SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 8

SILAR GIDAN AIKI





CHAPTER 8




Washe Gari
Hajiya Asma’u ne da Alhaji suna zaune akan dining table suna break fast, Alhajine ya ce ga biki na matsowa ya za’ai ne? Nazeefa dake kitchen gabantane ya fadi aranta tace bikin wa kuma dama za’ai biki a nan gidan ne ban saniba, Taji Alhaji ya Kara da cewa ki Kira mubin din muji shirye shiryen da shi yakeyi da Ina zasu zauna,
Nazeefa da take kitchen taji kirjinta ya Kara bugun dam kamar zata fadi Dan rikicewa! Hajiya ne ta tashi cikin yanga irin na manyan matan nan, Alhaji yabi bayanta da kallo aranshi yace thats My wife
  Hajiya direct dakin mubin taje tai knocking se gashi ya fito da alama ma Bacci yakeyi, Ta kalleshi tace” ka wanke fuska Babanka na nemanka, Gabanshine ya fadi yasan be wuce maganar Bikinsu da Haleema +

     Wanke fuska yayi yai brush sannan ya fito yazo ya samesu a dining, Sa hannu yayi ya yanko egg din dake gaban dad dinshi ya hada da Irish yasa a baki

   Dad dinshine ya bishi da kallo yace” me yasa baka da kunyane da ban kirakaba a Ina zakaci abincin? Sosa Kai yayi yace” Sorry dad, cup ya dakko yasa milk, bornvita da sugar sannan ya karkata flask yasa ruwan zafi, Ya bude food flask yasa kwai da Irish Hajiya da Alhaji se kallonshi sukeyi. Seda yaci ya koshi sannan Babanshi yace” Magana ne zamui dama

    Mubin ya saukar dakai yana sauraranshi 
Alhaji yace” maganar aurankune kasan yanzu be wuce 1month ba, Mubin yace” eh yace to dayan flat dinnan na Chan gefen anan zaku zauna, Komai kasan sabone kawai fenti za’a kara yi sannan abun daya Kama na kayan daki duk ni Zan Mata saboda Kai da ita Haleemar duk ya’yane a wajena kaima kaimun list din abunda kakeso

     Mubin yace” Ok Abba that’s why I love you, Badamuwa, Alhaji yace” yanzu ya kkeji aranka kana sonta KO? Eh yace inasonta dad sosai ma kuwa!  Eh din da zaice charaf se a kunnan Nazeefa wasu zafafan hawaye suka fito a idaunta taji kafafunta sun mata nauyi ta kasa tsayuwa dole ta sama waje ta zauna, Aranta tace” yau na shiga uku! Ina zansa kaina kaico na dana biyewa Mubin, Allah ka tausayamun Kasa banda ciki, Wasu zafafan hawaye na zubo mata Kamar ta fito kitchen din ta sanar dasu abun dake faruwa tsakaninta da mubin” sai tai tinanin ba Wanda zai yardama kuma ta tino da maganar mubin yace” idan har tabari Wani yasan suna soyayya to tabbas zatabar gidan, Hakanan tana aiki tana share hawaye da majina

Sungama maganarsu kenan Mubin ya tashi ya shiga daki yana murna, Ko banza ya gama cutar da Nazeefa,

     Alhaji da Hajiya suka shirya zasu shiga kasuwa, Wani dadi Nazeefa takeji Dan yau Mubin ze tabbatar da ita wacece wato ita zai cutar ko wani ajiyar zuciya tayi

   Tana ganin Su Hajiya sun fita kitchen ta shiga ta dakko wuka duguwa me kaifi, Ta ajiye a dakinta, Mubeen na ganin sun fita ya lallabo ya shugo dakin Nazeefa, batace Mai komai ba zama yayi akan kujera suna hira bata nunamai alamun ma da wani abun ba,

