SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 21
Falon suka wuce, Iyayanshi zaune suke kan kujera shi kuma yana kasa yana wasa da yatsunshi, gabanshi se dukan uku uku yakeyi+ Dad dinshine ya kalleshi yace” Mansur meke tafe dakai? Fadamun da sauri dant Zan fitane M.T ne ya gyara zama yace dad Dan Allah neman alfarma nakeyi a wajenku, Ku amince na aura Nazeefa inasonta! Dad dinshi Ya cire Glass din dake fuskarshi ya karemai kallo, tuni murmushin dake fuskarshi ya gushe, yace Ashe bakada hankali? What are you saying? Yarinyar data gama bin gidajen mutane zaka cemun ita zaka aura? Sam bazaiyuwaba! Karma in Kara jin wannan maganar a bakinka, Mansur ka sake tinani! amma banace akwai yarinyar da Zan hadaka da itaba? Kenan Allah kadai yasan abun da kuka aikata lokacin da ka kawota gidan nan! Zaka zo ka dameni kace wani zaka aureta ka shiga taitayinka Mansur turaki tsabagen rikicewa kasa motsi yayi, Dan kallon abun yake kamar a film? Mum dinshi kuma na zaune tana ba Alhaji hakuri Alhaji yace Sam bazaiyuba ya tashi ya shiga room dinshi, Wani Kwalla ihu Mansur yayi yabi mafaifinshi har daki ya na kuka, Rike rigan babanshi yayi kamar karamin yaro yana bashi hakuri akan ya amince Dad dinshi a fusace yace” get out of my room daga temako zakace wani zaka aureta hmm Mansur kasa tafiya yayi Dan ji yai kafarshi sunmai nauyi, Jiri kawai yake gani dakyar ya samu yakai kanshi daki Dan wani matsanancin ciwon Kai da yakeji Yana zuwa dakinshi gado ya fada
Wani zazzabi yaji yana shirin kamashi, Dan beyi expecting wannan reply dinba daga mahaifinshi, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun yace” Tashi yayi ya rufe ko ina na dakinshi yadan samu yasha panadol extra Dan wani kanshi yaji yana Saramai Dakyar ya lalubo waya, Kallon screen din wayar yayi yaga hoton Nazeefa, Hankalinshine ya Kara tashi Dan ganin yake tabbas daya rasa nazeefa gwanda ya mutu, Yarinyar da yakeso ta zama uwar y’ayanshi gashi dad dinshi naso yai Mai fuck up! chusa hannunshi yayi akanshi yana shafa gashin kanshi Dan wani irin yanayi yakeji, inama ace mafarki yakeyi dayaji dadi Yana cikin tinanine Call din Nazeefa ya shugo! Kallon wayar yayi ya kasa picking Dan Gabanshi fadi yakeyi sosai! Haka wayar ta gama ringing be daukaba, Bin wayar yai da kallo kamar wani tababbe Natsuwa yayi kome yake tinawa ohoo Call ne ya shugo wayarshi yana dubawa yaga Abdallah da sauri yai picking ya fara magana hello Abdallah kana inane? Abdallah yace” Ina gida mana bazaka zo bane? Mansur cikin wani irin murya yace I can’t come Dan Allah kazo akwai Dan matsala ne, Abdallah koda yaji Voice din M.T yasan akwai matsala kam Dan haka yace Mai I’m on my way right now, Mansur yace OK sai kazo, yana gamawa ko sallama basui ba ya cilla wayar Chan gefe ***** Bangaren nazeefa kuwa tun safiyar yau data tashi, jitai itama gabanta na mugun fadi, gashi tun jiya basu sake waya ba dan haka tadan damu kadan dukda tasan he’s doing fine inshaa Allah Bangaren Mubeen kuwa! Bayan tafiyar Su Nazeefa ji yai kamar an kara dasa Mai son Nazeefa, Dan he’s praying Allah yasa ta zama matarshi
Toofaaa…..muje zuwa ankusan kawo final.. lol Kiran Faeez yayi daya aramai phone dinshi wayarshi ba data zaiyi browsing yaga ko yau akwai kwallo, Dan haka faeez ba tare da wani tinaniba ya dauka ya bashi Yana bashi room dinshi ya shige ya Fara duba dial call! Yaci karo da 6ter *Naazee* smiling yayi ya kwashe number sannan yai saving a wayarshi da *ITA CE* sannan yamai damai da wayan ***** Mansur ne kwance a daki yana Tinanin How his life is going to be without Nazeefa, knocking din kofar yaji anayi, Yace waye Abdallah ne yace nine, OK yace, dakyar ya tashi yaje ya budemai, Suna hada ido, M.T ya marairaice kamar Wanda ya dade yana jinya Abdallah ya kalleshi yce” lafiya kuwa? Binshi da ido yayi har suka isa room din Mansur, Zam sukai Abdallah yace wai meke faruwane? Mansur yai kasa kasa da murya yace BOSS ne wai be yarda na aura Nazeefa ba Abdallah shuru yayi Dan maganar ta shige shi sosai, Sannan daga bisani yace amma meyasa? M.T yace kawai wai Dan na kawota gidan nan! Abdallah yace huh! Me mum tace? Mansur yace batace komai ba Wani iri yai da ido da seda Abdallah ya Dan tsorata🤣 Yace me mum tace, Shuru yai mai kamar besan abunda yake cewa ba…….. Muje zuwa Abdallah yace huh! Me mum tace? Mansur binshi da ido yayi kamar besan abunda yake cewa+
Abdallah ne ya matsamai yace wai lafiya kuwa? Be Strong mana “Sannan Mansur yace batace komai bafa Shuru dukansu sukayi na Dan mintina, Sannan Abdallah ya kalle Mansur yaga ya bashi tausayi, Shekara nawa yana dakon soyayyarta sannan se lokaci da ya kamata ace ya mallaketa se ace baza’a amince ya aure ta ba akwai matsala kam gaskiya Dafa Mansur yayi yace aboki you shouldn’t worry please, Zamui magana da mum kaji! Mansur ne ya kalle Abdallah yace dole fa indamu kasan Dad yai magana be chanzawa Abdallah yace nasani, muyi addua kawai! But kacima abinci? Mansur yace bazanci ba, Suna Cikin magana saiga call din Nazeefa ya shugo, Kallon wayar gaba dayansu sukai Har ya kusan tsinkewa Mansur be daukaba Abdallah ne yace pick mana, Girgiza Kai yayi alamun he won’t pick, Abdallah ne da sauri ya dauka ya kafa mai a kunne! Nazeefa cikin sanyin murya tace hello my love Yace” hea dear ya kike, hope kin kwana lafiya? Tace lafiya lau, but tun jiya najika shuru hope komai lafiya? Yadanyi shuru, Abdallah ya dag’amai Kai alamun kawai yace yes! Hakan yayi yace” eh lafiya lau My princess Nazeefa tace kawai na ji amma ban yardaba, kodai baka da lafiya ne? You sound somehow dear, smiling yayi bece komai ba! Haka dai suka gama wayar Amma da kaji voice din Mansur kasan yana cikin damuwa! Bangaren iyayan Mubeen kuwa sunje kasuwar sundawo har anci gaba da gyare Gyaren gidansu Nazeefa, Hankalinsu yadan kwanta but suka tino tsalleke rijiyar da sukai da baya sedai suita Hamdala
_Bayan Kwana biyu_ Mansur gaba daya ya fita hayyacinsa, dan ko zuwa part din Su mummy bayayi, Abinci kuwa sedai yaje gidan Abdallah yaci ko yaje restaurant, Hankalin mahaifiyarshi ya tashi sosai Dan idan yazo ya gaisheta in the morning be kara zuwa, dad dinshi kuma bayanan so mamanshi hankalinta Sam ba a kwance yakeba Bngaren Nazeefa kuwa kota Kira number Mansur be zuwa, so itama hankalinta a tashe yake tun randa sukai wayar nan dashi yau kwana biyu kenan phone dinshi a kashe Dan haka ta shigaa tianina barkatai gashi bata da number wani ballantana ta Kira taji meke faruwa *Washe Gari* Mansur ne Zaune akan sallaya ya idar Da sallar walaha, Knocking yaji anyimai dan haka a tinaninshi Abdallah ne, bude kofar kawai yayi Yana budewa sukai 4eyes da mamanshi, Kallonshi tayi sosai har ya Dan rame yayi baki, ajiyar zuciya tayi Tace Mansur. Idonshine ya cika da kwalla yace” Mum kamar zaiyi magana kuma saiya kasa, Suna tsaye a wajen mum tace Mu shiga ciki muyi magana Room din Mansur suka wuce, Tana zaune a kujera shi kuma yana kasa, Fara magana tayi tace” My Son kayi hakuri ka Dena damuwa zanyi convincing Dad dinka ya amince, Nima kuma harga Allah yarinyar tamun, kasan aure kowanne da yanda take zuwamai, Kasan mahaifinka Zai aurama Wata A chan masarautarsu Inyaso inka aureta sedaga baya ka aura nazeefan kaji Wani Ji yayi maganar tamai babba, shi yaushema zai iya auran wata, bare harya hada mata biyu, Shi kawai Nazeefanshi yakeso ba kowaba Mum dinshine tace” bakajini bane? Se a lokacin ya dawo dogon tinanin da yakeyi, Yace Mum kinsan bansan mata biyu dan gaskiya zanso in kwatanta adalci amma bazan iyaba, kar naje na cutar da dayan Dan ni zuciyata Nazeefa takeso Mum dinshine ta bishi da kallo a zuciyarta tana lalle Mansur sannan tace koma dai menene your father is ur Father adena fushi damu, So zanyimai magana dama anjuma zai dawo Yace OK Allah yakaimu *** Abdallah kuma tun tafiyarshi shima hankalinshi a tashe, Addua yakeyi Allah yasa Su dad Su amince dan shima yasan kaf yan matan da suke bin mansur ba wacce ta dace dashi Sai Nazeefa Dan sun shaku sosai kuma so sone duk inda yake baya boyuwa
Matar Abdallah ne taga yayi shuru tace cemai kaida Mansur dinnan sai Allah Yace eh din naji, Tace yaushe za’a kawomun matar ne mugaisa da ita? Abdallah yace kwanan nan, aranshi yce ke bakisan ma wainar da ake toyawaba Washe Gari* Nazeefa Tun safe data tashi take trying number Mansur sedai ace mata Switch off, Hankalinta a tashe yake Dan tasan ba karamin Abu bane Zaisa mutun ya kashe waya, Tinani barkatai take tayi aranta tace kodai beda lafiyane Dan Sam bata kawo wani Abu akan auransuba+ Kira takeyi harta gaji, Gaba daya batada walwala, da yake Mahaiyarta me lura ne sosai ta zo ta sameta tace meke damunki? Nazeefa tace bakomai, Umma hafsat tace kalleni dakyau Nina haifeki ki fadamun meke damunki? Nan Take Nazeefa ta kirkiro karya tace Mammah Wannnan mutumin ne beda lafiya yau kwananshi 2 ko magana be iyawa Subhanallah mamanta tace gaskiya dole ki damu, Yaya jikin nashi? Nazeefa tace da Sauki umma, Tace to Allah Kara sauqi Dan Allah kigaishehi, Nazeefa tace Inshaa Allah Umma sanan tabar dakin Tana fita Nazeefa Duba gallery dinta ta farayi nan taga wani pic na Love of her life yana smiling, kwalla ya xubo mata aranta tace inason wannan guy din! Kallon pics dinshi sosai tayi sannan tana ta Kira yaqi shiga, Samun waje tayi taci kukanta sosai, ita Tana ta tambayar kanta kodai tamai wani abune yake punishing dinta, Text ta turamai kamar haka, _I called ur line several times yaqi shiga Dan Allah idan ma laifi nama kayi hakuri dan na azabtu habibee, ina kaunarka har Abada_ sannan ta tura mai duk bayan minti kadan take duba message din ko yayi delivered idan taga beyiba setai tsaki ta jefar da wayan kan gado ammafa hahahhh Tana cikin dakin ranar dai ba wani walwala taiba, Ko abincima ta kasa ci, tana tinanintane bacci ya kwasheta Bayan tai bacci Mahaifinta ne ya dawo, Ya sama Umma a tsakar gida akan tabarma tayi shuru tana zaune Zama kusa da ita yayi yace lafiya Ina Nazeefa take Naganki ke kadai? Cemai tayi Nazeefa na daki bacci takeyi, kasan ko Wannan Saurayin nata bashi da lafiya? Yace Allah sarki, Allah ya bashi lafiya amma dai taci abinci KO? Tace Anya kuwa bansaniba Nan suketa hirarsu *** Nazeefa na bacci taji Wayarta Nata Kara sakonnin nata shigowa Dan haka tai zumbur ta tashi Daukar wayar tayi ta Fara karanta sakonnin da yake ta shugowa, mamaki ne sosai ya kamata aranta tana waye ne wannan me mun kalaman nan,
Text din karshe ta ke ta maimaita tawa kamar karatu, “Kisani idan har baki amince na aurekiba to tabbas Zan iya rasa raina, nine nan boyayyar masoyinki, I love you… Sake sake ta farayi what’s happening, Waye wannan kuma, Tsaki tayi ta ajiye wayar taji komai be Mata dadi, ita kam ko waye sedai yai hakuri Dan batada space a zuciyarta Dan Mansur ya riga ya I occupying heart dinta gaba daya So ba Wanda zata saurara koda waye kuwa Tagumi tayi jum, nan tinanin Mansur ya addabeta Dan haka ta dauka wayar ta kirashi still A kashe Salati tayi, Tace Anya ba mutuwa mansur yayi ba, Fitowa Waje tayi ta tarar da mahaifanta tuni ta zube a kasa sumammiya Salati suka Fara Umma Hafsatu ta ebo ruwa ta yayyafa Mata Ta fargado, daukarta sukai taka kaita daki, Suna tambayarta meya farune? Mansur kawai take ambata Nan mahaifinta Ya lallasheta yace karta damu, Jibi jibin nan zasu koma suje meke faruwa, Dan haka tai smiling Tace nagode Abba Umma kuwa ta dakko Mata abincinta taci ta koshi nandai suketa bata hakuri akan komai zaizo da sauqi inshaa Allah Chan yamma nayi Baban Nazeefa ya Kira Baban mubeen Akan aikin gidanshi, Yace angama dai KO Dan nasan akwai kudi akwai komai da komai! Baban Mubeen yace angama fenti ne kawai za’ai Dama banfada maka ba akwai wani gidan already angina shi Chan bayan gidana! Shine mukai shawara a gyarashi idan yaso kadawo be maka se cikin filayenka ka zaba se ai maka Wanda kakeso Bban Nazeefa yace OK Madallah nagode sosai Suna gama waya ya Kira Mubeen akan yaje chan gidan aikin ya gani, kafin yazo, so yake zuwa gobe agama komai Dan jibi zasu dawo Mubeen yaji wani sanyi aranshi yace OK Allah takaimu Daki ya shige Ya dauka wayarshi ya ya Kira line din Nazeefa, Dauka tayi tace Hello, ba ai magana ba ta sake cewa hello, Waye ne? Wani Murmushi yayi da yaji voice dinta sannan ya kashe Mubeen yace ahankali zaki dawo da sona ne, Shiryawa yayi ya tafi Wajen ginin Su Nazeefa yaga komai na tafiya daidai Se Chan dare ya dawo ya sanar da mahaifinshi yace Masha Allah Muje Zuwa