SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi ɗare ɗare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haƙora yake kai kace anmasa kyautar ƴan kuɗaɗe ne.+

Dakansa ya buɗe mata murfin motar ɓangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige ɓangaren driver haɗe da mawa motar key…

Tunda suka ɗau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba ɗaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya, akai akai yake satan kallonta tacikin madubi..

A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu, dai dai bakin ƙofar hall ɗin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall ɗin zasu gudanar da lecture.

A hankali ta buɗe murfin motar ta fito kafaɗarta ɗauke da jakar makarantar ta, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta nufi cikin hall ɗin kai tsaye, ko wai gensu batayi ba, tanashiga hall ɗin kallo yadawo kanta, take taji wani irin muguwar faɗuwar gaba haɗe da karyewar zuciya, gani take tamkar kowa yana ganin abun da yafaru da ita rubuce akan goshinta.

Karab idanunta suka sauƙa akan Husnah wacce take faman aikin haɗa wasu takardu dake gabanta. wani irin sanyi taji zuciyarta tayi sakamakon ganin husnah, domin kaf makarantar bata mu’amala da kowa bayan husnah, da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah, domin koda wasa batayi tunanin ganinta ba.

“Kamar mafarki nakeyi gaskia naji daɗi sosai ƙawata!” Husnah tafaɗa cike da tarin farinciki.

Zama sukayi a tare dai dai lokacin Sir Bature yashigo cikin hall ɗin, tsit haka ajin ya ɗauka ana ta sauraran lecture ɗin dayake yi musu, a zahirin gaskia tanajin abun da yake cewa, amma kwata kwata bata fahimtarsa, awa biyu suka ɗauka chur suna lecture, kafun daga bisani yafita daga ajin, gyara zama Husnah tayi haɗe da mai da kallonta ga Zahrah cike da kulawa tace ” Yanzu ina likitan yake ?”

Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa ” Ba maganar Doctor bace damuwata Husnah, babban damuwata shine gani nake tamkar abun da Zaid yamin yana rubuce a gaban goshina, Husnah gani nake tamkar kowa yasan abun dake damuna !” Zahrah taƙare maganar cikin raunin zuciya.

” Kada kice haka Zahrah, babu wanda yasan abun da yafaru dake, kada ki ɗaga hankalinki ƙawata kinfasan kowa da irin tasa ƙaddaran, kuma zuwa yanzu na tabbatar kin mai da al’amuranki ga Allah, shima Zaid nasan kinbarsa da Allah “

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi mai ciwo Zahrah tayi haɗe da kallon ƙawarta ta, cike da ƙuna tace ” Banda wata hanya wanda tawuce barinsa ga Allah, nasan nan bada jimawa ba Allah zai bimikin haƙƙina ” taƙare maganar cikin raunin zuciya,

Hannayenta Husnah ta kama suka fice daga cikin ajin, kai tsaye cafeteria suka nufa don cin abinci. Balaifi sosai tasamu nutsuwa a yau ɗin domin kuwa Husnah bata barta tayi kaɗaici ba. Ƙarfe 5 dai dai suka fito daga cikin lecture ɗin ƙarshe na ranan yau ɗin, kasan cewar ta kwana biyu bata zo makarantar ba, sai take jinta gaba ɗaya duk ta gaji, cikin nutsuwa take takunta yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, ba abun da zuciyarta keyi banda bugawa, gaba ɗaya tsoron fita daga cikin school ɗin takeyi, gani take tamkar tana fita za’a kamata, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafunta, dagani kasan bason tafiyar take ba. a hankali ta matsa gefe, haɗe da waigowa don ganin waye wannan ya matsa mata da horn ɗin motarsa, karab idanunta suka sauƙa akan sa, kasancewar gilasan motar tasa gaba ɗaya a sauƙe suke, sam batayi tsammanin ganinshi ba, murmushi yasakar mata haɗe da cewa ” Da baki matsaba ai dana take ki !” yafaɗi maganar cikin yanayin tsokana, ɗan guntun murmushi itama tayi haɗe da taɓe baki, “ai idan haka ta kasance zanfikowa jin daɗi ” Zahrah tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.

“Shigo mutafi!” yafaɗa cikin tsare gida.

Saurin kallonsa tayi bakinta ɗauke da tarin tambayoyi, amma kuma takasa koda motsa bakinta ne balle ta furta wata kalman.

“Kintsaya kina kallona, ba dole idan bazaki bini ba, saina yi tafiyata!” yaƙare maganar yana mai niyar tada motar tasa.

Da sauri ta zagaya haɗe da buɗe murfin motar, gefen mai zaman banza ta shiga haɗe da tamke fuskarta tamau tamkar wanda yagayamata magana marar daɗi.

Da ƙyar ya iya ɓoye dariyan dake cinsa, domin kuwa tsoro ya hango ƙarara akan fuskar Zahrah, “Naɗauka ai zakijamin ajine, da sai na tafi na barki ba ruwana!” yafaɗi hakan cike da shauƙi.

Harara ta watsa masa haɗe da sake turo baki gaba, cike da shagwaɓa wacce batasan tayi ba tace “Nifa idan surutu zakamin ka sauƙeni nayi tafiyata”

Yanzu kam kasa ɓoye dariyarsa yayi saida ya dara kafun ya ce ” Bazan sauƙe kiba ai bani na ɗauko ki na saki ba, zaki iya fita da kanki ma, ai nasan ke jaruma ce zaki iya kare kanki ako da yaushe, har ma zaki iya shiga cikin ko wani abun hawa da ƙwarin guiwarki !”

Saurin kallonsa tayi domin kuwa sarai ta fahinci inda maganganunsa suka dosa, wato dai shima ya hango zallan tsoron dake kwance akan fuskarta.

“Shikenan tunda haka kace” tafaɗi maganar tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar ta fita.

“Haba ƴar ƙanwata, nifa wasa nake miki, kiyi haƙuri ki bari na kaiki gida kinji ko!” Doctor yafaɗi maganar cikin lallashi, domin yafahimci cewa saurin fushi ne da’ita.

A cikin zuciyarta tayi hamdala, sakamakon hanata fita daga motar da yayi, domin dama burga ce kawai tsoron dake cikin zuciyarta bazai barta ta iya tafiya ba, duk runtsi tafiso shiɗin ya kaita domin tafi yarda dashi fiye da kowa a yanzun..

Kwantar da bayanta tayi akan kujeran motar haɗe da lumshe idanuwanta, gaba ɗaya jinta take a gajiye, ga wani irin ciwon kai dake damunta, a hankali take buɗe idanunta, a zabure tatashi zaune sakamakon ganin da tayi Doctor ya nufi wata hanyar da ita saɓanin hanyar gida.

“Inazaka kaini !” Tafaɗa a razane, kuma cikin yanayin tsoro,

“Saidake zanyi!” Yayi maganar babu alamar wasa akan fuskarsa.

“Dan Allah kayi haƙuri ka sauƙeni, ka barni naji da duhun dake cikin rayuwata, kada ka ƙaramin wani bala’in dan Allah!!” tuni hawaye sungama wanke fuskarta.

Wani irin kallo Doctor yayi mata haɗe da sakin murmushi bai kuma sake ce da ita komai ba, saima maida hankalinsa da yayi ga tuƙin da yake,

Yanzukam kuka mai sauti ta sanya haɗe da soma cewa ” Dan Allah kada ka sake cutar da rayuwata, zan iya amincema ka kasheni amma bazan iya jure wa ba, idan kaci mutumcina, wlh na yarda ka wurgani kan titinnan mota ta taka ni, amma dan Allah kada kamin komai!!” taƙare maganar cikin matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Daidai lokacin suka iso gaban wani makeken mall wanda yagaji da ƙawatuwa,

yana parking motar baiko kalletaba yayi saurin ficewa daga cikin motar haɗe da dannawa gabaki ɗaya ƙofofin fita a motar luck, domin yasan dole zatayi ƙoƙarin fita daga cikin motar,

STORY CONTINUES BELOW

Kuka sosai Zahrah keyi haɗe da sanya ƙarfinta tashiga dukan glass ɗin motar, tana mai ihun neman taimako amma babu kowa a wajen balle tasaran za a temaketa, domin kuwa wajen parking space ne.

“Ashe duniya cike take da azzaluman maza, ashe itakam rayuwarta a haka zata ƙare? wayyo Allah itakam ƙaddaranta kenan” abun da take faɗa kenan acikin zuciyarta tana kuka mai tsuma zuciya,domin a zaton ta hotel ya kawota zai kuma lalata mata rayuwa.

Daidai lokacin Doctor Sadeeq ya dawo hanunsa ɗauke da manyan manyan ledodi guda biyu, yana shiga cikin motar yakuma danna mata luck haɗe da mawa motar key da gudun gaske ya hau titi.

Zahrah kam muryanta har ya dashe kukanma harya daina fita domin gaba ɗaya ta gama sadaukar da cewa yau ce ranar mutuwarta, kukantane yasoma tsagaitawa ganin sun nufi hanyar unguwarsu, a hankali hawayenta suka daina zuba, yayinda tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, bakomai yasa hakanba face ganinsu da tayi sun shigo cikin unguwarsu tsulum, a bakin ƙofar gidan nasu yayi parking cike da kulawa yajuyo da kallonsa ga Zahrah wacce take ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, alamar taci kuka ta ƙoshi.

“Banga laifin kiba Zahrah, domin dole zakiji matuƙar tsoro, a iya tsawon rayuwata bantaɓa cutar da wata mace ba, kuma bazan fara akan ki ba, bazan taɓa iya cutar dake ba Zahrah, inaso ki yarda dani, ban kuma yi haka don na cutar dake ba, nabiya dake ta mall ɗinne don inaso muje kiyi sayayyan abubuwan dakikeso da kanki, amma sai naga gaba ɗaya kinfirgita, kiyi haƙuri na tsorataki ko ƙanwata !!” Doctor Sadeeq yafaɗi maganar cikin tsananin tausayawa da kuma lallashi ga Zahrah’n..

Kuka kawai Zahrah takuma fashewa dashi haɗe da cusa kanta cikin cinyoyinta, a hankali ya kama hanunta haɗe da matsewa a cikin nasa hanun, “Banason kuka Zahrah, bana ce kiyi haƙuri ba!” Dr yafaɗa cikin damuwa.

“Bakaine zaka bani haƙuri ba likita, nice zanbaka haƙuri, nayi maka mummunar fahimta, dan Allah kayi haƙuri, wlh tsoro nakeji banso wani abu yasake faruwa dani…!” taƙare maganar tana kuka sosai.

“Idan kinaso nayi haƙuri to kidaina kuka kinji ƙanwata!” yafaɗi maganar yana mai ƙare matse hanunta a cikin nasa hanun.

A hankali tashiga share hawayen dake ambaliya akan fuskarta, ji takeyi zuciyarta tayi mata sanyi.