    As usual kusa da ita sosai yazo ze fara tabata, ta dakamai tsawa  tace” karka kuskura ka tabani, abun yabashi mamaki yace” meyasa? Tace bansaniba, beji maganartaba saboda wani feelings da yakeji sosai, lips dinshi yakai kan bakinta ta shararamai mari tace” Dan wulakanci ni zaka cima mutunci? Ni zaka wulakanta

  Yai zuru zuru dashi yace” meye faru kinsan dai inasonki ko? Cikin kankanin lokaci ta haukacemai ta dakko wuka zata chakamai da yaga da gaske takeyi da gudu ya shiga dakinshi jinkinshi na rawa zufa sai ketomai yakeyi

Na shiga uku yace, Ba makawa tabbas taji maganar auren mune! Nazeefa kuwa buga kofarshi takeyi sosai tace” kabude na kasheka kowa ya huta, hankalinshine yai mugun tashi ya bude toilet ya shige gabanshi se dukan uku uku yakeyi
     
     Nazeefa kuwa inbanda kuka tana buga kofa ba abun da takeyi ta kusan 20mins ahaka tace” Mubin sedai inbaka fitoba amma saina kasheka, Bakin cikin daka sani Allah bazai barkaba, Tanata kuka da taga bashi da shirin fitowa ta zo ta zauna a falo tayi tagumi se kukan nadama takeyi

     Mubin kuwa yana tsoron Su hajiya Su dawo, ya rasa ya zaiyi ya lallashe Nazeefa kuma yasan ya fito ba karamin barna zatai Mai ba Dan haka wata hikima tazomai na ya Kira abokinshi Dr BASHIR

     Kiranshi yayi yace Dan Allah kazo gidanmu akwai Matsala ne, Nazeefa ce zata chakamun wuka

Dr Bashir yace what? Knife?

Mubeen yace eh

Dr Bashir yace ganinan zuwa dama Ina kusa da gidan, yace OK

   Befi 10 mins ba ya shugo gidan da sauri, Direct falo din ya wuce yana shiga sukai 4eyes da Nazeefa mikewa tayi tazo kusa dashi tace” ka fita KO na kasheka tana naagana idonta a juye Dan tsaban rikicewa da tashin hankali

Dr bashir yace” Kika kasheni kuwa kema a kasheshi Dan kinsan hukuncin kisa kisa Ne

Mutuwar tsaye tayi hawaye na zubuwa a idonta

Kallonta yayi yace” Dan Allah kiyi hakuri Ina mubeen? Fashewa da kuka tayi tace an cutar dani sai Allah ya sakamun

Dr Bashir ne yaje direct Kofar dakin mubeen yace” ka bude nazo

Jikinshi na rawa yace” are you sure bazataimun komai ba? Dr bashir yace bazatai maba ka bude 


Nazeefa na tsaye da jajayen idonta Nazeefa na tsaye da jajayen idonta tana jirane mubeen Ya bude kofar ta chakamai Wuka, Dr Bashir Ne ya tsugunna a gabanta yana rokanta akan please kartai mai komai tayi hakuri zasusan yanda zasui, +

Ko sauraranshi batai ba ita Burinta kawai ta illata mubin Dan ba karamin cutar da rayuwarta yai ba, Mubeen na daga daki ya rasa yazaiyi dan tashin hankali Kuka yafarayi shima nan take nadama tazomai akan cutar da rayuwar Nazeefa da yayi, aranshi yana na cutar da rayuwata meyasa Zan yaudareta

     Jirine ya kwasheta ta fadi a kasa kan kace meye jini ya Fara biyowa ta kafarta, Nazeefa na juyi a Kafet din cikin falon tana rik’e cikinta tana wayyo Zan Mutu, Zare ido Dr bashir yayi ya bugawa mubin kofa da sauri yace come out, Da mubin yaji muryanshi da sauri ya bude Kofar, yana bude kofar idonshi akan Nazeefa yacewa Dr Bashir ta chakama kanta wukane?

    Dr Bashir yace” bakaga kafanta bane miscarriage tayi, rudewa Mubin yayi yace” meye abunyi abokina please help me, Dr bashir yace” we should take her to hospital kawai, Mubin ya kalle kafet din dake falon yaga ya baci da jini, dafa kanshi yayi yace” Oh my God Wata sabuwa! Daukar Nazeefa yayi yasata a Bayan sit Sannan yazo Dr Bashir ya kamamai suka nannade karfet din parlour sukasa a bayan bot suka kaishi wajen wanke carpet

     Da sauri suka Isa hospital, Emergency room aka kaita aka gyarata, da yake Hospital din da Mubeen ne ke aiki kowa yayi shuru Dan tinaninsu Matar Dr Bashir  ne, An gyarata an gama Mata komai But akace ba yau zata koma gida ba saboda BP dinta yahau kuma ta zubar da jini Sosai
    Hankalin mubin yadan tashi saboda gida kawai se hikima ta tazomai yace” koda an tambayeshi Zaice batada lafiyane ya Kaita asibiti cos yasan no body will question him

Ankai Nazeefa aminity (private ward) komai an ajiye Mata Dr Bashir da mubin suna zaune ta bude ido, dagowa tayi tace” meya faru waya kawoni nan? Sannan ta duba hannunta taga An Mata setting line, Ana Kara Mata jini, Fincikeshi zatai mubin da sauri yazo ya Rik’eta yace Please kiyi hakuri jini ake Kara miki, Maida kanta tayi tana kuka da duk wani me tausayi saiya tausaya Mata, mubin kuwa in banda yi hakuri ba abun da yake cewa kanshi na kasa

Dogon tinani Nazeefa tayi tace” aranta tace to me ya faru Dani, Motsa kafanta tayi taji alamun da Always (Pad) a jikinta seta Fara tinanin Wato har wasannan da sukeyi da mubin ciki ya shiga, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun tace aranta amma a dayan bangaren Zuciyarta tana Allah nagode maka da hakan ta faru da bansan ya zanyiba

     Kallon Mubin tayi ta harareshi, gabanshi ya fadi ya farajin tsoro, Tashi yayi zai fita tace” idan ka fita wa zaiyi jinyana? Ina komai Kai kajamun? sunkuyar dakai yayi Yana Kara cewa Nazeefa kiyi hakuri please

DR Bashir shima sa baki yayi yace” Dan Allah kiyi hakuri, Tace rufemun baki Kai kasan abun da yai mun Ne zakazo da wani gemun karyanka kana wani bani hakuri, ko dama bakinku dayane

   Dr Bashir yai kasa kasa da murya yace” Allah ya baki hakuri, tace” yauwa, Kafe Mubin tayi da ido jikinshi se rawa yakeyi tace” Mubin ka kyauta kenan KO? Ta Fara magana kenan kuka yaci karfinta Mubin kuwa se bata Hakuri yakeyi

****koda Su Hajiya suka dawo kallon falon sukai sukaga ba carpet, Nazeefa suka kira sukaji shuru
Then Alhaji ya Kira mubin , Mubin naganin Ansa *P MAN* yace masu excuse me Dad Ne ke kirana, Nazeefa tace” ban yarda kaje ko Ina ka amsa waya ba ka amsa anan kuma kasa loudspeaker OK yace Mata

Picking yayi yace” Hello 
Dad yace kana inane?

Mubij cikin in’ ina yace Nazeefa ce ba lafiya kuma ba kowa a gidan shine na kawota hospital dinmu! OK good Alhaji yace” sannan ya Kara da cewa carpet din falo fa ya na Ina? In ina yayi kamar Wanda be Iya magana ba yace” tana Mopping din falo dinne ta Fara amai akan carpet din shine nakai wajen wankewa…OK ka kyauta yace” Allah kuma ya bata lafiya Yai sauri yace Ameen Dad

   Binshi da kallo tayi harya hada karya, Lalle ma mubin dinnan tace” meyasa baka fadamai gaskiya ba? Idonshine yai kanana yace Nazeefa Dan Allah Ki saurareni ki fahimceni

    Dagamai hannu tayi tace dakata Malam ba wani saurarawa tsakanina dakai, kalle halin daka jefani?
Nnn Yanda Kai karya yanzu, Ka sake kiran Dad dinka kacemai zakai night duty Dan Wallahi bazakatafi gida kabarni anan ba dole kayi gadina nah kaji idan da dadi

    OK yace Mata! Haka KO akai yanda tacemai haka yayi!

Kwana biyun datai a hospital aiko mubin ya bautu Dan gida ma dakyar take barinshi ya leka har yadan rame saboda tashin hankali

    Duk abunda takeso shi yakeyi, Kwananta uku aka sallamesu, Suna hanyar dawowa gida yai parking tace” meye haka? Yace magana plz nakeso muyi Dan Allah ki yafemun KO munje gida karki sanar da kowa abunda yafaru kinjidai abunda na fada shi zaki fada musu Dan Allah Nazeefa ki yafemun Asiri

Tab’e baki tayi tace tab aiko bazanyi karyaba, ga Yar aiki kaita cuta KO? To ka gama cuta na a duniyar nan.kaimun shuru Ko kasani yanzun nan Tom kuma kaima kasani badan a bun nan daya faruba da inamai tabbatar maka yanzu baka duniyar nan
  
   Hakanan yaja bakinshi har suka Isa gida, mubin ko cike yake da zullumin abunda zai biyomai baya, ba shiri mubin ya Fara addu’oi

  Bangaren Dr bashir kuwa shima ya danyi hankali yace” tab Gaskiya da matsala, Allah ya Kara rufa asiri, dakko ruwan faro yayi yasha, ya Fara tinanin Allah dai yasa Nazeefa ta rufawa Mubin asiri in ba hakaba akwai matsala Mubin Kullun tsoron Nazeefa yakeyi Dan Wani wani mugun kallo da harara takemai, Gaba daya tsoranta yakeji kuma ba komai bane illa ta fasa kwan abunda yai mata +

    Bangaren Su Mansur kuwa kullun addu’an Allah ya hadadashi da Nazeefa yakeyi, tun yana boyewa iyayanshi har ya kwanta ciwo seda aka kaishi asibiti akaga BP dinshi yayi high, heart dinshi kuma yadan kumbura.
   Koda iyayanshi sukaji hakan bakaramin tashin hankali suka shigaba, mamaki sukai sosai meke damun Mansur 
   Commissioner Ne mahaifin Mansur suka kebe da hajiya Mahaifiyarshi, Yake tambayanta meke faruwa da Mansur ne cos tun rashin lafiyar da tabayi suka Dena gane kanshi, Mahaifinshi yace” kodai shafan jinnune saboda Ko zaune yake ya Shugo seya razana!

    Beloved Mum din M.T tace” inajin sune kuma dai Alhaji yakamata amai   aure at least hankalin shi zai kwanta kaga he’s matured enough, Da yana da kannai AI da tuni yayi aure kasan son ji yakeyi kamar Dan 10 years 
    Commissioner yace” tabbas haka maganar ki din haka zamui
    Ward din da aka kwantar dashi suka shugo Bacci yakeyi hajiya na taba fuskarshi ya razana ya mik’e da sauri, Sukacemai Sannu yace yauwa

     Mamanshine ta kalleshi tace” Son meya jawoma High B.P gashi heart dinka wai ya kumbura tana magana tana Hawaye Dan mugun Son danta takeyi shi kadai suka haima a duniya..Kamo Hannunta yayi yace” mum bakomai ki kwantar da hankalinki

Tace” I hate seeing you like this, taya hankalina zai kwanta, kirkiro murmushi yayi yace” Mum Zan sama Sauki inshaa Allah,

   Phone din Dad dinshine yai ringing yana dubawa yaga Minister A. dauka yayi yace” already muna wajen meeting Kai muke jira…ohhh sorry I’m on my way yace, sai ya kashe wayar, kallon Mansur yayi yace” Sorry my dear yanzu zanje indawo

Mansur OK Dad, Hajiyarshi ta rakoshi har wajen Motor, nan body guards da escorters dinshi duk suka mik’e sukabi bayanshi kafin ya shiga motor saiga Babban Abokin Mansur kuma amininshi Wato Abdallah, durkusawa yayi  ya gaishesu suka amsa da fa’ararsu, Sannan yai musu yame jiki sukace dasauki Alhamdulillah, Dad ne ya kalleshi yace” Abdallah Ina saurine idan nadawo akwai maganar da zamuyi ya durkusar dakai yace” Ok Dad saika dawo yabarsu a wajen ya Shugo dakin Hajiyama a waje ya barta tanata kiran relatives da kawayenta an kwantar da Mansur

     Yar dayan komishinar da takeson Mansur tanajin beda lafiya, Dakko moto ta Kira kawarta tace tazo bakin titi ta jirata zata karata plz, OK tace Mata ta shirya shap shap tazo bakin titin kamar yanda ta umurceta

Tana daukan ta kasuwa suka wuce ta siyo kayan drinks da na kwalama ba karya ta kashemai kudi sosai sannan suka wuce Hospital din

Gudu take sosai Dan ta kosa taje taga Rabin ranta, Tana Isa masu gadin hospital din suka so Su raina Mata wayau wai bazata shiga ba, Kallonsu tayi a wulakance sannan ta ciro phone dinta tana latsawa,  wani Class mate dintane yazo wucewa yaganta yace” Allah temake Yar komishina, Masu gadin zare ido sukai yanda sukaga doctor yana Allah ya temake Yar komishina jikinsu na rawa suka tashi suka bude Mata sunamai bata hakuri KO kallonsu batai ba, Tana wucewa da moto tace” Allah ya temakeku da kun rasa aikinku yau

    Parking space ta samo ta fito daga ita sai riga da wondo da Dan wani gyale, gashi tasa highhill, Cin Karo tai da mum din Mansur a bakin reception, gaisheta tayi tai Mata yame jiki tace tasauki tai maza ta shiga ward din, Mum din Mansur girgiza Kai tayi aranta tace Allah kasa mudace

    Koda ta shiga da sauri takaraso inda aka kwantar da mubin, riko hannunshi tayi ta Fara hawaye tanamai yajiki, Hade rai yayi kamar omer, Yace dasauki sannan ya juyar da kanshi
    Meke damunka tace” yayi shuru

Kallon Abdallah tayi tace” what’s wrong with him, Mansur ne yai Mai alamu da ido akan kar ya sanar da ita, 
   Abdallah yace” kawai fever Ne se becin abinci
   Hawayene yaci gaba da zubuwa a idonta tace please dear love I don’t want to lose you kadinga cin abinci plz

Abdallah ne ya kalleshi yai Mai alamu da yace OK Dan Kar tai feeling bad, kallonta yayi yace” Yasmin don’t worry Zan dingacin Abinci
   Murmushi tamai tace really? Yace yes dear, tace Alhamdulillah

   Nan ta narkomai kayayyakin data siyimai tacemai gashinan anjuma zata dawo, hade rai yayi yace” nace miki Ina bukatane? KO banda halin siyane? Rike hannunta tayi tace” oh ohh M.T ba haka bane ra’ayinane AI nasan kafi karfin haka, OK yace cikin siririyar Murya aranta Tace” Mansur akwai rigima

Nizan tafi sai nazo anjuma yace” bazai kinzoba ki huta abunki, Duk abunda akeyi akan idon Seemah kawarta aranta tace Lalle kawata nason maso wanine akwai aiki kam

      Sallama sukai musu suka Kama Hanya…Mansur kuwa yace a gayas ahankali Dan kartaji…..hahaha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *