RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Murmushi ya sakar mata, ya mika mata hannu ta rike suka sauko. A baki ya dinga bata naman tana ci ta • ture hannunsa tana kaiwa bakinsa, wai dole sai shima yaci. Haka suka
Gama yaje ya wanko hannunsa ya sake yin brush ya daga ta cak sai bandaki ya wanke mata baki suka dawo kan gado. A hankali ya rada mata, “Baby wani kamshi nakejia jikin ki maisa kasala a ina kika samu. Yummah ko?” Yana maganar tare da zuge mata
zif din rigar wanda gabansa dogon zif ne. Hannunsa ta rike tan girgiza kai. Wutar dakin ya kashe gaba daya. Zakiyya ta nemi ta kurma ihu, cikin ikon Allah ta toshe bakinta. Mamaki ya kashe ta, dama haka Sultan ya iya soyayya yake kin yi mata Ta gigice iya gigicewa kamar za ta yi hauka haka take ji. Ta ci alwashin bai isa ya aikata wani abu da Nasreen a wannan daren ba, don haka ta
ZAMU TASHI
yi falo, ta kurma wani irin ihu, wanda ya shiga har cikin kunnen Nasreen da Sultan yake kokarin rabata da budurcinta, yake son raya wannan dare, yake son mayar da Nasreen cikakkiyar mace. Bai so tashi ba, amma yadda Nasreen ta rude ne yasa ya manneta a kirjinsa yana magana cikin sanyin murya, “Sorry kada ki fito bari inje ingani.”
Nasreen ta girgiza kai, dole ya taimaka mata ta mayar da kayanta ya kunna wuta tasa hijabi jikinta yana rawa, suka fito. A falon su ga Zakiyya tana makale da jikinta duk ta hada gumi. Nasreen ta karaso da sauri tana tambayarta, Menene? Lafiya kuwa?” Sultan ya dubeta cike da rashin yarda yace, “Ki yi magana man Ta nuna waje wai ta ga wani ya shigo da bakaken kaya. Haushi ya kara kama Sultan ya yi kamar ya juya abinsa, ya riga yasan halin Nasreen ba za ta bashi hadin kai ba, don haka yanemi waje ya zauna yanajin bakin ciki a ransa Nasreen sarkin tausayi ta dubi Sultan tace, “Dee ka zauna da ita ta riga ta tsorata yanzu haka shaidanun dare ne. Bari induba garin habbatus sauda sai ayi hayakinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng Sultan ya ji kamar ya kifa wa Nasreen mari, yadda bata damu da damuwarsa ba, sai damuwar wacce ta fi tsanarta fiye da kowa. Banza ya yi mata, ta gama dube-dubenta bata gani ba, ta dawo ta ce masa ya dan tofa mata addu’a. Sultan ya karasa babu abinda yake fadi ya dinga yi mata tofi ba tare da ya karanta komai ba. Ta dinga sakin ajiyar zuciya, haushi ya kara kama shi, bai san me Zakiyya take nufi da shi ba. A nan falon dukkansu suka kwanta, da zarar taga Nasreen ta fara barci sai ta fasa kara, haka za ta tashi a gigice ta tallabota tana yi mata sannu. Nasreen ta ji irin warin da Zakiyya take yi, don haka ta ci alwashin sai ta taimaka mata ta raba ta da wannan warin tunda ta kula abinda keyi mata katangar karfe da mijinta kenan. Tuni Nasreen ta cire komai a ranta ta ci alwashin sai ta daidaita Zakiyya da mijinta, ba za ta so mijinta yana zuwa yana shakar irin wannan warin ba, karshe ya illata shi. Sultan yana son ya yi mata rashin mutunci amma kuma ya kasa yin hakan saboda Nasreen ba za ta bari ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Abin takaici duk suka yi barci suka barshi yana zaman kunci. Haka ya zuba masu ido takaici yasa duk ya barsu anan ya wuce dakinsa. Da asuba ya fito ya sami duk basu nan, sun koma dakunan su, takaici ya sake kama shi, wato babu ruwansu da yadda ya kwana. Bayan ya dawo Masallaci ne ya fara shiri yana da taron da zai je da misalin karfe takwas na safiya, yana son fita da wuri don wuce wa wani wurin. Shirinsa yake tsaf a can cikin zuciyarsa kuwa kamar ya cinna wuta. Nasreen ta shigo hannunta dauke da plate ta yi Sallama, ya amsa ba tare da ya dago ba. Murmushi ta yi ta fahimci fushi yake yi da ita, bai san ita kanta dadin hakan ta ji ba, saboda tsoron da take ji. Da sauri ta ajiye plate din ta karaso tana sanya masa maballin riga. Suka dubi juna ta hade fuskarsu wuri guda ta dan Bashi fake a baki ta dube shi. “Ka tashi lafiya?” Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, “Eh” Murmushi ya kwace mata, bata sake magana ba, ta ci gaba da shirya shi har ta gama ta kamo hannunsa suka zauna. Tace, “Sai ka Www.bankinhausanovels.com.ng saika karya tukun ko ya girgiza kai a,a sauri nakeyi basai na karya ba sumba tayi masa sosai saida ta tabbatar da duk ya saki sannan ta janye jikinta tanajin wani iri a jikinta cikin mutuwar jiki ta dauki flate din ta kai masa kwan bakinsa babu musu ya karba haka ta dinga tura masa tana kai masa kofin shayin bakinsa saida ta tabbatar daya koshi sannan ta nufi turarukansa ta fesa masa kafan tana cewa kada wata taji min kamshin ka A tare suka Tito falon zai zaiyi waje, ta kamo hannunsa suka shiga dakin Zakiyya, shi dai sai dubanta yake yana mamakin irin wannan karfin halin. Barcinta take shaka mai rai da motsi. Dole suka juyo ba tare da sun sake magana ba. A bakin kofa ta tsaya. “To Allahya tsare Me kake son a dafa maka?” Sosai yake dubanta zuciyarsa tana gaya masa Nasreen ta daina sonsa. Zai fita sai ga Naufal yana shigowa. Ya dubi Sultan yace, “Dee barka da safiya. Kace za mu fita tare, Wallahi ko abin karyawa ban gani ba. Ni da irin wannan horon gara a sani a motar kawai inkoma Www.bankinhausanovels.com.ng gidanmu, ba. zan iya da horon yunwar da Nasreen take yi min ba.” Sai yanzu Sultan ya yi murmushi ya dafa Naufal yace, “Wato da a gida ne da tuni ka karya ko? Babu motar hayan da zaka hau, tare zamu je Kadunan, ina son Abba ya ga idanun Nasreen.” Nasreen ta dan yi tsalle ta kaiwa kan Naufal ran kwashi tana dariya, “Kana nufin nice ma mai barinka da yunwa ko? Tsaya ka bani minti biyu babu inda zaka je kana jin yunwa.- Da gudunta ta yi ciki Sultan ya rakata da idanu, tana dawowa da plate a hannu ta ajiye a tsakiyar falon, ta jawo hannun Naufal ta ajiye shi gaban Plate din sannan ta tallabi keyarsa, “Maza ka ci Dee yana jiranka.” Ta fago ta daga masa gira ta ce, “Ai zaka dan jira shi ko?- Dawowa ya yi ya zauna a kujera yana latsa wayarsa. Har Naufal ya kammala sannan suka wuce. Nasreen ta fada kitchen tana shirya masa abinda zai ci da rana. Sai wajen sha biyun rana Zakiyya ta farka ta biyo Nasreen kitchen tana hamma. Nasreen ta gaidata sannan ta gabatar mata da abin karywanta.
Bahu kunya ta dauka ta yi Palo tasha. sai wajen karfe ukun rani suka dawo a gajiye. gurguje ta hada masa ruwan wanka ya shiga ya yi kafin ya fito har ta gama jera masa abinci, ta wadata falcon da turarukan kamshi. Yana fitowa ya shaki kamshin ya rintse ido, har abada mace mai tsafta daban take. Ya kira Naufal suka zauna zaman cin abincin tare. Abincin ya tafi da hankalinsa, amma sai ya dake yaqi nunawa. Zakiyya ta zo ta zauna da shi, ita kuwa Nasreen ta shige ciki tana karanta littafan da Yumnah ta aiko mata da su, na gyara ne da salon sace zuciyar mai gida. Ta gamsu da dukkan bayanan Anti Rahama Hassan Zaria, da ta yi a cikin littafinta Don Ma’aurata, tabbas duk macen da za ta bi hanyoyin nan babu shakka ta gama mallake zuciyar mijinta. Tana kwance ta rufe fuska da littafin ya karaso ya dauke littafin yana dubawa. A lokacin ta bude idanu aikuwa ta yi tsalle tana son kwacewa amma ya hanata, suka yi ta zagaye dakin, karshe ya fito falo ta biyo shi ta haye bayansa ta fizge littafin. Zakiyya da ta ji kamar anwatsa mata barkono ta ci alwashin sai ta rama wannan cin fuskar. Tana fitowa Www.bankinhausanovels.com.ng
Nasreen ta kama kanta, domin ta tsani ta yi wa mutum abinda ita idan anyi mata ba za ta ji dadi ba. Ta koma daki domin dauko hijabi, kasancewar hakannan ta fito. Tana dawowa ta sami Zakiyya ta manne masa sosai, gabanta ya fadi da karfi, amma sai ta danne ta yi saurin korar shaidan ta saki fuska sosai ta karaso tana yi masa bayani akan littafin. Ya ture Zakiyya cikin wayau da dabara ya ce mata, “Nasreen ni kike son ki yi wa wayo?” Ta yi dariya kawai tana sosa kai, sannan ta sa kai ta fice. A waje -ta sami Naufal ya nausa cikin tunani. Ta dafa shi tana dubansa, “Naufal meke faruwa ne?” Girgiza kansa ya yi ya kwashe abinda ya ji Sultan suna fadi ranar a Kaduna wajen kasar gada. Nasreen ta yi shiru tana nazari, Anya kuwa maganar ta shafe mu? Kuma kasan wani abu ne? Idan ina kallon kamanninka da Yaya Haidar sai kawai in dinga jin kamar da gaske mu din jininsu ne. Ka dubi idanuna da kyau ka dubi idanun Umma, sai dai ta nuna min tsufa, amma idanun mu iri daya ne. Shiyasa ma na daina damuwa. Kada ka sake zama kana irin Www.bankinhausanovels.com.ng wannan tunanin kaji Naufal? Idan kana yi ni ma zaka sanya ni a cikin irin tunanin.” Naufal ya gyada kai. Sultan da ke tsaye a bayansu ya yi shiru yana nazari. Yaci alwashin yana isowa Kaduna zai yi duk yadda zai yi ya samo mahaifin yaran, don ya kula su Mahbub suna yi masa sanya, wanda zai iya jawowa har hutunsa ya kare bai kammala abubuwan da yake yi ba. Yau ma kamar kullum, cikin dare Nasreen din ce da kanta take ta fizge-fizge. Yana zaune ya kafeta da idanu, a ganinsa kawai sun hada baki ne suke son raina masa hankali. Sai da ya ga tana cizge dukkan abinda ke kanta, ta yi waje da gudun gaske. Sultan ya biyo bayanta, tuni ta yi tsakar gida sai zubewa ta yi a wurin. `Yan sanda suka yo kanta suna kokarin dagata, Sultan ya daka masu tsawa wanda yasa kowannensu ja da baya. Yana zuwa ya dagota yana dubanta. Da gaske ba ta numfashi, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi. Naufal ya fito a gigice yana duban Nasreen. Sai dai ya kasa cewa komai gabansa sai faduwa yake yi da karfi. Sultan ya dauketa suka koma ciki. Sun dade akanta suna yi mata karatu, sai a lokacin ta ci gaba da fizge-fizge. Sai wajen karfe ukun dare barci ya kwasheta. wannan lamari ba karamin daga hankalin Sultan da Naufal ya yi ba. Ita kuwa Zakiyya tana jin su ko lekowa bata yi ba, tunda dama uwarta ce tasa akayi mata tore. Da kyar Sultan ya lallashi Naufal ya tafi dakinsa ya kwanta, sai dai ya kasa barci, Salloli ya dinga yi yana rokon Allah, ya aiko mata da sauki. Sultan kuwa akanta ya kwana yana mata tofi. Washegari da kyar ya nufi Masallaci saboda tsabar barci da ke idanunsa. Ita kuwa Nasreen da kyar ta iya yin Sallah ta koma ta kwanta. A hanyar dawowa daga Masallaci ne Sultan yake kwantarwa Naufal hankali akan ta sami sauki sosai. Lamarin Nasreen abin sai ci gaba yake sake yi hakan ya daga hankalin Abba, har ma yaso zuwa ya dubata, Sultan ya hana shi. Dole ya daga waya yake sanar da Aslaf abinda ke faruwa. Aslaf ya gayawa Yummah. Babu bata lokaci suka ce wannan lamarin na Aljanu ne akwai wani wuri a Kano Abin yabo kurmi Market. Ta tabbatar masu idan suka je wurin sun sami maganin matsalar Www.bankinhausanovels.com.ng su. Sultan ya zaro wayarsa ya karbi lambar, 08036527328.
