Kai wanne irin mahaifi ne, “Me yasa baka san daraja da kima irin ta “Ya mace ba?
Don ta na ‘yarka, “da kai za’a taru a ci zarafin ta?” ku sake ta ko kuma wallahi duk da kana mahaifin nata na kai ka inda za’a k’watar mata ‘yancin ta a Matsayin ta na ‘ya mace.
“Kai d’an iska.Mahaifina ya daka mishi tsawa.Ina jin k’warton ta ne kai ko?
Balagar taka har ta kai ni da ‘yata ka riqa d’aga min jijiyar wuya.
Alh.Mikai’l ya dakatar da shi.”Kaga kwakis.
“Komai yaji, k’yaleta ba sai na gani ba.
Lallai Kwakis, Ya nake ganinka wani sha-sha kace kai ɗin ka iya haihuwa wannan ƴar dumaduma haka, kalleta da gani za’a huta a wajennan domin ta cika ta yi cindum
ya faɗa tare da kaiwa Kwakis duka su duka suka fashe da dariya
Alh. Mika’il yace.
“Kawai abinda ya kamata shine, ka saka min ita a gasar CACA muddin na ciyo ta zan mallaka maka kud’adenka idan kuma ka fad’i duka kud’in sun zama naka.
Albarkacin haihuwa
Waro ido Baba na yai.”Da gaske kake?
“Ahaf! Ina maka k’arya ne?
“Na rantse da gaske nake.
Kwakis ya k’yal-k’yale da dariya irin ta shakiyun tasha.kana yace.” Ka saka a ranka ka gama samun Ummy.
Dariya su ka yi gaba d’aya.
Ni kuwa Ummi cikin kuka na tashi na bar wajen.Saurayin na biye dani.
Sassanyar muryar sa ta katse min kuka na.
“Kiyi haquri.ki daina kuka Ummi komai yai farko zaiyi ƙarshe.
Ya fito da tissus.fari qal ya mik’o min tun kafin na karb’a k’amshin ya riga da ya gama to she min kunnuwa.
“Karb’e Ummi goge Fuskar ki.
Juyo wa nayi a mamakance ina mamakin ina yaji sunana.
Kina mamakin yadda akayi nasan sunanki ko?
batare da ya jira na bashi amsa b yace
”A bakin mahaifinki naji sunanki.
Lokacin da yake magana da Alh.Mika’il.
Da yake kinsan shi Alh.Mika’il sanannen mutum ne a garin nan duba da duk garin nan ba gidan da ake rayuwa irin ta gidansa kowa ya san da haka.
Yaransa kaf basa da kamun kai.duk irin rashin tarbiyya, irinta Sumayyah.Babban yaronsa Ali, yace gudu ban guri.sai uwa uba kuma ‘yar k’aramar ‘yarsa Farisa. To gara Sumayyah ita tana zama a gida sab’anin Farisa da sai ta Shekara tana yawon Duniya, ba karatu take ba ba komai ba.nayi mamakin yadda naga mahaifinki tare da Alh.Mikai’lu.
Shiru nayi domin kuwa bana da Amsar bashi.
Yaci gaba da cewa “Ki sani Ummi na tsogunta miki rayuwar Alh.Mikai’lu ne domin ki guje duk wata hanya da zata had’a ki da shi.Mutumin banza ne na bugawa a jarida.neman mata kuwa kamar bunsuru haka yake.
Zaki yi mamaki yadda nasan sirrin gidan Alh.Mika’ilu, da gidan mu da nasu suna fesing d’in junane.
Ko ma ba haka ba kowa a garin nan yasan zuri’a irinta gidan Alh.Mika’ilu zuri’ar banza ce.
“Ni suna na Dr. Yusif.”Ibrahim Shammal.
Saurin d’agowa nayi na zuba mishi ido.
Ibrahim Shammal.nayi sub’utar fad’a bansan cewa zancen ya fito fili ba illah ji da nayi yace.”Yes of coures.
Ni da kai na fa.
Mamaki ya kama ni.Alh.Shammal sanannen mutum yana daga cikin manya manyan masu fad’a a ji a k’asar nan. “Ummy ina zaki je ne haka?
Gida na fad’a baki na na k’yarma.
“Muje na raka ki.
“No, ka barshi ko iya haka na gode da kulawar ka gare ni, Ubangiji ya kasa maka da Alkhari kamar yadda kayi min.
Murmushi yayi, “Karki damu Ummy.Ina tare da ke, Har kullum nasiha ta a gare ki ki riqe mutumcin ki kalau.
Ngd da kulawar ka Insha Allah zanyi amfani da shawararka.
Ya dad’e tsaye yana kallonta har sai da ta b’ace wa ganinsa yarinya me nutsuwa da hankali.” Amma tayi rashin mahaifi na gari.
Isa ta gidan Dillaliya, ban dad’e ba muka fito tare da ita.
Shigar mu gidan, tarar wa nayi Umma ta fito da gadon.a qofar d’akinta.
Mu kad’ai take jira.
Yatsina fuska dillaliyar tayi kafin tace.
“Oh wannan gado ma ai duk gara ta zafce rabin sa.
Umma tace ki duba da kyau jan katako ne taya gara zata ce rabi, gado lafiyarsa kalau.idan yayi miki nawa kika siya?
To kinsan da shike yanzu damina ce ba wani ja kayan suke ba dubu takwas.
“Umma ta rik’e baki.”Haba dillaliya ki duba fa da kyau, wannan gadon lapiyayye shi za’a kira wa dubu takwas.
Kinga.”Habiba idan zaki siyar min a haka to idan ba zaki siyar ba na kama gaba na ina da safgogin yi a gida.
“Haba me ya kawo haka da ba siyar wa zanyi ba kinga ai ba zan kiraki ba, Amma don Allah ki d’aure ki qara wani Abu.
“To naji.na qara d’ari biyar.
Umma tayi jim daga bisani kuwa tace.”To Allah yai musu Albarka.
Kud’in ta fito da su tare da miqa ma Umma.
Ni kaina ina tausaya wa rayuwar Ummar mu ta na qoqari a kan mu matuqar gaske duk wasu kaya nata sun qare a dalilin hidimar da take yi da mu.
Muna zaune na zuba ma mai kwasar kayan gado ido ina hawaye.”Yanzu shike nan wannan gadon shine kad’ai wanda ya rage ma Ummar mu, kuma gashi a yau ma ta rabu da shi.
Fakam!Fakam.haka ya fad’o bako sallama yana k’yal-k’yatar dariya. “Habiba ! “Habiba !!
” Yau ta qare kenan d’an guntun gadon da shine kad’ai ya rage, yau tsiya ta sa an kad’ar.
“Hhhhhhhhhhhhhh!
Kuka na ya fito a fili ni Ummi wannan wanne irin Mahaifine Allah ya bamu?
Umma dai shiru tayi ta na kallonsa takai ci ya hanata furta uffan.
Sallamar Malamar makarantar su Amina ta katse shi daga raratun da yake yi.
Da sauri muka mik’e ni da Umma, a she kam abun da muke tunani ne ya kasance wato, Amina ce sharb’e kamar gawa, ciwonta na seckelar ya tashi.
Innalillahi wa inna ilai hirra ji ‘u na.
Ita ce kalmar da Umma ke ta faman nanatawa ke nan.
Da sauri na suri Amina, ikon Allah sai kallon mu Baba keyi yana dariya.tirqash!
Kud’en dake hannun Umma gaba d’aya karb’a nayi na fito da sauri na tari me napep.
Sai assibi.Amina ta fita hayyacinta matuqa.
Sai wani irin numfarfashi take yi.
GIDAN MIKAI’LU DUNIYA DA’DI.
Alh.Mika,lu ne tsaye, daga shi sai gajeren wando da yar k’aramar T.shet.tumb’ur -tumb’ur ya ta fo za ya shiga band’akin dake waje.
Da sauri Sumayyah ta qaraso tare da ruqo shi tace.”Daddy dakata na fa riga ka tun dazu nake sauri zani tafi wajen birthday d’in Surayya Abdullahi.
“Mika’il yace haba Baby, ki d’an dakata na matsu ne da yawa, Ina toleit d’in dake dakunan gidan?” Kinsan ni tolet d’in d’akina ya samu matsala.na d’akin Mum d’in ku kuma ta na ciki ta kulle kin san idan ta soma abu d’aya kamar mai shirin haife ciki.
Sumayyah ta kyal-k’yale da dariya kafin tace.”Gaskiya Daddy ni dai sai na fara shiga.
“To kiyi sauri ki fito, domin kuwa ina da baqon da zai zo ya gana da waccen BAGIDAJIYAR ‘yar uwar taki.
“Ok Bara nayi sauri na fito.
Mintina k’alilan Sumayya ta fito daga ita sai farin tawul.
Alh.Mika’l na zaune, A falo.
“Ke Baby, wannan wanne irin wanka ne hak
Shaf-shaf, ” Anya kin d’arje jikin ki ta ko ina?
Turo baki tayi.”Kaga Daddy na kira Ruk’y tun d’azu a waya a kan ta zo ta cud’ani, shiru ba ta zo ba da naga tana niyyar b’ata min lokaci shi ya sa nayi a bu na, buri na dai naga naje Birthday d’innan domin nice ta hannun dama, kuma fa gayu zasu so a wajen ba irin local girils d’innan bane.
“Da kyau Baby.Amma don Allah idan zaki tafi ki tafi da Ruk’y domin ina son ta turo min dancy warki Baby, don Allah kiyi rawa mai kyau kada ki bada ni.a rink’a cewa Sumayya ce ‘Yar gidan Alh.Mika’il bata iya rawa ba, kinga bazan so haka ba.ya fad’a tare da kwashewa da dariya.
Turb’une fuska Sumayya tayi ita a lallai bata so haka ba.
Jawo kayan makeup tayi, tana guna gunai da baki Um, um Daddy kai ma fa kasan ni ba baya bace wajen rawa, tun da haka kace nama fasa zuwa.ta watsar da kayan makeup d’in tsakar falon.
Cikin sauri ya taso ya soma da rarrashinta. tare da tattaro mata kayan da ta watsar d’in a k’asa. sorry, sorry Douther.” Na fa san ke gwana ce in dai so ki dage ne tare da zage kwanji.
Mai ya d’auko ya soma da shafa mata .
Ya riqe kunnensa uwa mai neman gafara sorry Baby na.
Dariya tayi.
Shigowar mai mata Makeup ya katse Summayya.
Tsawa Summtayya ta daka mata wanda ya sa ‘yan cikin ta hautsinawa na wucin gadi.
“Daddy ka ganta ko?
Sai yanzu ta ke shigowa bayan ta raina min hankali, kaga da na tsaya jiranta da tuni ko wanka banyi ba, A gaskiya Daddy a sake min wata me yin Makeup d’in domin mddin nace zan riqa jiran wannnan wata rana sai nayi missing d’in wani party.
Alh.Mika’l ya dubi Amina mai makeup yace.” Duk sadda ki ka kuma kuskure irin wannan ki sani wallahi zan sake ki, kinji ko?
Amina tace.”Ayi min Afuwa Daddyn Summayya.
“No ba Afuwa ta zaki nema ba Summayyah ki ka b’ata wa rai don haka Afuwar ta zaki nema kin gane?
Ok, Sumayyah kiyi haquri, ina neman Afuwa.
Gwad’a kai tayi ba tare da ta ce uffan ba.
Zama Amina tayi ta ci gaba da zuba wa Summayya.Makeup ta gani a fad’a.
Shigowar wani mutum ya katse, su wanda kallo d’aya zakai mishi ka tabbatar d’an daudu ne, duba da irin karairayar da yake yi.
Matsowa yai daf da Summayya.ya d’auko wani matsatssen d’inki.yana nuna ma Summay.yace ‘yar lelen Daddynta ince wannan d’inkin yayi miki ko?
Miqewa tayi tare da yin tsalle, tsigen d’an ficicin tawul d’in ya b’ingele.
“Sai kinyi babbar tela.
Shi kuwa jin an kira sa da mace kuma da ma abinda yake fata kenan ya sa shi yin murmushi.
” Gaskiya d’inkin nan yayi sosai kuwa ta fad’a tana qoqarin zira riga.shi kuma gogan naku ya zuba mata ido k’ur.
Mika:il ya zaro k’udi da bai san iya a dadin su ba ya miqa mishi yana cewa ka sha shagalinka…….
A’a Daddyn Summy “Don Allah ka bar d’anganta ni da k’ato meye ban-banci na da Summayyar taka.K’ululan gaban.ai baka sani ba Daddyn Summy abu d’aya na tsana a rayuwa shi yasa za ka ganni kamar namiji.
Ni fa mace mama na ta haifa ko da naga na fara k’ula-k’ulan nan na gaba tuni na fice na zama namiji shi yasa wani lokacin kaji wasu na d’anganta ni da Namiji idan ba ni na tunasar ba.
Gaba d’aya suka k’yalk’yale da dariya harda Summayya.da izuwa wannan lokacin ta gama saka kayan.sakin baki Daddyn yai yana duban ta, ” Summmy na wankan injin kinga yadda kika yi kyau kuwa?
Juyawa tayi ta kuma juyawa.
Wayar sa ya jawo ya dinga yi mata potona shi da ita.
Mika, l ya juyo ga d’an daudun yana cewa.
“Dama ina da wata k’angatarriyar ‘ya marar ji.Bagidajiya ina so don Allah ka gyara min ita da kalar d’inkunan da kake ma Summy, so nake naga ta waye ta fita daga duhun kai.
Ka auna ta ka kuma koya mata yadda ake saka kaya zan biya ka ko nawa ne bara na kira ta.
“Maryam ! Maryam !!”
“Na’am Daddy.
“Zo ina son ganinki.
Sanye cikin kamillalliyar shigar doguwar hijab ta qaraso.tare da d’urqusaws har k’asa.
“Gani Daddy.
Mayar da duban sa yai ga d’an d’audun yana cewa ” Ka ganta nan so nake kayi mata kaya matsattsu.daga yanzu ina so ka fara koya mata tirenin d’in wayewa.ina so ta goge ta waye ta iya shiga irinta ‘yan birni.
10,11