SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 9 BY FATYMA SARDAUNA
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kafun mintuna kaɗan dandazon mutane sun cika kan babban titin da hatsarin yafaru, kowa salati kawai yakeyi domin kuwa duk wanda yaga yanda motar Zaid tayi ƙwatsa ƙwatsa bazai taɓa tunanin mutumin dake ciki zai fito a raye ba, gaba ɗaya mutane carko carko sukayi kowa tsoron zuwa wajen motar yake gudun kada wuta ta tashi dashi, domin kuwa har motar tafara tashin hayaƙi, wasu daga cikin mutanen da suka taru a wajenne suka taimaka suka ƙarasa wajen motar, da ƙyar suka iya zaluƙo Zaid wanda gaba ɗaya fuskarsa ta ɓaci da jini duk jikinsa jini ne, kallon gawa kawai mutanen da suka ciro sa suka shiga yi masa, domin kuwa a yanda suka gansa babu alamar rai ajikinsa, babu kuma alamar cewa zuwa nan gaba zai iya
farfaɗowa, sai dai kuma ba’aja da ikon mai sama (ALLAH) Dai dai lokacin motar ƴan sanda suka ƙaraso wajen, kai tsaye su suka ɗauki Zaid suka sanyasa acikin motarsu, direct aka wuce asibiti dashi, duk da suma dai basu da tabbacin cewa yana da rai ko bai da shi….+
Emergency aka karɓi Zaid yayinda likitoti suka shiga basa taimakon gagawa domin kuwa sun gano cewa akwai rai ajikinsa, kawai de yayi mummunar buguwa ne….. Saida suka share masa jinin dake kan fuskarsa kafun Dr.Bilal ya iya shaida fuskar Zaid ɗin, take hankalinsa yaƙara tashi, tsananin tausayin Zaid ɗin ya kamasa, shin wani irin hali Alhaji Ma’aruf zai tsinci kansa idan yaji wannan mummunar labarin?,,,, haka dai sukayi iyaka ƙoƙarinsu wajen shawo kan al’amarin sai de kuma duk yanda suka so yadawo hayyacinsa abun yaci tura, abu ɗaya suka dogara dashi, idan har baidawo hayyacinsa nan da 3 days ba, to fa lallai akwai matsala…. Kallon sauran abokan aikinsa Dr.Bilal yayi haɗe da soma cire safar hanunsa, ganin haka yasanya suma suka cire nasu safan, daga nan suka fice daga cikin ɗakin…
Kallon sauran Doctor’s ɗin Dr.Bilal yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya. “Mubashi nanda 24 hour maybe zai yi farfaɗowa, sai de kuma Allah yasa buguwan da yayi bai taɓa masa lafiyan kansa ba”
“Insha Allah kansa bazai samu wata matsala ba, sai de kuma yakamata a nemi ahalinsa a sanar musu” Wani Dr. yafaɗi haka..
“Insha Allah” Dr.Bilal yafaɗi haka ga abokan aikin sa, bayan ya soma laluɓan Numbern Dad ɗin Zaid….
Alhaji Ma’aruf ne zaune a cikin katafaren falonsa wanda yagaji da haɗuwa, gefe dashi Hajiya Sajida ce tazuba tagumi daganinta kasan cewa tana cikin damuwa… “Menene abun ɗaga hankali har haka Hajiya? kinfasan Zaid ba yaro bane shi, kuma faɗuwar gaban nan da kikeji nima inajinsa, sai de kuma…..” Maganar Alhaji Ma’aruf ne ya katse sakamakon wayarsa da ta soma ruri alaman shigowan ƙira,,, mamakine ya bayyana akan fuskar Alhaji Ma’aruf ganin cewa Dr.Bilal ne ke ƙiransa,, bayan sun gaisane Dr.Bilal yayi gyaran murya haɗe da cewa Alhaji Ma’aruf ɗin yana buƙatar ganinsa,,, murmushi Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da cewa “Kakuwa ci sa’a ina gida, sai de ka hanzarta zuwa saboda zuwa ɗan anjima zan fita”
Ajiyar zuciya Dr.Bilal ya sauƙe haɗe da cewa “Kayi haƙuri Alhaji amma maganar bata gida bace, Magana ce me matuƙar mahimmanci kuma yana da kyau kazo ɗin”
Cikin ɗaurewar kai Dad yace da Dr.Bilal gashinan zuwa..
Kallon Alhaji Ma’aruf Mom tayi haɗe da cewa “Wayene, kuma me yake faruwa?” atake Mom taje romawa Dad waƴan nan tambayoyin..
STORY CONTINUES BELOW
“Bansan meye bane, amma idan naje zanji koma menene, Allah yasa dai ba matsalan Zaid bane” Alhaji Ma’aruf yafaɗi haka yana me nufar hanyar fita daga cikin falon nasa..
Da “Ameen” kawai Mom ta amsa masa domin kuwa tun ɗazu takejin faɗuwar gaba, kuma duk taji jikinta yayi sanyi..
Cikin mintuna ƙalilan Dad ya iso asibitin, kallo ɗaya yayimawa fuskar Dr.Bilal ya fuskanci cewa akwae damuwa…
Bayan sun zaunane Dad yakai dubansa ga Dr.Bilal wanda yarasa ta’inama zaifara sanar da Dad ɗin abundake faruwa…
“Inajinka Bilal kaƙirani ƙira na gaggawa sai gashi nazo kuma kayi shiru”
Ajiyar zuciya Dr.Bilal yayi haɗe da gyara zamansa “Bansan ya zaka ɗauki zancen bane Alhaji, amma kuma kasan me rai baya rabuwa da ƙaddarorin rayuwa….”
“Bangane inda maganan ka ta dosa bafa Bilal, inaga zai fi kyau kamin yanda zanfahimta” Dad yafaɗi haka ta hanyar katse Dr.Bilal daga maganan da ya keyi..
Ɗan numfasawa Dr.Bilal yayi haɗe da soma cewa.
“Wato Alhj kamar dai yanda na faɗa ma, ko wani bawa da irin tasa ƙaddaran, dakuma irin yanda take zuwar masa, bazan ɓoye maka ba Alhaji Ma’aruf, ɗazu aka kawo mana Zaid yasamu haɗari, yanzu haka yana accident & emergency munyi iyaka ƙoƙarinmu sai dai haryanzu bai farfaɗo ba, amma insha Allah muna sa ran farfaɗowarsa nan bada jimawa ba”
Tuni Alhj Ma’aruf yacire hula’r dake kansa, salati kawai yakeyi, iya ƙololuwan tashin hankali ya shigesa….. “Ɗana Zaid fa kace Bilal, ɗazu ɗazu fa muka rabu dashi, amma kaduba fuskar da kyau kuwa?” Dad yatambayi Dr.Bilal cike da tashin hankali.
“Ƙwarai Alhj, amma ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai dai dai ta, muje ka gansa domin kuwa zuwa anjima babu wani wanda zamu bari yagansa, saboda yana da buƙatar hutu sosai”
Babu musu haka Dad yabi bayan Dr.Bilal har zuwa ɗakin da Zaid ke kwance tamkar gawa, yayinda aka ɗaure gaba ɗaya kansa da bandage, sannan kuma an saƙalla masa wasu irin na’urori ajikinsa..
Hawayene suka cika idanun Alhj Ma’aruf alokacin da idanunsa sukai masa tozali da Zaid kwance kamar gawa,, “wannan wace irin jarabawa ce Zaid ya haɗu dashi, daga wannan sai wannan?” Alhj Ma’aruf yayi mawa kansa tambayar da baida wani me amsa masa ita…. Ganin da Dr.Bilal yayi cewa hankalin Alhj Ma’aruf yatashi sosai, yasanya ya jasa cikin office ɗinsa yashiga ƙarfafa masa guiwa akan cewa insha Allah nanda gobe Zaid ɗin zai iya farfaɗowa, suna kuma sa ran cewa idan ya farfaɗo bazai tashi da wani matsala ba sai de ɗan abun da baza’a rasa ba… Shi dai Alhj Ma’aruf jin Dr.Bilal kawai yakeyi, amma badon yana fahimtar abun da yake faɗa ba, a yanda yaga Zaid kamar gawa shiyafi komai ɗaga masa hankali, yanzu tayaya ma zaije ya fuskanci Hajiya Sajida da wannan magana ?……
Lokacin da labarin hatsarin da Zaid yayi ya’isa cikin kunnen Hajiya Sajida da labisat baƙaramin tashin hankali suka shiga ba, haka su kazo asibitin damuwa bayyane akan fuskarsu, da ƙyar Dad ya iya rarrashin su, amma duk da haka basu daina kuka ba….
****
Duka hannayenta ta ɗaura akan ƙuncinta, kallo ɗaya zakai mata kafuskanci cewa tana cikin damuwa, saboda lokaci ɗaya rama ta bayyana kanta ajikinta, ita kanta batasan meke damunta ba, sai dai tasan cewa zuciyarta tana ɗauke da damuwa me tarin yawa, takan tsinci kanta cikin wani irin hali idan tatuno da cewa aurenta da Dr.Sadeeq saura ƴan kwanaki ne suka rage, haka kuma takanjin matsanancin faɗuwar gaba aduk sanda Zaid yafaɗo cikin ƙwanyanta…
Wayarta ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira yayinda sunan Dr.Sadeeq yasoma yawo akan screen ɗin wayar. Cikin sanyin jiki ta ɗaga wayan haɗe da karawa akan kunnenta, cikin muryarta me sanyi tayi masa sallama.
STORY CONTINUES BELOW
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata, tamkar yana a gabanta, “Kitaimaka ki fito ina ƙofar gida” Abun Dr.Sadeeq yafaɗa kenan..
Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da cewa “gani nan fitowa…”
Tana aje wayar ta fidda wani irin numfashi haɗe da cije laɓɓanta, sai da tayi kusan mintuna 5 a zaune kafun ta miƙe tsaye haɗi da ɗauko wani mayafi ta sanya ajikinta….. Kaitsaye hanyar fita daga cikin gidannasu ta nufa…
Kanta duƙe a ƙasa haka take tafiya, harta ƙaraso wajen da motarsa ke fake….. Hanu tasanya ta ƙwanƙwasa glass ɗin window’n motar kasancewar yana cikin motar baifito ba. Ahankali ya sauƙe glass ɗin windo’n ƙasa, haɗe da sakar mata murmushi,, itama murmushin tayi masa haɗi da buɗe murfin motar tashiga bakinta ɗauke da sallama..
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa sallama’n nata, haɗe da kafeta da idanunsa, tun fitowarta agida yake kallonta, sosai kuma ya hango damuwa atattare da’ita.
“Nayi zaton bazaki fito ba kinyi fushi dani” yafaɗi haka still manyan eyes ɗinsa na kanta…
Murmushinta me kyau tayi masa haɗi da ɗan satan kallonsa, sosai yau ɗin yayi mata kyau, gashi fuskarsa taƙara haske sannan sajensa ya sha gyara,
” shima dai gaskiya kyakkyawa ne” tafaɗi haka acikin zuciyarta….
“Mezai sa nayi fushi dakai? nasan cewa hidima ne yayi maka yawa, kuma ae bani kaɗai bace, itama kuma waccar ɗin tana buƙatar kulawa daga gareka, kaga kenan bakayi laifin da zai sanya nayi fushi dakai ba” tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta…
Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da sake maida hankali da kuma idanunsa a kanta,, tabbas wannan abun da Zahrah keyi kishine, “to idan dai hartana kishinsa kenan tana son sa kamar yanda yake sonta?” tambayar da baiyi da amsarta, bazai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah batayi masa so me tsanani kamar yanda shi yake mata, amma kuma hakan bazai zamo wani babban abun damuwa a garesa ba, saboda yasani da yardan Allah watarana zata sosa zakumayi tayi masa SON SO…
“Ya aiki?” Zahrah ta faɗi haka ta hanyar katse masa tunanin dayakeyi gashi kuma yasanyata agaba sai kallonta yake kamar yasamu hoto..
Ajiyar zuciya ya sauƙe….. “Aiki babu sauƙi Princess yanzuma cancel ɗin wani aiki nayi nazo, saboda inaga yakamata ace nasan duk wani tsare tsaren da zakiyi, kingafa lokaci yana ƙara matsowa, banaso ayi komai a ƙurarren lokaci”
Murmushi kawai tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, cikin murya me sanyi tace “aini ba wani tsare tsaren da zanyi”
“Meyasa?” yatambayeta ataƙaice.
“Kawai”
itama tabashi amsa ataƙaice, domin ita har ga Allah bata da niyar yin ko wani irin program’s ne, ko walima batasa aranta cewa zatayi ba.
“Shikenan to, amma dai nikam zan shirya mana diner, saboda haka ki shirya, zankuma samu Husnah muyi magana da’ita akan yanda tsare tsaren bikin zai kasance sbd na lura kamar ke bason auren nan kike ba”
Saurin ɗago da kanta tayi ta kalleshi, giransa ɗaya yaɗaga mata yana murmushi..
Turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi haɗe da cewa “Nifa bance banason auren nan ba, kawai de banshiryawa program’s ɗin bane!” taƙare maganar cike da shagwaɓa …
Kallonta yashigayi na tsawon wasu mintuna kafun yayi murmushi….
“Meke damunki ne kwana biyu, ko baki da lafiya ne?” ya jefo mata tambayar da bata tsammata ba.
Kallon kanta tashigayi domin tambayartasa ta bata mamaki sosai, “me ka gani?” ta tambaya cike da tsarguwa.
“Naga kin rame ne, ko ba kya cin abinci ne? Ya kuma tambaya cike da kulawa.
Ɗan murmushi tayi haɗe da cewa “inaci”
“To ko dai aure kikeso ne?” yakuma tambayarta.
Saurin ɗago da kanta tayi takallesa saikuma tayi saurin maida kanta tsakan kanun cinyoyinta, wannan magana tasa da matuƙar sanya mutum jin kunya take..
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi yayi har saida haƙwaransa suka bayyana, dama yafaɗi hakane don yaga kunyarta to gashinan yagani cikin sauƙi…
“Kunyan me kikeji, dan natambaya ko aure kike so? ae dai naga kamar kin matsu da a ɗaura aurenne” wannan karon cike da zolaya yaƙare maganar..
Murmushi Zahrah tayi haɗe da sake cusa kanta a tsakankanun cinyoyinta, shi dai halinsa ne sanya mutum yaji kunya…
“Ya zamuyi da maganar ɗinkin kine?” yafaɗi haka don son kawar da wancan zancen..
Sai alokacin Zahrah ta’iya ɗago kanta, sai dai kuma bata iya kallonsa ba.
Wani ɗan abu dake manne acikin motar kamar drower yajawo haɗe da ciro wani babban envelop dake aje ciki…
“Kiyi manage da wannan kafun nasake dawowa” yafaɗi haka yana me ɗaura mata envelop ɗin akan cinyarta… Kallon mamaki tashiga yi masa saboda bata fahimci menene acikin envelop ɗin ba. Kansa ya jinjina haɗe da sakar mata murmushi,, ta buɗe baki zatayi magana kenan yayi saurin sanya hanunsa akan laɓɓansa haɗe da cewa “Shiiiii banson kice komai, kije gida zamuyi waya, kinji my beutiful Wife!” yaƙare maganar yana me kashe mata idanunsa ɗaya.
Murmushi kawai tayi masa haɗe da buɗe murfin motar tafice bayan ta riƙe envelop ɗin a hanunta,, yana ganin shigewarta gida shima yaja motarsa yabar ƙofar gidan nasu..
Ajiyar zuciya Zahrah tasauƙe sakamakon ganin irin maƙudan kuɗaɗen da Dr.Sadeeq ya bata,, wayarta tajawo haɗe da dannawa number’n Husnah ƙira, bugu ɗaya Husnah taɗauki wayar haɗe da cewa “Bride”
Murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa “ina buƙatar ganinki Husnah”
“Okay wannan ae ba’abun damuwa bane, bani nan da 30 minute inazuwa”
Cike da jin daɗi Zahrah ta kashe wayan, taji daɗi da Husnah tace gatanan zuwa, domin tabbas tana buƙatar taimakon Husnah.
Kamar yanda Husnah ta faɗa kuwa bawani ɓata lokaci ta iso gidan su Zahrah, Kuɗin da Dr.Sadeeq yabata ta miƙo mawa Husnah,, murmushi Husnah tayi bayan ta gama ƙirga duka kuɗaɗen, domin dai ita dama ƙirga kuɗi baya wani bata wahala, “200,000” Husnah tafaɗa tana kallon Zahrah.
Murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa ” Gaskiya ƙawata kin iya ƙirga kuɗi sharp-sharp saikace wata ma’aikaciyar banki!” cike da zolaya ta ƙare maganar,,, dariya suka sanya su duka biyu…
“Yanzu dai kamata yayi mufara ƴan shirye shiryen da zamuyi, kuma kinga yakamata ace tun yanzu kinfara gyaran jiki” Husnah tafaɗi haka.
“Gyaran jiki kuma Husnah ? to ae ni banga wani aebu ba ajikina da zan gyara” Zahrah tafaɗi haka tana me ƙarewa fatar jikinta kallo..
“Ae basai kinga wani aibu ajikinkiba zaki gyara Zahrah, ke dai yanzu tashi zakiyi muje gidan Auntie Amina takaimu wajen wannan me gyaran amaryan, kinsan tace mana 100,000 ne kuɗin aikinta, so kuma gashi yanzu munsamu kinga babu amfanin yin jinkiri, tashi maza muje” Husnah tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye.
Zahrah ma miƙewa tayi haɗe da janyo mayafinta ta yafa…. Sai da suka fita har bakin titi kafun suka samu taxi suka shiga direct gidan Aunti Amina (ƙanwar Maman Husnah) suka nufa, suna zuwa kuwa Auntie Amina tasa babbar ƴarta Suhaima wanda suke sa’anni da Husnah tayi musu rakiya zuwa gidan Hajiya Shuwa wanda itace me gyaran amarya, Hajiya Shuwa dai ƙwararriyar megyaran jiki ne, sosai take gayara mace daga uwar gida har amarya, sosai ta shahara a wannan ɓangaren ta iya gyaran jiki, sannan kuma ingantattun magunguna take haɗawa wanda idan kikasha saikin bada labari, Husnah ce taja Hajiya Shuwa gefe tace tayi mawa Zahrah gyara me kyau sbd ƙaddara yasa tarasa budurcinta, aikuwa babu cutarwa Hajiya Shuwa tace zata gyarata sosai da sosai, duk da abune wanda bazai taɓa yiwuwaba ace tadawo virgin, amma zatayi iyaka ƙoƙarinta taga ta haɗeta ciki da waje…. Hajiya Shuwa ta yankawa Zahrah rana cewa sati uku zasuyi suna gyarata, daga randa aka fara gyarata kuwa to fa fita ya ƙare mata sai dai idan da dare, domin ba’aso rana yataɓa ta… Haka suka baro gidan Hajiya Shuwa, daga nan Shoprite Husnah taja Zahrah suka nufa, 100k ɗin da yayi saura Husnah ta ɗauki 50k aciki ta jidawa Zahrah english wears masu kyau da nuna tsiraici, hatta kayan bacci sai da Husnah ta zaɓawa Zahrah, nagani na faɗa irin wanda ake ƙira dashi gwamma babu,, ita dai Zahrah kallon Husnah kawai take, amma takasa cewa komai, haka suka gama ƴan sayayyansu suka koma gida, sai da akayi sallan Magrib kafun Husnah tayiwa Zahrah sallama tatafi gida…….
STORY CONTINUES BELOW
*****
Ƙarfe 3 na yammacin yau kenan amma har yanzu Zaid bai farfaɗo ba, tun da safe ake sa ran farfaɗowarsa amma shiru har zuwa yanzu, gaba ɗaya hankalin Mom atashe yake, gani takeyi tamkar Zaid ɗin ya mutu ne, domin kuwa tun safe take tacewa abarsu su gansa, amma sam likitotin nan sun hanata ganinsa, saboda ba a buƙatar kowa yaje kusa dashi, sai dai idan harshi yafarfaɗo yabuƙaci hakan….
*****
Abu kamar wasa yau kwanan Zaid biyu acikin asibitin amma koda ɗan yatsarsa ne bai motsaba, wannan ne yaƙara jefa ƴan uwansa cikin tashin hankali, bama kamar Alhaji Ma’aruf domin kuwa Dr.Bilal yasanar masa cewa Zaid yakamu da wata irin ciwon zuciya me tsanani, wanda idan har ba’akiyaye ba to tabbas rayuwarsa tana cikin hatsari…
Sama sama yake fitar da numfashi ta bakinsa, yayinda ya soma buɗe manya manyan idanunsa a hankali. gaba ɗaya abun da yafaru dashi yadawo masa cikin kansa, saurin ɗago hanunsa yayi yashafi kansa wanda gaba ɗaya aka ɗaure masa shi da bandage,, dai dai lokacin Dr.Bilal yashigo cikin ɗakin,,, fari’a ne ya faɗaɗa akan fuskar Dr.Bilal sakamakon ganin da yayi Zaid yafarfaɗo…..”Alhmdlh sannu yajikin naka?” Dr.Bilal yatambayi Zaid daya kafesa da’idanu.
Bai iya amsa masa ba, sai kansa kawai daya ƙaɗa, lokaci guda kuma yasoma yunƙurin tashi zaune, “Auuushhhhh!” Zaid yafaɗi haka da ƙarfi yana mesanya hanunsa akan ƙafarsa na dama da take masa wani irin raɗaɗi..
“Sannu, kwanta ae basai ka tashiba akwai rauni sosai ajikin ka, musamman ma aƙafarka, saboda haka ka kwanta kawai” Dr.Bilal yafaɗi haka bayan ya ɗaga ƙafar Zaid ɗin na dama ya maida ita gefe saboda akwai ciwuka sosai ajikinta, ko kyakkyawan motsi ba’aso tayi, saboda ciwukan zasuji kamar ana ƙaiƙayasune…
Dr.Bilal yana fita bai jima ba saigasu Alhaji Ma’aruf da Mom sun faɗo cikin ɗakin,,, Mom na ganin Zaid ta fashe da kuka haɗe da ƙarasawa garesa ta kamo duka hannayensa,,, sannu kawai taketa aikin jero masa saikace wanda ya tafito a labour room.Lol…… Da kai kawai yake iya amsa musu sannun da suke yi masa,,, Dr.Bilal ne yakuma shigowa cikin ɗakin. hanunsa ɗauke da wasu magunguna haɗe da allurai… Kallon Mom yayi haɗi da cewa “Hajiya inaga yakamata ace anhaɗa masa ko tea ne saboda akwai allurai da magungunan daya kamata ace yasha, zakuma su iyayi masa illa idan har baici abinci ba,,, jikin Mom harrawa yake tace “Akwai ma abinci likita ae sainabashi yaci ko”
“A’a Hajiya tea yakamata ace yasha idan yaso daga baya saiyaci abincin” kafun ma Dr.Bilal yaƙare maganar Mom tanufi wani ɗaki da aka basu, wanda anan ma suka kwana, kuma dama akwai kayan haɗa tea wanda Labisat ta ɗauko musu a gida sukayi breakfast,,, mintuna kaɗan Mom tahaɗowa Zaid tea me kauri, da taimakon Dad Zaid yatashi ya zauna,, Mom dakanta take bashi tea ɗin saboda tsabar soyayya, shikuwa sai wani jan aji yake, idan takawo cup ɗin bakinsa sai yaɗan ɓata lokaci kafun yake buɗe baki yasha…. Ko rabin cup ɗin baishaba yakawar da kansa gefe alaman ya ƙoshi…
Duk yanda suka so yasha tea ɗin sosai hakan ya gagara, Zaid yana da taurin kan tsiya, idan baiso abuba babu wanda ya’isa sanyasa yayi dole.. Allurai guda biyu Dr.Bilal yayi masa, haɗe da basa magunguna masu kashe raɗaɗi da zafin ciwo…. Jin gina bayansa yayi da jikin pillow haɗe da lumshe idanunsa,, imagine fuskar Zahrah kawai yakeyi acikin idanunsa, kowani bugu ɗaya na zuciyarsa tare da soyayyarta yake tafiya, soyayyar Zahrah yazame masa rayuwa da numfashinsa, soyayyar Zahrah yazame masa jini acikin jikinsa, sai dai kuma baisan meyasa duk kwanan duniya Zahrah take ƙarayi masa nisa ba…
Labisat dake zaune a gefensa taɗan saci kallonsa, akaro na barkatai, tabbas ta fuskanci cewa yayanta yana cikin tarin damuwa, wanda damuwar ita ke haddasa masa faɗawa cikin matsala, amma kuma a iya zurfin hankali da tunanin ta tagano cewa SOYAYYA ita kaɗaice damuwar da take ɗaiɗaita nutsuwar ɗan adam alokaci guda, itace abu mafi saurin ruguza rayuwar ɗan adam, SOYAYYA bata da daɗi ko kaɗan, domin kuwa itama Soyayya ta ɗaiɗaita mata rayuwa batare da ƴan uwanta sun sani ba, har yau abun na ranta, takuma bunnesa acikin zuciyarta, sai dai kuma tana tsoron ranarda asirinta zai tonu, batasan wani kallo iyayenta zasu mata ba…
“Labisat!” Zaid yaƙira sunanta.
Saurin dawowa daga duniyar tunanin da take tayi haɗe da amsa ƙiran da yayi mata.
“Ina wayana?”
Idanu Labisat tashiga warewa ko zata hango wayartasa acikin ɗakin amma bataga ko alamar taba..
“Bro bangantaba sai dai idan su Dad suka dawo saina tambayesu ko…….”
“Enough” Zaid yafaɗa ataƙaice bayan yaɗaga mata hannu.. saboda yasanta yanzu saita cika masa kunne da cakwaikwaiwa.
Gum Labisat tayi da bakinta, haɗe da komawa mazauninta ta zauna, azuciyarta kuwa cewa take “Jarabansa baya taɓa ƙarewa yana a halin rashin lafiya ma amma baifasa gwada halin nasa ba”……..
*******
“Gaskiya Doctor yana ƙoƙari sosai Zahrah, kinga yanzufa yakuma turo dubu ɗari da hamsin a account ɗina, kuma kinsan shekaran jiya yaturo dubu ɗari wai kuɗin lalle, nidai nagama gane Doctor ɗin kinnan so kawai yake yajiki a hanunsa”
Murmushi Husnah tayi haɗe da cewa “Nima narasa yazanyi dashi Husnah two days ɗinnan yana min ɓarin kuɗi, idan nayi masa magana kuma sai yace wai amarya dole saida kuɗi”
“Ae kumafa gaskia yafaɗa, kinga dole sai akwai money abubuwa zasufi zama mana dai dai, yanzu kinga gobe nefa za’afara miki gyara yakamata mu kammala abubuwan mu tun ayau..” Husnah tafaɗi haka tana me yafa mayafi ajikinta. Zahrah batakai ga bata amsa ba Momyn Husnah tashigo hanunta ɗauke da wani ƙaton baƙin leda.
“Yanaga duk kunyi carko carko badai harkun gama hutawan ba?” Momyn Husnah ta tambaya, domin dama daga wajen me ɗinki suke shine suka biyo ta gidan su Husnah akan zasu ɗan huta..
“Eh Momy wlhy kinga yanzu Doctor yaturo mana da kuɗi Banki zamuje mu cire” Husnah tafaɗi haka ga mamanta.
“Ummm zancenki dai baya wuce na kuɗi ako da yaushe, wato shine Zahrah kika biyewa wannan mai idon kuɗin kuketa ƙwaƙule wa bawan Allah aljihun sa ko?”
Dariya Husnah da Zahrah suka sanya ƙwarai maganar Momy’n tabasu dariya.
“Momy wllhy ba haka bane, shine ma yake turowa ko tambayansa ma bamuyi ba” Zahrah tafaɗi haka tana murmushi..
Murmushi kawai Momy tayi haɗe da cewa “Aekuwa kun dai haɗu da ɗan arziƙi ne, amma angwayen yanzu ae basa ba da wani kuɗi me yawa,,, ungo wannan saikiyi maleji ko” Momy tafaɗi haka tana me miƙowa Zahrah ƙatuwar ledan dake riƙe a hanunta..
Idanu Zahrah ta waro ganin irin girman ledan amma kuma Momy tana cewa wai tayi maleji…
Husnah ce tayi saurin karɓan ledan haɗe da soma fito da kayan ciki, wasu tsala tsalan laces ne guda uku masu kyau da tsadar gaske, sai kuma wasu haɗaɗɗun kuloli masu kyau har guda uku, kuloline irin wanda suka amsa sunansu kula wanda gidan masu da akwai suke amfani dasu, dagani kai kasan kulolin sunja naira.. Daɗine yakama Zahrah har batasan sanda ta faɗa jikin Momy ta rungumeta ba, sai kuma ta saki kuka.
“Kuka kuma Zahrah? share hawayenki wannan ai ba wani abubane da zai sanyaki kuka ba, kamar ɗiyata Husnah haka na ɗaukeki, share hawayen kinji” Momy takare maganar cike da lallashi.. Godiya sosai Zahrah tayimawa Momy wanda bazai faɗuba, sosai kyautan momy’n yafaranta ranta domin kuwa kayane na alfarama daga kan laces ɗin har zuwa kan kulolin….
Momy nafita Zahrah ta rungume Husnah cike da jin daɗi..
Murmushi Husnah tayi haɗe da cewa “Ƙawata yanzu ba lokacin godia bane, dare zai mana idan bamuje bank ɗinnan ba” dariya Zahrah tasanya, domin ita wani lokacin Husnah daria take bata, komai yinsa take a gaggauce gaba ɗaya tafi kowa ƙosawa ayi auren…
Koda sukaje Bank basu wani shawahala ba suka cire kuɗin, daganan kuma gidan su Zahrah suka dawo,,,, suna dawowa suka samu Inna tamusu ɗan wake, aikuwa ba ɓata lokaci suka shiga loda mawa cikinsu. suna gamawa kuwa Zahrah tashiga haɗa abubuwan buƙatanta domin gobe da sassafe zata je gidan Hajiya Shuwa bakuma zata dawoba sai 7 na dare, haka ƙa’idan gyaran nasu yake sam ba’aso rana yana dukanka, saboda zafin rana zai iya ɓata gyaran da suka soma batare da sun kammala ba……….Tun adaren tagama haɗa gaba ki ɗaya abubuwan da zata buƙata. Kwanciya tayi lamo akan katifarta tana me sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, tun safe sai yanzu tasamu hutu, kai gaskia hada hadan aure babu sauƙi, ace mutum yazama busy saikace wani engine, itama mace kenan inga Dr.Sadeeq kuma, wanda haƙƙin raba kati da sauran abubuwa yake kansa…+
Ajiyar zuciya takuma sauƙewa akaro na barkatai, “ƙaddara kenan mai sauya al’amura da yawa, kana naka kuma Allah na nasa, koda amafarkine bata taɓa tunanin wai wani zai lalata mata rayuwa ya rabata da budurcinta ba, amma cikin ikon Allah saigashi haka ta kasance, lallai babu mai iya ja da’ikon Allah, idan yaturoma ƙaddara babu wanda ya’isa hana ta zuwa gareka, siraran hawayen da suka biyo takan ƙuncinta ta sanya hanu ta share haɗi da gyara kwanciyarta, tunani cike da zuciyarta haka bacci ɓarawo yayi awun gaba da’ita.
Asibiti….
Idanunsa ya tsaida ƙyam akan ceiling ɗin daya mamaye saman ɗakin, gaba ɗaya hankali da nutsuwarsa basa garesa, zuciyarsa tayi nisa akan soyayyarta ta yanda bayaji baya kuma gani, kamar dai yanda yayi nisa yanzu wajen tunaninta,, a hankali ya sauƙe idanunsa daga kan ceiling ɗin haɗe da dawo da kallonsa ga ƙafarsa na dama wacce take naɗe acikin bandage, sosai ƙafar takeyimasa raɗaɗi jiyake tamkar ana barbaɗamasa barkono aduk saƙo da lungu wanda ke ɗauke da ciwo, hakanan yake bakowani irin ciwo ne idan yaji zaiji zafinsa ba hartakai ga zafin ya hanasa sukuni, amma kuma saigashi zafin wannan ciwon yakan iya hanasa motsa ƙafarsa, amma kuma duk da wannan tsananin zafi da ciwon nasa keyi masa ko kwatan kwacin rabin zafin da yakeji azuciyarsa game da soyayyar Zahrah baikaiba, ada yaɗauka so ƙaryane, sai ayanzu yafuskanci cewa so gaskiya ne musamman ma irin nasa salon soyayya’r …. Lumshe idanunsa yayi haɗe da ɗan matse lips ɗinsa, idanunsa na ɗokin ganinta, yayinda kunnuwansa ke ɗokin jin muyarta, sai dai kuma yana acikin hali wanda bazai iya zuwa gareta ba,, haka yayita saƙawa da kuncewa shi kaɗai har bacci yayi gaba dashi.
Washe Gari……
Da sassafe Zahrah tayi wanka haɗe da shirya kanta cikin wani jan yadi me sauƙin kuɗi, amma kuma yayi mata kyau sosai ajikinta kasancewarta me farar fata,,, wani ɗan madai daicin mayafi wanda kalansa yakasance ja irin kalan kayan dake jikinta ta yafa, a ƙagauce tayi karyawanta, domin kuwa Hajiya Shuwa tace tazo da wuri, inda Allah yataimaketama sun samu hutu a makaranta da badon hakaba ma da batasan yanda zatayi ba…
Wayarta da ɗan ƙaramin hand bag ɗinta ta ɗauka haɗe dayiwa Inna sallama domin kuwa Baffa bayanan yatafi yola. Adawo lafiya Inna tayi mata, da “Ameen” ta amsa haɗe da sakai tafice daga cikin gidan..
Tafe take tana ɗan latsa wayarta number’n Husnah take ƙoƙarin ƙira don ta sanar mata cewa tanaso su haɗu agidan Hajiya Shuwa,,, batakai ga dialing number’n Husnah’n ba wata baƙar mota ta faka adai dai gabanta, da sauri taɗago idanunta takai dubanta ga motar haɗe da ɗan matsawa baya, take zuciyarta tashiga yi mata lugude..
Buɗe murfin motar yayi yafito fuskarsa ɗauke da murmushi..
STORY CONTINUES BELOW
Baki sake Zahrah take kallonsa cike da mamaki…
“Auntyna!” kyakkyawan saurayinnan daya fito daga cikin mota yafaɗi haka ga Zahrah yana murmushi..
Kallon tuhuma Zahrah tashiga yi masa haɗe da ɗan sake ja baya dashi, batasanshiba bata kuma san waye shiba, amma kuma lokaci ɗaya ta shiga yimawa fuskarsa kallon sani kamar akwai wani wanda tasani wanda wannan ɗin kekama dashi.
“Uhh sorry my kyakkyawar auntie, na tsorataki ko? kiyi haƙuri nafiso inyi miki surprise ne, shiasa na hana bro yasanar dake zuwana” yaƙare maganar still yana murmushi ..
“Waye kai?” Zahrah ta tambayeshi cikin ɗar ɗar.
“Sunana Samad” saurayinnan yafaɗi haka yana me bayyana murmushi akan fuskarsa, da’alama dai shi mutum ne me yawan fari’a.
Kallonsa tashigayi domin taɗan gano wani abu atattare dashi, tun bata kai ga cewa komai ba wayarta tasoma ƙara alaman shigowar ƙira, kallonta ta maida kan wayarta ta, ganin sunan Dr.Sadeeq na yawo akan screen ɗin wayar yasanyata ɗaga wayar haɗe da ɗan sake matsawa gefe.
“Brother na yazo wajenki kuwa?” abun da Dr.Sadeeq yatambaya kenan bayan ya amasa sallaman da tayi masa.
Kallonta tamayar ga Samad dake tsaye, tabbas sai yanzu tagano kamannin watake gani akan fuskar saurayin..
“Eh bansaniba ko shine a tsaye a gabana yanzu, amma wannan yacemin sunansa Samad” Zahrah tafaɗa cikin ƙasa ƙasa da murya, domin batason wancan ɗin yaji..
“Yauwa shine, please my dear kishiga yakaiki gidan gyaran jiki’n kinji, ni zanzo na ɗaukoki idan kuka gama, daga yanzu harzuwa bayan aurenmu banaso kina shiga motocin haya” Dr.Sadeeq yafaɗi haka ga Zahrah cike da kulawa.
Mamakine yakama Zahrah sosai domin ita sam bata faɗa masa ma zata fara zuwa gyaran jiki ba, to a ina yasamu labari?” tambayar da bata da amsarta,, jin da tayi alamar cewa yakashe wayartasa ne yasanya itama tacire tata wayar daga kan kunnenta… Murmushi tasakarmawa Samad haɗe da ƙarasowa garesa..
“Matsoraciya da kin ɗauka saceki zanyi ko?” Samad yatambaya cike da tsokana.
Dariya taɗanyi me sauti haɗe da cewa “sosaima kuwa”
Dakansa ya zagayo ya buɗe mata murfin motar yana me cewa “Ashe dai Bro matsoraciya yasamomana”
Dariya sukayi dukansu,, zama tayi acikin motar haɗe da ɗaura hand bag ɗinta akan cinyarta,, zagayawa wajen zaman driver Samad yayi haɗe da kunna motar suka hau titi..
A hankali Samad ke tuƙa motar yayinda yake ta yiwa Zahrah hira, mintuna kaɗan Zahrah ta sake dashi suka soma hira, saboda tafahimci cewa shi ba irin mutanen nan bane masu zafin rai, ya nada sauƙi tamkar yayansa gashi fuskarsa bata rabo da murmushi, sai dai kuma fa Dr.Sadeeq yafisa kyau duk da kuwa cewa suna kama, kuma shi ɗinma balaifi yana da nasa kyau’n..
A ƙofar gidan Hajiya Shuwa Samad ya faka motar haɗe da kallon Zahrah cikin sigar tsokana yace “Yauwa Malama nakawoki sai ki bani kuɗi na ko”
Dariya Zahrah tayi harsaida haƙwaranta suka bayyana.
” Kabini bashi yanzu banda kuɗi” tafaɗi haka tana me ƙoƙarin buɗe murfin motar.
“To shikenan inabinki bashi” Samad yafaɗi haka yana ɗan dariya. Itama dariyan tayi kana tafice daga cikin motar. Murmushi kawai Samad yayi haɗe dayin reverse ya cilla motarsa kan titi.
Zahrah kuwa tana shiga gidan ta iske Hajiya Shuwa zaune a falo tana karyawa, gaisawa sukayi da Hajiyan kana takoma gefe ta zauna… Hajiya Shuwa kuwa tana kammala yin breakfast, ta dafa wani ruwan wanka wanda yasha turaren ƙamshi na jiki haɗe da wasu surrukan ƙamshi na mussaman, ceda Zahrah Hajiya Shuwa tayi, tashiga cikin ruwan ta kwanta dayake acikin bathtub ta haɗa ruwan wankan, babu musu Zahrah tacire kayanta haɗe da shiga cikin bathtub ɗin ta kwanta luf,, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai domin kuwa ƙamshin haɗaɗɗen turaren da’aka sanya acikin ruwan shikaɗai ya’isa yasanya maka nutsuwar zuciya.. Saida Zahrah tayi 30 minute acikin wannan ruwan, kafun Hajiya Shuwa tabata izinin fitowa, wani ruwan wankan kuma aka haɗa mata takumayi, tana fitowa kuwa Hajiya shuwa tasoma mulke mata jiki da wani haɗaɗɗiyar dilka me kyau wanda take ɗauke da wasu irin sinadarai masu gyara jiki dasanya ƙarin laushin fata… Gaba ɗaya dai wunin yau Zahrah tayishine ba kaya daga ida sai wani ɗan towel domin kuwa wannan na bushewa tana wankewa za’ace takuma shafa wancan, wasu irin haɗin magunguna masu kyau Hajiya Shuwa ta bata tasha wasu sunmata daɗi wasu kuwa bauri suka mata, amma yata iya tunda ita takawo kanta yazama dole ta jure…
STORY CONTINUES BELOW
A asibiti kuwa Zaid ne yakafe kai da fata akan cewa lallai shi sai ambasa sallama duk da kuwa cewa yanajin ciwo ajikinsa amma yakafe akan cewa shi bazai iya jure zaman asibiti’n ba.. Alhaji Ma’aruf ne yasamu Dr.Bilal akan maganar sallaman da Zaid ya buƙata……
Gyara zama Dr.Bilal yayi haɗe da maida kallonsa ga Alhaji Ma’aruf cikin sigar da Alhj Ma’aruf ɗin zai fahimta yasoma cewa…
“A gaskia zamansa anan ɗin zaifi akan komawarku gida, har yanzu akwai tarin ciwuka a jikinsa yana da buƙatar kulawarmu sosai, saboda haka inaga babu amfanin baku sallama kamar yanda ya buƙata, yakamata ne ace sainan da sati guda sannan zaku karɓi sallaman ku”
Ajiyar zuciya Dad ya sauƙe haɗi da cewa
“Shikenan badamuwa Doctor amma kuma yamaganan ciwon nasa babu wani magani da zaku ɗaurasa akai wanda zai sanya cutar tafita daga jikinsa kwata kwata?”
“Eh to akwai magunguna da dama, amma kuma dole shima sai yakiyaye saboda yawan shangiya dakuma tunanin da yakeyi sukaɗai sun isa sanya ciwon nasa yaƙara faɗaɗa, inafata kuma zaku guji shiga ɓacin ransa, saboda idan ransa ya ɓaci zuciyartasa zatana bugawa da sauri wanda hakan kuma zai iya kawo wata matsala ta daban” Dr.Bilal yaƙare maganar yana me ƙoƙarin cike wani file dake gabansa..
Ajiyar zuciya Alhj Ma’aruf yakuma sauƙewa akaro na barkatai,, cike da jimami yamiƙe daga zaunen da yake haɗe da miƙawa Dr.Bilal hanu suka kumayin musabaha,, har bakin fita office ɗin Dr.Bilal yaraka Alhj Ma’aruf daga nan sukayi sallama…
A hankali yake gutsuran green colour apple ɗin dake riƙe ahanunsa, zuwa yanzu bayajin daɗin komai, sannan duk abun dayaci baijin test ɗin abun acikin bakinsa, apple kaɗai yake iyaci sai kuma roasted fish, amma bayansu baya iya cin komai.. Idanu Mom tazura masa ƙwarai zuwa yanzu kam tagama karantar yanayinshi, damuwa ce kurum tayi masa yawa kuma bazata taɓa iya jurar ganin ɗanta acikin damuwa ba…
“Zaid” mum taƙira sunanshi cikin murya me taushi.
Kansa yaɗago ya kalli mahaifiyartasa batare da ya amsa ƙiran da tayi masa ba.
Matsowa kusa da shi tayi haɗe da kama hanunsa cike da kulawa tace
“Meke damunka ne Zaid? inaso yau kasanar dani duka damuwarka ni mahaifiyarkace Zaid baikamata ace ka ɓoyemin damuwarka ba”
Ajiyar zuciya Zaid ya sauƙe haɗe da sake kwantar da kansa ajikin pillow. “Inasonta Mum!” abun da Zaid ya’iya faɗa kenan cikin murya me rauni.
Ajiyar zuciya Mum ta sauƙe haɗe da kallon Zaid ɗin da kyau
“Nayi tunanin zuwa yanzu kamanta da maganar wannan yarinyar Zaid, ka daure zuciyarka ka nemi wata wanda ta dace dakai”
Kallon Mum ɗinnasa yayi da’idanunsa wanda suka sauya kala alokaci guda, shikaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa aduk sanda yaji wata kalma dake masa nuni da ya haƙura da Zahrah, duk wanda yace masa ya haƙura da Zahrah gani yake tamkar basonsa yake ba…
Wani irin murmushi me ciwo Zaid yayi haɗe da kama duka hannayen mahaifiyartasa yasanya acikin nasa hanun.
“Banajin zan’iya cigaba da zama babu ita akusa dani Mum, inasonta sosai, amma kuma ita tsanar da tayi mini haryafi soyayyar danakeyi mata yawa, ina buƙatar taimakon ki Mum!” gaba ɗaya muryarsa ta bayyana rauninsa,, take Mum taji zuciyarta ta karye yayinda tausayin ɗannata yasake dira acikin zuciyarta..
“Insha Allah zanyi iyaka ƙoƙarina Wajen ganin kasamu cikar burinka kaji Zaid, ka kwantar da hankalinka, banason damuwarka!” Mum tafaɗi haka cike da lallashi saikace wani ƙaramin yaro haka tashiga lallaɓa Zaid, Allah sarki uwa me daɗi sai gashi harya ɗanji sanyi acikin ransa……
****
Sai ƙarfe 7 na dare Zahrah tasamu kanta daga gyaran da takesha wajen Hajiya Shuwa, a ƙagauce tayi sallan isha haɗe da cin abincin da Hajiya Shuwa ta kawo mata domin kuwa tuni Dr.Sadeeq yayi mata waya akan cewa yana kofar gidan Hajiya Shuwa’n yana jiranta..
Ita kanta daɗi da nutsuwane suke sauƙar mata idan tashaƙi daddaɗan ƙamshin turaren da ke tashi ajikinta, inakuma ga wani na daban idan yaji…
STORY CONTINUES BELOW
Tafiya take cikin nutsuwa hartaƙaraso inda yake tsaye yajingina a jikin motarsa…
“Kayi haƙuri na shanya ka ko?” Zahrah tafaɗi haka tana me gyara zaman jakarta dake rataye akan faɗarta.
” Girmankine ae ƴan mata na” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me ƙoƙarin buɗe mata murfin motar. Kyakkyawan murmushi tasakar masa haɗe da shiga cikin motar ta zauna, zagayawa yayi shima yashiga haɗe da tada motar suka hau kan titi.
Saida sukayi nisa da tafiya kafun yadawo da kallonsa gareta …
“Da ruwan zinare aka wanke kine naga gaba ɗaya kin ƙara kyau sai walwali kike” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me binta da wani irin kallon shauƙi…
Dariya ne yaso ƙwacema Zahrah amma saita basar haɗe da ɗaga masa kai alamar “Eh”
Murmushi yayi kawai haɗi da jefa watermelon sweet acikin bakinsa.
Tafiya suke babu wanda yace da ɗan’uwansa ƙala harsuka iso ƙofar gidansu Zahrah…
Yana parking ɗin motar yadannawa kowacce ƙofar fita daga cikin motar lock. Saurin ɗago da kai Zahrah tayi ta kallesa , murmushi yasakar mata haɗi da kashe mata idanunsa ɗaya, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da marairaice fuska cike da shagwaɓa tace “Please bacci fa nakeji duk nagaji kabuɗemin na fita”
“Naƙi wayon, so nake mota ta ta gama ɗaukar daddaɗan ƙamshinki wanda yake shirin rabani da nutsuwata kafun saina buɗe miki”
Hanu tasanya ta toshe bakinta gudun kada sautin dariyar da takeyi ya fito.
“Au dariyama kikemin ko? to ae ba iya motata bace kaɗai nakeso taɗauki ƙamshin hardani kaina, saboda haka bana matso kusa dake sai nasamu wannan daddaɗan kamshin”
Da sauri Zahrah ta matsa gefe hartana manna jikinta da murfin motar…. “Please kazauna to a inda kake, ae nataho da turaren zan baka saika shafa” cikin zallan shagwaɓa tayi maganar..
Dariya Dr.Sadeeq yayi haɗe da girgiza kansa “Zahrah akwai tsoro, shi da wasa yake mata ma” yafaɗi haka acikin zuciyarsa.
Amma afili saiyace “A’a ni naƙi wayon najikinki nakeso”
Sake takurewa tayi haɗe da noƙe jikinta “Dan Allah Yaya Sadeeq kabari Allah zan tsammaka turaren saika shafa” gaba ɗaya tarikice kamar wanda yace zaiyi mata wani abun..
Dariya kawai yayi haɗe da cewa “Nifa wasa nake miki ƴan mata babu abun da zanmiki, kiyi bacci lafiya gobe ma Samad ne zaizo ya kaiki” yaƙare maganar yana me cire lock ɗin daya sanyawa ƙofofin motar, aikuwa da sauri tabuɗe murfin motar ta fice, hartana manta ƴar ƙaramar Hand Bag ɗinta. Ko wai wayoshi batayi ba tashige cikin gida da sauri… Dariyane yakamasa sosai, dubi yanda tafirgice masa alokaci ɗaya, lallai idan har haka take akwai aiki ja agabansa.
Da wannan tunanin yaɗauki hanyar komawa gida, bayan daddaɗan ƙamshin turarenta yagama kashemasa jiki yasanyashi jin wani irin shauƙi na musamman……
Zahrah kuwa tana shiga gida ta turo ƙofar gidan haɗi da sanyawa ƙofar sakata, direct ɗakin Inna ta wuce can ta sameta tana aikinta najin radio. Kwanciya tayi akan wata doguwar kujera dake ɗakin Inna’n, mintuna kaɗan baccin gajiya yayi gaba da’ita…….
Dr.Sadeeq ne kwance akan makeken gadonsa yayinda idanunsa ke kallon sama, amma azahirin gaskia idanunsa bawai sama suke nuna masa ba, kyakkyawar fuskar Zahrah kawai suke hango masa, ƙwarai matuƙa shi kam Allah yasani ko gobe da za’a ɗaura aurensa da Zahrah yanaso, saboda yana matuƙar buƙatarta akusa dashi, sosai yakejin abubuwa dayawa agame da’ita wanda baicika jinsu akan sauran mata ba, shidai yabarwa kansa cewa Zahrah ta musammance ko acikin ƙasaitattun mata kuwa samun kamarta sai an dage, hand bag ɗinta dake aje kan ɗan ƙaramin drower’n dake kusa da gadonsa ya jawo haɗi da kai hand bag ɗin kusa da hancinsa…. lumshe idanunsa yayi haɗe da sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, sosai ƙamshin yayi masa daɗi irin ƙamshin jikinta hand bag ɗinnata ma keyi, lallai shikam ƙamshin yayi masa daɗi sosai, baiƙi ace ma ya kwana yana shaƙan daddaɗan ƙamshin ba, haka dai yayita tunani kala kala yana riƙe da hand bag ɗinnata bacci ɓarawo yayi gaba dashi……
STORY CONTINUES BELOW
Zaid kuwa kwana yayi yana mafarkan Zahrah saidai kuma sam mafarkan basuyi masa daɗi ba, saboda acikin mafarkin sam babu alamar zata zamo tasa, saima gudunsa dayaga tanayi, duk da cewa yasan harzuwa yanzu Zahrah tana sonsa amma kuma baiga alamar cewa zata saurara masa ba, amma shi awajensa duk wannan ba abun damuwa bane matuƙar Zahrah zata amince ta auresa to shikuma zaiyi iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin yamantar da’ita tsanarsa da tayi dakuma tarin laifukan daya aikata a gareta…..
****
Ahankali tagama ware idanunta akan robber ceiling ɗin daya mamaye duka saman ɗakin na Inna,, wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe haɗi da rumtse idanunta,,, yau shine kwana na biyu kenan da Zaid yake zuwa mata acikin mafarkinta, sai dai kuma ba’ahalin daɗi yake zuwa mata ba, sosai take ganin damuwa ɗauke akan fuskarsa, amma kuma sam batasamun daman yi masa magana acikin mafarkin nata, duk da kuwa yanda take matuƙar son faɗa masa wani abu, amma dazaran tabuɗi bakinta zatai masa magana saitaji harshenta yayi mata nauyi takasa cewa dashi komai,,, wannan shine babban abun dake damunta, ita kanta batasan me takeson faɗa masa ba… Da ƙyar ta’iya tashi daga kan kujeran takoma nata ɗakin bayan taɗauro alwalan sallan asuba.. tana idar da sallah’n asuba ɗin ta ɗauko Al’QUR’ANI ta tasoma karantawa. Ba’ita ta idar da karatun ba sai ƙarfe 7 na safe, wanka tayi haɗe da shirya kanta cikin wani baƙar abaya, ita kanta tasan tayi kyau, gashi rana ɗaya kawai da soma gyaran jikin nata amma har fatarta ta murje tayi kyau… Yauma dai aƙofar gidansu ta’iske Samad yana jiranta,,, haka suka tafi suna hira gwanin ban sha’awa, Samad yana da saurin sabo daga jiya zuwa yau harsun saba sosai…. Yauma dai gangariyan gyara tasamu daga Hajiya Shuwa, ƙamshi kawai jikinta ke fitarwa….
Agurguje.
Bayan sati ɗaya….
Sosai Zahrah ta samu sanji ajikinta daga fara gyran jikin nata zuwa yanzu, wani irin walwali da sheƙi fatarta keyi gashi lokaci ɗaya taƙara haske komai nata yaƙara zama abun burgewa dakuma sha’awa,, sai dai yanzu kwata kwata bata da wadataccen lokaci saboda agidan Hajiya Shuwa take wuni, Husnah kuwa tuni ita da Doctor sun gama tsara duk wani tsare tsaren su, duk da Zahrah tace bazatayi wani program ba, amma Husnah takafe kai da fata akan cewa sai sunyi shagali ko babu yawa ne ma, saboda haka tuni ta zayyana mawa Dr.Sadeeq cewa ranar Laraba za’agudanar da tsantsarerren kamu wanda za ayi shi a wani babban katafaren Hall dake cikin garin abuja, ranar jumma’a kuwa zasu yi ƙayataccen walima domin ranar asabar ne ɗaurin auren, asabar ɗin da dare kuma za’ayi diner… Dr.Sadeeq baiji ɗar ba haka yasakarmawa Husnah kuɗi yace tayi duk wani abun daya dace… anko kala uku Husnah ta fitar kowani program da za’ayi da anko ɗinsa, ita dai Zahrah bata da tacewa, tasakar mawa Husnah komai…
Miƙewa tsaye yayi daga zaunen dayake haɗe da soma taka ƙafarsa wanda take ɗauke da ciwo cikin nutsuwa. Ahankali yake takawa yana me rumtse idanunsa da’alama dai yanajin zafin ciwon… Dai dai yakusa isa ƙofar fita daga ɗakinne Dr.Bilal yaturo ƙofar ɗakin yashigo..
“Ka kasa hakuri ko?” Dr.Bilal yatambayi Zaid cike da kulawa.
Ɓata fuska Zaid yayi haɗe da sanya hanunsa yadafa jikin bango gudun kada ya faɗi
“Ina fata kataho da takardan sallama na?” abun da yafito daga bakin Zaid kenan cike da zaƙuwa..
Murmushi Dr.Bilal yayi haɗe da jinjina kansa baisan wani irin dalili ne yasanya Zaid keson barin asibitin batare da ya tsaya yaji sauƙi ba, kofa tafiya me nisa baya iyawa, amma kuma gaba ɗaya yatashi hankalinsa akan sai anbasa sallama..
“Kwantar da hankalinka Zaid yanzuma nazo ne nataimaka maka domin su Dad ɗinka suna jiranka a waje yau kwanan gida zakayi” Sai alokacin Zaid ya’iya sake ransa, sakamakon jin dayayi cewa kwanan asibitiya ƙare masa…
Da taimakon Dr.Bilal Zaid ya iya takawa harzuwa inda motar su Dad ke jiransa.. A gidan baya ya zauna haɗe da kwantar da kansa ajikin kujera, bakomai ne ya sanya sa matsawa da sai an sallamesa ba face marari’n da idanunsa keyi masa nasan kallon fuskar Zahrah, ya ƙosa matuƙa yasanyata acikin idanunsa… Harsuka isa gida Zaid tunanin Zahrah yakeyi..
Yana shiga ɓangarensa ya faɗa bathroom haɗe da sakarmawa kansa ruwa, yajima tsaye agaban shower ruwa na dukansa kafun daga bisani ya yi wanka… sharp sharp ya shafa mai ajikinsa haɗe da feshe jikinsa da turaruka masu daɗin ƙamshi. 3 guater combat jeans yasanya wanda yatsaya masa iyaka guiwarsa, kasancewar kalan wandon nasa baƙine yasanya rigar polo shirt ɗin dake jikinsa takasance fara ƙal. Sosai yayi kyau duk da kuwa cewa rama ta bayyana ajikinsa sai dai kuma hakan bai sanya faffaɗan surar jikinsa komawa ba..
Ahankali yakejan ƙafar tasa har ya iso compound ɗin gidan nasu, driver na ganinsa ya kwaso aguje haɗe da ƙarasowa wajen Zaid ɗin da sauri,,, “Barka da fitowa ranka ya daɗe, fita zamuyi ne?” driver yatambaya cike da girmamawa.
Kai kawai Zaid ya’iya gyaɗa masa, aikuwa ba ɓata lokaci Driver yafiddo da wata farar range rover daga cikin parking space, yazo ya faka adai dai inda Zaid ke tsaye… A daddafe haka Zaid ya buɗe murfin motar yashiga yayinda driver yayiwa motar key suka bar cikin gidan… Bayan sun hau kan hanyane Zaid yafaɗama driver’n inda yakeso ya kaisa….. Kamar yanda Zaid ya faɗamasa inda zai kaisa, bai ƙaraba bai kuma rageba, adai dai ƙofar gidan yatsaya da motar cak.. Cike da halin isa Zaid yace da driver’n ya sauƙa yanemamasa yaro,, babu musu kuwa driver yabuɗe murfin motar yafita, wani yaro yagani da’alama aika zashi, baiyi wata wata ba ya ƙira yaron, yaron kuwa bawani nuƙu nuƙu yaƙaraso wajen da motar take tsaye… Cike da girmamawa driver’n yace “Oga ga yaro nasamu” sauƙe glass ɗin motar Zaid yayi haɗe da kallon yaron. Nuni Zaid yayi masa da gidansu Zahrah yace yaje yace ana kiranta… Mintuna kaɗan yaron yafito daga gidansu Zahrah haɗe da sanarmawa Zaid cewa ance batanan.. Har yaron yatafi Zaid bai iyacewa komai ba, wani iri yaji acikin zuciyarsa baiso ace masa batanan ba, amma yazaiyi dole zaije yaƙara dawowa….
Tundaga wannan ranar kusan kullum Sai Zaid yazo gidansu Zahrah amma maganar ɗayane batanan, gaba ɗaya kansa ya kulle yashiga damuwar rashin ganinta sosai, tabbas yana da buƙatar sanin inda take zuwa, watarana idan akace masa batanan haka zaizauna zaman jiranta amma kuma harya ƙaraci zamansa yatafi koda me kamanninta ne bai gani ba….
Shirye shiryen aure yasake kankama, hakan yasanya amarya da ango suka shiga busy, koda yaushe Zahrah tana gidan Hajiya Shuwa, wasu abubuwa na hidiman bikin ma Husnah Zahrah ta barwa, saboda ita bata da wani ishashshen lokaci,,, Ɓangaren Dr.Sadeeq ma dai yanda Zahrah tazama busy haka shima ya shiga busy hidima sosai yakeyi, hakan yasa ko haɗuwa da junansu basayi sai dai suyi waya wannan ma bako da yaushe ba. Yanzu Samad ne ke ɗawainiyar kaita duk inda zataje shike kuma ɗaukota….
Yau Aurensu yakasance saura sati guda kenan ita da Dr. Tafe take tana zuba sauri burinta ɗaya shine tasamu abun hawa wanda zai kaita gida, saboda yau Samad yabata excuse akan cewa bazai samu daman zuwa ɗaukota ba… Ƙarfe bakwai da rabi na daren yau kenan, yau ta makara sosai wajen dawowa gida, atsorace take matuƙa saboda gaba ɗaya arean unguwar su Hajiya Shuwa’n yaɗauki shiru… Tafe take ta sunkuyar da kanta ƙasa, bata ankara ba saijinta tayi tayi karo da mutum, da sauri ta matsa baya haɗe da sanya hanu ta dafe goshinta… Kallonta ta mayar ga mutumin da tayi karo dashi… take ta ƙara ware manya manyan idanunta, sakamakon ganin wanda ke tsaye a gabanta da tayi,, sosai gabanta yatsananta faɗuwa yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da sauri sauri…
Wani irin ƙayattacen murmushi yasakar mata wanda ya bayyana asalin kyawunsa, haɗe da buɗe duka hannayensa alamar ta taho garesa…….
Kyakkyawan murmushinsa ne ɗauke akan fuskarsa still hannayensa a ware suke, alamar ta taho zuwa garesa.+
Ahankali tashiga takawa tana nufar inda yake, ganin haka yasanya Zaid sakin ajiyar zuciya me ƙarfi, haɗe da sake sakin murmushi alokaci na ba adadi,, koda tazo gareshi yana shirin yaji ta rungumesa amma kuma sai yaji saɓanin haka, domin kuwa tana zuwa kusa dashi, sai gani yayi ta raɓa ta gefensa ta wuce batare dako kallonsa tayi ba. Cikin hanzari yasha gabanta haɗe da kamo hanunta. Cak ta tsaya daga tafiyan da takeyi haɗi da rumtse idanunta,, a hankali ya zame guiwowinsa ƙasa, ya durƙusa mata, duka hannayenta ya kama ya riƙe acikin nasa hanun….
Cikin murya me ɗauke da matuƙar rauni yace da’ita…… “Koda kalamaina baza suyi tasiri acikin zuciyarki ba, dan Allah inaso ki tsaya ki saurareni, ki dubi halin danake ciki Zahrah, banda wani sauran farinciki a duniyar nan idan har babuke a tare dani, haƙiƙa nayi nadama nakumayi dana sanin abun dana aikata a gareki, amma dan Allah Zahrah kiyi haƙuri kiji tausayina ki yarda muyi aure, wallahi namiki alƙawari zandaina duk wani abu danakeyi, zan baki farinciki me ɗorewa, zan mantar dake duk wani damuwa, me yasa bazaki cigaba da sona ba Zahrah? meyasa bazakiji tausayina ki yarda da tuban danayi ba, inasonki Zahrah so irin wanda bantaɓa yiwa kowa irinsa ba acikin wannan duniyar, zan iya fansar da komai nawa idan har zaki amince ki aureni, zan iya rayuwa babu komai babu kuma kowa, amma bazan iya rayuwa babu keba, zan iya sadaukar da duka dukiyata, dakuma duk wani abu nawa dana mallaka, matuƙar zansameki amatsayin matata, dan Allah Zahrah ki yarda dani mana, ninefa Zaid, nine mutumin da kika fara so acikin rayuwarki, shin mai yasa bazaki tausayamin ba, kikalli cikin idanuwa na Zahrah hakan kaɗai ya’isa bayyana miki irin tsananin ƙaunar danakeyi miki, inasonki, wallahi inasonki Zahrah!!..” gaba ɗaya zuciyarsa ta karye, sosai rauninsa ya bayyana… A kan fuskar Zahrah kuwa hawayene ke zuba tamkar anbuɗe famfo sannan kuma haryanzu idanunta akulle suke, yayinda harkawo yanzu hannayenta ke cikin nasa hanun. Bazatace yaushene ko kuma tayayane itama ta tsinci kanta da zamewa ƙasa ba, ta dai tsinci kanta da kafa guiwowinta a ƙasa. kukane yaci ƙarfinta bazata kuma iya cewa ga abu ɗaya dake damunta ba… Hanunta tashiga ƙoƙarin cirewa daga cikin nasa hanun, amma kwata kwata Zaid yaƙi bata daman hakan saima ƙara matsowa kusa da’ita da yakeyi… 1
“Zahrah!” yaƙira sunanta cikin wata irin murya da bata fita sosai…
Manyan manyan idanunta da suka cika da ruwan hawaye ta ɗago haɗe da waresu akansa, batare da tace dashi komai ba,, wani irin kallo yakeyi mata wanda yake ɗauke da tarin ma’anoni masu yawan gaske.. Hanunta dake cikin nasa hanun ya shiga murzawa haɗe da langwaɓar da kansa gefe yana me cigaba da kallon fuskarta. Hawayene yaziraro daga cikin idanun ta zuwa kan ƙuncinta, sam bata taɓayin zato ko tsammani ba, saijin sauƙar bakinsa tayi akan ƙuncinta, yayinda yasanya harshensa yana me lashe ruwan hawayen dake gudu akan ƙuncin nata. wani irin bugawa zuciyar Zahrah tashigayi da sauri, yayinda numfashinta keshirin ƙwace mata batare da tashiryawa hakan ba,, cikin ɗan kuzarin daya rage mata tayi saurin tureshi gefe haɗi da miƙewa tsaye, ƙoƙarin kama hanunta yakuma yi amma saidai baisamu daman hakan ba domin kuwa tuni harta fara tafiya. “Zahrah” yakuma ƙiran sunanta amma sai dai ko waiwayosa batayiba balle yasaran zata amsa masa.. Jefa ƙafarta kawai take batare dako da ganin gabanta tanayiba, gaba ɗaya ƙwalla suncika mata idanu, yayinda ƙirjinta ke mata luguden duka kanta kuwa tamkar anɗaura mata gungumen ice haka takeji yamata nauyi…2
STORY CONTINUES BELOW
Cikin Hanzari Zaid yarufa mata baya, yana me ƙiran sunanta amma kuma bata amsa masaba, haka kuma bata tsayaba, dai dai lokacin wani me taxi yazo wucewa da sauri Zahrah taɗaga masa hanu, aikuwa take yatsaya,, ganin haka yasanya Zaid yaƙara sauri don yaga alamar tafiya zatayi batare da ta tsaya ta sauraresa ba,, amma ina yamakaro domin mai taxi ɗin yana tsayawa Zahrah ta buɗe murfin motar tashige haɗe da cewa mai taxi ɗin yatada motar sutafi.. Zaid na ƙarasowa wajen, me taxi ɗin kuma na figar motar ya cillata kan titi.. Wani irin iska me zafi Zaid ya fesar daga cikin bakinsa, sam baiso haka ba, yaso ace yaji koda kalma ɗayane daga bakinta, amma kuma duk da haka yamatuƙar jin daɗin ganinta, gashi kuma har kusa da’ita yasamu yazo, babban abun farincikin kuma shine har numfashinta ya shaƙa. Take yaji zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi, yayinda daɗi da kuma nutsuwa suka cika masa ruhinsa.. Cike da farinciki haka yakoma inda yabar motarsa…..
Zahrah kuwa ko acikin taxi hawayenta kasa tsagaitawa sukayi, saima kara tuttulowa da suke tamkar ana hankaɗosu… Ahaka har mai taxi ɗin yakawota ƙofar gidansu. Kuɗinsa tabasa ko canji bata tsaya karɓa ba ta wuce cikin gida.. A zauren gidan nasu ta tsaya haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, sam bataso kowa yasan halin da take ciki, ta barwa Allah dakuma zuciyarta…
Tana shiga cikin gida Inna tayo wajenta da sauri
“A’ina kika tsayane Zahrah? gaba ɗaya duk kinsa hankalinmu yatashi, munsan bakya kaiwa iwar haka baki dawo ba” Inna tafaɗi haka tana me ƙaremawa yanayin Zahrah’n kallo.
“Bansamu abun hawa bane Inna, yau Samad yana da wani uzuri shi yasa baisamu daman ɗaukoni ba” Zahrah tafaɗi haka tana me ƙwaƙulo murmushi ta aza akan fuskarta..
Da kallon tuhuma Inna tabi ta harta shige cikin ɗakinta, tana shiga cikin ɗakin ta dannawa ƙofarta sakata, a hankali tazame ƙasa haɗe da jingina bayanta da ƙofar, kana ta cusa kanta cikin cinyoyinta, wani irin kuka tashiga rerawa me tsananin bantausayi, Yazatayi da rayuwarta ne itakam, da badon kada tayi saɓo ba da sai tace wannan ƙaddaran nata yayi mata girma dayawa, amma sai dai kuma ba’aja da ikon Allah, haƙiƙa tayi imani cewa komai zaizo yawuce, domin kuwa komai yayi farko yana da ƙarshe, amma kuma sai dai tana da yaƙinin cewa kafun nan wataƙila zuciyarta tayi bindiga ta tarwatse,, “yazatayi da abun da takeji acikin zuciyarta?” tambayar da kullum saitayi mawa kanta kenan, amma kuma zancen ɗayane shine bata da amsar da zata bawa kanta.. Tana cikin kukan taji wayarta na ƙara, amma ko ɗago kanta batayiba haka wayar taƙaraci tsuwanta har ƙiran ya katse, wani ƙiran ne yakuma shigowa still har wayar ta katse batako ɗaga ido ta duba taga waye yake ƙiranta ba.. Kuka tayi sosai kafun tatashi daga durƙushen da take takoma kan katifarta,,,, kwanciya tayi luf tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai, yayinda tsikar jikinta ke yawanta tashi, idan tatuno kusancin da suka samu ɗazu ita da Zaid, bakomai ke dagula mata lissafi da kuma hautsina mata ƙwaƙwalwa ba kamar idan tatuna da yanda yasanya harshensa akan kumatunta yanashan hawayenta, yana me kuma yi mata wani irin kallo wanda yakasa ɓacewa daga cikin idanunta,,, batasan me Zaid yakeso a tattare da’ita ba, wataƙila rayuwarta yakeso, wataƙila kuma hauka yakeso yaga tayi, baisan yatakeji idan ta gansa ba, baisan metakeji agame dashi aduk sanda taɗaura idanuwanta akansa ba, sake gyara kwanciyarta tayi, tabbas tana da buƙatar samun wani wanda zata faɗawa gaba ɗaya damuwarta, tana da buƙatar wanda zai kwantar mata da hankali yakuma samamata nutsuwa, tana kuma buƙatar wanda zai fayyace mata abun dake cikin zuciyarta, koda hakan zaisanya tasamu sauƙi da salama,, haka dai Zahrah tayi bacci zuciyarta cike da tarin tambayoyi…..
Zaid ne kwance akan wata haɗɗɗiyar kujera mai kama da gado, wanda take aje cikin wani irin katafaren falo wanda aka ƙawatasa da kayan ƙyale ƙyale dakuma more rayuwa. Murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda kyawawan idanunsa suke a lumshe, wani irin shauƙi me tsanani yakeji a tattare dashi, a iya ganinta da yayi jiyake tamkar anyaye masa gaba ɗaya damuwarsa ne, idanunsa yasake lumshewa haɗe da sake shaƙan daddaɗan ƙamshin da yakeyi masa yawo acikin hanci, ƙamshin da tun ɗazu yakasa barin hancinsa, “wani irin daddaɗan ƙamshine haka Zahrah’nsa keyi?” ya tambayi kansa,, tabbas zai so ace iyanzu Zahrah na kusa dashi, dakuwa kwana zaiyi manne da’ita yana shaƙan wannan daddaɗan ƙamshin nata, sannu ahankali wani irin muguwar kasala ke dirar masa, yayinda wani irin sha’awarta me tsanani ya kawo masa ziyara,, a hankali yasanya harshensa ya lashi laɓɓansa haɗe da sanya hanu yashafi ƙwantaccen beard ɗin sa wanda koda yaushe yake ƙara ƙawata masa fuskarsa,, a hanakali ya ware manyan idanunsa wanda suka soma sauya launi daga farare zuwa kalan bacci, wanda idan ka kallesu dole zasu sauƙar maka da kasala… Laptop ɗin dake kusa dashi ya ɗauka, haɗe da buɗewa, take hoton kyakkyawar fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin,, murmushi yayi haɗi da sanya hanu yashafi kan screen ɗin laptop ɗin..
STORY CONTINUES BELOW
“Inasonki Zahrah!”
ya faɗi haka cikin wata irin murya me ɗauke da matsanancin shauƙi. Take yaji yana matuƙar sha’awan kallon vedion dayayi mata ɗazu batare da tasani ba, lokacin fitowarta daga gidan Hajiya Shuwa. Wayarsa da vedion ke ciki ya ɗauka haɗe da kunnawa, kallon vedion yakeyi yana murmushi, amma kuma kwata kwata saƙonnin da suke shigowa ta Email ɗinsa sun hanasa sakat.. Kai tsaye fita daga ɓangaren vedion yayi ya kutsa cikin Email ɗin nasa, saƙonnin abokanan business ɗinsa ne, sama sama yakaranta saƙonnin, haryana shirin fita daga cikin Email ɗin sai kuma idanunsa suka sauƙa akan saƙon Jasheer wanda yaturo masa,, hakanan yaji gabansa yaɗan faɗi saboda yasan duk saƙon da zaizo daga Jasheer to akan Zahrah ne,, buɗe saƙon yayi haɗe da ƙurawa hoton da Jasheer yaturo masa idanu.. Wani irin abu ne yaji ya taso yatokare masa maƙoshi, yayinda idanunsa suka kaɗa sukai jajur dasu, take gashin jikinsa suka mimmiƙe, wani irin juyawa yaji kansa nayi masa,, shin dagaske katin ɗaurin auren Zahrah idanuwansa suke gane masa ko kuwa? sake waro manya manyan idanuwan nasa yayi aikuwa ba ƙarya idanun nasa keyi masa ba, sunan Zahrah ne rantaɓe ajikin katin dakuma sunan Dr.Sadeeq,, wani irin ƙara Zaid yayi haɗe da yin cilli da wayartasa, take ta bugi bango takuma faɗowa ƙasa lokaci ɗaya ta tarwatse.. Cikin matsanancin ɓacin rai jikin Zaid yasoma rawa take yaji wani irin matsancin zafi a dai dai saitin zuciyarsa, lokaci ɗaya wani irin tari ya tasomai, take yasoma tari babu ƙaƙƙautawa, sai ga jini na fita ta bakinsa abun mamaki, abun da bai taɓa gani ba arayuwarsa,, da ƙyar yasamu tarin ya tsagaita, amma kuma duk da haka ƙirjinsa bai daina yi masa ƙuna ba, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi har cikin cikinsa kuwa yakejin zafin,, a hankali ya jingina bayansa da jikin bango, haɗe da rumtse jajayen idanunsa, numfashi yashiga fitarwa a hankali, daga ni kai kasan yana matuƙar jin ciwo,, cikin yanayi na wahaltuwa haka ya daddafa zuwa cikin ɗakinsa, ƙaramin drower’n dake gefen gadonsa ya jawo haɗe da ciro magungunansa, tsabar ɗacin da yakeji a maƙoshin sa da ƙyar ma ya iya haɗiye magungunan… Kwanciya yayi akan gado haɗi da rumtse idanunsa, baisan ina zai tsoma rayuwarsa ba, baisan tayaya zai fara jure rashin Zahrah akusa dashi ba… Kamar dai yanda Zaid yaga rana haka yaga dare, koda kuwa na minti guda ne baiji wani salama ko sanyi acikin zuciyarsa ba, haka ya share awanni masu yawa cikin ciwo,, sai da yayi sallan Asuba ƙafun wani irin bacci me nauyi ya sace sa batare daya shiryawa hakan ba……
*****
Zahrah kuwa yau da wani irin irin matsanancin ciwon kai ta tashi, gaba ɗaya idanunta sunyi luhu luhu dasu, da gani kai kasan cewa kuka tasha ta ƙoshi.
Yau ya kasance aurenta da Dr.Sadeeq saura kwanaki shida kenan tana ƙirgawa kuma acikin kwanakin nan ne zasu fara gudanar da shirye shiryen da suka tsara,, gaba ɗaya ji takeyi bata marmarin auren, sannan kuma ji takeyi komai yafice mata arai, bawai kuma don batason Dr.Sadeeq ɗin ba, tun shekaran jiya Dr.Sadeeq yakawo mata ɗinkunanta da kuma kayan da zata sanya a kamu da wajen diner, amma kuma ko duba kayan batayi ba balle taga ma ko sunyi mata ko basuyi mata ba, batasan meyake damunta ba, amma tabbas tasan akwai wani baƙon al’amari dayake ta kusanto rayuwarta aduk kwanan duniya. Yau hakanan tatashi taji ko gyaran jikin ma batason zuwa, amma kuma dazaran tace bazata jeba tasan Inna zata sanyata agaba da yawan tambayoyi, don haka ma gwamma kawai ta je ɗin zaifiye mata… Sauri sauri haka ta shirya tafito, saboda tasan cewa yanzu haka Samad na ƙofar gida yana jiranta… ai kuwa tana fitowa taga motar Dr.Sadeeq fake a ƙofar gidan nasu, murmushi kawai tayi haɗe da ƙarasawa wajen motar… “Allah sarki Samad yana da haƙurin jira, da Dr.Sadeeq ne da yanzun ya ƙirata a waya” tafaɗi haka a zuciyarta dai dai sanda taƙaraso gaf da motar, buɗe murfin motar tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama, “Kayi haƙuri Samad nabarka kana ta jira” tafaɗi haka tana me ƙoƙarin rufe murfin motar, batare da takalli Inda Samad ɗin ke zaune ba.
Tana rufe murfin motar tadawo da kallonta wajen zaman driver fuskarta ɗauke da murmushi,, a maimakon taga Samad saitaga Dr.Sadeeq, mamakine ya bayyana akan fuskarta alokaci guda, sake ware idanu tayi tana kallonsa, da’alama dai ganinsa yabata mamaki sosai…10
STORY CONTINUES BELOW
Murmushinsa me kyau yayi mata haɗe da kafeta da idanunsa wanda suke sauƙar mata da wani irin yanayi na kasala ajikinta.. Itama murmushin tayi masa haɗe da shagwaɓe fuska….
“Ni dai nayi fushi!” tafaɗi haka a shagwaɓe… 2
“Tuba nake”
Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me kama kunnuwansa da duka hannayensa.. alaman ban haƙuri.
“Ni dai naƙi wayon” tafaɗi haka tana me kaɗa idanunta.. Murmushi yayimata haɗe da kamo duka hannayenta yasanya acikin nasa hanun, lumshe idanunsa yayi alokaci guda haɗe da buɗewa
“Nayi kewarki sosai Zahrah na!” yafaɗi haka cikin wata murya me sanyi.
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da soma ƙoƙarin janye hanunta daga cikin nasa hanun, amma kuma bata samu daman hakan ba. “Meyasa jiya kika ƙi ɗaga wayana?” yatambayeta cike da kulawa bayan yagama karantar yanayin da take ciki. Sai alokacin ne ma Zahrah ta tuno da cewa jiya taga missed calls ɗinsa, sanann kuma bata bi bayaba,, ƙaƙalo murmushi tayi haɗe da cewa ” Kayi haƙuri nayi bacci ne alokacin”
Kansa ya jinjina badon wai ya gamsu da abun da ta faɗa ba,, ta da motar yayi suka hau kan titi. Saida sukayi nisa a tafiyar kafun yadawo da kallonsa gareta, sosai tayimasa kyau komai nata ya canja, sai dai kuma kallo ɗaya yayimawa fuskarta yafuskanci cewa tayi kuka, dafari yaso tambayarta meke damunta, amma kuma sai kawai ya share,,, sama sama yake janta da hira harsuka iso gidan Hajiya Shuwa… Yana ganin shigewarta cikin gidan ya sauƙe ajiyar zuciya ƴaɗe da kifa kansa akan steering motar, “meke damun Zahrah ne?” ya yiwa kansa tambayar a bayyane, amma sai dai kuma bayida amsar da zai bawa kansa…. A jiyar zuciya yakuma sauƙewa akaro na barkatai, zuciyarsa cike da tunani kala kala yaja motarsa yabar ƙofar gidan……. Ɓangaren Zahrah kuwa kwana biyun nan wasu irin magunguna masu ƙarfin gaske Hajiya Shuwa take bata tanasha, hakan kuwa shike taimakawa wajen hautsina mata tunaninta, wani irin abu takeji acikin jikinta wanda kai tsaye za’a iya ƙiransa da suna sha’awa, ko da yaushe yanzu Zahrah cikin jin feelings take, hattakai ta kawo yanzu alwala ma baya daɗewa ajikinta yake karyewa saboda sosai sperm ke fita ajikinta, duk kuma ɗaya daga cikin aikin magungunan ƙarin ni’iman da Hajiya Shuwa ke bata ne, lallai ita kanta tasan cewa Hajiya Shuwa tayi mata babban haɗi me matuƙar kyau…… (su Doctor za’asha nice😜🙈)
Tunda bacci ya ɗaukeshi da asuba bashi yafarka ba sai ƙarfe 9:30 am, da wani irin zazzafan zazzaɓi yatashi, wanda ya zamana ko ɗaga kansa ba ya’iyawa hatta numfashima da ƙyar yake iya fitarwa. Yana a wannan halin ne yaji anturo ƙofar ɗakin nasa, bai iya ɗago kansa ya dubi ko waye ba amma kuma duk da haka ya gane waye ne yashigo cikin ɗakin… Dasauri Alhj Ma’aruf yaƙaraso garesa…
“Lafiya Zaid meke damunka?” Alhaji Ma’aruf yafaɗi haka yana me kai hanunsa jikin Zaid, da sauri yajanye hanunsa daga jikin Zaid ɗin domin kuwa jiyayi jikin Zaid ɗin yaɗau zafi rau kamar wuta. “Subahanallah, bana ƙira Doctor yanzu” Dad yafaɗi haka yana me ƙoƙarin ciro wayarsa daga cikin aljihu,, bugu biyu Dr.Bilal yaɗauki wayar, cike da damuwa Dad yace yanason ganinsa jikin Zaid ne yatashi. take Dr.Bilal yace gashinan zuwa..
Zama Dad yayi jigum agefen gadon Zaid ɗin, gaba ɗaya yarasa mekeyi masa daɗi, sosai matuƙa cutar Zaid ke damunsa, yana matuƙar ƙaunar Zaid sam bayaso wani abu ya samesa, musamman ma yanzu da Dr.Bilal yashaida masa cewa Zaid ɗin yana ɗauke da ciwon zuciya me tsanani… Mintuna kaɗan Dr.Bilal yaƙaraso gidan, babu wani ɓata lokaci kuwa yashiga yiwa Zaid wasu ƴan gwaje gwaje, drip yaɗaura masa bayan yayi masa wasu allurai guda biyu wanda zasu taimaka wajen kawar da zazzaɓi da kuma ciwon da kansa keyi masa uwa uba kuma su sanyasa bacci, saboda idan yana a cikin hayyacinsa bazai taɓa barin zuciyarsa ta huta ba, yin hakan kuma shike ƙara sawa ciwon yayi tsanani… Bayan sun fito compound ɗin gidan ne Dr.Bilal yagyara tsayuwarsa haɗe da duban Alhaji ma’aruf,, bayani yashiga yimawa Alhaji Ma’aruf ɗin sosai agame da ciwon Zaid ɗin. Bayan sun kammala maganan ne Alhj Ma’aruf yakoma wajen Zaid da tuni wani baccin wahala yasake ɗaukansa……
STORY CONTINUES BELOW
*****
Rana bata ƙarya, ranar yau takasance laraba kuma yautake kamun Amarya, tun da safe gidan su Zahrah yake acike ƴan uwan Inna sun tattaro ƙwansu da ƙwarƙwatansu sun garzayo, don haka tuni gida yaɗauki hargowa da hayaniyan mutane yayinda amarya kuwa tunsafe take ƙunshe a ɗaki acewarta cikinta ne keyi mata ciwo,, Husnah da Suhaima ne suka taimaka wajen ɗebe mata kewa ta hanyar zama da’ita…..
Ƙarfe uku na yammaci kenan amma tuni gidansu Zahrah ya ɗinke da mutane, ciki kuwa hadda ƴan matan school ɗinsu wanda Husnah ce ta gayyacesu, domin ita dai Zahrah bata da wasu ƙawaye Husnah ce kaɗai ƙawarta… Kowacce ka kalla acikin ƴan matan nan tasha kyau cikin kayan anko ɗinta. Husnah ce tsaye akan Zahrah tana ta faman ɓaɓatu akan cewa Zahrah’n ta tashi su tafi shagon meckup domin tuni Dr.Sadeeq yaturo freinds ɗinsa waƴanda zasu kaisu shagon yin meckup ɗin suna ma jiransu aƙofar gida,, ita dai Zahrah yau jitayi gaba ɗaya bakinta ya mutu sambatajin wani kuzari ajikinta. Kayan da zata sanya da duk wani abun da zatayi amfani dashi, Husnah ta ɗaukar mata haɗe da kama hanunta suka fice daga cikin gidan. Wasu haɗaɗɗun motoci suka shiga kai tsaye aka wuce dasu wani shahararren shagon meckup….
Kwalliya sosai shahararriyar meyin meckup ɗinnan ta tsantsarawa Zahrah akan fuskarta lokaci ɗaya saiga Zahrah ta sauya kamanni asalin kyawunta yasake bayyana tamkar wata balarabiya ita kanta Zahrah saida tayi mamakin ganin kanta, tabbas dabadan tasan ita ɗin ceba, to da sai tace sanja mata fuska akayi, kowa yaga kwalliyanta saiyayi santi saboda tasha kyau iya kyau.. Wani doguwar rigan leshi me kyau da tsada ta sanya ajikinta, take kyakkyawar surar jikinta ya bayyana kansa acikin kayan, sosai ɗinkin yayi kyau yakuma amshi jikinta, zama tayi aka tsantsara mata haɗaɗɗen ɗaurin ɗankwali akanta, yayinda aka nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyar kanta, ita dai tsayawa tayi kamar wata statue tana mamakin irin baiwar kyawun da Allah yayi mata, daga riganta har zuwa kan takalminta dakuma ɗan karamin fos ɗin dake rike ahanunta kalarsu yakasance light peach ne, yayinda stones ɗin kayanta suka kasance farare, lokacin da su Husnah sukayi tozali da Zahrah ihu dakuma shewa suka sanya haɗe da tsantsar mamakin irin kyawun da Zahrah tayi, kowa dai yasan Zahrah kyakkyawace amma kuma basuyi tunanin kyawunnata har ya kai hakaba, lallai duk namijin daya samu Zahrah amatsayin mata yayi babban gamdakatar. Take su Husnah suka shiga ɗaukarta hotuna da kuma vedios suna watsawa a instagram dakuma whatsapp, suna cikin buga selfie abokan ango suka ƙaraso don ɗaukar ƙawayen amarya,, duka ƴan matan kowacce da motar da tashiga, yayinda aka bar Zahrah da Husnah sukaɗai saboda Ango yace shi dakansa zaizo yaɗauki amaryarsa… Ƙawaye basu jima da tafiya ba wayar Husnah tasoma ƙara,, murmushi tayi haɗe da kallon Zahrah adai dai lokacin da taɗaga wayar takara akan kunenta, “To ranka shi daɗe gamunan fitowa” abun da Husnah tafaɗa kenan haɗe da miƙewa tsaye hannuwan Zahrah takamo haɗe da miƙar da’ita tsaye..
“Angonki yaƙaraso yace nafito masa dake” murmushi kawai Zahrah tasakar mawa Husnah kana ta sunkuyar da kanta ƙasa.. A hankali Zahrah ke takawa yayinda rigar jikinta kejan ƙasa, babu abun dake tashi ajikinta sai daddaɗan ƙamshin turare,, gaskiya Zahrah tayi kyau sosai ayau ɗin..
Ware idanu Dr.Sadeeq dake zaune acikin motarsa yayi yana me kallon Zahrah, shima yasha ado cikin wata farar gezina me matuƙar kyau da tsada yayi kyau sosai da sosai, kwarjininsa yasake fitowa fili….. Har Husnah ta buɗe murfin motar ta tura Zahrah ciki bai rufe bakinsa ba haka kuma bai ɗauke idanunsa daga kallon da yakeyi wa Zahrah ba, lallai ne godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) daya tsara wannan kyakkyawar halitta, kullum kuma koda yaushe yana kallon kyawun Zahrah amma kuma yau saiyake ganin kyawun nata yafi na koyaushe ƙawatuwa.. A hankali ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunsa,,, Zahrah kuwa tunda tashiga cikin motar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana me wasa da yatsun hanunta,, Motar Habeeb dake bayan ta su Zahrah Husnah tashiga,,, atare motocin suka tashi tafiya sukeyi ahanakali akan titin…
“Zahrah!” Dr.Sadeeq yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi dakuma sauƙar da nutsuwa. Kasa amsa masa Zahrah tayi, hakanan taji wani irin nauyinsa ya lulluɓeta.
“Kinyi matuƙar kyau sosai, sai yanzu nasakejin cewa nayi babban sa’a dana sameki, inasonki sosai Zahrah na, ina fata watarana nima kisoni tamkar yanda nake sonki!”
Sai alokacin Zahrah ta ɗago kanta, haɗe da sakar masa ƙawataccen murmushi, jiyayi gaba ɗaya ta kashesa da salon murmushin nata, a hankali ya matso daf da’ita haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya riƙesu gam acikin nasa, wani irin soyayyartane yaji yana ƙara shiga jikinsa, jiyakeyi tamkar ya jawota jikinsa ya rungumeta kozai sake samun nutsuwa acikin zuciyarsa…. Harsuka iso katafaren hall ɗin daya cika maƙil da jama’a zuwan amarya da ango kawai ake jira, amma Dr.Sadeeq bai ɗauke idanunsa akan abar ƙaunarsa ba, wani abun daya ƙara rikitar da Zahrah takasa cewa dashi komai shine yanayin yanda yake mata magana da wata irin murya me sanyi… Motarsu na’isowa wajen taron, mc yasoma shela cewa ga ango da amarya sun ƙaraso, take guri yasake ɗaukan shewa yayinda kowa yazura idanun ganin ango da amarya, waƴanda suka zo wajen dan gulma suka sake miƙa wuya musamman ma familyn Dr.Sadeeq wanda anriga da angama gayamusu cewa amaryan ƴar matsiyata ne saboda haka suka baza idanuwan ganin ta don kashewa idanuwansu ƙwarƙwata…. Habeeb ne ya buɗewa Dr.Sadeeq ƙofar motar yafito, yayinda shikuma Dr.Sadeeq da kansa yazagayo ya buɗe mawa Zahrah nata ƙofar,,, cikin nutsuwa ta zuro ƙafafunta waje, kafun daga bisani tafito daga cikin motar, hanunta ɗaya Dr.Sadeeq yakama suka soma taku cike da nutsuwa,, wajene yaɗauki shewa masu murna nayi masu baƙinciki ma sunayi, haka masu ɗaukar amarya da ango hoto da vedio’s ma duk sunayi,, gaba ɗaya family’n Dr.Sadeeq ƙamewa sukayi ƙam ganin kyawun amarya ya tsoratasu sosai, saboda basu taɓa tunanin haka zasuga amaryan ba, sunyi tunanin zasu ganta wata almajira da’ita amma kuma sai suka ga saɓanin tunaninsu, lallai ba’abanza ba Dr.Sadeeq ya liƙe akan cewa shi dole sai’ita, takai takuma cancanci ayi mata fiye da haka ma… Har amarya da ango suka ƙarasa mazauninsu mutane basu daina yimusu vedio’s ba, haka kuma idanu bai ɗauke daga kan suba………Sunkuyar dakai ƙasa Zahrah tayi gaba ɗaya ita kunyar mutanen dake tare a wajen takeyi, tunda take bata taɓa shiga irin wannan taron ba, sai gashi yau akanta ma akeyin taron, ba abun dake damunta kamar yanda idan taɗaga idanunta take ganin idanuwan mutane akanta kowa ita yake kallo da waƴanda suka santa haddama waƴanda basu santa ba,, matso da kansa yayi kusa da’ita haɗe da kawo bakinsa wajen kunnenta “Anan ma kunya zaki nuna?” ƙasa ƙasa yayi maganar. satan kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi amma kuma batace dashi komai ba, haka dai masu yin vedio suka ci gaba da ɗauka yayinda….. Hmmmm kamu dai yayi kamu yakuma ƙawatar amma kuma sai dai sam amarya Zahrah ta kasa sakewa komai a ɗari ɗari takeyinsa, abu biyune suka haɗe mata kunya dakuma rashin sabo, saboda bata taɓa zuwa irin waƴannan wajen ba, wannan ne karonta na farko, gashi kuma kamun yatara mutane sosai, su Husnah sunyi rawa sosai sun raƙashe Amarya kuwa ae ko taka kafarta bata’iya ba gaba ɗaya nauyi da kunya sun hanata sakat…. sai gab da magrib aka tashi daga kamu kowa yasamu abun arziƙi ankuma cika ciki da abinci na musamman da kuma lemuka… Yanzu kam mota ɗaya Zahrah da Husnah harma da Suhaima suka shiga, yayinda Dr.Sadeeq shikuma yashiga wata motar ta daban… Jingina bayanta tayi da kujera haɗe da kwantar da kanta akan kafaɗan Husnah, duk hiran da Husnah da Suhaima keyi jinsu kawai takeyi, sosai sanyin AC’n dake cikin motar yake ratsata har hakan yaso sanyamata zazzaɓi, haka dama ita take matuƙar ta shiga hayaniya to kanta sai ya ɗanyi mata ciwo, uwa uba kuma idan sanyi yayimata yawa saita ɗanyi zazzaɓi.. Harsuka isa gida Zahrah ko uffan batace ba duk da kuwa yanda su Husnah kejanta da hira, amma iya abun da take iyayimusu shine murmushi… Fitowarta a wanka kenan, sauri sauri ta zura wata doguwar riga me kauri ajikinta,,, kallon ta ta mayar ga Husnah wacce taketa faman chatting a wayarta sai nurmushi kawai take zubawa..+
“Wai ke da waye ne haka? a iya sanina dake ke ba mutum bace me yawan chatting da’alama dai munsamu ƙaruwa” Zahrah tafaɗi maganar cikin sigar tsokana… Dariya Husnah tayi haɗe da ɗage giranta sama. “Ƙwarai kuwa tawan, wallahi ɗazu na haɗu da wani guy a wajen kamunki, ina tunanin ya kwantamin arai”
Dariya Zahrah ta sanya haɗe da neman guri ta zauna akusa da Husnah haɗi da kwantar da kanta akan kafaɗan Husna’n….
“Husnah kinsan ya so yake?” tambayar da ta fito daga bakin Zahrah kenan..
Mamaki tambayar da Zahrah tayi mata ya bata amma kuma batasan menene dalilin dayasanya Zahrah tayi mata wannan tambayar ba…
“Eh zan iyacewa nasansa zankuma iya cewa bansan saba, saboda banyi wani zurfi acikinsa ba, amma kuma ke kinsan bana yaudaran kaina Zahrah, duk wasu alamomin so nasansu, saboda hakane ma nayardarwa kaina cewa nakamu da soyayyar Yazeed so matsananci!” Husnah tafaɗi haka tana me wasa da wayar hanunta, da’alama sunan Yazeed kaɗai da ta ambata yasanyata cikin shauƙi..
Ajiyar zuciya me ƙarfi Zahrah ta sauƙe haɗe da ɗago kanta daga kan kafaɗar Husnah, hannayen Husnah takama cikin murya me sanyi tace da Husnah “Wasu irin alamomi ne kesanyawa mutum yagane cewa yakamu da so? sannan kuma inaso ki sanar dani menene hukuncin zuciyar da ta makance har take ƙoƙarin sake son wanda yacutar da’ita, wanda kuma baida wani amfani a wajenta”
STORY CONTINUES BELOW
Kallon mamaki haɗe da ɗaurewar kai Husnah tashiga yi mawa Zahrah, ƙwarai itakam maganganun Zahrah sun sanyata a duhu me Zahrah take nufi?
“Banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zanfi fahimta idan har kika warware maganar tazama abu guda, amma kuma ni a ganina babu amfanin zuciyar da zata so wanda baida amfani a wajenta, sai dai kuma amma kinsan shi so wani zubin yakan makantar da komai naka ne tahanyar da baka isa kayi yaƙi dashi ba, amma kuma shi so kala kala ne, kowani so da’irin ƙarfinsa haka kuma da irin rauninsa, wani son yana fita, wani kuma sai ahankali zai fita, wani kuwa baya taɓa fita har gaban abada, amma shi wanda baya fita har abada shi ake ƙira da ƙauna, ita ƙauna kuma idan zafinta yatashi ƙona ka, to ƙunan yakan kasance me tsananin zafi da raɗaɗi bakamar na so ba, ina fata dai Ƙaunar Doctor ce tasanya kikamin wannan tambayar?” Husnah tafaɗi haka tana murmushi.. Wasu siraran hawayene suka silalo daga cikin idanun Zahrah zuwa kan ƙuncinta.
“Zahrah kuka kuma?” Husnah tatambaya cike da mamaki domin ita sam bataga abun kuka acikin maganar da sukeyi ba, hasalima ita Zahrah’n ce tafara ɗago maganar ba wai ita ba.
Hanu tasanya ta share hawayenta haɗe da sakin murmushi, “Bakomai Husnah kawai dai idanuna ne tunɗazu sukeyimin zafi, kinsan ban saba da irin wannan kwalliyar da akamin ba, bacci ma nakeji bana ɗan kwanta, idan kingama ki rufe mana ƙofa” Zahrah tafaɗi haka fuskarta ɗauke da murmushin dole..
Har Zahrah ta kwanta Husnah bata ɗauke idanunta daga kanta ba, sosai ganin hawayen Zahrah’n yabata mamaki duk da kuwa cewa tana lure da’ita a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya acikin damuwa take wuni, amma gudun kada ta dameta da tambaya yasanyata sharewa bata tambayeta ba, amma tasan damuwa kam akwai shi jingim acikin zuciyar Zahrah…
Kusan mintuna talatin hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, amma kuma ko kyakkyawan motsi taƙi tayi gudun kada Husnah ta fuskanci cewa batayi bacci ba,, bazata taɓa bari kowa yasan damuwarta ba, ta yarda ta amince zata haɗiye duk wani damuwarta acikin rai da zuciyarta ita kaɗai, koda kuwa damuwartata zata kasheta, tabbas wannan abun da takeji ba abu bane wanda zai ɓoyu ba, amma kuma zatayi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta maidashi ɓoyayyen sirrinta a haka har baccin gajiya ya ɗauketa, tana bacci babu jimawa kuwa ƙiran Dr.Sadeeq yashigo cikin wayarta, ganin ya nace da ƙiran ne yasanya Husnah ɗaga wayar ta shaida masa cewa Zahrah tayi bacci, to kawai yace haɗe da ajiye wayar..
Wani irin tausayinta ne yaji ya dirar masa acikin zuciyarsa, hakanan yaji yau soyayyarta yasake shiga zuciyarsa fiye da ko yaushe yayinda tausayinta yakuma ɗarsuwa acikin zuciyarsa, yaso jin muryarta acikin wannan daren amma kuma hakan baisamu ba, haka yashare yashiga cikin abokansa suka cigaba da sabgoginsu……
Kafe cak idanunsa suke akan haɗaɗɗen zanen POP’n dake mamaye saman ɗakin wanda aka ƙawatasa da ado me matuƙar burgewa, a hankali yake fitar da numfashi me zafi daga cikin hancinsa,, ahalin yanzu ba ciwon da yakeji bane damuwarsa, yafi damuwa da ganin Zahrah’nsa fiye da komai, yanzu kenan saura kwana uku a ɗaura mawa Zahrah’nsa aure da wani bashi ba, rumtse idanunsa yayi da sauri haɗe da haɗiye wani irin yawu me ɗaci daya tsaya masa a maƙoshi, abu kamar wasa saiga ƙwalla suna gangarowa daga cikin idanun Zaid, hanu yasanya yashafa gefen fuskarsa inda yaji sauƙar ɗumin wani abu kamar ruwa,, ruwan hawayen daya fito daga cikin idanunsa ya lakato ahanunsa koda yaga cewa hawayene ke fita daga cikin idanunsa sai yasaki wani irin murmushi me matuƙar ciwo, rayuwa kenan babu yanda bata juyawa bawa, watarana kaga me kyau watarana kuwa kaga mummuna, ƙaddara kenan babu tayanda bata zuwarwa bawa, haƙiƙa SO babban cutane ga bawa musamman idan baka samu abun da kakeso ɗin ba, tabbas ya jarabtu domin ko a iya haka Allah yabarsa ya horasa horo mafi tsanani ma kuwa, tabbas Zahrah itace rauninsa, rasata kuma shine abu wanda zaifiye masa komai ciwo acikin rayuwarsa, baisan wani irin zazzafar soyayya yakeyiwa Zahrah ba, ashe tun dama yaudaran kansa yayi ba sha’awarta yake ba sonta yake, amma kuma saboda wani banzan tunani da kuma banzar hujjan sa yasanya ya kasa yarda da hakan, idan yace zai misalta irin tarin yawan nadaman da yayi kawo daga randa ya yiwa Zahrah fyaɗe zuwa yau to tabbas yayi ƙarya, ya cutar da’ita, ya zalunceta, tabbas yasan bai kyauta mata ba, sannan kuma baiga laifinta da ta ƙishi ba tabbas shida kansa ya san cewa bai cancanci ta sake yarda dashi ba, saurin rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hannayensa da ƙarfi, bakomai ne yasanyasa yin hakan ba face tunowa da yayi lokacin da idanunsa suka rufe ya shigeta da ƙarfin gaske yanajin wani irin ihun da tayi amma saboda bushewar zuciya irin tasa haka bai saurara mata ba,, kansa yashiga duka da hannayensa biyu kamar mahaukaci, ihun da Zahrah keyi masa alokacin da zai keta mata haddine yashiga dawowa cikin kunnuwansa ji yake tamkar alokacin ne abubuwan suke faruwa,,, ihu yashiga yi batare daya sani ba, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu, Mum da shigowarta falon nasa kenan taji ihun Zaid na tashi daga cikin bedroom ɗinsa, cikin sauri hartana haɗawa da tuntuɓe tanufi ɗakin nasa,, kwance tagansa akan gado yaɗaura duka hannayensa akansa yana wani irin ƙara tamkar wani wanda aljanunsa suka tashi..3
STORY CONTINUES BELOW
“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, Zaid! Zaid!!” Mom taƙira sunansa cikin matuƙar ruɗewa,, girgiza sa Mum tashiga yi cike da ruɗewa sunansa kawai take ƙira, a tunaninta Zaid ɗin nata ya haukace ne, yanajin muryar Mom ɗinsa acikin kunnensa yatashi a zabure haɗe da faɗawa cikin jikin mahaifiyartasa, abun mamaki saiga Zaid nan na kuka tamkar wani ƙaramin yaro, ita kanta Mum kasa motsi tayi haka ta tsaya kamar statue, wai da gaske Zaid ɗin tane wannan, kuka fa yake, anya kuwa ba aljanune suka shiga mata jikin ɗa ba?.
“Zaid” Mum takuma ƙiran sunansa cikin murya me sanyi domin kuwa itama tuni ƙwalla harsun cika mata ido… “Please help me Mum, i don’t want to lost her!” abun da Zaid ke faɗa kenan yana kuka,, mamaki marar misaltuwa ne yakuma kama Mum wannan wace irin masifa ne ya ruski Zaid wace irin tsinanniyar soyayyace wannan datake shirin haukata mata yaro? lallai yazama dole tayi wani abu, bazata taɓa bari tanaji tana gani ɗanta ya rasa ransa akan wata ba, wai dama ashe haka so yake? idan kuwa haka so yake to sai dai muyi fatan Allah yarabamu dayin so me tsanani….
Kansa mum tashiga shafawa ahankali cike da tausayawa tace “Ka kwantar da hankalinka Zaid, kayi haƙuri kasamawa kanka nutsuwa, badai kana sonta ba?”
Kai Zaid ya kaɗa tamkar wani ƙaramin yaro.
“Insha Allahu zata zamo taka, zaku rayu da’ita rayuwa ta har abada, kadaina damun kanka kaji my son!”
Mum ta ƙare maganar cike da lallashi..
Kansa ya kwantar akan kafaɗan mahaifiyartasa lokaci ɗaya yashiga sauƙe ajiyar zuciya irin dai yaro ƙarami yayi kuka ya ƙoshin nan…. Bayansa Mum take shafawa a hankali sai gashi cikin mintunan da basufi 10 ba Zaid yasoma fidda numfashi a hankali cike da nutsuwa da’alama dai bacci ne ya ɗaukesa, Mum tana tabbatar da cewa Zaid ɗin yayi bacci ta tattaro duka ƙarfinta haɗe da zameshi akan kafaɗanta ta kwantar da kansa bisa kan pillow’n sa haɗe da ja masa bargo ta rufeshi, kallon fuskarsa Mum tashigayi cike da tsananin tausayinsa, tajima tana kallonsa kafun daga bisani tayi masa addu’a ta shafa masa akan fuskarsa, cikin sanyin jiki ta tashi tafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni……1
*Washe Gari*
Tun safe kwararriyar me zanen lalle wanda Dr.Sadeeq ya ɗaukarwa su Zahrah bayan yabiyata maƙudan ƙuɗaɗe tazo gidan,, zanen jan lalle me matuƙar kyau aka tsantsarawa Zahrah akan hanu da ƙafarta, abunka da farar fata take zanen jan lallen yafito akan fatarta yayi kyau sosai,,, lokacin da ta wanke zanen lallen nata hakanan ta tsinci kanta da sakin murmushi ita kanta sosai zanen yayi mata kyau gashi ya ƙara ƙawata farar fatarta gwanin sha’awa. Wayarta dake ringing ta ɗauka haɗe da karawa akan kunnenta, cikin wata irin kasalalliyar murya taji yace “Amaryata” murmushi tasakar masa me sauti haɗe da cewa “Umm” Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa yagyara zama haɗe da cewa “Ki ɗan bani aron minti 10 daga cikin lokutanki na yanzu inason ganinki” ya ƙare maganar yana wani lullumshe ido kamar wanda yake a gabanta. Ajiyar zuciya Zahrah tayi haɗe da cewa “Gani nan zuwa” tana aje wayar ta ɗauki wani haɗaɗɗen mayafi wanda aka masa ado da fararen duwatsu ta yafa ajikinta yayinda haɗaɗɗen gashinta dayasha saloon ya bayyana kansa ta cikin mayafin..
Tana fitowa tsakar gida ta kalli Husnah wacce yanzu ake zana mata nata lallen, murmushi tayi mata haɗe da kashe mata ido ɗaya, dariya suka sanya su duka domin sukaɗai suka san ma’anar hakan…. Murmushi yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya alokacin dayaga fitowarta daga cikin gida,,, buɗe murfin motar tasa tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama,, cikin murya me ɗauke da kasala ya amsa mata sallaman haɗe da maida kallonsa gareta. Murmushinta dake ƙara mata kyau akoda yaushe tayi masa haɗe da ɗan tsaida idanunta akansa,,,, shiɗinma kallonta yake batare dayace komai ba, azuciyarsa kuwa mamakinta yake ta yanda ta’iya tsaida idanunta akan sa a yau ɗin, bayan kuma yasani sarai batayi masa dogon kallo.
“Namiki kyau ne ƴan mata?” yatambayeta yana me duban kansa,, dariya ne ya kwace mata amma kuma saitayi saurin sanya hanu ta toshe bakinta,
“Wow! gaskiya wannan zanen lallen yayi kyau sosai!” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin kamo hanunta, sam shi bai lura da zanen bama sai yanzu,, saurin maida hannayenta cikin mayafin dake jikinta tayi haɗi da cewa “Sai an biya kuɗi me yawa sannan ake kallon wannan zanen” murmushi yayi me sauti, ba ɓata lokaci ya sanya hanu acikin aljihunsa, kuɗi yaciro wanda baisan ko nawa bane, ya ɗaura mata akan cinyarta.
“Karki hanani gani please” yafaɗi maganar yana me marairaice fuska,
“Naƙi wayon kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan” tafaɗi haka cikin sigar wasa.
STORY CONTINUES BELOW
“Laluma aljihunsa yayi dama da hagu amma kuma yaji babu ko sisi, kawai saiya marairaice idanunsa yana kallonta, dariya yanzu kam tashigayi, sai da tayi dariyarta ta ƙoshi sannan tace “Kasan baka da kuɗi kuma kakeson ganin zanen lallena?”
Jin shiru bai bata amasa ba yasanyata saurin ɗago kanta ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata idanu kamar wani wanda bai taɓa ganinta ba, murmushi kawai tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sosai takejin wani iri ajikinta idan yana kallonta.
“Zahrah na!” yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi. Zahrah bata iya amsa masa ba, sai dai ta dawo da kallonta gareshi..
Yabuɗe baki zaikumayin magana kenan wayarsa tasoma ƙara,,
“Hajiya”
shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, dakatawa da maganar yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa.. Hajiya dake zaune akan kujera cikin yanayi na ɓacin rai tace
“Kana’ina ne?”
“Ina wajen Zahrah Hajiya” yabata amsa cike da girmamawa.
“Kabar duk abun da kake kazo gida inason ganinka” tana kaiwa nan azancenta ta kashe wayar.
A hankali ya zame wayar daga kan kunnensa haɗe da sauƙe ajiyar zuciya kallon Zahrah yakumayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
“Hajiya nason ganina yanzu, ki riƙe wannan saboda hidimar walimanki na gobe, maybe bazaki sake ganina ba sai bayan na angonce!” yafaɗi haka yana me miƙa mata wasu kuɗaɗe masu yawa daya ciro daga cikin wata ƴar loka dake cikin motar.
“A’a ae bana buƙatar komai don mungama duk wani abun da zamuyi, kuma komai na walima yazama ready, sannan kuma inada kuɗi a wajena ka….”
“Shiiii kinsan banason yawan musu please ki karɓa kinji baby na, ki ajiye kobazakiyi komai dasu ba nasan zasu miki amfani wani lokaci” yafaɗi haka ta hanyar katseta daga maganar da takeyi batare daya bari ta ƙarisa ba,, badon ranta yasoba ta amshi kuɗin haɗe dayi masa godiya kana ta buɗe murfin motar ta fice, shima tada motar nasa yayi yabar ƙofar gidan, zuciyarsa cike da mamakin ƙiran da Hajiya tayi masa, Allah dai yasa ba wata matsalan ne takuma kunnu kai ba, idan dai har akan aurensa da Zahrah ne tofa shikam gaskiya sai dai kowama yayi haƙuri saboda ayanzu baijin zai iya sanja muradin sa…
Fuska ɗauke da mamaki Dr.Sadeeq ke cewa “tafasa aurena kuma Hajiya?”
“Badole tafasa aurenka ba, wace uwa ce zata yarda da irin abun da katsiro dashi? tun ma ba’aje ko inaba kana nuna banbanci ƙarara, gashi abanza ka jawo zubewar mutumcin dake tsakanina da Hajiya Furaira, yanzu da wani ido kakeso nasake kallonta!” Hajiya tafaɗi haka cikin ɓacin rai.
Sunkuyar dakai ƙasa Dr.Sadeeq yayi yana me hamdala acikin zuciyarsa da aka soke batun aurensa da Saleema, dama shi Allah yasani ko ya auri Saleema ba lallaine yakamanta mata adalci ba, saboda abun a bayyane yake yafi ƙaunar Zahrah fiye da kowacce mace a yanzu idan aka cire mahaifiyarsa dakuma ƴar uwarsa ta jini.
“Dama haka kakeso ai shikenan burinka yacika, gakuma kayan lefe dakuma kuɗin auren da kakai can sun dawo maka dashi, sai kaje kayi ta fama da wacce zuciyarka ta zaɓa ma ni tashi kabani waje !”
Sumi sumi haka Dr.Sadeeq yatashi daga gaban mahaifiyartasa cikin sanyin jiki yafice daga cikin falon…
Yana shiga ɗakinsa yasaki wani irin ajiyar zuciya, wayyo Allah shikam daɗi kasheshi, dama yafi kowa tunanin yanda zaman nasu zai kasance saboda shi a tsarin rayuwarsa bai da niyar auren mace sama da ɗaya bare yanzu daya samu Zahrah yasan cewa ita kaɗaima ta’ishesa rayuwa, yaji daɗin fasa wannan auren ƙwarai…
*Zaid*
Gaba ɗaya jikinsa yaƙi daɗi duk yanda yaso koda a daddafene yaje yaga Zahrah hakan yagagara, saboda wunin yau ma gaba ɗaya baiyishi cikin daɗi ba, kasancewar ciwon zuciyarsa yatashi yasanya Dr.Bilal ya dinga basa magani masu sanyasa bacci gudun kada ya matsantawa kansa da tunani, haka dai yanaji yana gani tashi zaune ma yagagaresa, haka ya kwana yana begen ganin Zahrah….
*Friday*
Kowa dake gidansu Zahrah shirin zuwa wajen walima kawai yakeyi, yayinda amarya Zahrah tasha kyau cikin wani haɗaɗɗen sari da aka ɓata lokaci wajen naɗa mata shi ajikinta, yauma dai meckup aka tsantsara mata akan fuskarta nagani na faɗa, take fuskar amarya Zahrah yaci gaba da walwali,, motoci Dr.Sadeeq yaturo suka kwashesu har zuwa inda za’a gudanar da walima,,, walima fa ya ƙayatar saboda Malami aka ɗauko na musamman yagudanar da wa’azi akan yanda ake zamantakewar aure, sanan kuma yaƙara da wa’azi me ratsa jiki harsaida amarya tayi kuka,, bayan anƙare walima ne kuma aka soma rabon abinci haɗe da kyaututtuka kamar su memo da kuma jaka wanda Dr.Sadeeq ne duk yayi su, sai dai babu hoton amarya da ango ajiki sai dai sunansu kawai. Walima fa yaƙayatar kowa sai dai yace Alhmdlh haka aka tashi a taron walima kowa yanacikin farinciki,, yayinda gobe asabar kuma take ɗaurin aure💃.Yauma dai kamar jiya agajiye take matuƙa, suna komawa gida ta yi wanka da ruwa me zafi sai alokacin ta ɗanji ta samu nutsuwa a jikinta. Kwanciya tayi luf akan katifarta haɗe da jawo wayarta tasoma buga game, tayi hakanne gudun kada tunani ya samu daman bijiro mta acikin zuciya…+
“Kinada baƙo a waje fa Zahrah” maganar da tafito daga bakin Husnah wacce shigowarta ɗakin kenan..
“Baƙo kuma Husnah?” Zahrah tatambaya cike da mamaki.
“Ƙwarai kuwa amma sai dai gaskiya inaga ba ya ɗaya daga cikin abokan Doctor, yakamata kije ki gansa dan naga kamar yamatsu dason ganinki” Husnah tafaɗi haka bayan tayi mawa kanta masauƙi akan katifar da Zahrah take kwance…
Cike da mamaki Zahrah tamiƙe tsaye haɗe da ɗaukar mayafi ta rufa ajikinta, hakanan taji tamatsu da taga waye ne ke neman nata…..
Tana fita waje tasoma raba idanu ko zata hango wanda akace yana ƙiranta, sai dai kuma bata ga kowa ba…
“Zahrah” taji anƙira sunanta daga bayanta,, da sauri ta juya don ganin kowaye.
Wani kyakkyawan saurayi handsome guy tagani tsaye a bayanta yana ta zuba murmushi, kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikekken ɗan gaye ne, kuma ɗan hutu, domin kuwa fatar jikinsa da kuma kayan dake sanye ajikinsa kaɗai sun isa tabbatar maka da hakan..
Takowa yashigayi gareta, har saida yazo kusa da’ita kafun ya ja ya tsaya, kallon kallo suka shiga yiwa juna, Zahrah kallon mamaki da kuma al’ajabin me ya kawosa wajenta take yayinda shikuma yakeyi mata kallon ƙurilla,, wani yawu ya haɗiya a maƙoshinsa bayan yagama ƙare mata kallo daga samanta har ƙasanta… “Zahrah ko?” yafaɗi haka yana me nuna ta da yatsarsa…
Kai kawai Zahrah ta’iya jinjina masa alamar “Eh” still amma kuma idanunta nakansa..
Murmushi yakuma yi mata haɗe da gyara tsayuwarsa “Naji daɗin ganinki ƴan mata, sunana Abid, nasan baki sanni ba amma kuma idan babu damuwa me zai hana muje mota sai muyi maganan, saboda nazomiki da wata magana ce me mahimmanci” yafaɗi haka yana me sake dubanta da kyau…
Kallon sa itama ta sakeyi sosai kafun ta ce. “Kafaɗi duk abun da zaka faɗa anan inaji, amma bana buƙatar shiga cikin motarka” ta ƙare maganar tana me ɗage kanta sama.
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi Abid yakumayi akaro na barkatai “lallai ba’a banza ba Zaid yakasa magance matsalarsa yarinyar akwai taurin kai” yafaɗi haka acikin zuciyarsa…
“I’m sorry bacutar dake zanyi ba, kada kiji tsorona, nazo miki da magana ne me matuƙar mahimmanci, nasan abune me wahala amma kuma keda kanki zakiso ace kinzamo silar ceto rayuwar da take shirin gushewa, nasan bazakiso ace ta sanadiyarki Zaid ya rasa rayuwarsa ba, kina da tausayi Zahrah, me yasa bazaki yarda ki aure sa ba?” abunda ya fito daga bakin Abid kenan..
Kallon baka da hankali Zahrah tashiga bin Abid dashi, da ƙyar ta’iya cewa “Bansan maganar Zaid bace takawoka wajena ba, da bantsaya ɓata lokacina wajen saurararka ba, don bazan ɓata lokacina abanza ba, dan Allah kufita a rayuwata, kacewa Zaid ya ƙyaleni na huta, domin kuwa ko maza sun ƙare a duniya bazan taɓa auren Zaid ba!” Zahrah tafaɗi haka cikin dakiya dakuma ɓacin rai…
“Ba gaskiya bane Zahrah, wannan maganar da kika faɗa ba daga cikin zuciyarki tafito ba daga bakinki tafito, kobaki furta ba raunin kalamanki sunnuna cewa kinason Zaid har yanzu, me yasa bazaki yafe masa ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, dan Allah Zahrah ki taimaka ki auri Zaid, haƙiƙa nida Zaid muna biyewa zuciyarmu muna aikata abunda baidace ba, amma kuma ina me tabbatar miki da Zaid ɗin dakika sani a yanzu bashine wanda kika sani ada ba, soyayyarki ta sanjawa Zaid tunani, soyayyarki ta juyamasa ƙwaƙwalwa, wallahi ke kaɗaice muradinsa acikin duniyar nan, Zaid baisan damuwa ba sai akanki Zahrah, yayi nadama me tsanani akan abun daya aikata miki, akan ki Zaid yafara sanin menene ƙunci, akanki yafara sanin menene ɗacin soyayya dakuma zaƙinta, haka akanki Zaid ya kasa fuskantar gabansa dakuma bayansa, akan kine kuma dalilinkine Zaid yakamu da ciwon zuciya me tsanani, ahalin yanzu Zaid yana acikin wani hali, Zahrah ke kaɗaice zaki iya sanjasa ki kuma ceto rayuwarsa please koba don nida Zaid ba kodan ceton rayuwarsa ki taimaka ki auresa!” Abid yaƙare maganar cike da raunin murya sosai yake matuƙar tausayin Zaid musamman ma dayaje yagansa yau, gaba ɗaya yafita hayyacinsa…
Murmushi me tsananin ciwo Zahrah tayi haɗe da sanya haƙoranta tacije lips ɗinta, kallon Abid tayi kana ta girgiza kanta
“Meyasa ku kazamanto mutane masu tsananin son kansu? Zaid rayuwarsa kawai zai rasa, amma ni gani da raina ta sanadiyarsa ne kuma narasa farinciki na, rayuwata tazamo marar amfani a gareni, ya katsemin farinciki dajin daɗi na, yakawo kansa gareni alokacin dayaga dama, yakuma sanyamin soyayyarsa alokacin dayaga dama, sannan yakuma ketamin haddina alokacin da yaga dama, yayimini duk wani abu da ransa keso alokacin dayaga dama, nima kuma yanzu nadawo mutum zankumayi duk wani abun daya dace alokacin dana ga dama, idan shi ne ya aikoka da waƴannan yaudararrun kalaman to kaje kasanar masa cewa kalaman naku basuyi aiki akai na ba, zaifi kyau kubarni nayi rayuwar aurena cikin farinciki da salama, domin kuwa gobe iwarhaka najima da zama matar wani insha Allah, inaso kuma kasani cewa najima da barin Zaid da Allah, haƙiƙa ya cutar dani, amma kuma dama hakan yakasance rubutaccen ƙaddarata ne wanda Allah ya rubuta, kaje kawai Abid bana tunanin sake burin haɗa rayuwata da ta Zaid!” hanu tasanya ta sharce hawayen da suka silalo daga cikin idanunta haɗe da juyawa tasoma tafiya…2
“Komai yana hanunki Zahrah idan har kikace afasa aurenki da wanda zaki aura aɗaura da Zaid nasan iyayenki zasu amince, shin maiyasa bazaki cika muku burinku ba? kinasonsa shima kuma yana sonki, ki amince ki aure sa, wallahi namiki alƙawari ko nawa kikeso aduniyar nan zan mallakamiki shi koda kuwa duka dukiyata kika buƙata nabaki zan baki, amma bazan tilastaki ba sai dai inaso kisani idan Zaid ya rasa rayuwarsa a yanzu kece SANADI” Abid yana kaiwa nan azancensa yabuɗe murfin motarsa, wata ƴar madaidai ciyar jaka ya ɗauko, takawa yashigayi harsai da yazo kusa da’ita kafun ya tsaya… “Ki amshi wannan jakan idan kika buɗe laptop ɗin dake ciki zakiga yanda Zaid ya koma A SANADI’N SONKI” Abid yafaɗi haka yana me miƙa mata jakar.. Tsintar kanta tayi da kasa ƙin karɓan jakar, yana bata jakar ya juya yayi tafiyarsa,,, har motar Abid ta ɓule Zahrah na tsaye sororo hanunta riƙe da jaka,,, saurin share hawayenta tayi, haɗe da nufar cikin gidan su,,, sumi sumi haka ta shige cikin ɗakinta, abun yayi mata daɗi sosai data iske Husnah hartayi bacci,, mayafinta ta cire haɗe da neman waje ta zauna, kanta ta kifa akan guiwowinta, damuwane cike azuciyarta, takasa sanin wani hali take ciki, kanta ta ɗago takalli jakar da tashigo dashi, da sauri tajawo jakar haɗe da buɗeta, a hankali ta zaro laptop ɗin dake cikin jakar, saida ta ƙarewa laptop ɗin kallo kafun ta buɗeta, tana danna wani madanni laptop ɗin takawo haske take kyakkyawan hoton fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin, mamakine yakamata ganin hotonta wanda batasan ma dashi aduniya ba, balle tasan yaushe ko wace ranace aka ɗauketa hoton ba, ƙurawa hoton nata idanu tayi tamakasa yin komai, bata ɗauke idanunta akan hoton ba har saida hasken screen ɗin laptop ɗin ya gaji dan kansa ya ɗauke.. Ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe haɗe da sake kunna laptop ɗin, batasan inazata shiga ba, bata kuma san mezata fara dubawa ba, hakanan ta ji zuciyarta ta ingizata da tashiga ɓangaren hotuna,, tana kutsawa ɓangaren hotuna, hotunantane suka farayi mata wellcome, mamakine yasake kasheta ganin hotunanta kaca kaca babu adadi acikin laptop ɗin, wanda ita a iya tsawon tarihin rayuwarta ma bata kasance mace meyawan sonyin hoto ba, yanzu haka ko hotonta ƙwaya ɗaya bata dashi acikin wayarta,,,, bata da me amsamata tarin tambayoyin dake ranta dan haka kawai saita shiga wuce hotunan nata, hotunan Zaid takuma cin karo dasu wanda saida gabanta yayi wani irin faɗuwa yayinda ƙirjinta yashiga dokawa da sauri.. da ƙyar ta’iya view ɗaya daga cikin tarin hotunan nasa, sanye yake da wandon jeans baƙi dakuma wata farar riga saikuma hular sanyi daya sanya akanshi yayinda kunnensa ke sanye da farin earpiece, yayi kyau matuƙa a hoton domin kuwa fuskarsa ɗauke take da wannan ƙawataccen murmushin nasa wanda yake ƙara masa kyau ako da yaushe… Ƙura mawa hoton nasa idanu tayi, saitaga tamkar shiɗinne da kansa agabanta, batasan sanda wasu hawaye suka silalo daga cikin idanunta zuwa kan ƙuncinta ba,, tajima tana kallon hoton nasa, haka kuma hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta, ɓangaren vedios takuma kutsawa, sai dai vedion farko da ta gani shine wanda yakusa tarwatsa mata zuciya, yakuma ɗaga mata hankali,, Zaid tagani kwance akan gadon asibiti ansanya masa oxygen, yayinda aka dasa masa wasu ƙarafan na’urori akan ƙirjinsa dai dai saitin zuciyarsa, da badon ɗan abu kamar computer’n dake gefensa wanda shike nuna alama yana da rai ba, to tabbas da saidai ace dashi gawa,,, wani irin sarawa taji kanta yayi, yayinda wani irin kuka yazo mata alokaci guda, saurin sanya hanu tayi ta toshe bakinta haɗe da rumtse idanunta, a hankali ta jingina bayanta da bango,,, hawayene suka shiga gudu wani na koran wani akan fuskarta,, duk yanda taso daurewa kasawa tayi saikawai tafashe da wani irin kuka me sauti, kuka take sosai yayinda ta rungume wannan laptop ɗin akan ƙirjinta,,,, kamar amafarki Husnah kejin gunjin kuka natashi acikin ɗakin, dayake ita ba me nauyin bacci bace yasanyata buɗe idanunta ahankali, aikuwa dagaske ba amafarki bane, kukan Zahrah taji raɗau acikin kunnenta, da sauri ta tashi zaune haɗe da dawo da kallonta inda sautin kukan ke fitowa,, sake waro idanunta tayi ganin da tayiwa Zahrah na kuka tsakaninta da Allah. “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Zahrah meyafaru kike irin wannan kukan?” Husnah ta tambaya cikin ruɗewa… Jin muryar Husnah acikin kunnenta yasanya, tataso daga inda take da sauri ta faɗa jikin Husnah ae kuma saita ƙara volume ɗin kukan nata,, kai Husnah ta dafe cike da tashin hankali, “Allah yasa dai bawani gagarumin abubane yafaru” Husnah tafaɗi haka acikin zuciyarta.18
STORY CONTINUES BELOW
“Kiyi shiru dan Allah Zahrah, kinga dai yanzu dare ne sokike kowa saiyaji gunjin kukan ki? kiyi shiru kisanar dani meke faruwa” Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da damuwa… Yau Zahrah tsintar kanta tayi da kasa daina kuka, ji ma take tamkar Husnah ingizata take da ta ƙara volume,, sororo haka Husnah tayi ganin Zahrah taƙi daina kukan, zame ta tayi daga jikinta haɗe da nufar inda aka aje musu ledan ruwa na pure water, guda ɗaya ta zaro acikin ledan haɗe da fasawa ta tsiyaya acikin cup,, dawowa tayi ta zauna haɗi dakai kofin ruwan bakin Zahrah, babu musu Zahrah ta amshi kofin takai bakinta, gaba ɗaya ruwan dake cikin kofin tashanye tas haɗe da aje kofin agefe, ajiyar zuciya tasoma sauƙewa akai akai amma na kuka,,, kwanciya tayi luf haɗe da sanya hanu ta dafe kanta dake matuƙar sara mata,,, idanu kawai Husnah ta zuba mata tana me mamakinta, gaba ɗaya aƴan kwanakinnan talura Zahrah ta maida kuka abinci da kuma ruwan shanta, ita yanzu hartama fara tunanin ko aljanune suka shiga jikin Zahrah’n,, bayan kamar minti goma Husnah taƙira sunan Zahrah,, amma kuma saitaji shiru Zahrah bata amasa mata ba, hakan ne yasanya tayi tunanin cewa Zahrah’n tayi bacci, raɓawa gefen Zahrah’n itama tayi ta kwanta, mintuna kaɗan bacci yakuma surarta, Zahrah na jin sauƙar numfashin Husnah nafita a hankali ta tabbatar da cewa Husna’n tayi bacci, ahankali ta ware idanunta dasuka cika tab da ƙwalla, sarai tanaji sanda Husnah taƙira sunanta, taƙi amsawa ne gudun kada ta tonawa kanta asiri, saboda batason wannan sirrin yafita daga cikin zuciyarta, har abada tafiso ta bunneshi ita kaɗai batare dakowa yaji koya gani ba, ada tana ganin cewa ita mahaukaciya ce datakeson wanda ya zalunceta, sai ayanzu ta sake tabbatarwa kanta cewa shi so babu ruwansa, idan zai shiga jikinka baya duba wani cancanta ko matsayi haka nan yake faɗa ma, ashe da fari tayi ƙarya da tace zatayi yaƙi da soyayyar Zaid a zuciyarta, ashe ba’a iya yaƙi da soyayyar da take acikin jini da tsoka,, ada tana tunanin cewa zuciyarta bata kyauta mata ba, ashe itace bata kyautawa kanta ba, yanzu ta gamsu cewa so ne ya lalata mata rayuwa ba wai Zaid ba, ashe so shine ya yaudareta, ashe so shine yaci amanarta, ashe Zaid bai aikata mata wani babban laifi ba So ne ya aikata mata laifi me girma, inama da ana ganin so, to da tayi masa roƙo takuma yi masa magiya akan cutarwar da yayi mata daya barta haka,, itakuma SO shine ƙaddaranta, ada ta ɗauka idan tafaɗawa mutane cewa tanason mutumin dayayi sanadiyar rugujewar rayuwarta, kowa zai ɗauketa mahaukaciya wacce batasan me takeyi ba, amma kuma ayanzu tagane cewa wanda duk ya mata kallon mahaukaciya akan soyayyar da takeyia Zaid, to ko kaɗan baisan menene SO ba, SO shine wanda ke sauyawa mutum tunani alokaci ƙanƙani batare daya shiryawa hakan ba, SO shine wanda ke makantar da idanun mutum yazamanto bayaji baya gani, haka kuma tasanadiyar SO wasu ke salwantar da rayuwarsu, SO shike sawa kabi wanda baidace dakai ba, SO shike sawa amaka wulaƙanci amma kuma gobe ka koma inda aka wulaƙanta ka, SO shike sawa mutum yazalunceka amma kuma bazakaga laifinsa ba,kuma koda ma kagani bazaka iya juya masa bayaba, SO yana da matuƙar haɗari sannan yafi kowani abu saurin ɗaiɗaita tunanin meyinsa, SO shikaɗaine abun da zafinsa ke narkar da zuciya,,,,SO shine babban jagoran zuciya haka kuma shine raunin ta,, hanu ta sanya takuma dafe kanta wanda takeji kamar zai zazzago ƙasa,, hmmm kamar dai yanda Zahrah taga rana haka taga dare bacci sam yaƙauracemawa idanunta…..9
(Kada kuga laifin Zahrah dan ta ci gaba da son Zaid, haƙiƙa Zaid ya cancanci Zahrah taƙisa mugun ƙi mawa kuwa, amma kuma SO bazai taɓa barin haka yafaru ba, wallahi Soyayya tawuce gaban kwatance, so babu ruwanshi da wai ancutar dakai ko ba a cutar dakai ba, shi so kaitsaye yake abunsa batare da yatambayeka shawara ba, nikam bana ganin laifin Zahrah dan taso Zaid domin shi so baya fita acikin sauƙi, sannan kuma zafinsa yanada matuƙar illa, ba’akanta aka fara ba, sau da dama zakuga namiji yana zagi dakuma dukan matarsa amma kuma duk da haka tanazaune dashi saboda tana sonsa, haka kuma saudadama zakuga Saurayi yayi amfani da soyayyar da budurwarsa takeyi masa ya yaudareta sun aikata zina, daga baya kuma idan ciki yashiga jikinta sai kuga yagujeta, saboda yasamu abun dayakeso daga wajenta, amma kuma idan harson gaskiya takeyi masa saikuga bata daina sonsaba duk dakuwa irin girman abun dayayi mata,, wallahi soyayyar gaskiya bata taɓa gushewa koda kuwa girman laifin da mutum ya aikata maka bazai misaltu ba, haƙiƙa idan banda sharrin SO babu wata mace da namiji zaiyi mata fyaɗe kuma ta dawo tacigaba da sonsa, wannan sharrin SO ne kawai wanda bashida magani😭 nidai nace ko guba baikai so hatsari ba, wallahi so mugune, inkun ganshi kukamaminshi kumai duka😰)2
STORY CONTINUES BELOW
Ƙarfe 2 na dare ciwon Zaid yatashi sosai, abun gwanin ban tausayi, zuwa yanzu kam ciwon nasa yasoma fin ƙarfin tunanin Doctor’s domin kuwa sai anyi tunanin cuta tayi sauƙi saikuma tadawo, yanzu haka bincikensu yanuna musu cewa zuciyarsa ce takumbura, gaba ɗaya hankalin Alhj Ma’aruf yakai ƙololuwa wajen tashi, Mum kuwa yanzu bata da aiki saina kuka dare da rana, hakanne ma yasanya Alhj Ma’aruf yanke hukuncin tattara Zaid ɗin sutafi Jermany, saboda ya ga abun yana nema yafi ƙarfin likitotinmu na nan, saboda koda yaushe Zaid cikin aman jini yake, lokaci ɗaya ya lalace yayi wani irin rama, kamar ma ba
Zaid ba…..11
Washe Gari (Asabar)
*ƊAURIN AURE*
Tun ƙarfe 8 na safe gidansu Zahrah yake acike yayinda ƴan uwansu na nesa suka soma hallara don ɗaurin aure,, hayaniya ne ke tashi kota ina acikin gidan…
Ɗakin Zahrah na garzaya don inga awani hali take ciki…
Kwance take akan katifarta yayinda duka jikinta ke rufe da bargo, amma duk da haka bargon bai ɓoye rawan da jikin nata keyi ba, karkarwa kawai takeyi acikin bargon yayinda jikinta yaɗauki zafin zazzaɓi zau..
“Kitashi kisha maganin nan dan Allah Zahrah, kinga fa babu amfanin zama da ciwo batare da kinsha magani ba” Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da lallami..
Kai kawai Zahrah ta’iya kaɗawa alamar “A’a bazata sha ba” komagana ma yanzu bata iyayi saidai kawai ta kaɗa kai, hakan yafarune kuma saboda ciwon kai me tsanani da ta tashi dashi a safiyar yau ɗin,, duk yanda Husnah takaɗa ta buga akan Zahrah tatashi tasha magani ƙiyawa tayi, sai ruwan hawaye dake ta fita daga cikin idanunta, dole haka Husnah ta ƙyaleta..1
10:30 tuni ƙofar gidansu Zahrah yasake cika da jama’a bamasaka tsinke, hayaniya ne kawai ke tashi tako ta ina, yayinda tsala tsalan motocin ango suka ƙaraso,, hmmm Dr.Sadeeq yasha kyau sosai cikin wata haɗaɗɗiyar gezina milk colour me matuƙar kyau da tsadar gaske, ɗinkin rigane da wando saikuma gare, amma kuma sunyi masa kyau sosai, yayinda ya ɗaura tsadadden agogo a hanunsa na dama, takalmin ƙafarsa kuwa ƙirar kamfanin GUCCI ne me matuƙar kyau,, ango fa yasha kyau iya kyau, sai yau nima nasake tabbatarda cewa shiɗin ma wani Handsome guy ne mezaman kansa, domin kuwa duk ƙwaƙwan mutum babu ta’inda zai kushesa, yahaɗu iya haɗuwa sonkowa ƙin wacce ta rasa😜, bakin ango fa yaƙi rufuwa sai murmushi kawai yake, yayinda abokansa keta tsokanansa,, shidai kawai murmushi yaketa zubawa, bazai taɓa iya misalta irin tarin farincikin dayake ciki ba, haƙiƙa yau yana cikin nishaɗi dakuma jin daɗi, yau takasance babban rana agareshi ranar da duk wani gauro da gauruwa suke jira, ranar da duk wani mai hankali da nutsuwa yake biɗar zuwanta wato RANAR AURE, shikam sai dai yace Alhmdlh yagodewa Allah mai kowa me komai daya nuna masa wanann rana… Baffa na hango shima yau cikin farinciki yake, yasha adonsa cikin farar shaddansa riga da wando dakuma gare, su uban amarya manya,,, 11:00 am dai dai dandazon jama’a suka shaida ɗaurin auren SADEEQ KHABEER SARDAUNA (Dr.Sadeeq) da amaryarsa FATIMA ADAM (Zahrah) akan sadaki naira dubu ɗari,, masha Allah ana kammala ɗaurin aure aka soma taya ango murna da Allah yasanya alkhairi, ae kuwa fuska asake haɗe da tarin annuri Dr.Sadeeq ke amsawa, hamdala kawai yakeyi acikin zuciyarsa shikenan Zahrah ta zama tasa mallakinsa halaliyarsa… Bayan angama musabahane kuma aka ɗunguma zuwa wani babban hotel wanda anan za’a gudanar da receiption….16
Lokacin da labari ɗaurin auren ya’isa ga kunnen Amarya wani irin faɗuwar gaba wanda bata taɓa jin irinsa ba taji ya rusketa, shikenan yanzu tazama matar Doctor, zuciyar tane tashiga bugawa da sauri sauri yayinda har ƙirjinta yasoma amsawa, take taji wani abu maikama da tsananin tsoro ya lulluɓe mata jiki,ae kuwa sai neman ɗan kuzarinta tayi ta rasa,jitayi gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mutu laƙwas kamar ansassare mata su,, sake duƙunƙunewa tayi acikin bargo tashiga rera kuka marar sauti, ita bata tsani Dr.Sadeeq ba ko kaɗan, amma kuma tarasa meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarta….
STORY CONTINUES BELOW
(Kuyi haƙuri Team Zaid wallahi nima Allah jikina gaba ɗaya yayi sanyi sai dai kuma kunsan ita ƙaddara bata taɓa sanjawa dole saitazo a yanda Allah ya aikota😭 yanzu haka jinake kamar ruwan jikina ya ƙare😥)9
Ƙarfe 2 dai dai jirginsu Zaid yatashi daga cikin garin Lagos Nigeria zuwa Jermany saidai shi Zaid sam baisan wainar da ake toyawa ba saboda baya cikin hayyacinsa kwata kwata, tunda suka baro Abuja har suka iso Lagos baisan inda kansa yake ba….1
Ɓangaren ango kuwa reception aka gudanar gangariya, anci kaji ansha fruits juice kowa cikin sa yayi haniƙan sai dai godiyar Allah da sanya albarka…
Amarya kuwa koda ruwane takasa sanyawa acikin cikinta, rashin lafiya sosai ya tsananta a gareta, zuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sundaina fitowa, sai numfashin wahala da take fitarwa ta bakinta kawai,, kasancewar anata hidima yasa babu wanda yadamu da cinta kokuma shanta, Husnah ce kaɗai ke tsaye akanta tana bata kulawa.
“Dan Allah Zahrah ba danniba kitashi inrakaki toilet kiyi wanka kizo kisamu koɗan sabon kayane kisanya kingafa zuwa anjima za’a zo ɗaukarki!” Husnah tafaɗi haka tana me ƙoƙarin tada Zahrah dake kwance zaune.
Da taimakon Husnah Zahrah taje banɗaki tayi wanka, koda tafito wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar atamfa Husnah ta bata tace ta sanya, babu musu tasanya saigashi kuwa rigan tayi matuƙar yi mata kyau ajiki, da ƙyar Husnah ta lallaɓata tashafa mata powder haɗe da man leɓe, sai kace wata ƙaraman yarinya,,, komawa gefe Zahrah tayi ta takure bayan Husnah tagama shiryata, still Husnah maganar abinci tayi mata amma Zahrah tasake bushe idanunta tace ita sam bazataci abinci ba batajin yunwa (Ninaga jarfa saikace wanda aka mawa auren dole 😏)…7
Ƙarfe 5 tsala tsalan motocin ɗaukar amarya suka shiga fakawa a ƙofar gidansu Zahrah motocine reras masu kyau har guda 15 suka zo don ɗaukar amarya yayinda motar da amarya zata shiga ta banbanta da duka sauran motocin don tafi duka sauran kyau..
Zahrah na zaune wata Aunty Ladi ƴar uwar mahaifiyarta wacce tazo daga Niger tashigo cikin ɗakin babban mayafi me kyau ta ɗauka haɗe da rufe Zahrah dashi, miƙar da’ita tsaye tayi cikin farinciki tace
“Allah yayi yauzaki tafi ɗakinki amarya muje ɗakin Inna’n taki aimiki nasiha”
aitun kan aƙarasa ɗakin Inna Zahrah ta ɓarke da kuka wiwi, (Wayyo Allah, wallahi duk rashin daɗin gidanku randa zaka barshi saikaji ciwo acikin ranka harna tuna da nawa ranan 😭🙈)1
Nasiha Inna da sauran matan dake ɗakin suka shiga yi mawa Zahrah akan tabi mijinta sauda ƙafa inayi bari na bari, komin ƙanƙantan ɓacin ransa ta gujesa, duk kuma wani abu datasan bayaso kada ta aikata, sannan kuma taji taƙi ji tagani taƙi gani, takuma riƙi haƙuri don shine tubali kuma gini haka ƙinshiƙin zaman aure, bawai idan anyi aure kullum soyayya ake ci ba, a’a watarana dole sai kunɓatawa juna, dole sai kunyi haƙuri kundanni zuciyarku tukun zamanku zaiyi daɗi, sannan kuma idan tasan tayi masa laifi kada tayi girman kai, tasameshi har ƙasa ta duƙa tabasa haƙuri, domin kuwa har kullum shine sama da’ita, yanzu amatsayin uba yake agareta bata da wani wanda yafishi,, wayyo Allah Zahrah tayi kuka sosai harda shiɗewa, Allah sarki sabo turken wawa duk da cewa Inna watarana tana hantararta amma yau duk saitaji babu daɗi tafiyan Zahrah’n saiga Inna tana hawaye tana jan majina, shikenan Inna kuma fa cin kaza ya yanke mata lol 😂.
Su Inna suna gama nasu nasihar aka garzaya da’ita wajen Baffa,, wayyo Allah Zahrah tana ganin Baffanta ta faɗa jikinsa haɗe da sake ƙara volume ɗin kukanta, Allah sarki take Baffa shima yasoma hawaye, daƙyar ya’iya daure zuciyarsa yayi mata nasiha, duk dai maganar ɗayace shine tabi mijinta sau da ƙafa takumayi masa biyayya akan duk abun dayace, sannan kuma tazamo me haƙuri akan dukkan komai, sannan kuma yaroƙi yafiyarta akan abun dayayi mata baya, tana kuka tace tajima da yafe masa kuma ita baimata komai ba, itama tanemi yafiyarsa yakumace ya yafe mata😭
Haka Aunty Ladi da Husnah suka fita da Zahrah tana kuka Husnah kanta kuka take, yanzu itama haka watarana za’a zo a ɗauketa daga gaban Momynta akaita can cikin wasu dangin😭…
Anasa amarya acikin mota sauran ƙawaye da ƴan uwa ma kowa yashiga motar da ransa keso, bayan komai yakammalane motocinnan suka gangara kantiti, atare suke tafiya wani abayan wani, sannan kuma komai anitse akeyinsa babu wani hargowa…1
Direct gidansu Dr.Sadeeq aka wuce da amarya, domin kuwa 8:00 pm nayi za a wuce wajen diner…
Abun mamaki tarba me kyau Hajiya tamawa amarya dakuma danginta, ko kaɗan bata nuna musu ɓacin rai kokuma tsana ba, sai dai su Aunty Raliya dasuketa binsu da wani irin kallo dake nuni da cewa baƙaunarsu sukeyi ba, ɗaki guda aka warewa amarya, balaifi ɗakin yayi kyau sosai, akan gado Aunty Ladi ta zaunar da Zahrah, mintuna kaɗan da shigowansu ɗakin wasu ƴan mata suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye dakuma na sha abun gwanin burgewa, gaskiya sun samu tarba na mutumci daga Hajiyar Doctor……
Wayar Husnah ce tafara ruri ganin wanda ke ƙiran nata yasanya ta ɗaga wayar bawani ɓata lokaci
“Bestie’n mu how far?” abunda wanda yaƙirata acikin wayar yafaɗa kenan..
Dariyane yakamata amma saita taƙaita dariyan haɗe da cewa “I’am fine sai dai gaskiya na gaji”
Murmushi shima yayi haɗe da cewa “Ina Amaryata Allah yasa tana lafiya, nayi kewarta sosai rabona da’ita fa tun ranan alhamis” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me gyara kwanciyar dayayi akan gadonsa…1
“Kamar kuwa kasan kainaketa so kaƙira, wallahi yau tun safe Zahrah taƙicin komai kuka kawai takeyi, gashi bata da lafiya temperature ɗinta ya hau sosai” Husnah tafaɗi haka ga Dr.Sadeeq.
“Subahannallah, keda su waye aɗakin?” Dr. yatambayi Husnah cike da zaƙuwa..
Kallon waƴanda ke cikin ɗakin Husnah tashiga yi kafun tace
“Gaskiya munada ɗan yawa”
“Oh my God to shikenan, please anjima kikawomin ita ina cikin boys guaters kinji”
“To shikenan zan kawota insha Allah”
Daga haka suka kashe wayar murmushi kawai Husnah tayi bayan ta’ajiye wayar tata gaskiya azamaninnan idan mace tasamu wanda ke sonta kamar irin sonda Dr keyiwa Zahrah yakamata ta riƙeshi da kyau hanu tara tara domin samun irinsu wahalane dashi, saboda yanzu zuciyoyin yawancin mutane duk taɓaci da yaudara………