“Bakya kyau idan kina kuka, kinfi kyau idan kina dariya, kije gida kiyi wanka ki huta, banso kisake zubar da hawayenki kinji Zahrah, ungo wannan ledan kishiga gida, akwai waya a ciki na samiki sim da komai, akwai games dayawa a ciki,nasan zai ɗebe miki kewa, banson ganinki cikin damuwa Zahrah, kije gobe zanzo na kaiki school dakaina, Allah yasa bazakimin gardamaba ” yaƙare maganar yana ƴar dariya.

Murmushi itama Zahrah tayi haɗe da ƙarɓan ƙatuwar ledan dayake miƙo mata, batare da tayi masa gardama ba, cikin rashin kuzari ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, harsai da yaga shigewarta cikin gida kafun ya ta da motar tasa ya bar unguwar tasu..

Zahrah tanashiga cikin gida kai tsaye ɗakinta tawuce, jakarta da ledan da Dr Sadeeq ya bata ta ajiye. Kayan jikinta tashiga cirewa, zani ta ɗaura a kirjinta haɗe da sanya hijabi tafice daga cikin ɗakin, zaune ta taradda Inna a tsakar gida, sannu da gida kawai Zahrah tayi mata, haɗe da shigewa cikin bayan gida, tana fitowa a wanka ta bi lafiyar katifarta domin dama dai bata wani jin yunwa, ledan da Doctor yabata ta jawo haɗe da buɗewa, kyawawan dogin riguna ne suka bayyana acikin ledar saikuma dangin su snacks dasu choculate, kyakkyawar kwalin wayar da tagani acikin ledar taciro SAMSUNG GALAXY S10 shine sunan da ke rubuce ajikin kwalin wayar, wani irin faɗuwa gabanta yayi take nunfashinta yashiga gudu akai akai, bazata taɓa mantawa ba shima da haka yafara, daga ƙarshe kuma ya dasa mata babban tabo acikin zuciya da rayuwarta mai wahalan gogewa, saurin sake kwalin wayar tayi haɗe dayin watsi da kayan da suke zube a gabanta, talauci bahauka bane, bazata sake bari haka yafaru da’ita ba, hawaye ne suka shiga sauƙa akan ƙuncinta, haƙika soyayya bata mata adalci ba, kwanciya tayi lamo akan katifa tana nai sauƙe a jiyar zuciya, jin da tayi zuciyarta na shirin dawowa ɗanyea shakaf ne yasanyata tashi ta ɗauko littafi mai tsarki wato Al’Qur’ani tasoma karantawa domin rage damuwar dake damunta a zuciya….

STORY CONTINUES BELOW

“Salima kuma Hajiya?” Doctor Sadeeq yatambaya cikin muryar damuwa.

“Ƙwarai kuwa Sadeeq, ko ita Saleema’n tana da wani aibune? ƙwarai nayaba da hankalinta dakuma tarbiyanta, saboda haka nagama yanke shawarata, gobe zanfaɗamawa ƙanin mahaifinku yaje yatambayo maka aurenta, idan ma a so nane banso bikin yawuce nanda wata ɗaya ” Hajiya tafaɗi maganar babu alamar wasa akan fuskarta.

Cike da sanyin jiki Doctor Sadeeq yace ” Shikenan Hajiya, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma dakin ƙara haƙuri, nan bada jimawa ba zan kawo wacce nakeso”

“Hmmm ai aikin gama yariga daya gama Sadeeq, nagaji dajin wannan zancennaka, koda yaushe haka kake cewa, to yanzu dai nagaji da ƙaululan dakakemin saboda haka natsaida magana,zaka iya tafiya”

Gaba ɗaya hukuncin da Hajiyar tasa ta yanke masa baiyi masa daɗi ba, amatsayinsa na Namiji bai dace ace anyimasa dole akan aure ba, shi sam Saleema ma bata ɗaya daga cikin irin tsarin matan dayakeso, amma yazaiyi tunda dai Hajiya ta kafe, yasanta da wuyar sha’ani, idan tace eh zaiyi wuya kuma tace a’a, jiki a mace haka yafice daga falonnata, kaitsaye ɓangaren sa yanufa, yanashiga cikin falonnasa direct friedge yanufa, goran ruwa mai sanyi ya ɗauko, haɗe da zama akan kujera, saida yasha ruwan fiye da rabin gora, kafun yashiga sauƙe ajiyar zuciya, wayarsa yaciro acikin aljihun rigarsa, kai tsaye lambar sim ɗin dake cikin wayar daya bata, ya danna wa ƙira, saidai yaji saɓanin tunaninsa, domin kuwa cemasa akayi wayar a kashe take, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da aje wayartasa a gefe, “Maiyasa nadamu da’ita sosai ne?” yatambayi kansa, bayan kuma yasan baida amsa,

“Inatausayinta sosai,amma kuma bayan tausayi inajin wani abu na daban a ga me da’ita, menene wannan abun ? yazama dole nasan menene amma tabbas ina da burin inganta rayuwarta ” Ƙaran wayarsane ya katse sa daga zancen zucin da yakeyi, ganin da sabon number ake ƙiran nasa yasa bai ɗauki ƙiranba, saima tashi dayayi yawuce cikin bedroom ɗinsa…

Washe gari.

Yau tunda safe takammala shirinta, tayi kyau cikin shigar ta ta atamfa riga da sket, yayinda lufayant dake jikinta ya kasance hot pink colour, sama sama tasha ruwan shayin da Inna ta dafa, tana kammala shan ruwan shayin ta ɗauki jakarta haɗe da nufar hanyar waje. domin batamaso likita yazo yasameta, tafiso tayi tafiyarta, sam bataso yanashiga cikin rayuwarta, takuma yanke shawaran gaya masa yafita acikin rayuwarta, domin sam baikamata tasake bawa wani namiji dama ba.

Turus haka taja ta tsaya, domin kuwa tsaye tagansa ajikin motarsa, yasha ado cikin wata blue ɗin shadda, sam batai tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacinba.

Murmushi yayi mata haɗe da soma takowa harzuwa inda take tsaye.

“Baki tsammaci ganina a dai dai wannan lokacin ba ko?” yatambayeta kansa tsaye yana mai kafeta da idanu.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa “Ina kwana”

“Lafiya ƙalau, yakika tashi?”

“Lafiya” tabasa amsa a taƙaice, haɗe da sunne kanta ƙasa, domin hakanan taji yamata wani irin kwarjini.

“Muje kada kiyi latti ko” Doctor yafaɗa yana mai yi mata nuni akan cewa tashige gaba.

Bazata iya musa masa ba, domin kuwa yayi mata kwarjini sosai, don haka cikin sanyin jiki tanufi wajen motar tasa, shikuma yarufa mata baya, gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi, alƙawarin da ta ɗaukawa kanta nacewa zata faɗa masa yafita a rayuwarta gaba ɗaya ya ruguje, domin kuwa tanaganinsa taji bakinta yamutu murus, tana shiga cikin motar ta lumshe idanu, domin kuwa wani irin daddaɗan ƙamshi cikin motar keyi, cike da nutsuwa yake tuƙin nasa, yayinda jefi jefi yake satan kallon Zahrah, wanda gaba ɗaya hankalinta yana ga ababen hawan da suketa hada hada akan titin.

“Maiyasa ki kaƙi kunna wayar dana baki?”

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi haɗe da soma wasa da yatsun hanunta, “Babu” tafaɗi hakan cikin sanyi murya.

“Ko kuma dai bakyason kyauta daga gareni ba “

Saurin kallonsa tayi, jin abun da yace, ai kuwa karab idanunsu suka haɗe a waje ɗaya, saurin sadda kanta ƙasa tayi, domin batason haɗa idanu dashi kokaɗan, “Bahaka bane, kawai dai banson rayuwata tasake cutuwa ne” tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.

Kansa ya jinjina haɗe da cizon lips ɗinsa, “Eh ta wani wajenma kina da gaskia, amma ai bada wata manufa na baki ba, amma idan kinaga zaki takura to shikenan saikiyi abun da yadace” shima yayi maganar da iya gaskiarsa.

Daga haka dukansu basu sake ce da junansu komaiba, har suka iso cikin makarantar, yauma har gaban lecture hall ɗin su ya kaita, sai da kuma yaga shiganta cikin hall ɗin kafun yayi tafiyarsa.

Koda aka tashi yauma shiya zo da kansa ya ɗauketa, sai dai tunda suka kama hanya harsuka isa gida babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu.

A daidai ƙofar gidan su ya tsaida motar, haɗe da juyo da kallonsa gareta ƙoƙarin fita tasomayi daga cikin motar, cikin wata irin murya mai sanyi yace “Inason magana dake”

Kallo ɗaya tayi masa ta kau da kanta gefe, “Wace irin maganace ?”

“Maganace mai matuƙar mahimmanci , amma kuma tana buƙatar ishashshen lokaci ” Doctor yaƙare maganar yana mai duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.

“Inajinka” Zahrah tafaɗa a taƙaice,

“Bakina jina zaki ce ba, hankali da tunaninki nakeso kibani “

Gyara zamanta tayi haɗe da ɗan satar kallonsa, batare da tace komaiba.

Kwantaccen sajen dake kan kumatunsa ya shafa, haɗe da cewa ” No kada kiyi zaton wani abu zance, dama alluranki ne banƙara sa miki ba, kuma akwai matsala idan banyimiki su ayau ba!”

Gaba ɗaya idanunta ta ƙwalalo su waje, yayinda tsoro yacika zuciyarta, “Dan Allah kayi haƙuri wallahi na warke, yanzu banajin komai ajikina!” taƙare maganar lokacin da muryarta ke rawa, alamun zatayi kuka.

“A’a ni gaskia banyarda da cewa kin warke ba, saboda naga kina yawan sanya kanki a damuwa kuma jiya ma dana riƙe hanunki naji zazzaɓi a jikinki, don haka kawai zan ƙarasa miki yanzu” yaƙare maganar yana mai shirin buɗe wani ɗan ƙaramin drower dake cikin motar, take allurai suka bayyana, ai a ɗari Zahrah ta buɗe murfin motar haɗe da rugawa zuwa cikin gida, ko tsayawa ɗaukar jakarta batayi ba.

Dariya sosai Doctor Sadeeq yasanya, hadda riƙe ciki, shi dama burinsa yaga yanayin tsoronta, domin idan tana cikin wannan yanayin tsoron sosai take burgesa, ɗaukar jakar nata yayi haɗe da fita acikin motar kai tsaye yanufi cikin gidan. Yana sallama Inna ta tarbesa da fari’a, haɗe da cewa “Ai dama nasan tare kuke domin daganin yanda tashigo a guje nasan cewa ba ita kaɗai bace” ɗan guntun murmushi yayi haɗe da cewa ” waifa dan nace zanmata allurane, shine duk tabi ta ruɗe, kuma yau bazan bar gidannan ba harsai na mata alluran nan, ko yakikace Inna?”

Idanu Zahrah tasake gwalowa jin abun da yake cewa, gaskia ita daya mata allura gwamma yabata magani amma sam batason allura, kuma ita taji sauƙi, amma su sundage akan cewa wai bataji sauƙi ba, kafun ta gama zancen zucin da takeyi taji muryarsa a bakin ƙofar ɗakin yanacewa Inna ta ɗauko masa ita….Sake matse jikinta tayi ajikin bango, haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.+

“ZAHRAH!” taji muryarsa yana ƙiran sunanta, cikin tsoro da ɗar ɗar, ta buɗe ƙofar ɗakin nata, kallo ɗaya yayi mawa cikin idanunta yakau da kansa gefe, domin kuwa wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, gaskia Zahrah tana da abubuwan ɗaukar hankalin ɗa namiji da yawa a tattare da’ita.

Batare da yakuma kallonta ba, ya miƙomata jaƙarta dake riƙe a hanunsa, da sauri ta fusge jakar haɗe da komawa cikin ɗakin ta,ta kuma datse ƙofar, murmushi kawai Doctor Sadeeq yayi haɗe da girgiza kansa, kallonsa yakomar ga Inna, cikin girmamawa yayi mata sallama, bayan ya cika mata hanunta da alkhairi, cike da farinciki Inna tayi sallama dashi, don tsabar daɗi ma har kusan ƙofa ta rakasa, tana mai zabga masa godiya.

Tafiya yake amma shi kaɗai yake murmushi, sosai Zahrah take burgesa, yanason komai na yarinyar, fushinta, dariyanta, tafiyarta, nutsuwarta, dama duk wani abu nata, tabbas Zahrah tana ɗaya daga cikin irin matar da yake fatan mallaka a matsayin matarsa ta sunna, ko dai zai jarrabane ?” ya tambayi kansa, saurin dukan seterin motar tasa yayi haɗe da cije laɓɓansa, “Ka dawo cikin hankalinka Sadeeq, maikake shirin aikatawa ne haka?” yatambayi kansa a fili.

“No baikamata nayi haka ba, dole zanyi haƙuri !” yafaɗi hakan cikin karyewar zuciya, dai dai lokacin kuma ya iso gaban makeken gate ɗin gidansu, mai gadi yana gama wangale masa gate ɗin ya cusa motar tasa zuwa cikin gidan.

Saida tagama ƙaremawa wayar kallo kafun ta danna madannin da zai sanya wayar ta kawo haske, nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da jingina bayanta da jikin bango, “Yazama dole kikawo sauyi acikin rayuwarki Zahrah, kada ki bari abunda Zaid yayi miki, yazama sanadiyar lalacewar duk wani farinciki dake cikin rayuwarki” zuciyarta ta faɗa mata hakan cike da ƙarfafa mata guiwa, “Amma tayaya hakan zai kasance, bayan banda wani ginshiƙi dazai taimakamin ?” Zahrah tatambayi kanta, sake gyara zamanta tayi haɗe da ɗaukar wayarta, kai tsaye tashiga wajen dazai sadata da apps ɗin wayar, Word Charm shine game ɗin daya ɗauki hankalinta, duk cikin apps ɗin dake wayar, dama tanason game ɗin, don haka kaitsaye tashiga tasomayi, take taji kewa da kaɗaicin da take ji sun soma ragewa, a wannan rana dai Zahrah batayi wani dogon tunani da takura kanta ba, dazaran taji ta takura zata ɗauki wayarta tasoma buga game, idan ta gaji da buga game ɗin kuwa, sai ta shiga Instagram shima sosai yake rage mata kewa (nima haka, lol)..

STORY CONTINUES BELOW

Tayi kyau sosai cikin blue rover gown ɗin dake jikinta, wata baƙar lufaya ta sanya a jikinta wanda yataimaka wajen ƙarawa shigar tata kyau da armashi, batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, ta dai shafa man leɓe dakuma kwalli, amma duk da haka tayi kyau, dama mai kyau ko baiyi kwalliya ba kyawunsa baya ɓuya.

Kasancewar yau baza su jima a makaranta ba, yasanya bata ɗauki jakaba, sai wasu ƴan littatafai da ta ɗauka a hanunta, sai kuma wayarta, koda ta fito tsakar gidan zaune a bakin murhu ta iske Inna tana tuyan ƙosai, wanda Baffa yace ayi na karyawa.

“Inna ni zanwuce makaranta” Zahrah ta faɗa tana mai ƙoƙarin gyara zaman lufayan dake jikinta.

“Bazaki tsaya ki karyaba Zahrah”

Baffa dake fitowa daga cikin ɗakinsa ya faɗa.

Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da shafa cikinta “Banajin yunwa sosai Baffa, kuma ina tsoro kada na makara!”

“Eh kina da gaskiya, kinga kuwa tun ɗazu likita, yazo yana jiranki, bayanda banyi da shi ba akan yashigo, amma sam yaƙiya, don haka gwamma ki hanzarta, a dawo lafiya ” Baffa yaƙare maganar yana mai yunƙurin komawa cikin ɗakinsa.

“Ameen Baffa nagode!” Zahrah tafaɗa cike da farinciki, domin kuwa karo na farko kenan a rayuwarta da taga tsananin kulawan Baffa a kanta.

Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushinsa, ga mamakinsa sai yaga itama ta sakar masa murmushi, wanda yayi matuƙar taɓa masa zuciya, domin kuwa bakaɗan ba tayi kyau, da tana murmushin.

“Saiyanzu ki ka ga daman fitowa? kinshanyani kamar kin aje dutse” Doctor yafaɗi maganar yana mai turo baki gaba, tamkar ƙaramin yaro.

Dariya sosai Zahrah ta shiga yi, domin yanayin yanda yayi maganar yazama dole wanda ya gani ya dara, hangame baki Dr yayi yana kallon yanda take dariyan, abun da bai taɓa gani ba kenan, tun haɗuwar su da’ita, bai taɓa ganinta tana dariya ba sai yau, ashe ma duk kyawunta da yake gani, bai ga komai ba, domin da tana dariyan tafi masa kyau.

Hanunta tasanya ta toshe bakinta, haɗe da tsagaita dariyan da takeyi, kallonsa tayi haɗe da cewa “Bakaga yanda kazama yaro ba dakana maganan nan, tamkar ɗan shekara takwas!”

Murmushi yayi haɗe da jefamata hararan wasa, cikin yanayin da yayi magana ɗazu yakuma cewa “Shine kikemin dariya ko? sai na faɗaki da mamana!” ai kamar yaƙara mata fower’n da riyan nata ne, nan take taci gaba da dariyanta, hadda ɗan guntun ƙwalla a idanunta, wani irin sanyi da nishaɗi yaji yana huda zuciyarsa, tabbas bashida wani buri da yawuce yaga Zahrah tana cikin farinciki Alhmdlh, yau gashi ta sanadiyarsa tana dariya dakuma nishaɗi,

“Kayi haƙuri, bazan sake shanyaka ba, amma gaskia ka iya shagwaɓa da yawa!” Zahrah tafaɗa dai dai lokacin da tayi mawa kanta mazauni acikin motar, haryanzu dariyane kwance akan fuskarta.

“Wato dai yau mugunta kike ji dashi, dariya hadda hawaye!” Doctor yafaɗa cikin nishaɗi.

“Bahaka bane, kai ɗinne dai kawai kabani dariya!” itama ta basa amsa cikin nishaɗi.

“Dagaske kike, saboda ni kike wannan nishaɗin? ” Dr ya tambayeta cike da zaƙuwa, duk da kuwa cewa yasan sabo da shiɗinne take nishaɗin.

“Eh mana, saboda kaine, kasan kaban dariya sosai, kuma nasan bama ni kaɗaiba, duk wacce takalleka a irin wannan yanayin dole zatayi dariya”

Ajiyar zuciya Dr ya sauƙe haɗe da murza key ɗin motar, suka ɗau hanyar da zata sadasu da titi.

“Idan kina dariya kinfi ko yaushe kyau ƴan mata na!” Dr yafaɗa cikin muryar nutsuwa.

Saurin maida kallonta garesa tayi, jin abun da yafaɗa tayi kamar wani almara, sai kuma taga yanayinsa tamkar bashine yayi maganar ba.

Yi tayi itama kamar bataji mai yace ba, mai da kallonta tayi ga titi, tana mai kallon yanda ababen hawa suke gudanar da hada hadansu.

STORY CONTINUES BELOW

“Maiyasa ki ka ƙi cin abinci? ko kinfiso ki zauna da yunwa ne?” Doctor ya jefo mata tambayar da batayi zato ba.

Kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kanta gefe, “Banjin yunwa ne, sannan kuma banaso na yi latti”

tafaɗi maganar a taƙaice.

Baice da’ita komaiba, saima buɗe ɗan ƙaramin drowern dake jikin motar yayi, wani haɗaɗɗen cake dake cikin wani ɗan ƙaramin kwali ya ciro, haɗe da ɗaura mata akan cinyarta, ” Kici, kuma banson musu” yanayin yanda yayi maganar zai tabbatar ma da cewa, ba wasa yake ba.

“Nagode, amma zanci idan muka fito a lecture” itama ta faɗa kai tsaye.

“Yanzu nakeso kici, umarnine bawai shawara ba” yakuma faɗi maganar cikin yanayi mai nuni da cewa da gaske yake maganar.

Batason yi masa musu, domin koba komai yayi mata halacci a cikin rayuwarta, a hankali take gutsuran cake ɗin tana kaiwa bakinta, duk da cewa cake ɗin yayi mata daɗi.

Duk abun da takeyi yana lure da’ita, yanayin yanda take tauna abincin shiyafi komai burgesa.

Saida taci cake ɗin fiye da rabi, kafun ta dawo da kallonta garesa, “Naƙoshi” tafaɗa tana mai yatsine fuska.

“Dole sai kin cinye, domin kuwa ni idan nabawa mutum abuna, bai isa yacemin ya ƙoshi ba, dole sai yacinye koda kuwa ya ƙoshin”

Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa “Dagaske nake naƙoshi, amma da alama dole kakeson min”

“Dolen dole ma kuwa” yafaɗa dai dai lokacin da yagama parking motar tasa, domin kuwa harsun kawo cikin makarantar tasu, hanu ta ɗaura akan murfin motar da niyar buɗewa ta fita, tuni ya dannawa ƙofofin luck, saurin kallonsa tayi domin bata fahimci hakan da yayi me yake nufi ba.

“Babu inda zakije, matuƙar baki cinye cake ɗin nan ba” yafaɗi hakan yana me jingina bayansa a jikin kujeran da yake kai.

Ƙwaɓe fuska Zahrah tayi cikin sigar lallashi, tace “Kayi haƙuri, naƙoshi, idan naci da yawa, bazan iya karatu yanda ya kamata ba!”

“Um,Um, naƙi wayon, saura kaɗanne fa please kicinye shi mana Zahrah!” Doctor Sadeeq yaƙare maganar cikin lallashi.

“Um, Um, na ƙoshi, gaskiya idan naci zai cutar dani, zanyi ƙatuwa da yawa, ni kuma banaso nayi ƙatuwa!” cikin zallan shagwaɓa Zahrah tayi maganan.

Dariya sosai Dr Sadeeq ya sanya, domin kuwa maganar Zahrah ta bashi dariya, wai ita bataso tayi ƙatuwa hmm.

“To ai yaune kawai, kuma kinga bazakiyi ƙatuwa ba, nima banso kiyi ƙatuwa da yawa, amma inaso kiyi ƙatuwa kaɗan!” yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya isa sanyawa mutum mutuwar jiki.

Batace dashi komaiba, domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, ɗaukan ragowan cake ɗin tayi, tashiga turawa acikin bakinta, tamkar wacce aka bawa guba.

Dariya Doctor Sadeeq yashiga yi mata ƙasa ƙasa, domin kuwa yanda takecin cake ɗin, dagani kasan dole a kayi mata bawai a son ranta bane. tana cinyewa ya miƙomata goran ruwa, ai kuwa ba musu ta karɓa ta shiga sha, domin dama duk cake ɗin ya shaƙeta.

Cikin yanayi na shagwaɓa da ɓata fuska tace ” Na cinye yanzu zan iya tafiya!”

Dariya Dr yayi haɗe da cire luck ɗin da yasanyawa ƙofofin motar “Zaki iya tafiya, amma kikula da kanki sosai, sannan idan kun fito a lecture wani zai kawo miki saƙo daga nine ki amsa”

“Wani saƙo?” Zahrah ta tambaya cike da ɗaurewar kai.

“Zakiyi latti,kiyi sauri kije” Dr yafaɗi hakan don kawar da tambayar da tayi masa.

Bata sake cewa komai ba tabuɗe murfin motar tafice, yauma dai sai da yaga shiganta cikin hall ɗin kafun yatada motarsa yabar cikin makarantar, direct shima asibiti ya nufa, domin yau yanada aiki sosai.

STORY CONTINUES BELOW

Sosai yau ta gane Lecture ɗin da akayi musu, saɓanin sauran ranakun da suka wuce wanda ba komai take fahimta daga cikin abun da ake koyar musu ba.

Fitowarsu kenan daga lecture, tafe suke su biyu, yayinda Husnah keta mita, wai jimawan da sukayi suna lecture, yasanya tanemi gaba ɗaya abincin cikinta ta rasa.

Dariya Zahrah tayi haɗe da cewa “Nikuwa kinga ɗigo na yunwa banaji, domin kuwa yau ɗure, a kamin dan dole na”

“ɗure kuma bestie? Amma badai Inna da Baffa bane sukaimiki ɗuren bako?”

“Doctor Sadeeq ne!” Zahrah tafaɗa a taƙaice.

“Doctor Sadeeq kuma? lallai kuwa Doctor yayi babban ƙoƙari, shiyasa na ganki yau kina cikin farinciki” Husnah tafaɗa tana mai ƙoƙarin gimtse dariyar da take ƙoƙarin taso ma ta, domin ita kam ta hango wani babban al’amari dangane da Doctor dakuma Zahrah.

“Maikike nufi?” Zahrah ta tambayi Husnah cikin tsare gida.

Husnah batakai ga bata amsa ba, wani mutumi ya ƙaraso garesu, hanunsa ɗauke da wata leda, sallama yayi musu suka amsa masa.

Kaitsaye ya miƙomawa Zahrah ledar dake hanunsa, haɗe da cewa “Gashi inji oga”

Take maganar da Dr yafaɗa mata ɗazu a cikin mota, cewar wani zai kawo mata saƙo, ya faɗo mata, cikin sanyin jiki ta amshi ledan, haɗe da ce masa ta gode.

“Saurin karɓe ledan Husnah tayi daga hanun Zahrah, haɗe da cewa “Allah yasa abun daɗi ne, domin yawuna haryafara tsinkewa, kinsanni ba baya bace wajen kwaɗayi”

“Wow special gift!!” Husnah tafaɗa sanda idanunta suka gane mata abun da ke cikin ledar,

“Amma ba haka naso ba, ƙawata naso ace wani abun ci ne kinga da sai na morewa bakina!” Husnah ta ƙare maganar tana mai ɓata fuska.

Dariya Zahrah tayi haɗe da sanya hannayenta ta dafa kafaɗun Husnah, cike da nishaɗi tace ” Allah ƙawata, ki rage kwaɗayi, yanzu idan abun ci ne, yazuba mana wani abu a ciki, mukazo mukaci, ya cutar da mu,kuma fa? kinga kwaɗayi ya jawo mana kenan,kuma bai mana rana ba”

“Dan Allah malama sakeni, nayarda da Dr nasan babu abun da zai ɓamu wanda zai cutar da mu, kedai kawai mugunta ne irin naki, bayan kinsan inajin yunwa, muje cafeteria muci abinci please!” Husnah tafaɗa tana mai daɗa kwaɓe fuska.

“Yi haƙuri ƙawata bani nakar zomonba, muje sai kici abincin ko” Zahrah tafaɗa cike da kulawa.

“Ungo kayan shafanki, domin kuwa cigaba da riƙesu ma, ƙaramin yunwa zaiyi” Husnah ta ƙare maganar tana mai miƙomawa Zahrah ledar dake hanunta.

Dariya kawai Zahrah tayi haɗe da amsar kayan, sarai tasan Husnah bata da haƙurin yunwa ko kaɗan.

Ice cream kawai Zahrah tasha, yayinda Husnah kuwa ta cika cikinta da shinkafa. Yau darasi biyu garesu kacal, don haka suna fitowa kowa ya yi ƙoƙarin kama gabansa.

Waige waige tashiga yi ko zata hangosa, amma babu alamar komai irin motarsa, wayarta ce ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, Number ne ke yawo a kan screen ɗin wayar babu suna, dama kuma batayi tunanin Numbern zai fito da suna ba, domin batayi saving numbern kowa ba, wama ta sani da zatayi saving number’nsa.

Har saida wayar ta kusa katsayewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran, “Zahrah! na gaji, da yawa, aiki yamin yawa, please ga nan driver na, zaizo ya ɗaukeki ya kaiki gida, kiyi haƙuri kinji ƙanwata!!” Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin kwantar da murya, da gajin yanda muryansa take fita slow kasan cewa a matuƙar gajiye yake.

A jiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa “Shikenan kahuta lafiya”

“Yauwa Ƴan mata na, ki kulamin da kanki” ƙit ya kashe wayar, ba tare da ya tsaya ya saurari mai zata ce ba.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da girgiza kanta, “Hmm wai itace ƴan mata, itakam yanzu ai ta wuce a ƙirata ƴan mata saidai sauran Zaid” tafaɗi hakan a zuciyarta, take kuma taji idanunta sun kawo ruwa. Dai dai lokacin motar Dr Sadeeq ta ƙaraso inda take tsaye, kasan cewar yayi mata bayanin cewa driver’n sane zaizo ɗaukarta, dan haka batayi wani jinkiri ba, ta buɗe murfin motar tashiga, ko kallon inda driver’n yake batayi ba, “ZAHRAH!” muryan Dr Sadeeq ya daki dodon kunnuwanta, saurin maida kallonta inda taji muryan tayi, ai kuwa shiɗinne kwance a jikin kujeran gidan baya, idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da ɗage giransa ɗaya sama, “Surprise!” yafaɗa fuskarsa ɗauke da murmushi.

Murmushi itama tayi masa, haɗe dayin ƙasa da kanta, domin yanayin yanda yayi mata maganan, yasanya taji jikinta yayi sanyi.

“Dawo nan muzauna, ki bar driver yayi aikinshi”

Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da turo baki gaba, cike da shagwaɓa tace “Ni dai kabarni na zauna anan ɗin ma yayi!”

“Nace ki dawo nan muzauna ko!” yafaɗi hakan babu alamar wasa akan fuskarsa.

Cike da sakalci Zahrah ta dawo gidan baya inda yake zaune, ko kallonsa batayi ba saima langwaɓewa da tayi a jikin kujera. Har sukayi nisa a tafiyan babu wanda yace da ɗan uwansa ƙala, cikin shagwaɓa tace “Bakace min aiki yamaka yawa ba, amma mai yasa kazo?”

“Saboda ya cancanta nazo, ina da burin baki kyakkyawan kulawa a ko da yaushe, ko bakiyi farinciki da hakan ba?”

“Nayi farinciki sosai!” Zahrah tafaɗa kai tsaye, domin kuwa sam batason irin kallon da yake yawan yi mata a wasu lokutan.

Baisake ce da ita komai ba, shima sai ma komawa da yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran motar.

A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah’n, kallo ɗaya tayi masa haɗe da buɗe murfin motar tayi ficewarta, yana ganin shigewarta gida, yace driver ya ta da motar suje.

Bayan Sati Biyu….

Wani irin shaƙuwa ne mai ƙarfi yashiga tsakanin Doctor Sadeeq da Zahrah, kullum shi ke kaita mkaranta shi kuma ke ɗauko ta, sosai yake bata kulawa, baya son duk wani abu da zai ɓata ranta, ko ya sanya taji ba daɗi, ɓangaren Zahrah ma, sosai take kiyayewa dashi, tana iya ƙoƙari wajen ganin bata musa masa idan ya umarceta da tayi abu, ko kaɗan batajin wani abu a dangane dashi, tana dai yi masa biyayya tana kuma ganin girmansa, domin kamar yanda yace ta ɗaukesa, a matsayin ɗan uwa, to a matsayin ɗan uwan ta ɗaukesa, domin kallon yaya take masa, sannan kuma sosai wayarta take ɗe be mata kewa, yakanyi ƙoƙari wajen ganin ya ƙirata a waya, a kowani dare, sai dai hiran tasu bata tsayi suke sallama da juna, sosai rayuwarta tasamu canji, bakamar da ba, duk da cewa abune mawuyaci manta abun da ya faru da’ita, amma takanyi ƙoƙari ƙwarai wajen ganin ta gusar da duk wani damuwarta.

Tsaye yake a gaban tangamemen dressing mirror ɗin dake kafe a jikin bangon ɗakin nasa, yayi kyau sosai cikin riga da wandon shadda dake jikinsa, ba abun da jikinsa keyi banda tashin ƙamshi, hannayensa duka yazura a cikin aljihun wandon shaddan dake jikinsa, tabbas a kwai wani al’amari mai girma dake cikin zuciyarsa, haƙiƙa kuma akwai abun da yakeso ya furta,amma tayaya, baisan da wani manufa zata ɗauki zancen ba, baisan wani amsa zaiji daga bakinta ba, wannan shiya hanasa furta mata tsadaddan kalman dayake ta ɓoyewa tsawon lokuta, bayajin zai samu abun da yakeso daga gareta, bakuma yajin zai samu amincewarta, ya tabbatarwa kansa cewa, a yanzu lallashi take buƙata fiye da komai, sannan kuma bata buƙatar wata magana wanda zata zamo sanadiyar rugujewar ɗan farincikin da ta soma samu, sai zuciyar sa ta ƙarfafa masa guiwa, saikuma gangar jikinsa tayi sanyi laƙwas.

“Ba’asan jarumin Namiji da tsoro ba!” wata zuciyarsa ta furta masa hakan.

Ƙwarai ya yarda da cewa shi ɗin jarumi ne, amma kuma gurin da yake da muradin isar da saƙonnasa wajene mai rauni, dole zai fuskanci ƙalubale guda biyu, rashin nasara, ko kuma, yin nasara, wayarsa ya ɗauka ya sanya a cikin aljihunsa, kai tsaye ya fice daga cikin ɗakin nasa, yana shiga cikin motarsa ya bata wuta, kai tsaye unguwar su Zahrah ya nufa, sosai ya yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, lallai yazama dole ya bayyana mata sirrin dake kwance cikin zuciyarsa, sai dai yasan balallai ta aminta da ƙuɗirinsa ba, amma zai jarraba ya gani.

A ƙofar gidansu yayi parking motarsa, haɗe da ciro wayarsa, ya danna wa Number’n Zahrah ƙira, sai dai harzuwa lokacin zuciyarsa fat fat haka take bugawa. tana ɗaga wayar yace “Ina ƙofar gidanku, dan Allah kizo ki sameni” banji mai tace masa ba, sai gani nayi ya mai da wayar tasa cikin aljihunsa, haɗe da sauke nannauyar ajiyar zuciya….Tana aje wayan ta ɗauko wani rover hijab ɗinta ta sanya a jikinta, koda tafito daga cikin ɗakin nata, zaune ta iske Baffa da Inna, a tsakar gida, domin dai dama dare yasoma rufawa, cike da ladabi tace ” Baffa Doctor Sadeeq yana ƙirana a waje”

Gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa ” to naji ƙaran tsayuwar mota ai, ashe dai likitane yazo, to adawo lafiya”

Muguwar harara Inna ta jefamawa Zahrah, cike da masifa tace “Wato ni banza bankai matsayin da zaki tambayeni ba ko? wato Baffanki kaɗai kika gani a wajen?”

Cikin sanyin murya Zahrah tace “Kiyi haƙuri Inna, naga shi ya kamata na sanarmawa hakanne, tunda ya na nan!”

“Wuce kije ƙiran da yake miki kinji Zahrah’u, barta Salame yau masifa take ji dashi” Baffa yaƙare maganar yana mai wurgamawa Inna harara.

Bata kuma sauraran abun da Inna zatace ba tasakai tayi ficewarta daga cikin gidan..

Duk da cewa babu wadataccen haske a wajen, amma tana iya hango kyawun da kayan jikinsa sukai masa, “gaskiya Dr kyakkyawane shima” tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.

Da sallama ɗauke a bakinta ta ƙaraso inda yake tsaye, cike da fari’a Dr ya amsa mata sallaman da tayi haɗe da cewa “Wato sai anjamin aji kafun a fito ko?”

Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa “Bawani batun jan aji, ni a hakan ma inaganin na fito da wuri”

Shima murmushin yayi haɗe da cewa “Kinyi kyau!”

Still murmushi tayi, cikin son kawar da zancen da yayi na cewa tayi kyau, tace “Lafiya kuwa naganka a dai-dai wannan lokacin?”

Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da maida nutsuwarsa gareta “Maganar danazo miki da’ita Zahrah bata tsaye bace, yana da kyau mushiga mota, sai mu tattauna ko?”

Ɗan jim Zahrah tayi, haɗe da cije lips ɗinta, “Shikenan amma inafatan bazamu jimaba, kafasan banson fitowa waje da dare”

“Insha Allah, bazamu ɗau tsawon lokaci muna magana ba!” Dr yafaɗi hakan lokacin da yayimawa kansa masauƙi a cikin motar tasa, bayan ya kunna ƙoyin wutar dake cikin motar take haske ya gauraye cikin motar.

STORY CONTINUES BELOW

Gyara zama Zahrah tayi, haɗe da tattaro duka nutsuwarta “Inajinka” tafaɗa a taƙaice.

Wani irin numfashi Dr yayi, haɗe da fitar da iska daga bakinsa, sai yanzu yakejin cewa, bazai iya furta abun da yakawosa ba, gaskiya yanajin nauyi, baisan tayaya Zahrah zata karɓi muradinsa ba, kada maganar da zaifaɗa ma ta yazamo sanadiyar rugujewar nishaɗin da yake gani akan fuskarta yanzu, “Ta’ina zanfara?” ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.

“Lafiya kuwa, naga kayi shiru?”

Zahrah ta tambaya, cike da mamakin yanda yayi shiru, bayan yace akwai maganar da zasuyi.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗi da maida kallonsa gareta, saida ya tattaro nutsuwarsa kafun yace…

“Yazakiji idan wani yazo miki da batun soyayya a wannan lokacin Zahrah?” abun da ya iya fitowa daga bakinsa kenan, domin a gaskia shikam yarasa ta’ina zai fara.

“So kuma? wani irin so?” Zahrah ta tambaye shi cike da mamakin kalaman nasa.

“So na Aure Zahrah!” yafaɗi maganar cikin ɗar ɗar.

“Au..r..e.. Kuma Likita? Aure fa kace, dama akwai wani wanda, zaiji kwaɗayi da sha’awar aure na ne? hmmm a gaskia bana tunanin haka, domin kuwa babu wani wanda zai so ni da rayuwata, a yanda nake ɗinnan!” Zahrah tafaɗi hakan da’iya ka gaskiyar ta.

“Kada kice haka Zahrah, akwai mata masu rauni da yawa irin ki, amma an auresu, kuma anzauna dasu, ke me yasa zaki yanke ƙauna da….”

“Dan Allah kadaina min wannan zancen Doctor, banjin zan sake son wani ɗa namiji a duniyar nan”

Zahrah ta katse shi da ga maganar da yakeyi, ci gaba tayi da cewa

“taya kake tunanin zansake kai kaina tarkon da ya ruguzamin rayuwa, shi So ɗin dakake faɗa yanzu, shine ya ruguzamin rayuwa ta, ya rabani da duk wani farinciki na rayuwata, shin idan kace min na sakeyin So, kamin adalci kenan? ” Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.

“Kada kice haka Zahrah, kefa musulmace, kuma ke mace ce, nasan kina da sanin cewa, kyautatuwar rayuwar ƴa mace shine aure, haka kuma rayuwar ƴa mace bata cika hundred percent sai da aure, haka kikeso ki ƙare rayuwarki ba aure? ko kin manta cewa cikar mutumcin mace shine a ganta gidan mijinta? yin Aure shine burin kowacce mace ta ƙwarai, nasan kema wannan shine burinki, kada shaiɗan yayi amfani da abun da yafaru dake, ya ruguza miki rayuwa, ya hanaki aikata sunna!”

“Hakan shine burina amma ada, wa zai aureni a yanzu? waye zai ɗaukawa kansa duhu? waye zai ɗauki sauran da wani yaci ya rage, sauran da wani ya tarwatsa, ya zuba ƙazantarsa, acikin cikinta, waye zaiyi hakan? bazan yaudari kaina ba, nasan babu wani wanda zai aureni a yanda nake, bantaɓa aure ba, amma kuma niba budurwa bace a yanzun, ya cuceni yariga ya karɓe abun da nake burin bawa mijina na sunna, waye zai yarda da haka?”

“Nine nan Zahrah, Nasan komai a kan ki, kuma zanyarda da duk wata ƙaddaranki, nine wanda zan sharemiki hawayenki, kece damuwata bawai budurcin kiba, kiyarda dani dan Allah!!” Doctor Sadeeq yafaɗi hakan cikin jajircewa..

Kamar sauƙan aradu haka Zahrah taji sauƙan kalamansa a cikin kunnuwanta, cak ta tsaida kukan da takeyi haɗe da, da hangame baki tana kallonsa, gani take kamar ma baya cikin hayyacinsa, ƙaryane tayaya za’ace Namiji mai aji, kamar Doctor yace wai ya amince da ƙaddaranta zai aureta, wannan ba gaskia bane,

“Kada kiyi shakka ko kokonto, ba yaudara’nki nake ba, dagaske nake har cikin zuciyata, don Allah ki bani dama Zahrah, burina da fatana kawai ki amince min!”

Kai Zahrah ta shiga girgizawa, cikin tsananin ɓacin rai da danasin sauraransa da tayi tasoma cewa ” Nayi Babban kuskure, haka kuma na tabka nadaman baka daman shigowa rayuwata da nayi, ashe dukanku haka halinku yake, macutane ku azzalumai, ashe bazaku taɓa sanjawa ba, dama ɗaya kawai idan aka baku, sai ku nemi shigo da manufarku, kaicona da abun da Zaid yayi mini baikasance IZNAH ga rayuwata ba, kaicona dana sake aminta da kai, kaicon zuciyata, kafita a rayuwata dan Allah, kaje banaso nasake ganinka ko kuma jinka, katafi kayi nisa da ni, kabarni na rayu cikin salama dan Allah!!” gaba ɗaya hawayen ɓacin rai yagama wanke mata fuska, ƙoƙarin fita daga motar ta somayi, cike da tashin hankali Doctor Sadeeq ya riƙo hanunta, ko kaɗan baiyi zato ko tsammani ba, saijin sauƙar mari yayi akan kumatunsa, Zahrah ce ta ɗaukesa da lafiyayyen mari, babu abun da ke kwance akan fuskarta banda tsananin ɓacin rai,

STORY CONTINUES BELOW

“Koda wasa kada kasake ƙoƙarin taɓani, mayaudari, dama haka kuke bakuma zaku canza ba!!” fuuuuu haka Zahrah tafice daga cikin motar tamkar kububuwa.

Tamkar statue haka Dr Sadeeq ya tsaya, komai nasa daina aiki yayi, sai numfashinsa dake fita da sauri, ganin komai yake tamkar al’amara, wai yau shine Zahrah ta mara da hanunta, a hankali yasanya hanunsa ya shafi kan kumatunsa inda Zahrah ta wankesa da mari, ko kaɗan baiga laifin Zahrah ba, kuma baiji zafin marin da ta masa ba, babban damuwarsa da tashin hankalinsa, shine yanda yaga Zahrah tana kuka wiwi, sannan kuma ranta yayi matuƙar ɓaci, tabbas da yasan abun zai ɓaci har haka, to da baiyi gigin furta mata kalmar cewa zai aure ta ba, ko da na minti ɗaya ne bayason ɓacin ran Zahrah, yanzu yasan haka zata kwana tana kuka, maiyasa? maiyasa na kasa jurewa? ni nake burin faranta rayuwa da zuciyarta, amma sai gashi da kaina nasake ruguza farinciki’nta maiyasa? yatambayi kansa da ƙarfi, cike da haushin kansa ya sanya hanunsa duka biyu ya daki siterin motar tasa, wani irin haushin kansa yakeji, yayi dana sanin sanar da’ita abun dake cikin zuciyarsa, “mai yasa na yarda nazamo LOSER?” ya tambayi kansa cikin ƙunan zuciya, yakusan 10 minute yana zaune a cikin motar, da ƙyar ya’iya tada motar yabar cikin unguwar tasu…

Zahrah kuwa tana shiga gida, kaitsaye ɗakinta ta wuce, zamewa tayi a ƙasa, tashiga rera sabon kuka, lallai tayarda cewa Ƙaddaranta mai girma ce, daga wannan sai wannan, bata taɓa zato ko tunani’n haka zai fito daga bakin Dr Sadeeq ba, ko da wasa bata taɓa ayyana wani abu a ranta ga me da shi ba, maiyasa zai zo mata da wannan maganar a daidai wannan lokacin? maiyasa zai sake maida ita uƙubar da tayi nasaran samun bakin fita daga cikinsa? tabbas yanzu kam tayarda cewa duhu yasamu mazauni a cikin rayuwarta

“Bawanda zai soni a haka, shima nasan ba sona yake ba, wata manufarsa kawai yakeson cimmawa, ashe ƙaddarorina suna da yawa?” ta tambayi kanta cike da ruɗu.

Sanin bata da amsar bawa kanta, yasanya ta cigaba da kukanta, ganin hakan bazai fishsheta ba yasanya ta ɗauro alwala tazo ta fara gabatar da salla, haɗe da miƙamawa mai kowa mai komai duka lamuranta…

Koda Doctor ya isa gida, baije koda ɓangaren mahaifiyarsa bane, kai tsaye ɓangarensa ya nufa, gaba ɗaya jiyakeyi duniyar ta masa ƙunci, saboda cimma muradinsa yasake sanya Zahrah a damuwa, kwanciya yayi lamo akan gado, zuciyarsa cike da tarin tunanuka kala kala, gaba ɗaya kalamanta ne suke yawo a ƙwaƙwalwarsa, babu kalman da tafi tsaya masa a rai kamar inda takecewa ” Natabka nadamar baka daman shigowa rayuwata da nayi, katafi ba naso na sake ganinka ko kuma jinka!!” wannan kalamannata sunfi komai ɗaga masa hankali, sam shikam ya ma manta da marin da tayi masa, saboda bai ɗauki marin a matsayin komaiba, shidai shiga damuwarta ne bayaso, baisan wani irin so yake mawa Zahrah ba, bayason ganinta a cikin damuwa, ba kuma yason ɓacin ranta, amma tayaya Zahrah zata fuskancin hakan? Yanaso ya aureta yakuma inganta rayuwarta, ba budurci’nta bane abun so a gareshi ita kanta ce abarsonsa, haƙiƙa kowani namiji yana burin auren mace yasameta a budurwa, shima kuma yana burin hakan, amma son da yakemawa Zahrah, yasanya zai iya karɓanta a yanda take.. Haka Doctor yayita saƙawa da kuncewa, da ƙyar bacci ɓarawo yayi nasaran ɗaukarsa.

Ɓangaren Zahrah ma dai hakanne takasance da ƙyar ta’iya runtsawa a wannan dare….

*TURKEY*

*ZAID* ne zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera, sanye yake da riga long slive, white colour yayinda wandon jikinsa ya kasance baƙi, suit ne baƙi ɗaure a saman kayan nasa, sosai yayi kyu a cikin shigartasa, hanunsa riƙe yake da wani dogon kofi na glass, bakomai ne acikin kofin ba face giya, a hankali yake sipping giyar tasa, yayinda ya ɗaura ƙafansa ɗaya kan ɗaya, gefensa kuwa Abid ne zaune shima dai irin shigar Zaid ɗinne a jikinsa, sai dai shi nasa kalan sun kasance blue, “Lokaci fa yana tafiya Zaid, yakamata ace yau munkoma New York, amma bansan dalilinka nacewa muzauna anan ba, ni fa duk yanda instanbul takai ga haɗuwa da daɗin zama, batakaimin new york ba, kasan can akwai mata ƴan harka, amma ni gaskia nan a takure nake!” Abid yakai ƙarshen zancennasa cike da ƙosawa.

STORY CONTINUES BELOW

Kyakkyawan murmushinsa yayi haɗe da maida kallonsa ga wani kyakkyawan ruwa dake gudana a gefensu,

“Inason zaman Instanbul sosai Abid, domin yanayin garin yanasawa inajin shauƙin abar sha’awata!!”

“Bangane shauƙin abar sha’awan kaba? wai meke damunka ne? kusan tsawon watanni kenan dana fuskanci sauyawa a tattare dakai”

“Sha’awa nakeji Abid, matsanancin sha’awarta nakeji!”

Zaid yafaɗa cike da tsananin shauƙi.

“Sha’awa? wacece ita?” Abid ya tambaya cike da zaƙuwa, domin shikam yarasa wace irin macece Zaid ya kejin sha’awa’rta haka, ko da yaushe cikin maganarta yake, kuma ita kaɗai yakejin sha’awa.

“ZAHRAH NA!” Zaid yafaɗa cikin wata murya mai ɗauke da ma’anoni.

Dariya sosai Abid yasanya, hadda riƙe ciki, “Zahrah fa kace Zaid, wannan villager girl ɗin, koba sugar baby’nka ba?” Abid yatambaya yana ƙoƙarin gimtse dariyar da ta tasomai.

” Tana da matuƙar mahimmanci a wajena Abid, bantaɓajin irin abunda nakeji akanta ba, inason kasancewa da’ita a koda yaushe, inaso tazama ita ce mace guda ɗaya dazanna yin sex da’ita dare da rana, sha’awarta tamun mummunan kamu Abid, kasan yanda nakeji kuwa ?” Zaid ya tambayi Abid cikin sigar rashin wasa.

“Kokaɗan bansan ya kakejiba, amma kuma Zaid wannan ba sha’awa bane SO ne” Abid yafaɗi hakan da iya gaskiyarsa, domin shi abun da ya fahimta kenan.

Dariya sosai Zaid yashiga yi, haɗe da sanya hanunsa ya daki kafaɗan Abid.

“Shirmen banza, wai SO? menene SO Abid? kasan me kake faɗa kuwa, taya sha’awa zata zama SO, so fa kananufin wai inasonta ne, hahaha Abid ƙwaƙwalwarka ƙaramace, taya za’ayi nayi soyayya da’ita, sha’awace kawai kuma da zaran na sakeyin sex da’ita nasan komai zai wuce, tun farkoma danasan ban ƙoshi da’itaba, ai da banbari ta tafiba!!” yaƙare maganar yana mai ɗaga kofin giyarsa yakai baki.

Murmushi kawai Abid yayi, domin yafi kowa sanin cewa Zaid bayason gaskia, amma tabbas shikam anasa hasashen zuciyar abokinsa takamu da so, yana kuma da tabbacin idan har Zaid zaiyi sex da Zahrah sau ɗari, to wannan sha’awar bazata taɓa barinsa ba, saboda dama ba sha’awar bace So ne.

“Shikenan naji ba soyayya bane, sha’awa ce, amma kasan dai yanzu bazaka taɓa samunta ba ko, wataƙilama ta mutu, domin ina da tabbacin cewa baka shigeta da wasa ba”

“Dole zan sameta ne Abid, dole sai ta dawo gareni, kuma dole ta ƙara yarda da ƙudurina a karo na biyu, aure baya ɗaya daga cikin tsarina, amma idan taƙi yarda dani, saina aureta!”

Saurin kallon Zaid Abid yayi jin abun da yake fitowa daga bakin Zaid ɗin, “Aure kuma Zaid? Abid yafaɗa cike da mamaki.

“Ƙwarai zan’iya aurenta Abid, ƴan matan tana burgeni fiye da zatonka, inason komai nata, tana da kyau na fili dana baɗini, ni nasan mai naji a cikinta Abid, bakuma zanso nasake rasata ba, sha’awarta yasa koda yaushe cikin tunaninta nake, na kuma gama yanke hukunci, nan da sati ɗaya zankoma Nigeria, badon kowa ba sai don ita, nayi missing tattausan laɓɓanta masu zaƙi kamar zuma!!” Zaid yakai ƙarshen zancennasa yana mai lumshe idanunsa, da suka soma zama ja lokaci ɗaya.

Hangame baki Abid yayi yana kallon Zaid, “Anya kuwa ba aljana Zaid ya haɗu da’ita ba?” yatambayi kansa, tabbas baitaɓa ganin Zaid acikin hali makamancin wannan ba, gaba ɗaya Zaid ya sauya, yarage yawan yin sex da mata, a cewarsa wai bayajin daɗinsu, sannan kuma koda yaushe cikin tunani yake, to idan ba so ba meke da munsa ? Abid yakuma tambayar kansa.

A hankali Zaid ya buɗe idanunsa, haɗe da miƙewa tsaye kwalbar giyansa dakuma kofi ya ɗauka a hanunsa kai tsaye yanufi wani babban bene inda anan masauƙinsu yake, da kallo kawai Abid yabisa har ya ɓacewa ganinsa..

Yana shiga cikin ɗaki ya ɗaga kwalbar giyarsa ya kafa a bakinsa, saida ya shanye giyan tas kafun yayi wurgi da kwalba’r, kaitsaye ya nufi inda ma’ajin zane zanen sa suke, Caboard papers ne dayawa acikin wajen kuma duka ɗauke suke da hoton zanen fuskar Zahrah a jiki, wani ma iya bakinta kawai ya zana, wani ko iya idanunta ya zana, yana yawan yin zanen ne idan matsanancin kewa da sha’awarta ya da mesa, ɗaukan caboard paper’n dake ɗauke da zanen bakinta yayi haɗe da mannawa akan nasa bakin, wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, domin kuwa ji yayi tamkar itaɗince da gaske, zamewa yayi ya zauna a ƙasa daɓas, haɗe da warwatsa caboard paper’s ɗin akan jikinsa.

“Inakewarki Sugar Baby’na ,nayi missing komai naki, duk da cewa nasan kina fushi dani namiki da zafi, amma kiyi haƙuri wannan karon bazan miki da zafi ba, a hankali zan bi da ke tayarda zakiji daɗi har brain ɗinki, zakuma za ki saba da ni a sannu, na miki alƙawari zandawo gareki!, kina sona?” yatambayi zanen fuskarta dake jikin wani ƙaton caboard paper, “Nasan har yanzu kina sona ko Zahrah na?” still dai wannan zane yakuma tambaya, murmushinsa mai kyau yakumayi, haɗe da sanya hanu yashafi gefen kumatunsa.

” Kiyi murmushi Zahrah na, nakusa zuwa gareki, a yanzu zan iya sadaukar da komai na zuwa gareki, amma fa banso kina yawan fushi, duk da cewa idan kina fushi kinfi kyau !”

Haka Zaid yayita sambatun sa har bacci ya ɗaukesa a wajen.2

Kwance take akan ƙirjinsa, yayinda fuskarta ke ɗauƙe da murmushi, a hankali ya matso da fuskarsa daf da tata, cike da matsanancin sha’awa ya kamo lips ɗinta na ƙasa yashiga tsotsa a hankali, cike da ƙwarewa yake cusa harshensa cikin bakinta, cike da soyayya ta soma tsotsan harshensa tana mai lumshe idanunta, a hankali yayi ƙasa da hanunsa zuwa ƙirjinta, cikin salo yashiga shafa breast ɗinta, yanayin yanda suke sucking tongue ɗin junansu, shiyasanyasu suka fice a hayyacinsu lokaci guda, ƙasa yayi da kansa zuwa ƙirjinta, yana shirin ɗaura bakinsa a kan nipples ɗinta kenan, taɓace masa ɓat, dai dai lokacin yafarka a hargitse, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, duk da cewa sanyin A.C na aiki a cikin ɗakin amma shi gumi yake haɗawa, da ƙyar ya’iya miƙewa ya shiga bathroom haɗe da sakarmawa kansa shower.

ba yau yafara wannan mafarkin ba, amma maiyasa Zahrah take gudunsa acikin mafarki, takan ɓacewa ganinsa a daidai lokacin da yake matsanancin buƙatar ta….Yajima tsaye a gaban shower ruwa na dukansa, mafarkinsa na yau ne yatsaya masa a rai, duk da kuwa cewa ba wannan bane karo na farko, daya fara yin irin wannan mafarkin. Koda wasa baiyi niyar komawa America a yau ba, amma yanzu yaji ajikinsa cewa komawarsa can ɗin yafi masa, domin kuwa mararsa har ƙullewa take saboda sha’awa, gaba ɗaya kwana biyunnan da suka shuɗe baiyi sex ba. A gurguje ya shirya kansa, bayan yasanar da Abid cewa shima ya kimtsa zasu wuce America a yau. Suna zuwa airport basu wani daɗe ba, jirginsu yaɗaga zuwa sararin samaniya….+

Nigeria

Washe garin ranan da Dr yazo da dare yafaɗi muradinsa..

Tun tashinta takejin ƙunci a zuciyarta, hakanan take jin ta tsani komai na duniyar, badon lecture’n da zasuyi yau mai amfani bane, to tabbas da bazata je makarantar bama.

Doctor Sadeeq ne tsaye a tsakiyar ɗakinsa, yayinda hannayensa duka biyu ke sanye cikin aljihun wandonsa, shima kallo ɗaya zaka masa kafahimci cewa yana cikin damuwa, kallon sa yamaida kan agogon bangon dake saƙale ajikin bangon ɗakin na sa, ƙarfe 7 da rabi na safe kenan, tabbas yasan yau ƙarfe takwas suke da lecture, yanaji a jikinsa cewa yayi mata laifi mai girma, sannan idanunsa suna matuƙar son ganinta, to amma a yanda yakeji bazai iya zuwa gareta ba, “idan ma naje nace mata me?” yatambayi kansa. ” Nariga dana furta mata abun dake cikin zuciyata, dole zanbata lokaci domin samun dawowar nutsuwar ta” yafaɗi hakan a bayyane, wayarsa ya ɗauka haɗe da kutsawa cikin dialing call ɗinsa, numbern drivernsa yashiga ƙira kai tsaye, ƙara biyu wayar tayi, drivern yaɗauki ƙiran, kasancewar driver’n yasan gidan su Zahrah, yasan ya kai tsaye, bai tsaya yi masa wani kwatance ba, yace masa yaje ya ɗauketa ya kaita makaranta, da “to” kawai driver’n ya amsa masa, katse ƙiran yayi haɗe da cilla wayar tasa zuwa kan gado,

“Yasan balallai ta yarda tabi driver’n ba, domin yanayinta da yagani jiya, kaɗai ya isa ya tabbatar masa da hakan, amma burinsa ne ya bata ingantacciyar kulawa, shiyasa baiyi ƙasa a guiwaba wajen sa driver’n nasa kaita makarnta, saboda baiso ta hau wani abun hawa bayan nasa….

Ko kwalli, yau bata shafa ba, balle kuma uwa uba fawder, zumbuleliyar doguwar riga ta sanya, haɗe da ɗaura ƙaton hijab akai, kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa tana cikin damuwa da ƙunci.

Koda tayi mawa su Baffa sallama, suma sun fahimci cewa yanayinta ya sauya, amma sai suka share babu wanda ya tambayeta.

Tana kai ƙofar gida zuciyarta tayi wani irin bugawa, sakamako’n ganin motar Dr Sadeeq, da tayi fake a ƙofar gidan nasu, tsayawa tayi cak ganin cewa driver’n sane yafito daga cikin motar, saɓanin shikansa Dr ɗin.

Cike da girmamawa Mudi driver ya ƙaraso inda Zahrah ke tsaye.

” Ranki shi daɗe barka da safiya! dama yallaɓoi ne yace nazo na kaiki makaranta, shi ba zai samu daman zuwa ba, wani aiki ne ya riƙesa, kawo jakar na karɓamiki” Mudi driver ya ƙare zance’n nasa yana mai ƙoƙarin karɓan jakar dake riƙe a hanunta. Saurin ja da baya tayi haɗe da fusge jakarta, cike da ɓacin rai tace.

“Kakoma kace masa bana buƙatar kulawarsa koda kaɗanne, ka kuma ce masa injini yafita a rayuwata, saboda bana buƙatarsa!” tanakai ƙarshen zancennata tasakai tayi tafiyarta.

STORY CONTINUES BELOW

Da kallo kawai Mudi driver yabita. “Uh ni naga bala’i, daga taimako kawai, to Allah ya kyauta” Mudi yafaɗa yana mai komawa cikin motar, key yayimawa motar haɗe da nausata kan hanya, tabbas zai koma ya shaidawa uban gidansa, duk abun da tace a faɗamai..

Cikin ikon Allah tana isowa bakin titi tasamu mai taxi, bawani ɓata lokaci tashiga yaja sukayi gaba, bayan ta sanar masa inda zai kaita.

Tun shigowarta cikin ajin, Husnah ta lura da mugun sauyawan da fuskar Zahrah’n tayi, domin kuwa kowa ya kalli idanunta, zai fahimci cewa tayi kuka har ta ƙoshi. kasancewar Zahrah’n na shigowa malami yashigo, yasanya Husnah bata samu damar tambayarta komai ga me da sauyawarta ta ba.

Koda aka fito daga lecture, kan dakalin da suka sama zama, yauma sukai mawa kansu masauƙi.

“Wai meke damunki ne Zahrah? gaba ɗaya kinsauya, bayan jiya ba haka muka rabu dake ba, sannan kuma na kula cewa, yau ba Dr bane ya kawoki, maike faruwa?” Husnah ta tambaya cike da kulawa, ga ƙawarta ta.

“Inacikin matsala Husnah! a she a yanzu babu wani, wanda zai taimakeka don Allah sai don biyar buƙatar kansa? na ɗauki yarda ta na basa, na ɗaukesa tamkar ɗan’uwa, na’aminta dashi, nayi saurin yadda haɗi da sakewa dashi, bantaɓa zaton haka zata faru ba, ashe shi abun dake cikin zuciya da ruhinsa daban ne, wani abune saɓanin tunani na!” Zahrah tafaɗa tana mai share ƙwallan daya gangaro daga cikin idanunta.

“Banganeba, kinsani a duhu, maikuma ya sake faruwa? ki faɗamin !” Husnah tafaɗi hakan cike da zaƙuwa, don ta ƙosa taji menene matsalar ƙawarta ta.

“Kinsan abun da yafaru dani Husnah, Zaid yaci mutumci na, ya ƙwaci budurcina da ƙarfin tsiya, ya halaka min rayuwa, shin kinaga akwai wani namiji dazai soni tsakani da Allah, bayan yasan abun da yafaru dani?” Zahrah ta tambayi Husnah.

“Haryanzu banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zaifi kyau ace kiwarwaremin komai!” Husnah tafaɗi hakan cikin rashin fahimta.

“Ba gaskiya bane Husnah, bai faɗawa kansa da zuciyarsa gaskiya ba, baizamanto gaskiya ba, soyayyar da yakemin ba gaskiya bace, Husnah bazan yaudari kaina ba, domin nasan babu tayanda za’ayi cikekken namiji mai aji da lafiya kamar Doctor Sadeeq, yace wai ni yake so ya aura! ina kokonto akan al’amarin !” gaba ɗaya hawaye sun gama wanke mata fuska, lokacin da takai ƙarshen zance’n nata.

Nannauyar ajiyar zuciya Husnah ta sauƙe, domin kuwa sai yanzu ta fahimci inda matsalar ƙawartata take, dakuma abun da ke damunta.

“Doctor da kansa yace zai aure ki Zahrah?” Husnah ta tambaya, bayan ta aza hannayenta duka akan kafaɗun Zahrah.

Kai kawai Zahrah ta’iya gyaɗawa, alamar “eh”

“Ba wasa bane Zahrah kamar yanda kika ɗauka, haka kuma ba yaudara bane kamar yanda kike tunani, har yanzu keɗin mai kyauce, kuma haryanzu keɗin haɗaɗɗiyar mace ce abar so ga kowani irin namiji, ba’akanki a ka faraba, baikuma dace ki ɗau hukunci mai tsanani gawanda baiji ba bai gani ba, kina tunanin Doctor Sadeeq yaudaranki zaiyi ?” Husnah ta tambaya.

“Ƙwarai kuwa Husnah, ke kanki kinsani, namiji kamar Dr ba sa’an aurena bane, ko lokacin danake ɗauke da mutumcina yafi ƙarfina, balle yanzu danake fanko, inaso kisani wannan karanbani’n shi na tafka a karon farko, yazo yazamemin babbar matsala, domin kuwa nayaudari kaina, na sawa zuciyata soyayyar wanda har gaban abada yafi ƙarfina, yakuma yi mini rata, na yaudari kaina danaƙi amfani da tunanin cewa Zaid yafi ƙarfina, bazan taɓa yarda nasake aikata haukan dana aikata a baya ba Husnah!” Zahrah tafaɗa cike da raunin murya dana zuciya.

“So baitaɓa zama haukaba Zahrah, kada kicemin kin wulaƙanta Doctor saboda abun da Zaid yayi miki, kada ki yarda da tunaninki nacewa gaba ɗaya maza mayaudara ne, kowa da irin halinsa, kuma masu irin halin Zaid basa ɓoyuwa a kamanni da halaye, soyayyarsa ce kawai tarufe miki ido, har ki ka kasa hango mummunar manufarsa a kanki, yana da kyau ki nutsu kiyi tunani, inada tabbacin cewa Dr Sadeeq, ba zai taɓa cutar da rayuwarki ba, kema kuma yakamata kisan hakan, kada tunaninki ya gushe ki kasa tantance fari da baƙi, wlh ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq ba mutumin banza bane, bakuma zan ɓoyemiki ba, tabbas idan kika tsaya wasa da damarki, to zata miki mummunan suɓucewa, haƙiƙa Dr Sadeeq haɗaɗɗen gaye ne, wanda ko wacce mace zatayi fatan samunsa a matsayin mijin aurenta, nasan idan nace miki kiyi soyayya yanzu na haɗaki da babban aiki, amma zai kyautu ace ki koyawa zuciyarki soyayyar Dr Sadeeq, shawara nake baki Zahrah, idan kuma har kikayi amfani dashi, bazaki taɓa danasani ba, dan Allah ƙawata kiyi tunani mai kyu!” Husnah tafaɗi hakan cikin son ƙarfafawa Zahrah guiwa.

STORY CONTINUES BELOW

Hawayen dake zuba daga cikin idanunta ta sanya hanu ta share.

“Bazan iya ba Husnah, bazan iya taɓa sake son wani ba a cikin rayuwata, kada ki ga laifina, nasan Dr Sadeeq yafi ƙarfina, yana da asali, yana da ƴan uwa, yanada gata, yana da kuɗi, yanakuma da ƴancin da zai zaɓi matar aure wacce ransa keso, nikuma fa? idan kikayi dubi da tushena, to ban cancanta da zama inuwa ɗaya da shi ba, nifa yanzu banda wani ƴancin da zan iya zaɓin mijin aure da kaina, sbd akwai nakasa acikin rayuwata, dole sai mai tawakalli ne zai iya aure na, to maiyasa zansanya kaina a cikin wahala? balallai farincikin da Dr Sadeeq ke ƙoƙarin bani yakasance dauwamemmeba, nafaɗamasa yafita a rayuwata Husnah, a yanzu bana buƙatar kowani namiji, zaifi kyautuwa a gareni nayi rayuwata ni kaɗai, nayarda da ƙaddarata, amma kuma yazama dole na kiyaye sake jefa kaina a haɗarin soyayya!”

Rungume Zahrah,

Husnah tayi ajikinta, sosai tausayin ƙawarta ta ya kamata, haƙiƙa Zaid yacutar da rayuwar Zahrah, ya rabata da duk wani sukuni nata, amma a kwai Allah.

“Haƙiƙa dole zakiji ciwo Zahrah, amma yana da kyau ki zurfafa tunani, ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq auren ki yakeso yayi bada wasa ba, amma abun da kikayi masa baki kyauta ba, ki basa haƙuri, koda kuwa bazaki auresa ba, yayi babban ƙoƙari acikin rayuwarki, kiyi nazari, amma kuka ba naki bane, kuma yana da kyau rama halacci da alkhairi !”

Gaba ɗaya Zahrah jitayi jikinta yayi laƙwas, take marin da ta shararawa Dr Sadeeq akan fuskarsa ya dawo mata, wani irin faɗuwar gaba taji, ko kaɗan batayi tunanin zata iya kai hanunta jikinsa da sunan duka ba, amma a daren jiya ɓacin rai yasanya idanunta rufewa, harta iya ta mare sa batare da tayi tunanin komai ba, tabbas komai yayi mata bai cancanci mari daga gareta ba.

Gaba ɗaya kasa sakewa a cikin makarantar Zahrah tayi a wannan ranan, dole ta tattara yanata yanata ta dawo gida.

Zaune take jigum akan tabarma yayinda hannuwanta ke dafe da ƙuncinta, idan da za’a ce za’a kasheta idan bata faɗi, tunanin me take ba, to tabbas da sai dai a kashetan, amma ita kanta batasan tunanin mai take ba.

Inna da fitowarta kenan daga bayi, hanunta riƙe da buta, kama ƙugu tayi, haɗe da maida kallon ta zuwaga inda Zahrah ke zaune tayi jigum.

“Wai lafiyanki kuwa Zahrah? meke damunki ne? tun safe haka kike sukuku, yanzu kuma kinyi tagumi tamkar wacce akamawa mutuwa, kodai halinki na da, kike son dawowa dashi ne? to wallahi bazan ɗau wannan iskancin ba, tun wuri ma kisani!” Inna taƙare maganar cikin faɗa faɗa.

“Ko ɗaya bahaka bane Inna, narasa taya zan ɓullowa matsala ta ne!” Zahrah tafaɗa cike da sanyin murya.

“Matsala! wace irin matsala kuma?” Inna ta tambaya cike da son jin gulma.

“Inna wai Likita ne yace zai aure ni !” Zahrah tafaɗi hakan cikin sarƙewar murya.

“Likita yace zai aure ki!” Inna ta maimaita maganan cikin ƙaraji haɗe da sanya duka hannayenta biyu ta dafe ƙirjinta.

Kai kawai Zahrah ta’iya gyaɗa mata domin zuwa lokacin har ƙwalla sun soma cika mata ido.

Wani irin guɗa Inna tasa, haɗe da sake kama ƙuƙu, “Lallai kuwa, wannan babban al’amari ne, mai ɗauke da tarin farinciki, Allah yasa dai kin amince masa?” cike da zaƙuwa inna taƙare maganar.

“Bazan iya ba Inna, kuma ma ni yanzu babu batun aure a tsarina,zan zauna kawai naƙare rayuwata cikin ƙaddarata!” Zahrah tafaɗa lokacin da hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa.

Salati Inna ta sanya, haɗe da soma tafa hannaye.

“Amma kedai Zahrah anyi shashar banza, sokuwa marar wayo, ashe dai baki da hankali, yanzu a yanda kike ɗin nan, kin samu ance za’a aure ki a haka, kice wai baki amince ba, lallai yau nasake tabbatar mawa da kaina cewa ke wawuyace, to wlh baki isa ba, baki isa ɓarar mana da alkhairan da zamu samu ba, aure dole ko kina so ko bakya so, wato kinfiso kita zama damu, goɗo goɗo dake ba aure ko, to kisa aranki cewa aurenki da likita ba fashi, dole!”

“Babu wanda zai mata dole!” Muryan Baffa dake shigowa cikin gidan yakaraɗe kunnuwansu.

“Maikake shirin faɗa ne malam, kakosan me ta aikata kuwa, Likita fa yace yanason aurenta amma taƙi?”

“Ƙwarai kuwa duk na saurari zancen ku, magana ta gaskia Salame, baza’ayiwa yarinyar nan dole ba, yanzu lokacin ta ne, yakamata a bar rayuwarta tasha iska hakanan!” Baffa yafaɗi maganar sanda yayi mawa kansa masauƙi akan wani ɗan dakali dake tsakiyar gidan.

“Laaaa shikenan kuma, kakosan abun da kake cewa? kana nufin zuba mata idanu zamuyi, ba mu isa mu sata dole ba? wani shan iska kake ƙoƙarin samawa rayuwarta, sanin kankane cewa babu wani wanda zaizo yace zai jajiɓeta a yanda taken nan, don kawai likita ya rufa mata asiri yace zai aureta, saikayi ƙoƙarin hure mata kunne.”

“Tashi ki koma ɗakinki kinji Zahrah, kiyi tunani mai kyau, idan kin yanke hukunci to kisanar dani!” Baffa yafaɗa cike da kulawa.

Cikin rashin ƙarfin jiki haka Zahrah ta koma cikin ɗakinta, yayinda take jiyo bala’in Inna a tsakar gida.

Jingina bayanta tayi da bango, haɗe da lumshe idanunta, saiyanzu take jin cewa bata kyautawa Doctor Sadeeq ba, amma kuma shima baikyautu ace yazo mata da magana mai nauyi kamar wannan ba, ko da wasa bata taɓa kawowa a ranta cewa wani zai sota anan kusa ba, gaba ɗaya ta cire soyayya a tsari da jerin rayuwarta, tabbas sai dai ta yaudari kanta, amma tasan bazata taɓa ƙara son wani ɗa namiji ba a rayuwarta, ta yarda da shawaran da Husnah ta bata, amma kuma abune mawuyaci, tarayyanta da Dr Sadeeq yazama mai ɗorewa, shin dagaske aurenta yakeso yayi koko shima wata manufartasa yakeson cimmawa? tatambayi kanta tambayar da bata da amsa, “Idan bakiyi aure ba, haka zaki dawwama Zahrah?” wata zuciyarta tayi mata wannan tambayar. hawayene suka shiga gudu akan fuskarta, lalllai akwai babban ƙalubale a gabanta.

Zaune yake akan derny table ɗin dake tangamemen falon Hajiyar tasa, plate ɗin abinci ne aje a gabansa, yayinda yake juya spoon ɗin dake cikin abincin dake gaban nasa a hankali, kusan mintuna 10 kenan da kawo masa abincin, amma yakasa koda kai loma ɗaya ne na abincin bakinsa, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya garesa.

Cike da tuhuma Hajiya da tun ɗazu take kallon sa tace

“Wai meke damunka ne Sadeeq? gaba ɗaya yanayinka ya sauya, kowa yaganka yasan cewa kana cikin damuwa? gashi nace kaje gidan su Saleema, amma kayi banza da maganan bakaje ba har yau”

Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga mahaifiyar tasa.

“Inada damuwa Hajiya!” yafaɗi hakan cikin sanyin murya.

“Subahanallah! damuwa kuma Sadeeq, damuwar me?” Hajiya ta tambaya cike da kulawa, Allah yasani tana matuƙar son ɗan nata.

“Nasamu wacce nake so ne Hajiya!” Sadeeq yafaɗa cikin ɗar ɗar, don baisan ya Hajiyar tasa zata ɗauki al’amarin ba.

“Kasamu wacce kake so? wani irin magana ne wannan, wato so kakeyi kamai dani ƙaramar mace ko, to wallahi baka isaba, bazai taɓa yiwuwa ba, nariga dana gama magana da iyayen Saleema, har ƙanin mahaifinka yashigo cikin lamarin, saboda haka wannan batun kama dainasa tun kafun ranka yakai ƙololuwa wajen ɓaci, banason shirme!” Hajiya tafaɗi maganar a fusace, haɗe da tashi tabar masa falon.

Tabbas dama yasani ko da Zahrah ta amincewa aurensa, to balalle ne Hajiyarsa ta amince masa ba, amma yasan cewa yanamawa Zahrah so mai tsanani, kuma insha Allah, zai aure ta ya rayu da’ita har zuwa ƙarshen rayuwarsa, domin yaji hakan a jikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *