SALON SO CHAPTER 2

SALON SO CHAPTER 2

 


Da Alhaji ibrahim ya gayawa inna shawarar da suka yanke na hada Haidar da jawahir aure, Inna ta yi murna ta yi godiya ga Allah ta sa wa abin albarka burinta zai cika ke nan na hade kan zuri’arta. Bayan Alhaji ya dawo yana cikin iyalinsa suna hira ya kalli jawahir ya ce mata, Jawahir dan uwanki fa na zaba miki wanda za ki aura, wato Haidar Cikin fargaba da tashin hankali ta wuntsilo daga kan kujerar da take zaune ta dirkushe a gaban Uban tana kuka ta rike kafafuwansa tana rokonshi, Don Allah Dady ka yi min rai kayi hakuri kada ka aura min yaya Haidar, wallahi ba ya so na ba ya kaunata, ba ma shiri da shi. Dady kada ya je ya shake ni namutu Dady ku yi asarata. Ba abin da zai faru jawahir yana son ki ba zai yi miki komai ba, ki yi biyayya a gare mu insha Allahu za ki ga kyan abin kin ji.?” Ta daga kai ta mike ta yi dakinta tana kuka mai ban tausayi ga mai sauraro. Momy ta kalle shi ta ce, Dan Allah ka hakura da auren nan tun da yarinyar ba ta so kuma yanzu an daina yayin auren dole.” Ya yi saurin daga mata hannu, Dakata don Allah ba na so ki ari halin da ba naki ba ki sawa kanki. komai da kika sani mukaddari ne daga Allah, yanda nake son jawahir ba zan taba cutar da ita ba, ko na kai ta inda za ta cutu ba. Ki sani duk wani Uba an fi so ya zabarwa ‘yarsa miji na gari, ki yi la’akari da shekarun jawahir sha bakwai fa, to a ina ta ga hankalin da tunanin da za ta iya zabawa kanta miji na gari? Ki yi hakuri ki barwa Allah zabinsa Momy ta ce, Shi ke nan Alhaji Allah ya zaba mana abin da ya fi alheri Cikin lokaci kankani an kawo kudi har an sa ranar aure wata biyu kacal. Hankalin jawahir ya kara tashi duk ta fige ta rame ba ta da aikin komai da ya wuce kuka kullum. Ita ta kasa zuwa ta gayawa Dadynta a fasa auren nan do ita ba yanda za a yi Dadynta ya gaya mata magana ta tsaya ja in ja da shi, don haka yamma tana yi a surare ta yi gidan Inna A gigice ta shiga kowa ya kalle ta ya san tana cikin tashin hankali. Inna ta tare ta cikin tsoro da tashin hankali tare da cewa, Ke kuwa yarinyar nan me ya same ki haka kika yi irin wannan ramar haka? Jawahir ta saki wani tsumammen kuka, hankalin Inna ya kara jagulewa tana tunanin ko wani ne ba shi da lafiya ko mutuwa aka yi musu. Ganin yanda Inna ta rude ne ya sa ta yin shiru amma idanuwanta be daina zubar da hawayen ba, Inna ta ce, Jawahir me yake faruwa ne? Ki gaya min waye ya mutu?” Jawahir ta ce, Don Allah Inna ki hana Dady ya hada aurenmu da yaya Haidar wallahi inna ba ma son junanmu ko kadan ni da shi halinmu be zo daya ba, irin rayuwar kowanne daban. ko an yi auren ba dadin zama da juna za mu ji ba. Inna da a zo a na bata zumunci ai gwanda ma kada a yi ko ba gaskiya ba? Inna ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba, jawahir ta suka daga kujerar ta rirrike kafar Inna tana gunjin kuka, Ki taimakamin inna kada rayuwata ta salwanta. Inna ki yi wa Dady magana ya janye maganar aurenmu. Innata kamo jawahir ta rungume ta tana rarashinta ki yi hakuri jawahir, komai nufin Allah ne, ba na son yin shisshigi a lamarin aure, don ba mu san abin da Allah ya boye ba, amma zan yi kiran Alhajin na yi masa maga…….sallamar Haidar ce ta katse mata zancenta. Ya shigo wujiga wujiga kamar wanda aka jefo har ya furgitar da Inna. Inna ta ce, Lafiya Haidar me ya same ka haka duk ka yankwane kamar marar lafiya.?” Ya ce, inna. Abba da Aunty sun takura min wai sai na auri waccan kwailar yarinyar. Inna ki dube ni yanda nake a rasa wanda za a ce na aura sai wannan tatsitsiyar, haba inna gaskiya ba a yi min adalci ba.” inna ta daga masa hannu ta ce, “To ya isa haka ka je gida ka kirawo min Auntyn taka. Ka biya gidan kawun naka ka kirawo min shi, ina son ganin sa. ya ce, “To ya yi waje cikin fushi. Jawahir ta sake fashewa da kuka ta ce Inna kin ji irin wulakancin da yake yi min ko, wai ba zai iya fadar sunana ba sai dai ya ce min kwaila ko tatsitsiya amma ake kokarin lika min shi haba inna ai ba ayi min adalci ba. Inna ta ce, “Ki yi hakuri bari su zo sai a san abin yi. Bayan sllar magariba Aunty ta iso shi kuwa Dady sai da aka yi sallar insha’i amasallacin gidan inna sannan ya shigo cikin gidan tuni daman jawahir ta koma gida haidar kuwa daman bai dawo ba. Bayan gaishe-gaishe da wasa da dariya na uwa da ya ya, Inna ta yi gyaran murya ta ce, ” Daman abin da ya sa na tara ku game da maganar auren yaran nan ne. Inna ga a hakura da hadin nan kada zumuncin da ake ta ikirarin ya zo yana lalacewa. Dady ya ce, ” Inna duk ki rabu da yaran nan insha Allahu hadin auren nan nasu babu abin da zai jawo mana sai alheri saboda bayan ranmu zumuncinsu ba zai lalace ba. Amma yanzu ba kwa ganin yanda ba su damu da junansu ba, nan gaba abin ya zame musu gaba me karfi. Inna tace, “Gaskiya haka ne. Aunty ta ce, “To yaran nan fa mu muka haifesu ba su suka haife mu ba, to don me za mu bi son rainsu bayan mun san gaskiyar magana inda take Inna ta ce, to shi kenan Allah ya yi mana zabi na alheri suka yi addua suka shafa kowa ya nufi gidansa. Yau da gobe taki wasa kwance ta shi babu wuya a wajen Allah cikin ikon Allah lokacin biki ya zo ana ta shirye shiryen biki. Biki ne da yaye da ‘yan uwa suke ta yi masa shiri na musamman wanda za mu ce su kadai suke yin abinsu, don Ango da Amarya na cikin mummunan bakin ciki da bacin zuciya. Ba yanda ba a yi d a jawahir ta je ta rabawa kawayenta katin biki ba amma taki da ta ga ma za a matsa mata sai ta gudu gidan inna. Da inna ta yi mata maganar rabon katin bikin sai ta sa mata kuka dole sai aminiyarta ce da manyan kawayenta suke ta shige da fice na bin kawayen duk inda suke suna kai musu katin biki na gayyata. ******** ******* ******** ********* ********* Bangaren Angon kuwa Haidar abun duniya duk ya dame shi, ganin da gaske suke lamarin nan ba za su fasa aura masa wannan kwailar yarinyar ba. idan ya zauna shi kadai yana yawan tambayar kansa cewa, “Wai su abba me suka gani ajikin jawahir har suke kokarin aura masa ita? wayarsa ce ta yi kara yana dubawa ya ga Abbansa ne da sauri ya amsa, “HELLO ABBANA. Abban ya ce, “Ka zo yanzu ina son ganin ka a falon sama.” “To abba ga ni nan zuwa. “Ya mike cikin hanzari ya nufi bangaren babanshi ya hau samansa. “Assalamun alaikum.” “Alaikas salamu, shigo Haidar. Aka amsa masa tare da ba shi umarnin ya shiga . Haidar ya shigo ya durkusa a gaban Abban nashi ya ce, “Abba gani. Abban ya ce haidar me kake so ka nuna min ne? kana so ka tozarta ni a idon duniya su san ban isa da kai ba?. Ya dago a firgice ya ce Abba me ya faru kuma? haidar na nema maka auren yarinya ka ki kula da lamarin ga shi yau saura kwana biyu daurin aure, babu wani shiri da kake yi. Yanzu da ba dan na bawa abokinka katunan daurin auren ya rabawa abokananka ba da haka za a daura maka auren ba abokin ango ko daya, kuma ko wajen jawahir din baka je ba bare ka san me take bukata da za ka ba ta ko? Haidar ya ce, ka yi hakuri Abba ganin dana yi kuna tsaye akan komai duk kun gama wani shiri da zan yi shi ya sa ban mayar da kai ba, amma don Allah Abba ka yi hakuri in an jima zan je gidansu jawahir din don na ji abin ta take bukata. “Yauwa Haidar ko kai fa Allah ya yi muku albarka . Ya dauko kudi dubu dari ya ba shi to Haidar ga wadannan sai ka ba wa jawahir din. “Abba da ka bar shi ga kudi can da na ware zan kai mata na shagalin ‘yan mata kawayenta. Ba komai hada ka kai mata gaba daya ai abubuwan shagalin da yawa. “To Abba an gode, Allah ya saka da alheri. Amin dana Allah yayi maka albarka. Da yamma Haidar ya gama shirinsa ya hau motarsa ya nufi gidansu jawahir. Ya tura maigadi ya yo kiranta . maigadi ya daga waya ya buga cikin gidan mummy ce ta dauka. maigadi ya rissana ya gaisheta kamar tana kalonsa sannan ya fadi sakon Haidar na son ganin jawahir. momy ta ce Ai ba ta nan tan gidan inna maigadi ya gayawa Haidar to sai Haidar din ya shiga ya gaisa da momy ya fito ya nufi gidan Inna. Yayi sallama falon ya shiga ya ga jawahir kwance kan cinyar Inna ya kalle ta ya doka tsaki. A zuciyarsa ya ce, “Sangartacciyar yarinya in an yi auren na ga jikin uban wanda za ki hau. Inna ta ce, “Lafiya daga shigowarka kake tsaki?” yace, “Bakomai inna suka gaisa suna hira tare ya dan taba wasan jika da kaka ya ce, “Inna tursasani fa aka yi na zo wajen waccan. Inna ta ce, “Ai ga ta bari na bagu waje. yace a a inna ki yi zamanki ba sai kin tashi ba,

ji zan yi dame da me take bukata. Inna ta ce bari na fita kwafi jin dadin sakewa.” Sunfi tsawon rabin awa ba wanda ya ce da kowa komai, Haidar ya kalli ta ya ya mutsa fuska tare da tabe baki ya yi tsaki, “Ke in banda kinci albarkacin iyayenmu da sai kin raina kanki, don ni banga abin so a jikinki ba. Domin baki da cikakkiyar surar dazaki ja hankalina. Don haka ma in kin shigo gidan sai kiyi hakuri da irin zaman da za kiyi don ba wai wani abu ne zai shiga tsakaninmu ba. Ya debo kudin da Abban ya bashi dubu dari ya jefe tada su. “Ga shinan ba don halinki ba kuma wai a aljihuna na baki ba Abba ne ya bayar a kawo miki tatsitsiyar kawai.” Yayi daya falon da inna tashiga yayi mata sallama, “Inna mun gama zan tafi don akwai ragowar shirin da ban kammala ba. Inna ta ce, “To Haidar a sauka lafiya, ya fito da kudi dubu hamsin ya ba ta ga wannan inna ke ma kya yi hidimar bikin. “To duk ni kadai Haidar ? to na gode Allah ya saka da alheri, ubangiji ya albarkaci wannan auren naku. Shi dai ya yi ficewarsa . INNA ta shigo gurin jawahir ta kula da halin datake ciki don saboda tsananin bakin ciki da takaicin da haidar ya haifar mata sai ya hadu ya dunkule mata a kirji ga hawaye ya ki fitowa bare in ya zuba ta ji sa ‘ida. Kan ka ce meye wannan kirjinta ya hau zafi ga ba daya jikinta sai ya hau kakkarwa yana bari. inna ta rikice tana cewa, “Lafiya jawahir, yanxu fa na barki kalau dake me ya same ki.? Ta nunawa inna kirjinta ta ce inna kirjina ne yake ciwo, “Da kyar take iya maganar. sai numfashinta yakoma fita sama sama, ba jimawa abu ya ci tura idan ta ja numfashin sai ya dade be dawo ba. Hankalin inna ya yi masifar tashi ta kidime da kyar ta iya kiran direbanta a waya ta kira shi ya zo da sauri suka hadu suka kinkimi jawahir suka sa ta a mota inna ta shiga ya ja suka tafi asibiti Inna asibitin da Daddy yake zuwa za muje?” inji direban. “EH can za mu je mana” suna isa asibitn aka dora ta abin tura marasa lafiya a ka shigar da ita wani daki. likitoci biyu suna tsaye akanta. Can suka fito inna ta mike da sauri ta tare su “Yaya likita? Yace, inna ki kwantar da hankalinki, damuwa ce ta yi mata yawa da bakin ciki, amma za ta samu sauki idan an ankiyaye dokokin da likita zai kafa mata. Yanzu mun ba ta gado an kwantar da ita.: A ka nunawa inna dakin da take ta shiga ta zauna a gefen gadon sannan ta zaro waya ta bawa me aikinta ta ce ta buga gidan Dady da gidan Aunty ta gaya musu. Cikin mintuna kadan ‘yan gidansu duka sun zo har Dady da momy can gidan Aunty ma ta sako Haidar a gaba dole ya tuko motar suka zo. Gaba daya sun gewaye gadon da take kwance, kowa ya sa mata ido. Likita ya shigo ya zare ledar karin ruwan da ta ya sa mata wata. likita ya gaisa da Dady ya ce, dady sai an rinka kula da lafiyarta dole ne a rinka barin zuciyarta tana hutawa don a samu nutsuwa a rinka kiyaye duk wasu abubuwa ko maganganu da za su rinka bata mata rai a rinka yawan lallabata da rarrashinta har ta warke, idan ba haka ba tana gab da kamuwa da ciwon zuciya.” Dady ya ce, “Ba komai likita insha Allahu za a kula kuma Allah ma zai kiyaye. Shin kuwa Haidar ya yi zukulu yana tunani a zuciyarsa ya ce, “Anya kuwa ba shi ya haddasawa jawahir wannan matsalar ba? shi fa musulmi ne ya kamata ya yarda da kaddara ko ba komai jawahir yar uwarsa ce yana da imani don haka ya tausaya mata halin da ya ganta a ciki. dazun nan ya gama gaya mata maganganu ga shi yanzu halin da take ciki. Dayan biyu ko rai ko mutuwa. Washegarin jikin jawahir ya yi sauki don tana iya komai da kanta wajen magariba Dady ya matsantawa likita sai ya sallami jawahidr sabo da gobe daurin aurenta Likita ya rubuta mata takardar sallama da magunguna Washegari aka daura auran Haidar da Jawahir, daurin auren da ya samu halattar manyan mutane da ‘yan boko abokanansu haidar da yaya Abba da Nasir. Anyi taro lafiya an gama lafiya mata kuma sun shiga hadaniyar biki. Haka kawayen amarya suke ta shiga da fice na gudanar da hidimomin bikin kawarsu, amarya kuwa ba ta um bare um-um kowa kallon sa take yi. kakarta ta wajen uwa Hajiya Rabi ta zaunar da ita tana yi mata nasiha ki yi hakuri jawahir ki zauna a gidan mijinki lafiya ba ki da wani gata da ya wuce dakin mijinki. Ki rinka taka tsantsan da harshenki, kada ki gaya masa bakar magana ko wace za ta sa shi yayi fushi saboda lahirarki.” kowa dai ya ta mata nasiha zai ce ta ji tsoron Allah ta yi biyayya ga mijinta. An gama biki amarya ta tare a tsantsareren gidan angonta da yake nasara G.R.A. Kowa ya fashe ‘yan kawo amarya sun watse sai ita kadai kwal a cikin gidan sai maigadi da yake bakin get. Tana zaune tana tunanin irin zaman da za su yi da HAIDAR har bacci ya fara daukan ta a zaune ta ji an turo kofa anyi sallama an shigo. Ta yi saurin gyara zamanta . Ya shigo dakin ya nemi waje ya zauna.

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *