SALON SO CHAPTER 8
Ta yi dan dum kamar ba za ta yi magana ba sannan
ta ce, “Kai da wa?”
Ya ce, “Ni da Kausar”
Ta ce, “Ko a musulunci dakin da ka kwana nan ne
yake da hakkin yi maka abinci. To amma tun da
hakan ba ta samu ba ni ya zama dole na hada maka, amma ita kuwa wadda ka ambata ban ga
dalilin da zan girka mata wani abu na ba ta ba, don
ba zamanta na ke yi ba, kuma ni na ajiyeta ba.
Kafin ya ce, wani abu ta juya tayi komawarta dakin.
Jawahir bata fasa hada break din ba don idan tayi
kamar za tayi fushi sai ta tuno abubuwan da Anti Maryam ta gaya mata to sai ta daure tayi ko ba
komai yanzu tana ganin nasara don kulawar da
Haidar yake yi mata ba kaman a farkon aurensu ba.
A babban falon ta shirya masa komai ta koma daki
ta tsala wanka ta yi kwalliya ta gani a fada da wani
tsadadden material ta yi kyau har ta gaji da kyan, ta sha adon gwala-gwalai kamar ka sace ka gudu.
Kamshi ne yake tashi a kowacce kafa ta jikinta. Ta
fito falon Haidar yana bisa tebir yana break shi ma
ya sha tsantsarerren adonsa da shiga ta alfarma.
Yana hango jawahir ya fara sambatu a zuciyarsa,
“Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi kyakyyawar halittar yarinyar nan, ko yaushe zan
ga fuskar da zan latsa jikin yarunyar nan, har na
gani gado daya da ita? Kai wannan rana da na
suma dan dadi Tina daya daga cikin ‘yan aikin
Kausar ne ta zo ta
kama kafar benen Haidar za ta hau, jawahir kuma sannan ta fito daga sashenta shi ne ta doka mata
tsawa, “Ke zo nan
Tina ta taho jikinta na rawa ta durkusa kasa a
gabanta, jawahir ta ce, “Uban wa ya ba ki ikon
hawa benen nan? Ko dakin sa’anki ne a ciki? Me za
ki yo? Wa ya aike ki?
Tina ta ce, Anti ce ta ce na hau na share.
Jawahir ta ce, “Wacece Anti?”
Tina ta ce Kausar Jawahir ta ce, “Ke dabbar ina ce
ko na ce
mahaukaciyar ina ce da za ki zo ki haye dakin megida?
Ko ku hudu aka auro ne ban sani ba? Tina ta
girgiza kai, “To wallahi ki sani wannan ya zamo na
farko na karshe ko falon nan kada na kuma ganin
dayar ku ta zauna a ciki, da kun shigo ku yi wajen
uwar dakinku ko kuma ku yi zamanku can bangaren masu aiki don ni ba zan yarda da
kwashe kwashe da tarkace ba.
Tina ta ce, “Ki yi hakuri Anti zan kiyaye gaba.”
Jawahir ta ce, “A’a ni ba Antinku ba ce, ga Antinku
can wadda ta kwaso ku ta zo ta zube ku. Ya kamata
a ce kuna gidan mazajenku kuna bautar aure amma ga shi kuna zaune kuna bautawa wata
katuwar banza, don kwadayi, wato kun fi
kwadayin abun duniya da rahamar Ubangiji ko?
Tina ta girgiza kai, jawahir ta ce “To ki gayawa
ragowar ‘yan uwanki ku yi kokari ku fito da mazaje
a yi muku aure ku je can ku samu ‘yancin kanku ku yi wa Allah bauta.
Tina ta rissina tana cewa, “Mun gode Anti insha
Allahu za mu gabatar da masoyanmu. Jawahir ta yi
mata izinin tafiya ta fita. Haidar yana zaune yana jin
su ko ba komai
zuciyarsa ta yi dadi da kalaman da ya ji jawahir tana yi yana alfahari da hankalinta. Gefe daya kuma
yana tunanin ko dai jawahir ta fara son sa ne don
ya ga kamar tana kishinsa, to Allah ya sa haka ne.
Kausar ta bude kofar sashenta ta fito tana yamutsa
fuska ta dokawa jawahir harara ta nufi wajen
Haidar tana yamutsar fuska irin ta marasa lafiya ta ce, “Darling cikina fa ya ki daina ciwon kuma sai na
rinka jin kamar yana harbawa ko cikin wata biyu
yana fara motsi ne?
Haidar ya kamo ta ya zaunar da ita kan cinyarsa,
“Kausar
kada fa ki wahalar min da baby, ba kya son cin abincin ne yunwa ce take sa shi motsin dole bude
bakinki na ba ki, ki ce. Ta bude ya zuba mata,
“Yauwa kausar ko ke fa ai gwanda ki ci.
Jawahir ta ji wani katutun bakin ciki da kishi ya
tokare mata makoshi, lallai ma tsanar da mutumin
nan yake yi min ta kai tsana, duk tsawon lokacin da na dauka a gidansa ya kasa kusantata amma daga
zuwan wata har ya ba ta ciki, wallahi ba zan yarda
ba sai dai a yi wacce za ayi.”
Ta nufi gun su gadan-gadan a lokacin da Haidar ya
sa mata cinyar kaza ke nan a baki jawahir ta
tankwabe tare da dankar wuyan Kausar ta ce, “Wallahi sai ta yi amansa, ai ni ba baiwarta ba ce da
zan yi mata girki ta zo tana ci.”
Haidar yayi yayi ta sake ta taki shi kuwa ya fitar da
hannu ya shara mata mari. Jawahir ta yi saurin cika
Kausar yayin da ta dafe kuncinta zafin marin ya
gigita ta inda ta rarumi faramtin tangaran me nauyi ta kwadawa Haidar a gabansa tuni Haidar ya dafe
wajen ya kwalla kara ya zube kasa.
Hankalin jawahir ya yi mutukar tashi da ganin halin
da Haidar yake ciki sai ta sa kuka na shiga uku
yaya, Yaya don Allah kayi hakuri wallahi ba da
sanina na yi maka ba, Yaya ka yi hakuri ka tashi na tuba na daina ba zan sake ba. Kausar kuwa kofa ta
nufa ta kirawo megadi da yaron gidan suka kama
shi suka sa shi a mota ta shiga ta tuka motar suka
tafi asibiti. Aka kama shi aka shigar da shi daki
suka tsayar da Kausar a waje can likitan ya fito ya
ce ta je ta nemo dan uwansa namiji. Kausar ta mike ta shiga motarta ta yi gidansu Haidar.
Ta yi salllama falon inda ta samu Abbansa da Anti ta
durkusa ta gaishe su ta ce, “Daman Haidar ne ba shi
da lafiya har an kwantar da shi a asibiti shi ne na zo
na fada
Cikin hanzari Abba ya mike ko direba bai jira ba ya fita ya hau motarsa ya tafi inda Kausar ta shiga tata
motar ta rufa masa baya. Anti ta ce mata, “Duk halin
da ake ciki ta yo mata waya ta gaya mata. Ta ce to.
Lokacin da su Abba suka isa sannan Haidar yana
bacci don haka Abban ya wuce office din Doctor,
likita ya mike tsaye ya mikawa Abban hannu suka gaisa, sannan suka zauna. Likita ya ce, “Daman
Alhaji larurar da take damun Haidar ce abin babba
ne. Cikin firgita da dimauta Abban ya ce, “Me ya
same shi? Likitan ya ce, “To dai a bincikenmu mun
gano
buguwa ce mai tsanani ya yi a gabansa wadda har ta jawo masa mutuwar gabansa, don ba shi da
wani kuzari da zai iya kusantar mace bare ya iya
biya mata bukatarta. Abban ya dafe kai tare da
fadin, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, yanzu shi
kenan
dana ya nakasa? Likita me ya jawo masa buguwar.? Likitan ya ce, “Kada ka damu Alhaji za mu yi bakin
kokarinmu na ganin ya samu lafiya ya dawo
normal.
Abba ya yi masa godiya ya koma dakin da Haidar
ya ke ya
zuba masa ido yana bacci. Jawahir kuwa tun bayan tafiyarsu Haidar asibiti ta
kasa samun sukuni sai kuka take yi tana tunanin a
wane hali Haidar yake yanzu, ta kasa samun
sukunin zuciyarta. Kawarta Bilki ta yi sallama ta
shigo, “A’a lafiya jawahir na ganki haka?
Jawahir ta ce, “Kyale ni Bilki na bi ta dokin zuciya na aikata abin da zai dame ni. “Me yake faruwa ne?”
Jawahir ta kwashe komai ta gaya mata. Bilki ta ce,
“Wallahi ba ki kyauta ba, don yanzu Haidar son ki
yake yi sosai da kin sani ba ki yi masa wannan
dibar albarkar ba, don ba mutunci ba ne mace ta
kai hannu kan mijinta da niyyar duka. Tace, “Uhm kyale ni Bilki zafin marin ne ya gigita ni
ban san lokacin da na kwada masa ba, karar da ya
yi ce ma ta dawo da ni hayyacina.”
Bilkisu ta ce, “Yanzu ba surutu za ki tsaya ba tashi
mu je asibitin ki ga yanda jikin nasa yake. Ta ce,
“Kai anya kuwa na je?” Ta ce, “Kwarai ma kuwa, ai tashi kawai mu tafi.
“To ai ban san asibitin da ta tafi kai shi ba.
“To bari na gano idan direban ya dawo sai mu
tambaye shi wanne asibitin ne, ta yi waje. A can
asibiti kuwa Abba ya koma gida Kausar tana
waje, Haidar ya farka Faruk ya gani a gefen gadonsa a zaune, Faruk ya ce masa, “Sunnu ya
kake jin jikin naka? Ya ce, “To da sauki zan ce,
“Haidar ya yi tsu can ya ce Faruk ina jawahir?”
Cikin mamaki Faruk din ya ce, “Me za ka yi mata?
Haidar ya ce, “So nake na san halin da take ciki.”
“Me ya same ta?” In ji Faruk, Haidar ya kwashe yanda abin ya faru ya gaya masa, Faruk ya ce, haba
Haidar me ya sa za ka mare ta? Ai kai ma ba ka yi
dai-dai ba. Wallahi yanxu jawahir tana tsananin son
ka tun da take yi maka duk abin da kake so, kuma
take tsananin gudun bacin ranka, ga shi har ta
kasa jure kishinta ta nuna karara. Haidar ka rage zafin zuciya in ba haka ba wata ran zai kai ka ya
baro ka.
Haidar ya ce, “Ai yanxu ya ma kai ni ya baro din, ni
dai don Allah so nake yi ka je gidan ka gano min
halin da take ciki inda hali ma don Allah ka rarrashe
ta ku taho tare.”26