SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 5

SILAR GIDAN AIKI





CHAPTER 5





Mubin ne Zaune a office dinshi yayi tagumi yana mamakin rashin Kama kan wasu matan, aranshi yana Allah na tuba ai ko aure zanyi ban so na aura wacce ta kawo kanta gareni balle kuma yaran nan dako gama zama yanmata basui ba, Tsaki yayi ya dakko file din wata patient ya Fara rubuce rubuce

Babban Abokinshine ya shugo da yake shima doctor ne but from different hospital, Sallama yamai ya amsa yamai nuni daya zauna

Doctor Bashir ya kare ma Mubin kallo yace why are you looking so Dull? Kaga yanda ka rame kuwa? Kodai Kai rashin lafiyane?

Girgizamai Kai yayi alamun aa, Bashir ya Kara kallonshi yace” then what’s wrong with you? M your frnd tell me koma menene koza Mu sama mafita..

Mubin ne ya tattara natsuwarshi guri daya ya Fara bashi labarin halin da ake ciki, Anaso a hadashi da wata shi kuma Yar aikin gidansu yakeso!

Bashir ya kalleshi cik’e da mamaki yace YAR AIKI fa kace kasan me kke fada

D’aga Mai kai yayi yace” ofcouse I love her kuma ita nakeson ko yaushe nadinga jina kusa da ita I mean na dinga hada shimfida da ita

Bashir murmushi yayi yace” Wow boy kace aure kake so haka! But me su mama sukace? Yace they did not agree saiyasa nadan shiga damuwa ai
Doctor Bashir ajiyar zuciya yayi yace gaskiya akwai chakwakiya, amma ita Yar aikin tana sonkane? Girgiza Kai yayi alamun aa, Bashir yace” to wannan ai aikin banzane farko kafin kayi komai ka Fara Neman soyayyarta cikin ruwan sanyi sannan sekasan abunyi

Mubin yace Allah hakane abokina? Bashir yace” yes I’m serious ka jaraba ka gani Yace” tom shikkenan

Nan Sukasha hirarsu ta abokai Dan dama sun dade basu haduba,

*********
Wani mota ne Chan na hango karshen titi anyi parking dinshi, taya daya ancireshi ansa wani karfe yadan rik’e wajen, Wani mutumine na hango a cikinshi da alamun ya gaji yana jiran wasu mutane ne, shingid’a yayi yana latsa wayar hannunshi, ga zafi ya addabeshi Dan haka yadan cire rigan jikinshi dagashi sai vest, vest dinma yadan dagashi sama kana hango gaggasar daya zagaye cibiyarshi, iska yaji ya Fara ratsa jikinshi Bacci ya kwasheshi

Bangaren Nazeefa kuwa Tasha Riga da wando ta dakko dogon hijab dinta ta saka zataje kasuwa danyn cefane, fita tayi tana trekking a kafa Dan bata samu abun hawaba tafiya takeyi harta tsallaka titi Mota tagani batai zaton akwai kowa bama, direct wajen motar ta tafi Dan ita a rayuwarta tana son kallon cikin mota, duk inda taga mota seta lekashi koda akwai mutane ne

Dan haka na nufa motar, ganin windows din motar a bude tasa Kai ta Fara leke, hango wani mutun tayi KO cartoon ne ko ba mutun bane Oho Dan kyan mutumin abun kallone, bacci yakeyi but zakace yana smiling, kallon daidai bakin tayi itama ta fara murmushi tace wannan abun da kyan kallo yake, bin jikinshi tayi da kallo dan wannan ne Karo na farko datasan yanayin jikin maza, Sedata gama kallon jikinshi sosai sannan ya farka daga baccin da yake Dan yaji a jikinshi Ana kallonshi, hada ido sosai sukayi na kusan 5mins sannan yasa hannu ya ja Yar vest dinshi, yace malama Dan Allah kiyi hakuri ki wuce anan, bansan me yakawoni nan ba karki cutar dani

Nazeefa kuwa najin haka tasa kafa ta zuga da gudu tana Aljanine Wallahi

Inba Aljaniba wazaizo karshen titi yazauna shi kadai,

Mutumun kuwa da sauri ya fito daga motar kafin ya fito hartasha kwana, dakko rigarsa yayi ya zira a zuciyarshi yace” da rabon zanga wannan aljanar ce

Dakko wayar yayi ya Kira abokinshi yace yazo akwai Matsala Dan yanzu yaga wata aljana da hijab, Dan be taba ganin me kyan taba

Hankalin abokin nashine ya tashi sosai yacemai gashinan Zuwa

*********
Nazeefa da gudu da shiga cikin kasuwa, dasauri ta siya abunda zata siya duk saurayin data kalla fuskarshi saitaga ya Koma mata na aljanin da tagani acikin moto

Ahaka dai ta gama siyayyan duk a tsorace, da zata dawo gida machine tasamu direct har gida

Koda ta dawo gida a tsorace ranar tai aikin girki, Mubin kuwa na Lura da ita aranshi yace yarinyar nan akwai abunda ke damunta

Bangaren Mutumin kuwa bayan tafiyar Nazeefa ba abunda yakeyi inba gumiba, lalle yau ya hadu da aljanah shi abun bacin ranma datagama kallon mai wajen al’aurarsa, Tsaki yayi amma daya tino irin 4eyes da sukai da ita saiya kara tsokata🤣A tsaye bawon Allah nan yake yana kallon wayarshi, ganin fuskarta yayi ya Kara kidemewa, addu’a ya Fara yi sannan hankalinshi yadan daidaita, ya tsundama cikin tinani Saiga Abokinshi nan da yake a kafa yazo Sam beji alamun tafiyar mutun ba

Ji yayi andafashi ta baya, har zai zura da gudu sai yaji muryanshi yace Mansur Turaki nine fa!

Wani doguwar Nunfashi yaja sannan ya kalla Abdallah abokinshi yace” a tsorace nake wallahi let’s go home

Abdallah ya kalleshi yace wani irin tsoro? Be a man mana kana abu kamar mace, idan mun tafi gidan wazamubar wa mutun anan?

Mansur turaki se waige waige yake yace bazaka ganebane ido hudu mukai da ita

Abdallah yace ita wa? Yace Aljanna yana magana yana Kara waige waige

Abdallah ya kwashe da dariya yace I need to see this Aljanna! Mansur Turaki yace hmm you’ll never see her kuwa!

Nan Abdallah daya lura M.Turaki a tsorace yake, sai yamai hikima sunata Dan hiran addini haka har ya kawar Mai da tsoron, suna Hira saiga masu gyaran motor sun iso Suka gyara musu sannan suka tafi gida!

Suna Isa gida M.T jikinshi ya rikice kamar me aljanu! Hankalin hajiyarsu ya tashi sosai, take tambayan Abdallah meye faru

Nan Abdallah ya kwashe komai ya sanar da ita

Yace” ina hanyane ya kirani wai nazo ya hadu da aljanah,

Hajiya Zainab ta zare ido tace aljana kuma? A Ina? Kaga saiyasa banaso ya fita shi kadai, Yace yes that’s what he told me, Wai yana hanyane motarshi ta lalace shine ya tsaya kafin masu gyara suzo shine ya ganta

Hankalinta ya Kara tashi balle yanda M.T yake ihu yana gatanan…gatanan hannunta tasa A fuskarshi tana karontamai addu’o’i

Waya Hajiya Zainab ta dakko ta sanar da dad dinshi, yace OK yanama Hanya but yana ta makaki

Abdallah ne ya temakawa Mum suga shigar Da shi daki, Jikinshi sai rawa yakeyi wannan kenan!
****
     Bangaren Nazeefa kuwa itama ranar wuni tayi inbanda waige waige ba abun da takeyi, Abincima dakyar ta samu ta gama Dan ranar Baban su Mubin zai dai dawo! Dan haka ranar ga tsoro ga Tasha wahala wajen girki

mubin ne yasha wanka yayi kyau Ana jirar isowar Dad in banda murmushi ba abunda ya keyi

Nazeefa kuwa tana daki da yake tasha aiki ta gaji,  itama shiga wanka tayi, ta fito tazo ta shafa Vaseline abunta, ganin bawanda zai shugo dakin tasa Dan vest dinta da wando kayan ya amshe jikinta sosai

Saboda lokacin Zafine, Shingida tayi a yar katifan dake dakin ta shiga tinanin iyayanta Ko sunada rai Ko sun mutu oho, Janyo akwatin ta tayi Dan Kara bincikar numbern wayan mahaifinta da zatazo aka    bata but she couldn’t find it, Hakanan ta mayar da akwatin ta kwanta, Tino Aljanin datai acikin mota tayi kamar yana Mata gizo, Kwalla ihu tayi ta fita da gudu shi kuma a daidai lokacin Mubin ya zo wucewa zai shiga kitchen, fitowar da tai ta bigeshi dukansu suka fadi

Gaba dayansu wani Shocking sukaji a jikinsu, Nazeefa data kalle fuskar mubin Kara rikicewa tayi taga fuskarshi gaba daya ya koma na Aljanin data gani, kankameshi tayi sosai tana ka barni, Ka kyaleni plz bazan Kara fitowa ba

Mamaki mubin abun ya bashi gashi ta rikeshi gam kuma tana ya saketa me take nufi? Sundau lokaci a haka sannan ta sakeshi ta shiga daki, Mubin kuwa hankalinshi tashi yayi kitchen din da bai shiga kenan ba ya koma daki

Feelings (Sha’awa) sosai yakeji ya rasa inda zaisa kanshi, balle idan ya tino irin kallon datakemai seya kara rikicewa, sedayai sosan gaske sannan ya daidaita kanshi, tinowa da lemon din dake fridge dinshi yayi cos yana rage feelings tashi yayi ya bude Dan fridge din da yake dakinshi ya dakko lemon din yasha sannan yadanji relief but Son Nazeefa kuwa sai Kara ruruwa yake a Heart dinshi,

Ita kuma Nazeefa na shiga daki kulle kofarta tayi, kuka Sosai takeyi duk Taji ta tsana aljanin da ta gani Dan shi yai Mata causing din duk abun nan, Tsaki tayi ta share hawayenta

Sannan ta tashi ta chanza wani kayan, kwata kwata ta kasa natsuwa a dakin se leke takeyi ta labule, tsoron sosai takeji gabanta sai fadi yakeyi like something terrible is going to happen……Misalin karfe 4 na yamma Abban su Mubin ya dawo daga Dubai, yan unguwa sai leke akeyi saboda jiniyar da sukaji sunsan inba Alhaji Sada ba to babban mutun ne ko wani kosa a gwamnati +

   Nan aka shiga tsegumi yan unguwa dan Su abun mamaki yake basu wai yaushe Alhaji Sada yai kudi, Gashi koda yai kudin ba temakawa mutane yakeyiba, Kowa tambaya yake shin a Ina ya gaji wannan kudin? Wasu kam suce Dan yankan Kaine! Dan kan kanin lokaci ya mallaka abubuwa da dama

    Tunda ya shiga gidan escort dinshi sai zagaye sukeyi da bindiga a unguwa, Mubin kam kanshi kato yayi shi gashi a dole Dan me kudi

Bangaren Su Faeez kuwa Sunyi exams aranar zasu dawo hutun semester Dan haka Dad dinsu ya tura driver yaje ya dakkosu

Faeez Da Faeeza sai zumudi sukeyi sun kosa su dawo gida su hadu da farin cikinsu Mahaifinsu

Misalin 6 na yamma suka dawo gidan, Da gudu faeeza taje gun mahaifinta Dan ta dade bata ganshiba, Yanaji da ita sosai saboda ita kadaine yarshi Mace, kuma me kama da uwar yayanshi, Se makalewa takeyi a jikinshi, Mamanta ta harareta tace kinfa girma, dad dinsu yai dariya tace” KO tsufa tayi she’s still my baby Ki kyaleta.

     8:00PM kowa ya halarta a dining table, kallo daya zakai musu kasan kowannansu na cikin farin ciki da annashuwa, Sunci sunsha kowa ya koshi Alhamdulillah, Suna tashi Hajiya ta kwalla ma Nazeefa Kira akan tazo ta kwashe kayan dasukaci abinci, Faeez yadanji ba dadi arai Dan yasan duk me aikin da aka kawo guduwa sukeyi Dan wahalar aikin gidan

    Batace komaiba tazo ta kwashe ta shiga kitchen ta wanke na wankewa sauran kuma tasa a fridge ta gyara kan dining din

    A falo din babansu suka baje sunata hira har kusan karfe 11 na dare, sannan Dad dinsu yace kowa yaje ya kwanta akwai gobe sai suci gaba da hiran nan yaran suka tafi Hajiya kuma ta Fara nunuwa mijinta soyayya da kauna tace” Alhaji akwai magana nan ya rungumeta yace” su Bari gobe zasuyi maganar! Tace OK habibi nah

       ******
Bangaren M.T kuwa koda mahaifinshi ya dawo direct asibiti aka wuce Dashi aka bashi gado Dan inbanda fisge fisge ba abun da yakeyi, hankalinsu yai matukar tashi sosai

Abun ya daure musu kai sosai, Hajiya kuwa inbanda kuka ba abun da takeyi, Dan KO makamanshin haka Mansur betabayiba

Alhajine yake ta bata hakuri, akan ta Dena tada hankalinta sudai sumai fatan Samun sauki, Nan dai nabarsu…..

   Tun Asuba Nazeefa ta tashi ta daura breakfast, Soya Arish tayi sannan ta dakko raguwar farfesun kazan jiya ta dumama masu, Sannan ta soya kwai, Tasaka ruwan zafi a flask!

D.table tazo ta jerasu Sannan ta share ko Ina tasa turaran wuta, Tadan kunna A.C saboda lokacin Zafine, Kowa ya Shugo fallon Seyace Wow a a zuciyarshi Dan wani sanyin kamshi da yake tashi

Alhajine da Hajiya suka fito rik’e da hannunsu a daidai lokacin mubin shima ya fito daga room dinshi yar karamar tsaki yayi aranshi yace kun tsufa amma kullun cikin soyyayya kuke, nima kubarni na aura wacce nakeso Mana, Da tinani barkatai yaje kan dining table din, Suna cin abinci amma da kunga Mubin kunsan baya cikin hayyacinsa Feelings yakeji sosai, Babanshi na Lura dashi yace Kai tashi ka wuce Daki Lol, Alhamdulillah yace a ranshi dan se ahankali yakeji, yana shiga daki as usual lemon ya dakko yasha sannan ya zauna yana nazarin Wani Abu

Bayan sungama breakfast Faeeza na manne da babanta, Kallonta yayi yace” yarinyata kije daki zamui magana OK tace ciikin shagwaba,

Tana fita Hajiya tace” yauwa Alhaji muyi maganar daya kamacemu please, Alhaji yace Ina sauraronki

Tace” Mubin ne ya dage wai bazai aura Haleema ba kuma Tace inbar bahakaba Sai ta tona *SIRRIN* da muke boyewa, Kan Alhaji ya dau chaji ya kwalla ma Mubin Kira saigashi ya Shugo, Samun waje yayi ya zauna nan Dad dinshi yadingamai Fada akan beda hankaline ze aura Yar Aiki, Ko so yake *sirrin* da suke boyewa ya fito

Mubin ne ya dago Kai a gigice yace” Wani sirri, Dad Sirrin ya Dade be fitoba ni Nazeefa nakeso ita kuma Zan aura, Alhaji ne Kai ma Mubin Mari……..

mubin ya rike kumatunsa, Dad yace yaron banza Kawai, in badan nayi kokari akan wannnn sirrin ba da yanzu……Sai hajiya tai sauri ta rufemai baki tace” be kamataba Alhaji

Mubin Bude room din yayi ya fita ya ja kofar da karfi ji kake ghamm, Dad zama yayi yai tagumi yace”  bazaiyuwa ba, Tunda yaron nan ya Fara haka akwai matsala

AI Hajiya kinga irintanan, Dan me aka dakko wannan Yar aikin? Yanzu gashi tanaso ta zaman mana karfan kafa! 

_Hahaha Ina daga waje nai shewa nace ai tukunnama senan gaba zata zaman muku karfan kafa_

Alhaji yaci gaba da fada yace gaskiya a fitar mana da ita anan gidan bansan ganinta

Hajiya ta riko hannunshi tace”.  ta fadamai wani sirri a kunne  tace irin sirrin da mukasha yi wannan karon ma shi zamuyi

Murmushi yayi yace to angama sai yasa nake Kara sonki habibty…..

Shin Wani Sirrine wannan wai dasuke boyewa?


Kuma Wani sirri zasuyi?

Chakwkiya…….haha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *