin cikin ganin Jidda ya sake kama zuciyarta. Tabbas Jidda da Alameen kyawawa ne na _ ~bugawa a jarida.Nasreen ta rungumeta tana fadin “Allah ya saka da alkhairi ya sa zumuncinmu har abada. Ba zan gaji da roKa maku Aljannah ba.” Nasreen ta sake waiwayawa tana neman likitan da ya yi mata aiki. Yana tsaye yana ta murmushi tace, “Dr mun gode.”Ya Karaso yana murmushi, “Kukan kiran Dee ya Kare ko? Yanzu babu wata damuwa ko? Daga yanzu Dee shi zai zauna da ke har mu sallameki, tunda dai mu bamu iya jinya ba, Dee shi kadai ne ya iya.” Nasreen ta sunne kanta a jikin Sultan tana dariya Kasa-Kasa. Sun burge shi sosai don haka yace, “Allah ya dorar da zaman ‘* lafiya a tsakanin ku, Allah ya nesantaku da dukkan abin Ki. Ina fatan zaka taimaka ka * dan zauna da patient din mu domin samun natsuwarta da kuma kasancewarta cikin farin ciki?” Sultan ya shafi fuskarta yace, “Dr, Kafata Kafar matata, nasha wahala da babu ita a cikin gidana, gaba daya sai gidan ya yi min girma bana jin dadin komai. A yanzu haka na dauki hutu ina son cin amarcina yadda ya kamata ko Babyna?”
Naufal ya shafi kansa yana dariya KasaKasa Al-amecn ya nuna masa naufal da baki, Sultan ya tabe bakinsa alamun bai damu ba. Naufal ya mike yana dubanta, “‘Ku gama hira da Deedi, sandarki Www.bankinhausanovels.com.ng tana nan, ko kuma in ce maki dan jagoranki yana waje yana jiranki. Na huta da shan kira. Abu kadan Naufal! Zo ka yi min kaza, Naufal! Meya sa kayi kaza? Naufal ka tafi ka barni. Oh sunana ya kusan Karewa a bakinki.” Sultan ya kai masa duka ya kauce yana kwasar dariya. Nasreen ta marairaice kamar za ta yi kuka, “Dee ka ganshi ko? Yana ’ tsokana ta.”
Sultan ya mayar da kanta a bisa kafadarsa. ““Kyale shi zan rama maki, kuma dole yaci gaba da yi maki wanki har ki warke. Zan bashi wahala akan abinda ya yi maki.” Ta sake dagowa tana dariyar jin dadi, ta tsura masa idanu, shi ma ita yake duba. A hankali duk aka watse aka barshi da matarsa. Ya dan waiwaya ya ga babu kowa, don haka ya jawota gaba daya jikinsa yace, “Ashe zan sake ganin wadannan idanun masu haske da kyau? Allah na gode maka.” Nasreen ta kwanta tana kallon bayansa, “‘Deeena, me yasa aka yi min Karyar ba zaka zo ba?” Hannunsa yana bisa kanta ya ce, “Da gaske da ba zan sami zuwa ba. Bani da lafiya Baby, hakannan ban warke ba na taso. Matsala tana ta faruwa a cikin gida, Umma ta koma ta sami Mairo a matsayin matar Abba. Babu tashin hankalin da ba ayi ba, daga Karshe ta tsine min.” Ya yi shiru abinda yana ci gaba da cin zuciyarsa, yana mamakin ta -. inda mata suke KoKarin haramta halas.
Nasreen tace, “Hasbunallahu Wa n1’imal wakil.”
Muryarta ta soma rawa, a lokacin da ta dago tana taba jikin Sultan. Zafi ne rau, haka har yanzu zazzabin bai sake shi ba. Sultan ya zame hannunta yana girgiza mata kai, “Idan kika yi kuka zan koma in Kyaleki. Kin dai san aiki aka yi maki, gara ki bi idanun nan a hankali har su Karasa warkewa, bana son kukan nan.” Dole Nasreen ta shanye hawayenta tana sake dubansa. “Yanzu da tsinuwan Umma ka hau jirgi ka taho nan?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Girgiza kai ya yi “Baba Mu’azzam ya Zo, ta janye tsinuwanta har ta Kara da sa min albarka. Amma ina tabbaiar maki ba za ayi zaman lafiya a gidan Abba ba, saboda har yanzu Umma tana cike da tsanar Mairo akan aure mata miji da tayi. Nasreen ina danasanin wannan aure, ina jin zuciyata tana tuhumata da rashin kyautawa Umma. Duk da ko wata ce can Abba ya aura sai Umma ta aikata fiye da abinda ta aikata a cikin gidan mu. Amma babu komai babu abinda ya gagari Allah. Ya Karfin jikin?”’
Ya Karashe da tambayarta yadda jikinta yake. Bata iya bashi amsa ba, zuciyarta tana tausayawa Umma, domin abin akwai zafi da cin rai
Kwana biyu kawai Nasreen ta Kara a cikin asibitin, wanda suka yi shi cikin wasa da dariya, haka taga tattali agun Sultan kamar ta koma cikinsa ya boyeta. Ko da aka Sallameta, Sultan ya hana su dawowa Najeriya ya tabbatar masu sai ya more kudinsa zai bar Kasar. Babu wanda ya musa, domin su kansu ba su son komawa gida. Yau tana kwance a Kafafunsa suna dan taba hira tace masa, “Dee kana waya da Anti Zakiyya kuwa?”Ya daga kai, “Eh muna waya wani abu ne?” Girgiza kan ta yi, “Babu komai na dai tambaya ne kawai.” Ta tashi zaune ta tsurawa yatsun Kafarsa ido, kamar mai nazari. Hakan yasa ya tsargu ya dube ta, “Lafiya ° ki ke min irin kallon nan?” Idanunta ta dago ta dora a bisa nasa, ya” yi saurin janye idanunsa yana duban Kafar.
Ta ce “Gani na yi Kafafunka iri daya da na Naufal.” Murmushi ya sakar mata, “To menene abin mamaki? Na fada maki ke jinina ce, ke ce kawai baki gamsu da bayanina ba.” Nasreen ta dan langwabe, “To na yarda da kai Dee, amma ka gaya min su waye iyayena? Ka gayamin ina son insan ni wacece?”
Sultan ya dake, ya shafi kumatunta ya matso da ita jikinsa sosai, “Ke rubutacciya ce. Ina fatan shikenan kin fahimci ke wacece ko? Oya tashi mu je mu kwanta ko kuma in zane dan bakin nan da bulala.”Nasreen ta yi murmushi tace, “Lahh ai ba a zane baki Deena.”
A kunne ya rada mata wata magana ta sunkuyar da kai kunyarsa ta kama ta, ta ruga da gudu tana WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG KyalKyaltar dariya. Sultan ya saki ajiyar zuciya da Karfi ya mayar da kai ya jinginar a jikin bangon yana nazarin ta hanyar da ya kamata ya biyo wa Nasreen. A ganinsa lokacin boye-boye ya wuce, yana ganin fada mata gaskiyar za tafi, domin lokacin da zai sada ta da danginta ya yi. Yana tunanin lokacin da zai mayar da hankalinsa akan matsalolin Nasreen ya yi. Ko babu komai a yanzu ya riga ya gama da matsalar idanunta, tana iya ganin kowa. Yana nan zaune bai tashi ba, ya ji hannaye masu taushi suka rufe masa idanu, sannan aka sumbace shi a goshi, “Nasreen
kin Kware a wasa ko? Idan na kama ki ba zan
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG