SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 3 BY Xayyeesherthul-humaerath
Www.bankinhausanovels.com.ng
Karatun tai hankali kwance sunfito ke nan dai,dai gate din makaranta zasu fita wata Yarinya da zata kai shekara ashirinne ta dumfarota da sauri, bangaje Nafeesa tai har sai da glass dinta ya fadi kasa, “Maga tayi ai,ke har kin isa ki tabamin Mutansir a makarantarnan,yar matsiyata, ko me kika masa ma ya nace miki oho, da alama dai ba a barsa haka ba, anga ‘Ya’yan masu dukiya ana Neman hanyar shige masu Amman tsoro ya hana,to wallahi ahir dinki, ko da gaske ko da wasa naji cewa kina son Mutansir kin Riga kin kade yarinya ba ma ke kadai ba hatta Shi wannan driban da wannan ma’aikaciyar asibitin,makauniyar banza da wofi,wata yar shila da ke ,ko inama abun so ajikinnan ? Mtsww.” Cewar Fatima tare da cigaba da yiwa Nafeesa wani mummunan kallo.
Tunda Nafeesa ta durkusar da kanta bata dago ba,ban da hawaye ba abunda ke zuba daga idanunta, Magana ta farayi cikin ruwan Sanyi, “Habibbty Bani Glass din nasaka bana gani.”
Ita kan ta Maryam sai da hawaye ya fara bayyana daga fuskarta tsabar tausayin Nafeesa da take.
Karfan Glass din Nafeesa tai tare da sawa a idonta ta rik’e hannun Maryam suka cigaba da tafiya.
Tsaki Fatima tai domin bata so hakan ba Sam ta lura kamar Nafeesa bataji zafi sosai ba,hakan yasata kara tunkararta cikin sauri tare da shan gabanta, Glass din fuskar Nafeesa ta kwace tare da cigaba da tafiya batare da tace komai ba.
Maryam ba kokarin yin Magana Nafeesa ta rik’e mata baki, “Habbibty kar kice komai, wannan kaddaratace, kisa anafe kawai kar drebanku ya gaji da jiranki.”
Kallon kawartata tai cike da tausayi, “A hakan zan Sa ki Anafe bayan nasan ba gani kike sosai ba, ki bari in karbo glass din wajenta sai dreban ya kai mu duka, wani iskancin ma Dan sunga ana barinsune.”
Nafeesa ta kank’ame hannun Maryam , “Dan Allah ka da ki tada rikice akaina ni ba yar kowa bace kamar yadda ta Fada Amman na San cewa watarana zatayi nadamar abun da tamin,ni kawai akai ni Asibiti Gun Mammah ta nemamin wani glass din,Idon ciwo yake min habibbty wallahi ciwo ya faramin.”
Cikin sauri Maryam ta laluba Jakarta tare da Ciro wani karamin glass , “Sorry Habibbty barin Sa miki wannan kan muje asibitin to.”
Bayan ta sa mata glass din haka Maryam ta rik’e Nafeesa suka Shiga mota.
Suna shiga Mota Nafeesa ta Sa hannu ajakarta tare da lalubo wani littafi mai suna
*Ajaliin mace* Fasihin marubucin nan nata ne dai ya rubuta, kallon littafin tayi tare da rugumarsa tamkar mutum, wani kayataccen murmushi ta sake,domin ji take duk damuwar da ke ranta ta kau,indai tana tare da littafin da Farincikin ranta ya wallafa,rubutunsa tamkar muryasa gareta,sunansa tamkar hotonsa ne garesa, bangon littafin kuwa ji take tamkar bugun zuciyartane, ji take gabadaya ta nemi damuwar da ke ranta ta rasa,cikin murmushi ta ce, “Habibbty Dan Karantamin kinga bana gani da kyau Dan Allah, kan mu isa.”
Murmushi Maryam ma tayi ganin cewa damuwa ta fice daga fuska har zuciyar Kawartata,karban littafin tayi tare da fara karanto mata.
Da mamaki Nafeesa ta haddace littafin tsaf a kwakwalwarta domin kan Maryam ta kai Aya Ita ta karasa mata, Maryam na kuskure wajen furuci zata gyara mata.
“Kai Habibbty ai kin gama haddace littafinnan to miye kuma na sai na karanta miki?”
Murmushu Nafeesa tayi, “Na haddace littafin nan tamkar yadda na haddace Al’Qur’ani mai girma,ko ina kika tabomin zan Iya karasa miki batare da na kalla ba,Amman kin San me? A kullum ina so akarantamin ko ni na karanta,domin aduk lokacin da nake sauraren kalaman banajin muryar kowa akunnena sai na Marubucina,sautin Muryarsa kadai ke sauka acikin kunnuwana, Habibbty mutane da yawa na fadin cewa karyane dan wani ya ce zai iya rasa ransa in ya rasa masoyinsa ko? To ni nasa araina cewa duk ranar da na tabbatar da cewa bazan Taba samun Yaya Nafseen ba, ba makawa zan Iya mutuwa nan take, Ina yi masa so fiye da yadda kowa ke tsammani,in ana maganar soyayya sai kije ana Sa Majnoon da Laiyla to ni ko Kadan basa gabana domin ji nake na ninnkasu natakasu a soyayyata,ko da ace Nafseen ba zai soni ba,akwai wani sirri tsakanina da shi, kuma inada tabbacin ya sani a ko ina yake ma duk da cewa ba mu San juna ba, kin san menene Habibbty?”
Maryam na gyara zama domin jin me Aminiyarta ta zatace dai,dai da lokacin da dreba ya tsaya domin sun iso asibitin batare da ma sun sani ba.
Nafeesa ta ce, “Yawwa Mun Iso.”
Suna fita Maryam ta kalli Aminiyarta ta, “Habibbty fadamin sirrin.”
Murmushi Nafeesa tai, “Sirrin,kina son jin Sirrin Habibbty?”
Maryam ta ce, “Sosai ma .”
Nafeesa ta ce, “
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
“Zan Fada miki sirrin Amman sai lokaci ya yi.”
Cike da Murmushi Maryam ta ce, “Allah ya kaimu zan so ko jin wannan sirri domin na San na mussamanne tamkar yadda Habibbtyna ta kasance ta mussaman.”
“Umm ni kam kai ni gun Mammahna.” Cewar Nafeesa.
Rik’e mata hannu Maryam tayi har suka shiga cikin asibitin, Mammah na ganin Nafeesa gabanta ya fadi tare da karasawa garesu cikin sauri.
“Nafeesa meya sameki? Ina glass din na ganki da wani kuma? Ya naga idonki ya yi wani iri ma lafiya kuwa.” Cewar Mammah.
Rike hannun Mammah Nafeesa tayi , “Aa fa Mammah fad’uwa Glass din ya yi kuma ya fashe,shi ne iska ta tabamin ido ya fara hawaye.”
Mammah ta kalla Maryam, “Anya kuwa Ku dai fadamin gaskiya.”
Maryam ta ce, “Hakane Mammah da naga ta fara hawayenne yasa na bata nawa glass din ko iskanne ya tare mata.”
“OK To Bara in dauko dayan,Allah ma yataimaka biyu na karban mata daman.”
Fadin Mammah.
Maryam ta ce, “Habbity kar dreba ya gaji da jira Bara in tafi sai mun hadu goben.”
“OK bye bye Na gode habibbtkuri
aida Anty.” Cewar Nafeesa tana dagawa Maryam hannu.
Bai fi minti Biyar ba da tafiyar Maryam, Mammah da Nafeesa ma suka tafi gida,kasancewar dutyn rana Mammah ke da shi.
Nafeesa zaune tana ta karatun littafi kamar yadda ta saba, ta kai karshe tai karo Da number Jameel Nafseen, a kullum tana ganin number nan kuma tana Sa rai da kokarin kira Amman tsoro da kwarjini ya hanata ko Da ta dau number Da niyar kira kan ya shiga zata katse,ayau kam ta cire tsoro tare da kudiri niyar kiransa, daukan number ta ta danna kira zuciyarta ce ta fara bugawa cikin sauri da mamaki maimakon numberta fara ringing sai taji cewa akashe,tun daga ranar kullum sai ta gwada kira Amman wayar nan dai akashe hakan kuma bai Sa ta fasa ba.
****Safiyar lahadi ba Boko ba islamiya hakan ya Sa ta dauko wayarta tare da bude data chatting ta fara tare da lekya group din su na mata zallah ta ji ana maganar wani film mai suna Abu Hassan, bata wani tsaya ta saurari chat din ba karaf sai taji ana fadin cewa ai Jameel Nafseen ne ya tsara labarin, tsayawa tayi da chat din tana tunani shin dama sahibin nata har Films ya ke rubutawa? .
A zuciyarta take fadin, “Ya zamemin dole in nemi fina,finan da ya rubuta sannan akan su zan fara kallo.”
Bata gama sak’e,sak’en ba karaf sai taji wata ta turo message , “Ai yawancin Marubuta yanzu sun dawo online, Dan natabajin Yayata da kawarta na fadin cewa akwai group na Marubuta anan whatsApp kuma duk marubutannan na ciki daga manyan har yaran.”
Da sauri Nafeesa ta bi wannan yarinyar private, sallama tayi mata tare da fadin , “Dan Allah zaki iya min hanya in shiga group din marubutannan?.”
Tayo mata reply da , “Eh to nima kawar Yayatace ke rubutu tana ciki, Amman ance zallan Marubuta ake sawa ciki.”
Tunani Nafeesa ta tafi kan ta bata amsa, “A yau zan zama marubuciya kuma zan rubuta labari indai zai iskeni ga Nafseen,.”
Bayan ta gama tunanin da Sauri tayo mata reply , “Ok nima ina rubutun ai ko zaki Iya hadani da kawar Yayar ta kin?”
Batare da tace komai ba, ta turo mata da number mai dauke da suna Nusaiba.
Saving din number Nafeesa ta fara yi sannan ta shiga wajen kira ta kira ta.
Ringing wayar ta fara har ta kusa katsewa kan Nusaiba ta dauka.
Sallama Nafeesa ta fara yi mata tare da gaisuwa,sannan ta ce, “Dan Allah Anty Nusaiba so nake asani cikin group din marubuta nafara rubuta littafi Amman ina bukatar ma su min gyara.”
Washe baki Nusaiba tai domin irin sune yan karyan nan ma su so ace sune suka San kaza ko suka yi hanyar kaza, sai da ta gama washe bakin ta kan ta ce, “Ok karki damu da nayi rubutu Amman yanzu na daina, akwai Matar Yayana da ke yi dai kuma tana cikin group din zan bada numberki ta saki.”
Hamdala Nafeesa tai har cikin ranta tana mai farincikin hakan.
Nusaiba ta ce, “Ko kuma ma dai kiyi min magana WhatsApp yanzu sai in Sa asakin.”
Nafeesa ta ce , “To na gode Anty Allah saka da alkairi.”
Nusaiba ta amsa da Ameen kan ta katse wayar da sauri ta fita adakin tare da nufan wani bangare, tana shiga ta ce, “Aunty Farida kizo kar inji kunya yau ta guna aka biyo Neman alfarmar shiga Group din nan na ku da kikace min akwai su Fauziya D Sulaiman da ma sauran marubuta da mawaka?”
Farida ta ce, “Eh fa ya akayi to.”
Nusaiba ta ce , “Watace ta kirani wallahi wai tana son shiga ko tayama akayi ta sami numberta oho ni dai ki taimaka asata zan baki number ta WhatsApp.”
Murmushi Farida tai, “Hmm Hajiya Nusaiba ke nan bakomai ki turo za asata Allah Sa group din ma da waje Dan cike muke fam.
Nusaiba ta ce, “Ni dai ataimaka kar ta rainani.
Dariya kawai Farida tai kasancewar tasan halin Nusaiba da shegiyar karya da kuri
Intaso karyartama cewa take ita ke rubutun ba Antynta ba.
Nafeesa kuwa tuni tayiwa Nafeesa magana WhatsApp kamar yadda ta bukata.
Ko reply Nusaiba ba tai mata ba kawai ta turawa da Farida Number.
PC Farida ta bi Bamai Dabuwa tare da fadin, “Dan Allah asa min wannan writern sabuwace.”
Ya yi mata reply da , “OK bara dai in duba Allah Sa da kwai waje.”⁹