Babu bata lokaci ya kira su ya yi masu bayanin yadda take yi. Suka ce suna da buKatar ganin mara lafiyar. Ganin yamma ta yi duk suka yanke shawarar gobe za su wuce da sassafe. Haka akayi da Safe Dr Aslaf ya fito da. mota, suka kama hanyar Kano. Cikin hukuncin Allah suka iso da ita, babu bata lokaci aka dubata aka bata magunguna, sannan suka tabbatar masu turen aljanu akayi mata. Dole suna dawowa suka sauka a Kaduna, da nufin kwana gobe sai su wuce Abuja. Nasreen tana ganin Abba ta kafe shi da, idanunta. ~Abba ya Karaso yana dubanta, “Nasreen.” Ya kira sunanta cike da fara’a itama cikin sauri ta Karasa wurinsa ta kama kuka, “Abbana, sai yau nake saka a idanuna,” Sun yi mamakin yadda take magana, bayan bata cewa um bare, um-um. Abba ya dafa kafadanta yace, “Ki, daina kuka Nasreen kin ga ba lafiya gareki ba.”Tare suka Karasa falon, ya yi wa Dr Yummah Godiya akan irin taimakon da sukayi wajen kai Nasreen gun magani. Umma ma sun gaisa babu yabo babu fallasa. Anti Mairo tana dakinta jin muryarsu yasa ta fito, tana kula da irin kallon da Umma take aika mata, sai ta kauda kanta. Abin mamaki ciwon Nasreen bai tashi ba, haka sun fara yi mata amfani da dukka magungunan. Sultan yana son yi wa Mairo magana, yana tsoron Umma, dole ya cire duk wani tsoro ya ce, “Anti Mairo ko ki leko mu.- Mairo ta dan yi dariya kawai, Umma kuwa ta sake cika babu alamun wasa a tare da ita. Kamar an ce ta dubi kafafun Nasreen, ta kafe su da ido babu ko kyaftawa. Gabanta yana ci gaba da fadiwa. Tunani ne kala-kala a cikin kwakwalwarta, tana kuma mamakin ta yadda za ayi kafafun Nasreen ya yi kama da nata. Sai yanzu ta sake karewa yarinyar kallo, tana kama da wata a cikin danginta. Haka suna diban kama da ita kanta Umman. Gabadaya ta gigice tana girgiza kai, “A’a sai dai idan idanuna ne suke yi min gizo.” Zumbur ta mike ta shiga wurin Hafsat ta ce, “Hafsa kin kuwa ga abinda na gani? Nasreen kafafunta iri daya da nawa.” Www.bankinhausanovels.com.ng Hafsat ta yi murmushi tana ci gaba da ninke kaya, “Umma sai you kika kula’? Ai hatta idanun Nasreen irin naki ne. Ki dubi Naufal da kyau ki dubi Yaya Haidar kamanninsu ya baci. Abin ya .dade yana bani mamaki, amma da yake zama wuri daya yana sauya kamanni sai ban damu ba.” Umma ta dafe kirji da karfi tana cewa, “Ko dai Abbanku ne yayi cikin yaran nan? Wallahi ban yarda da shi ba.” Hafsat ta dubeta da mamaki, tace, “Umma me ya kawo irin maganar nan kuma? Ai ba da zuri’ar Abba suke kama ba, da zuri’arki suke kama.- Umma ta zazzaro mata manyan idanunta tana dubanta, “Kaf zuri’ata basu san komai ba, in banda Alqur’ani da Hadisai, me yasa za ki ce da zuri’ata suke kama? Kai bana son maganar nan abarta kawai.” Umma ta fada zuciyarta cike da tunani. Washcgari suka tattara suka koma Abuja, suka bar Umma cikin tunani da tarin damuwa. Kwanaki biyar ta dauka tana amfani da magungunan ta ji sauki sosai kamar bata taba yin wata lalura ba. Zakiyya kuwa ta rantse in dai
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG