SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 17

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 17

Hajiya Haleema tun a cikin motor ta Fara kuka tana yau na shiga uku, yan sandan da suke tare sukace idan baki mana shuru ba sai kin sani + mubeen Kuwa, hankalinshi gaba daya ya tashi, aranshi yace ace arzikin Su Nazeefa ne Innalillahi wa inna ilahir rajiun, hawaye suka zubomai se addua yakeyi Dan yasan ba wanda zai iya kwatansu sai Allah, bare irin wulalancin da sukaiwa Nazeefa **** Bangaren Hajiya Zainab kuwa Maman Mansur sun koma gida, zama sukai gaba dayansu a falo se tattauna al’amarin nan sukeyi, lalle yanzu duniya ba gaskiya, Uwa daya Uba daya sai ka cutar da Dan uwanka! Alhaji yace” kibari kawai Yanxu yazamui? Hajiya Tace yanzu maganar na wajensu ai, duk yanda sukeso haka za’ai dasu Mu dama Namu temako ne kawai Sannan Alhaji ya kalle Mansur yace” Sannu da kokari, kayi hakuri da zargin da mukai maka, Mansur yace” haba dad ai hakan da kukai daidaine, yanzu ai da temakonku kuma, Ina alfahari daku sosai da bani goyon baya, Allah ya Kara maku lafiya Hajiya tai smiling itama Tace that’s my son, Tarbiyan da muka baka still yananan, keep it up. Allah kuma ya Kara tsaremu baki daya yace Ameen *** Bangaren Su Nazeefa, Sun shiga gidan se kallo suke tayi, Malan Nalado yace sannu ya’ta kinsha gwagwarmayar rayuwa, kiyafe mana please, Umma Hafsatu kuwa rungumo Nazeefa tayi tana kuka itama tana mai Kara bata hakuri, Tace bakomai Haka Allah yaso yanxu finally gashi na hadu daku! Baba megadi kuwa se zirga zirga yakeyi, shima da yaji maganar kasa sukuni yayi. Yace tabbas Allah da girma yake, Yar aikin da tazo gidan Ashe gidan wan mahaifintane uwa daya uba daya hmmm

**** Kwanansu Biyi a prison, duk sun fitaa hayyacinsu Nazeefa kuwa Kullun dakyar take bacci Dan tinanin Mansur hanata sukuni yakeyi, abincima dakyar take ci, Seda mahaifiyarta ta lura da hakan take tambayarta me yake damunta sedai Tace Mata bakomai Bangaren Mansur kuwa, Shima hakan take, Dan 2days dinnan dabe gantaba jinshi yake kamar a daure, Cos he’s missing her irin Sosai dinnan Washe gari bayan kwana uku! Yai wanka ya kintsa yace wa mum dinshi zaije gidansu Nazeefa suji ya za’ai da mutanan nan Tace kamar ka shiga raina, ya kamata muji ta bakinsu, Dan yanzu komai yana hannunsu, amma dukda bansan hukuncin da zasu yankeba ba please ka basu hakuri karsu dau wani mummunan mataki akansu Dan Allah Mansur yace OK Mum zanje duk yanda ake ciki Zan sanar daku, Tace alright ba komai, Dad dinkama tun 6 ya shirya sunada meeting a Abuja driver ya kaishi, Yace OK naga call dinshi kam this morning tace yauwa Saika dawo A kula da hanya please, kiss yai Mata a kumata yace mum inshaa Allah

Mansur ne sanye da kayan track suit, (Sport wears) Black a jikinsa saboda lokacin sanyine yayi kyau sosai, sannan ya dauko motar mamanshi Fara Sol Tada motor yayi, me gadi ya bude Mai gate ya fita, tunda ya fita yaji gabanshi na mugun fadi yace Allah yasa lafiya Ameen Tafe yake a hankali har ya Isa gidansu Nazeefa, knocking yayi mai gadi ya fito Yace Dan Allah ya kiramai Nazeefa, Yace angama ranka shi dad’e Da sauri yaje dakin ya samesu suna zaune suna having break fast around 10:00AM, Yace Wai Nazeefa tazo inji Mansur, dasauri ta tashi Tace” OK je kacemai ganinan zuwa Shiga daki tayi ta dakko hijab dinta, tace Mama Ina zuwa wannan mutumin ne daya temakeni suka ce madallah Ki gaishe Shi tace zaiji Fita tayi Cikin natsuwa abunta Hijab dinta har kasa! Shi kuma Mansur yana cikin mota yana kare Mata kallo ta glass, yana gainta yaji hankakinshi ya kwanta, Amma kirjinshi nata bugun uku uku Bude mata motor yayi yai Mata alamu data shugo, Dag’a kafada tayi wai ita bazata shugo ba, Dan haka shi ya fito, Yana fitowa sallama yai Mata ta amsa Kowa yai shuru Dan gaba dayansu sun tsinta kansu cikin kunya🤸🏻‍♀ Bude mata motor yayi yai Mata alamu data shugo, Dag’a kafada tayi wai ita bazata shugo ba, Dan haka shi ya fito, Yana fitowa sallama yai Mata ta amsa + Kowa yai shuru Dan gaba dayansu sun tsinta kansu cikin kunya

Sundau kusan 15mins ba wanda yacewa kowa komai, Mansur kuwa folding din hands dinshi yayi yana kallonta kamar yau ya Fara ganinta Dan wani tsatstsareta da ido yayi KO kiftawa bayayi, Jan hijab dinta tayi ta rufe fuskarta Tace Dear kallon ya Isa haka mana cikin wani irin murya tai maganar Smiling Mansur yayi yace toh gimbiya kece kullun kara kyau kikeyi balle na kwana biyu ban gankiba, kinsan yanda naji kuwa? Kara jin kunya tayi sosai ta kara jan hijab dinta ta rufe fuskarta sosai Mansur kuwa bin ilahirin jikinta da kallo yayi a ranshi yace Masha Allah Nazeefa kinsan me ya kawoni kuwa? Ki bude fuskarki muyi magana! Tace OK Nan take ta bude suna hada ido ya daga Mata gira yai smiling yace I love you a hankali, labenshi tabi da kallo dukda ahankali yace sai da ta gane abunda ya fada Smiling kawai tayi Dan tanajin shi sosai a heart dinta “Yace huh nagaji da tsayowan nan KO Mu koma cikin mutane gimbiya? Batai Mai musu ba Tace OK ranka shi dad’e Bude Mata yayi ta fara zama sannan yaje ya bude shima ya zauna, Tada motor yayi yace akwai maganar da zamui dake ne But zaifi kyau in muna tafiya, Kin amince? Saboda son da taji tanamai da tsintar kanta cikin wani irin yanayi idan suna tare batasan sanda tace Na amince ba! Kallon lips dinta yayi sanda tai maganar yace yeah that’s my baby! Tafiya suka farayi a slow irin tafiyar masoya, yasa wani sauti me dadi a cikin motar Ga wani kamshin turaren da ke tashi a cikin motor, suna tafe yana Mata hira jefe jefe tana bashi amsa, Da yaga surutun nashi yayi yawa se yai shuru Yaci gaba da driving dinshi! Ta bude baki cikin shagwaba Tace why the silent kuma? Yace naji kamar Ina damun gimbiyar tawa ce Tace laaaa a’a ni bance haka ba “Yace OK Dear Samun waje yayi yai parking, Yace dama akwai maganar da zamui dake, akan maganar Su Wa ennan nan (baban mubeen) da iyalansa ya kamata kuce wani abu

Tace tabbas hakane Kagani for now bazance komai ba se abunda iyayena suka yanke, Yace hakane idan kin koma gida sai kui maganar duk yanda sukace ba damuwa, Amma mutanan nan ko hmm Allah ya shiryasu, Tace kabari kawai Ameen, kowa son zuciya yamai yawa, Tace wlhi kuwa Allah ya Kara tsaremu tace Ameen Sai ku koma gida ko? Yace no inaso kidan rakani wani wajen ne dad ya aikeni, Tace OK muje tom Wani babban plaza suka sauka, Duk inda suka wuce aita gulmarsu ace sun mugun dacewa, Dan tafiya suke suna hira irin hiran nan na soyayya da shakuwa. Wani babban shagu suka shiga, yace a zaban Mai atamfofi guda 10, shadda ma guda 10, masu kyau se takalma da hijabai da huluna Haka aka za6an Mai masu kyau ya basu kudin suka kama hanya, Still yace tayi hakuri ta rakashi wajen tailor din da ke masu dinki Tun daga nesa tailolin suka hango motar Hajiya suna azama itace sai washe baki sukeyi Dan sunsan zasu sama kudi gashi kwana biyu shagon duk basu sama aiki ba so a yunwace suke Suna ganin anyi parking sukazo suka tarbeshi, Sallama sukai Mai ya amsa sannan ya bude boot suka kwasa kayan suka Kai cikin shago Yaran shagon kuwa suna ganin Nazeefa sai gaishe da ita sukeyi, A ciki har wani yace Ya Alhaj kayi matane bamuda labari Murmushi yayi ya kalle Nazeefa itama maganar ya bata dariya ta murmusa, Mansur yace itadai Zan aura inshaa Allah Sukace Allah ya sa, Gaskiya kun dace! Allah yakaimu da rai da lafiya, gaskiya ya Alhaj daga gani zakai sa’ar mace Mansur ya biyesu yace Allah KO? Sukace ai daga Fara’arta, Itadai Tace Allah ya shiryaku tai fece warta a shagon ta shiga mota Yace ga kaya nan irin na yan tsofaffi zakui musu na iyayantane, ya musu kwatancen yanayin jikinsu sukace Angama ya Alhaj Da zai tafi ya basu kudin aikinsu sosai, sannan ya Kara musu kusan 3k KO wani mutun daya, suna ta samai Albarka, yana fita suka dakko kayan suka Fara aikinsu…. Kallon agogo tayi taga kusan 2 hours sukai Tace huh please ka kaini gida, Kar ace na dade Dan Allah Kara sonta yaji ya shigeshi, da ba wani dadewa sukai ba Amma ta damu Su koma gida da wasu yan matan ne kuwa KO a jikinsu

Yace tabbas inshaa Allah zanyi dacen Mata kuwa, speed na motar ya Kara sai gasu a kofar gidan, yai parking Tace ita Sam bazata Shiga ita kadai ba sedai suzo Su shiga tare Beyi Mata musu ba ya bita suna tafe, Tun Shugowarsu suka hangesu ta window, malan Nalado yace Anya yaran nan ba soyayya suke yiba? Umma Hafsatu tace nima nayi zargin haka dan ba kowane Zan tsaya maka haka ba Suna cikin hiran ne saiga Su sun shugo, kunyace ta Kama Mansur sosai, ya tsugunna ya gaishesu sukai Mai godiya sosai, yace bakomai Sannan yai musu sallama Zai tafi, Nazeefa kuwa jitai kamar ta bishi Dan tanason Mansur Sosai Rakashi tai har waje, Seda taga ya shiga motar sannan ta dawo gida Tana shiga room dinta na aikinta ta shiga, dama tunda sukazo gidan dakin faeeza take kwana Dariya sosai tayi tace Ohh no Nazeefa Yar aiki yanzu na sama promotion, kallon inda Mubeen yake tsayawa tayi, taji moment din da sukai spending tare nason dawo Mata! Da gudu tabar dakin taje ta kwanta a dakinta tana tinanin both mubeen and Mansur But yafi tinanin Mansur🤸🏻‍♀ dan shine bugun numfashinta Ganin tinanin zanyi mata yawa ne yasa ta dawo parlour tazo ta zauna Kusa da mahaifiyarta sosai taje kamar zata shige jikinta, Tace mammah nah nayi missing dinki sosai fa, Ina sonki, rungomota tayi tace bayan mun miki laifi ko ince na miki laifi, inadai Kara neman yafiyarki, Cewa tayi laaa kamar karamar yarinya Tace bakuimun laifi ba nikam, Yauwa tace Mama munyi magana da Wanda ya zo dazu taqi fadan sunanshi + Da yake sun gane wanda take magana sai suma suka share Taci gaba da magana Tace tace” wani shawara zaku yanke ya kamata musan abunyi, Malan Nalado yace to Alhamdulillah kawai Mu yafe musu, Yanzu ai tun ba aje KO inaba Allah ya nuna musu KO ya kikace Hafsatu? Umma Tace” Ehnmm Hakane gaskiya, kawai a kyalesu Duk Wanda ya rike Allah zai ta ganin haske ne, sune a kasa Wani Mikewa Tsaye Nazeefa tayi Tace umma da Abba bangane a yafe masu ba duk wahalan da suka jefamu, na tabbata harda wahala ya Kara sa kuka tsufa tana magana cikin shawaba tace ni gaskiya …….. Ta zunburo baki ta tashi ta shige daki inyeee Su Nazeefa an zama butters lol Binta da kallo sukai, Umma Tace ke yarinya ce, Bakisan meye duniya ba, Malan nalado kuwa binsu da kallo kawai yayi Hiran Su suka ci gaba, Nazeefa kuwa na shimfede a kan gado, Tinanin Mansur ta farayi, je tai inama suna tare, she loves him from the button of her Heart, gaskiya ba karya ita kanta tasan sun dace

Bangaren Mansur din ma hakan take Dan gaba daya komai nashi ya maida Nazeefa, password na wayarshi, Na laptop Kai harta screen din wayarshi ma Nazeefa ce akai, sonta a jininshi yake sosai, he loves her irin totally dinnan, but idan ya tuno wani abun kuma sai yaji Anya iyayanshi zasu Bari ya aura Nazeefa, duk dadin da yakeji idan ya tina da kamar wuya a bari aureta se yai shuru yaita addu’a Bayan kwana Biyu Mansur ne ya Kira Abdallah yace su hadu a wajen A & B PLAZA Kamar karfe 10 na safe yace alright Kasancewar weekend ne ba aiki, Abdallah suna kwance da matarshi tayi bacci ya zame jikinshi ya shiga wanka, ya shirya yasa light brown colour shadda yayi kyau sosai, ya dakko hula ya saka, Bacci takeyi taji kamshin turarenshi ya buge hancinta ta farka Tsareshi da ido tayi tace banganeba Ina zaka kuma yau weekend? Kusa da ita yazo ya zauna yace kiyi hakuri these days zanyi busy sosai, saboda muna binciken wani Abu ne Tace banganeba kai ba Dan jarida ba amma kullun bincike Rungumeta yayi, yace yes hakane amma kiyi hakuri I’ll tell you everything Bari dai komai ya lafa kinji matata, Smiling tayi Tace OK bakomai, Halan kaida Mansur ne KO? D’aga Mata Kai yayi alamun eh tace dama ai nasani, Aminan juna, Allah ya Baku sa’a ya temakeko yace Ameen sannan yai ficewarshi Napep yahau ta tafi chan, Yana sauka yaga Mansur a cikin motarshi, Wajenshi ya Nufa suka gaisa yacemai ya Madam, Abdallah yace Alhamdulillah tana gaisheka Wani babban shago IPhone suka nufa, nan Ya siyowa Nazeefa waya IPhone latest one, sannan ya biya Company MTN da ZAIN yasai Mata layuka duka biyu Yai mata register, Abdallah ne ya kalleshi yace yauwa Mansur ya aka karene da mutanan nan? Yace dama yanzu nakeson muje gidan tare dakai duk abunda suka yanke shine daidai Suna cikin maganar ne telanshi ya kirashi yace angama dinkunan da ya basu yace wow da sauri haka? Sukace yes ranka shi dade, yace OK to gashinan zuwa, Direct shagon suka nufa suka amsa kayan, Sannan suka wuce gidan Su Nazeefa. Me gadi yana ganin motor yasan na waye da sauri, Yaje ya budemai yace ya shugo dashi kawai, Nazeefa tace duk sanda yaga motor ya budemai ya shiga Parking space ya samu, Nazeefa na ganinsu, tace Umma mutumin nan yazo Bari inje, Sukace OK Fita tayi wannan karon gyalen abayar ta yafa, Tun fitowarta Dukansu suka bita da ido…Tsabagen kallo Mansur har yana sauke glass Dan gaba daya ta chanza bazakuce Yar aiki bace da! Mansur yaga Abdallah nata kallonta Wani kishi yaji yace Malan take your eyes off wannan kaya nane! Bin Mansur da kallo yayi yace da yake nima inada kayan ai, dukansu dariya sukai adaidai lokacin Nazeefa ta karaso, Wani kallo da mubeen yai Mata jitai kamar ta nitse kasa Dan wani yanayi taji yanabin ilahirin jikinta, Sannunku da zuwa tace sukace yauwa, Abdallah yace gimbiya sarautar Mata rufe ido tayi Mansur yace kaga daga zuwanta zaka daman mun ita KO? Ita kam kunya taji ta rufe fuskarta Yace well Nazeefa ba zama mukazo yi munzo nan akan maganar mutanan nan ya muke ciki dasu ne? Tace yeah jiya dama munfara maganar dasu umma baridai na kirasu Mansur yace noo Bari Mudai Mu shugo, Tace OK Tai tafiyarta Mansur ya bi bayanta da kallo yana lashe baki, Abdallah ne ya bigeshi yace gidan sirikan mu kake fa, sosa keya yace Ohh Fitowa sukai ya umurce Abdallah daya temaka Mai Su shiga da kayan Daya amso wajen dinki Abdallah na gani yace sannu Da kokari Na Nazeefa yace yauwa Fito da kayan sukai Daga bayan boot suka nufa falon, suna zaune suka gaisar dasu suka amsa sannan su umma sukai musu godiya akan kokarin da sukai musu Mansur yace bakomai, emm umma da Abba nazone Mu tafi Chan inda aka kai mutanan nan Yace yauwa Dan nan Allah yama albarka, Zasu tafine yace ga wannan kayan na kawo muku, suna budewa Nazeefa taga ai kayan da suka je tarane suka siyo har an dinka lalle Mansur Nan Su umma suka mai godiya sosai, sukaimai addua sukace dama basu Dana chanzawa Sannan suka tashi suka tafii

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *