SALON SO CHAPTER 7
Yana saukowa babban falon ya ji fitinan nan
kamshi jawahir mai har gitsa masa kwalkwalwa ya
yi hamdala ga ubangiji yayi godiya ga Allah da
jawahir ta dawo hannunsa
Bai ganta a babban falon ba don haka ya yi sallama
a nata falon ya tura kofar ya shiga. “Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya
hallici wannan kyakyyawar budurwar yarinya sai
ka ce balarabiya. Anya ba aljanu ne suke
yaudararsa suna neman bude masa ido ba.?
“Me ya sa kika tafi wani wajen ba da izinin mijinki
ba har tsawon shekara daya? Kina ganin kinyi dai dai kenan? Ko kin manta aure kike yi? Ya za ki da
dumbin zunubin tashin hankalin da kika sa mijinki
a ciki.?”
Ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka don Allah
yaya kayi hakuri ba zan sake ba. Ya ce, “Shikenan
ba wani abu sai dai ki kiyaye gaba. Kin ga yanzu ba mu kadai ne a gidan ba kina tare da abokiyar zama
don haka ki kiyaye kin san ba na son hayaniya
bare abin da zai daga min hankali. Shiru ta yi ba ta
ce komai ba don ta san idan ta yi magana hawaye
ne zai zubo don wani dunkulallen abu da ya tokare
mata makogaro, ni na san ba komai ba ne sai kishi. Ya ce, “Ba ni break din na ci, “Ta mike tsam ta kai
masa gabansa ta durkusa tana hada masa shayin
ya yi kauri da madara, bonbita, neskofi, da
sauransu. Ta bude masa fulas din soyayyen dankali
ne da wainar kwai, sai gasasshiyar kaza da ta gasa.
Ya ce, “Je ki falo na ki dauko biredi. “Ta dan yi dum ya ce, “Ba ki ji ba ne? Ta ce, “Yaya matarka fa tana
saman?
Yace, “Ba komai je ki, ki dauko min ai bacci take yi.
Haka ta tafi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki
shi dai yana tsananin kaunar jawahir yarinya me
tsananin hankali da biyayya ga saukin kai ga kuma uwa uba ta hada komai da yake tsananin SO a jikin
mace.
Jawahir dai har ta hau sama ta sauko ba ta ga
matarsa ba. Ta shigo falon ta da siririyar sallamarta
ya amsa mata ta zo gabansa ta durkusa ta miko
masa, ya ce, “To zauna mu sha ta girgiza kai, ya hada kai tare da cewar ba na son gardama zauna
mu sha.
Ta zauna suka fara birek Haidar danna birek dinsa
yake yi yana ci sosai don yaushe rabon da ya yi
break ma a gidansa tun jawahir tana nan.
Ita kuwa a yangace ta ke ci kamar mai cin magani ya kalle ta ya ce, “Ke ba za ki bude baki ki ci ba ne?
Wato kin fa dawo za ki rinka kin cin abinci ki kuma
ramewa ko? Can da yake suna tursasa ki ki ci ai ga
shi nan kin yi kiba to ni ma na daina kyale ki dole
na matsa miki ki ci ki koshi. Haka ya takura ta ta ci
da yawa. Daga nan ya fita ya tafi office cikinsa da koshi.
Jawahir kuwa ta rufe kofar falonta ta yi zamanta a
dakinta. Dan haka ba ta san wainar da suke toyawa
ba. Da ta ji yunwa ragowar birek dinsu na safe ta
dauka ta ci ragowar kazar da Yogourt roba biyu ta
ji ta koshi kuwa. Shi kuwa Haidar a office duk ya kasa samun sukuni
ganin yanda jawahir ta koma. Karfe shida ya tashi
daga office ya yi gida. Ya yi sallama falon shiru ba
kowa bare a amsa masa. Ya haye samansa ya tube
ya yi wanka ya dauro alwala ya yi sallar magariba
ya sako kananan kaya ya sauko kasa ya shiga dakin Kausar.
Tana tare da ‘yan aikinta suna aikin bautarsu na
matsa mata kafa wannan abu yana konawa Haidar
rai.
Suka yi gaggawar fita daga dakin. Ya zauna tare da
cewar, “Ina abincina.? Ta ce, “Na ga ba ka cin abincin masu aiki shi ya sa
ban ajiye maka ba, ya ce, “Okey kin kyauta. “Ya
mike ya fice kawai ya shiga dakin jawahir shiru sai
dai ya ji motsin ruwa a bandaki wanka take kenan,
don haka ya nemi gefen gadonta ya kishingida
yana shakar daddadan kamshin da dakin ya ke yi. Jawahir da ba ta san da mutum a dakin ba ta gama
wankanta ta dauko tawul iya gwiwa ta fito gashin
kanta duk ya bazu ya manmanne mata a fuska ta
bude kofar tolet din ta fito. Tana ‘yar wakarta ta
nufi gaban mudubi. Subhanallahi! Ai tuni hankalin
Haidar ya so gushewa don ganin kyakkyawar kirar jawahir, jiki mulmul da shi ga shi jajir santsi yake yi
da sheki, santala santalan cinyoyinta kamar na
Baturiya.
Ta zauna gaban mudubi ta fito da mayukanta da
hadin turarukanta ta fara mulke jikinta. Sam ba ta
kula da wani a dakin ba tana shirin yaye tawhul din don shafe jikinta sai ta hango kamar mutum ta
mudubin tuni ta razana ta yu kara cikin
dimautacciyar murya da takaicin rashin kwancewar
tawul din ta ya ce, “A’a jawar meye haka?
Ta ce, “To Yaya ai tsoro na ji ban san ka shigo ba, ya
ce, “Okey sorry, sorry je ki ki gama shirinki. To kuma sai ta kasa shirin a gabansa sai daya dakin
ta shiga ta karasa shirinta ta fito cikin doguwar riga.
Tsarki ya tabbata ga Allah, wannan yarinya da
kyau take ga iya diresin kamar aljana. Abun da
Haidar yake fada kenan a zuciyarsa. Har ta zo
gabansa ta durkusa ta ce, “Sannu da zuwa yaya.” Ya ce, “Yauwa jawahir kin ci abinci? Ta girgiza kai
ya ce, “To me kika ci.?
Ta ce, “Yogourt da ragowar naman daxu. Ya ce,
“Shi ne zai rike miki ciki? Me ya sa kike son sakaci
da cikinki ne?
Me ya sa baki girka kin ci ba.?” Ta ce, “Ai gani na yi ba ni kadai ce a gidan ba.
To in ban da abinki jawahir ke da gidanki sai an
girka an ba ki? Ke da na san ki da kyankyami, za ki
rinka cin abincin me aiki ne?” Ta girgiza kanta, ya
ce,
To kin gani ki rinka girkinki kina ci kin ji ko.
Yanzu me za ki ci, ko za mu fita muje mu sayo wani
abin ne ko kuma mu je gidan abinci.
Ta girgiza kai, “A’a zan girka wani abu yanxu
Ya dube ta ya ce, “Dare be yi miki ba. Ta ce, “A’a ba
komai. Tun da ta soma magana yake jin wani abu, zil-zil yana tsarga masa don jin dadin muryarta da
shaukin begenta. Ya mike ya fita jikinsa a sanyaye
kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya fito ya hau
samansa sai ya tarar da Kausar a kwance a kan
gadonsa tana nishi. Ya isa kusa da ita da saurinsa
ya ce, “Lafiya?” Menene ya faru? Ba yanzu na barki a dakinki ba. Ta ce, “Wallahi fama nake yi da ciwon
mara tun safe daurewa kawai na ke yi ka daure ka
kaini asibiti yanzu.”
Haidar ya ce, “Yanzu ya dace mu fita asibiti mu bar
jawahir ita kadai a gidan? Kausar ta ce, “Haba
Haidar me yake damunka ne me zai same ta, ba ga masu aiki nan a gidan ba, ko ka fi so ni na kwana
ina murkususu?”
Ya ce, “To shikena tashi muje. Lokacin da suka fito
don tafiya sannan jawahir ta fito falon za ta shiga
kicin wannan shi ne karo na farko da jawahir ta ga
Kausar ita ma Kausar ta ganta. Ba su yiwa juna magana ba sai Haidar da ya ce zamu fita yanzu
zamu dawo.
Jawahir ta shiga kicin kamar ba ta ji me yake cewa
ba, suka fice jawahir ta zauna a babban falo ta
kunna kallo, salkamar da taji ce ta sata saurin
juyowa. “Lalala Bilki yau ke ce a gari?” Gaskiya ba ki da alkawari, ni na za ta ma kin manta da ni.”
Bilki ta ce, “Haba jawahir ya zan yi na manta da ke,
kin san tun ranar da muka zo nan gidan Haidar ya
kore mu nake jin tsoron kada nazo na jawo miki
wata fitinar. To sai da na ji labarin aurensa na so na
zo sai na ji tsoron kada ya cire min kafa daya shi ya sa na hakura na fasa zuwa.
Jawahir ta ce, “Yanzu ya aka yi kika zo?
“Uhm ke dai bari, tare muke da direba munje gidan
kawar Hajiyarmu kusa da ku ne na ga ba zan iya
wuce gidanki ba.
Jawahir tayi murmushi, “Amma gaskiya na gode na kuma ji dadin zuwanki, don akwai labari da labarai
ma sai dai ga shi dare ne da za ki daure da kin zo
min da rana mun wuni muna hira.
Bilki tayi ajiyar zuciya ta ce, “Kina ganin in na zo
babu wata matsala ko Haidar yana nan.”
Jawahir ta ce, “Ba komai wallahi ba zai ce miki komai ba.
To shi kenan jawahir na fita kin ga dare ya yi sai na
zo din
“Okey Bilki na gode don Allah ina sa ido kada fa ki
ki xuwa.”
“Insha Allahu zan zo” Tayi sallama ta tafi. Jawahir ta soya indomie da kwai ta gasa masa kifi
ta hada masa lemon kwakwa da madara ta zuba a
jug ta cilla masa kankara ciki ta jere komai a kan
tebir din falon ta shiga sashenta ta ci na ta ta watsa
ruwa ta wanke bakinta ta je ta yi kwanciyarta. Sai
goma na dare su Haidar suka dawo. Kausar ta wuce dakinta Haidar kuwa ya nufi tebur din da
abinci yake don yunwar da yake ji tun break din
safe da ya yi a dakin jawahir.
Ya bude komai ya ci ya yi kat, ya rinka shan lemon
kwakwar nan yana nishadi a kasan zuciyarsa
kuwa sai shiwa jawahir albarka yake. Da ya gama ya murda kofar dakinta yau ma a rufe gam, ya
koma dakinsa yau ma ya kwanta yana murkususu
da ya rufe idonsa kyakkyawar surar jawahir yake
gani. Ga wata muguwar sha’awarta da tayi masa
mugun kamu haka ya rinka juyi yana murkususu.
Sai da asuba ya tashi ya yi alwala ya yi Raka’atainil Fajri ya yi ta karatun Alkur’ani ya yi addu’arsa ya
shafa. Ya dade yana lazimi sannan ya sauko falon
kasa ya zauna ko zai ga jawahir ta fito ya samu ya
ganta ko zuciyarsa ta lafa da tsananin radadin
kaunarta.
Ya yi sa’a kuwa ta bude kofarta ta fito tana sanye da abaya da karamin farin hijab, da ya sha adon
bakin les, tana rike da carbi a hannunta ta yi kyau
kamar ita ta yi kanta.
Duk motsin da tayi sai komai na jikinta ya motsa.
Yanda jikinta yake girgiza shi yake dada motsawa
da Haidar sha’awarta. Jawahir ta yi mamakin ganinshi a falon, don haka
ta karasa gabansa tayi saurin xubewa ta gaisheshi.
Ta mike ta nufi kicin idonsa na kanta.
Ya ce, “Jawahir” Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya
ce, “Don Allah idan break za ki hada ki hada da
mu.25