SOORAJ
CHAPTER 2
Cikin sanyinta ta nufi inda teacher Abdallah ya nuna mata. Ɗaya daga cikin ƴan matanne ta bita da wani irin kallo. teacher Abdallah yana ganin ta zauna ya fice daga cikin class ɗin bayan ya bata jakar makarantarta mai kyau. +
Gaba ɗaya jinta take atakure, kasancewar kusan gaba ɗaya rabin ƴan ajin idanunsu na kanta.
“Sannu!” matashiyar budurwan dake gefenta ta faɗa, wacce aƙalla bazata wuce sa’an Ziyada’n ba.
Sai alokacin Ziyada ta ɗago da kanta ta kalli wacce tayi mata maganan. murmushi tayi mata haɗe da cewa “Yauwa!”
Murmushi itama yarinyar tayi tare da sake cewa.
“Sunana Nasmah, kefa?”
“Sunana Ziyada” Ziyada ta bata amsa tana mai ɗan faɗaɗa fari’an dake kan fuskarta.
“Nice name!” Nasmah tafaɗa tana mai ɗaukan wani text book dake gabanta.
Ɗan satan kallonta Ziyada tayi haɗe da yin murmushi, duk da cewa bata fahimci me Nasmah’n take nufi ba.
Shiru Ziyada tayi bata sake cewa komai ba, yayinda suma ƴan matan sukayi shiru, Nasmah gaba ɗaya hankalinta nakan littafin dake hanunta, yayinda wacce ke gefen Ziyada ta ɓangaren damanta kuwa ko ƙala bata ce ba, sai dai time to time tana yawan kallon Ziyadan, maganane abakinta amma saboda halin jin kai irin na Shukhra ta kasa cewa komai.
Wani malami ne ya shigo cikin ajin, dukansu ɗaliban suka tashi tsaye haɗe da gaidashi, sai da ya ɗan yi rubutu kaɗan akan white board ɗin da ke cikin ajin sannan ya basu izinin zama.
Darasin Maths yake koyar musu cike da ƙwarewa, yayinda gaba ɗaya ƴan ajin suka bada attention ɗinsu gareshi, ciki kuwa hadda Ziyada, wacce ɗigo ɗaya na daga cikin abun da yake koyarwa bata fahimta ba, jinsa kawai take, tana kuma kallon yanda yake solving guestions. Tambaya yayi da sauri wacce ke gefen hagunta, wato Shukhra kenan ta ɗaga hanu, ya ta da ita ta bashi amsa, ƴan ajine suka hau yi mata tafi. Haka dai ya gama yi musu karatun ya fita abunsa. Yana fita baifi da mintuna 5 ba wani Malamin Biology ya kuma shigowa. Tunda malamin yafara darasi’n ta kafe allon da idanu, turanci yakeyi musu cike da ƙwarewa, sannan gaba ɗaya explanation ɗin da yayi musu da turanci yayi su, tunda ya shigo babu wani wanda yayi Hausa haka kuma shima ko A akalmar hausa bai ambata ba, kamar dai yanda wancan malamin maths ɗin yayi haka shima wannan ɗin, hakanne ma yasa sam bata fahimtan komai, domin kuwa turanci zalla suke basa ko ɗan surkawa da yaren da zata gane wato Hausa, lokacin da taga kowa ya ciro littafinsa yana rubutu itama sai ta buɗe jakarta wanda Teacher Abdallah ya bata, bayan littatafai dake cikin jakan hadda wasu tarin kayan snacks. Wani littafi ta ciro haɗe da pen. Dayake Teacher Abdallah ya ɗan koya mata rubutu a lesson ɗin da sukayi, hakan yasa rubutun bai wani bata wahala ba, sai dai kuma bata wani ƙware sosai ba. Gani tayi shima kafun ya fita saida yayiwa ƴan ajin tambayoyi, amma inda Allah Ya taimaketa ita bai tambayeta ba, kuma ko dama ya tambayeta saidai ta bashi amsar shiru. Yana fita wani malamin yakuma shigowa shima dai yaɗan jima yana musu darasi kafun ya fita. Yana fita aka buga ƙararrawan fita break, gani tayi da ɗai ɗai ɗaliban ajin ke ficewa zuwa waje, Shukra ce ta miƙe tafice daga cikin ajin.
STORY CONTINUES BELOW
“Bazaki fita break bane?” Nasmah dake ƙoƙarin tashi tsaye ta tambayeta.
Samun kanta tayi dayin murmushi haɗe da cewa.
“Zan fita”
Ganin kowa yana fita da jakarsa rataye akafaɗarsa ne, yasa itama ta ɗauki ƙatuwar jakarta ta rataya akafaɗanta, sai da ajin ya zama babu kowa acikinsa sannan ta miƙe ta nufi hanyar fita, awani babban barandan dake gaban ajin ta tsaya tana mai bin ɗaliban dake ta hada hadarsu a harabar makarantar da ido, kowani ɗalibi ka gani yana tare da abokinsa, yayinda wasu kuwa sukaiwa kansu mazauni akan kujerun da akayi da siminti wanda ke ƙarƙashin wasu bishiyoyi dake harabar makarantar, zama tayi akan makeken dakalin dake ƙofar ajinsu, yayinda ta zuro da ƙafafunta ƙasa, aranta wani daɗi takeji wai yau itace acikin makaranta makarantar ma ta boko, yunwa takeji na ƙwaƙulan cikinta don haka ta buɗe zip ɗin jakarta, wani cake dake cikin wani haɗaɗɗen leda ta ciro, tare da fito da goran peach ɗin dake cikin jakar, ɓare ledan cake ɗin tayi ta soma gutsura ahankali, gani take kamar idanun gaba ɗaya ƴan makarantar akanta suke, musamman ma da taga duk wanda yazo gilmawa ta inda take sai ya kalleta, tana cikin cin cake ɗinne, ta hango Nasmah da Shukrah na tahowa zasu dawo aji. Suna ƙarasowa gareta Shukra ta wuce yayinda Nasmah ta tsaya akusa da ita, cike da kulawa tace.
“Me kikeyi ke ɗaya anan?”
“Babu” Ziyada ta bata amsa tana karkaɗe Hijabinta da burbuɗin cake ya ɗan zuba akai.
“Tashi muje Class, ko kin gane lecture’s ɗin da akayi mana yau?” inji cewar Nasmah.
Ɗago kanta tayi ta kalli Nasmah’n, samun kanta kawai tayi da girgiza mata kai alaman “A’a”
“Okay to muje Class” Nasmah tafaɗa tana mai ƙoƙarin haura dakalin ƙofar ajin nasu.
Tare suka shigo ajin ita da Nasmah, Nasmah ne ta ciro littafin Maths ɗinta, ahankali ta shiga yiwa Ziyada bayani dalla dalla da Hausa yanda zata fahimta, abun mamaki kuma sai gashi ta ɗan gane wasu abubuwan, tana kammala koya mata Maths ɗin ta ɗauko Biology shima ta koya mata, aikuwa harma tafi gane Biology’n akan Maths ɗin, kasancewar shi baida lissafi, bakamar Maths ba, har subject ɗin da akayi musu na ƙarshe kafun break wato Agric science saida Nasmah ta koyawa Ziyada, Alhamdulillah kuma ta fahimta sosai, akuma ɗan lokaci ƙanƙani wata ƴar shaƙuwa ta shigo tsakaninsu da Nasmah, duk abun da sukeyi Shukrah na jinsu, amma ƙala bata ce musu ba, saima wata fakekiyar wayarta data ciro ta soma latsawa. Suna kammala karatun aka dawo break.
Sosai suke shan karatu basu suka samu kansu ba sai ƙarfe 1 na rana nan ma sallah aka fito dasu. Nasmah ne ta jata suka nufi masallacin dake cikin school ɗin, Nasmah saida ta jirata tayi alwala sannan itama tayi, atare suka shiga cikin masallacin nan suka iske Shukrah tana sallah, gefe suma suka samu suka tada nasu sallan, suna idarwa Nasmah ta sake kama hanun Ziyada suka fito daga cikin masallacin. Aji suka koma kowa yaciro abincinsa yafara ci, ita dai da bata da wani abinci sai snacks shi ta ciro ta ɗanci kaɗan, Nasmah ce tayi mata tayi’n soyayyen doya da naman kaza wanda tazo da shi, amma sam taƙi ci babu yanda Nasmah batayiba akan taci amma taƙi dolenta ta haƙura.
5:00 pm daidai shine lokacin tashinsu akowacce rana, yauma biyar na cika dai dai aka kaɗa ƙararrawan tashi. Tare da Nasmah suka fito tana fitowa ta hango Kamalu driver tsaye ajikin mota, sallama tayiwa Nasmah da Shukrah sannan tanufi inda yake tsaye.
Tana shiga yaja motar suka bar haraban makarantar.
Tana shiga cikin falon, daddaɗan ƙamshin turare ya daki hancinta, ko ina na falon a gyare yake tsab. Ƙofar ɗakinsa ta kalla, sannan ta wuce ɗakinta. Tana shiga ta soma cire kayan uniform ɗinta, ban ɗaki ta shiga ta yi wanka, yanzu babu abun da bata iya amfani dashi ba na cikin banɗakin.
Tana fitowa awanka ta sanya kaya haɗe da faɗawa kan gado, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, wani irin gajiya haɗi da bacci takeji, basaban ba, idanunta ne suka sauƙa akan wani ƙaton akwati dake aje cikin ɗakin. Tashi tayi ta nufi inda akwatin yake tana buɗewa taga kayane shaƙe acikin akwatin, kama daga kan dogin riguna riga da sket ƴan kanti, da kuma dogin wanduna, murmushi tayi haɗe da lumshe idanunta, batasan da wani baki zata gode masa ba, amma tabbas Ya Zama MADUBI acikin rayuwarta, da sannu itama zata haskaka ta zama kamar wata TAURARUWA. Komawa tayi ta kwanta cike da ɗokin sababbin kayan da tayi masu yawa. Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasa tatashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala bata tashi akan sallayan ba saida ta yi sallan Isha, tana gama naɗe sallayan da tayi sallah akai, ta faɗa kan gado, wani irin baccine ke fusganta, tana kwanciya kuwa bacci ya ɗauketa ko lufayan dake jikinta bata cire ba.
Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa abun yaci tura, kwance yake akan makeken Royal bed ɗinsa wanda yaji lallausan bedsheet. Idanunsa dake alumshe ya buɗe haɗe da sanya hanu ya dafe kansa dake wani irin sara masa kamar zai faɗo ƙasa haka yakeji. Gaba ɗaya duniyar bata yi mashi daɗi, ƙuna yakeji acikin zuciyarsa abubuwa da yawa ne suka haɗe masa, hanunsa na dama ya sanya akan cikinsa wanda ke ɗauke da manya manyan 6 packs, ahankali ya ke murza fatan cikinsa, idanunsa gaba ɗaya sun kaɗa sunyi jajur dasu. Cigaba yayi da murza fatar cikinsa da ɗan ƙarfi haɗe da cije laɓɓansa. “Sai yaushe ne zai zama mutum me cikakken lafiya? sai yaushene zai san cewa shima Namiji ne? yaushe ne damuwarsa zata gushe? yaushe ne zaiyi bacci acikin farinciki da nishaɗi? yaushene zaiji abun da yake buri da fatan ji watarana? Abun tambayar aransa shine yaushe ne yazama haka? yaushe ne kuma zaici wannan jarabawar tasa mai wahala?” waƴannan tambayoyin su yakeyiwa kansa akullum, sau tari yakan cire rai amma yasan Allah na sane dashi idan yana darai watarana zai dace, amma kuma yaushene wannan ranan zata zo? shine abun da baisani ba, tashi yayi ya zauna still hanunsa nakan fatar cikinsa yana murzawa. Ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da sauƙowa daga kan gadon, gaban window ɗinsa ya nufa, tsayawa yayi ajikin window’n haɗe da sanya hanu ya yaye labulen window’n, buɗe glass ɗin window’n yayi take wata iska mai daɗi ta bugi fuskarsa, lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu alokaci guda, ɗaga kansa yayi yana kallon sararin samaniya, farin wata ne ya haske ko ina da ina. Ahankali ya kejin nutsuwa na sauƙar masa, sosai yakejin daɗin ni’imar dake hurawa, yajima tsaye ajikin window’n kafun ya dawo cikin ɗakin. Kwanciya yayi akan gado yayinda ƙafafunsa ke ƙasa, ahaka wani bacci ya ɗaukesa, dagani kasan bajin daɗin baccin yake ba.
** **
Tun 7 ta kammala duk wani shirinta, saboda ta fahimci ba aso azo late a makarantar, duk yanda ta buga sammako wajen fita, amma bata iske shi afalo ba, saidai ta iske daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa, haka tashiga mota Kamalu driver yaja motar suka tafi batare da tayi tozali dashi ba.
Kamalu driver na tsaida motar ta ɗauki jakanta haɗe da soma ƙoƙarin buɗe murfin motar. “Ga wannan Oga yace abaki” Kamalu driver ya tsaidata tahanyar faɗan haka, yana mai ciro kuɗi acikin aljihunsa.
Kallon kuɗin tayi sannan ta kalli Kamalu driver. “Ni kuma mai zanyi dasu to?” ta tambaya cike da mamaki.
“Haka dai yace abaki, hala ko kuɗin taran ki ne” Kamalu driver yafaɗi haka yana me ƙara miƙo mata kuɗin.
Cikin sanyin jiki tasa hannu ta amshi kuɗin, sannan tafice daga cikin motar aranta tana mai cewa da zaran takoma gida zata tambayeshi, hala ko wani abu ya keso tasayomasa da kuɗin.
Yau ta riga Shukra da Nasmah zuwa saboda haka ita kaɗai ta zauna tayi jigum, ba wani jimawa sosai sai gasu sunzo atare, ga mamakinta yau fuskar Shukra asake take babu tsumewa kamar na jiya, Nasmah na ganinta ta saki murmushi haɗe da ƙarasowa ta zauna akusa da ita. “Yau munyi late kin rigamu zuwa” Inji cewar Nasmah dake ƙoƙarin sauƙe jakarta dake kafaɗarta.
Ta buɗe baki zatayiwa Nasmah magana kenan malami ya shigo ajin. Sai bayan yafita ne suka ɗanyi taɗi da Nasmah.. Yau dai sosai Nasmah tasake jawota jikinta ko ina zasu tare suke zuwa kuma Shukra na biye dasu saidai bata cika yawan magana ba. Hatta sallah yau atare sukayi su duka ukun. Ko da suka idar da sallan ma tare sukaci abinci wanda Shukrah ce tazo musu da jallop rice wacce taji ɗanyen kifi.
Yauma agajiye ta dawo daga school ɗin tana idar da sallah ta soma bacci.
*** ***
Yau kimanin sati guda kenan tana zuwa makaranta, Alhamdulillah yanzu kam tana ɗan fahimtan wasu abubuwa musamman da Nasmah ta dage da koya mata, acikin waƴannan kwanaki tayi sabo da Nasmah sosai, duk da cewa Shukra na shiga sha’aninta yanzu amma sunfi sabo da Nasmah, aduk tsawon kwanakinnan bata taɓa ganinsa ba koda sau ɗaya ne, saidai idan ta fito falo tana samun tsaraban ƙamshinsa dayake barmata akowacce rana.Kamar dai yanda kowa ya sani saturday ranar hutuce ga yawancin ɗaliban makarantar boko. To haka ranar yau ta kasance saturday wato (Asabar). Zaune take aƙasa ta tanƙwashe ƙafafunta, jakar makarantarta ne agabanta, sai kuma wani littafin English ɗin dake riƙe a hanunta, lecture’n da akayi musu jiya take dubawa, so take karatun ya zauna akanta sosai, don taji malamin nacewa wani sati zai basu Assignment. Tunda tayi sallah ta ke riƙe da littafi, gaba ɗaya hankali da nutsuwarta naga littafinta so take ta iya duk wani abu da aka koya musu, a yanda ta ba da himma ne yasa ta fahimci wasu abubuwa da dama, wato shi karatu ɗan naci ne idan kanace masa da yardan Allah Zaka iya, sannan zaka gane komai sannu ahankali, yarda da wannan da tayi ne yasa abubuwa da yawa dake cikin karatun da take suka zauna akanta. Yunwar da ta soma ƙwaƙulan cikinta ne yasa ta aje littafin haɗe da jingina bayanta da jikin gado, ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci, kasancewar daren jiya bata wani samu isashshen bacci ba, domin kuwa jiya ba tayi bacci da wuri ba, har sai wajen ƙarfe 12:30 na dare sannan ta kwanta, karatu tayi sosai, sannan gashi kuma yau tayi tashin sassafe sakamakon wani irin zazzaɓi dake ta sanɗanta tun jiya da rana, amma dayake zazzaɓin baiyi ƙarfi ajikinta ba hakan yasa bata jikkata ba.
***
Duk da cewa yau Asabar amma bayajin zai iya zaman gida, shi kansa yasan yana da buƙatar hutu amma kuma yasan ko ya zauna agida hutun nasa bazai samu yanda yakeso ba. Fitowarsa awanka kenan yana ɗaure da towel a ƙugunsa, sannan kuma ga wani ɗan ƙaramin towel still dake riƙe a hanunsa, yana tsane ruwan dake kansa. Yana gamawa ya ɗauko handryer, da shi yayi amfani wajen busar da gashin kansa, mayinsa mai ƙamshi ya shafa, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar dake kansa, mayukan gashi har kala uku ya shafawa kansa, take gashin kannasa ya ƙara bayyana sheƙi da kuma walwali. Dogon wandon jeans wanda ke ɗauke da zane irin na kayan sojoji ya sanya, wandon irin mai yawan aljihunnan ne sannan ƙasan wandon atsuke yake da rubber, wata farar t-shirt ya sanya ajikinsa, take kyawunsa ya sake bayyana sosai kayan suka amshi jikinshi, kasancewarsa namiji mai murɗaɗɗiyar surar jiki, gun ƴar ƙaramar drawer’n da yake aje drugs ɗinsa ya nufa, wani magani dake cikin sachet ya ciro, tare da ɓallan guda biyu ya watsa abakinsa, sannan yakora da ruwan swan. Hanunsa riƙe da goran swan ɗin ya nufi falo. +
Yana shiga cikin falon ya soma bin ko ina dake cikin falon da kallo, ko alaman datti babu acikin falon, hakanne ya tabbatar masa da cewa tabbas gyara falon akayi, duk da cewa dama babu wani datti acikin falon, amma dai kallo ɗaya zakayi kasan an gyara falon.
Kitchine ya wuce ya tafasa ruwan zafi acikin heater cup, yana gamawa ya juye a flask. Zama yayi akan dinning tare da haɗa tea ɗinsa. Sanya kofin tea ɗin yayi agaba ya kasa koda ɗauka ne yakai bakinsa, sai jujjuya spoon ɗin dake hanunsa yake acikin cup ɗin, yanayin yanda ya nutsu yayi shiru shine abun da zai baka tabbacin cewa tunani yakeyi. Tabbas kuwa tunanin yake, maganganun da mahaifinshi yayi mishi masu tsauri su suke damunshi, bai ɗauka fushin da mahaifannashi keyi dashi har yakai haka ba, bai taɓa tunanin suma zasuƙi fahimtarshi ba, maganan da Abbanshi yayi mishi akan cewa wai ya nemo matar aure ya aura, acikin ƴan ƙanƙanin lokaci idan ba haka ba kuma kada ya sake ƙiran wayanshi shine abun dake damunsa, tabbas hukuncin da Abbansa yayi mishi yayi tsauri da yawa, koda wasa baitaɓa tunanin zasu sake kawo mishi maganar aure nan kusa ba, ya ɗauka zasu fahimceshi a wuce wannan stage ɗin, ashe abun ba haka yake ba. Wayarsa dake gefensa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira, jikinsa a sanyaye ya ɗaga ƙiran tare da kara wayar akan kunnensa. 2
STORY CONTINUES BELOW
Mas’oud dake zaune acikin motarsa yace
“Gaye na shigo Abuja fa yanzu”
Cike da ɗan mamaki Sooraj yace
“Da gaske?”
“Bakayarda ba?” murayar dake cikin wayar Sooraj ne ta bayyana raɗau acikin falon, da sauri Sooraj dake zaune akan dinning ya kalli ƙofar falon.
Mas’oud yagani yana murmushi.
Murmushin da iya kansa leɓe Sooraj yayi tare da kashe wayarsa.
“Kai ɗan rainin hankaline Mas’oud” Sooraj yafaɗi haka yana me kallon Mas’oud dake takowa zuwa garesa.
“Ni ne ɗan rainin hankali, ko kuma nida kai ne dukanmu ƴan rainin hankali?” Mas’oud ya faɗi haka yana mai ƙoƙarin jawo wata kujera dake fuskantar wacce Sooraj ke kai ya zauna.
Still ɗan guntun murmushinsa yayi, haɗe da ɗaukan kofin tea ɗinsa ya ɗanyi sipping kaɗan.
“Sauƙar yaushe?”
ya tambayi Mas’oud.
“Banwuce 30 minute da sauƙa ba” Mas’oud yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin ɗaukan wani cup zai haɗawa kanshi tea, duk da cewa bawani damuwa da tea din yayiba kawai don yanajin yunwa ne ya sanya zai sha.
Ɗan sipping tea ɗin kaɗan yayi, tare da kallon Sooraj da yaketa aikin juya tea da spoon ɗin dake hanunsa, ya ɗan karanci damuwa akan fuskar Sooraj ɗin, amma da yake yasan kwanan zancen sai kawai ya share haɗe da cewa..
“Ya maganan waƴannan kayanne? kasanfa yanzu babu kaya aƙasa”
Ajiyar zuciya Sooraj ya sauƙe haɗe da cewa “Next week zanje USA zan taho dasu”
Kai Mas’oud ya jinjina cike da gamsuwa sannan yace.
“Amma baka karɓi ribanka na wannan month ɗin bafa”
Shiru yayi baice komai ba, aƙalla yaɗauki kusan 4 minute bai tankawa Mas’oud ba, ganin haka yasa Mas’oud yin murmushi kawai ya cigaba da shan tea ɗinsa.
Ganin bazai iya shan tea din bane yasanya shi miƙewa tsaye, yana ƙoƙarin barin wajen Mas’oud yace.
“Inason muyi magana dakai”
Komawa yayi ya zauna tare da ɗaukan wayarsa ya soma latsawa “Inaji!” yace ataƙaice.
“Aure nakeso nayi” Mas’oud yafaɗi haka yana wata ƴar dariya.
Ajiye wayan Sooraj yayi tare da dawo da duk wani attention ɗinsa ga Mas’oud.
“Aure kuma?” ya tambaya da ɗan mamaki.
“Eh Aure mana, gaskia Raj na gaji, shekaru 29 fa ba wasa ba, ko so kake na zauna sha’awa ta kasheni, bansamu na kawar da ita ba?” Mas’oud yafaɗi haka yana mai kafe Sooraj din da ido.
Sunkuyar da kai ƙasa Sooraj yayi tare da cije laɓɓansa, wani irin abu mai ƙuna yaji acikin ƙirjinsa, ahankali ya ɗago kansa ya kalli Mas’oud ɗin cikin wata irin murya kamar mai koyon magana yace “Sha’awa!”
“Banason na faɗa halaka Raj, amma seriously ina da buƙatar mace akusa dani, ina da buƙatar zama cikakken mutum nima, inaga kawai zan tura su Baba gidansu Aisha su tambayomin izinin aurenta kawai, inaga hakan shine mafita, amma kai maikagani?” Mas’oud ya tambayi Sooraj.
Wata murmushi yayi wanda shi kaɗai yasan mene meaning ɗin murmushin, leɓensa na ƙasa ya sake ɗan ciza tare da fesar da iska ta bakinsa. “Allah Ya sanya Alkhairi!” Sooraj yafaɗa ataƙaice.
“Ameen” Mas’oud ya amsa yana maison karantar yanayin da Sooraj ɗin ke ciki, saidai kuma sam ya kasa gano wani irin yanayi Sooraj ɗin ke ciki, domin kuwa Sooraj murɗaɗɗen mutum ne da wahala gane gabansa da bayansa.
“Abba ya faɗamin yanda kukayi dashi, ina fata dai zakayi abun da ya keso?” Mas’oud ya tambayi Sooraj.
Miƙewa Sooraj yayi daga kan dinning haɗe da ɗaukar wayarsa ya bar wajen,, da kallo Mas’oud ya bisa har ya shige ɗakinsa, kai kawai Mas’oud ya girgiza, sannan yadawo cikin falon ya zauna.
Yana shiga cikin ɗakinsa ya rufo ƙofar gam, jingina bayanshi yayi da jikin ƙofan tare da rumtse idanunshi, wani iri ya keji acikin jikinsa, baijin ayau zai iya ɓoye rauninsa, inama da ace zai iyayin kuka, inama da ace akwai wani wanda zaiyi sharing ɗin damuwarsa dashi, inama da ace zaiji abun da Mas’oud ya keji, hanu yasa ya dafe saitin ƙirjinsa da keyi masa zafi. Aƙalla ya ɗau kusan sama da mintuna 10 tsaye ahaka, da ƙyar ya iya jan ƙafafunsa ya zauna akan gado, haryanzu idanunsa a rufe suke, jin kansa yake nayi masa ciwo, kwanciya yayi akan gadon tare da buɗe idanunsa, numfashi yake fitarwa a hankali…. Saida yaji yaɗan dawo normal sannan yatashi ya fita falo, can ya samu Mas’oud, sake ɗan tattaunawa sukayi kafun daga bisani suka bar gidan baki ɗaya.
Gumine keta fitowa daga jikinta, zaune take agefen gado ta takure jikinta waje ɗaya, wani irin ciwo mararta da cikinta keyi mata, sake matse ƙafafunta tayi, laɓɓanta kuwa sai rawa suke kamar wata wacce take jin sanyi, ahankali sautin kukanta ke tashi acikin ɗakin, jin mararta take kamar zata ɓalle ga zazzaɓi mai zafin gaske da ya rufeta. Jin bazata iya daure ciwon ita kaɗai bane, yasa ta tashi a daddafe ta nufi falo. Tana kaiwa tsakiyan falon ta faɗi a wajen tare da sakin wani ƙara, ciwonne ya ta so mata gadan gadan, kwanciya tayi aƙasa tanata mutsu mutsu da ƙafafunta yayinda ciwon ke ci gaba da nuƙurƙusanta. Kuka take sosai hatta numfashinta saida ya soma seizing.
Dawowarsu kenan daga Sheraton hotel inda sukaje suka gudanar da wani business ɗinsu, atare suka shigo cikin falon. Akuma daidai lokacinne kukanta ya dirarmusu acikin kunnuwansu, a ɗan razane Mas’oud ya kalli Sooraj, shima kallonsa yayi amma sai ya share ya ƙarasa cikin falon, idanunsa yaɗan waro ganin yanda take yashe aƙasa gaba ɗaya ta fita acikin hayyacinta, ɗan kwalin dake kanta ya zame gefe yayinda gashin kanta ya watse akan carpet ɗin dake malale a tsakiyar falon, yanayin yanda yaga takeyi shine abun daya ɗan tsoratashi domin kuwa ta shiɗe sosai da alama ma bata cikin hayyacinta, amatuƙar tsorace Mas’oud ke kallon Yarinyar yana kuma kallon Sooraj, koda wasa baitaɓa tunanin Sooraj yana tare da yarinyar ba, a iya tunaninsa Sooraj yajima da sallamanta ta kama gabanta, wani irin bahagon tunani ne ya ɗarsu acikin ran Mas’oud, bakinsa cike suke da tarin tambayoyi amma dole ya adana tambayoyinsa.
Ƙarasawa inda take yayi haɗe da ɗan durƙusawa hanunsa yakai yaɗan bugi fuskanta “Ke!” ya faɗa yana mai sake ɗan tattaɓa fuskarta.
Wani irin nishi tayi take kuma gaba ɗaya jikinta ya sake komai nata ya daina motsi. Ya ɗan razana kaɗan da al’amarin nata, ɗaukarta yayi caɗak ajikinsa ya nufi ƙofar fita daga falon. Tsananin mamaki shiya hana Mas’oud rufa masa baya, tsayawa yayi yakasayin komai kamar wani statue, ganin tsayuwar baza ta kai mishi ba yasa ya rufa musu baya, lokacin da ya fita waje har Sooraj ya sanyata acikin mota yana ƙoƙarin shiga gidan driver, da sauri Mas’oud yaje ya shiga motar. Gudu sosai Sooraj keyi akan titi mintuna kaɗan suka isa asibiti, likitoti ne suka karɓeta sukayi ciki da ita.
Zama yayi akan wata kujera haɗe da sanya hannayensa ya rufe fuskarsa da tafukan hannunsa. Agefen Sooraj Mas’oud shima ya zauna shiru yayi ko wanne daga cikinsu da irin nazarin da yakeyi acikin ranshi, tambayoyine cike azuciyar Mas’oud, shi kuwa Sooraj ya marasa wani tunanin zaiyi, abubuwa sunyi masa yawa, ahankali idanunsa suka kaɗa sukayi jajur dasu, tananne kawai zaka iya fahimtar tarin damuwan da yake ciki. Wani likitane ya fito daga cikin ɗakin da aka kwantar da Ziyada, ce wa yayi su Sooraj ɗin su sameshi a office ɗinsa, babu musu suka tashi suka rufa masa baya.
Ajiyar zuciya Sooraj ya sauƙe abayyane tare dayin ƙasa da kansa.
Mas’oud ne yayi ƙarfin halin cewa “Yanzu likita wani hali take ciki?”
Gyara zama Likitan yayi haɗe da cewa “Kamar yanda na faɗa muku a farko, ba wani babban matsala bane, yawancin mata sukan samun irin wannan matsalan idan zasu fara period, to itama tana ɗaya daga cikin irin waƴannan matan, amma babu wani damuwa zata warke insha Allah, yanzu haka ta samu bacci, da ta farka kuma zamu baku Sallama, ga wannan saiku sayo shine magungunan da zatana sha” likitan ya faɗi haka yana me miƙowa Mas’oud wata ƴar farar takarda da yayi rubutu ajiki, amsa Mas’oud yayi tare da ɗan satan kallon Sooraj wanda har yanzu kansa ke ƙasa bai ɗago ba. Hanu dukansu suka miƙawa likitan suka gaisa daga haka suka fice daga cikin office ɗin, direct wajen da ake biyan kuɗi Sooraj ya nufa, kuɗin gadon da aka kwantar da ita ya biya, sannan suka nufi pharmacy. Bayan sun karɓi maganin Sooraj ya sake biyan kuɗi, direct motarsa ya nufa, ganin haka yasa Mas’oud ya biya abaya. Harya buɗe murfin motar muryar Mas’oud ta doki dodon kunnuwansa ɗan tsayawa da abun da yakeyi yayi tare da juyowa ya fuskanci Mas’oud.
“Wacece ita awajenka? Sannan mai yasa ka ajiyeta agidanka? Me wannan rayuwar da kukeyi take nufi?” Mas’oud yayi masa duka waƴannan tambayoyin alokaci ɗaya.Buɗe murfin motar yayi ya shiga, batare da yace wa Mas’oud dake tsaye ƙala ba, zai rufe murfin motar ne, Mas’oud yayi saurin riƙe murfin ransa aɗan ɓace yace.
“Wai hakan da ka keyi me yake nufi ne Sooraj? me kake tunani idan su Abba sukaji abun da ka aikata? menene amfanin hakan!!” +
Wani iska ya fesar daga bakinsa, tare da jingina bayanshi da jikin kujeran motar.
“Mai kakeson ji daga gareni Mas’oud?” yafaɗi haka cikin wata murya mai sanyi.
A ƙufule Mas’oud yace.
“Bansani ba” Juyawa Mas’oud yayi afusace yabar wajen, da ƙafansa ya nufi hanyar fita daga cikin asibitin, Sooraj na kallonsa ya tari taxi ya shiga, yana ganin tashin taxi ɗin ya jawo murfin motarsa ya rufe, kifa kansa yayi akan steering motar, tare da sauƙe wata ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya, ya ɗauki kusan mintuna 6 ahaka, kafun daga bisani ya ta da motarsa ya fice daga cikin asibitin. Direct wani super market ya nufa, zama yayi akan wata kujera, tare da umartan wata ma aikaciyar wajen da ta haɗa masa duk wani abu da tasan mace na da buƙata, kama daga kan suturun sawa da dai sauransu, take ita kuwa tashiga aikinta, kaya masu kyau ta jidar masa hadda su pants, kasancewar tasan duk wata mace indai ta girma to tana da buƙatarsu, bai da mu da yawan kuɗin kayan ba haka ya cire ya biya, yaran dake aiki a wajen su suka kwashe kayan suka kai mishi cikin mota.
Kafun ya koma asibitin saida ya biya ta wani hotel yayi take away, sannan ya ɗauki hanyar komawa asibitin. Yana shiga asibitin direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa.
Tana kwance tana baccinta cikin kwanciyar hankali.
Zama yayi akan wata kujera dake gefen gadon tare da lumshe idanunsa. Kamar jiran zuwansa take ahankali ta ɗan soma motsawa, jin motsinta da yanda numfashinta ke fita ne, ya san yashi buɗe idanunsa, haɗe da maida kallonshi gareta.
Ahankali ta soma ɗan ware manyan idanunta harta buɗesu tarwai, saidai kuma kallo ɗaya zakayi mata kasan taji jiki, domin kuwa hatta ƙwayan idanunta saida suka sauya kala, sunyi wani fari fat dasu.
Tashi tayi ta zauna tana mai ɗan cije laɓɓanta, sam batasan da cewa yana cikin ɗakin ba. “Aushhh” taɗan saki wani ƙara, saka makon murɗawan da taji maranta yayi, ɗan yarfe hannuwanta ta somayi, tare da soma yunƙurin sauƙa daga kan gadon, Idanunsu ne ya sarƙe acikin na juna, ji tayi gabanta ya wani irin faɗuwa, da sauri tayi ƙasa da kanta, tare da haɗiyan wani yawu dake maƙale a maƙoshinta.
Aƙalla yaɗauki kusan 50 second yana kallonta, abun da bai taɓa yi ba kenan, ahankali ya janye idanunsa daga kanta tare da kawar da kanshi gefe.
Shiru ne ya shiga tsakaninsu na kusan mintuna 2, jin wani abu me ɗumi tayi ya fito daga jikinta, hakan yasa ta ƙosa ta je banɗaki ta duba ko menene, ganin zaman bazai kaita ba yasa ta sauƙa daga kan gadon, banɗaki’n dake cikin ɗakin ta shiga tare da rufo ƙofar, tashi shima yayi ya fita daga cikin ɗakin.
Bugun zuciyarta ne ya tsananta, duk da kasancewar tasan abun da ta gani ajikinta mai yake nufi, amma sai da ta ɗan tsorita.
“Yanzu yazatayi kenan? wa zata faɗawa ya taimaketa?” Tambayar da tayiwa kanta kenan. Ji tayi ana knocking ƙofar banɗakin, ai saura ƙiris ta zame awajen da take tsaye saboda tsoro, atunaninta Sooraj ne ke buga ƙofar, ƙafafunta ne suka soma rawa. “Taya zata fara faɗa masa matsalanta?” still ta kuma sake tambayar kanta, jin anata buga ƙofar ba a tsaya ba, ya sa ta taho cikin sanɗa ta buɗe ƙofar, wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe, sakamakon ganin wata likita mace da tayi tsaye abakin ƙofar, ashe ma ita ke buga ƙofar ba Mai taimako ba, saɓanin tunaninta.
STORY CONTINUES BELOW
“Sannu ya jikinnaki?” nurse ɗin ta tambayeta.
“Da sauƙi” Ziyada ta bata amsa tana ɗan ƙaƙalo murmushin dole.
“Masha Allah haka ake so ae, ga wannan saiki kimtsa kanki ko” nurse ɗin ta faɗi haka tana me miƙo mata wata baƙar leda dake hanunta.
Karɓan ledan tayi tare da komawa cikin ban ɗakin, tana buɗe ledan taga pad’s da kuma pant’s ne aciki, wani ƙaton ajiyar zuciya ta sauƙe, gefe guda kuwa tsananin mamaki haɗi da kunya ne ke ɗawainiya da ita, da farko dai mamakin yanda akayi nurse ɗin tasan halin da take ciki take, na biyu kuma tsantsar kunyar nurse ɗin ne ya kamata, wani pant ta ɗauko wanda anriga da an maƙala pad ɗin ajikinsa, kallon yanda aka maƙala pad ɗin tayi da kyau, sai da ta ciro wani pant ɗin ta gwada maƙalawa taga yayi sannan ta sauƙe ajiyar zuciya, kasancewar dama bata san ya ake amfani dashi ba. Aɗaɗare ta fito daga banɗakin sai dai rashin ganin kowa da tayi acikin ɗakin hakan sosai yayi mata daɗi. Tana zama akan gado, akaturo ƙofar ɗakin, wannan nurse ɗin ce dai ta kuma dawowa, bayani tayi mata sosai akan yanda zata kula da kanta, da kuma yanda za tana tsabtace jikinta, sannan tace mata taje yayanta na jiranta a mota. Ɗaukan ledan da nurse ɗin ta bata tayi, sannan suka fito atare da nurse ɗin, har bakin motar Sooraj nurse ɗin ta rakota sannan sukayi sallama.
Tana shiga cikin motar ko gama gyara zamanta batayi ba ya yiwa motar key. Saida suka hau titi sannan ta ɗan saci kallonsa ta gefen idanunta, maganane abakinta, amma yanda fuskarsa take babu alaman wargi, yasa taja bakinta tayi gum, ita ayanda ta fuskanta ma shine, shi ko da yaushe ahaka fuskarsa take.
Basu yi wani tafiya sosai ba, ta ga ya gangara gefen titi tare da tsaida motar cak, juyawa yayi ya ɗauko wata leda dake aje a sit ɗin baya, miƙo mata ledan yayi tare da cewa.
“Kici yanzu yanzun nan sai kisha magani”
Baijirayi mai zata ceba ya buɗe murfin motar ya fita, tana kallonsa ya shige cikin wani waje mai kama da kamfani, wanda yake gaba kaɗan da inda ya aje motar tasa, ledan ta buɗe ta ciro take away ɗin, rubber spoon ɗin dake jikin take away ɗin, ta zare haɗe da sanyawa acikin abincin. ahankali take tsakalan abincin, gaba ɗaya bata wani jin daɗin bakinta, duk da cewa tana jin yunwa amma batajin abinci zai wani samu shiga cikinta sosai, bata wani ci abincin sosai ba, ta rufe take away ɗin tare da maidashi cikin ledan, goran ruwan da tagani a inda ya tashi tasanya hanu ta ɗauka, buɗewa tayi tare da kai bakin goran bakinta, lumshe idanunta tayi, tare da sauƙe wani irin ajiyar zuciya, tayi imani duk wani abu da zai fito daga gareshi to ƙamshi yake, hatta goran ƙamshinsa take, tana son wannan ƙamshin nashi har acikin ranta, bama ita kaɗai ba ta tabbatar duk wanda yaji ƙamshin nashi dole zai so sa. Bata fargaba sai kawai jin motsinsa tayi a gefenta, da sauri ta kalleshi don sam batasan da zuwanshi ba, buɗe wani waje mai kama da ɗan ƙaramin drawer dake cikin motar yayi, magungunanta ya ciro, da kansa ya ɓare magungunan ya miƙa mata, aƙoƙarinsa na ya zuba mata magungunan acikin hanunta ne hannayensu suka haɗe waje guda, da sauri ya zuba mata magungunan acikin tafin hanunta, tare da zare nashi hanun, ba don taso ba haka tasha magungunan kasancewar suna da ɗan ɗaci, tana sha ta jingina bayanta ajikin kujera tare da lumshe idanunta. Tuƙi yake amma gaba ɗaya hankalinshi na ga wayarsa yana duba wani saƙo da aka turo masa, ahaka har suka isa gida.
Yana danna horn mai gadi ya wangale masa gate ya tura hancin motar ciki.
Jin sun tsaya ne yasa ta buɗe idanunta ahankali, ganin yana ƙoƙarin fita daga cikin motar ne, yasa itama ta buɗe murfin motar ta fita. Sawa yayi Kamalu driver ya shigar masa da kayan da ya sayo ciki.
Yana shiga cikin ɗakinsa ya kwanta flat akan gado tare da lumshe idanunsa, kamar an tsikareshi haka ya buɗe idanunsa da sauri, bakomai yasa hakan ba face, ganin oily eyes ɗinta da ya keyi suna yi masa yawo acikin nasa idanun, hakan kuwa na sawa yaji wani iri ajikinsa.
Ban ɗaki ya wuce ya haɗawa kansa ruwan wanka..
STORY CONTINUES BELOW
Itama tana shiga cikin ɗakinta, gado ta hau ta kwanta, tare da cusa kanta acikin pillow, abu kamar wasa sai ga wani sabon bacci ya sake ɗaukanta…
*** Tsakanin jiya da yau Alhamdulillah ciwon ya ɗanyi mata sauƙi, kwana biyunnan jinta take atakure, zuwa yanzu ta saba da makaranta, shiyasa takejin zaman gidan gaba ɗaya bayayi mata daɗi, gashi shima Ogan gidan ba ganinshi take ba, ita kaɗai take rayuwarta, jakar makaramtarta ta ɗauko ta shiga haɗa littatafanta, tana gamawa ta jawo ledan abincin da aka kawo mata ta soma ci, bata wani ci mai yawa ba ta ture abincin gefe, jin gidan ya ɗauki shiru babu alaman motsin kowa acikinsa ne yasa ta fita zuwa falo, kusan kullum TV plasma’n dake cikin falon a kashe yake, amma yau ga mamakinta akunne ta sa meshi, zama tayi akan sofa tare da maida hankalinta ga TV’n, tana nan zaune acikin falon har aka ƙira sallan Isha sai alokacin ta tashi ta koma ɗaki, tana shiga tayi kwanciyarta, kasancewar ba sallah takeyi ba.
1:30 na dare, ƙaran taɓa gate ɗin gidan da ake, shine yayi sanadiyar tashinta daga bacci, ahankali ta sauƙo daga kan gadon, bakin window ta nufa don ganin wake taɓa gate ɗin, duk da babu wadataccen haske aharabar gidan, amma inuwarsa kaɗai yasanya tagane wanene, domin akaf gidan babu wani mai irin yanayin jikinsa shi kaɗai ne, tana ganinsa da kansa ya buɗe gate ɗin gidan, sannan ya koma ya shigo da motarsa ciki, tana ganin ya mai da gate ɗin ya rufe ta ɗan saki wata ajiyar zuciya, mamaki da wani kokonto ne suka ɗarsu acikin zuciyarta, don son sake tabbatarwa da kanta cewa shiɗinne ko ba shi bane, yasa ta ɗan buɗe ƙofarta ahankali fitowa tayi ta tsaya abakin ƙofar, dai dai lokacin shi kuma ya buɗe ƙofar falon ya shigo, key ya murza ajikin ƙofar sannan yabar key ɗin ajiki, Yana maiƙoƙarin cire rigar dake jikinsa ya ƙarasa gaban fridge. Buɗewa yayi ya ɗauko goran Fearless. Wuceta yayi tamkar baiganta ba, alhali kuma tunshigowarsa idanunsa suka gane masa ita, harya ɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar ɗakin nasa, sai kuma ya dakata batare da ya juyo ba yace.
“Me kikeyi anan?”
Ziyada dake ƙoƙarin komawa ɗaki, taji sauƙar muryartasa tamkar rugugi acikin kunnuwanta, da sauri ta juyo garesa saidai bata iya kallonsa ba, duk da cewa ya bata baya.
“Babu”
Tace murya asanyaye.
“Wani abu ya faru ne?” Yasake tambayarta still batare daya juyo ya kalleta ba.
“A’a” Ta bashi amsa muryarta naɗan rawa, hakanan idan yana gabanta sai taji wani irin tsoronsa ya kamata.
Murɗa ƙofarsa yayi ya shige ciki
tare da rufo ƙofar, tana tsaye taji ya murzawa ƙofar key ta ciki, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da komawa nata ɗakin itama, da ƙyar ta samu bacci yasake ɗaukanta.
Shikuwa bai iya samu bacci ya ɗaukesa ba, har sai da yasha maganin da ke taimaka masa wajen sanyashi bacci, duk da haka dai baccin baiyishi cikin daɗin rai ba.
7:00
Daidai ta gama shiryawanta, tayi kyau acikin uniform ɗinta kamar kullum, tana kammala saka white socks ɗinta, tasoma jin ana knocking ƙofar falon, school bag ɗinta ta rataya bisa kafaɗanta sannan tafi ta zuwa falon, dama bata saba ganinshiba don haka batasa aranta zata ganshi ba. Tana buɗe ƙofar wanda ke kawo mata abinci kullum yaɗan yi mata murmushi, itama murmushin tayi masa tana ƙoƙarin gaidashi ne ya miƙo mata wata kula mai kyau wacce take da ɗan mariƙi a samanta.
“Madam ga saƙonki inji Oga” yace da ita.
Karɓa tayi, shikuma ya juya yayi tafiyarsa, komawa cikin falon tayi tare da buɗe kulan. Kulan irin mai hawa ukunnanne wato (3pieces) hawan farko da ta buɗe soyayyen dankali ne aciki wato chips da kuma ƙwai, sai hawa na biyun dake ɗauke da gasashshen nama mai albasa, hawan ƙarshe shine ke ɗauke da shinkafa fried rice wacce taji liver, ɗaukan kulan tayi ta riƙe ahanunta, tana fita waje ta samu Kamalu yana tsaye ajikin mota yana jiranta. Tunda suka ɗauki hanyar makarantar yau Kamalu keta mata zuba, ita dai ba gadon magana bace hakan yasa take amsa masa kaɗan kaɗan, shikuwa sai labarai yaketa bata, ganin yanda take amsa masa ne, yasa aranshi yace “Duk yanda akayi itaɗin jinsin Oga ce, da’alama duka zuri’arsu haka suke basason magana”
Yau kam Su Nasmah sun rigata zuwa, tana zama Nasmah ta ce “Ki koma kinyi late”
Dariya ta yi tare da ɗan satan kallon Shukrah, matsawa kusa da Nasmah tayi sosai cikin ƙasa da murya tace.
“Yau maiyasamu Shukrah na sake ganin fuskarta babu walwala?”
Baki Nasmah ta taɓe haɗe da cewa. “Hmm barta kawai kekam wahalane bai ishetaba, wai fa soyayya take kullum kuma sai sunyi faɗa da saurayin”
Idanu Ziyada taɗan zaro waje cike da mamaki tace. “Soyayya!”
“Eh Soyyayya” Nasmah ta faɗa tana ɗan kallonta.
Shiru Ziyada tayi tare da jin wani abu acikin ranta. “Kenan dama Soyayya gaskia ce?” tambayar da tayiwa kanta kenan sannan ta kuma sake tambayar kanta “Menene alamomin soyayya?”
“Yanaga kamar kina tunani” Cewar Nasmah da ta shiga mamakin yanayin da taga Ziyada ta shiga.
“Babu” Ziyada tafaɗi haka tana ɗan yin murmushi, Malamin English ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka bada gaba ɗaya hankalinsu gareshi.
Yau a wajen da aka tanadar musamman dan cin abincin ɗalibai sukaci abincinsu, ita dai Shukrah gaba ɗaya bata da wani walwala, Ziyada da Nasmah ne kawai suketa sha’aninsu. Shaƙuwar da ke tsakanin Ziyada da Nasmah shine ke ƙarawa Ziyada jin daɗin rayuwar makarantar. Yau ba atashesu ba har sai biyar da rabi kasancewar anshiga dasu meeting akan jarabawan da zasu fara next month. Agajiye ta dawo gida ga ciwon cikin dake sanɗanta, da ruwan zafi tayi wanka sannan ta kwanta.
11:00 ta farka daga ɗan baccin daya ɗauketa, wani irin ciwon da cikinta keyi mata shine abun daya ɗaga mata hankali, Kuka take hanunta dafe da saman mararta wanda takejinta kamar zata ɓalle.
Yana zaune akan gado yana danna laptop ɗinsa, ahankali ƙaran kukanta ya shiga kawowa kunnensa ziyara. Ɗauke hanunsa yayi daga kan laptop ɗin tare da yin shiru yana mai sauraran yanda kukan nata ke tashi. Kallon agogo yayi yaga ƙarfe 11:10 na dare, wata ƴar ƙaramar tsuka yaja tare da sanya hanu ya dafe goshinsa. “Me na ɗaukowa kaina ne?” tambayar da yayiwa kansa kenan. 3
Jin kukannata na daɗa ƙaruwa ne yasan yashi miƙewa, ƙofar ɗakin ya buɗe ya fita, tsayawa yayi ajikin ƙofar ɗakin da take yana mai tunanin shiga cikin ɗakin. Jin taƙi daina kukan ne yasashi murɗa handle ɗin kofar ya shiga. Yashe ya ganta aƙasa tanata birgima gaba ɗaya gashinta ya watse akan tiles, kuka take irin na fitar hayyaci. Ƙarasawa yayi inda take yashe aƙasan tana ta mutsu mutsu, hannayensa yasanya ya kama kafaɗunta, jin sauƙar hanun mutum akan kafaɗunta yasanya ta kama hunun nasa ta damƙe da ƙarfi, da ɗayan hanunnasa da bata kama ba yayi amfani wajen ɗago haɓarta, gaba ɗaya fuskarta ta ɓaci da hawaye, zara zaran eye lashes ɗinta sun jiƙe da hawaye sun manne akan fatarta. Hanunsa dake cikin hanunta ta ƙara matsewa tare da sakin wani ƙara, ji take kamar taita buga kanta ajikin gini ko zata samu salama, ganin yanda take shiɗewa ne yasanya shi ɗagata caɗak ya nufi kan gado da ita, kwantar da ita yayi, tare da ɗauko magungunanta ya bata.
***
After 30 minute har yanzu gunjin kukanta ne ke tashi acikin ɗakin, sama da mintuna talatin kenan da bata magani amma har yanzu ciwon bai lafa ba, tun tanayin kukan da duka jarumtarta har takai tanayin kukan acikin yanayi na galabaita, hankalinsa ne yasoma tashi, wayarsa ya ɗauka ya ƙira Number’n Dr.Waleey, shaida masa abun dake faruwa Sooraj yayi, shiru yayi yana maijin amsar da Dr.Waleey ke bashi, cikin rashin ƙarfin guiwa ya aje wayartasa bayan sunyi sallama da Dr.Waleey’n, shiru yayi haɗe da zuba mata mayun idanunsa, sosai zuciyarshi ta karaya akanta, wani irin tausayinta yaji ya daki zuciyarsa, duk wanda yaganta acikin irin wannan halin sai ya tausaya mata, musamman yanda tayi buji buji da gashin kanta, ga numfashinta dake ƙoƙarin sarƙewa tsabar kukan da tayi, maganganun Dr.Waleey ne suke dawowa cikin kunnensa. Bayajin zai iya aikata abun da Dr.Waleey yace yayi, sannan kuma bayajin zai iya jure ganinta acikin halin wahala, baisan maiyasa yake jin son taimakonta ba tun farko, ayanzu yanaji inama da ace tun farko bai taimaketa ba, rumtse idanunsa yayi da ƙarfi sakamakon yanda yaga takeyi, baida wani zaɓi wanda ya wuce ya taimaketa, tashi yayi ya nufi gadon, sautin bugawar zuciyarshi ne ya tsananta yayinda ƙirjinsa ke tsalle kamar zai faɗo ƙasa, da ƙarfi bugun zuciyarsa ke harbawa…Ƙirjinsa ne ke ta dokawa kamar zai fito waje. Yana ƙarasawa gaban gadon yaja ya tsaya tare da kafeta da idanunsa, jin kukanta yake har acikin ransa, hannayen rigansa ya ɗan naɗe tare da nufar toilet ɗin ɗake cikin ɗakin, heater ya kunna ya tari ruwan zafi acikin wani ɗan madaidaicin bucket, towel ya ɗauko sannan ya fito daga cikin toilet ɗin. Ƙafansa ɗaya yasanya ya taka kan gadon, baisan tayaya kuma ta ina zai fara ba, hakan baikamacesa ba, sannan kuma sam hakan ba aikinsa bane, saidai kuma sosai yake tausayin halin da take ciki. Aƙalla yaɗau kusan mintuna 10 a haka ya kasa aikata komai, yayinda ita kuwa har yanzu take aikin kuka gaba ɗaya tasake fita hayyacinta, zama yayi akan gadon tare da sanya towel ɗin acikin ruwan zafi, hannayensa ne suka ɗauki rawa, ya kasa koda kai hanunsa jikinta, zuciyarsa bugawa take, hanunsa yakai kan wuyanta ya ɗan taɓa, ji yayi babu wani zazzaɓi sosai ajikinnata, rumtse idanunshi yayi tare da kai hanunsa kan lafeffen cikinta, tamkar wanda aka jonawa shocking haka hannayensa ke rawa, da ƙyar ya iya ɗan ɗage rigan dake jikinta yayi sama dashi, still hannayensa na rawa yasanya hanu ya ɗanyi ƙasa da sket ɗinta, towel ɗin yaciro daga cikin ruwan zafin tare da ɗan matsawa ya rage ruwan dake jiki, sake rumtse idanunshi yayi tare da ɗaura towel ɗin adai dai kan cikinta, wani ƙara tasanya tare da ɗan soma yunƙurin tashi zaune, baisan sanda yasanya ɗayan hanunsa ya maida ita ta kwanta ba, sai alokacin ya samu damar buɗe idanunshi ya sauƙesu akan fuskarta, hawaye ne kawai ke gangarowa ta gefen idanun ta, gaba ɗaya ta galabaita. Sake danna towel ɗin yayi akan cikinta, gani yayi ta sake rumtse idanunta, ahankali yake ɗan matsa towel ɗin akan cikinta, ƙasa ya somayi da towel ɗin daidai kan mararta ya tsaya, Yanayin yanda yake matsa towel ɗin akan maranta ne, yasanya ta jin wani ɗumi na ratsa gaba ɗaya ilahirin jikinta, sake maida towel ɗin cikin ruwa yayi tare da ɗan matsewa, sake manna mata yayi akan maranta, haka yadinga yi mata har tsawon wasu lokuta, ahankali kukanta ya tsaya cak, wani irin ajiyar zuciya take sauƙewa akai akai, fitar numfashinta ne ya soma sanja sauti, ya zama na yana fita slowly, duk wannan abun da yake mata, bai bari idanunshi sun kaishi ga kallon jikinta ba. Cikin wani irin yanayi na wahala ta kamo hanunsa na hagu ta riƙe acikin nata hanun, ganin haka yasa ya aje towel ɗin agefe, ɗan ranƙwafowa yayi tare da kawo bakinshi dai dai saitin kunnenta, ahankali ya soma hura mata iskan dake bakinsa acikin kunnenta. Daddaɗan ƙamshin turarensa ne ke ziyartan hancinta, yayinda iskan bakinsa dake hura mata ya kasance garkuwa wajen samun nutsuwarta, ahankali taji wani irin salama na sauƙar mata, cikin wani irin yanayi hucin numfashinsu ke gauraya waje guda, jin yanda sautin numfashinta ya sauya ne, yasanyashi ɗan ɗago da kansa ya dube ta, gani yayi tana fitar da numfashi ahankali da alama bacci ne ya ɗauketa, wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da ɗago kansa daga ranƙwafon da yayi, hanunsa dake cikin nata ya kalla wanda ta damƙeshi gam. Ƙoƙarin cire hanunsa daga cikin nata yayi, amma yaji ta sake riƙe shi gam, cikin ɗan dabara ya samu ya zare hanunshi, hannayensa ya ɗaura akan kafaɗunta tare da gyara mata kwanciya, blanket ya rufa mata, sannan ya rage mata hasken ƙwan wutan dake cikin ɗakin, tashi yayi ya fita tare da jawo mata ƙofar. Ɗakinshi ya koma yayi kwanciyarsa, ya jima kafun bacci ɓarawo ya samu damar ɗaukarsa. +
Tunda ta kwanta ba itace ta farka ba sai ƙarfe 8:00 daidai na safiya, ahankali take buɗe gajiyayyun idanunta da suka kumbura sukayi luhu luhu dasu, kasancewar daren jiya tasha kuka sosai, tashi tayi ta zauna akan gadon tare da sanya hanu ta shafi saman mararta, ko ɗigon ciwo bataji ajikinta saidai kasala kawai dake damunta, lumshe idanunta tayi tana mai ƙoƙarin son tunano abun da ya faru da’ita a daren jiya, ita dai bazata iya cewa ga abun daya wakana ba, amma tabbas tasan ta ganshi acikin idanunta, sannan kuma taji daddaɗan ƙamshinsa acikin hancinta, amma wata zuciyar ta na faɗa mata cewa ba shi bane. Zuro ƙafafunta ƙasa tayi daga kan gadon tare da tashi tsaye, banɗaki ta wuce ta haɗawa kanta ruwan wanka mai ɗan ɗumi, sosai taji daɗin wankan da tayi domin ya ƙara taimakawa wajen warware mata gajiyan dake jikinta.
STORY CONTINUES BELOW
Cikin sauri sauri ta zura kayan uniform ɗinta, safa’nta ta sanya tare da ɗaukan school bag ɗinta, duk da batasan ƙarfe nawa bane yanzun, amma tabbas da dukkan alama yanda taga rana ta bayyana raɗau tasan tayi latti, fitowa falon tayi tana mai ƙoƙarin cusa wani littafi dake hanunta acikin jaka, sam bata lura dashi ba kasancewar bata kawo ma aranta cewa zata ganshi ba.
“Ina zakije?” muryarsa ya doki dodon kunnenta, cak ta tsaya daga tafiyar da takeyi, tare da dawo da kallonta zuwa inda taji sautin muryar ta fito.
Zaune yake akan dinning table yasha kyau cikin riga da wando na suit amma baisanya suit ɗin ba, sai dai tana aje agefensa, parking shirt ne ajikinsa Navy blue colour wanda ta ƙara masa kyau. Cup ɗin tea ne ahanunsa yana sha da kaɗan kaɗan.
Bazata iya jure kallonshi ba, saboda sosai yake mata kwarjini. “Dama zanje makaranta ne!” tabashi amsa cikin muryarta mai sanyi.
Shiru yayi kamar bazai amsa mata ba, sai kuma ya ɗago kansa yaɗan kalleta. “Zokici abinci!” yace da ita ataƙaice.
Duk da tasan cewa tayi latti, amma bazata taɓa iya faɗa masa hakan ba, batasan tayaya zata iya fara zama tare dashi ba, amma ya zatayi? Ƙarasawa gaban dinning ɗin tayi tare daɗan durƙusawa. “Ina kwana!” tace dashi cikin sassanyar murya.
Kansa kawai ya kaɗa mata batare da ya amsa ba, aɗaɗare ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dake dinning table ɗin. Food flask da kuma plate ɗin dake gabanshi ya turo mata, kana ya cigaba dashan tea ɗinsa, wayarsa ya ɗauka yasoma latsawa. Buɗe food flask ɗin tayi ta ɗan ɗibi abincin kaɗan, gaba ɗaya ta kasa sakewa taci abincin, jin kanta take atakure, duk abun da takeyi yana lure da ida ta gefen idanunshi, miƙewa tsaye yayi tare da ɗaukan suit ɗinsa ya sanya.
Saida ya ɗanyi tafiya kaɗan sannan ya tsaya, batare da ya juyo ya kalleta ba yace.
“Yau bazakije school ba kizauna agida” Baijira abun da zata ce ba yayi gaba abunsa.
Bata ɗauke idanu akanshi ba har saida yafice daga cikin falon.
“Yau bazakije school ba ki zauna agida”
Tamaimaita abun daya faɗa cikin ɗan nazari, kenan yana nufin tazauna agida kada taje makaranta? Babu mai amsa mata, hakan yasa ta ci gaba da tsakalan abincin. Bata wani ci abincin sosaiba tatashi ta koma ɗaki, uniform ɗinta ta cire sannan ta dawo falo ta zauna, ƙurawa tv idanu tayi tana kallon yanda ake koyar da girki.
***
Shikuwa yana fita daga falon direct wajen lafiyayyar motarsa ƙirar Range Rover Blue colour ya nufa, yana shiga Kamalu driver yaja suka fice daga cikin gidan. Yau meeting suke dashi a Transcop hilton saboda haka direct can suka wuce. Tun ƙarfe 9 da suka shiga meeting ɗin basu suka fito ba sai 11 daganan yawuce office.
Ziyada kuwa dake zaune agaban tv, duk wani abu da ake koyarwa na girki taɗaukeshi tsab akanta, hatta abun da tagani jiya a kitchine wani mai kamar kofi,(Blender) yau taga yanda ake amfani dashi, ashe abun markaɗe ne ita bata sani ba, suna gama koyar da girkin, suka sako wani film shine abun daya ƙara ɗauke mata hankali. Ba itane ta tashi agaban tv’n ba harsai bayan sallan Azahar. Kitchine ta shiga cike da karambaninta yau taci alwashin sai tayi girki. Ruwa ta zuba atukunya cike da karambani ta kunna gas, duk abun da taga sunyi acikin tv’n ta riƙeshi yana kanta, ruwan na tafasa ta wanke shinkafa ta zuba, fridge ɗin dake cikin kitchine ɗin ta buɗe ta ɗibi kayan miya, saida ta wankesu sannan ta ɗauko irin abun da taga sunyi markaɗe aciki gaba ɗaya kayan miyan ta juye acikin blender tare da ɗaukanshi can ca ɗak takaishi gaban socket, kamar yanda taga sunyi haka itama tayi ta jona sa ajikin socket, ƙaran da taji yayi kaɗai saida ya kusa fasa mata ƙirji, don baka ɗan ba ta tsorata, can gefe ta koma tana ganin ya markaɗu ta siɗaɗo da ƙyar ta iya kashe socket ɗin, duba shinkafarta tayi taga ta nuna, haka ta sauƙe shinkafar batare da ta kashe gas ɗin ba, da sauri sauri ta juye markaɗen acikin wata tukunya sannan tasanya mangyaɗa akan markaɗen don ita agarinsu haka suke miyansu. Baƙaramin jimawa tayi ba kafun ta samu miyan ya soyu mata, hmmm nan akeyinta sam batasan me zata sanyawa miyan don kashe mata tsami ba, haka ta zuba kayan haɗi ta rufe miyar, mintuna kaɗan ta kashe gas ɗin lokacin miyar tayi, komawa ɗakinta tayi tayi wanka, wata doguwar riga blue colour ta sanya mai kyau, rigan irin arebian gown ɗinnan ce, sosai ta amshi jikinta, zuciyarta fara tas ta nufi kitchine ɗin, daɗi takeji yau zataci abincinta, bata taɓa mantawa awasu lokuta da dama a ƙauye idan tayi girki babanta yaci yakan yaba girkin sosai, sannan ita kanta Inna Ma’u idan tanacin girkin har santi take, hakanne ma yasa aka sallama mata gaba ɗaya girkin gidan. Food flask ta ɗauka ta juye shinkafan aciki, sannan ta ɗauki plate ta zuba nata, miyan ma juyeshi tayi acikin wata kula gaba ɗaya kulolin takaisu kan dinning table ta ajiye..
Akan sofa ta zauna tare da ɗan ƙwashe ƙafafunta, cikin ɗari ɗari takai loman farko na abincin bakinta, saboda atunaninta miyan tayi tsami sosai, sai dai kuma koda taci abincin, ga mamakinta sai taji miyar batayi wani tsami sosai ba, hasalima mutum zai iyaci hankalinsa kwance. Sosai taci abincin tana kammalawa ta je kitchine ta wanke plate ɗin. Dawowa falon tayi ta zauna, tana zama tajiyo ƙarar horn ɗin motarshi, tashi tayi da sauri ta tafi jikin window ta ɗan leƙashi, yatsun hanunta tashiga murzawa aranta tana cewa.
“Allah yasa ya yarda yaci abincinnata”Tsaye take ajikin window tana mai jiran shigowanshi, amma kuma sai dai ga mamakinta har anshare sama da mintuna 10 baishigo cikin falon ba, sake gyara tsayuwanta tayi, tare da soma murza ƴan yatsun hanunta. Buɗe ƙofar falon yayi ya shigo, yana mai ƙoƙarin cire suit ɗin dake jikinshi, idanunsa ne suka sauƙa akanta, amma saiyayi saurin kawar da kanshi gefe, tare da ƙarasawa cikin falon, aje suit ɗinnasa yayi akan kujera tare da cire agogon dake ɗaure atsintsiyar hanunshi, gaban fridge yaje tare da buɗewa ya ɗauko goran ruwa, ɓalle murfin yayi tare da kaiwa bakinsa, saida ya tabbatar da cewa babu komai acikin goran, sannan yayi wurgi da goran cikin dustbin, dawowa cikin falon yayi ya ɗauki suit ɗinshi kana ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, gaba ɗaya ma yi yayi kamar baisan da zamanta acikin falon ba, tana ganin shigewarsa cikin ɗaki. Ta saki wani gauron numfashi, sam bazata iya yi masa magana ba, kwarjininsa ya wuce gaba ɗaya tunaninta, sumu sumu haka ta wuce tayi ɗakinta.
Kwance yake acikin jakuzzie ɗinsa, wanda yasha haɗaɗɗen ruwan wanka, daga kan ƙafafunsa zuwa ƙirjinsa, gaba ɗaya lume suke acikin ruwa, kansa da hannayensa ne kawai suke waje, yayinda kyawawan idanunsa suke alumshe, kana ya ɗan jingina bayan kanshi da jikin jakuzzie’n, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya tare dashi, sam kwana biyunnan baya cikin wata gamsashshiyar nutsuwa, tunani da damuwa sune abun da suka sakoshi gaba, akullum kuma ako wacce rana jin kansa yake tamkar wani baƙon halitta, ya sani acikin rayuwarshi akwai tawaya sosai, amma kuma baison ya zamanto mai rauni saboda hakan, baiso yazama ɗaya daga cikin irin mutanennan da basa iya riƙe damuwarsu, shikansa ya sani da ace lafiyarshi ƙalau, to da bazai taɓa iya kai wannan lokaci mai tsawo haka, batare da mace akusa dashi ba, “Menene matsalarsa? mecece damuwarsa? meyasa baya iya zama da mace?” yasan duk waƴannan abubuwan iyayensa suna da buƙatar sani, “Amma mai yasa basa tambayarsa?” wannan tambayar shi ne abun da yake tambayar kanshi akullum, baikamata don ya kasance Namiji su sakar masa ragamar rayuwarsa ba, duk da cewa ya girma amma tabbas yana da buƙatar kulawan Iyaye atare dashi.
Wani numfashi yaja tare da fesarwa alokaci guda, wani irin tausayin kanshi yakeji, sosai yake tausayawa al’amuranshi, baisan taya zai dubi wata mace yace yana sonta ba, haka kuma baisan wace macece zata iya zama ta jure lalurar shi ba, bazai taɓa yaudaran kanshi ba, saboda yasan babu wata mace da zata iya jure zama dashi ayanda yake, musamman ma idan tasan ƙatuwar matsalan dake tare dashi, yasani shi me raunine ako da yaushe, safe, dare, rana, babu wani lokaci da zaizo masa yana cikin farinciki da walwala, sau da dama yakanji kamar yayita kuka, ko da zai samu salaman rage ƙuncin dake cikin zuciyarshi, saidai hakan baya samuwa ayanzu, sakamakon zuciyarsa da tayi tauri, haƙoransa yasa ya ɗan ciji laɓɓansa da ƙarfi, shi kaɗai yasan me yake ji, haka kuma shi kaɗai yasan kalan ƙunci da yake ciki, sama da shekara 10 kenan da haske ya gujewa rayuwarsa, azahiri acikin haske yake rayuwa, amma kuma idan aka duba bayansa duhune dulum mai wuyar kalluwa. Cikin rashin kuzari haka yayi wanka, tare da ɗauro towel akan waist ɗinsa ya fito daga cikin toilet ɗin.
Zama yayi akan gado tare da ɗauko mayinsa ya soma shafawa, yana kammalawa ya feshe jikinsa da body spray mai daɗin ƙamshi. 3 guater jeans and white t-shirt ya sanya, laptop ɗinsa mai ɗauke da tambarin apple asaman murfin ya ɗauka, tare da ficewa daga cikin ɗakin. Aje laptop ɗin yayi akan rug tare da buɗe fridge ya ɗauko goran pepsi mai matuƙar sanyi. Zama yayi akan rug ɗin, tare da tanƙwashe ƙafafunsa, buɗe laptop ɗinshi yayi ya soma gudanar da aikinsa kamar yanda ya sabayi akowacce rana.
**
Ziyada kuwa komawa ɗaki tayi, tayi kwanciarta, harta fara bacci ta tuno cewa wulaƙanta abinci ba kyau, hakan yasa ta fito saɗaf saɗaf kan dinning ɗin ta nufa, abincin yana nan kamar yanda ta ajiye sa, ɗaukan kulan tayi ta fice daga cikin falon, direct wajen maigadi ta nufa nan ta sameshi zaune shida Kamalu driver suna hira, kulan abincin ta basu, duk da basusan menene aciki ba saida sukayi mata godiya, ita kuwa ta juya ta koma ciki. Zama Kamalu driver da maigadi sukayi, suka ci shinkafa da miyan, sam basuji wani abu na’alamar rashin daɗi acikin abincin ba, haka suka ci abincin sukayi nak.
STORY CONTINUES BELOW
*** ***
Washe Gari.
Tun kafun 7 yau ta kammala shirinta bayan tayi wankan tsarki, saboda tun jia da yamma bata ga komaiba, hakan yasa taji ajikinta cewa ta samu tsarki. 7 nayi suka bar gidan.
Zuwanta yayi daidai da zuwan Nasmah, nan suka zauna suka soma taɓa hira kafun Shukra tazo….
*** ***
Bayan sati biyu.
Alhamdulillah. Ayanzu sosai Ziyada take gane karatun da ake koyar musu, duk da cewa turanci har yanzu yana bata wahala, sannan kuma bata iya wani abu sosai daga cikinsa ba, amma duk da haka sosai take gane karatun, saboda kullum idan malami yazo yayi musu lecture yana fita Nasmah zata ƙara fahimtar da ita, yau suke shirye shiryen farayin test don haka daren jia, kusan kwana tayi tana biye karatun Maths ɗin da akayi musu, tun daga zuwanta har kama daga wanda akayi batanan, duk Nasmah tayi ƙoƙari wajen ganin ta koya mata.
Sunyi test ɗinsu lafiya, inda ko wanne ɗalibi dake cikin ajin yake sa ran cinyewa, ita ma Ziyada tayi ƙoƙari ƙwarai, domin kuwa acikin guestions huɗu da akace su amsa, ta samu ta amsa uku, kuma aranta tana sa ran cewa zataci duka ukun. Koda aka raba musu paper’n test ɗinnasu, ta samu six ɗayan da batayi ba kuwa tasamu zero, domin dama shine keda yawan maki har 4 mark yake dashi, duk da haka ma taji daɗi sosai.
Kwana biyunnan gaba ɗaya basu da wani hutu ko acikin school, kullum cikin karatun test suke ga exams ɗinsu dake ta gaba towa, kasancewar exam ɗin third term ne, shi zai kaisu s.s 2, hakanne yasa gaba ɗaya hankalin ɗaliban dake cikin school ɗin atashe yake, domin kuwa matuƙar bakaci exam ɗin ba, to fa repeat ɗinka za ayi babu ruwansu dakai ɗan waye. Ɓangaren Ziyada kuwa abun ya haɗe mata sosai, domin kuwa ta dage tana koyan karatun da akayi baya kafun ta shigo, ga kuma wanda akeyi musu yanzu hakanne yasa gaba ɗaya brain ɗinta ta ɗauki charge, saidai kuma cikin ikon Allah da kuma tsananin nacin da tasanya aranta karatun yana zama akanta. Ayanzu kwata kwata ta daina haɗuwa da Sooraj, bata sanin fitarsa bata kuma sanin dawowarsa, duk da kuwa tsananin son ganinsa da take, amma hakan baya samuwa agareta. Agajiye ta ɗaura kanta akan kafaɗan Shukra wacce take ta faman latsa babbar wayarta. Ɗan kallonta Nasmah tayi tare da cewa.
“Badai kin gaji da karatun ba?”
“Nagaji mana Nasmah, zan bari sainaje gida kawai naci gaba!”
“Amma kinsan fa Monday zamu fara exam ko?” Shukrah tafaɗa tana me maida wayarta cikin jaka.
Murmushi Ziyada tayi tare da cewa “Har kingama shan soyayyan?”
Hararanta Shukrah tayi tare da cewa “Nifa wallahi kunsamin ido, hmm kawai don bakusan daɗin soyayya bane ba shiyasa”
“Daɗi? hmmm ina daɗi acikin wannan abar da kullum sai anbata miki rai? wallahi Shukra inaganin kawai wahalar dakanki kikeyi, s.s one kaɗai fa muke, amma wai ace ke har soyayya kike hmmm Allah ya kyauta!” Nasmah tafaɗi haka tana ɗan taɓe bakinta, ita sam wannan tsarin na soyayya baiyi mata ba, saboda ita atsarinta idan zatayi soyayya tafiso sai taje irin 2 hundred level ɗinnan.
“Hmm kwata kwata bazaki gane ba Nasmah, amma kema watarana nasan zakiji abun da nakeji!” Shukrah tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin tashi tsaye daga zaunen da take.
“Ba abun da zan gane!” Nasmah tafaɗi haka cike da jin haushi.
Murmushi Ziyada tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, haka nan tunaninsa ya faɗo mata arai, jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, kallonta Shukrah tayi tare da cewa. “Muje ki rakani kinji share wannan abar” Still murmushi kawai tayi sannan tabi Shukrah suka tafi, Nasmah ma binsu tayi tace bazata zauna ita kaɗai ba, direct ɓangaren da ake koyar da girke girke dake cikin makarantar suka nufa, ƴan department ne dayawa awajen kowa yana baje basirarsa, gani tayi Nasmah tashiga itama ansoma bugawa da ita, tsayawa tayi daga gefe tana kallonsu, dukkan abun da sukeyi tana haddace shi akanta, sunjima awajen kafun suka koma class.
Koda ta koma gida gaba ɗaya bata wani samu sukuniba karatu ta dinga yi, har wayewar gari ta shirya tatafi makaranta, acikin ƴan kwanakinnan wani abu da ta fara fuskanta shine sauyawar da jikinta yasomayi, hips ɗinta ne taga sun ƙara faɗi, yayinda ƴan saffa saffan breast ɗinta suka ɗan ƙara girma, skin ɗinta ta sauya tayi wani fresh, ga kyawun da fuskarta take ƙarawa ako da yaushe, ita kanta sau da dama idan ta kalli kanta takanyi mamakin yanda kamanninta ke ƙara sauyawa. Tun ɗazu su Nasmah suka fita break suka barta, kasancewar bata ƙarasa note ɗinta da wuri ba, miƙewa tsaye tayi bayan ta kammala note ɗin, maida littafinta tayi cikin jaka tare da ficewa daga cikin ajin.
Wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar benz ce ta kunno kai cikin makarantar. Adai dai kusa da parking space ɗin makarantar yayi parking motar, buɗe murfin motar yayi tare da zuro ƙafafunsa waje, cikin yanayinsa na nutsuwa yafito daga cikin motar, haɗaɗɗen saurayine mai kyau da gayu, ba fari irin tas ɗinnan bane, amma yana da nasa irin salon hasken, direct idan ka ganshi zaka ƙirasa da mai kyau, kasancewar babu laifi shima yana da nashi kyau’n, irin Handsome guy ɗinnan ne mai son ado da gayu, dogone amma basosai ba sannan yana da ɗan faffaɗan jiki, yana da wani kwantaccen sajen da yaƙarawa fuskarsa kyau, sanye yake da riga da wando na jeans masu kyau, yayinda ya rufe gashin kansa da facing cap blue colour. Cikin isa yake takunsa yana mai ɗan kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa, direct office ɗin principal ya nufa. Ta baya baya take tafiya tana dariya yayinda Nasmah ke biyota da ɗan sauri sauri, ɗan juyawa tayi sam bata ankara ba, saiji tayi ta bugu da mutum yayinda kanta ya daki ƙirjin mutumin da ta buge, da sauri ta juyo tare da sanya hanu ta dafe goshinta cikin yanayi naɗan jin zafi tace. “Auchhh!!” Shima hanu yasanya ya dafe ƙirjinsa, daidai saitin inda kanta ya buga.
Ɗan zame hanunta tayi daga kan fuskarta, idanunsune ya sarƙe cikin na juna, ɗan matsawa baya tayi tare da sake kallonsa.
“Kayi haƙuri dan Allah bankula bane!” tace dashi cikin murya mai sanyi. 1
Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi mata tare da cewa. “Babu damuwa!” shima cikin sanyi yayi maganar, yana mai ɗan ƙara faɗaɗa murmushin dake kan fuskarsa. Raɓawa tayi taɗan gefensa ta wuce, Shukrah da Nasmah suka bita abaya. Kafeta da sexy eyes ɗinsa yayi har saida yaga shigarta class sannan ya ɗauke idanunsa, sannan ya juya ya nufi inda zashi. 2
Har ta zauna akan sit ɗinta tana dafe da goshinta, don taji zafin buguwar da tayi baɗan kaɗan ba.
Dariya Shukrah tayi tare da cewa “Wai miye hakan kike dafe da goshi sai kace wanda kika bugi dutse?”
“Ai inajin da dutse da shiɗin basu da maraba!” Ziyada tafaɗi haka tana mai ɗan mulmula goshinta.
Dariya su Nasmah suka sanya. “Dole zakiji zafi mana, daganinsa ai zaki san ma’abocin yin gym” Shukrah ta faɗi haka tana mai ƙoƙarin murzawa Ziyada goshinta. Malami ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka nutsu, tare da maida hankalinsu kansa. Kwana biyunnan duk ba atashinsu da wuri yau har 5:30 sannan aka tashesu.
**
Tana shiga cikin ɗakinta ta soma rage kayan jikinta, banɗaki ta shiga tayo wanka. Riga da sket ƴan kanti ta sanya sannan taɗan yafa wani ɗan ƙaramin ɗan kwali akanta. Direct kitchine ta wuce, duk wasu ƴan ƙananan girki yanzu babu abun da bata iyaba. Indomie ta dafa bawai don tanaso ba saidon yunwan dake damun cikinta. Gaba ɗaya kwanukan da suka ɗan yi ƙura a kitchine ɗin ta kwashe ta kai gaban sink wankesu tayi tas, sannan tayi mopping kitchine ɗin. Acikin kitchine ɗin ta zauna taci abincinta, tana gamawa ta wanke plate ɗin data ɓata. Zame ɗan kwalinta tayi ta ƙarasa gaban sink, hanu tasa ta tari ruwa ta wanke fuskarta, tana maiƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin tanufi hanyar fita daga kitchine ɗin, harta jefe ƙafarta na hagu acikin falon, da wani irin ƙarfi taji an jawota cikin kitchine ɗin tare da sanya hanu aka rufe mata baki gam.Numfashinta ne yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, saboda tsabar tsananin tsoron da ta samu kanta aciki, ƙasa tayi da idanunta, tana me kallon hanun da aka rufe mata bakinta dashi, hanun namiji ta gani, wanda ke ɗauke da kwantattun gargasa da sukayi luf akan farar fatarsa, jikinta ne ya ɗauki tsuma, wani irin tsoro mai ƙarfi ya ziyarceta, wani ɗan corridor dake cikin kitchine ɗin ya shiga da ita, ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi, ba tare da ya sake mata bakinta ba, ya juyo da ita suka zama suna fuskantar juna, idanunta ta zaro waje tana me sake kallonsa. Sake mata bakinta yayi, tare da ɗaura hanunsa akan laɓɓansa cikin ƙasa ƙasa da murya yace.
“Shiii!! kada kimin ihu, ina da baƙi a falo ki zauna anan kada ki fito” yana gama faɗan haka ya saketa, tare da juyawa ya nufi hanyar fita daga cikin kitchine ɗin, bakinta a wangale haka ta bisa da kallo har ya fice, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da jingina bayanta da jikin bango, har acikin zuciyarta tayi bala’in tsorata, duk atunaninta wanine daban yazo saceta, hanunta ta ɗaura adaidai kan chest ɗinta dake ta bugawa da ƙarfi, aƙalla takusan mintuna 9 ahaka, kafun tasamu ta iya daidaita nutsuwarta, kan wani plastic chair dake cikin kitchine ɗin ta zauna, tare da kifa kanta akan cinyoyinta. 3
Shikuwa Sooraj yana barin kitchine ɗin, komawa cikin falo yayi, wajen abokan business ɗinsa, da suka kawo masa Ziyara, yana zaunene amma gaba ɗaya hankalinsa naga ƙofar kitchine, sam bayaso tayi gangancin fitowa, ba tsoronsa ganinta da zasuyiba, tsoronsa shine wani irin bahagon kallo za suyi masa? tabbas ba lallai suyi mishi kyakkyawan zato ba, shikuwa ko kaɗan bayason ayi masa irin wannan kallon. Sunjima suna tattaunawa akan business ɗinsu, kafun daga bisani sukayi masa sallama, har bakin motarsu ya rakasu, shima daga rakiyarsu bai dawo cikin gidanba, motarsa ya shiga ya fice daga gidan gaba ɗaya. 1
Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan ne yasata takowa saɗaf saɗaf taɗan leƙa cikin falon, ganin ba kowa acikin falon yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Fitowa daga cikin kitchine ɗin tayi ta wuce ɗakinta.
*MONDAY*
Yau yakasance ranar da zasu fara exam, 8:00 am daidai zasu shiga exam ɗin inda zasu fara da Biology. Zaune suke akan wani bench su dukansu ukun, kallon Shukra da Nasmah Ziyada tayi murya asanyaye tace.
“Tun safe ƙirjina yaketa bugawa, wani irin tsoro nakeji, anya zan iya zana exam ɗinnan kuwa?”
Kallonta Shukra tayi tare da ɗanyin murmushi.
“Zaki iya mana, ki daure ki ƙarawa kanki confidence, amma ai babu wani wahala” Shukra tace haka cikin son ƙarawa Ziyada ƙarfin guiwa, shiru sukayi daganan basu sake cewa komai ba. Takwas na cika dai dai suka shiga jarabawa, 1 hour suka ɗauka suna rubuta exam ɗin, cike da jin daɗi Ziyada ta miƙa booklet ɗinta, sannan tafito daga cikin exams hall ɗin, tsayawa tayi ajikin wata bishiya tare da lumshe kyawawan idanunta, wani nishaɗi takeji acikin ranta saboda tana da yaƙinin cewa zata ci duka tambayoyin da ta amsa. Su Nasmah ne suka fito nan suka haɗe suka ci gada da hiransu, kasancewar yau paper biu zasuyi ƙarfe 10 daidai suka sake shiga wata jarabawan na Islamic. Suna kammala jarabawan kowa ya fara haramar komawa gida, tsayawa tayi tare da dafe goshinta, gaba ɗaya ta manta batace da Kamalu driver yazo ɗaukarta da wuri ba, gashi yanzu sun gama exam kowa na ƙoƙarin ko mawa gida. Kai tsaye ta nufi babban ƙofar gate ɗin makarantar. Tana fita daga cikin gate ɗin ta soma kalle kalle, batasan ya zatayi ba don bata da wata mafita, gashi su Shukra sun tafi. Wata baƙar motace tazo ta tsaya agabanta, hakan yasa ta ɗan ja baya. Ahankali ya sauƙe glass ɗin windo’wn motar, kyakkyawar fuskarsa ta bayyana wacce ke ɗauke da murmushi.
STORY CONTINUES BELOW
Kallonshi tayi tare da sauƙe idanunta ƙasa, tabbas bazata manta shiba shine wanda ta buge kwanaki.
Murmushi yakumayi tare da buɗe murfin motar ya fito, takowa yayi har zuwa inda take, murmushine akan fuskarsa wanda suka bayyana dimples ɗinsa. “Tsayuwa acikin rana bai kamaceki bafa ƴan mata” yafaɗi haka yana me ɗan ɗaga kansa ya kalli sararin samaniya.
Ɗago manya manyan eyes ɗinta tayi, tare da sauƙesu akan fuskarsa. Idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna, murmushi yaƙara yi mata tare da cewa.
“Mai kikeyi anan? ba’azo ɗaukarki bane?”
Samun kanta tayi ta kaɗa masa kai alamar “Eh”
“Okay muje na sauƙeƙi agida” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin buɗe mata murfin motar, ɓangaren mai zaman banza.
Saurin kallonsa tayi tare da ɗan matsawa can gefe, sam batajin zata iya shiga motar, ita da batasan kowa ba banda MR. HANDSOME (Sooraj) yaza ayi ta yarda ta shiga motar wani, kalan ma yaje ya sayar da ita. Abunda tafaɗa acikin ranta kenan.
Ganin alaman cewa bata yarda dashi bane yasanyashi sake ɗanyin murmushi cike da son ya gamsar da ita yace. “Calm down dear, i will not hurt you, trust me!”
Yanzu kam salon kallon da tayi masa, yana ɗauke ne da ma’anoni masu yawa. Horn ɗin motar da taji abayanta ne yasata waigawa, ai kuwa Kamalu driver ta hango acikin mota, da sauri ta juya ta nufeshi, buɗe murfin motar tayi ta shiga, ƙarasowa yayi har jikin motar, sannan yayi knocking glass ɗin window, Kamalu driver ne yayi ƙasa da glass ɗin tare da ɗan dubansa, shikuwa idanunsa akan kyakkyawar fuskarta yake, cikin ƙasa da murya yace. “Yace kin ƙi yarda dani ko? ba damuwa ki kulamin da kanki!” yana gama faɗan haka ya juya ya nufi wajen motarsa.
Tafiya suke amma gaba ɗaya tunaninta yana ga maganan da ya gaya mata “Kikulamin da kanki!” mai hakan yake nufi kenan? tambayar da take ta yiwa kanta kenan gaba ɗaya kanta ya kulle, ahaka har suka isa gida.
Tsaye yake agaban drawer, dagashi sai dogon wando fari dake sanye ajikinsa, yayinda murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta bayyana, gaba ɗaya shape ɗin bayansa abun burgewa ne. Kayansa yake cirowa daga cikin drawer’n yana shiryawa acikin trolly bag ɗin dake aje kan gadonsa. yana gama shirya kayannasa ya ɗauki wata rubber t-shirt yasanya ajikinsa. Wata jaka ya ɗauko irin wacce ake goyawa a baya, buɗe jakan yayi ya zuba wasu takardu aciki, saida ya tabbatar daya haɗa komai nasa wanda yasan zai buƙata, sannan ya ɗauki wayarsa ya sanya acikin aljihunsa, direct falo ya nufa. Direct dinning area ya nufa, haɗa tea ɗinsa yayi, tare da dawowa cikin falon ya zauna. Sipping tea ɗin yake ahankali, yayinda lokuta zuwa lokuta ya ke kai dubansa ga agogon bangon dake cikin falon. 6 pm daidai jirginsu zai tashi. 5:40 ya kammala gaba ɗaya abubuwan da zaiyi, ɗaukan troly ɗinsa yayi tare da rataya jakarsa akafaɗansa, yana fitowa daga cikin ɗaki, dai dai lokacin ita kuma tana fitowa daga kitchine, sanye take da riga da wando na pakistan sai kuma hijab dake jikinta. Idanunsu ne ya sarƙe acikin na juna. Da sauri ya ɗauke kansa, ya nufi hanyar fita daga cikin falon, bin bayansa tayi da kallo harya fice daga cikin falon. Samun kanta tayi da kasa ɗauke idanunta daga bakin ƙofar fita daga falon, komai nasa abun burgewane, wasu irin hawayene suka cika idanunta, sannan suka samu daman fitowa alokaci guda. Jingina bayanta tayi da jikin bango, tare da ɗan cije laɓɓanta, akullum rayuwarta ta baya, ta zame mata abun tunawa, tunanin babanta ne akullum yake damun zuciyarta, tayi rayuwa cike da rashin gata da kuma ƴanci, ta taso cikin maraici, sam bata wani san menene daɗin mahaifiya ba, tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu, har i’yanzu tana buƙatar sanin wacece ita, gaba ɗaya rayuwar da tayi abaya cike take da duhu, Maraici, Kaɗaici, da kuma Ƙunci su suka cika rayuwarta ta baya, babu wani wanda ya damu da ita, itake shanye damuwarta komai girmansa, ɗan zamewa tayi ta zauna daɓas akan tiles ɗin dake malale a wajen, lumshe kyawawan idanunta tayi, tare da soma murza ƴan yatsun hanunta. Ƙamshin turarensa da taji yana shiga hancinta ne, yasanya ta buɗe idanunta da suke cike tab da ƙwalla, ganinshi tayi tsaye akanta ya zuba mata idanunsa masu matuƙar rikitata.
Saurin ɗauke idanunsa yayi daga kanta, domin bazai taɓa iya juran kallon yanda ƙwayan idanunta ke cike da ƙwalla ba, envelop ɗin dake hanunsa ya miƙo mata, hanunta na rawa haka ta amshi envelop ɗin, shikuma ya juya ya fita, samun kanta tayi da kasa buɗe envelop ɗin jiki asanyaye ta koma ɗaki.
6:00 pm daidai jirginsu ya ɗaga zuwa sararin samaniya. Jingina bayanshi yayi da jikin kujeran da yake zaune, tare da lumshe idanunsa, wani tunani da yazo ranshi ne yasanyashi sakin murmushi, lokaci guda kuma ya haɗe fuskarsa tare da buɗe idanunsa da sukayi jajur dasu.
*** ***
Wasa wasa har sunyi sati ɗaya da fara exam, a ɓangaren Ziyada kuwa sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa tana amsa tambayoyin jarabawan da iyakayi mata, da duka iya ƙoƙarinta.
Zaune take a inda aka tanadar musu don cin abinci, kasancewar yau ta riga su Nasmah fitowa daga ɗakin jarabawan, yasa take zaune ita kaɗai, kanta ta kifa akan ɗan madaidaicin table ɗin dake gabanta wanda yake zagaye da kujeru.
Wani irin ƙamshin turarene yashiga kawowa hancinta Ziyara, lumshe idanunta tayi tana mai shaƙan ƙamshin turaren batare da ta ɗago kannata ba.
Ahankali ya jawo kujeran dake fuskantar nata ya zauna. Sexy eyes ɗinsa ya zuba wa ƴan yatsunta dake aje kan table ɗin. Hakanan taji kamar akwai mutum akusa da ita, saboda hakane yasa ta ɗan ɗago kanta, waro idanunta tayi cike da mamaki, duk da cewa aƴan kwanakinnan yaɗan matsa mata, amma kuma sam bata tsammaci ganinsa a wannan lokacinba. Murmushi yayi mata tare da ɗage giransa sama. “Surprise!” yafaɗa yana me sake ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo. Kawar da kanta gefe tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.
“Idan kina cikin yanayi na damuwa kinfi kyau, but even at that, i don’t want to seeing you in this situation, ki ɗan saki fuskarki kinji ƴan mata na!” Ya faɗi maganar yana mai langwaɓar da kansa gefe tamkar wani ƙaramin yaro. Yanayin yanda yayi maganar shine abun daya sanya ta ɗan juyo ta kalleshi, irin kallon daya keyi mata ne ya sanya taji jikinta yayi sanyi. Yana shirin sake yi mata magana ne wayarsa ta soma ringing alaman shigowan ƙira. Ɗaga wayan yayi tare da karawa akan kunnensa, baiwani jima yana wayanba ya kashe, tare da maida wayar cikin aljihunsa. Miƙewa tsaye yayi, tare da ɗan ranƙwafowa dai dai fuskarta. in a silent voice yace. “Kina da kyau sosai, komai naki me kyau ne, zanyi baƙin ciki idan kika kasance saɓanin tunani na!!” yana gama faɗin haka ya juya ya soma tafiya, binsa tayi da kallo har ya ɓacewa ganinta. Dai dai lokacin su Nasmah suka ƙaraso. Shukrah na zama ta kwashe da dariya. “Har angama shan love ɗin?” Nasmah tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin gumtse dariyarta.
“Love kuma?” Ziyada ta tambaya.
Dariya Shukrah da Nasmah suka sanya tare da tafawa, ganin haka yasa Ziyada ci gaba da sabgoginta, domin ta sansu abu mai sauƙi ne su fassarata da wata manufar. 1
*** ***
LAGOS NIGERIA.
SOORAJ!!!
1:00 am, ƙarfe ɗaya na dare, kwance yake akan makeken gadonsa, wanda yaji zanin gado na alfarma. Sanye yake da white pencil jeans ajikinsa, bai sanya riga ba hakan yasa gaba ɗaya surar jikinsa take abayyane, musamman ma sick packs ɗinsa, wanda suka samu daman kwantawa raɗau akan fatar cikinsa, sama sama yake jiyo motsin mutane acikin kunnuwansa, ahankali ya buɗe idanunsa, aikuwa nan ya tabbatar da cewa ba karya kunnuwannasa keyi masa ba, tabbas motsin mutanene acikin gidansa, saƙƙowa yayi daga kan gadon tare da nufar ƙofan fita daga cikin ɗakin, ahankali ya murza handle ɗin ƙofar ya fita, taku uku kacal yayi ya samu kanshi a babban falon dake gidan, hanu yasanya akan makunnin ƙwan wutan dake falon ya kunna, kunnawansa yayi daidai da sakar masa bullet da akayi akan ƙirjinsa, wani ƙara yasanya sakamakon wani irin zafi da raɗaɗi da suka ratsa shi, tun daga ƙasan ƙafarsa harzuwa tsakiyar kansa, kafun yayi wani yunƙuri ansake sakar masa wani bullet ɗin akan hannunsa, wani irin azabane yaji yana huda jijiyoyin jikinsa, yana ratsawa ta ƙwaƙwalwarsa, take idanunsa suka soma rufewa, wani irin abu yaji acikin jikinsa wanda bai taɓa jin irinsa ba, take yafaɗi awajen baya ko motsi.Jini ne ke fitowa daga jikinsa yana malala akan white tiles ɗin da ya mamaye gaba ɗaya falon. Wasu ƙattin maza guda biyune suka fito daga maboyarsu, wato bayan labule kenan inda suka ɓoye, ko wannensu fuskarsa sanye take da mask, dukansu suna sanye da baƙaƙen kaya, sannan kuma kowannensu ahanunsa ɗauke take da bindiga, ɗan ranƙwafowa ɗayan yayi tare da ɗaura hannunsa adai dai saitin hancin Sooraj, jin baya numfashine yasa ya kalli ɗayan ɗan uwannasa. Alama yayi masa da ido akan su tafi aiki ya kammala, babu wani ɓata lokaci, aƙagauce suka fice daga gidan.. 10 minute da tafiyarsu saiga ƴan sanda har mota biyu. Alhaji Ilyass (maƙocin Sooraj) dake laɓe jikin gate ɗin gidansa, yana ganin ƴan sanda ya ƙaraso garesu haryana jin tuntuɓe, aruɗe yace. “Yauwa ranka ya daɗe kun ƙaraso? Ni ne nan naƙiraku, tabbas naji ƙaran harbin bindiga awannan gidan har sau biyu, saboda haka duk yanda akayi babu lafiya!” yafaɗi haka yana me sharce gumin dake yankowa ta gaban goshinsa, gaba ɗaya atsorace yake, ƙiran ƴan sandan ma da yayi baƙaramin Jahadi yake ganin yayi ba, saboda tsorone cike fal aransa. +
Cike da rashin tsoro haka ƴan sandannan suka rarrabu, kowanne daga cikinsu ya saita kunamar bindigarsa, ƙiris sukejira su saki harsasai, haka sukayi cikin gidan Sooraj, ahankali suka tura ƙofar falon suka shiga, ganin bakowa acikin falon yasa suka shiga ƴan dube dube, yayinda wasu daga cikinsu suka nufi bedrooms ɗin dake cikin falon, ɗaya bayan ɗaya haka suka shiga suna dubawa, ɗaya daga cikin ƴan sandan ne idanunsa suka sauƙa akan jinin dake kwance ya daskare akan tiles, jawo ogansu yayi ya nuna masa jinin, aikuwa suna leƙa bayan kujera sukaga mutum yashe aƙasa, gaba ɗaya jini ya ɓata jikinsa, aɗan razane sukayi kanshi, daidai lokacin sauran ƴan sandan suka dawo cikin falon. “Sir gaba ɗaya fa mungama duba gidannan bakowa acikinsa” suka faɗa suna mai kallon Sooraj dake yashe aƙasa. Shiru ogannasu yayi tare da ciro wayarshi acikin aljihunsa ya danna ƙiran asibiti. Kallon sauran ƴan sandan yayi yace subi hanya duk wanda suka gani sukamashi. hakan kuwa akayi duk suka watse yazama saura mutane ƴan ƙalilan. Ƙarar jiniyan ambulance ne yacika gidan. Ɗaukan Sooraj akayi aka sanyashi acikin ambulance ɗin, suka wuce asibiti.
Babban asibitin dake cikin garin Lagos suka wuce dashi, direct ɗakin bada taimakon gaggawa aka nufa dashi, duk da cewa basu da tabbacin cewa yana da rai ko bayidashi. Dr. Femus shine mutumin daya fara cire handglobes ɗin dake hanunshi, kallon sauran abokan aikinnasa yayi yace. “He is dead!” Jikinsune gaba ɗaya yayi sanyi, saboda haka suma suka soma ƙoƙarin cire handglobes ɗin dake hanunsu.
Dr. Fawwaz da bai yarda da abunda Dr.Femus yace ba, yaɗan matso gaf da Sooraj ɗin tare da kama hanunsa ya riƙe, sannan ya ɗaura kansa adai dai saitin ƙirjinsa inda zuciarsa ta ke. Da sauri ya ɗago da kansa tare da cewa “Bai mutu ba, zuciyarsa na bugawa, muyi sauri mucire masa bullet ɗin dake jikinsa!” nan suka duƙufa aikin cire bullet ɗin dake jikinsa. Sunyi masa gwaje gwaje sosai, inda suka tabbatar da cewa bai mutu ba, amma kuma su kansu basu san awani condition yake ba, abu ɗaya suka sani shine, zai iya wucewa tacan zai kuma iya tashi, duk wannan na Allah Ne. Duk abun daya kamata suyi mishi sun masa, sannan suka killaceshi awani ɗaki na musamman.
***
Gaba ɗaya ta hargitsa gadon, sai juye juye take, ta ya mutsa ko ina, gashin kanta gaba ɗaya ya watse akan gadon, yayinda ta sanya hanunta ta damƙi zanin gadon da iya ka ƙarfinta, duk da cewa sanyin ac na tashi acikin ɗakin, amma ita wani irin gumine ke fitowa daga jikinta. Arazane ta ware manya manyan idanunta da sukayi jajur dasu, tashi tayi ta zauna tare da dafe ƙirjinta dake bugawa da sauri. “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!!” tafaɗa cikin wata murya me rauni, kawai saita samu kanta da fashewa da kuka, kuka tayi sosai wanda itakanta batasan na menene ba, aƙalla taɗauki kusan 40 minute tana kuka harsaida muryarta ta dashe, idanunta ne suka sakeyin jajur dasu, jin ana ƙiran sallan asuba ne yasata miƙewa ta nufi toilet, doguwar rigan dake jikinta ta cire tare da tsayawa agaban shower ruwa yashiga dukan ta, bazata iya tuna mafarkin me tayi ba, amma tabbas tasan taga wani abu wanda yake shirin taɓa rayuwarta, wani irin bacci tayi wanda adunia bata taɓa bacci marar ɗaɗinsa ba, MR. HANDSOME shine wanda tunaninsa ya kutso cikin rai da zuciarta, aƙalla ta ɗauki kusan sama da 15 minute tana tsaye ruwa na dukanta, da ƙyar ta iya ɗauro alwala tafito, domin gaba ɗaya bata jin ƙarfin jikinta.
STORY CONTINUES BELOW
Tsayawa tayi agaban madubi tare da kallon kanta, hanu tasanya ta shafi jajayen idanunta wanda suke cike tab da ƙwalla, ai kuwa take hawayen suka gangaro kan ƙuncinta, ita kanta batasan kukan metakeyi ba, kawai dai tasan tanajin ƙunci acikin zuciyarta, tanajin wani irin babu daɗi acikin ranta, tanajin wani ƙaton rauni ya rataya awuyanta, gaba ɗaya tuna nin mai taimakone ga cika ranta, gefe guda kuwa sosai takejin faɗuwar gaba, tana fatan kada wata mummunar ƙaddara tasake
samunta. Sosai ta jima a raka’an ƙarshe tana kai kukanta ga mai duka, addu’a take kome zai sameta Allah Ya kawo mata shi da sauƙi. Haka ta zauna akan sallaya har gari yayi haske, ko samun daman sake duba takardan jarabawanta ma batayi ba, gaba ɗaya jin kanta take acikin ƙunci. Akullum cikin kuzari da ƙarfin jiki ta ke shirya kanta zuwa makaranta, amma yau hakanan take sanya uniform tunani fal ranta. Jakarta ta saɓa akafaɗa tare da fitowa cikin falon, akullum ta saba haɗawa kanta break fast amma yau batajin zata iyacin komai. Ba irin tambayan dasu Shukrah basuyi mata ba, akan tasanar dasu abun dake damunta, amma tace dasu sam batasan meke damunta ba. Suna fitowa a exam ta tsaya ajikin wata bishiya, tare da tsaida idanunta akan hanyar shigowa makarantar, hakanan tasamu kanta da son ganinsa, duk da cewa bawai ta wani damu dashi bane, amma yau da takejin kanta wani iri sai taji tanason ganinsa, tasan ko ma yaya zai iya cireta acikin ƙuncin da take ciki. Har Kamalu driver yazo tana tsaye ajikin wannan bishian, Saidai kuma har zuwa lokacin bata ganshiba kamar yanda taso, haka ta koma gida zuciarta ba daɗi. Indomie ta dafa amma haka ta kasa ci, dole ta zauna jigum tana kallon TV….
LAGOS NIGERIA….
Ƴan sanda da kansu suka koma gidan Sooraj sukayi bincike, inda suka gano cewa shiɗin cikakken ma’aikacin CBN ne, don haka direct branch ɗinsu dake Lagos suka nufa, BM ɗin wajen wanda yakasance tamkar aboki ga Sooraj, shi suka samu suka sanar dashi gaba ɗaya abundake faruwa, aikuwa baƙaramin tashi hankalinsa yayi ba, koda yaje yaga halin da Sooraj yake ciki tamkar gawa, saida ya zubda ƙwalla, nan yaƙira wayan Mas’oud yasanar masa komai da komai, ai Mas’oud tamkar wani zararre haka yazama, wani irin mugun tashin hankali yasamu kanshi aciki, batare daya sanar dasu Abban Sooraj ba ya hawo jirgi yataho Lagos.
Kallon Mas’oud Babban likitan asibitin yayi tare daɗan gyara zamansa yace. “Inaga basai anfita dashi waje ba ae, amma tunda ka matsa zaku iya fitar dashi, saidai kuma dole muna buƙatar ku ƙara mana sati ɗaya, idan baidawo cikin hayyacinsa ba shikenan sai ku fita dashi”
Shiru Mas’oud yayi tare da sanya hanu ya kama kanshi, adunia ayanzu babu wani mutum dayake tausayi sama da SOORAJ. Cikin cushashshiyar muryarsa yace. “Shikenan Dr. Babu damuwa Allah dai ya bashi lafiya!” da “Ameen” doctor ɗin ya amsa nan sukayi musabaha, Mas’oud ya nufi ɗakin da Sooraj yake kwance, duk da ba abarin kowa ya shiga, amma zaka iya hangoshi ta glass ɗin window’n ɗakin. Tsayawa yayi ajikin window tare da sauƙe idanunsa akan Sooraj wanda yake kwance flat, bazaka taɓa cewa akwai rai ajikinsaba, saidai na urar dake jikinsa kawai dake aiki, wani irin hawayene suka cika idanun Mas’oud, har baisan sanda suka silalo kan ƙuncinsa ba. “Wani irin ƙaddarori masu girma ne haka suke ɗawainiya da RAJ? yaushe RAJ zai huta? yaushe RAJ zaiyi dariya yayi farinciki kamar kowa? yaushe damuwar RAJ zata yaye?” abun da Mas’oud yake ta tambayar kansa kenan, tausayin SOORAJ yakeji mai tsanani, ayanzu baisan da wani baki zai iya furtawa iyayen Sooraj wannan mummunar labarinba, yace musu ɗansu yana cikin halin rayuwa ko mutuwa, ko kuwa yace musu ɗansu yazama marar amfani, ya zamanto tamkar gawa. Hanu yasanya ya share hawayen dake kan fuskarsa, aransa yaci alwashin nemo duk wani wanda yake da hanu akan harbin SOORAJ, wayarsa dake ƙara ya ciro ya duba, ganin commisioner’n ƴan sanda ne ke ƙiranshi, yasanyashi fita daga cikin asibitin baki ɗaya bayan ya ɗaga wayar ya kara akan kunnensa.
***
Zaune take akan wani ɗan dakali, yayinda shi kuma yake tsaye abayanta, ɗan ranƙwafo da kansa yayi daidai saitin kunnenta ahankali yace.
“Sau ba adadi na faɗa miki banaso ina ganin damuwa akan fuskarki” yaƙare maganar yana mai zagayowa ya zauna aɗan kusa da ita.
Raunannun idanunta ta ɗago ta kalleshi, ga mamakinsa sai kawai yaga hawaye sun gangaro daga cikin idanunta. Jiyayi wani abu ya soki zuciarsa, lumshe sexy eyes ɗinsa yayi tare da buɗesu alokaci guda.
“Menene?” yatambayeta cike da kulawa. Samun kanta tayi da cusa kanta acikin cinyoyinta ta fashe da kuka. Hankalinsa ne yaji ya tashi, cikin yanayi na rashin jin daɗin kukannata yace. “Meke damunkine Baby? wani abu ya samekine? ko wanine ya taɓaki? ko kuma anɓata ranki ne? please dear na faɗamin meke damunki!!” yayi maganar cike da tsantsar nuna kulawarsa gareta.
Ɗago kanta tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, ita kanta batasan awani yanayi take ciki ba, batasan meke damunta ba, hakan kawai tasamu kanta da cewa “Yayana ne, yau kusan kwana 10 banganshiba, kuma sannan inayawan jin faɗuwar gaba, inaso naganshi, bansan ina zanganshi ba!” wasu sabbin hawayene suka sake gangarowa daga cikin idanunta.
Ɗan kafeta da idanunsa yayi tare da ɗan yin murmushi, hakanan yanayin yanda tayi maganar ya burgeshi, yanason mace mai shagwaɓa sosai. “Kiyi haƙuri kinji Baby na, very soon yayanki zai dawo gareki”
Ɗago idanunta dake cike da ƙwalla tayi ta kalleshi, shima kallon nata yake, cikin wani irin yanayi dayake matuƙar kashe jikin mace, janye idanunta tayi daga kansa, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, wasa ta shigayi da yatsun hanunta, aranta tunanin mai taimako ne kawai ke yawo, duk bayan kowani bugun zuciarta ɗaya da tunaninsa take tafiya. “Ziyadah!!!” yaƙira sunanta cikin wata cool voice. Da sauri ta kalleshi cike da mamaki haɗi da yarinta tace.
“A ina kasan sunana?”
Murmushi yayi tare da cewa “Kamar yanda shaƙan numfashi da fitarsa keda matuƙar mahimmanci haka sanin sunanki yake da mahimmanci a wajena, saidai kuma ke ko sau ɗaya baki taɓa tambayar nawa sunan ba why?”
Wani murmushi tayi tare da cewa “To meye sunanka?”
Dariya yayi harsaida fararen haƙwaransa suka bayyana, sosai tambayar tata ta basa daria. “Sunana FAROUK YUNUS HAMMA ni haifaffen ɗan garin Kano ne, domin har yanzu iyayena acan suke, aiki ne ya kawoni Abuja, ina zaune a unguwar Wuse zone 2, ke kuma sunanki Ziyadah kina zaune a unguwar Asokoro, iya abunda nasani akanki kenan”
Dariya Ziyada tayi tare da kallonsa. Shima kallonnata yayi, miƙewa tayi ta soma tafiya batare da tace dashi komai ba, da kallo ya bita harta ɓacewa ganinsa, ajiyar zucia ya sauƙe tare da lumshe idanunsa, yanason komai nata, musamman ƴan saffa saffan cute lips ɗinta masu kyau, ya ɗan jima awajen kafun ya tashi ya shiga motarsa ya tafi……
***
Mas’oud ne keta kai kawo atangamemen falon Alhaji Mai Nasara, gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa, baisan ta ina zai fara ba, baisan taya Alhaji Mai Nasara zai ɗauki maganarsa ba.
“Mas’oud yana ganka a atsaye? Bismillah kazauna mana” Inji cewar Alh. Mainasara, da fitowarsa kenan daga cikin ɗaki. Jikin Mas’oud na rawa haka ya zauna akan kujeran tare da sanya hanu ya dafe kanshi.Jikin Mas’oud na rawa haka ya zauna akan kujeran, tare da sanya hanu ya dafe kanshi.
Kallonsa Alhaji Mansur Mai Nasara yayi tare da cewa. “Yanayin ka kaɗai ya tabbatarmin da cewa ba lafiya ba Mas’oud, meke faruwa? wani abu yasamu SOORAJ ne?” Alhaji Mansur Mai Nasara ya tambayi Mas’oud, fuskarsa cike da damuwa. +
Shiru Mas’oud yayi ya kasa cewa komai. “Tabbas akwai matsala kenan” Inji cewar Alhaji Mansur.
Kai Mas’oud ya kaɗa alamar “Eh”
“Sooraj ne?” ya kuma tambaya.
Kai Mas’oud yasake kaɗawa alamar “Eh”
Hanu Alh.Mansur Mai Nasara yasanya ya dafe daidai saitin zuciyarsa, da ke ɗanyi masa zafi, gaba ɗaya acikin kwanakinnan haka yakejin faɗuwar gaba na ruskarsa, sannan gefe ga Ummu (Hajiya Sulaimiya) ta sameshi da zancen cewa tana yawan mugayen mafarkai akan ɗanta Sooraj. Lallai tun da yaga Mas’oud a birkice haka, yasan matsalan babbace. Hular kansa ya cire tare da ajeta agefe, har fargaban tambayar Mas’oud ɗin yake wani hali Sooraj din ke ciki, Sooraj shi kaɗaine ɗansa, sannan kuma yana matuƙar sonsa, sam bayason wani abu ya samu Sooraj, baisan yazaiyi ba, shi ya haifi Sooraj amma baisan Sooraj wani irin mutum bane, komai nasa aɓoye yake,baya bayyana duk wani sirrinsa. kullum cikin ƙunci da damuwa zaka ganshi, ada suna tunanin rashin zama da mace shine matsalarsa, amma da sukayi masa aure, sai suka ga ashe wannan bashine matsalarsa ba.
“Abba akwai matsala, Sooraj yana asibitin Lagos baida lafiya, hari aka kai masa a gidansa dake Lagos!” Mas’oud ya faɗi haka idanunsa suna mai cikowa da ƙwalla.
Arazane Abba yatashi daga zaunen dayake, tare da rumtse idanunsa. Muryarsa amatuƙar raunane yace. “Kada kacemin wasu sun cutarmin da Sooraj, Mas’oud, zan iya jure komai, amma banda labari mummuna akan Sooraj, sun kashemin shi ko? ” idanun Alhaji Mansur tuni sun ciko da ƙwalla.
“Ka kwantar da hankalinka Abba, Sooraj bai mutu ba kawai dai yana da buƙatar kulawarku ne ayanzu” Mas’oud yafaɗi haka yana mai ɗan share ƙwallan daya zubo daga cikin idanunsa.
“Kayi mana booking flight Mas’oud, amma banaso Ummu ta sani, yau zamu tafi Lagos” Alh. Mansur yafaɗi haka cike da damuwa.
Gaba ɗaya Alh. Mansur baya cikin nutsuwarsa, hankalinsa atashe yake sosai, baisan awani hali zaije ya taradda tilon ɗansa ba. Babban damuwarsa ma itace Ummu, tabbas yasan idan Ummu taji to dole sai ciwonta ya tashi.
***
Yau aɗan acikin nishaɗi ta dawo gida, domin kuwa kwana biyunnan sosai Farouk ke ɗan ɗebe mata kewa, babban abun dayasanya ta shaƙu dashi, shine irin yanda yake kawar mata da damuwarta, yana sakewa da ita sosai, sannan kuma yana bata dukkan kulawansa, ako da yaushe yakan kashe ayyukansa yazo gareta, hakan yasa tayi sabo dashi.
Gobe zasu kammala jarabawansu, sannan kuma agoben za’a basu hutu. Fitowarta awanka kenan ta sanya wata doguwar riga ja, kitchine ta wuce, tsaye tayi agaban gas tare dayin shiru, damuwarta ne ta dawo sabuwa fil. Motsinsa takeson ji acikin gidan, rashin jinsa da kuma rashin ganinsa yana damunta sosai, tanason koda ƙamshinsa ne taji, hakanan takeji ajikinta cewa baya lafiya. Cikin rashin daɗin rai haka ta soya indomie taci sama sama. Tunda tayi sallah take aikin duba littafin Physics da zasuyi gobe. Kamar kullum idan ta kwanta mafarkinsa kawai take, yauma hakance ta kasance domin kuwa gaba ɗaya shitake ta gani acikin mafarkinta, yanayin halin da take ganinsa acikin mafarkin sam baya mata daɗi.
STORY CONTINUES BELOW
Ƙarfe goma daidai suka fito a exams, direct wajen assembly suka nufa. Hutun 3 weeks kawai aka basu, duk da haka ɗaliban sunji daɗi sosai.
Cikin sanyin jiki ta ɗago idanunta ta kalli Farouk wanda shima kallonta yake, gaba ɗaya idanunsa sunyi wasu narai narai dasu, harshensa yasanya ya ɗan lashi kan lips ɗinsa.
“Banason wannan hutun, kwata kwata banason duk wani abu da zai nesantani da ganinki pretty na, da gaske nake inasonki har acikin zuciyata!!” jin sauƙar kalaman nasa acikin kunnuwanta, ya sata jin tamkar aradu ce ta sauƙa, idanunta dake kan fuskarsa ne suka kawo ƙwalla, “So……na!!” tafaɗa murya asarƙe..
Kallonta shima yayi cikin wani irin yanayi, ɗan matsowa kusa da ita yayi, tare da kai hanunsa ya kama nata hanun. “Nasan ke ƙaramar yarinyace, sannan kuma bakisan menene so ba, dan inasonki bawai yana nufin zan cutar dake bane, ban taɓa jin soyayyar wata mace azuciyata kamar yanda nakejin taki soyayyarba, Inasonki Ziyadah, dan Allah Kada ki ƙini, tun ran da naganki nakamu da Sonki, har abada kuma zan ci gaba da sonki, namiki alƙawari bazan taɓa rabuwa dake ba!!” Yaƙare maganar cikin wata murya mai sanyi, yayinda gaba ɗaya yanayin idanunsa suka sauya. Hawayene suka gangaro daga idanun Ziyada, karo na farko arayuwarta da wani yafurta mata kalmar SO, karo na farko arayuwarta da wani namiji ya tsaya yayi mata magana cikin kulawa har haka, saidai kuma sam bata fahimci kalamansa ba. Ganin yanda hawaye yake fita daga idanunta ne ya sanyashi, kai hanunsa fuskarta da niyyar share mata hawayen, da sauri taja da baya, tare da ƙwace hanunta dake cikin nasa. Juyawa tayi cikin yanayi na gudu gudu sauri sauri tabar wajen, ƙiran sunanta Farouk yake amma ko waiwayosa batayi ba, balle yasa ran tsayuwarta, ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, tare da lumshe idanunsa da suka soma sauya kala, har acikin jininsa yana jin son yarinyar, komai nata me kyau ne, kallonta, tafiyarta, nutsuwarta, sau babu adadi yakan samun kansa cikin wani irin yanayi idan yana tare da ita, da ƙyar ya iya shiga motarsa yabar cikin makarantar.
Ziyada kuwa direct inda su Nasmah ke zaune ta nufa, tana zuwa ta faɗa kan cinyar Shukrah, tare da rumtse idanunta.
Kallon kallo Nasmah da Shukra suka shiga yiwa juna, cike da tsantsar kulawa suka haɗa baki wajen tambaryarta. “Lafiya Ziyada? meke damunki?” duk waƴannan tambayoyin sunyi mata shine alokaci guda.
Ɗago kanta dake kan cinyar Shukrah tayi, gaba ɗaya hawaye ya ɓata mata fuska. Ganin haka yasa suka ƙara ruɗewa.
“Kuka Ziyada, meke faruwane?” Inji cewar Shukra dake ƙoƙarin share mata hawaye.
Kanta taɗan girgiza cikin muryarta mai ɗauke da rauni tace. “Bansan me yake nufi ba Shukra, bansan menene So ba, bansan ya akeyinsa ba, gaba ɗaya ya juyarmin da tunanina, dan Allah Shukra ki faɗamin menene SO?” taƙare maganar tana mai sakin ɗan guntun hawayen dake maƙale cikin idanunta.
Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da ɗanyin murmushi. “Dama nasan haka zata faru Ziyada, saboda tun randa yasake dawowa nasan ya kamu da sonki ne, So ba ƙarya bane ba Ziyada, akwaita azuciyar kowa, kuma sannan Allah Ne ke halittarta aduk inda yaso akuma lokacin da ya so, zaki gane kin kamu da son mutum ne kaɗai, ta hanyar yawan tunaninsa, yawan damuwa dashi, zai dinga faɗo miki arai aduk wani halin da kike ciki, ƙunci, ko daɗi, amma ni aganina Farouk baida aibu, domin irin Farouk ko wacce mace zataso yin soyayya dashi, gayen yayi tako ina” Shukra taƙare maganar tana sakin murmushi.
Jin kalaman Shukra yasanya jikin Ziyada yin sanyi, hakan yasa ta juyar da kanta gefe, gaba ɗaya kalaman Shukra sun ɗaure mata kai, musamman ma inda tace wai “Idan kanason mutum zakana yawan tunaninsa, sannan zaina faɗowa ranka ako da yaushe” “Me taimako” shine sunan data fara ambata acikin rai da zuciyarta. Da sauri ta girgiza kanta, sam bazata taɓa sakewa tasoma wannan banzan wasan dashi ba, shi cikekken namiji ne, wanda haɗuwa da kyawunsa har sun wuce gaban kwatance, tayama za’ayi tasoma wannan banzan wasan akansa, kawai dai saboda ya taimaketa ne, yasa takejinsa har acikin jikinta, amma idan ba haka ba ita wacece da har tunaninsa zaina damunta? duk wuya duk daɗi bazata taɓa manta wacece ita ba, Ƙasƙantacciya, wacce bata da wani gata, wacce tataso cikin talauci da maraici. Lumshe gajiyayyun idanunta tayi, tare da sanya hanu ta tallafi ƙuncinta. Tanajin su Nasmah da Shukra suna hira, amma takasa sa musu baki, ahaka har Kamalu driver yazo ɗaukarta, cike da kewar juna tayi sallama da su Nasmah. Ko acikin mota jigum tayi gaba ɗaya damuwowi sun cika zuciyarta.
Lagos Nigeria.
Kuka sosai Alh.Mansur yayi alokacin dayaga yanda ɗansa Sooraj ya dawo, gaba ɗaya ba abanbanceshi da gawa, domin kuwa har yanzu baisan inda kansa yake ba. Gaba ɗaya yashiga damuwa, duk da cewa sosai likitotin suka dage wajen ganin sun bawa Sooraj ɗin kulawa. Waya Alh. Mansur yayiwa babban abokinsa Dr.Mohd dake aiki ababban asibitin Abuja, Dr.Mohd ƙwararren likitane wanda yasan aikinsa, domin kuwa aduk Abuja shine babban likita, maganar da sukayi da Dr. Mohd ne yasanya Alh.Mansur yi musu booking flight, ƙarfe 6 na yammaci daidai jirginsu ya ɗaga zuwa sararin samaniya.
Koda suka isa Abuja Kamar gawa haka aka shiga da Sooraj Intensive Care Unit.
Jigum haka Abba ya zauna, tare da sanya hanu ya dafe kansa. Gefensa Ummu ce wanda tabiyo flight daga Kaduna tazo, kuka take sosai, Abba yayi rarrashin duniya amma sam taƙiyin shiru.
Tafe yake yana tuƙa mota, amma gaba ɗaya hankalinsa baya tare dashi, tunani yake akan abunda zuciyarsa ke raya masa, har azahiri yana ganin hakan shine daidai.
Zaune take akan rug ta nannaɗe ƙafafunta, farcen ƙafanta take yankewa, amma azahiri hankali da tunaninta yana wani waje. Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar falonne yasa ta ɗago kanta da sauri, Dai dai lokacin Mas’oud ya buɗe ƙofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Ganin Mas’oud yasata tashi tsaye da sauri, murya asanyaye ta amsa sallaman nashi. Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yana mai ɗan ƙare mata kallo 6
Gaisheshi tayi cikin murya me sanyi, fuskarsa aɗan sake ya amsa mata, kitchine ta shiga ta ɗauko cup, sannan ta buɗe fridge ta ɗauko masa ruwa, akan glass stull ɗin dake gabansa ta ajiye ruwan. Tana shirin komawa ɗaki taji yaƙira sunanta “Ziyadah!”
Tsayawa tayi cak tare da ɗan juyowa takalleshi “Na’am” ta amsa masa murya asanyaye.
“Ɗauko mayafinki kizo akwai inda zamuje” Yafaɗa yana mai ɗan kurɓan ruwan da ta kawo mai.
“To” tace murya asanyaye. Sannan ta wuce ɗaki, jigum tayi tana mai tunanin ina zasu, wata zuciyarne tasoma ƙoƙarin kawo mata wani mummunan tunani, hakan yasa tayi saurin ɗaukar lufayanta tasanya, tare da ɗaukan takalmi flat shoe ta zura aƙafafunta, lokacin da tafito falon a tsaye ta sameshi yana ta kaikawo da alama yana cikin damuwa.
Yanaganinta yace “Yauwa muje ko” haka suka fito yana gaba tana biye dashi abaya, gani tayi ya tsaya yanawa me gadi magana , hakan yasa taɗan tsaya itama agefe.
Tafiya suke babu wani wanda yace da ɗan uwansa wani abu. Har saida sukayi nisa da gidan kafun yaɗan rage gudun motar, kallonta yayi tare da cewa. “Inaso daga yanzu ki fara amsa sunan ƙanwata, SOORAJ baida lafiya yana asibiti yanzu haka, nasan yana da buƙatar kulawanki adaidai wannan lokacin, please Dan Allah Ziyada ki kula da Sooraj, shiɗin mai rauni ne akowani ɓangare, kulawarki kaɗai yake da buƙata”
Ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, yayinda idanunta suka cicciko da ƙwalla, damuwa ƙarara ta bayyana akan fuskarta, duk da batasan asalin sunansa ba , amma jikinta ya bata cewa SOORAJ shine me taimakonta. Har suka isa babban asibitin bata sake cewa komai ba, saidai gaba ɗaya bata da natsuwa. Haka suka shiga cikin asibitin jiki asanyaye, direct wani ɗan ɗaki suka nufa, suna shiga Mas’oud ya durƙusa tare da sake gaishe da su Abba da Umma, Abba ne kaɗai ya iya ƙarfin halin amsawa domin Ummu kam Kuka take har yanzu, cike da ladabi Ziyada ta durƙusa har ƙasa ta gaidasu, Abba ya amsa yana me kallonta, sai alokacin Ummu dake kuka ta ɗago kanta ta kalli Ziyada. Ganin irin kallon da Ummu keyiwa Ziyada yasa Mas’oud cewa.
“Amm Abba dama wannan ƙanwatace ƴar Baffana ne dake Sokoto, tana karatune anan, sannan kuma suna da kyakkyawan alaƙa tsakaninta da Sooraj, shine nace mai zaihana tazo tana tayaku kula dashi tunda yanzu sunyi hutun makaranta” Yaƙare maganar yana ɗan sosa bayan kanshi, domin shi kansa yasan ya shiryota.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da cewa “Tabbas hakan da kayi ka kyauta Mas’oud, domin dama kaga zaman Ummu’nku anan bazai yi wuba, saboda tunda tazo kuka take, nikuma banason kukannan!” Abba yafaɗi haka cike da damuwa.
Ɗan ɗagowa Ziyada tayi ta kalli wacce ake ƙira da Ummu, tsananin kaman da tagani na me taimako akan fuskar matar shiya sanya tayi tunanin ko mahaifiyarsa ce, to amma idan da yana da iyaye aida tasan bazai zauna agidansa shi kaɗai ba, dole ne zai zamana iyayensa suna tare dashi.
Kallon Ziyada Ummu tayi sosai, wani tunanine yake ɗarsuwa acikin ranta, bazatace bata yarda da maganganun da Mas’oud ya faɗa ba, amma ita ta haifi Sooraj tasan kusan gaba ɗaya halayyarsa, mutumin da bayason mu’amala dako wacce irin mace yau shine za’ace wai akwai kyakkyawar alaƙa atsakaninshi da wata?.
Abba da Mas’oud ne suka tashi suka fice daga cikin ɗakin, kasancewar alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba. Ummu ne tafito daga toilet ɗin dayake cikin ɗakin, fuska da hannayenta duk ruwa da’alama alwala tayi. +
Kallon Ziyada dake zaune jigum tayi. “Jekiyi alwala” Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin shimfuɗa darduma akan tiles. Sumu sumu haka ta wuce toilet ɗin ta ɗauro alwala, hanu tasanya acikin hijab ɗin dake jikinta, ta zaro ɗan kwalin dake kanta, shimfiɗawa tayi akan tiles, sannan ta hau tare da daidaita tsayuwarta, akan ɗan kwalin ta gabatar da sallan Magriba, ko da ta idar da sallan, samun kanta tayi dayin shiru, tare da jingina kanta da jikin bango, gaba ɗaya jin zuciyarta take babu daɗi, babu wani abu da takeson gani sama da Helper ɗinta, sosai hankalinta yake atashe, sannan gefe guda kuma, ga kukan da taga mahaifiyar Sooraj ɗin nayi yasake ɗaga mata hankali.
Dukansu daga ita har Ummu babu wacce tatashi daga kan abun sallanta, har aka ƙira sallan isha, baga Ummu kaɗai ba hatta Ziyada saida tasanya Sooraj cikin addu’anta. Ƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin kanta take, aka turo ƙofar ɗakin aka shigo. Alh.Mansur ne dakuma Mas’oud, Mas’oud ne ya aje basket ɗin dake hanunsa, tare da kai dubansa gareta.
“Ziyada ki zubawa Ummu abinci taci, kema ki ɗebi naki kici, zuwa anjima likitotin sun tabbatar mana da cewa zamu samu ganinsa!” Mas’oud yaƙare maganar cike da ɗan yanayi na damuwa. Alh.Mansur kuwa kasa ma cewa komai yayi, zama kawai yayi akusa da Ummu tare dayin shiru.
Ɗaukan basket ɗin Ziyada tayi tare da zaro wasu plate, kulan dake cikin basket ɗin ta buɗe tare da sanya spoon ta zuba lafiyayyar jalop rice wacce taji bushashshen kifi acikin plate ɗin. Cike da ladabi ta ƙarasa gaban Ummu, cikin muryarta dake rawa tace. “Ummu ga abinci”
Kai Ummu tagirgiza cike da damuwa tace.
“Banajin zan iya cin abinci batare da na sanya ɗana a idanuna ba, kici kawai!” gaba ɗaya muryar Ummu rauni kawai take bayyanawa.
Hanun Ummu Alh.Mansur ya kamo, cike da tsananin so da kuma nuna kulawa ga matartasa yace. “Ki kwantar da hankalinki Sulaimiyya, Isha ALLAH Sooraj zai samu lafiya, addu’an mu kawai yake da buƙata bakomaiba, kibar kukannan haka kuka banaki bane.” Kallon Ziyada yayi tare da cewa.
“Miƙomin abincin nan na bata” karɓan plate ɗin abincin Abba yayi yashiga lallaɓa Hajiya Sulaimiyya akan taci, amma gaba ɗaya ta daburce taƙi ci, hawayene kawai ke silalowa daga cikin idanunta, shima kanshi Abban ƙarfin hali kawai yake amma damuwane ninke aƙasan ranshi.
Gaba ɗaya itama Ziyada kasa cin abincin tayi, lomanta uku ta ture plate ɗin abincin gefe, ji tayi ko kallon abincin batasonyi, hawayene suka ziraro daga cikin idanunta, da sauri tasanya gefen hijabinta ta share, tausayin halin da taga Iyayensa aciki take, musamman yanda taga hawayen mahaifiyarsa ya kasa daina zuba, jitayi gaba ɗaya zuciyarta ta karye..
Da ƙyar Abba yasamu Ummu taci 4 spoon na abincin. Dr.Mohd ne dakanshi turo ƙofar ɗakin ya shigo. Cike da tausayawa ya dubi dukkaninsu, da sauri Alh.Mansur yataso daga zaunen da yake yana cewa.
“Dr.Mohd ya dai, akwai wani cigaba ko kanaga kawai gobe mu wuce Germany ɗin?” Yanayin yanda Alh.Mansur yayi maganan kaɗai ya isa sanya zuciyar mai sauraro karyewa, domin kuwa kallo ɗaya zakayi masa kasan baya cikin wata nutsuwa, sosai rashin lafiyar Sooraj ɗin ke damunshi.
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar Zuciya Dr.Mohd yayi tare da kama hanun Alh. Mansur suka fice daga cikin ɗakin, ganin haka yasa Ummu fashewa da kuka, domin atunaninta wani abunne ya kuma sake faruwa, Mas’oud ne yayi ƙarfin halin fara rarrashinta.
“Calm down Alh.Mansur kazauna!” Dr.Mohd yafaɗi haka akaro na uku kenan, domin kuwa tun ɗazu yaketa yiwa Alh.Mansur ɗin tayin wajen zama, amma saboda ruɗun da Alhajin ke ciki, sam ya kasa zama.
“Bazan iya zama ba Dr.Mohd, hankalina amatuƙar tashe yake, kafaɗamin maiyasa ka kawoni office ɗinka? Shin wani abu yasake faruwa da SOORAJ ɗinne?”
“Na faɗama ka kwantar da hankalinka Alhaji, Insha Allah Sooraj zai farfaɗo nan bada jimawa ba, sai dai kawai akwai wata matsalane da sai yanzu, da mukayi masa gwaji muka san da ita!” Dr.Mohd yafaɗi haka yana mai shakkan abun da zai faɗawa Alh.Mansur, kasancewar baisan tayaya Alhaji’n zai ɗauki maganartasa ba.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’n!! Doctor mai kuma yasake faruwa?” Alhaji Mansur ya tambaya cike da damuwa.
“Amm bawata matsalabace Alhaji matuƙar za akula, nace dama tuncan kunsan cewa yana ɗauke da ciwon zuciya ne?”
Ai tamkar rugugin aradu haka Alhaji Mansur yaji sauƙan kalaman Dr.Mohd acikin kunnuwansa.
Daɓas haka Alhaji Mansur ya zauna tare da sanya hanu ya dafe kansa. “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!!” kawai yaketa ambata acikin rai da zuciyarsa. “Shikenan kuma lokacin dazai rasa ɗansa mafi soyuwa agaresa yazo, haƙiƙa wannan ƙaddaran tana da girma agaresu baki ɗaya, Allah yabasu ikon cinyeta!” yafaɗi haka acikin zuciyarsa. 2
Aƙalla yaɗauki kusan sama da 12 minute ahaka,
Idanunsa da sukai jajur dasu ya ɗago ya kalli Dr.Mohd.
“Idan nafahimci kalamanka Doctor kanaso kace dani Sooraj ɗana yana ɗauke da ciwon zuciya ko?”
“Ƙwarai kuwa haka nake nufi Alhaji, amma ciwon batayi tsanani sosaiba, idan har ya riƙe magani da yardan Allah Zai iya warkewa ako da yaushe, kada ka tashi hankalinka Alhaji, Insha Allah komai zaizo da sauƙi!!”
Inji cewar Dr.Mohd wanda yake cike da buri da kuma fatan ƙarfafawa Alhaji Mansur ɗin guiwa. 1
Ajiyar zuciya Alhaji Mansur ya sauƙe tare da cewa.
“Ni musulmi ne kuma nayarda da ƙaddaran da Allah Ya aikomin mai kyau ko marar kyau, kowani cuta aduniya tana da maganinta, cutar mutuwa ce kaɗai bata da magani, haƙiƙa komai da komai na Allah Ne, samun cuta da kuma sauƙi duk waƴannan ikonsa ne, kafun ka tsara naka shi yajima da tsara nashi, idan Allah Ya ƙadarta maka ƙaddara mummuna babu wani mahaluƙi daya isa sauya maka ita, haka idan ya nufeka da kyakkyawa babu wanda ya isa sauya maka ita, babu wani abu aduniya da yafi ƙarfin ikon Allah da kuma Addu’a, zamuyita addu’a Insha Allah komai zai zamo tarihi watarana!!” handkerchief ɗin dake cikin aljihunsa ya ciro tare da sanyawa yaɗan share ƙwallan da suka cika idanunsa. 1
Murmushi Dr.Mohd yayi tare da cewa “Haƙiƙa duk wani musulmin ƙwarai irinka akeso yakasance Alhaji Mansur, Allah yayi mana jagora”
Da “Ameen” kawai Alhj Mansur ya iya amsawa, sannan suka tashi suka fice daga cikin office ɗin.
Direct ɗakin da su Ummu suke suka nufa.
“Hajiya zaku iya ganinsa yanzu” faɗar Dr.Mohd.
Dukansu suka ɗunguma sukabi bayan Dr.Mohd ciki kuwa harda Ziyada. Wani waje suka nufa daganin wajen kasan na musammanne sannan kuma secret waje ne, wani ɗan corridor suka shiga sannan suka samu kansu a gaban wani ɗaki. Dr.Mohd ne ya tura ƙofar ɗakin ahankali, sannan suma suka rufa masa baya, Ziyada ce tayi na ƙarshen shiga. Tana shiga ɗakin idanunta suka hasko mata shi, kwance yake akan wani gado mai ɗan faɗi, fuskarsa na kallon sama, sanye yake da dogon wando babuko riga ajikinsa, sai bandage ɗin da aka lilliƙa awajen da akayi masa aikin cire bullet. Wata ƴar wayane aka sanya masa atacikin hancinsa, sosai ya ƙara haske, gashin kansa kuwa sun kwanta luf, sam batasan lokacin da hawaye suka gangaro daga cikin idanunta ba, jitayi ƙafafunta gaba ɗaya bazasu iya ɗaukarta ba. Hakan yasa ta jingina bayanta da wani dogon ƙarfe dake kusa da ita. Ummu kuwa sai aikin share hawaye kawai take da handkerchief ɗinta, shi kansa Alh.Mansur baƙaramin dauriya yayi ba da baiyi kuka ba, musamman ma da yanzu yasan cewa ciwukan ɗan nasa sun zame masa biyu. Mas’oud ma saida ya share ƙwallan tausayin abokinsa, domin kuwa duk wanda yaga Sooraj ahaka sai ya tausaya masa. Hannu Ummu takai ta shafi kansa, wasu sabbin hawayene suka sake fitowa daga cikin idanunta. Bazata iya jurewa ba, hakanne yasanya ta juya da sauri ta fice daga cijin ɗakin, koda ta fita waje tsayawa tayi ajikin wata rumfa tasaki kukan tausayin Sooraj, ganin Ummu tafita yasa Alh.Mansur binta saboda yasan aikin kuka zataje tai tayi, bayan kuma tana da Hawan jini, sam bayason ciwonta ya tashi.
STORY CONTINUES BELOW
Mas’oud ne ya kalli Ziyada dake ta zubar hawaye ta kafe Sooraj ɗin da kyawawan idanunta, duk abun da ke wakana ma sam ita batasan anayinsa ba, gaba ɗaya hankali da tunaninta suna ga Mr.Helper ɗinta, har batasan sanda hawaye ke zuba daga cikin idanunta ba.
“Ziyadah!” Mas’oud yaƙira sunanta murya asanyaye. Sai alokacin ta dawo daga duniyar tunanin da take, bata iya amsa ƙirannasa ba, saidai ɗago kai da tayi ta kalleshi.
“Ki share hawayenki ba komai kuka ke magancewa ba, kiyi masa addu’a kawai, yafi buƙatar hakan agareki” Mas’oud yafaɗi haka yana mai cusa hannayensa acikin aljihun wandonsa.
Kai kawai ta iya jinjina masa alaman “To” domin bazata iya cewa dashi komaiba ayanzu, gaba ɗaya jikinta ya mutu, zuciyarta tayi rauni, duk wani tunaninta ya tsaya cak.
Dr.Mohd ne yace sutafi hakanan saboda ba aso hayaniya tayi yawa a inda yake.
Alh. Mansur ne ya kalli Mas’oud tare da cewa. “Mas’oud kakaisu gida, nikuma zan zauna anan”
“Banajin zan iya komawa gida Alhaji, nikam nafiso na zauna anan” Ummu tafaɗi haka cikin muryarta da ta soma dashewa saboda kuka.
“Zaman asibiti banaki bane Sulaimiyya kuje kawai gobe da safe sai kuzo!” Alh.Mansur ya faɗi haka aƙagauce saboda sam bayason musu.
“Abba me zai hana kabiyomu na sauƙeku idan yaso ni sai nadawo na kwana anan ɗin”
“A’a Mas’oud baza ayi haka ba, nine nan zan kwana, kuje kawai saida safe idan Allah Ya kaimu, sannan kuma banyarda kabarsu su kaɗai agidaba, ka kwana agidan kaima” Alhaji Mansur yana gama faɗan haka ya juya ya koma cikin asibitin. Babu yanda Ummu ta iya haka ta shiga cikin motar Mas’oud ya ɗauki hanyar Maitaima dasu inda anan gidan Abba dake Abuja yake. Wani irin tamfatsetsen gida Ziyada taga sunshiga, gaba ɗaya ginin gidan, gidan sama ne, gida ne mai kyau da girma, komai na gidan gwanin ban sha’awa ne, ko ina dake cikin gidan awadace yake da hasken ƙwan wuta, Mas’oud ne yasanya key ajikin ƙofar ya murza. take babban ƙofar falon ta buɗu. haka suka kutsa kai cikin babban falon dake cike da kayan more rayuwa, kayan ƙyale ƙyale dana ado. Komai na cikin falon tsab tsab yake, Mas’oud ne ya buɗe gaba ɗaya bedrooms ɗin dake cikin falon, acan sama bedroom ɗin Ummu yake hakan yasa ya wuce sama direct ya buɗe mata nata ɗakin. Ɗakin dake kusa dana Ummu yace da Ziyada ta shiga, gobe zai kawo mata kaɗan daga cikin kayanta. Saida ya tabbatar da cewa dukansu sunshiga ɗakunansu, kafun ya dawo ƙasa shima ya shiga wani ɗaki.
Aƴan kwanakinnan tasaba duk dare saitayi wanka kafun ta kwanta saboda yanayin zafi da ake ciki, amma yau hakanan tasamu kanta da rashin duk wani kuzarinta, damuwar dake kwance aranta ma bazata bari tayi wani baccin kirkiba balle har aje ga yin wanka. Hijabin jikinta ta cire tare da ɗalewa kan gadon ta kwanta jigum, yayinda ta sanya hannayenta ta tallafe ƙuncinta. Tunanin Mr. Helper ne ya tsaya acikin rai da zuciyarta, ganinsa da tayi acikin ciwo yau yasanya hankalinta gaba ɗaya ya tashi, wani abu takeji agame dashi, wanda takasa tantance menene amma ta ta allaƙa abun da sunan TAUSAYI, juyin duniya tayi amma bacci yaƙi ɗaukarta, haka tayita saƙe saƙe har kusan asuba sannan tatashi ta ɗauro alwala.
Kamar yanda bacci ya guji Ziyada haka ya gujewa Ummu, haka Ummu ta kusan kwana tana sallah, sauƙi kawai take nemawa ɗanta awajen ALLAH, kuka kam tayishi, domin tun tanayinshi da iyaka ƙarfinta, har hawayen suka daina fita.
7:30 daidai taji anayi mata knocking ƙofar ɗakin da take ciki, dama tana zaunene akusa da ƙofar hakan yasa ta miƙe taƙarasa jikin ƙofar. Koda ta buɗe Mas’oud tagani tsaye. kafun yace wani abu tayi saurin cewa “Ina Kwana”
“Lafiya lau” ya amsa yana me miƙo mata wata leda dake hanunsa.
“Kayankine kishirya, saiki fito kiyi breakfast, anjima zamu koma asibiti”
Amsar kayan tayi tare dayi masa godiya, ta koma cikin ɗaki, shima juyawa yayi ya koma wajen Ummu dake zaune afalo, tun ɗazu ba abun da yake sai aikin rarrashi.
Wanka tayi sannan ta ɗauki doguwar rigan material blue wanda yakawo mata tasanya, ɗinkin rigan irin rapper gown ɗinnan ne, sannan tana da ɗan guntun hanu, kallon kanta tayi acikin madubi, tare da kallon rigan azahiri, mamakin inda yasamo rigan take, domin kuwa tasan baya ɗaya daga cikin kayanta nacan gidan, gaba ɗaya ma kayan daya kawo mata sabbi ne, kuma duk daga ɗinkin materials sai wasu atamfa guda biyu wanda aka musu ɗinkin riga da sket. Jihabin data gani haɗe da rigan material ɗin ta ɗauka tasanya ajikinta, kasancewar white skin gareta saigashi kayan sunyi mata kyau sosai. Afalo ta iskesu duka suna zaune, cike da ladabi ta rusuna ta gaishe da Ummu, amsa mata gaisuwan nata Ummu tayi tanaɗan dubanta. 1
Akan sofa ta zauna tare da tanƙwashe ƙafafunta, Mas’oud ne ya turo mata plate ɗin soyayyen chips gabanta tare da kofin tea.
Bata wani iyacin abincin sosaiba, tea ɗinnema ta ɗansha da yawa. Mas’oud ma sama sama yaci abincin, Ummu kam adole takecin abincin, hakan ma saboda umarnin da Alh.Mansur ya bata ne, da yace “Idan tasan bataci abinci ba karta sake tazo asibitin, idan bahaka ba kuwa zata gamu da fushinsa.” banda haka babu abun dazai sanya tasanya wani abu na abinci acikinta.
Yauma dai aɗakin jiya suka zauna, gaba ɗaya zuciyoyinsu babu daɗi. Sai ƙarfe uku sannan Dr.Mohd yayi musu jagora zuwa ɗakin da Sooraj ɗin yake.
kamar jiya haka Ummu tayita aikin ƙwalla, Ziyada ma idanunta sunyi tab da hawaye, ɗan matsawa kusa dashi tayi tare da kafesa da idanunta, gani takeyi kamar zai buɗe idanunsa, gani take kamar bacci yake idan katasheshi zai tashi, gani take kamar duk abun da suke yana jinsu, dubanta takai kan ƴan yatsun ƙafarsa, ƙurawa babbar yatsar ƙafansa ta dama idanu tayi, gani tayi kamar yatsar nasa tana motsawa, gefen hijab ɗinta ta sanya ta share ƙwallan dake cikin idanunta, wanda suka sa take ganin komai dishi dishi, sake kallon yatsar ƙafannasa tayi, sai kuma taga bata motsi, da alama gizone idanunta keyi mata.
Kallon Alh.Mansur Dr.Mohd yayi tare da nuna Ziyada yace.
“Matarsa ce?”
“A’a ƙanwarsace” Alh.Mansur yabashi amsa shima yana mai kallon Ziyada wanda idanunta ke cike da ƙwalla.
Kai Dr.Mohd ya jinjina tare da cewa “Inaganin ka ɗauki Hajiya ku koma gida kawai, ita sai kubarta anan, naga kamar yarinyar bata da hayaniya zamanta awajensa bazai kawo wata matsala ba, amma idan Hajiya ce zata zauna kasan dole saita ƙara ta da hankalinta”
Cike da gamtsuwa da kalaman Dr.Mohd, Alh.Mansur ya jinjina kansa. “Tabbas maganarka haka take doctor, yanzu kuwa zamu tafi insha Allah”
Da ƙyar da dabara Abba yasanya Ummu agaba yana rarrashinta sukabar cikin asibitin, tare da Mas’oud wanda shine ke tuƙasu.
Ziyada ita kaɗai akabari acikin ɗakin daga ita sai SOORAJ wanda bashida maraba da gawa. Akan kujeran dake gefen gadon ta zauna, tare da kifa kanta ajikin gadon. Tananan zaune har aka ƙira sallan Magriba, Sallah tayi sannan ta dawo ta zauna. Kallon kyakkyawar fuskarsa tayi, zara zaran eye lashes ɗinsa ne suka kwanta aƙasan idanunsa, sukayi luf dasu gwanin burgewa, gani tayi gumi nata fesowa akan goshinsa, mamakine ya kamata domin kuwa sanyin AC har yaso yin yawa acikin ɗakin. ɗan kwalinta ta ɗauka tashiga goge masa gumin. Atunaninta ko sanyin AC’n ne yayi masa kaɗan hakan yasa taɗan ranƙwafo da kanta zuwa daidai fuskarsa, ahankali tashiga hura masa iskan bakinta akan fuskarsa. hannunta takai kan nasa hanun tashiga goga masa taushin tafin hanunta akan fatarsa, tanayin hakane cikin wani irin yanayi mai ɗauke da nutsuwa. Aƙalla taɗauki kusan sama da mintuna goma tana yi masa haka. Jin ana ƙiraye ƙirayen sallan isha ne yasata miƙewa daga zaunen da take, ta juya kenan kamar amafarki haka taji ya damƙi hanunta.Kamar amafarki haka taji sauƙan hanunsa acikin nata.
Da sauri ta waiwaya zuwa gareshi, amma sai taga ko motsi baiyi ba, hasalima idanuwansa akulle suke da’alama bai dawo cikin hayyacinsa ba. Ahankali ta koma ta zauna tare da kafe sa da ido, zara zaran eye lashes ɗinsa da suka kwanta luf luf take kallo, ahankali tayi ƙasa da idanunta tana kallon ɗan ƙaramin pink lips ɗinsa wanda suka ɗan bushe. Idanunta ta sake mayarwa kan lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa, baƙaƙen hairs ne kwance luf akan fatarsa, komai nasa me kyaune kuma gwanin burgewa. Kanta ta mayar jikin gadon tare da lumshe idanunta. Wani irin tausayinshi takeji, daga wani ɓangare na zuciarta kuwa tunanin Farouk ne yazo yayi tsaye. Bazata iya faɗin me takeji game da shi ba, amma tabbas akansa tanajin wasu baƙin al’amura suna ziyartan ta. Zare hanunta dake cikin nasa hanun tayi tare da miƙewa tsaye, toilet tashiga ta ɗauro alwalan sallan isha’i.
Tajima tana zaune akan sallayan. Wasu siraran hawayene suka silalo daga cikin idanunta, kallonta takai zuwa garesa, wasu sabin hawayene suka sake fitowa daga cikin idanunta, hakanan batasan me yasa ba aduk sanda ta ɗaura idanunta akansa takanji zuciarta ta karye, tasan da cewa ita mai raunice tun tuni, amma akansa raunin da takeji na dabanne. Tajima zaune akan sallayan har kusan 9 pm sannan ta tashi ta koma bakin gadon ta zauna. Kanta ta ɗaura adaidai saitin kanshi tare da lumshe idanunta. Mintuna goma tsakani bacci ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.
Ahankali breath ɗinta ke fita, yayinda hucinsa ke sauƙa adaidai saitin kunnensa, ahankali yasoma buɗe idanunsa har ya waresu gaba ɗaya, akan zanen pop’n dake cikin ɗakin ya tsayar da idanunsa, sosai idanun nasa suka sauya kala daga farare zuwa kalan ja, sannan lokaci guda suka ƙanƙance sai tarin eye lashes dake samansu wanda yayi wara wara, wani irin ciwo yakejin kansa nayi masa, yayinda yakejin wani zogi na musamman adai dai chest ɗinsa. Lumshe gajiyayyun idanunsa yayi tare da sauƙe wata gajiyayyar ajiyar zucia. Ahankali ya ɗan yunƙura tare da ɗan jingina bayanshi ajikin pillow, saida ya ɗan cije pink lips ɗinsa sakamakon wani irin zogi dayaji ƙirjinsa nayi, hanunsa yakai kan wani ɗan madanni dake gefen gadonnasa ya ɗan danna da ƙarfi har saida yayi ƙara. 3 minute tsakani saiga wata Nurse tashigo cikin ɗakin da gaggawa. Ganinsa azaune yasa tashiga tambayarsa jikinnasa. Da kai kawai ya iya amasa mata, ganin haka yasa tafita da hanzari don ƙiran Dr.Moh’d.
Baƙaramin daɗi Dr. Moh’d yaji ba sakamakon jin cewa wai Sooraj ya farfaɗo, da ƙwarin guiwarsa haka ya nufo ɗakin da Sooraj ɗin ke kwance.
Checking ɗinsa yayi sosai sannan ya tambayesa ko akwai wani abu dake damunsa. Kai kawai Sooraj ya iya girgizawa, sannan yayi masa nuni da chest ɗinsa daidai inda aka ɗaure da bandage. Alaman nanne kawai ke masa zafi.
Wasu magungunan kashe zogi Dr. Moh’d ya basa ya sha, sannan yace masa yaɗan kwanta zuwa da safe. Har Dr.Mohd yagama abun da zaiyi yafita Ziyada na bacci bata sani ba. Shiru haka Sooraj ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa, tunanine cunkushe acikin ransa, _ƘADDARA_ itace abun dake ɗawainiya da rayuwarsa, sau da yawa yakansamun kansa acikin ƙuncin rayuwa, sai dai dole ayanzu zai daure don yaga yayi faɗa da zuciyar da take ƙoƙarin hanasa ɗaukar ƙaddaransa.
STORY CONTINUES BELOW
6:00 am dai dai Ziyada ta buɗe idanunta, awahalce tayi miƙa saboda wani irin ciwo da taji duka jikinta nayi mata, gaba ɗaya duk wani gaɓa dake jikinta yayi tsami. Kallonta tamayar ga Sooraj wanda yake kwance luf acikin gadon idanunsa a rufe da’alama bacci yake, kallon small lips ɗinsa tayi tare da ɗan murza idanunta, A hankali ta buɗe ƙofar toilet ta shiga, gaban sink ta tsaya tare da ɗauro alwala, koda ta fito sallaya ta shumfuɗa tare da tada Sallah, koda ta sallame sallan bata tashi akan sallayan ba, sai dai lokaci zuwa lokaci tana kae dubanta zuwa gareshi.
7:00 am dae dae acikin asibitin tayiwa su Alhaji Ma’arouf da Mas’oud. Koda Dr.Moh’d yabasu kyakkyawan labarin farfaɗowan Sooraj baƙaramin farinciki sukayi ba, har suna rige rigen shiga ɗakin da Sooraj ɗin yake.
Da farinciki ɗauke afuskokinsu duka suka shigo cikin ɗakin, cike da ladabi Ziyada ta gaidasu, kowa fuskarsa ɗauke da annuri ya amsa mata, Ummu kam tuni tayi kan Sooraj, hawayene suka cika idanunta tab, hannunta ta ɗaura akan fuskarsa murya araunane tace. “SOORAJ!” jin muryan Ummunsa acikin kunnuwansa yasanyashi buɗe idanunsa ahankali domin dama ba bacci yakeba kwana yayi idanunsa biyu batare da ya runtsaba. Kuka ne ya ƙwacewa Ummu domin kuwa wani ƙaunar ɗannatane ya sake shiga zuciyarta, sosai takejin tausayinsa duk da ya kasance me laifine agaresu, Hanunsa Abba yakama cike da ƙarfin guiwa haɗe da farinciki yace.
“Alhamdulillah! Yajikin naka, meke maka ciwo yanzu?”
Ɗan yunƙurawa yayi zai tashi Mas’oud yataimaka masa wajen sanya masa pillow a bayansa. Breath me ɗumi yafitar sannan ya kalli Abba cikin wata irin murya yace “Banajin komai Abba, kawai inaso na koma gidane, nagaji da zaman nan!” yaƙare maganar yana ɗan ɓata fuska.
Farincikine yasake cika zuciyarsu jin cewa bayajin komai. Murmushi Abba yayi tare da dafa kafaɗan sa yace.
“Ka kwantar da hankalinka, zannema maka sallama awajen Dr.”
Ɗan ya mutsa fuska yayi tare da kawar da kansa gefe, idanunsu ne suka sauƙa acikin na juna, dai dai lokacinne kuma ƙwallan da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa kan ƙuncinta, da sauri yajanye idanunsa tare da ɗan cizan lips ɗinsa. Ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon ya somayi, Mas’oud yace “Ina kuma zaka?”
“Wanka!” Sooraj yabashi amsa ataƙaice. Bathroom ɗin dake cikin ɗakin ya shiga, long pencil jeans ɗin dake jikinsa ya cire tare da tsayawa agaban shower ruwa na dukan jikinsa, Sai da ya soma jin sanyi na ratsa cikin jikinsa sannan yakashe shower’n, dai dai lokacinne kuma aka soma knocking ƙofar toilet ɗin, yana buɗewa Mas’oud ya miƙo masa wani Blue pencil crazy jeans, tare da sabon brush da maclean, karɓa kawai yayi yakoma cikin bathroom ɗin, saida yasanya trouser’n kafun yayi brush, ruwa ya sanya yasake wanke fuskarsa. Sannan yafito daga cikin toilet ɗin. Zama yayi akan gado, lokacin har Ummu tagama haɗa masa tea. Miƙa masa cup ɗin tayi, amaimakon ya karɓa sai ya ɓata fuska tare da kawar da kansa gefe, alaman bazai shaba.
“Kayi haƙuri kasha kaji, Dr. Moh’d yace akwai maganin da zakasha kuma dole saika ci abinci!” Abba yafaɗi haka cikin rarrashi.
Karɓan cup ɗin yayi tare da kaiwa bakinsa, da kaɗan kaɗan yake sipping tea ɗin, hakanan yakejin bakinsa babu wani ɗanɗano, bai wuce rabin cup yasha ba ya aje kofin, dai dai lokacin Dr.Moh’d ya dawo hanunsa ɗauke da magunguna.
Ita dai Ziyada tana daga zaune akan sallaya tana ganin ikon Allah, mamakin yanda ake shagwaɓasa kamar ƙaramin yaro take, daga cikin zuciarta kuwa wani irin sanyin daɗi takeji na ganin ya buɗe idanunsa har ma ya tashi, Mas’oud ne ya dawo gefenta tare da jawo wata farar kujera ya zauna akai, plate ɗin dake hanunsa ya miƙa mata, abincine aciki Chips and onion soup wanda yaji ƙwai, karɓa kawai tayi ta ajiye batare da takai koda loma ɗaya bakinta ba.
“Ziyadah!” Mas’oud yaƙira sunanta cikin ƙasa ƙasa da murya.
Bata amsa masa ba sai dai ɗago kanta da tayi ta kalleshi.
STORY CONTINUES BELOW
“Kukan na menene?” yatambayeta yana me ɗan satan kallonta.
Hanu tasanya ta shafi gefen kumatunta, sai alokacin ta tuna da cewa hawaye sun sauƙo daga idanunta kuma bata share ba, hannunta tasanya ta goge hawayen tare da yin ƙasa da kanta, tasoma wasa da yatsunta.
Murmushi kawai yayi tare da cewa. “Kici abinci, Sooraj ne damuwan kuma yatashi, saboda haka baikamata kina sa kanki adamuwa ba!”
Ɗan mareraice fuska tayi tare da cewa “Banajin yunwa ne fa!”
“Kici ko ba yawa” yafaɗa ataƙaice domin shima bawai yana da yawan magana sosai bane, saidai har aransa yana tsoron kada Ummu ta ranfo cewa babu wata alaƙa atsakaninsu.
Dole take kai abincin bakinta bawai don tanajin wani daɗinsa ba, duk da cewa abincin babu laifi amma hakanan takejinta wani iri. Duk abunda sukeyi Sooraj wanda ke zaune gaban Dr. Moh’d ana naɗa masa sabon bandage yana lure dasu.
Koda Alhaji Ma’arouf yanemi da Dr.Moh’d abasu sallama, cewa yayi subari sai zuwa yamma kafunnan da yardan Allah Sooraj ɗin yasake samun ƙarfin jiki. Abba ne ya dubi Mas’oud wanda suke ɗan taɗi sama sama da Sooraj yace.
“Inaga yakamata kakai su Ummunku Gida idan yaso anjima sai su dawo”
Badon Ummu tasoba haka Mas’oud ya dawo dasu gida.
Ziyada.
Banɗaki tashiga tare da rage kayan jikinta, wanka tayi haɗe dayin brush, koda ta fito sama sama ta shafa wani body lotion ajikinta, riga da sket na wani swiss material sky blue and pink colour tasanya, ahankali ta ƙarasa gaban window’n dake cikin ɗakin ta tsaya, hanunta tasanya taɗan yaye labulen tare da jan glass ɗin window’n gefe, lumshe idanunta tayi sakamakon wani daddaɗan iska daya ratsata, Dayake ɗakin da aka bata yana sama, hakan yasa daga bakin window’n tana iya hango ƴan tsirarun motocin dake ta shawagi akan babban titin dake malale agaban gidan, tunanin Farouk ne yasoma yi mata kutse acikin zuciyarta, hakanan kyakkyawar fuskarsa ke yawo acikin idanunta, tun rananda ta ganshi takejin wani baƙon yanayi adangane dashi, daga wani ɓangare na zuciyarta kuwa RAUNI ne da Tausayin rayuwarsu ita da SOORAJ, sai dai kuma sau da dama takanjinta cikin wani irin yanayi idan ta tuna da cewa har yanzun ita bakowa bace, sannan takanji babu daɗi idan ta tuna cewa itaɗin watace wacce bata da gata, watace wacce bata da madafa, hannu ta sanya ta share hawayen dake bin ƙuncinta. Jin tsayuwar na neman gajiar da itane yasa takoma kan gado ta kwanta, luf tayi tana tunanin halin rayuwa. Yamma nafara gabatowa direct suka wuce asibiti. 1
Ƙarfe 5 daidai suka fito daga cikin asibitin tuni Abba da Ummu sun shige mota, Mas’oud ne ke gefen Sooraj wanda yake takawa ahankali sanye yake da farar button shirt marar nauyi, harma ana iya hango surar jikinshi, Ziyada ce ke biye dasu abaya hannunta ɗauke da food flask. Wata baƙar Benz suka nufa, da kansa ya buɗe gidan baya yashiga ya zauna. Ganin haka yasa Ziyada ta sulale ta nufi motarsu Abba, dayake driver ne zai tuƙasu sai kawai ta buɗe murfin gefen mai zaman banza ta zauna.
Saida suka ɗau Hanya kafun Mas’oud ya saisaita gudun motar batare da ya juyo ba yace. “Ankama waƴanda suka kaimaka hari, amma kuma taurin kai yasanya sunƙi faɗan wanda ya sasu”
Sooraj da ke lafe jikin kujeran motar ya lumshe idanunsa, batare daya ɗago da kansa ba yace “Babu amfanin faɗansu ae”
Mamakine yakama Mas’oud harsai daya ɗan juyo ya kalli Sooraj ɗin. “Meyasa?” yatambaya da mamaki.
“Saboda nasan kowa ya sasu!” yafaɗa ataƙaice domin bayason maganan tayi tsawo.
Shiru Mas’oud yayi tare da ɗan cije laɓɓansa, shikam har acikin ransa ya tsani wannan halin Na Sooraj daga anfara magana sai ya nuna ya gaji. Saida suka ɗanyi nisa kaɗan kafun Mas’oud yace. “Har yanzu bansan mekake nufi da Ziyada ba, menene ma’anar zamanta atare dakai? mekake tunanin su Ummu zasuji aransu idan suka san gaskian lamarin?”
Sai alokacin Sooraj ya ware idanunsa, shikansa saida yayi tunanin haka, amma duk yanda suka ɗauka zai bari ahakanne kawai.
Shirun da Yaji Sooraj ɗin yayi yasanya shima Mas’oud baisake cewa komai ba harsuka iso gaban tamfatsetsen gidan. Suna shiga ko gama daidaita parking Mas’oud baiyiba Sooraj yasoma yunƙurin fita daga cikin motan.
Atare dukansu suka nufi babban falon gidan. Direct Sooraj wajen wata ƙofa dake cikin falon ya nufa, koda yashiga samun kansa yayi acikin wani ɗan corridor, daga corridor’n straight wata ƙoface take facing mai tahowa. tun daga corridorn har zuwa gaban ƙofar, ƙawace yake da farin haske da kuma wasu green and white flowers masu kyau. Ahankali ya buɗe ƙofan ya tura kansa ciki, ganin komai dake cikin ɗakin nead yasanyashi maida ƙofar ya rufe. Simple royal bed golding colour ne acikin ɗakin, sai kuma wani tangamemen drawer me ɗauke da mabuɗai 10, gaba ɗaya jikin murafen drawern glass ne, ɗakin babu wasu tarkace aciki amma duk da haka yayi kyau sosai, kayansa ya cire tare da buɗe drawer’n ya zaro wani light yellow towel sabo ƙal ya ɗaura ajikinsa, kai tsaye ya wuce bathroom. Aƙallla yaɗauki sama da 1 hour yana wanke jikinsa da kansa, harsai da yasoma jiwo ƙiraye ƙirayen sallan Magriba, kafun ya ɗauro alwala. Koda yafito daga cikin bathroom ɗin gaba ɗaya jikinsa ajiƙe yake da ruwa, ɗan ƙaramin brown towel ne riƙe ahanunsa yana goge kansa, ƙarasawa gaban dressing mirror yayi tare da jawo wani lotion ɗinsa mai ƙamshi yasoma shafawa, saida ya kammala kafun ya dubi kanshi amadubi, duk da irin ciwon da yayi amma hakan baisanya jikinsa ya sauyaba, kallonsa yamayar kan murɗaɗɗun muscles ɗin hanunsa na dama, wasu irin murɗaɗɗun jijiyoyine suka fito raɗa raɗa ajikinsa, numfashi mai zafi ya fesar daga bakinsa tare da ɗan lumshe idanunsa, jiyayi wasu abubuwa na yawo acikin brain ɗinsa, take jijiyoyin jikinsa suka sake fitowa gashin jikinsa kuwa lokaci guda suka soma miƙewa, tamkar mai wani irin ciwo haka jikinsa ya soma rawa, cikin wani irin yanayi yasanya hanunsa ya daki mirror’n take ya tarwatse yayinda hanunsa kuwa take yasoma fidda jini domin mirrorn ya yankesa sosai. Dai dai lokacin Ziyada taturo ƙofar ɗakin tashigo hanunta ɗauke da tray. Shigowansa yayi daidai da juyowa yafuskanci bakin ƙofan, idanunsune yasarƙe acikin na juna amatuƙar tsorace tasaki tray ɗin dake hanunta tare da sulalewa awajen tana kallon cikin idanunsa da suka zama tamkar garwashin wuta.Cikin sauri tasoma tattara glass bowl ɗin daya tarwatse akan tiles ɗin, gaba ɗaya jikinta ɓari yake. Baiko kalli inda take ba ya juya ya koma toilet. Jiki asanyaye haka ta tattare wajen. Moper taɗauko tazo tasoma ƙoƙarin goge wajen da fruit salad ɗin ya ɓata, gashi gaba ɗaya glass bowl ɗin da fruit salad ɗin ke ciki ya tarwatse awajen. +
Wanke hanunsa yayi acikin sink tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel ya goge gumin dake fesowa ta goshinsa, atunaninsa zuwa yanzu bata cikin ɗakin don haka ya murɗa handle ɗin ƙofar toilet ɗin ya fito, ganinta a durƙushe tana tattare fasassun glasses yasan yashi saurin ɗauke kansa daga gareta, direct gaban closet ɗinsa ya nufa, wani Pencil Combat jeans black ya ciro sai kuma wata white button shirt, kallon agogo yayi yaga har lokacin sallan Magriba yaɗan gota, tsuka yaja ahankali tare da ɗan cizan laɓɓansa.
Gaba ɗaya jikinta ɓari yake, tsoro takeji kada yayi mata faɗa ko yace zaiyi mata wani abun. Jin takunsa na isowa gareta yasanya batare data kulaba ta sauƙe hanunta akan wani fashasshen kwalba, yana cakanta kuwa saiga jini, wani ƙara ta sake cike da ɗan tsoro, dubanta takai ga hanunta wanda har yaɗan fara fitarda jini, take tasoma jin wani irin raɗaɗi. Sooraj dake tsaye agaban dressing mirror yana dressing hanunsa daya yanke, baiko waiwayo ya kalleta ba, yi yayima tamkar baiji ƙaran nata ba, yana kammala dressing ɗin, ya ɗauki kayansa ya wuce toilet.
Haka tacigaba da gyara wajen, duk da cewa hanunta nayi mata zogi amma haka ta daure.
Yana fitowa daga cikin toilet ɗin sassanyan ƙamshin turaren dake fita ajikin kayansa ya daki hancinta, cikin takunsa na isa yaƙaraso ta bayanta ya raɓa yafice daga cikin ɗakin batare da ko kallonta yayi ba. Tanajin rufewar ƙofarsa, tasaki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, sai alokacin ruwan hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa. Cikin mintuna ƙalilan ta gama gyara wajen, tattara fasassun glasses ɗin tayi tazubar a durstbin, daganan ta wuce ɗakinta duk raɗaɗi ya isheta.
Yana fita kaitsaye babban masallacin dake gefe da gidannasu kaɗan ya nufa, anan yayi sallan Magriba, haka ya zauna har aka ƙira sallan Isha. Koda ya idar da sallan bai ko motsaba, istigfari yashiga yi acikin zuciyarsa, duk ƙoƙarinsa nason kawar da tunanin dake neman addabar zuciyarsa abun yaci tura, kansa ya jingina ajikin bango tare da lumshe idanunsa, numfashi yake fitarwa ahankali yayinda yake furta kalman “Astagfirullah!” daga bakinsa ahankali. Ahankali nutsuwa ke sauƙa ajikinsa, yayinda yaji damuwarsa na gushewa, sosai yaɗanji sanyi acikin zuciyarsa. Ƙarfe 9 daidai yabaro cikin masallacin ya nufo gida.
Ziyada
Gaba ɗaya ɗan yankewan da tayi ya ɗaga mata hankali, sosai yake mata zafi da zogi, fitowarta daga toilet kenan tana ta faman hura iskan bakinta adaidai saitin wajen data yanke, zama tayi akan gado, tare da jawo school bag ɗinta, gaba ɗaya zaman kaɗaici ya isheta sam batajin daɗin zaman da take yanzu burinta shine akoma makaranta. Tajima tana dudduba littatafanta kafun daga bisani bacci ɓarawo yayi awun gaba da ita.
_SOORAJ_
Yana dawowa daga masallaci direct ɗakinsa ya wuce, gaban Computer ɗinsa ya ƙarasa tare da soma lallatsata, koda ya kunna wayarsa kuwa saƙon gaisuwane da kuma na jaje waƴanda abokai da ƴan uwa suka tara masa suka dinga shigowa, bai tsaya wani duba saƙon ba yamaida wayar ya ajiye, har ƙarfe 11 yana kan computer. Aɗan gajiye yaƙarasa gaban fridge, bottle water ya ɗauko tare da ɓalle murfin, magungunan dake hanunsa ya watsa abakinsa tare da bin kansu da ruwa, long jeans ɗin jikinsa ya cire yasanya wani 3 guater, hanunsa yakai kan makunnin wutan ɗakin ya kashe take duhu ya mamaye gaba ɗaya ɗakin. Kan lafiyayyen gadonsa ya hau tare da danna makunnin bedside lamp, take wani ɗan haske dark blue yabayyana acikin ɗakin. Lumshe idanunsa yayi tare dajawo pillow yaɗaura kansa akai, wata ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya hanu ya shafi ƙasan maranshi, wanda yakejinsa aɗan kumbure, duk yanda zuciyarsa taso sanyashi dogon nazari yaƙi aminta da hakan, haka kuma yaƙi bawa brain ɗinsa daman yin tunani kamar yanda yasaba akoda yaushe, dayake acikin magungunan dayasha akwai maganin dayakesa bacci sosai, hakan yasa acikin mintuna kaɗan bacci ya ɗaukesa.
STORY CONTINUES BELOW
Washe Gari.
Tuni tatashi tayi sallan asuba, ɗan madaidaicin ƙur’aninta ta ɗauka tashiga tilawan aƙur’ani, dayake ana koya musu amakaranta shiyasa tamai da hankalinta sosai, tana kammalawa ta wuce toilet donyin wanka.
Ahankali ta buɗe ƙofar bathroom ɗin tare da sako kanta, duk dacewa tasan ita kaɗaice acikin ɗakin, amma hakanan take jin kunyan fitowa da towel ajikinta, kamar wata marar gaskia haka ta rakuɓo ta fito, zama tayi akan stull ɗin mirror tare da ɗaukan body lotion ɗinta tashiga shafawa, tana gamawa ta murza powder akan fuskarta, wani peach colour oil lipstick ta goga akan lips ɗinta wanda yaƙara bayyana asalin kalan lips ɗinnata, wata simple maroon colour Straight gown ta sanya ajikinta, duk da kasancewar rigan tana da ɗan faɗi amma hakan baihana hips ɗinta bayyana ba, ɗan kwalin rigan da yakasance tamkar gyale shita ɗauka ta yafa ajikinta, daidai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, da sauri ta waiga zuwa bakin ƙofan, idanunta ne ya sauƙa acikin na Ummu da sauri tayi ƙasa da kanta, tare daɗan durƙusawa, cike da ladabi tace da Ummu. “Ina kwana!” Fuska asake Ummu ta amsa mata da “Lafiya lau kin tashi kenan?”
Kanta ta kaɗa alamar “Eh”
“To biyoni mushiga kitchine saboda yau mu zamuyi aiki kafun masu aiki su ƙaraso”
Babu musu tabi bayan Ummu suka fito daga cikin ɗakin, direct tamfatsetsen kitchine ɗin dake cikin babban falon suka nufa, kitchine ne da aka ƙawatashi sosai tamkar wani haɗaɗɗen falo haka kitchine ɗin yake, komai na cikinsa light green and milk colour ne. gyaran su carrots da green beans Ummu ta bata, cikin mintuna ƙalilan ta kammala, haka ta ɗebo irish patatoes tashiga ferewa tana musu yankan chips, yayinda Ummu kuma ke kula da miyan egusin da zatayiwa Abba wanda zaici tuwo dashi, da taimakon Ummu Ziyada ta haɗa liver and garlic sauce, sannan ta soya chips, kasancewar Ummu tasan Sooraj daga fruits sai tea sune abincinsa yasanya dakanta ta haɗa masa fruit salad, Ziyada kuwa Ummu ne ta nuna mata yanda zata haɗa milk shake, haka kuma da taimakon Ummu ta samu tayi pepper soup ɗin cow meat, tuwon semo miyan egusi wanda yaji kifi Ummu tayiwa Abba tare da Coconut juice domin Abba baicika shan drinks ɗin company ba. Ziyada ce keta kai kawo tsakanin dinning area dakuma kitchine, tsab tagama jere duk abincin da sukayi akan dinning table, komawa kitchine ɗin tayi ta haɗa gaba ɗaya kwanukan da suka ɓata tasoma wankewa. Ummu naganinta taɗanyi murmushi tare da ƙarasowa gareta “Wannan ba aikin ki bane kibarshi idan masu aiki sunzo zasu ƙarasa” Ummu tafaɗa cike da kulawa.
Ɗan murmushi Ziyada tayi cike da jin nauyin Ummun tace “Ummu kibari nima zan iya!”
Murmushi Ummu tayi haɗe da cewa “To Naji, amma dai yanzu lokacin cin abincine muje maza” Babu yanda ta iya haka ta tsame hanunta acikin wanke wanken tabi bayan Ummu. Tanasanya ƙafarta acikin falon ƙamshin da ke matuƙar tafiya da imaninta wanda tasan mutum ɗaya ne tak me amfani dashi ya daki hancinta, lumshe idanunta tayi alokaci guda tare da buɗewa, ƙoƙarin gyara mayafinta take har suka iso dinning arean, idanunta ne suka sauƙa akanshi sanye yake da riga da wando farare, sosai yayi wani irin kyau, gashin dake kwance akan fuskarsa sai sheƙi yake, idanunsa nakan iphone 11 pro max ɗinsa da alama gaba ɗaya hankalinsa na kan wayan. Hakanan taji wani irin abu yashiga dukan ƙirjinta amma saita daure tayi ƙasa da kanta. Kujera Ummu taja ta zauna tare da cewa “Ziyada yi serving ɗinmu”
Jiki asanyaye haka Ziyada tashiga serving ɗinsu, ɗaukan glass bowl ɗin fruit salad ɗin da Ummu tace mata nashine tayi ta ajiye agabanshi, cikin sanyinta ta juya zata bar wajen.
“Ina kuma zaki?” muryan Ummu ya katseta.
“Uhumm dama ɗaki zankoma!” tafaɗa tana mai wasa da yatsun hanunta.
“Zauna idan kinci abinci saiki tafi ɗakin!” Ummu tafaɗi haka tana me jawo mata kujeran zama wacce take facing na Sooraj.
Sam musu ba al’adanta bane don haka kamar wacce aka cirewa laka ajiki haka ta zauna akan kujeran aɗaɗare, hanunta har rawa yake alokacin data soma serving kanta, chips ta ɗiba ɗan kalan acikin plate sai liver sauce shima kaɗan. Milk shake dinne dai tasanya har rabin cup. Abba da Ummu tuni sunfara cin abincinsu amma banda ita da Sooraj, ita kam wani iri haka takeji domin bata saba zama da manya ba, sam ita batasan wannan soyayyan ba, shikuwa Sooraj tunda yazauna ma bai ɗago kanshi ba screen ɗin wayarsa kawai yaketa shafawa, kamar wacce aka razana haka taɗauki fork tashiga tsakalan chips ɗin da ɗaya ɗaya tana kaiwa bakinta. Aƙalla yaɗauki sama da 10 minute yana latsa phone dinsa kafun ya ɗago, bowl din fruit salad ɗinsa yajawo ahankali yasanya spoon aciki, 2 spoon kawai yayi ya sake mayar dakansa ga wayarsa, Ummu gaba ɗaya tana lura dashi, duk da tasan cewa bayida yawan cin abinci, amma yanda yanzun yaƙi maida hankali yasha fruid salad ɗin yasanya taji ba dadi acikin ranta, cike da kulawa ta ƙira sunanshi “SOORAJ!”
Ahankali yaɗago kanshi ya kalleta batare dayace wani abuba.
Ɗan ɓata fuska Ummu tayi tare da cewa. “Kasan dai me Dr. yace akanka ko? saboda haka yanzu lokacine da zakaci abinci sosai, rashin cin abincin shine zaisa kadingajin kanka kamar baka da lafiya”
Ɗan yamutsa fuska yayi tare da kaɗa mata kansa alamar “Yaji”
Kansa yamaida ga bowl ɗin ya ɗeɓo fruid salad ɗin yakai bakinsa. Abba daya kammala cin tuwonsa ya ɗago yana goge hanunsa da tissue. Sam babu wanda yayi zato saijin muryarsa sukayi yace.
“Sooraj Ina magananmu ta tsaya?”
Dummmm haka Sooraj yaji gabansa yafaɗi, har acikin ransa yama manta da maganan da sukayi da Abban.
Shirun da yayi yasa Abba ci gaba da cewa. “Ayanzune zan matsamaka fiye da da akan maganan aurenka Sooraj, kaduba kai bakajin kunya ne ace har yanzu mahaifiyarka itace zata nunamaka abun daya dace? kula dakai ayanzu ba haƙƙin mahaifiyarka bane, yakamata ne ace kana da mata domin kulawa da irin waƴannan abubuwan, saboda haka ina mai tabbatar maka da tunkan nama abun dazaisa kaji babu daɗi ka nemo mata kakawomin ko acikin satinnan ne ni zan aura maka ita!” Cikin maganganun Abba gaba ɗaya babu wasa, yana gama faɗan haka ya miƙe tsaye yabar wajen. Gaba ɗaya tunanin Raj ne ya tsaya cak, sam baiyi tunanin Abbansa zai sake tada wannan maganan ba, musamman ma da yanzu bawai wani lafiyane ya isheshi ba, inama da Abba yasani dabaiyi maganan nan ba, domin kuwa gaba ɗaya ya sukurkutamasa tunani, duk wani ɗan annushuwan dayake ciki ya kau. 2
“Ina fata dai kaji abun da mahaifinka ya faɗa ma? kasan shi kakumasan abun da zai iya aikatawa saboda haka tunkan yazaɓama da kanshi kai kazaɓarwa kanka, don na tabbata wannan karon bazai maka da sauƙi ba!” Ummu tafaɗi haka itama tana me miƙewa tsaye, bata wani tsayaba tabi bayan mijinta, akabarsu su biyu akan dinning table ɗin. 2
Hakanan Ziyada taji murfin ƙirjinta na ƙoƙarin faɗawa.
“Aure akeso yayi?” ta tambayi kanta, sam bata wani fahimci inda kalaman Iyayen Sooraj ɗin suka dosa ba, amma kuma da dukkan alama aure sukeso yayi, tsintar kanta tayi da kasa cigaba da tauna chips ɗin dake bakinta sai kawai ta haɗiyeshi.
Shikuwa Sooraj hannayensa yasanya ya rufe fuskarsa da tafukan hanunsa, wani numfashi me ɗumi ya fesar ta bakinsa, wani irin dokawa ƙirjinsa keyi, sam bayason yaji anyi masa maganan da zata alaƙantasa da mace, bayajin zaiyi aure a irin wannan lokacin, bayamajin akwai wata wacce zata soshi ayanda yake, koda ma wata ta soshi shibabu soyayya atsarinsa, baisan menene so ba, baitaɓayi ba baisan yazai fara ba.
1
Sam bazata iya jure zaman wajenba, don haka saɗaf saɗaf tamiƙe tsaye tare da juyawa zata bar wajen.
“Waye sa’anki dazakibar masa ragowan dattinki anan?” 4
Husky voice ɗinsa yadaki dodon kunnenta wanda ya tilasta mata tsayawa, jikinta naɗan rawan tsoronsa ta juyo, plate ɗin data ci abinci tasoma ɗaukewa sannan ta haɗa dana su Ummu ta nufi kitchine, har yanzu bai sauƙe hannuwansa daga kan fuskarsa ba amma kuma komai take yana kallonta. Baitashi akan dinning arean ba harsaida ta tsabtace wajen ta goge, duk abun da takeyi atsorace takeyinsa, fatanta ɗaya kar tayi kuskure yayi mata masifa, tana tsaka da goge kan haɗaɗɗen royal table ɗin yatashi cikin tafiyarsa ta isa yanufi ɗakinsa. Tana ganin shigewarsa ɗaki, ta saki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, tare da share hawayen dasuka silalo daga cikin idanunta.