SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 14

SILAR GIDAN AIKI




CHAPTER 14



Nazeefa na ta soma tafiya cikin unguwar, kowa se kallonta yakeyi, Dan ta koma abun tausayi sosai, KO Ina tabi aita maganarta, Haka tai ta tafiya har ta shugo GRA
Gidage masu kyau ta fara gani, Dan haka tai ta shiga tana tambayan ko za a dinga musu wanke wanke da share share kowa se yace akwai masu aikin, Wani gidan ma idan ta shiga korarta akeyi, hakanan ta hakura ta shiga cikin unguwa sosai +

Kallan yanayin unguwan tayi chan ta hango wata mata tana zaune kamar hajiya taga Mutane sai zuwa wajenta sukeyi, Dan haka Nazeefa ta nufa wajenta

A gefe ta tsaya rike da yan kayanta a hannu, Seda ta bari kowa ya watse sannan taje wajen matar tace Dan Allah ki temakeni ni bakuwace!

Matar kallonta tai daga sama har kasa tace” To amma fa kinyi amma baki goge sosaiba, Nazeefa tace” Banganeba

Matar tace” daga ganinki baki waye ba, Tana tsaye a waken saiga wasu maza biyu suka gaisar da Hajiya sukace wannan fa? Angama ciniki da itane? Dayan yace tamunfa

Nan Take Nazeefa tagane abunda suke nufi tace Innalillahi, Allah ya shiryeku tai maza ta bar wajen, dayan yace kaji Yar kauye Ki tsaya Ki kwasa arziki bazakiba

Nazeefa da karfin hali tace Arziki Idan na iskancine banaso tai gaba abunta tana hawaye tana addu’an Allah ya Kara tsareta damu gaba daya

Wata Mata tagani tana soya dankali ta lalubo 30 naira dinta tace abata

Matar ta amsa kudin ta mika mata, Nazeefa waje ta samu ta zauna taci, dakun ganta kunsan ta Fara fita hayyacinta, gashi bata sama Wajen rabawa ba, hakanan take bi gida gida tana bara idan dare kuma yayi ta sama zauren mutane tai bacci

Haka dai rayuwarta ta kasance cikin kunci da tashin hankali

*****
Bayan Kwana biyu, mahaifiyar Haleema ce ta kintsa tsab tazo gidan yarta, Haleema tai farin cikin ganinta sosai, nan takawo Mata drinks da abinci Tasha ta koshi sannan suka wuce bedroom

Nan take tambayarta yaya batada ciki ne ko meya faru, ita taji shuru gashi ankusan 3years da auransu ita fa hankalinta ya Fara tashi saboda tasha Mata maganar se tace Time ne beyiba, to yanzu kam ya kamata ace tanada ciki kodan cikan wani buri nasu

Haleema ne ta gyara zama tace” Mum I told you bansan haihuwa yanzu, Kinsan Nayi planning tun kafin nai aure

Wani wawan Mari mamanta ta sakar mata tace” Shikkenan kin kashemu, Planning fa kikace

Haleema rike kumatunta tayi tana hawaye ta tsana kanta!

Mahaifiyarta tace kinyi shawara dani? Yanzu sai kiji ance za ai miki kishiya Haleema kin kashemu

Tace mum kiyi hakuri zange a cire mun dama implant ne? Tooo tace mata tana kallon dakin se a lokacin ta Lura da yanayin Haleema duk ta kode, ce Mata tayi meya faru dake ne ko bakyajin dadine?

Haleema tace mum lfyna lau Mubeen mugune, cutana yakeyi ni Zan biki gida

Harararta tayi tace uwarshi din nanan? Tace Eh, Hajiya ta tashi fuuuuuu se sasan Maman mubeen

A falo ta tarar dasu Faeez da faeeza sundawo Hutu, shugowa tai KO sallama,

Mamansu Mubeen tana ganinta tace” Hajiya zauna mana

Tace bazama ya kawoni ba, kashedi nazo nai muku, ki sanar da danki inason ya’ta na aurar mai da ita so banga dalilin da zai dinga wahalar mun da ita ba, yarinta gakyau da diri duk an sukurkutarmun da ita, kijamai kunne tom

Bata jira amsar taba tai ficewarta ta buga musu kofa ji kake ghammm

Maman Mubeen Dan takaici kasa magana tayi

Faeeza kuwa sarkin rashin kunya tace jibeta da kafa kamar agwagwa mtsww wlhi senayi maganin Haleema ita zata zugata

Faeez na tsaye yace duk kuyi hakuri wata Rana sai labari, Allah sarki Nazeefa nasan dake yaya ya aura bazai dama matsalar nan ba

Sudai binshi da ido sukai,Kowa da abun da yake hasashe a ranshi

Maman Haleema na zuwa sasanta Kudi tace ta bata, Dan haka ta shiga dakin mubeen ta dakko kudi kusan 100K ta kawowa mamarta tace yayi kyau ni Zan tafi

Bayan tafiyartane Mubeen ya dawo gida yaje sashen mamanshi ya gaisheta, zayyanamai duk abunda mahaifiyar haleema tayi, abun ya bashi mamaki sosai yace karta damu yasan mezaiyi, Nan ma ta Kira dad din Mubeen ta sanar dashi duk abunda ake ciki yace dama next week zai dawo zasusan abunyi dukansu tace Alright

Mubeen ne ya dawo sasahenshi ya shige daki yai wanka yazo kitchen ya soya kwai ya hada tea yasha abunshi

Kiran Abokinshi yayi Dr Bashir yace” yana gida yazo ya amsa sakon, Tashi Mubeen yayi ya bude akwatinshi Dan daukar kudi, Zare ido yayi yace Kodai banan na ajiye ba……..Dube dube yakeyi sosai yaga dai ba alamun kudi a wajen, Zare ido mubeen yayi yace kodai ba anan na ajiye ba? Kara birkita kayanshi yayi yaga beganshi ba, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yace” dafa kanshi yayi yace tabbas ba kowa zai dauka kudin nan ba Haleema ce!
Shiga dakinta yayi yace” bani kudin da kika dauka, Zare ido tayi hade da dafa karji tace” bangane inbaka kudinkaba dama ka aramun ne? Amsar data bashi yasa ranshi ya kara baci sosai, Ya sharara Mata mari sau biyu dama yanada cikinta

Kuka ta Fara, yace KO kukan jini zakiyi kiyi sekin fitomun da kudina

Suna cikin hakane sega Dr bashir yana knocking kofar, Kara bigeta yayi sannan ya rufo dakin yasa key yazo ya bude ma Dr Bashir

  Zama a falo yayi, mubeen ya tashi ya dakko Mai ruwa da abunsha ya kawomai, yasha, Yace plz kabani sauri nakeyi, Ciro waya Mubeen yayi yace bani account number din nan take yamai transfer, Yacemai Nagode sosai, har waje ya rakoshi

    Seda yaga yabar gidan sannan ya dawo, ya bude Haleema yai Mata kacha kacha kuwa yace bazai Iya zama da barauniya ba, shi ya gaji gaskiya, Nan Take ya saketa Saki Uku batare da yayi shawara da kowa ba, Kurma ihu tayi da seda sasan mahaifiyar mubeen sukaji suka fito

Nan suke tambayar Meya faru Mubeen ya sanar dasu Abundatai Mai shine ya sake ta, Alhamdulillah mahaifiyasu tace” Shine daidai sai Ki Kira uwarki ki sanar da ita

Kuka Haleema takeyi sosai tazo gaban Mum tana cewa plz taba Mubeen hakuri,

Maman Mubeen ta kalleta tace se yau kikasan dani? Shekaranki uku anan gidan befi sau biyu sukazo Kika gaisheniba, Kara kuka takeyi sosai, Mubeen kuwa tasowa yayi yace ta Kama gabanta ko yai Mata duka tunda batada mutunci

    Hakanan ta tattara kayanta aranar ta koma gidan uwarta, koda ta koma bata tatar da mahaifiyarta ba ta sama waje tai tagumi ta Zauna…..wannan kenan

*****
    Mansur ne ya kira Abdallah yace” mai ya shirya gashinan zuwa ya daukeshi, yace alright bakomai sai kazo
  Part din mahaifiyarshi yaje ya gaisheta yace Mum nagama shiri yanzu zamu tafi akwai abunda nakeson yine kamar yanda na fada miki, Idan munada lokaci sosai zanje Chan gida na gaishesu
   Mum dinshine ta kura Mai ido tace” OK Beloved son amma da kabari driver ya kaiku saboda nisan hanya fa

Mansur yace Mum karki damu ba yau zamu wuce direct ba inajin zamu sauka a wani garin Mu kwana gobe Mu dauke hanya tace OK hakan yayi sosai, Allah ya tsare yace Ameen
    Fitowa yayi ya shiga mota be tsaya ko inaba se gidan Abdallah

Koda ya shiga yace Amarya ba zama zamui ba nazo Zan tafi da angonki an bani dama? Dariya tayi tace wane ni sai kundawo Allah ya tsare a kula da hanya, sannan Ta kawomusu abinci tace gashinan idan kunji yunwa Ku tsaya kuci

  Mansur yace woo kinason mijin nan naki, Abdallah kallon matarshi yayi yai mata kiss a daidai lokacin Mansur yakai idonshi, saurin kauda Kai yayi yace” uhm Nima na gaji zanyi auren nan na huta

***
Da daddarena Mum din Mansur turaki and his beloved dad suke hira, Mum tagumi tayi tace” kaga yakamata Mu matsawa Mansur fa ya fito da matar aure shekaru na tafiya, Dad dinshi yace nima abun na raina Bari yadawo Tace Ok….

    Kwanan Su Mansur 3 a garin, Kullun Matar Abdallah cikin waya da text suke ciki, Mansur yaga kamar ya toyemai hakki, So basukai ga zuwan garin Yan uwan mamanshiba sukace gobe zasu dawo cos yaga Abdallah a takure yake, Abdallah kuma yayi yayi dashi akan suje yace aa se Wani time

Tunda zasu dawo gaban Mansur se fadi yakeyi, Addu’a yakeyi amma gabanshi se Kara tsananta fa bugawa yakeyi, Kawai yace khairan inshaa Allah,

Abdallah yace meye yace bakomai, Nan suka dauka hanya suna tafiya suna hira, Abdallah ya Fara gyangyadi,

Mansur ganin Abdallah ya fara bacci se ya Kara gudun motor, Chan ya hango Kamar wata mata a tsaye a titi, Addu’a yake tayi dai Dan gabanshi Kara bugu da sauri yakeyi, Karasowa yayi ahankali lokacin Still Abdallah na bacci, Kurma Ihu Mansur yayi Allah yasa be sake sitiyarin motar ba da sai sunyi accident, Mansur  Cikin Ihu yace Aljanah, Aljanah a kunnan Abdallah, A firgice ya tashi yace tana Ina? Ganin Mansur ya tsayar da motor yasa Abdallah ya fito ya turashi dayan site din, Shi kuma Abdallah ya zauna a mazaunin Driver!

Karema Macen da Akace Aljanace Abdallah yayi saiyaga Tabbas Aljanar Mansur ce! Faduwa tayi a wajen tace ku temakeni wallahi ni mutun ce ba Aljanah ba

Abdallah ne da karfin hali ya fito amma bakinshi addu’a yakeyi, Tsugunnawa A gabanta yayi taga tabbas itace! Allah Mai iko yace

    Mansur kuwa Tsorone ya kamashi ganin Abdallah ya fita shima yai kokari ya fito, Karema fuskarta kallo yayi sosai yace” Abdallah she’s d one, Aljanace meyasa ta biyomu nan? Yana magana tsabar tsoro seda yai in’ina Dan maganar bata fito da kyau ba

Kubani kuwa tace” Zan mutu, Mansur besan sanda ya tashi ya bude mota ya dakko ruwan faro ba, Idonshi cike da hawaye!

Abdallah kuwa in banda ikon Allah ba abunda yake cewa!! Tana gama shan ruwan ta fadi a kasa sumammiya, Mansur and Abdallah na kewaye da ita, Mansur ne Ya kalle Abdallah yace” me yakamata muyi? Kodai Mu kaita asibitine yana magana muryarshi na rawa! Wait Mugani Abdallah yace”

Suna tsugunne a wajen kusan 30mins sukaga Nazeefa bata farfado ba Dan ta mugun galabaita, Abdallah ne ya taba Mansur Dan kallon da yake ma Nazeefa ya baci kamar zai cinyeta, yace Mu kamata musata cikin muto mukaita asibiti,

“Mansur ne ya sake baki yana kallonshi kamar wani tababbe Dan shi kwata kwata hankalinshi be jikinshi, Abdallah ne ya sake magana yace MANSUR, What’s wrong with you? I said we should take her to the hospital kayi shuru! Mansur yace OK let’s go, daukarta sukai suka sata a back seat hade da kayanta, Sannan suka shiga motor suna tafe Abdallah na driving

Mansur ne ya hade rai wai Dan me Abdallah zai taba ta, nan take yaji yana kishin Aljanar sa, Abdallah ya lura da hakan yai banza dashi

Tafe suke Suna hira jefi jefi, Nazeefa ta farka, Tace” Dan Allah Ku kasheni, na gaji da duniyar nan, A tare suka hada baki sukace astagfirullah, baiwar Allah meya faru haka?

Nazeefa kuwa inbanda kuka ba abun da takeyi, sunyi tafiya me Nisa tace Ku saukeni anan! Mansur ne ya juya sukai 4eyes dashi nan take jikinta ya Fara rawa, Tace Aljani!! Shikkenan nasan rayuwata tazo karshe, me yasa kake so ka cutar Dani, menai maka, ba rannan na baka hakuri ba

Dukansu was surprise da sukaji maganarta, Abdallah aranshi yace” Lalle ikon Allah sai kallo, they are meant for each other
   Cuku cuku ta farayi ta naso ta bude kofar ta fita, waigowa sukai sukaga alamun fita takeso tayi, then Abdallah yai locking all d doors,

Mansur kuwa se kallonta ta mirrow yakeyi, da sun hada ido da Nazeefa ta harareshi ta murguda Mai baki, Wata sa’in har kunkunai takeyi, Shi dai sedai yai smiling

Abdallah kam Sam be Lura ba, Se faman driving dinshi yakeyi

Sun shugo cikin unguwar su, Abdallah ya daga glass din motor, Allah yasa me bakin nan ne, Wanda sedai na ciki ya hango na waje badai na waje ya hango na ciki ba,

Abdallah ya kalle Mansur yace” yanzu ya zamui? Kaga I can’t take her to my house saboda matata, yanzu ya zamui? Mansur yace” dama nace ka tafi da itane? A wajena zata zauna mana! Gabantane ya fadi tace na shiga uku

   Abdallah kuma binshi da ido yayi becemai komai ba

Nazeefa kuwa tai banza dasu, aranta tana tinanin wani Abu,

Har gida Mansur ya Kai Abdallah amma be shiga cikin gidan ba yace agaida madam, Abdallah yace” plz abokina take care ni banso Ace zaku zauna da ita ba why not ka sanar da mummy? Kasan zaman mace da namiji se ahankali KO?

M.T yace” look into my eyes ni Dan iskane KO katabajin wani Abu makamancin haka? Abdallah ya girgizakai yai shigewarsa, Itadai Nazeefa na kallonsu ta glass batasan me suke tattaunawa ba

Mansur ne yazo mazaunin driver, ya Fara driving ahankali, Nazeefa kuwa in banda addu’a ba abun da takeyi,

Tafiya ya soma tace” malan Ina zaka kaini? Waigowar da yai suka hada ido taji ta kasa karasa maganar Da zatai, Kallon jikinta tayi taga riganta duk datti, gasu sun yage, nan take kunya ya kamata, Aranta tana tambayar kanta meyasa bataji kunya da dayan nanan ba? Meyasa ta kasa karasa maganarta? Waigowa ya karayi yace” Inajinki me kike cewa?

Murza Hannunta ta tafari tace” bance komai ba, Mansur kawai Smiling yayi yaci gaba da driving,

Wani babban PLAZA suka nufa, yace Mata yana zuwa, Ya kulle duka motor Dan karma tace zata Fito

Fitan dayai tabi bayanshi da kallo tace” wow Guy dinnan ya hadu fa, Ashe akwai irinsu a duniya!

Wani babban shago yaje ya siyo Mata riguna dogaye a kalla Kala 10, da takalma da jakunkuna se hijab, da kayan kwalliya da turaruka masi kyau ya dawo yasasu a bot,

Shiga motor yayi ya duba agogon hannunshi yaga 6Pm ya kusa,

Nazeefa ce tace an Kira wayarka, dubawa da sauri yayi yaga Sweetheart❤ Ohh God yace Sweetheart ne bari nai sauri

    Yana cewa Sweetheart taji duk ranta ya baci, taji haushinshi for no reason

Tafiya kadan sukai suka shugo wani layi, Wanda kana ganinshi kasan KO a masu kudin se Manya Wanda suka Kama kasa

Wani babban gida taga sun nufa yana horn, aka budemai, Mansur yace” kinga wanchan gidan? Muna zuwa daidai wajen ki tsugunna ki sauri ki shiga

Kallonshi tayi tace tab a mike Zan shiga se kace munafuka KO wata Yar iska! Hade rai yayi yace nadai fada miki

A daidai wajen yai parking yace ki fito! Kamar xata fito a tsaye setaga hallacin da yai Mata qila ta silar shi ta sama jin dadi, se tai yanda yace Mata kawai

Tana shiga yace” Alhamdulillah, karaf a kunnanta! Kallonshi tayi ido cikin ido tace Hmmmmm

Koda Nazeefa ta shiga part dinshi, kulle part din yayi dankarma masu aiki suce zasuje Su gyaramai part din suga wata, Nazeefa kam dataga yasa key samun waje tayi a tsakar gidan ta zauna tai tagumi hawaye se zubo Mata yakeyi tace wani irin rayuwane wannan?

Yanzu haka rayuwata zata kare a wahala, wannan daga gani mugune, tsaki tayi seta farabin gidan da kallo ya hadu sosai

Muje Zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *