SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 2 BY FATYMA SARDAUNA
Www.bankinhausanovels.com.ng
” Lafiya kuwa Zaid wakake nema ne ?” Bash yatambayeshi,, ɗan taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa ” bakomai kawai ina duba yanayin unguwar ne ” yaƙare maganar yana mai komawa cikin motarsa yazauna,,, sama sama Bash da Zaid sukayi magana, domin kwata kwata hankalin Zaid baya jikinsa, burinsa kawai shine idanunsa su sake yi masa to zali da wannar kyakkyawar fuska da jikin, daya gani…..+
Tunda Zahrah tafito daga gidan su Husnah tafuskanci cewa da akwai mai binta a baya, hakan yasanya taji wani irin tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, don haka ta ƙara ɗaga ƙafufunta, “Assalamu Alaikum !!” muryan Namiji mai cike da kamala ya doki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya da tafiyan da takeyi batare da ta juyo ba,, cikin takunsa na burgewa ya ƙaraso gareta, kyakkyawan saurayi ne, mai ɗauke da launin fata choculate colour, dogo ne amma ba har canba, yanada faffaɗan jiki mai burgewa, sannan yana da kwarjini ba laifi,, murmushi yayi mata haɗe da cewa “Ƴan Mata bazaki amsa sallaman nawa bane ?” saurin sunkuyar da kanta ƙasa Zahrah tayi haɗe da cewa “Wa’alaikassalam”
Lumshe idanunsa yayi domin kuwa bakaɗan ba zazzaƙar muryarsa tadaki ƙahon zuciyarsa ” Sunana JABEER, Idan bazaki damuba, inaso kibani adireshi’n gidanku, sai nazo, domin a matsayinki na mace mai mutumci baikamata natsaidaki a bakin hanya ba ” Jabeer yafaɗa hakan yana mai kafeta da idanu,, gaba ɗaya kanta ɗaurewa yayi don haka, batare da tace dashi ƙala ba, tacigaba da tafiya, da sauri sauri,, roƙonta Jabeer yashiga yi akan ta tsaya ta saurareshi, amma ina Zahrah ƙara ɗaga ƙafanta tayi domin ita tsoro ma yabata, ganin da Jabeer yayi cewa bazata tsaya bane yasanya shi ƙyaleta kawai tayi tafiyarta, amma a zuciyarsa ya ƙudura aniyar nemota komai daren da ɗewa ….. Zahrah tana komawa cikin gida kaitsaye ɗakinta tawuce, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa a kai akai tamkar wacce tayi gudu, idanunta da suke lumshe ta buɗe su ahankali, haɗe da da sanya harshenta ta lashi lips ɗinta na ƙasa, Allah yasani gayen ya burgeta amma kuma tanajin tsoro gaskia, domin bata saba tsayuwa da samari ba……
Birgima kawai yakeyi akan makeken gadonsa, kwana huɗu kenan daganinta amma da ya rumtse idanunsa, hoton kyakkyawar surarta yake gani, baisanta ba, baisan wacece itaba, amma wani irin sha’awarta yakeji, tabbas yazama masa dole komawa unguwar Suleja ko Allah zaisa yasake ganinta,, wayarsa dake ringing ne yakatse masa tunanin da yakeyi, DADY shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayara, ɗaukar wayar yayi a kasalance haɗe da karawa akan kunnensa “To” kawai naji yace haɗe da cilli da wayartasa gefe, tashi yayi daga kwancen dayake haɗe da ɗaukan rigarsa yasanya, ya fice daga cikin ɗakin…..
Kai tsaye babban falon Dadyn nasa yanufa, can ya iske Dadyn nasa tare da Mom ɗinsa, zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, fuskarnan tasa babu yabo ba fallasa, yace “Dady gani ” Gyara zama Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da cewa ” Banaƙira ka bane don muyi dogon magana, naƙiraka ne don na sanar maka cewa zuwa yanzu yakamata ace kafitar da matar aure, kagama karatunka, ga kuɗinan kana samu ba’adadi, to mai yarage maka idan banda Aure Zaid ? a gaskia banajin daɗin zamanka haka ba aure, saboda haka kafito da matar aure “
” Yauwa gaya masa dai Alhaji, tunda ni nayi maganar har nagaji bai ɗauka ba, ga Khausar ɗiyar ƙanwata nan ma, sai ayi tuwona mai na ” Mom tafaɗa tana murmushi,,,,
Dasauri Zaid yaɗago yakalli Mom ɗintasa, jin abun da take faɗa, wai Khausar, cab aiko mata sun ƙare a duniya bazai auri muciya da zani ba, yanda yasan mata ciki da bai, yana da tabbacin cewa Khausar tana ɗaya daga cikin irin matannan marassa ni’ima wanda idan kana sex dasu zakana jinsu kamar dusa, babu wani ɗanɗano,,
“Kayi shiru” Dad yakatsesa daga tunanin daya keyi,,
” ka ƙara bani lokaci Dad insha Allahu zan kawota nan bada jimawa ba, amma gaskia maganar Khausar Mom ki barshi, domin kwata kwata ni bana jinta acikin zuciyata ” yana kaiwa nan a zancensa yasakai yafice daga cikin falon,, da idanu kawai Dad da Mom suka rakasa, har abada shidai Zaid bamai iya masa sai Allah, duk yanda ka ɓullo zaice ba haka ba…..
Koda yakoma ɗakinsa wanka yayi, haɗe da ficewa daga cikin gidan baki ɗaya,, baizarce ko’inaba sai babban gidan giya dake Abuja, can yaje yacika cikinsa yayi tatul, daganan yasamu abokiyar shaiɗanansa, suka yi watsewarsu…..
Zahrah sunfara Exam, don haka tuni kanta yaɗau zafi, karatu kawai takeyi baji ba gani, cikin ikon Allah kuwa komai nata yana tafiya adai dai, domin dai tana sa ran cewa zata samu kyakkyawan sakamako,,,
Hadari ne yahaɗu sosai acikin garin, yayinda sama tayi baƙi, ruwa ake tsammata yanzu ko anjima, yau amakare suka fito da ga exam, duk yanda Husnah taso Zahrah tashiga su rage mata hanya ƙiyawa tayi dole yasa Husnah ta ƙyaleta, tana fitowa daga cikin makaranta, ruwa ya ɓarke tamkar dama jira ake tafito, duk adaidaita sahun da Zahrah tatare baya tsayuwa, domin ruwan ƙara ƙarfi yake, jikin wata bishiya Zahrah ta lafe, duk da kuwa cewa ruwan baifasa dukanta ba, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe jagwab, ba abun da kayanta suke sai ɗigan ruwa, rigace irin rover gown ɗinnan ajikinta, saikuma rover hijab da taɗaura akan rigan, sanadin jiƙewan da sukayi yasanya, kayan lafewa acikin jikinta, take komai najikinta ya bayyana, hatta shatin breast ɗinta saida yabayyana, domin rigar ce kaɗai ajikinta, batasa breziya ba,, abu kamar wasa haka aka share 1 hour ana tafka ruwan sama, gashi duk bayan minti ɗaya dare ƙarayi yake, sanin cewa tsayuwarta a wajen kan iya haifar mata da matsala, yasanya ta shiga tafiya a cikin ruwan duk da cewa bata ko iya ganin gabanta,, gudu kawai yake shararawa akan titin batare da yayi tunanin komaiba, daidai Zahrah tahau kan tsakiyar titin, dai dai shikuma yaƙaraso wajen,,, wani irin burki Zaid yataka da ƙarfin tsiya, domin ƙiris yarage yabita kanta,, Zahrah kuwa tsabar firgici kasa motsawa tayi daga wajen, hannayenta taɗaura akan kunnenta haɗe da rumtse idanunta gam,, tundaga ƙasanta yasoma kallonta harzuwa samanta, saurin rumtse idanunsa yayi alokcin da idanunsa suka hasko masa shatin nipples ɗinta daya bayyana tacikin hijabinta, ” wayyo Allah na !!” yafaɗa a hankali, yayinda ya sanya hanunsa yariƙe bananarsa da alokaci guda tayi wani irin harbawa,, cikin rashin ƙarfin jiki da kuzari yafito daga cikin motar haɗe da nufar inda take,, kallon fuskarta yashiga yi, jin hucin numfashin mutum akusa da’ita yasanyata buɗe idanunta ahankali, sake waro idanunta tayi domin ganemawa kanta shin abun data gani gaskiya ne ko ƙarya, kyakkyawar fuskarsa tashiga ƙaremawa kallo, tamkar taga baƙon halitta, waishin aljanine ko mutum ? tatambayi zuciyarta, kallon kallo Zaid da Zahrah suka shiga yimawa juna, yayinda ruwan sama keta dukansu, tsareshi tayi da idanunta, bata ko ƙyaftawa, ahankali yakai hanunsa zuwa kan fuskarta yashafa kumatunta, saurin ja da baya Zahrah tayi, haɗe da ƙwalalo idanunta waje, abun da wani ɗa namiji baitaɓa yi mata ba aduniya kenan wato taɓa jikinta, saidai ko muharraminta,, wani irin munafukin murmushi daya ƙawata zallan kyauwunsa yayi haɗe da komawa cikin motarsa yazauna, ƙofan dake gefen mai zaman banza ya buɗe, haɗe dayi mata nuni da hanunsa alamar tashigo, tsoro ne yakama Zahrah, amma tabbas bata da wani dama dayawuce tashiga motar tasa, domin idan ta tsaya tofa saidai ta bushe amma bazata samu abun hawaba gashi dare sai ƙarayi yake,, sumi sumi haka tashige cikin motar tazauna haɗe da takure jikinta waje ɗaya,, kallonta yayi tagefen ido haɗe dayi mawa motar tasa key, batare daya ce da’ita ƙalaba suka soma tafiya,, cike da tsananin mamaki take kallonsa ganin da tayi kaitsaye yanufi hanyar Suleja da’ita batare da ya tambayeta ba, saida suka kawo daidai inda yataɓa ganinta kafun yayi parking motar tasa haɗe da juyo da kallonsa gareta wani irin shu’umin kallo yajefeta dashi haɗe da cewa ” inane gidan ?” kasa amsa masa tayi saima baki da tasake tana kallonsa kamar tasamu statue (gunki), a hankali ya hura mata iskan bakinsa akan fuskarta, take tayi saurin kawar da kanta gefe, “kabarni anan ma ya’isa nagode ” tafaɗa a taƙaice haɗe da yunƙurin fita daga cikin motar, saurin riƙo hanunta yayi haɗe da cewa “Kifaɗamin inane gidan ?” yayi maganar cikin wata irin cool voice maisanya nutsuwa,, “kwanancan ne ” tabasa amsa a taƙaice,,, a dai dai ƙofar gidan su yayi parking motar tasa, saurin buɗe murfin motar Zahrah tayi haɗe da ficewa, hartana jin tuntuɓe wajen shiga gida, tsabar sauri,, wani irin murmushi Zaid yayi, haɗe da fito da harshensa ya lashe pink ɗin laɓɓansa, “Sugar Baby !!” yafaɗa in a low voice, yakai kusan 2 minutes aƙofar gidan kafun yaja motarsa yatafi…….
Koda Zahrah tashiga gida bata iske kowa a tsakiyar gidan ba, don haka kai tsaye ɗakinta tawuce, kayanta dake ɗigan ruwa ta cire haɗe da ɗaura zani a ƙirjinta, fita tayi ta shanya jiƙaƙƙun kayan nata akan igiya, kana ta dawo ɗaki, wata doguwar riga mai kauri tasanya domin sosai takejin sanyi a cikin jikinta, zama tayi akan katifarta haɗe da lumshe idanu, saurin ware idanunta tayi, alokaci guda, bakomai yasa hakanba kuma face, kyakkyawar fuskar mutumin ɗazu dake yi mata gizo acikin idanunta, tsikar jikinta ne yashiga zubawa, sakamakon tunowa da yanayinsu naɗazu da tayi, “Yanada kyau !!” tafaɗi maganar a fili, amma anya ba gamo kikayiba kuwa Zahrah ?” zuciyarta taje fomata wannan tambayar, take kuma tsoro yashiga zuciyar Zahrah saikuma tafara addu’a idan Aljani ne ma Allah yarabata da sharrinsa…..
Zaid kuwa daga gidansu Zahrah nasu gidan yayi, koda yacire kayan dake jikinsa kwanciya yayi luf akan makeken gadonsa, yanamai sauƙe ajiyar zuciya, lallai yau yayi gamo da gamdakatar, ashe gaskia Bash keyi da ya ce masa a area’n akwai kyawawan ƴan mata, saidai a yanda ya fuskanta ita ɗin ba ƴar hannu bace, domin ya hango hakan acikin idanunta,, murmushi mai sauti Zaid yayi haɗe da cewa “Kisaurari dawowana gareki My Sugar Baby !!”…..
Bayan Sati Ɗaya da haɗuwan Zahrah da Zaid….
Tun randa Zahrah ta haɗu da wannan haɗaɗɗen gayen hankalinta ya kasa kwanciya, ko kwanciya bacci tayi, to fa shike zuwa mata a mafarkinta, dazaran tarufe idanunta kuwa kyakkyawan murmushinsa take gani, duk yanda taso yakice tunaninsa acikin zuciyarta hakan yacitura, saidai ako dayaushe tana mai gargaɗin zuciyarta da ta tsaya a iya matsayinta, kada ta haura matsayin da bata can can ci zuwa ba..
Ɓangaren Zaid kuwa iskancinsa yake bugawa son ransa, zina ƙara yaɗuwa takeyi a cikin jini da zuciyarsa,, yau yashirya cewa zaikai mawa Sugar Baby ɗinsa ziyara,,
Tsab yashirya kansa cikin wasu irin tsadaddun riga da wando, na blue jeans, bakaɗan ba kayan suka amshi kyakkyawan jikin Zaid, yayinda tulin gashin kansa yasha gyara sai sheƙi yake, agogon rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hanunsa, haɗi da baɗe jikinsa da shu’umin turarensa mai rikirkita ƴan mata,, haƙiƙa Zaid yana da kyau mai burgewa, Zaid haɗaɗɗen Namiji ne wanda kowacce mace idan tagansa saita ƙyasa, bazan iya misalta muku haɗuwar Zaid ba amma Zaid ya wuce duk inda kuke tunani,ga kuɗi ga kyau, shiyasa yake abun da yakeso,,, car key ɗinsa ya ɗauka haɗe da ficewa daga cikin ɗakin,, kaitsaye parking space ɗinsa ya nufa, haɗaɗɗiyar motarsa ƙirar Range Rover blue colour yashiga haɗe da bata wuta yafice daga cikin gidan,, yana tuƙi amma earpiece ne sanye a kunnensa yanashan ƙiɗa, kai tsaye Unguwar Suleja yanufa,,
Zahrah ce zaune a tsakar gida, tana wanke mawa inna kayanta, sanye take da wata atamfa irin mai sauƙin kuɗinnan amma, duk da haka atamfar tayi mata kyau ajiki, Inna kuwa nagefe akishingiɗe tana sana’artata cin goro,, wani yaro ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, Zahrah ce ta amsa masa Inna kuwa ko kallonsa batayi ba, domin a tunaninta baraka dake binta bashine ta aiko mata,, ” Wai Zahrah tazo inji wani a waje ” yaron yafaɗa, zuciyar Zahrah ce tayi wani irin tsalle tamkar zata fito waje, yayinda inna dake kishingiɗe tamiƙe zumbur haɗe da cewa ” Zahrah kuma ? kai yaro anya kaji da kyau kuwa ?” kai yaron yagyaɗa haɗe da cewa “Eh wani ne yace inkirata, kuma Zahrah yacemin,,
STORY CONTINUES BELOW
“Wanin dame yazo? a tsaye kagansa ? koko amashin ? kokuma dai amota ? yaro faɗamin da maiyazo ? ” Inna ta tambayi yaron,, “Awata irin ƙatuwar mota yazo mai kyau ” yaron yafaɗa, domin shidai abun daya gani zai faɗa,,
“hehehhe ! jekace tana zuwa ɗan yaro ” Inna tafaɗa tana mai tashi tsaye, “To” kawai yaron yace haɗe da juyawa yafice daga cikin gidan,,
“Tashi maza maza kije kada ki ɓarar mana,, banza kinaji ana ƙiranki amma kinwani shantakewa a waje ɗaya ” Inna tafaɗa tana mai hararan Zahrah, da take ƙame a waje ɗaya, gaba ɗaya hankalinta baya jikinta…. hijabinta dake rataye kan igiya tasanya haɗe da nufar ƙofar fita daga gidan cikin sanyin jiki,,, tana fitowa daga cikin gidan yakafeta da mayun idanunsa, haɗe da sanya harshensa ya lashi laɓɓansa, Zahrah kuwa ganin bataga kowa awajen ba sai mota yasanya ta juyawa daniyar komawa gida, *”ZAHRAH”* taji ankirasunanta da wani irin murya wanda bazata taɓa manta ta ba duk da kuwa cewa sau ɗaya tak ta taɓa jin muryar a rayuwarta,, saurin juyowa tayi don taga daga ina muryar tafito, daidai lokacin ya sauƙe glass ɗin window’n motar, idanunta sukai mata tozali da kyakkyawar fuskarsa wanda bazata taɓa mantashi ba har abada kuwa,, wannan shu’umin murmushin nasa ya yi mata haɗe da cewa ” shigo mana, kodai tsorona kikeji ne ? ” a hankali ta sauƙe idanunta daga kansa haɗe da kaɗa kanta alamar a’a, amma still tana tsaye bata shiga motar tasa ba, wani murmushin yakuma aika mata haɗe da buɗe murfin motar tasa yafito, saida yazo gab da’ita kafun yatsaya haɗe da sanya hanunsa yaɗago haɓarta, wanda hakan yasanya ta jefa idanunta cikin nasa, ” Haka kikafiso ko ? kowa yazo wucewa yaganmu tsaye ?” yaƙare maganar yana mai rage girman idanunsa,, wani irin zubawa tsikar jikin Zahrah ya shiga yi, saurin ja da baya tayi domin kusancin nasu yayi yawa,, batare daya sake ce da’ita komaiba yajuya yashige cikin motarsa, haɗe da buɗe mata ƙofar mai zaman banza, cikin sanyin jiki Zahrah tashiga cikin motar amma bata rufe ƙofar motar ba, saishi ne ya jawo ƙofar yarufe da kanshi, kallonta Zaid yashigayi harnatsawon minti biyu kafun yayi murmushi, haɗe da cewa “Baki iya gaisuwa ba ne ?” wani irin kunya ne yakama Zahrah kwata kwata ita tama manta da ana gaisuwa, gaba ɗaya ganinsa ya ruɗata,, “Inawuni ” tafaɗa cikin sassanyar muryarta,, “bani amsawa saida ma na roƙa ” yafaɗa yana ɗan hararanta, ɗan guntun murmushi kawai tayi haɗe da sake sunkuyar da kanta ƙasa, tanamai wasa da yatsun hanunta, “Zahrah!!” yasake ƙiran sunanta cikin kasalalliyar murya, kasa amsawa Zahrah tayi saima ɗago kanta da tayi taɗan saci kallonsa, haɗa idon da sukayi yasa tayi saurin maida kanta ƙasa,, “Bakiyi mamakin zuwa na ba ?” yajefo mata tambaya, alokacin da bata shirya ba, da ƙyar ta’iya cewa “nayi” satan kallonsa tayi ta gefen ido, “Idan namiki kyau ne kijuyo kikalleni da kyau, bawai ki tsaya kina satar kallo naba, yafaɗi maganar kaitsaye, wani irin kunyane yakama Zahrah sam batasan cewa yana ankare da’ita ba, da sauri ta cusa kanta tsakankanun cinyoyinta, haɗe da ɓoye fuskarta, gyara zama Zaid yayi haɗe da cewa ” dama nazo na ganki ne, kuma naganki zaki iya tafiya tunda kunyana ma kikeji ” yafaɗi maganar ataƙaice, ahankali tabuɗe murfin motar da sauri tafice bata ko waigo tasake kallon sa ba, tashige cikin gida,, yana ganin wucewarta cikin gida, yasauƙe ajiyar zuciya haɗe da sakin ɗan guntun murmushi, “da sannu zaki shigo hannu ” yafaɗa acikin zuciyarsa, wani yaro dayake wucewa yaƙira haɗe da basa wata ƙatuwar leda yace yakai gidan su Zahrah’n, daganan yayi mawa motarsa key yabar cikin unguwar tasu,
Zahrah nashiga gida yaro yabiyota da ƙatuwar leda, “wai inji wani a waje” har Inna najin tuntuɓe wajen ƙwatan ledan ahanun yaron, “to, to,to kace angode ko yaro” Inna tafaɗa tana washe baki, yaron baice da’ita ƙalaba yafice da ga cikin gidan,, zama Inna tayi akan tabarma haɗe da zazzage ledan, kayane suka soma faɗuwa acikin ledan saikuma bandir ɗin kuɗi ƴan dubu dubu ɗauri ɗaya daya faɗo, waro idanu Inna tayi haɗe da dafe ƙirji, afili tace ” Nashiga Uku ni Salma mainake gani haka, ke Zahrah ɗan fashi, ko ɗan yankan kai, kika jajiɓo mana? ” Zahrah dake ɗaki jin abun da Inna kecewa yasa tayi saurin fitowa danganin meke faruwa,, turus itama tayi domin ganin abun dake zube agaban Inna, ɗaukan kuɗin Inna tayi tashiga juyawa, haɗe da washe baki, “Lallai ko ma waye ne wannan mutumin dayazo wajenki Zahrah baƙaramin mai kuɗi bane ” Inna tayi maganar tana mai shunshina kuɗin hanunta, saurin cusa kuɗin tayi aƙasan ƙugunta, haɗe da soma juya kayan dake zube gabanta, dogin riguna ne ƴan ubansu kala uku sai lufayu, guda uku, dagani kai kasan masu tsadan gaske ne, kuɗin Inna taciro tasoma irgasu, dan tsabar naci saida Inna ta irge kuɗinnan tas dubu ɗari ne cus, dafe ƙirji Inna tayi cike da tsananin mamaki tace ” Dubu ɗari awannan zamanin ? lallai ne inji masu faɗi sukace
arziki na’inda yake, aikuwa yau miyar zallan nama zamuci acikin gidannan, Allah yakashe ya bamu, ke Zahrah tsayuwan mekike ? maza ɗauko hijabinki kijemini bakin hanya nan kisayo mini ɗanyen nama da kuma danƙwaleliyar kaza ƴar gashi, yau bushasha zanyi ” Inna taƙare maganar cike da farinciki, haɗe da wurgi da guntun goton dake hanunta,, cikin sanyin jiki Zahrah takoma ɗaki taɗauko hijabinta, kuɗi takarɓa a wajen Inna, kai tsaye tawuce aikan da Innan tayi mata, zuciyarta fal da tarin tambayoyi haɗe da tunani…..
Zaid kuwa daga wajen Zahrah guest house ɗinsa ya wuce, bayan yabiya yaɗauko sabuwar karuwarsa da yayi, maisuna Laylerh,,
Gaba ɗaya Zaid ya ruɗe ganin da yayi mawa Lylerh tsaye a gabansa tsirara haihuwar uwarta, saiwani banƙaro masa ƙirji takeyi, duk don ta ɗauke hankalinsa, duk dacewa ba irin macen da bai gani ba, amma Lylerh ta ɗan rikitasa, domin ta nada abun dayake so sosai ajikin mace wato breast, shi namiji ne mai son breast sosai, madaran holandia dake riƙe ahanunsa, yashiga zuba mata akan nonuwanta harzuwa ƙafanta,, bakinsa ya ɗaura akan nononta yashiga tsotson su haɗi da lashesu, yayinda yazura yatsansa ta ƙasanta, yana mai wasa da gabanta, a hankali, babu inda Zaid baibi yasuɗe ajikin Lylerh ba, cikin zafi zafi yake murza breast ɗinta, hanunsa kuwa yajima da nutsewa aƙasanta, duk kuwa yanda Lylerh taso su haɗa baki da Zaid yayi kissing ɗinta ƙiyawa yayi, sai dai yayi romance ɗinta yadda yaka mata, kwantar da’ita yayi flat akan gado, yayinda ya haye saman ruwan cikinta hannayensa yakuma ɗaurawa akan breast ɗinta yashiga murzawa, yayinda ya shiga goga bananarsa a dai dai wajen fitsarinta,, wani irin shishita Lylerh keyi domin ko ahaka Zaid ya barta ta gamsu, cike da ƙwarewa Zaid ke sanya bananarsa cikin HQ ɗin Lylerh, saida yatabbatar dacewa tanutse ciki kafun yasoma aiki, gaba ɗayansu hankalinsu baya jikinsu, domin sunyi nisa wajen aikata zina,,, balaifi Zaid yasamu gansuwa da Lylerh, domin dai Lylerh ta tsuma kanta da maganin mata yanda yakamata,, kuɗi masu yawan gaske Zaid yabamawa Lylerh, amatsayin ladan iskancin da yayi da’ita, duk da cewa itaɗin ba gadon tsiya bace, domin Babanta mai kuɗi ne sosai…..Zahrah ce kwance a ɗaki, bayan ta dawo daga aikan da Inna tayi mata,, zuciyarta cike take da saƙe saƙe kala kala, na farko tanason sanin wayeshi, maikuma yakawosa gidansu, haƙiƙa tasan cewa ya girmewa ajinta, amma sai gashi zuciyarta ta maƙale da tunaninsa, duk yanda taso manta shi a cikin zuciyarta hakan yagagara, amma cire tunaninsa acikin zuciyarta yazama dole, domin kuwa hanyar jirgi da ban, ta mota ma da ban,,,, a ranan nan da ƙyar bacci ɓarawo yayi awun gaba da Zahrah, dazaran ta kulle idanunta, kyakkyawan murmushin sa ne ke yi mata gizo….+
Yau tana ƙirga wa kwanansa shida kenan dazuwa wajenta, amma har izuwa yau ɗin tunaninsa yakasa barinta tayi sukuni, bakomai yafi ɗaukar hankalinta a tattare da shiba kamar ƙawataccen murmushinsa mai burgewa, (Murmushin shu’umanci) uwa uba kwarjininsa yana ruɗata, wani irin son sake ganinsa takeyi…
A ɓangaren Zaid kuwa abubuwane sukai masa yawa, yayinda hankalinsa ya karkata zuwaga harkan kasuwancin sa, kwata kwata baya samun zama, amma komai yake Zahrah na maƙale a ransa, burinsa ɗaya shine Allah yakai damo ga harawa, ko baici ba yayi birgima, har ya hasasho, yanda zai keta mawa Zahrah rigar budurcinta, tun da yaganta yayi rantsuwa, cewa sai ya ɗanɗani zumanta, kuma bazai bar rantsuwarsa yatafi a banza ba…
Zahrah na zaune a tsakar gida, idanunta kekan handout ɗin dake riƙe a hanunta,, idan kayi mata kallon farko zakai zaton karatu takeyi, amma idan kakuma kallonta, to akasin haka zaka gani, domin gaba ɗaya hankali da tunanin ta ya tafi ga Zaid ya hanata sakat, karatun ma bako da yaushe yake shiga kanta ba,, wani yaro ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, Inna ce tayi saurin amsa masa, “Wai ana ƙiran Zahrah a waje ” yaron yafaɗa, baki Inna ta washe haɗe da cewa “ɗan albarkan nanne yazo na sani, je kace gatanan fitowa yanzu yanzun nan ” wani irin bugawa zuciyar Zahrah tayi, hakanan ta tsinci kanta da faɗuwar gaba, take kuma taji zuciyarta tayi sanyi,, lufayan da Inna ke miƙo mata ta amsa haɗe da zurawa ajikinta, kaitsaye tafice daga cikin gidan,,,
Tsaye yake a jikin motarsa yasha ado cikin wata blue shadda, sosai kayan yayi masa kyau, domin kuwa shiɗin ma ba baya bane wajen kyau,, turus haka Zahrah taja ta tsaya, ganin wata baƙuwar fuska ba wacce take tsammani ba,, murmushi yayi mata haɗe da yi mata nuni almar ta ƙaraso,, gaba ɗaya jitayi farincikinta ya gushe, sam bashi taso gani ba, taso ace Mai kyau (Zaid) ɗinta ta gani,, cikin sanyin jiki ta ƙaraso inda yake haɗe dayi masa sallama,, amsa sallamar nata yayi fuskarsa cike da fari’a,, sake gyara tsayuwa Jabeer yayi haɗe da cewa ” kiyi haƙuri a wancan lokacin na tsaidaki a’inda bai dace ba, amma yanzu gani nabiyoki har gida, ina fata zakiyi marhaba da zuwana “
Ɗan jim Zahrah tayi, domin ita bata da wani amsa da zata basa, ganin haka yasanya Jabeer ci gaba da cewa ” kamar yanda na faɗamiki a farko ni sunana Jabeer, ina zaune ne a unguwar asokoro nida mahaifana, ni ma aikacik banki ne,, tun daga randa na fara ganinki na ji na kamu da soyayyarki, idan har bazan takuraki ba inaso kibani dama don gwada sa’ata agareki… ” Jabeer yaƙare maganar yanamai kallon Zahrah, ɗan jim Zahrah tayi kamar wata mai nazari, ita dai batasan maizatace dashi ba, domin ita bata taɓa soyayya ba, kuma ita batama jisa acikin zuciyarta ba,,, ganin bazatace komai ba yasa Jabeer cigaba da yi mata bayanin kansa, haɗe da ƙoƙarin kafa gwamnatin sa wajen ta,, daga ƙarshe dai cewa tayi yabata dama tayi tunani,, yakoji daɗin hakan domin yanasa ran cewa zai samu karɓuwa a wajenta,,,, koda tazo tafiya maƙudan kuɗaɗe ya bata, amma sam Zahrah taƙi amsa, bayanda baiyi da’ita ba akan ta amsa amma taƙi, dole ya haƙura, saida yaga shigewarta gida kafun yayi mawa motarsa key yafice a unguwar tasu baki ɗaya……..
STORY CONTINUES BELOW
Zahrah nashiga gida Inna tayo kanta tana mai cewa ” Mai arzikin nan ne ko ? bansan a’ina kika samosa ba,amma gaskia banaso ya kuɓuce mana, saboda haka kiriƙesa da kyau “
cikin sanyin Murya Zahrah tace “Bashi bane Inna, wani ne daban” wata uwar harara Inna ta doka mawa Zahrah haɗe da cewa “to idan bashi bane wani ɗan iskan ne ? nifa kinganni nan banson harka da talakawa, domin a gaskia bazan ƙare rayuwata cikin talauci ba ehe, in ma baƙin ciki ne yasa kika kori mai arzikinnan to yazama dole ki bashi haƙuri ya dawo, kam bala’i ga samu gakuma rashi, ina bazai yi wuba, shi wannan ɗin a mai yazo ba dai a ƙafa ba ?”
“a mota” Zahrah tayi maganar kai tsaye, sam batajin daɗin abun da Inna keyi, shigewa ɗakinta tayi, yayinda tabar Inna tsaye tana faman ɓaɓatu ita kaɗai a tsakar gida….
Jigum tayi, zuciyarta cike da tarin tunani kala kala, “Bazai zo ba, dama nasan ya girmewa ajini, mai yasa nadamu dashi ? maiyasa nake yawan tunasa akowani lokaci ? maiyasa zuciyata keson jefa kanta inda bata dace da zuwa ba ? yazama dole na daina tunasa kwata kwata a rayuwata, to amma yazanyi da wannan daya kawomin tallen soyayarsa gareni ? ” Zahrah tayi maganar a fili,, haka dai Zahrah tayi ta saƙe saƙe acikin zuciyarta…
Bayan Kwana biyu da zuwan Jabeer….
Misalin ƙarfe 8:30 pm, Zahrah ce kwance akan ƴar yalolon katifarta, yayinda idanunta ke lumshe, da’alama bacci keson ɗaukarta…. Shigowar Inna da sauri cikin ɗakinnata shiya sanya tayi saurin buɗe idanuwanta, domin shigowar Inna ɗakinnata a dai dai wannan lokacin bainuna alamar lafiya…. ” Miye kika wani zura min idanu kamar mayya, tashi kije waje wannan mai arzikinne yakuma da wo wa ” Inna ta faɗa cike da zumuɗi,, dumm haka ƙirjin Zahrah ya buga,, ganin Zahrah tayi saƙare yasa Inna, cewa “zaki tashi kijene kokuwa saina mangareki ” sumi sumi Zahrah tamiƙe haɗe da ɗaukar hijabinta tana ƙoƙarin sanyawa a jikinta,, saurin fusge lufayar Inna tayi haɗe da wurgi dashi gefe, wani gyale dake hanunta, ta miƙomawa Zahrah’n haɗe da cewa ” ungo yafa wannan banson wannan shirmen koda yaushe kina nanuƙe da lufaya kamar wata mayya !” badon Zahrah taso ba haka ta yafa gyalen da Inna ke miƙomata, har zaure Inna ta raka Zahrah, saida taga ficewarta kafun ta koma gida,, kasancewar gari gaba ɗaya yayi duhu hakan yasa bata iya hango wanda ke cikin motar, kuma zuciyarta bata bata akan cewa shiɗinne ba, saboda ba motar da yazo da’ita ranan bane watace daban,, don haka tafara zaton ko bashi bane,, wani irin daddaɗan ƙamshine yashiga yawo acikin ƙofofin hancinta, kallonta ta maida izuwa inda ƙamshin ke fitowa, mutum ne tsaye a wajen amma bazata iya shaida ko waye bane, saboda duhu,, wani irin tsoro taji yakamata kaddai mai satan mutanene yabiyota har gida, da sauri tajuya don komawa gida, taku ɗaya yayi kacal, ya cafko hanunta, wanda hakan ya haifar masa da zubawar tsikar jiki,, jawota yayi gab dashi, cikin wata irin murya yace ” Shiiii idan kikayi magana saina yankaki !” jikin Zahrah ne yaɗauki rawa haɗe da ɓari, tsoro ne ya lulluɓeta a sakamakon jin abun daya ke faɗi, shikenan itakam Inna tajawo mata, tana zaman zamanta ta tilasta mata fitowa gashi wani zai yi garkuwa da’ita,, babban abun daya da gulamata lissafi, bai wuce yanda jikinsa da nata ke manne awaje guda ba, ga ƙamshin sa gaba ɗaya yagama rikitata,, a hankali ya ɗaura kansa a gefen wuyanta, wanda hakan yasanya tattausan sajensa gogar fatar wuyanta, lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu a lokaci guda, ” Kinshirya mutuwa yanzu kokuwa ?” yaje fo mata tambayar data kusa tsinka ƴaƴan hanjinta,, cikin rawan murya tace “dan Allah kayi haƙuri kada ka cutar dani wallahi ni marainiya ce, da Allah kaɗai na dogara ” tuni hawaye sun wanke kan fuskarta, wata irin dariya Zaid yayi mai cike da mugunta, hannayensa yasanya duka biyu ya juyo da’ita gabansa, yazamana suna faced ɗin juna, wayarsa ya dannan take hasken tocila (torch light) yabayyana, rufe idanunsa yayi haɗe da kai hasken tocilan kan fuskarsa, cikin mayaudariyar murya yace ” fatan baki manta da wannan fuskar ba” sai a lokacin Zahrah taɗago idanunta ta sauƙesu akan kyakkyawar fuskar Zaid, wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da yin hamdala acikin zuciyarta,, wani irin ƙawataccen murmushi Zaid yayi mata, haɗe da kashe mata idonsa ɗaya, ” matsoraciya ” yafaɗa cikin murya mai sanyi,, hararan wasa Zahrah tayi masa haɗe da cewa “ko wama matsoraci ne idan har yaga mutuwa ” murmushi Zaid yayi haɗe dayi mata wani irin kallo, mai ɗauke da ma’anoni dayawa, wani irin yawu ya haɗiye alokacin da idanunsa suka sauƙa kan cikakkun breast ɗinta… “Muje mota” yayi maganar yana mai nufar inda motarsa ke fake,, bamusu itama ta biyo bayansa,, kan kujeran mai zaman banza ta zauna, haɗe da takure jikinta waje ɗaya, sam itakam sa gyale bawai yawani damunta bane, tafiso koda yaushe tazamana cikin hijabi, domin yana kare mata tsiraicinta, gashi yanzu duk ta takura kowani motsi tayi sai surarta ya bayyana,, “Yauma bazaki gaisheni bako ?” Zaid yafaɗa daidai sanda yajefa wani sweet cikin bakinsa,, sunkuyar da kanta ƙasa tayi cike da kunya, itakam balaifinta bane, i dan ta gansa ne komai ke kuncemata,, kallonta yayi ta gefen idanunsa haɗe da cewa ” kinsan maiya kawoni unguwarku yau ?” “A’a” tabasa amsa a taƙaice,, “SOYAYYA !!” yafaɗa cikin wata irin murya mai ɗauke da shauƙi,, “Soyayya kuma ?” Zahrah tatambaya domin sam bata fahimci inda kalamannasa suka dosa ba,, “INASONKI ZAHRAH !!” Zaid yafaɗi maganar yana mai kafeta da idanunsa, cikin tsananin mamaki Zahrah ke kallon Zaid, ko da wasa bata taɓa zaton zaiyi mata maganar soyayya anan kusaba, “Kinyi shiru sanar dani idan kinasona ” Zaid yafaɗa yana mai kama hannayenta yashiga murzawa a hankali,, wasu irin ƙwallane suka shiga gangarowa daga cikin idanunta zuwa kan fuskarta, ” kada ka yaudareni, ni macece mai rauni da kuma naƙasu, kaduba gidanmu, kaduba irin shigar dake jikina, ka dubi kanka kasan cewa nidakai ba ɗaya bane, akwai tazara mai tarin yawa a tsakaninmu, ban taɓa soyayya ba, bakuma naso nafara soyayya a’inda zuciyata zata wahalta, don Allah kajanye maganar soyayyata a gareka, domin nida kai bamu daceba ” tuni hawaye sungama wanke fuskarta,, murmushi Zaid yayi haɗe da cewa “Ba labari nake baki ba, saboda haka ki farka daga baccin dakike, nabaki nan da 3 days ki koyamawa zuciyarki soyayyata, zan aureki idan har kin amince da hakan, bana buƙatar da cewar mu ko rashin sa,, ungo wannan idan kin koma ki kunnata saboda zan iya nemanki koda yaushe ” yaƙare maganar yana miƙomata wata leda dake hanunsa,, kai tagirgiza alamar bazata karɓa ba, take yaɓata ransa, wanda hakan yasa taji ba daɗi, haka dolenta ta karɓa,, saida safe tayi masa, kana ta shige cikin gida,, tana shigewa shima ya ta da motarsa yayi gaba…
Tana shiga cikin gida Inna tayi yo kanta tana washe baki, sakamakon ganin leda da tayi ahanun Zahrah, wafcar ledan Inna tayi haɗe da cewa “ɗan albarka yaukuma mai yakawo mana ?” kwalin danƙareriyar iphone 11 pro max Inna tafara cirowa, a je kwalin tayi a gefe haɗe da zazzage ledan a ƙasa, kayan snacks dasu choculate ne suka zubo, saikuma mai gayya mai aiki wato farare bugun Abuja, dariya Inna tayi haɗe da buga shewa, itakam Allah yakashe ya bata, lokacin yin arzikinta yayi,, jin shewan Inna yasa Baffa dake cikin ɗaki fitowa, “lafiya kuwa…. ” kasa ƙare maganar Baffa yayi sakamakon tozali da kuɗaɗen da ke gaban Inna da yayi……..Kasa ƙare maganar Baffa yayi sakamakon tozali da kuɗaɗen dake gaban Inna da yayi, cike da tuhuma yake kallon Inna yamakasa ce da’ita komai, ganin haka yasa Inna ta washe baki, haɗe da soma tattare maƙudan kuɗaɗen, cikin hanzari Baffa yasanya hannayensa duka biyu ya wawashi kuɗin, haɗe da cusawa cikin aljihunsa, da sauri Inna tayo kansa tana muzurai, haɗe da cewa “Haba Malam yazakayi haka, aidai katsaya nayi maka bayani kafun ka kwasa rabonka ko” harara Baffa ya watsamawa Inna haɗe da taɓe baki yace ” ba abun da bansani ba, nasan duk wani abu dakike shiryawa, kuma wallahi daga yau idan aka sake kawo kuɗi cikin gidannan ba ki jira dawowata munraba ba, ninasan matakin da zan ɗauka, yarinyace dai ƴar wa na ne, don haka babu wanda ya’isa ya gwadamin iko da’ita, kuma shima saurayin zaizo yasameni haka ake zuwa hira babu wani tambayar izini ba komai” Baffa yaƙare maganar yana mai nufar ƙofar fita daga gidan, yana fita Inna ta buga tsuka haɗe da cewa ” shikenan kuma ae tunda yagano abun danake shiryawa, bazai taɓa barina naci arziki ni ɗaya ba, mcheeew !” taƙare maganar tana mai tattare ƴan ragowan kuɗaɗen da Baffa ya bar mata, raba snacks ɗin biyu tayi taɗauki rabi, yayinda tabarmawa Zahrah rabi, waya kuwa danƙamawa Zahrah abunta tayi, domin ita keypad ma bawani iyata tayi ba, balle kuma shafa shafa (touching screen)… Jigum haka Zahrah tayi zuciyarta cunkushe take da tarin tunani kala kala, da zaran ta kulle idanunta, mood ɗinsu na ɗazu ne ke faɗo mata, wanda hakan yasanya takejin gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, batasan dame zata ƙira wannan yanayinba, saboda batasan ma da akwaishi acikin duniyar nan ba, duk dacewa bawani abune yashiga tsakaninsu ba, amma kusancin da sukayi da juna duk ya dagula mata lissafi, ga fitinannen ƙamshin turarensa daya kama jikinta, tamkar wacce tayi wanka da turaren,daga wani ɓangare na zuci yarta kuwa kaico takeyi da mummunan hali irin na Inna da Baffa, wato su baruwansu da koma waye zaizo wajenta, sudai kawai abasu kuɗi suka sani, koda ma iskanci takeyi su baidame su ba kuɗi kawai suke so, haƙiƙa rashin iyaye babban matsalane arayuwar ƴa mace musamman ma idan batayi dace da iyayen riƙo nagari ba, sai kuga rayuwarta nashirin lalacewa, akan abun da bai kai yakawo ba, Allah ka zama gatan mu aduk inda muke Ameen,,, a hanakali taciro wayar daga cikin kwalinta, subahanAllah shine abun da tafurta lokacin da’idanunta suka sauƙa akan haɗaɗɗiyar wayar, jikin wayar ma kaɗai abun kalloce balle kuma kakai ga shafata, tabbas idan baza ta mantaba, wannan wayar itace wacce taji ƴan school ɗinsu na magana sabuwar fitowa ce, kuma burin kowanni ɗan gata da ƴar gata, shine su mallaki wayar, domin kuwa aƙalla kuɗinta zaikai dubu ɗari biyar da tamanin,, wani irin faɗuwar gaba taji ya shiga zuciyarta a lokaci guda, take kuma mugun zargin Zaid ya ɗarsu acikin ranta, tabbas akwai abun daya ɓoye acikin zuciyarsa, amma idan ba haka ba babu yanda za’ayi yasiya mata wayan dubu ɗaruruwa, batare da suna da wani kyakkyawan alaƙa atsakaninsu ba, a maimakon ta kunna wayar kamar yadda ya umarce ta, batayi hakan ba saima mai da wayar tayi cikin kwalinta haɗe da cusata cikin kayanta, taƙudura acikin ranta cewa idan yasake da wowa zata mayar masa da wayarsa, domin ita bata kai martaba da ƙimar da zata riƙe wannan zuƙeƙiyar wayarba,, sam bacci ya ƙaurace mawa idanun Zahrah kalaman Zaid ne ketayi mata yawo acikin kunnu wanta, bama kamar kalmar *INASONKI ZAHRAH* daya faɗa, gaba ɗaya zuciyar Zahrah kasa sukuni tayi a wannan dare, da ƙyar bacci ɓarawo ya ɗauketa……+
Zaid kuwa yana barin unguwar su Zahrah guest house ɗinsa ya nufa, sai dai yau ba ya tare da kowacce karuwa, yana shiga cikin bedroom ɗinsa yasoma rage kayan jikinsa, saida yacire duk wani kaya dake jikinsa, kafun ya ɗaura towel a ƙugunsa kaitsaye ya shige bathroom,, a ƙalla ya kwashi kusan 1 hour a cikin bathroom ɗin kafun yafito, sanye da rigar wanka a jikinsa, gaban mirror ɗinsa yaje ya ɗanyi shafa, combat jeans black ya sanya haɗe da black t-shirt, sosai kyawun Zaid ya bayyana acikin wannan kayan, wayarsa kawai ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin, makeken friedge glass ɗin dake cikin katafaren falon nasa yanufa, zuƙeƙiyar kwalbar wine mai tsadar gaske yaɗauko a cikin friedge ɗin haɗe da glass cup zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yayinda ya buɗe kwalbar wine ɗin ya tsiyaya a cup, kana yakai bakinsa, a hankali yake shan wine ɗin, yayinda idanunsa ke alumshe, bakomai yake hasa sowa ba sai kyakkyawar surar Zahrah wacce ke tafiya da imaninsa ako da yaushe, haƙiƙa ya kamu da tsananin sha’awar Zahrah, kuma alƙawari yaɗaukar mawa kansa idan dai har yacika *SHU’UMIN NAMIJI* kamar yadda abokansa ke ƙiransa, to sai ya keta mawa Zahrah rigar mutumcinta kota wani hali kuwa,, wayarsa yaɗauka haɗe da laluɓo numbern sim ɗin dake cikin wayar Zahrah, yana dialing aka sanar dashi cewa wayar a kashe take, wani irin munafukin murmushi Zaid yayi haɗe da sanya hanu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa, kashe idanunsa ɗaya yayi haɗe da cewa “My Sugar Baby bakijin magana ko ?” yayi maganar tamkar wanda yake gabanta,, sosai Zaid ya sha wine a wannan dare, da ƙƴar ma yasamu bacci ya ɗaukesa bayan yagama kwarara aman giyan da yasha …….
Yaune kwanaki ukun da Zaid ya ɗibar mawa Zahrah suka cika cif cif, don haka yau da wani irin matsanancin faɗuwar gaba ta wayi gari, haƙiƙa bazata yaudari kanta ba, tasani cewa ƙwarai zuciyarta ta aminta da Zaid to amma babban abun dubawa shine, shin Zaid ɗin yadace da rayuwarta kuwa? ko kaɗan bata hango dacewarsu da Zaid ba, duk da tasan cewa tana da kyawun da kowani ɗa na miji zaizo da ƙoƙon soyayyarsa gareta, amma bata tunanin haɗuwarsu da Zaid zaiyi dai dai, kallo ɗaya zakaima Zaid kafahimci cewa shiɗin mai tarin arziki ne, haka ma iyayensa, itakuwa bakomai bace face *TALAKA* ƴar *TALAKAWA* wacce talauci yabayyana tambarinsa ajikinta, sam bata mawa kanta adalci ba matsawar ta ɗauki kanta takai zuwa matsayin da bana taba, wasu irin hawayene suka shiga gangarowa daga cikin idanun Zahrah, yayinda zuciyarta keyi mata zafi, batasan menene so ba, domin bata taɓa yi ba, amma a yanda takejin Zaid acikin zuciyarta, yasa tafara kokonton cewa takamu da tsananin soyayyarsa, gaba ɗaya wunin yau a susuce tayi sa, damuwarta ɗaya idan Zaid yazo maizatace dashi ? idan ta furta masa kalmar ƙi to fa har abada bazata taɓa yafemawa kanta ba, domin ta cutar da zuciyarta, idan kuwa ta furta masa kalmar so, tofa ba makawa tajefa kanta acikin ɗauri ne mai wuyar suncewa…. Wunin ranar dai haka Zahrah tayi shi sukuku babu daɗi, fargaba ne fal cike a zuciyarta….koda tayi Sallan la’asar banɗaki tashiga tayi wanka , zama tayi akan katifarta, haɗe da ɗauko wata hand bag ɗinta, wanda ciki take ajiyar kayan kwalliyanta, duk da cewa dai itaɗin ba mace bace ma’abociyar yawan kwalliya,, hakanan ta tsinci kanta da son yin kwalliya a yau ɗin, hoda (powder) ta murza akan fuskarta, haɗe da shafa janbaki (lipstick) dark maroon colour, akan laɓɓanta, black eye pencil, tasanya acikin idanunta, haɗe da shafa mascara akan zara zaran gashin idanunta, take fuskar Zahrah tasakeyin kyau, duk da dama cewa itaɗin mai kyauce,, wata Arebian gown maroon colour tasanya ajikinta, sosai da sosai rigar ta amshi jikin Zahrah, tayi mata ɗas, duk acikin kayanta Zahrah tana matuƙar son rigan, domin kuwa maman khausar ce takawo musu, ita da khausar ɗin, daga Saudiya,, rigace mai kyau da tsadar gaske, uwa uba idan ta sanya rigar ita kanta tasan tanai mata kyau,, kan katifarta ta koma ta zauna, bayan tagama kimtsa kanta, jigum tayi tana tunanin waishin maiyasan yata yin kwalliya batare da wani dalili ba? “saboda Zaid zai zo, zuciyarta ta bata amsa, “idan kuma baizo bafa ?” tatambayi kanta, take wani irin faɗuwar gaba ya ɗarsu acikin zuciyarta, wanda batasan dalilin faruwan hakan ba,, abu kamar wasa, har yammaci ta rufa babu Zaid babu alamarsa, tuni jikin Zahrah yayi sanyi laƙwas,, hardai akayi sallan Isha, ba’azo daga waje ance anaƙiran Zahrah ba,, tuni ta wanke ɗan kwalliyan da tayi a fuskar tata ma, domin zuwa yanzu tacire rai da zuwan Zaid… Zaune take a tsakar gida, gabanta ɗauke da kwanon shinkafa da wake, a hankali take tsakuran shinkafan tana kaiwa bakinta, kallo ɗaya zakai mata kahango tarin damuwa acikin zuciyarta,, kamar daga sama wani yaro yashigo, yace wai anaƙiran Zahrah a waje,, wani irin farincikine ya lulluɓe zuciyar Zahrah, domin kuwa tana kyautata zaton cewa Zaid ne,, koda tashiga ɗaki don ɗauko mayafinta saida tasake murza powder a kan fuskarta haɗe da sanya kwalli a idanunta, Zahrah dai bata tsayananba hadda shafa jambaki,, wani rover hijab tasanya ajikinta, kalar maroon, wato kalar doguwar rigan dake jikinta, gaba ɗaya lufayar iyaka cinya ta tsaya mata, hakan kuma yayi nasarar bayyana surar jikinta, kasancewar lufayan mai rover ce, tayi kyau kuma balaifi, tamkar dai balarabiya, abunka da farar fata,, turarenta mai sauƙin kuɗi (TONY MONTANA) tafeshe jikinta dashi, take ta ɗau ƙamshi,, a hankali take taku harta fice daga cikin gidan nasu,, koda tafito daga gidan cikin nutsuwa take takunta, yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, zuciyarta kuwa bugawa tashiga yi akai akai,, kaitsaye tanufi wajen da taga motarsa na fake,, tun da tafito daga cikin gidan, ya kafeta da mayun idanunsa, masu rikita mata, sosai yau ɗin tayi masa kyau, hakanan yaji sha’awarta ta ninku akan nada,, tana ƙarasowa wajen motar ta sa, taja ta tsaya, still kuma kanta na kallon ƙasa tana wasa da yatsun hanunta, a. hankali yabuɗe murfin motar tasa haɗe da ziro ƙafafunsa waje, take wani irin fitinannen ƙamshin turarensa yacika ko’ina na wajen, a hankali ta lumshe idanunta, domin kuwa bakaɗan ba ƙamshin turaren nasa ya tafi da’ita,, kallonta ya shiga yi tundaga ƙasanta harzuwa samanta, kafun ya saki shu’umin murmushinsa, “MY ZAHRAH !!” yaƙira sunanta da wani irin murya mai sauƙar da kasala, kasa amsa masa Zahrah tayi saima sake sadda kanta ƙasa tayi tana mai wasa da yatsun hanunta,, murmushi yakumayi a karo na biyu, “yau kuma tsayuwa kikeji da shi ?” yayi tambayar cikin nuna halin ko inkula,, jin haka yasanya ta gane mai yake nufi, jiki a sanyaye ta nufi ɓangaren mai zaman banza tabuɗe murfin motar haɗe da shiga ta zauna,, a hankali Zaid ya yi ƙasa da kujerar dayake zaune, ɗan zamewa yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran haɗe da lumshe kyawawan idanunsa, a hankali Zahrah ta ɗan saci kallonsa haɗe da cewa “Ina wuni !” jin muryarta da yayi ta ratsa kunnuwansa yasa sa ɗagowa, yazauna haɗe da kafeta da’idanunsa, yakai kusan 3 minute yana kallonta “kinyi kyau !!” yafaɗa in a unigue voice ɗinsa, wani iri Zahrah taji a cikin jikinta, wannan shine karo na farko a duniya da wani ɗa namiji ya fara faɗa mata cewa tayi kyau,, cikin salonta na kunya, ta ɗago idanunta takalleshi karab idanunta suka sauƙa acikin nasa idanun, wani irin shock taji ajikinta, da sauri tayi ƙasa da kanta, cikin salonsa ya ce ” Idan kinajin kunyana ta ya ya zaki iya nunamin zallar soyayyar danake buƙata a wajenki ? inasonki da duka zuciyata My Zahrah ina fata kema zaki soni kamar haka ko fiye da haka ? ” a yanda yayi maganar idan kakallesa zaka iya rantsewa cewa bashine yayi ba,, jitayi jikinta gaba ɗaya yayi laƙwas, wani irin zazzafar ƙaunarsa takeji yana huda kowani irin saƙo na jikinta, a hanakali ta ɗago manya manyan idanunta da suka cika da ƙwalla, ta sauƙe su akan kyakkyawar fuskarsa, cikin murya mai rauni tasoma cewa “bantaɓa soyayyaba, bankumasan ya akeyinta ba, ni marainiyace bayan Allah sai Baffana nakedasu acikin wannan duniyar, nasan kafi ƙarfin ajina, dan Allah kada kayaudareni da soyayyarka ” taƙare maganar lokacin da hawaye suka shiga sauƙowa a kan fuskarta,, kafeta da idanunsa yayi harnatsawon wasu mintuna, shikaɗai yasan abun da yake saƙawa acikin zuciyarsa,, “Idan kin yarda dani to kibani soyayya da amincewarki, nikuma bazanci amanarki ba” yayi maganar cikin muryarsa mai sanyawa zuciyarta nutsuwa,, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da yimawa Allah godiya daya kawomata ma’agaji adai dai lokacin da ta ke buƙata, shirune yashiga tsakaninsu na ɗan wani lokaci, bayan Zaid yagama saƙa abun da zai saƙa acikin zuciyarsa, yasaki wani irin killer smile haɗe da mai da kallonsa ga Zahrah, “ya kamata ki kaini nagaidasu Baffa ko ” ya yi maganar yana mai kashe ma ta idanunsa ɗaya,, murmushi kawai zahrah tayi haɗi da cewa “banaje na sanar dasu to ” buɗe murfin motar tayi ta fice haɗe da shigewa cikin gida, bayanta kawai Zaid ya ƙura ma wa ido bakaɗan ba ya kwaɗaitu da yarinyar kuma insha Allah saiya cimma burinshi a kanta,, bawani jimawa Zahrah tafito daga cikin gidannasu, kamar dai ko da yaushe kanta duƙe yake a ƙasa harta ƙaraso garesa,, iso tayi masa zuwa cikin gidannasu, gaba ɗaya a takure take domin kuwa itace a gaba shikuma yana biye da’ita a baya, ahaka suka shiga cikin gidan,, cike da ƙyanƙyami Zaid yazauna akan tabarmar da Inna ta shimfuɗa ma sa a tsakar gidannasu, tunda yake a duniya yaune karo na farko a rayuwarsa da yafara zama cikin gidan talakawa, lallai idan yakama Zahrah ba zai mata da sauƙiba, da ƙyar ya’iya kai zuciyarsa nesa yagaisa dasu Baffa da suka ƙura masa ido, tamkar sunga baƙon halitta,, har rige rigen amsa gaisuwar tasa Inna da Baffa sukeyi, daganinsu kaga mayun ku ɗaɗe,lol, shirune yabiyo baya bayan sungama gaisawa, domin dai harga Allah Zaid bayi da abun cewa, saboda shi bai ma taba irin hakan ba, bayan iyayensa babu wasu wanda yataba gaisarwa da ladabi haka, sai gashi yau akan wata tatsitsiyar yarinya yazo yana kaskantar da kansa gaban talakawan unguwa, lallai yaci amanar jinkai dakuma ajinsa, amma yazaiyi tunda shiyake nema dole yayi biyayya,, ganin yayi shirune yasa Inna gyara zama hade da cewa, ” munagodiya sosai bawan Allah ga me da taimakon mu da kakeyi, Allah ubangiji yasaka da alkhairi, ” murmushi kawai Zaid yayi hade da mikewa tsaye, bandir din kuɗaɗe yaciro daga cikin aljihunsa, hade da ajewa akan tabarmar daya tashi,, tsadaddun takalmansa yasanya hade dayi musu sai anjima yafice daga cikin gidan, “bawan Allah harda dawainiya haka to to masha Allah, Allah yasaka da alkhairi ” Inna tafada tana mai washe baki,, Zaid yana ficewa daga cikin gidan, Inna da Baffa suka dakamawa kudin wawa, Zahrah dake tsaye a gefe kuwa idanunta ne suka ciko da kwalla, sam batajin dadin abun da Baffa da Inna sukeyi, suna nuna zalamarsu afili,, “Miye kika yi wani ƙasaƙe kina kallonmu bazaki bisa ba ” Baffa yafaɗa yana hararan Zahrah, jiki a sanyaye Zahrah tarufa mawa Zaid baya,,,, Zaid kuwa yana fita kaitsaye motarsa ya wuce, sosai yaji daɗin yanda ya hango zallan son kuɗi irin na Baffa da Inna, tabbas yanzu yasake samun ƙwarin guiwa akan burinsa, yanzu yasan cewa bazai wahala wajen samun galaba akan Zahrah ba,,, tana fitowa ya sakar mata kyakkyawan murmushinsa, wanda yake ƙara mawa kyakkyawar fuskarsa kyau aduk sanda yayi sa……