RUWAN ZUMA CHAPTER 1

Bismillahir rahmanir rahim.
February 1997…
A cikin d’akin wata matashiyar budurwa ce mai kimanin shekara sha bakwai tsaye a kan sallaya tana sallah, can bakin k’ofa ta waje kuma wani saurayi ne da shekarunsa zasu kai sha hud’u yake kaiwa da komowa, da alama jira yake ta gama sallah ya mata magana.
Tana idarwa ko addu’a bata yi ba ta jiyo muryansa a tsakar kanta tamkar zai tada gidan.
“Kalti Laila ga can mutumin jiya a waje, wallahi yau ma ya dawo.” Yace da ita yana mai shigowa cikin d’akin tun kafin ta masa iso.
Bata kulashi ba, haka kuma bata juyowa ba sai da ta gama addu’arta ta shafa sannan ta juyo da dara-daran idanunta ta zabga masa harara.
“Kai wani irin mutum ne Mas’ud? Ina jinka ka shigo gidan nan da gudu kamar wanda yayi gamo da aljanu.” Ta mik’e tsaye tana ninke abun sallar dake hannunta.
Da haka ta kwa6e hijabinta ta zauna bakin katifa tana mai jawo robar kayan kwalliyarta kusa da ita, dama fitowanta daga wanka kenan zasu tafi islamiyya. Mai ta fara shafawa sannan ta bad’e fuskarta da hoda tana gyarashi da wani tsumman zani.
Mas’ud da bai ji dad’in yanda yayar tashi ta kar6i zancen ba sai ya zauna kusa da ita ya zuba mata idanu baya ko ki!awa.
Laila da har lokacin zuciyarta bai daina bugu ba tunda ta ji labarin mutumin jiya, tace,
“Da kazo ka tasani a gaba kwalliyar kake so na maka? Kuma kasan zamu yi lattin zuwa islamiyya, gashi daga jin yanda jikinka ke tashin tsamin nan ko wanka baka yi ba. Don Allah ka tashi ka shirya mu tafi.” Ta k’arisa maganan tana shafa janbakin Majik a bakinta had’e da zizara kwalli a idonta. Mas’ud har zai bud’e baki yayi magana sai kuma ya fasa, mik’ewa tsaye yayi yana karkad’e rigarsa yayi hanyar fita amma murmushi ne a fuskarsa sosai saboda yasan yanda mutumin ya tsaya mata a rai dole ta nemi k’arin bayani. Har ya je bakin k’ofa ya tsinkayo muryar yayar tashi cikin kunya tana cewa,
“Umm… Mas’ud. Wai me mutumin ya fad’a?”
Ai da gudu ya dawo gefenta ya zauna bakinshi a washe yana cewa,
“Wai cewa yayi in yi kiranki. Har ya bani Naira d’aya, kin ganta nan.” Ya zaro kwandalar daga aljihunshi ya nuna mata.
“Hmm, kud’in nan ya maka yawa Mas’ud. Ka kawo in ajiye maka ka dinga kashewa a hankali.” Tace dashi tana mai kar6an kud’in ta sokeshi a k’asan katifarta.
Bai damu ba, haka ya tashi ya fita daga d’akin don yin wankan da ta ce yayi.
Yana fita ta sauk’e wata ajiyar zuciya wacce bata ma san ta rik’e ba, wai mutumin jiya ne a waje? Me kuma ya dawo dashi yau?
A gurguje ta gama shiryawa cikin ‘yar atamfarta d’inkin riga da zani. D’aurin d’ankwali ta kafa sak irin ta Maryam Babangida sannan ta d’auki turarenta da ke cikin wata guntuwar kwalba ta d’iga a hannunta sannan ta shafa a rigarta, ta maimaita hakan har sau uku sannan ta rufe ta ajiye.
Mayafi ta yafa wanda ya rufe dukkan ilahirin jikinta, kana ta d’auki Al Qur’ani mai rubutun Warshi ta rik’e a hannunta, da haka ta fito k’ofar d’akin ta samu takalminta kobashu ta sak’alawa k’afafunta.
In ka ganta a wannan lokacin zaka d’auka koktel (cocktail) ta nufa ba makarantar allo ba, don tsabar kwalliya da had’uwar da ta yi.
A tsakar gida ta bakin madafi ta hango mahaifiyarta zaune a kan kujeran tsuguno tana tankad’en garin masara.
“Ummii zamu tafi makaranta.” Ta ce da ita bayan ta iso gurinta.
“Sannu Dawisu uwar ado, wato ke duk fad’an da za’a miki akan saka jambaki in zaki tafi makaranta sam bakya ji ko? Jiya ba Marwa ce ke fad’amin malaminku ya sakaki goge bakinki da bayan takalmi ba?” Ummii ta tambayeta tana mai rik’e ha6a ganin nacewa da kuma taurin kai irin na Laila akan kwalliya har ya fara yawa.
“Ummii k’arya suke miki. Shatuwa kad’ai aka saka ta goge amma banda ni. Haba, da girmana da ajina a ce wai ni Laila Choge ce za’a saka ta goge bakinta da bayan takalmi? Ai ban ga wannan malamin ba kaf fad’in Kanon dabo.” Ta k’arisa maganan cike ta jin kai.
“A dai juri zuwa rafi.” Kad’ai Ummii ta fad’a kana ta cigaba da tankad’en ganin kishiyarta Tabawa ta fito daga d’akinta da buta a hannu.
Wani irin kallon sama da k’asa Tabawa ta bi Laila dashi kamar idanunta zasu juye. Ganin kallon yayi yawa yasa Laila yiwa Ummii sallama ta fita tana cewa Mas’ud da ya fito daga wanka,
“Ka sameni a hanya.”
Tana fita ta hango mutuminta na jiya yau ma tsaye a jikin besfanshi hannunsa bisa k’ugunshi, tsayuwa yayi irin ta gayu ajin k’arshe.
Zuciyarta ce ta k’ara bugawa a karo na biyu, ta rungume Al Qur’anin hannunta a k’irji sannan ta fara takowa ta zo zata wuce ta gabanshi ba tare da ta masa magana ba.
“Laila.” Ta jiyo sautin muryanshi a kunnenta a karo na farko tun had’uwarsu jiya. Dama yana magana ne? Ashe haka sautin muryarshi take da dad’i?
Tsayawa ta yi cakk, sannan ta juyo tana kallonshi fuskarta a had’e kamar wacce ta ga bak’in sak’o.
“Don Allah bani minti biyu daga cikin lokacinki.” Yace da ita yana mai cire hannunsa daga k’ugunsa.
Ta kai sakan biyar tsaye sannan ta tako ta iso gurinshi ta tsaya nesa tana kallonshi.
Gyara tsayuwarsa yayi ta hanyar mik’ewa da dukkan tsayinsa, hakan yasa dole sai Laila ta d’aga ido kafin ta ga kwayar idanunsa. Abunda yake k’ara burgeta dashi kenan, wato mutumin akwai tsayi bayan gayu da ya iya, shiyasa tun kafin ta san sunansa ta ji ya burgeta duk da cewa had’uwarsu ta farko ya 6ata mata rai.
Kawar da kanta ta yi bata son su had’a ido, zuciyarta na bugawa idan ta kalli tsabar kwayar idonsa.
“Assalamu alaikum.” Yace da ita bayan ya fuskanceta. “Wa’alaiku mussalam.” Ta amsa masa har lokacin bata dubeshi ba.
“Sunana Aliyu. Na san jiya ranki bai yi dad’i ba da abunda na miki. Ina mai baki hak’uri kuma na d’auki laifina da ban sanar da ke dalilin da yasa na yi hakan ba.”
“Ah to ya fi maka. Haka kawai ka aika a kirani a cikin gidanmu sannan in fito ka k’i mini magana har sai da na gaji na koma. A ina ake haka?” Tace dashi cikin k’uluwa don har lokacin abun na ci mata rai, sai dai duk abunda ya mata bai hana zuciyarta yaba tsarin halittarsa da kuma hana idanunta ganin gayunsa ba. Ai ita mutum mai tsa!a da ado ko mak’iyinta ne yana burgeta.
“Naji nayi laifi. Amma dalilin da yasa kika ga nayi haka saboda rashin sallamar da kika mini ne bayan kin fito kin sameni. Shirun da nayi jira nayi ki mini sallama saboda nasan kin san muhimmancinta.” Cewar Aliyu yana mai zuba mata ido yana nazarinta.
Zaro ido Laila ta yi kunya sosai ta rufeta har tana 6oye fuskarta da littafin hannunta. Wato duk wannan fushin da ta yi laifinta ne ba nashi ba? Ina ilimin zuwa islamiyyarta yake da ta kasa yi masa sallama bayan ta fito.
“Laa. Don Allah kayi hak’uri, mantawa na yi. Ina wuni.” Ta samu kanta da fad’i bayan ta bud’e fuskar tata.
“Lafiya kalau. Ya mutan gidan duka?” Ya tambaya yana mai yaba halinta na saurin d’aukar laifinta. Ashe yarinyar tana da hankali.
“Kowa lafiya kalau.” Ta bashi amsa tana kallon k’ofar gidan nasu ganin shiru har lokacin Mas’ud bai fito ba.
“Kar In tsayar da ke, naga kamar islamiyya zaki tafi ko?” Yace da ita yana mai tayar da besfanshi.
Ran Laila ya d’an sosu kad’an, daga fara magana har zai ce zai tafi? Lokaci d’aya kuma ta kwa6i kanta don tasan gaskiya ya fad’a. Wai me yake damunta ne? Ta tambayi kanta. Jiya suka had’u amma har bata son rabuwa dashi? Mas’ud ne ya fito daga gidansu ya nufosu yana dariya, ganinsa yasa Laila tamke fuska tana masa ido amma ina bai gani ba.
“Kalti Laila ba kin ce baza ki k’ara tsayawa dashi ba?” Mas’ud yayi kato6ara.
Aliyu da ke kan abun hawansa yayi dariya ya ce,
“Ashe haka kika fad’a? Gashi kuma ni yanzu ma na fara zuwa, kuma zan dawo anjima da dare. A yi karatu lafiya.” Da haka ya barsu tsaye kunya kamar ya kasheta.
Yana k’ulewa ta juyo gurin Mas’ud ta danna mishi rankwashi a tsakar ka.
“To waya tambayeka? Wallahi zan ci kaniyarka in baka daina wannan fad’i ba’a tambayekan ba. Yi gaba mu tafi Kafin mu yi latti.”
Da haka suka kama hanyar islamiyyar Mas’ud na sosa gurin da aka rankwasheshi, sai dai ko kad’an bai nuna ranshi ya 6aci ba, hasalima dariya yake yi yana mata gwalo.
Sun ci rabin tafiyar a haka Mas’ud na tsokanarta har ya sakata dariya,
“Ka san meya faru Mas’ud? Ina fitowa kawai na ganshi a waje yayi irin wannan tsayuwar da yake burgenin nan. Har zan wuce sai ya kira sunana, ya mini sallama. Shine yake fad’a mini dalilin da yasa jiya har ya tafi bai mini magana ba wai don ban masa sallama bane. Ka san kunyar da naji kuwa? Ji nayi kamar in ruga cikin gida.” Ta bashi labarin abunda ya faru tamkar tana magana da wata k’awarta.
“Kin yi fushin banza kenan? Ni dama na san dole ku shirya. Wallahi ko Kalti, gayen yana burgeni, Idan na ganshi sai naga babu wacce ta dace ta zama matarsa sai ke. Kin ga shi gayu, ke gayu ‘ya’yanku ma duk su tashi cikin gayu muna kaisu gidan d’aukan hoto ana musu jumbo kati.” Ya k’arishe maganan yana kallon sama alamar yana hasko hakan a idanunsa.
“To kai da kake ta surutunka ka ji yace yana sona ne? Ko nace maka Ina sonshi ne?” Ta fad’a tana d’an bugin kafad’arsa cikin wasa, yayin da fuskarta kuwa cike take da annushuwa.
“Ni nasan yana sonki ne, kuma wallahi shi zaki aura ba Abdul ba.” Mas’ud ya 6ata rai.
Zuciyar Laila ce ta buga da k’arfi wannan karon na wani abu na daban. Lokaci d’aya kuma fara’ar fuskarta ya d’auke.
Da haka Mas’ud ya juyo da niyyan mata magana amma ganin halin da ta koma yasa ya rufe bakinsa. Hannunta kawai ya rik’o, itama ta damk’e nata cikin nasa suka cigaba da tafiya. Ba dole sai sun yi magana ba, dashi da ita duk sun san abunda ke zuk’atansu.
Laila da k’aninta Mas’ud kenan wanda kaf fad’in gidan sun fi shak’uwa da junansu. Zasu iya kashewa su bunne ba tare da kowa ya sani ba, tsakaninsu babu raini ko fin k’arfi sai so da tausayin juna.
Labarin samarinta ka” babu wanda Mas’ud bai sani ba, haka itama ta san labarin abokansa har da ‘yan ajinsu mata da yake so, haka zata zauna ta saurari labaransa har watarana ta bashi shawaran ya aikawa yarinyar da yake so jolof d’in taliyar murji Idan an fita birek. Sai dai Mas’ud bai iya yin hakan ba, saboda tsoro da kuma kunya da yake ji. Wannan kenan.
Laila Kashim haifa”iyar garin Maiduguri ce dake jahar Borno. Mahaifinta Kanuri ne yayin da mahaifiyarta kuma take Shuwa Arab. Ita ce ‘ya ta uku a gurin mahaifiyarta da kuma gidansu gaba d’aya.
Madu shine yayansu babba, sai yayarta Ajidde wacce ke aure a nan cikin garin Kano, sai ita Laila, Mas’ud da ‘yan biyu Safa da Marwa wanda suke da shekara takwas. Mahaifinta Alhaji Kashim d’an kasuwa ne, ganin kasuwancinsa ya fi k’arfi a Kano yasa ya tattaro Iyalansa suka dawo garin Kano da zama lokacin Mas’ud na da shekara uku.
Bayan sun k’aura da shekara d’aya ne Alhaji Kashim ya auro Tabawa Bahaushiya wacce tana zuwa da shekara d’aya ta haifi d’iyarta Shema’u, daga ita kuma har yau Allah bai k’ara bata haihuwa ba. A gefe dai tana k’usk’us d’in cewa Hajiya Falmata Maman Laila ce ta hanata haihuwa sai dai bata ta6a bugan k’irji ta fad’a mata hakan a fuskarta ba.
Hajiya Falmata mace ce mara son magana amma idan an ta6ota bata da dad’i ko kad’an, ko da labarin hakan ya iso kunnenta murmusawa kawai ta yi tace,
“Allah ya gani bani da haihuwa ko rashinta a hannuna balle in bayar ko in hana wani. Allah shi yasan zuciyata da kuma abunda nake aikatawa, Idan nice silar rashin haihuwarta zai mata sakayya.” Ire-Iren wad’annan maganganun yasa masu gulman suka rage kawo mata tsegumi, ya kasancewa sai jifa-jifa.
Laila Kashim ruwan Kanuri da Shuwa bata yi hasken fatar Mamanta ba, bak’a ce, irin wannan bak’in da ake kira wankan tarwad’a mai kyau. Bata cika tsayi ba sannan bata da k’iba, sai dai Laila akwai halittar manyan cinyoyi wanda k’awayenta ke tsokananta cikin kishi. Wai da makaho ya rasa ido yace idon da wari.
Bata cika kyau irin shaharren kyau na bugawa a jarida ba, amma sai dai Idan har ta yi kwalliya da ado ta fito dole ka sake juyawa ka mata kallo na biyu, wannan farin jini ne da kuma kwarjinin da Allah ya bata.
Laila bata jima da dawowa gida daga GGC Dala ba inda ta gama makarantar Sakandire.
Tun tana yarinya take da son ado da kwalliya, ko da ta fara iyawa da kanta, wanka ya zama sau uku zata yi a rana sannan ta yi kwalliya ta zauna a bakin d’akin Mamanta tana yauk’i. Duk wanda bai yabi wannan kwalliyar ba to tayi fushi dashi kenan har sai ya yaba.
Abdul d’a ne ga abokin Babanta, wanda tunda ya kyallara ido ya ganta a bikin gama makarantarsu ya sanar da mahaifinsa yayi mata, Babanshi bai yi k’asa a guiwa ba ya samu Alhaji Kashim da zancen wanda yayi farin ciki da hakan, a take a lokacin yace ya bawa Abdul izinin neman auren Laila.
Ko da mahaifiyarta ta sameta da zancen bata yi musu ba, saboda ta san ba lokaci d’aya zata ji tana sonsa ba, sai dai har ga Allah ta rainawa hankalinsa da gayunsa a ranar da ya fara zuwa gurinta zance.
Dalilin mutuncin dake tsakanin mahaifansu yasa take kulashi ba tare da ta koreshi kamar sauran samarinta ba, saboda Abdul mutum ne mai son a sani da kuma nuna isa. A yanda yake zuwa mata hira cikin tinkaho kamar shi ya ajiyeta yafi k’ona mata rai. Gashi da son girma kamar gyambo.
Akwai wata rana da ya zo zance gurinta ya samu ta shiga makwabta gurin wata uward’akinta, ko da aka kirata ta zo, cewa yayi wai daga ranar in zata fita tana aika masa wasik’a saboda ya bata izinin fita.
A ranar kuwa Laila ta nuna masa iyakarsa, da abun ya mata zafi tace ta fasa soyayyar yaje ya nemi wata matar. Da kyar suka daidaita bayan ya rok’i uward’akinta ta bata hak’uri. Sai dai tun lokacin da Laila ta furtawa Mas’ud bata son Abdul shima yaji baya son Abdul d’in. A cikin zuciyarsa kuma yayi alk’awarin Kaltinsa baza ta auri wanda bata so ba.
Ana tsaka da hakan kuma sai ga Aliyu ya diro wanda kallo na farko da ta masa ta ji ya shige zuciyarta duk da cewa gamuwarsu ta farko bai yi mata dad’i ba, wanda kuma daga baya Laila ta dawo da laifin abunda ya faru a kanta.
Ana idar da sallan magriba Laila ta sake wani wankan ta ci ado tana jiran zuwan Aliyu. Haka kawai ta tsinci kanta da d’okin sake tozali dashi, sosai take jinshi a ranta wanda a yanzu ta tabbatarwa kanta cewa sonshi take yi.
Sai dai abun mamaki, shi Aliyu bai cika naci kamar sauran samarinta ba, har cikin ranta Laila ta tsani naci, amma kuma bata k’i Aliyu ya nace mata ba, shi kad’ai ta yardar mishi kuma zata so yayi hakan.
Ana idar da sallan isha itama ta idar da tata, kana ta k’ara hoda a fuskarta ta zauna jiran kiran Aliyu.
Ta fi minti goma a zaune amma shiru bata ji Mas’ud ya shigo ba, domin ta sakashi zama a k’ofar gida har Aliyu ya zo, gudun kar ya zo ya rasa d’an aika ya tafi.
“Kalti har yanzu fa bai zo ba.” Ta tsinkayo muryar Mas’ud a d’akin.
Yaushe ya shigo gidan har ya shigo d’akinta bata ji ba? Kenan ta fad’a a kogin tunani har haka? Har zata yi magana ta jiyo sallama a k’ofar gidansu.
Tabawa da take tsakar gida tana tatan gero ta amsa sallamar.
“Wai ana kiran Laila a waje.” Yace da ita.
“Tana zuwa.” Kawai ta fad’a yaron ya fita, ita kuma taci gaba da tatanta ba tare da ta kira Laila ba.
Shiru-shiru Laila na jiran ta ji Tabawa ta mata magana amma bata mata ba, ganin haka yasa ta mik’e ta k’ara duba fuskarta a madubi sannan ta dubi Mas’ud dake mata gulmar Tabawa wai ta cika bak’in hali da hassada.
“Ita ta sani, kai dai babu ruwanka da mata rashin kunya. Jiya naji tana kiranka ta aikeka kayi shiru ka k’i zuwa. Ka daina irin haka Mas’ud, wallahi bana jin dad’i.” Tace dashi tana fita daga dak’in.
Ko da ta fito tsakar gidan Tabawa bata bata sak’on kiranta da ake yi a waje ba, haka kuma Laila bata ko tanka mata ba ta fice daga gidan zuciyarta cike da farin cikin zata ga Aliyu. Sallama ta fara masa wannan karon ba tare da ta manta ba, ya amsa fuskarsa a sake yana aika mata da tsadadden murmushi mai sa zuciyarta bugawa cikin shauk’in sonsa. Bayan gaishe-gaishe Aliyu ya dubi Laila ya tattara nitsuwarsa guri d’aya yace,
“Kamar yanda na fad’a miki ni Sunana Aliyu Rufa’i, a nan unguwar Fagge nake da zama ni da mahaifiyata, yayana da kuma k’annena biyu. Mahaifina kuma Allah ya masa rasuwa shekara hud’u da suka wuce.”
“Sannu, Allah yaji kanshi da rahama.” Ta furta a hankali. Gyara tsayuwarsa yayi kana ya kira sunanta cikin taushi ya ce,
“Laila, na san kin fahimci me ya kawoni gurinki. Magana ce ta soyayya da kuma neman aurenki Idan Allah ya nufemu da kasancewa a rumfa d’aya a matsayin mata da miji. Ba zan miki k’arya ba Laila, tun daga ranar da na fara ganinki zuciyata ta kamu da matsanancin sonki. Ina son ki bani dama na nuna miki tawa salon soyayyar.”
Laila ta kanta ke k’asa dad’i kamar ya kasheta ta ciji la66anta tana murmushi mara sauti.
“Kin yi shiru baki bani amsa ba.” Yace da ita yana mai rage tsayinsa ko zai ga fuskarta.
Shiru ta yi wanda yasa Aliyu yayi murmushi mai sauti ya ce, “Shikenan, ki rubuta mini amsata gobe zan zo na kar6a. Zan tafi.”
Jin haka yasa Laila ta d’ago daradaran idanunta ta sanyasu cikin nashi fuskarta babu dad’i don bata so ya tafi tun yanzu ba.
Leda babba ya mik’o mata tak’i kar6a tana mak’e kafad’a, ganin haka yasa Aliyu ya ajiye mata kusa da k’afafunta ya ja babur d’inshi ya tafi.
Har ya 6ace mata da gani Laila bata koma cikin gida ba, zuciyarta cike take da tsantsar son wannan bak’on saurayi wanda ya sace zuciyarta cikin lokaci k’ank’ani. Sai da ta gaji don kanta sannan ta koma cikin gida tana nanata sunanshi a zuciyarta, suna mai dad’i.
Kai tsaye d’akin mahaifiyarta ta nufa ta nuna mata abunda Aliyu ya bata amma tace Abdul ne ya kawo, domin kuwa ta san mahaifiyarta da zafi idan har ta fad’a mata cewa wani ne zata mata fad’a akan cewa Abdul zata aura ta daina kula wasu samarin.
“Yayi kyau.” Kawai Ummii tace kana ta mik’awa Laila ledar. “Ummii ki d’auki wani abu mana in kina so.” Cewar Laila cikin karyewar zuciya ganin halin ko in kula irin na Ummii. “Ina da kayan kwalliya Laila, kayan shayi ma jiya Babanku ya siyo mana, ki ajiye a d’akinku kuna sha ke dasu Mas’ud.”
Jiki a sanyaye Laila ta dawo d’akinta tana ganin Mas’ud a ciki kuwa fuskarta ta washe ta zauna tana bashi labarin abunda ya faru. Dama tun fitanta yake zaman jiranta yaji me ake ciki.
Tana gama bashi labarin suka bud’e ledan suna kallon kayan ciki.
Kayan kwalliya ne a ciki irinsu hoda, janbaki, kwalli, turare har da lalle da kuma d’an kwali guda biyu wanda ake yayinsu a wannan lokacin. Sai kayan shayi madara, bonbita da suga.
“Mas’ud d’auko mana kofi da cokali a madafi mu fara dama madarar nan.” Cewar Laila tana k’ok’arin bud’e gwangwamin madaran da wata kwandalar da ta d’auko a k’asar katifarta.
Da gudu Mas’ud ya fita ya d’auko suka kwa6a madara da bonbita da suga suna sha suna hiransu yau duniya sabuwa ta musu dad’i.
Washegari lokacin islamiyya yayi suka fito domin tafiya, a waje suka tarar da Aliyu yana jingine da babur d’inshi. Bayan sun gaisa Mas’ud ya ciro wata envelope a cikin aljihunshi wacce ke tashin k’amshin turare ya mik’awa Aliyu. Laila dai gaba ta yi cikin kunya ta bar su tsaye. A hanya Mas’ud ya cimmata ya kwashe da dariya ya ce, “Kalti da kika tafi yana ta dariyarki wai kin cika kunya. Ki duba yau ma ya bani Naira d’aya, ni wallahi ban k’i koyaushe ya zo ba.”
“Sai kayi ta tara kud’i har ka sayi gida ko? Mas’ud ka rage kar6an kud’inshi fa. Kawo nan gobe zan mana waina.” Da haka ta k’ar6i kud’in suka cigaba da hiransu yana bata labarin yanda fuskar Aliyu ta washe da ya ga wasik’ar.
Soyayya ce mai tsa!a ta shiga tsakanin wad’annan masoya biyu wanda kullum sai Aliyu ya zo zance gurinta. Sai dai wani abun mamaki duk zuwansa har rana mai kamar ta yau da suka cika sati uku da had’uwa samari biyun basu ta6a had’uwa a k’ofar gidansu Laila ba, wato Aliyu da Abdul. Wani abun d’aurewar kai shine Aliyu bai ta6a mata maganan turo magabatansa ba kamar yanda Abdul yake mata nacin zai turo nasa a masa tambayar bayarwa.
Laila kuma so da k’aunar Aliyu ya rufe mata ido sai itama bata masa maganar ba, a tunaninta komai lokaci ne, shi da kanshi in ya ga lokaci yayi zai mata magana ta sanar da iyayenta.
A ranar bayan Aliyu ya bar gurin Laila da rana shi kuma Abdul ya shigo unguwar da yamma da niyyar hira da Laila ko da na minti sha biyar ne, sai ya wuce gurin Marka wata budurwarsa.
Sai dai ganin yanda Laila ta fito fuska a tamke yasa yasha jinin jikinsa.
Fuska babu walwala suka gaisa yana tambayarta ko lafiya. “Lafiya kalau nace maka, kawai bana jin dad’i ne.” Ta bashi amsa tana kallon gefe.
“Laila ko dai kin daina sona ne? Haba Laila, kwana biyu kenan bamu ga juna ba, na d’auka zaki yi marmarin ganina amma sai na ci karo da akasin hakan? Me na miki ne?” Shiru suka yi dukkansu wanda shi Abdul jira yake ya ji amsarsa, ita kuma Laila ta rasa ta yaya zata fara sanar dashi ya bar zuwa gurinta domin ta samu wani mijin aure.
“Ka ga Abdul, dani da kai duk mun sani cewa alak’armu bata da wani future, kullum muna cikin fad’a babu wata kyakkyawar mu’amala. Ina ga lokaci yayi da zamu daina yaudarar kanmu a kan abunda gaba ba zai yi wani tasiri ba, Ina nufin mu rabu Allah ya had’a kowa da rabonshi.” Ta fad’a a sanyaye k’irjinta na dukan uku-uku domin bata san yanda Abdul zai d’auki zancen ba.
“Me kika ce?!” Cikin k’araji ya mata wannan tambayar jikinshi na kyarma idanunshi har sun kad’a sun yi ja. “Rabuwa zaki yi dani Laila? Ki auri wani bani ba? Ina! wallahi ba zai yiwu ba. Tukunna ma wani shegen ne ya juyar da tunaninki domin nasan ba haka banza zaki ce in rabu dake ba. Ki fad’a mini, wani d’an iskan ne yake zuwa gurinki Laila?” Wannan karon tsayawa yayi a kanta dalilin ya fita tsayi yana huci kamar zai ci babu.
Sosai Laila ta tsorita domin ta yi tsammanin zai sauk’e mata mari, sai dai ganin ya matso daf da ita har suna shakar numfashin juna yasa ta ja da baya da sauri zata shige cikin gidansu.
Cikin azama Abdul ya rik’o mayafinta ya rik’e gam yana girgiza mata kai.
“Karki kuskura ki fara abunda baza ki k’arasa ba, tambayanki nayi wani shegen ne yake zuwa gurinki? Kenan jita-jitan da nake ji da gaske ne kina tsayawa da wani saurayi, na d’auka nine za6inki nine na dace dake ashe ke zagayawa kike yi kina cutata? Waye yake zuwa gurinki? Wallahi sai na sassareshi ko d’an uban waye ne!”
Duk wannan maganan da yake yi Laila mutsil-mutsil take yi tana k’ok’arin kwace mayafinta daga hannunshi amma ko gezau bai yi ba. Hawaye kuma tuni suka fara kwaranya a fuskarta tana kuka.
“Don Allah Abdul ka sakeni kar a zo a ganmu a haka, ka rufa mini asiri ka sake mini mayafina.”
“Sai kin fad’a mini waye yake zuwa gurinki.” Ya k’ara jawota kusa dashi ta hanyar jawo mayafin nata.
“Aliyu ne, Aliyu ne. Ka sakeni tun da na fad’a maka don Allah Abdul.” Ta fad’a cikin karaya domin bata son wani ya zo ya gansu a irin wannan hali domin bata san yanda zasu fassara hakan ba.
“A ina yake? Kuma d’an gidan uban waye shi?”
Da mamaki a fuskarta ta tsaya daga kokawar da take yi ta kalleshi cikin tsana da wani kallo mafi muni tace,
“Wannan ne kuma ban sani ba, kuma rabuwa da kai na riga da nayi har abada Abdul.” Da haka ta sake mishi mayafin ta shige gida da gudu hawaye na wanke mata fuska.
Kwala mata kira yake yi amma bata saurareshi ba har ta 6ace masa da gani. Kamar wani mahaukacin zaki ya fara kai kawo a k’ofar gidan yana kwallo da duk abunda ya tare masa hanya.
A fusace ya shige motar Babansa ya fita daga layin unguwar zuwa bakin titi in da wata majalisa ta wasu samari take.
A bakin hanya ya faka, sannan ya fito zuwa gurinsu Santali mai shago kuma shugaba na wannan majalisar, Santalin shi ya taso suka yi musabaha da Abdul sannan ya jashi gefe ganin kamar Abdul d’in kamar baya cikin hayyacinsa.
“Kai Abdul lafiyanka kuwa? Ka ga yanda jikinka yake 6ari kamar wanda ke masassara?”
“Kalau, kwanaki kace mini wani na zuwa gurin Laila, waye shi?”
A nan Sintali ya fad’a masa sunan Aliyu da kuma kwatancen gidansu.
Yana gama fad’a masa Abdul ya nufi mota kamar zai fasa ihu. Yana shiga motar ya daki sitiyarin yana huci ta baki da hanci.
“Sai naci uban Aliyun nan. Ko d’an uban waye shi.”
Daga nan majalisarsu ta Samarin Libati ya wuce kai tsaye, ya samu su Haruna da wasu mutum goma duk a zaune ana hira.
Daga tsaye ya basu labarin abunda ya faru suka fara ihu da alk’awarin sai sun lahanta mai son juyar da hankalin Laila. Sanduna na gora suka jida suka wuce unguwar Fagge koyawa masoyin Laila hankali lokacin har gari ya fara duhu.
SATI UKU da suka wuce a majalisar Libati samari ne kusan ashirin a zazzaune wasu a kan benci wasu kuma a kan tabarma suna hiran siyasa. Majalisar Libati ta matasa ce wacce suke shiga siyasa k’arkashin jam’iyyar da suke bi. Abdul shine za’a iya cewa shugabansu domin a gefen k’ofar gidan Babansa wannan majalisa take. Dama sun saba zama safe, rana d a kuma dare.
Shekara d’aya da ya wuce Abdul ya kawo musu shawaran shiga siyasa tunda suna da yawa kuma sun san mutanen unguwa. Gwamnatin da take ci a yanzu tare da su aka yi kamfe na cikin unguwa har da na k’ananan hukumomi da aka lura suna da himma. Cikinsu babu wanda gwamnati bata samawa aiki ba ciki har da Aliyu Rufa’i wanda abokinsa Haruna ya jawoshi ciki bayan jam’iyyarsu ta samu mulki, sauran matasan basu masa hassada ba wai don ganin bada shi aka yi siyasar ba, da haka aka mik’a sunayensu aka basu aiki dukansu.
Ana tsaka da hira Aliyu ya iso ya faka babur d’inshi a gefe ya samu guri ya zauna suka gaisa. Tsakaninshi da Abdul alak’a ce ta tsakanin memba da lida wanda Idan hira ya had’asu zasu yi ne ba yabo ba fallasa.
Wata budurwa ce ta zo wucewa aka watsar da hiran siyasa aka kafa ta ‘yan mata.
Aliyu bai so haka ba, domin shi hiran siyasa ya kawoshi domin ya ji ta inda za’a samu k’aruwa ko kuma wani muk’ami k’arami da zai gwada sa’arshi.
Kamar yanda kowa ke tashi da burin son zama wani abu, haka shima Aliyu ya tashi da son kasancewa Gwamnan Kano in da rabonshi. Wannan kenan.
Haruna ya ce,
“Kai Abdul har zaka zagi mata a kan yaudara? Alhali ga ka nan babban mayaudari mai neman ‘yan mata shida duk a lokaci d’aya, ga Marka, sai Fatima, Jamila, Saude, ga kuma Shatuwa sannan ga Laila duk kai kad’ai? Kuma shegen ba aurensu duka fa zai yi ba, Laila kad’ai yake da niyyar aure.” Labarin ya dawo kan ‘yan majalisar ake bawa.
Sauran suka dara suna cikawa Abdul kai wai ya zama Uban ‘yan yaudara shi kuma yana hura hanci kamar yayi abun kirki.
“Kuma duk cikinsu babu wacce ta gane ba ita d’aya nake zuwa zance gurinta ba, shiyasa zan iya kwana uku ban je gurin d’aya ba, Idan ta tambayi ba’asi sai in fad’a mata siyasa ce ta 6oyeni bata san soyayya bace.” Cewar Abdul yana kyakyatawa da dariya suna tayashi.
“Kai dai karka bari wani ya kwace maka Laila, domin duk cikinsu babu wacce ta iya ado, kwalliya sannan ga kyau kamar Ita.” Fad’in Hamisu kenan mataimaki kuma babban abokin Abdul.
“Kar kuma kasha mamaki Lailan da kake so wani ya je ya hure mata kunne tace shi zata aura ba kai ba mu ga k’arshen yaudara.” Cewar Nuru da dama cike yake da Abdul kan fad’a da suka yi akan wani kasafin kud’i.
“Wallahi, Tallahi na rantse da Allah babu shegen da ya isa yasa Laila ta saurareshi balle har tace shi zata aura bani ba. Kai dukkanku na baku dama ku je gurinta Idan ta kulaku shege nake.” Ya fad’a a fusace domin ya gane Nuru nemanshi yake da fad’a.
Ganin abun zai zama babba yasa sauran suka shiga tsakaninsu aka shashantar da zancen Haruna na cewa, “Abun bai kai haka ba Abdul, Nuru wasa yake maka.”
Kaf cikin samarin babu wanda ya d’auki zancen Abdul na zuwa gurin Laila a rai sai Aliyu, wanda halin Abdul na yaudara yasa yace zai nuna masa shi sakarai ne sannan shima zai d’and’ana masa zafin yaudara ya ji yanda sauran matan zasu ji idan ya rabu dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *