SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 22
Washe Gari Dad din mansur suna breakfast da mum dinshi suna dan taba hira, Dad yace 2days bana ganin Mansur hope all is well+ Mum ta nunfasa tace bakamai laifiba yaushe zaka ganshi, Murmushi yayi sannan ya ajiye cup din Shayin da yakesha, yace Jeki kiramun shi Tashi tayi irin na manyan matan nan, Yabita da kallo shi har yanzu yana matukar son matanshi, ga kudi ga gida ga komai amma Dansu daya, Kawai se ji nai ya furta Allah ya kawo masu albarka da tausayinmu Nai Maza Nace Ameen Ya Allah Mum din mansur tun kan ta shiga dakin taji wani irin Kara, aranta tace wannan karar daga Ina kuma? Tura kofar dakin tayi taga Mansur a kwance yana wani irin nunfashi, Da amai da yayi Da sauri ta karasa wajenshi ta rikeshi tana girgiza shi tana kiran sunanshi ina kamar besan ma da mutun a wajen ba Fitowa tayi da sauri ta shige part dinsu Tace Alhaji zo, Da zafin nama ya taso ya biyota a baya se dakin mansur Zare ido yayi Yazo yana jijjigashi mansur, Mansur Mansur! Ina hankalin Mansur gaba daya ya tafi Alhajine da kanshi ya fito ya kira sodojin gidan da suke aiki yace a tada moto guda 2 sannan ya kiramai Maza biyu suzo Su dauka mansur yana gama fada ya shige dakin Mansur din
Lukman ne (soja) babban cikinsu ya umurcesu da Su tada moto sannan ya aika soldier 2 dakin yace suje, Suna shiga Alhaji yai Musu nuni dasu dauka mansur Su shiga dashi moto Daukar mansur sukai se cikin motor sannan hajiya ta kulle Ko ina na gidan suma suka bisu tare da Alhaji Abdallah kuwa ahanya yaci karo dasu dama zaizo wajen hajiya yai Mata Maganar mansur yana ganinsu kawai yabisu har asibtin, suna zuwa emergency aka kaishi dan ya zama unconscious Hankalin kowa a tashe, Mum ta Fara kuka tinaninta Allah yasa karya mutu! Dad ma shuru kawai yayi Dan ya tsorata sosai yanda yaga Halin da Danshi yake ciki, Abdallah ma gefe se addu’a yaketama abokinshi Allah dai ya tada kafadunshi Suna wajen Kusan 2 hours Saiga doctor daya shiga dashi ya fito se zufa yakeyi, Mum taje ta tareshi tace” yaya jikin nashi? Bece Mata komai ba taga ya shiga wani room da sauri fashewa da kuka tayi tana shikkenan Ya mutu, Dad dukda babban mutun ne seda yai hawaye Dan shima ya Fara tsorota, Abdallah kuwa shiga toilet yayi yaci kuka Sannan ya fito Suna tsaye ba Wanda yace musu komai Sega wani doctor ya fito mum taci kwalar riganshi tace ya labarin Mansur ya mutu KO? Kallonshi yayi yace kune iyayanshi sukace eh! Yace Ku biyoni, Sannan suka shiga Wani room harda Abdallah samun waje sukai suka zauna Doctor din se kallonsu yake, Ya kalle baban Mansur yace kamar commissioner ne? Baban Mansur yace yes nine Sannan Doctor din yace gaskiya Akwai matsala babba, BP din SON Dinku yahau sannan ya kamu da ciwon Zuciya Dan tama kumbura sosai tana gab da fashewa, ga shi beyin nunfashi yanda ya kamata! Dad ya zare ido yace what my son da heart attack innalillahi wa Inna alaihir rajiun Doctor yace calm down, Mamanshi Ku ma se share hawaye take da Mayafinta idonta yayi jajir Baban Mansur yace yanzu doctor meye abunyi?
Doctor yace it’s not something big, tunda idan na fahimta ba gado bane so by God grace idan har anbashi abunda yakeso zai sama lafiya da sauri inshaa AllahAllah Ya kara da cewa I see no reason da idan har yaro nason abu saikaga iyaye sun hanashi, yanzu duniya ta chanza ba kamar daba! idan yaro nason Abu iyaye idan har sunyi bincike sunga ba aibu bane Su kyaleshi kawai, Idan kuma aibune karsu cema yaron bazasu yardaba gatse Su Mai nasiha da shawarwari I’m telling you yaron zai fahimta Baban Mansur yace gaskiyane Yanzu Ina son Dina? Yace nasan yanzu by now an kaishi ward ansamai oxygen sbd na fada muku beyin nunfashi dakyau Mikewa doctor din yayi yace Ku biyoni muje, doctor na tafe Su kuma Suna bayanshi har suka isa wani Dan madaidaicin daki doctor ya shiga suka bishi. Mansur ne kwance yana ta bacci abinshi kallo daya zakaimai kasan ya fita hayyacinsa sosai se drip din dake hannunshi Dad dinshine yazo kusa dashi ya shafa kumatunshi mum kuwa hannunshi ta kare gam, hade da karemai kallo Duk ya fita hayyacinsa kamar bashiba Muje Zuwa Mansur ne kwance a gado ana karamai Oxygen, Dad dinshi kuma lokacin da suka shugo ya kalleshi yai matukar tausaya mai, Shafa kumatunshi yayi, Mum kuma hannunta rike da nashi+ Mansur kuwa bacci yake hankalinshi kwance Dan besan ma me akeyiiba. Mum ne ta kalle Abdallah Da idonshi ya cika da kwalla tace Dan Allah kanada number din Nazeefa? Girgizakai yayi yace aa amma akwai a phone din Mansur din Dakko Wayar din mansur akai akaga a kashe, kunnawa sukai saiga texts din Da nazeefa tai ta turomai, Aran iyayan Mansur suna Allah Sarki, Daukar Number Nazeefan mum tayi ta Kira Koda ta Kira umma Hafsatu tai picking tace Hello Mai wayan tana bacci, Maman Mansur tace OK Suna zaune a wajen suna tattaunawa akan Babanshi Already yayi alkawari zai auramai wata Chan masarautarsu so sedai ya fara auran Nazeefan dan KO hankalinshi zai kwanta Nan Take Mansur ya bude ido yana yunkurin tashi, Abdallah da sauri ya rikeshi yana Sannu Kallon wajen yayi aranshi yace meya faru aka kawonin nan, Kallon dad dinshi yayi ya murtuke fuska ya juya chan bangaren Ranshi a bace Dad ne yace Sannu my son, Ya kkeji yanzu? Shuru yamai bece komai ba, Mum ne tace Ba magana ake makaba? Sannan yadan daga Kai alamun Da sauqi cos bamagana zai iyaba Dad ne baiji dadin abunda Mansur yamai ba yanda ya hade fuska Still baiyi fushi ba cos ta tun farko da ya amince da Mansur bemai taurin kaiba Mum ne tazo kusa dashi tanamai sannu kuma tana mai da albishir sun yardaa ya aura Nazeefan, wani irin yunkurin tashi yayi, ya bude idonshi sosai yana kallon dad dinshi, Dad din murmuhsi yayi yace yes na amince ka auareta my Son Kallonshi yayi sosai, Yana daga kai alamun na gode.. Taba cikinshi yayi alamun jin yunwa, Abdallah yace Bari Mu kira Dr Bamusan KO ance a baka abinciba
Dr ne ya shugo ya ganshi yaga jikinshi da sauqi kamar ba wanda aka kawo unconscious ba, Hand gloves Dr ya saka sannan yaciremai oxygen yace yes abashi amma bame gishiri sosaiba idan yaci abinci then saiyasha magani, Kusan 3 hrs din suna asibiti Dad yacewa mum tunga ga Abdallah suje gida Su taho musu da abinci Mum tace OK Bayan tafiyarsune Abdallah Ya dauka Wayarshi ya Kira matarshi, Yace yana asibiti kartajishi ruwa Aminin shine beda lafiya, Tace ayya bakomai to Allah karamai lafiya saika dawo **** Bangaren Nazeefa kuwa tana tashi daga bacci ta raromo wayarta ta gwada kiran Number Mansur, taga yana ringing, Picking shima yayi da Sauri tace Salamu Alaikum, Nazeefa Ce ta fashe da kuka tace Dan Allah menai maka kabi ka kashe wayanka Shuru yayi yaji sam beson kukanta dan wani iri yakeji a jikinshi, Taci gaba Da mgana hope dai lafiya? Meke faruwane wai kayi magana mana! Mikowa Abdallah wayar yayi, a daidai lokacin tana Kara cewa kayi magana kozanji sanyi araina please, Abdallah yace sorry Nazeefa bazai iya magana fashewa da kuka tayi tayi waje da sauri ta fada kan cinyar Mum dinta Umman tace tace meke faruwane? Tace Mansur ne fa jikinshi yayi tsanani Dan Allah Umma kubarni inje inyaso saikuzo daga baya, Subballah tace Bari baffanki ya dawo Suna zaunema saigashi ya dawo, Nan Umma ta bashi lbrin komai Yace tayi Hakuri karta damu zuwa gobe dama zasu koma chan kadunan gaba daya Dan dazun nan Baban Mubeen ya kirashi yace angama komai hatta kujeru da gado da duk abunda ake bukata a gida ansa komai Harda abinci Umma tace to Alhamdulillah, Allah yakaimu goben Dan haka suka Fara harhada kayansu, Nazeefa sai murna takeyi ranar Wuni sukai suna chating da Mansur amma batacemai gobe zasu dawo kaduna ba Dan setambayanta yakeyi yaushe zaki dawo sedai tacemai very sooooooooooon Washe gari Su nazeefa sun tashi tun asuba se shirye shirye sukeyi, Dan haka tai switch off din wayarta gaba daya, Makota sai zuwa sukeyi, Haka kawarta tazo se kuka takeyi wai zasu rabu tasan ta tafi dinnan se ansake ganinta,+ Nazeefa sedai tai smiling tace Zan dinga zuwa inshaa Allah, haka suka tattara kayansu, Sukasa a gefe, Sannan Baban Nazeefa yace ki Shiga Chan gidan Ki kira maman Su Usman, tace to shiga gidan tai sai ga shi sunfito a tare sun shugo gidan Su Nazeefa, dad din nazeefa yace zamu tafi birni ga gidan nanan na baki halak malak, ki zauna da marayun yaranki, ga number wayatanan dana Nazeefa duk Abunda kike bukata ki bugo ki fadamun, Allah ya tsareku, mijinki mutumin kirkine ya temakeni sosai a rayuwa, malama lamunde ta fashe da kuka tace nagode kwarai, Allah ya saka da alheri Yace bakomai Makota kuwa se Mai godiya sukeyi, Yace kuma zaizo nan ba da dadewaba a gyara babban masallacin unguwar da yake neman gyara
Nan ma sukace Alhaji Nalado Allah yaja kwana, Allah kuma ya biyama bukatunka na alheri yace Ameen, Sannan Ya bisu da kudade masu yawa nan ma yasha addua yace bakomai ai Ana tare Sannan Nazeefa itama taba kawarta kaya tabata kudade Tace ta kula da kanta, idan tana bukatan wani Abu ga number dintanan ta kirata cos bazata taba mantawaba lokacin mahaifinta nada rai Nazeefa gidansu take zuwa suci dadi kuma duk abunda babanta ya siyo mata seya siyowa Nazeefa, ansha yan koke~koke Baban Nazeefa yace ai basun tafi kenan ba zasu dinga zagayowa inshaa Allah Sannan suka Dan tsagaita da Kukan Bangaren Mansur turaki kuwa, Tun asuba yake kiran numbern Nazeefa shuru, hankalinshine yai matukar tashi, Tinani kawai yakeyi, jikinshi yadau rawa ga wani zafi sabon zazzabi ya kamashi *** Su Nazeefa sun gama shiryawa Babanta ya dauka waya ya Kira Baban Mubeen yace gasunan yanzu zasu taho “yace OK Kiran mubeen da faeez yayi yace Su kasance cikin shiri, nan da kamar 4 hours suje garrage su dauko Su Nazeefa, Faeez aranshi yace Alhamdulillah, Mubeen kuwa Daki ya shiga yai smiling yace Kwalliya zanyi cos kafin taga saurayinta nizata Fara gani…Lol
Sannan dad din Su mubeen ya kira Hajiya asmau Da faeeza yace Su shiga kitchen Su daura musu abinci dan they are on thier way, Faeeza taji dadi sosai saboda nazeefa zata dawo, Dan haka basu bata lokaci ba suka nufa kitchen, Farsusun gaji akai sannan aka soya wasu, sai jallof rice da sukai yasha hadi sosai KO ina ya biye da kamshi Da wani hadadden Apple juice After 4 hours Baban Nazeefa ne ya Kira Baban Mubeen yace gasunan suna gab da tashar moto, Yace Alright Dad mubeen ya kirasu dukansu yace sunkusan karasowa, yanzu abunda zasui shine su dakko abincin duka Su tafi Chan gidan Su Nazeefan, idan sun saukesu then saisu Wuce Su dakkosu Sukace OK fito wa yawa gaba daya sukai, Mubeen ya saukesu sannan suka wuce Moto park da faeez Suna Isa KO 20mins ba suiba saiga Su nazeefa, Sa Sauri sukaje wajensu sukai musu sannu Da zuwa sannan suka dauka kayan suka sa musu a bot Mubeen kallon Nazeefa kawai yakeyi yaga ta Kara kyau, ta rage haske ga boobs dinta daya fito sosai da hibs dinta kodan ta ramene ne Oho, aranshi Alhamdulillah yace Tafiya sukai kadan suka shugo cikin unguwarsu Wani tanfatsetsen gida nazeefa taga mubeen ya tsaya Faeez ya fita ya bude Mai gate, Sake baki nazeefa tayi hardasu Umma suna mamakin Wai nan gidansune, A zuciyata nace Baku shiga cikiba ma tukunna Samun parking space yayi, Sannan kowa ya fita, Azuciyarsu sunata Alhamdulillah Shiga falon sukai, Kowa bin dakin da kallo yayi, gidan ya matukar haduwa, duk kyan Gidan alhaji bawa me kada kwana casain to gidansu nazeefa ya fishi kyau, Suna shiga dakin wani kamshi ta KO Ina abunka da sabon gida Nazeefa ce ta Fara lekawa duka dakunan taga wow sunyi kyau ga dakinta Da take ganin yafi na kowa kyau, Falo da dawo tace gaskiya gidan yyi kyau Masha Allah Babanta kuwa ya kalle Baban mubeen yace sannu da kokari gaskiya gidan ya yi sosai Dad mubeen beci komai ba sudai suna gefe Nazeefa kuwa se rawan Kai takeyi Kamar karamar yarinya, Mubeen kam se kallonta yakeyi Dan idan taka behaving like small child Kara shiga ranshi takeyi Duk giftawar KO motsin da nazeefa tayi se mubeen ya bita da ido, Dan yanzu ta cika ta KO Ina Masha Allah Muje Zuwa