SOYAYYAR MU CHAPTER 1

SOYAYYAR MU CHAPTER 1

“Don’t be pushed around by the fears in your mind. Be led by the dreams in your heart” ◇◇◇◇◇◇◇◇◇ KATSINA STATE Ta iso qofar gidansu dake layin shagari avenue a cikin garin Katsina inda take ƙoƙarin sauke jakar ta ‘yar madaidaiciya ta tafiya (trolley) daga ‘yar ƙurƙurar da tayi shata tun daga tashar mota ta garin katsina inda ta sauka. Bayan ta biya shi kuɗin shi yayi gaba ne ta ja jakar ta nufi cikin gidansu. Tafe take cikin sauri domin cike take da kewar ‘yan gidan nasu. Sanye take cikin baqar jallabiya ta zamani qirar Dubai wadda ‘yan mata suke yayi.+ Takalmin da ke qafar ta mai tudu ne irin wanda ake kira wedge baqi sannan ta nada gyalen jallabiyar a kanta. Tana sanye da madubin ido a fuskar ta don kare rana. Maigadin su Malam Rabi’u shine ya dauko mata jakar ta har qofar falon su, ta karba tare da yi mishi godiya. Ko da tayi sallama ta shiga gidan babu kowa a falon don haka ne ta nufi dakin da ya kasance nasu ita da yayar ta. Shigan ta dakin ke da wuya ta tarar da yayar ta kwance a kan gado tana zubar da hawaye. Ta saki jakar dake hannunta ta ruga zuwa gareta tana tambayar ta “Ummi lafiya?” Ummu Salma ta taso da sauri tana qoqarin goge hawayen ta tare da fadin “a’a Aisha saukar yaushe? Ai nayi zaton kin fasa ne da na ji ki shiru tun dazu”. Aisha tace “Ummi kenan, mu bar wannan zancen ki fada mun me ya same ki kike ta kuka”. Salma ta gyara zama yayin da tace “babu komai Sis, idanuwa na ne suke mun ciwo”. Aisha ta haye bisa gadon tare da fadin “haba Ummi baki saba da irin wannan qaryan ba, don Allah gaya mun abinda ya same ki”. Salma dai fashewa tayi da kuka tare da kwanciya bisa cinyar Aisha tana fadin “ya cuce ni Aisha….. ya cuce ni….” Aisha cikin ruɗani take tambayar Salma “Ummi waye ya cuce ki?” cikin kuka Tace “Mubarak ne”. Dafe qirji Aisha tayi tare da fadin “Yaya Mubarak?? Me ya miki?” Cikin kuka Salma tace “kin san duk tsawon lokacin da muke tare ashe qarya yayi mun cewar shi ne mataimakin Manajan kamfanin da yake aiki ashe goge-goge yake yi, abin da ya fi bata mun rai shi ne idan har ya gaya mun gaskiya zai hana in so shi ne? A tunanin shi don matsayin shi zan so shi?? Wallahi Aisha da ya fada mun gaskiya da babu abin da zai hana in so shi tunda ai arziki na Allah ne kuma shi yake bayarwa ga dukkan wanda ya so kuma yake hana ma wanda ya so”. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta cigaba da fadin “Jiya Zuwaira ta zo domin ta shaida mun ta samu aiki shine ta tarar da mu a waje muna hira…. Bayan sun gaisa ne take tambayar shi yaya aikin shi wanda hakan ya tabbatar mun da lallai ta san shi. firgitar da yayi ce tasa na gane akwai wani abu. Bai iya amsawa ba sai yace mun bari ya ƙyale ni tunda nayi baquwa. Na raka shi bakin get duk hankalin shi a tashe. Bayan mun yi sallama ne na dawo cikin gida da sauri ina tambayan Zuwaira yadda ta san Mubarak. A bakin ta nake ji cewa ashe lokacin da ta je karbar takardar ta na fara aiki ta tarar da shi a bakin qofar ofishin daraktan kamfanin yana goge qasa (mopping) har yake shaida mata cewar zata dan jira domin daraktan bai iso ba. Ta dade zaune a wurin alhalin shi Mubarak din yana ta goge-gogen shi kuma suna dan taba hira jefi-jefi. A nan ne ya dinga bata labarin yanayin aikin nashi a kamfanin da irin ihsanin da mai kamfanin yake ma ma’aikatan shi gaba daya”. Salma ta cigaba da kuka tare da fadin “wallahi Aisha soyayyar da nake ma Mubarak ta tsakani da Allah ce amma kin ga yadda ya ɓullo mun”. Hankalin Aisha ya tashi matuƙa domin ta san yadda Ummi take masifar ƙaunar Mubarak. STORY CONTINUES BELOW  A nan ne ta dafa Salma tare da fadin “Ummi kiyi haƙuri, Allah ma ya taimaka an gano halin shi tun yanzu, tabbas yaya Mubarak bai kyauta ba kuma sai na je har kamfanin da yake aiki na zazzaga mishi rashin mutunci yadda nan gaba ko sa shi aka yi yayi ma wata abin da yayi miki wallahi ba zai yi ba”. Salma ta miƙe da sauri tare da fadin “a’a Aisha ki bar shi kawai na bar shi da Allah”. Aisha tayi murmushin takaici tare da fadin “haba Ummi, dadi na da ke sanyin zuciya. Ai yadda ya sa ki kuka haka sai na gaya masa baqaqen maganganun da har ya mutu bazai manta da su ba”. Kafin Salma ta sake yin magana ne Aisha ta canza hirar tare da tambayar ta “wai ina Umma ne? Nasan dai Abba yana Kasuwa” Salma tace “Umma ta tafi gidan Hajiya Maimuna tun dazu…” Aisha ta katse ta tare da fadin “shine kika shigo daki kina ta kuka kika bar qofar falo a bude? Idan wani ya shigo fa? Don ma dai anyi sa’a Baba Rabi’u yana nan” Salma tace “sis wallahi hankali na ne a tashe shiyasa” Aisha tace kiyi haquri Ummi, insha Allahu damuwan da Mubarak ya jefa ki will surely come to pass, ni dama saboda yaudaran da guys suke yi ma shiyasa bana kula su”. Salma ta ce “Aisha kenan, Allah ya kai mu ranar da soyayya zata yi miki mugun kamu” Aisha tace “Allah ya kiyaye Ummi, ai ni wanda zai sace zuciya ta sai ya shirya”. Salma tayi murmushi tare da fadin “okay ooo…” Aisha dai shafa cikin ta tayi tace “akwai abinci a gidan kuwa? Wallahi yunwa nake ji” Salma ta harare ta tare da fadin “see who is talking, kamar da gaske. Yanzu a zubo miki abinci ki ci cokali biyu ki ce ya ishe ki” Cikin dariya Aisha tace “Ummi na gyaru ai, baki ga har nayi qiba ba?” Salma ta sake hararar ta tace “qiba a hakan? Tashi ki shiga ki watsa ruwa ki yi sallah sai ki fito ki ci abincin” Ta miqe tana dariya tare da fadin “alright then”. *************** Bayan Aisha tayi wanka tayi sallah sai ta nufi falo cikin ƙananan kaya na wandon jeans da kaftan shirt wadda ta sauka har gwiwan qafar ta. Ta fito tana qoqarin daure gashinta da hair band wanda har ta iso wurin dinning bata samu ta daure gashin ba a dalilin zamewa da yake yi. Ta tarar da Salma tana ta shirya mata abinci kala kala akan tebir wanda har salman tana fadin “yau zan ga iyakar gyaruwan da like ikirarin kin yi” Aisha wadda take dariya tace “yanzun nan zan cinye abincin nan you will see, dan taimaka mun da gashin nan tukun” Ta miqa ma Salma hair band din. Salma ta karba tare da fadin “Aisha hoo…. ke kuwa har yau baki koyi daure gashin nan ba?” Cikin shagwaba ne tace “wallahi Ummi zamewa yake yi” Salma tayi dariya tace “ai gashin naki ne tabarkallah, ashe su Inna har yanzu suna nan suna fama….. na ma manta ban tambaye ki ba ya kika baro su?” Tace “suna nan, suna ma gaishe ku” Salma tace “muna amsawa”. Aisha tace “amma tare zamu koma ko? Yakamata ki je Kaduna ki yi mana kwana biyu” a daidai lokacin da ta gama daure mata gashin ne tace “i’m not sure gaskiya sis” Cikin shagwaba Aisha tace “haba Ummi gaskiya yakamata ki je, kin dan jima fa baki je ba” Salma tace “its okay zan yi tunani akai, yanzu dai zauna ki ci abincin in gani” Aisha tayi murmushi ta ja kujera kamar da gaske ta janyo filet da cokali ta zuba abinci daidai yawan yadda dan shekara biyar ke ci. Salma ta kalle ta baki a bude tana fadin “meye haka??” Tabe fuska tayi tace “abinci ne Ummi”. Salma ta fashe da dariya tare da fadin “lallai ma Aisha kina buqatar a fara zane ki, aikuwa shiyasa kullum kike qara komawa kamar ‘yar tsana” cikin shagwaba Aisha tace “idan na cinye ai zan qara” Salma tace “toh bisimillah” yayinda ta kafa mata ido. STORY CONTINUES BELOW  Aisha ta kai cokali na uku bakin ta ne suka ji sallaman Umma. Tsalle ta yi ta nufi wurin Umman da gudu tare da amsa sallaman tana fadin “Umma oyoyo sannu da zuwa” ta qanqame ta cikin murna. Umma cikin murnan ganin autar ta tace “a’a ‘yar gidan Abba saukan yaushe? Ai na zata sai gobe zaki taho da muka ji shiru” Tace ”Umma sai da muka je kasuwa ne tare da Inna sannan na taho”. Umma tace “yaya kika baro su? Suna nan lafiya?” tace “Lafiyan su qalau Umma duk suna gaishe ku. Kuma Inna tace in taho mata da kuka, dama ta ce wannan karon idan na manta sai ta zane ni”. Umma tayi dariya ta ce “ai ta ma dade bata zane ki ba sarkin qiriniya”. Gabadayan su suka fashe da dariya. Sun zauna a falo sun shiga hira ne Salma ta biyo Aisha da filet din abinci tace “gimbiya baki cinye abincin ba balle ki qara kamar yadda kika ce” zaro idanuwa Aisha tayi tare da fadin “wallahi Ummi na qoshi”. Cike da mamaki Salma tace “Aisha lafiyar ki kuwa? Umma kin ga ta fara ko? Yanzu fa ta zuba abincin nan kuma cokali uku ta ci, jin sallaman ki shine yanzu take fadin ta qoshi”. Umma tace “haba Aisha yanzu horon da Innar ki tace zata yi miki akan ki dinga cin abinci ashe baiyi tasiri ba?” Aisha tace” Umma kiyi haquri anjima zan ci da yawa” Salma tace “aikuwa yarinya baki isa ba, yau ko dure ne sai nayi miki” A haka suka sa ta a gaba ta cinye tana ta yi musu mita akan cewa cikin ta zai fashe. Umman wadda ta miqe domin shiga dakin ta tace “yarinya ko tsoron kada ulcer ta kama ki ba kya yi, Allah ya shirye ki”. *************** Gab da za’a kira sallan magrib ne su Aisha suka kammala abincin dare, suna jerawa kan tebir Abban su yayi sallama, cikin hanzari Aisha ta ajiye cokullan da ke hannun ta, a guje ta ruga tana fadin “Abba oyoyo…..” ta maqale a jikin shi kamar mage, ta karbi kayan dake hannun shi tare da fadin “Abba sannu da zuwa” Abba cikin farin cikin ganin autar shi yace “Aisha kenan har yanzu dai baki girma da shirme ba ko? Ya hanya? Ya kika baro su?” tana dariya tace “lafiya qalau Abba, suna gaishe ku” Yace “muna amsawa” Salma ta qaraso wurin su tayi ma Abba barka da dawowa. Abba yace “su Salma yau dai baki har kunne an ga Aisha” dariya suka yi gaba dayan su. Abba ya nufi hanyar dakin shi yayin da yake tambayan su “ina Umman ku take ne? Na ji ta shiru” Salma tace “tana dakinta” A lokacin ne Umma ta fito tana fadin “a’a Abban yara sannu da zuwa, ya kasuwa? Abba yace “Alhamdulillahi, bari in hanzarta in samu jam’i”. Umma ta ce “toh”. Ita ma dakin ta koma domin yin sallah, su Aisha ma bayan sun gama jera komai da komai bisa tebir suka nufi dakin su domin gabatar da sallah. ************ Suna kan tebir suna cin abinci Abba yake tambayar Aisha “ya mutanen kaduna? Kin baro su lafiya ko?” Aisha tace “lafiyan su qalau Abba” Yace “kin dai sanar musu kin iso lafiya ko?” Tace “eh Abba ina sauka tasha na kira su” Salma ce tace “Abba kalla plate din Aisha…” Abba ya kalli plate din cikin mamaki yace “Aisha har yau baki fara cin abinci kamar yadda kowa ke ci ba ko? Har yanzu kina nan da eating disorder dinnan ko? Wai me ke damun ki ne?” Umma tace “wallahi Abban yara wannan abu yana bani mamaki, na rasa gane me ke damun wannan yarinyan, gashi bata son cin abincin arziki sai kayan zaqi, duk da qwarewa da kika yi wurin girki sai dai ki dafa wasu su ci, Allah ya shirye ki” Aisha dai shiru tayi tana sauraron su. Abba ya cigaba da fadin “Ni wallahi gudu nake kada ulcer ta kama ta amma tunda likitoci sun bayyana mana lafiyan ta qalau shikenan ai” Umma tace “shiyasa ba kya qiba kullum kina nan kamar bulala” haka dai suka sa Aisha a gaba Salma tana ta yi mata dariya. Bayan sun kammala ne suka dan taba hira a falo sannan Salma da Aisha suka yi ma Umma da Abba sai da safe suka nufi dakin su. Bayan sun sauya kayan su zuwa na bacci ne suka hau gado. Anan ne Aisha tace “Ummi ina kula da ke ba kya walwalar kirki, dariyan da kike ta yi ma bata kai ciki ba, kina yi ne kawai don kada su Abba su fahimci abinda kike ciki. Please Ummi ki daina tunanin Mubarak Insha Allah zaki samu wanda ya fi shi”. Salma ta saki ajiyar zuciya tare da fadin “na gode sis”. Sun kwanta kenan Salma ta miqa hannun ta zata kashe wuta, Aisha ta riqo hannun ta tare da fadin “don Allah Ummi kada ki kashe wutan nan” Salma ta ce “shima duhun baki daina tsoron shi ba? Ba ga ni nan tare da ke ba? Kiyi addu’a kawai kiyi bacci kinji ‘yar qanwa ta?” Cikin sanyin murya Aisha tace “toh Ummi” Salma tana kashe wutan Aisha ta qanqame ta wanda har ta ba Salman dariya. Aisha tayi bacci da qudurin cewa washe gari zata je kamfanin da Mubarak yake aiki domin ta ci masa mutunci a dalilin yaudarar yayar ta da yayi. ◇◇◇◇◇◇◇◇ “Every instant of our lives is essentially irreplaceable: you must know this in order to concentrate on life” ◇◇◇◇◇◇◇◇ WACECE AISHA? Malam Abdullahi Usman mutumin garin qanqara ne a cikin jihar Katsina. Mahaifin sa Malam Usman ya rasu tun qanwarsa Hajara tana shekara bakwai a duniya.+ Mahaifiyar su Gwaggo Aisha ta cigaba da kula da su. Cikin ikon Allah Abdullahi yayi karatu zuwa sakandire inda ya samu sana’a ta hannu yana yi. Sana’ar ɗinki ita ya fara yi, a cikin sana’ar ne ya hadu da wani mutumin kirki mai suna malam Bello wanda yake bashi dinkuna masu yawa kuma yana jin daɗin dinkunan da yake mishi. Ta dalilin haka ne suka shaqu da har ya bashi shawaran mai zai hana ya dawo Kano inda suke sana’ar sayar da atamfofi domin sana’ar tana ci sosai. Ko da Abdullahi ya kawo ma Gwaggo shawarar sai ta amince da hakan domin sana’ar ɗinkin ta fara isar ta a dalilin basir da ya sa dan nata a gaba. Dayake Abdullahi mutumin kirki ne mai riqe gaskiya shi yasa al’amuran shi suka yi kyau. Malam Bello ya hada shi da maigidan su Alhaji Murtala wanda ya fuskanci kyawawan halayen sa cikin qanqanin lokaci. A dalilin haka ne har ya saka shi cikin wadanda yake aike qasashen waje irin su Dubai , China , India, Ghana, Cotonou da sauran su don siyo kaya. Abdullahi ya kasance mutum mai tattali a rayuwar shi, a dalilin haka ne cikin dan qanqanin lokaci dan albashin da yake samu yayi yawa. A cikin albashin ne yake ciyar da mahaifiyar shi tare da qanwar shi Hajara har ma yake biya mata kudin makaranta. Yana taho musu da kayan sawa babu laifi a kusan duk lokacin da zai je Katsina. Wata rana Maigidan shi Alhaji Murtala ya shaida masa cewa zai aike shi jahar Borno domin ya jagoranci shigowar wasu gyaluluwa da yayi oda. Abdullahi ya isa garin Maiduguri lafiya a inda ya shiga kasuwa domin gudanar da abinda ya kai shi garin. Bai ankara ba ya hango wata ‘yar kyakkyawar yarinya fara sol kamar tsada, tayi shiga ta alfarma tana qoqarin siyan awarwaro a wani shago dake tsallake daga inda yake tsaye. A nan take Abdullahi ya ji a ran shi lallai ya samu matar aure. Yayi sauri ya tsallako zuwa inda take yayi mata sallama ta amsa cikin natsuwa. Abdullahi ya gaishe ta tare da bayyana mata cewar ta birge shi ne shine yace bari ya zo su gaisa. Da yake Halima mai fara’a ce sai ta bayyana godiya a fili. Daga nan ne ya shaida mata sunan shi tare da gabatar mata da taqaitaccen tarihin shi da abinda ya kawo shi garin Maiduguri har yake ce mata “gashi ban ma gane shagon da nake nema ba, shagon wani Alhaji Idris dan Borno”. Halima ta kalle shi tana murmushi tace ni sunana “Halima Idris kuma wanda kake nema shine mahaifi na wato Alhaji Idris dan Borno”. Abdullahi ya saki ajiyar zuciya tare da fadin “Alhamdulillah, Allah ya taqaita mun wahala na hadu da Halimatus Sadiya diyar Alhaji Idris”. Gaba dayan su suka yi dariya. Halima ta yi ma Abdullahi jagora zuwa shagon mahaifinta Alhaji Idris, sun tarar da shi yana shirin fita ne Halima take gaya mishi cewa yayi baqo daga Kano. Anan ne Baban nata yake fadin “aikuwa na yi ta jiran shi na ji shiru”. Abdullahi ya gaishe shi tare da shaida mishi cewa shi ne wanda Alhaji Murtala ya aiko domin karbar kayan da yayi oda. Alhaji yayi ma Abdullahi barka da isowa yayin da suka shige shagon gaba daya….. A dalilin wannan tafiyar ne Abdullahi ya hadu da Halima wadda bayan ya dawo gida ne ya shirya komawa garin Maiduguri domin neman soyayyar ta wanda yake sa ran auran ta idan har ta amince da shi. Abdullahi bai samu matsala ba wurin amincewar Halima domin yarinya ce mai hankali da natsuwa kuma ta yaba da halin Abdullahi qwarai. Ba tare da bata lokaci ba Alahji idris ya amince da buqatan Abdullahi na son auran ‘yar sa wanda ya umurce shi da ya turo magabatan shi don a daidaita maganan aure. STORY CONTINUES BELOW  Babu laifi Abdullahi ya kashe kudi a bikin shi saboda dai dama auren ‘yan maiduguri sai ka dan girgiza. An sha biki lafiya aka kawo amarya garin Katsina gidan angon nata Abdullahi wanda ya kama haya a nan kusa da gidan mahaifiyar shi. Halima ta kasance mai kirki domin idan Abdullahi ya tafi kano kusan ma a ce a gidan Gwaggo take kwana har sai ya dawo. Ta shaqu da Gwaggo da Hajara sosai kuma ba qaramin taimakon Gwaggo take yi ba wurin ayyukan gida. Halima bata da son jiki ko alama, ga ladabi da biyayya ga tsafta, uwa uba kuma ga addini. Ba da jimawa ba Hajara ma tayi aure, ta auri Malam Aminu wanda shi lecturer ne a polytechnic na Kaduna. Tana zaune a can gidan ta a garin Kaduna. Da taimakon Alhaji Murtala ne Abdullahi ya bude shago nashi na kanshi a kasuwan cikin garin Katsina inda yayi fice a wurin sayar da atamfofi, shadodi, lessuka, jallabiyoyi, gyaluluwa da sauran su. Allah ya albarkaci kasuwancin nasa domin har ya gina dan madaidaicin gida sannan ya siya mota ‘yar madaidaiciya ta hawa. Gidan Abdullahi yana dauke da dakunan barci uku kowanne da kewayen shi da falo harda dinning a ciki, ga kicin harda store gwanin ban sha’awa. Ya kuma gyara ma Gwaggo gidanta tare da samo mata mai aiki wadda take tsabtace mata gidan. Bayan shekara biyu ne da auren Allah ya ba Halima haihuwa. Ta haifi yarinya mai kama da Abdullahi wadda ta ci suna Ummu Salma. Akwai lokacin da Alhaji Murtala ya so ya biya ma Abdullahi Makka amma shi Abdullahi ya nemi alfarma da ya biya ma Gwaggon shi. Bayan dawowar ta ba da jimawa ba Allah yayi mata rasuwa. Sun ji mutuwar gwaggon su amma kuma sanin cewa duk mai rai mamaci ne yasa suka rungumi qaddara tare da yi mata addu’a. Bayan shekaru uku da haihuwar Salma ne Halima ta sake haihuwar diya mace, amma wannan karon mai kama da ita ta haifo. Yarinyar ta ci sunan gwaggo wato Aisha. Daga nan kuma Allah bai sake basu haihuwa ba. Abdullahi ya hana a boye sunan Aisha don haka ne ake kiran ta da sunan ta. Ita Hajara Allah ya qaddara bata samu haihuwa ba. Da farko ta sa abun a ran ta har ta shawarci malam Aminu da ya qara aure amma yayi fafur yace ai baza su fidda rai ba, Allah mai bayarwa bai manta da su ba. A haka ne tun tana damuwa har tayi tawakkali Lokaci ya ja har su Salma da Aisha sun yi nisa a makarantan firamare, lokacin da Aisha take da shekara shidda ne Hajara ta samu ciki wanda ya bata wahala matuqa. Ta haifo dan ta kyakkyawa wanda aka sanya ma suna Zaid, daga shi Allah bai sake basu haihuwa ba. Salma yarinya ce mai haquri, natsuwa, da sanyin rai, ta kasance ko da jan ta fada aka yi bata ramawa wanda har yasa ake tunanin qila bata da qarfi ne. A bangaren Aisha kuwa abun ba haka yake ba, ita ta kasance mai tonon fada ga rashin haquri domin duk wanda ya mata laifi sai ta rama ko da kuwa an fi qarfin ta. Salma da Aisha sun shaqu sosai kuma Allah ya sanya suna da matuqar qoqari a boko da islamiyya. A dalilin haka ne suka yi fice a makarantar su yadda duk wata gasa da za’ayi a makarantar boko da islamiyya sai ka ga ‘ya’yan Malam Abdullahi Usman a ciki. Wannan ne yasa iyayensu suke alfahari da su tare da qoqarin biya musu dukkanin buqatun su na yau da kullum da rufin asirin da Allah yayi musu. Lokacin da Salma ta kammala firamare ta samu FGGC Bakori a inda ta tafi Boarding wato makarantar kwana. Ita kuma Aisha da ta gama FGC Kaduna ta samu inda ta wuce Kaduna amma ta zauna gidan Innan ta Hajara tana zuwa a matsayin day student wato ta jeka ka dawo. Makaranta ita tayi sanadiyar rabuwar Salma da Aisha, wannan ne yasa basu haduwa sai an yi hutu. A kwana a tashi babu wuya, bayan Salma ta kammala sakandire ne ta samu shiga State University ta Katsina inda ta karanci Computer Science. Ita kuma Aisha Kaduna State University ta shiga lokacin da ta gama nata karatun a FGC kaduna inda ta karanci Economics. Allah ya taimake su sun gama makaranta da qarancin shekaru. Ita Salma sai da ta kammala sakandire sannan ta sauke Al-Qur’an a dalilin zaman ta a makarantar kwana, ita kuwa Aisha dayake ta jeka ka dawo ta yi tun tana Aji uku (JS 3) ta sauke. STORY CONTINUES BELOW  A yanzu haka Salma tana koyarwa ne a wata makaranta dake kusa da gidan su wanda ita dama tun tana qarama burin ta kenan ta ga tana koyar da dalibai a matsayin malama. Salma yarinya ce Kyakkayawa, har yanzu kamaninta da mahaifin ta yana nan saidai ta dauko haske daga wurinn mahaifiyarta. Tana da kamun kai shiyasa duk da ba wani shekaru gareta ba ake ganin girman ta. A yanzu haka tana da shekaru Ashirin da uku a duniya. Salma da Mubarak sun yi shekara kusan daya da rabi kenan suna soyayya wadda Mubarak ya ruguza da kan shi a halin yanzu a dalilin qarya da yayi mata. A dayan bangaren kuma Aisha ta kasance yarinya marar jin magana da rashin haquri, abu daya yake birge mutane game da ita wanda ya sa ba’a ganin rashin jin nata, tana da bala’in qoqari, gaba daya tun da ta fara makaranta ita take na daya a ajin su, gashi dukda ba karatun komfuta tayi ba ta bala’in iya ta. Wannan ne yasa ake kiran ta “computer Guru” tun a makaranta, yanzu haka da first class ta fito daga jami’a. Aisha yarinya ce fara sol, domin ta fi kowa haske a gidan hatta Umman su da ta dauko hasken daga wurinta ta zarce ta. Kamannin ta daya da mahaifiyar ta, kyakkyawar gaske ga gashi baqi qirin mai tsantsin gaske dogo har gadon baya, kusan za’a iya cewa gashin har yayi mata yawa. Aisha ita ta dauko ainihin kamarnin mahaifiyar su gaba da baya. Har ta kammala makaranta ita ake ce ma “most Beautiful” saboda kyau. Tsiririya ce amma akwai qira (shape) mai kyau. Ita ba doguwa ba sannan kuma ba gajera ba. A tunanin mutane rashin qiban ta yana da nasaba da rashin son cin abinci (Allahu a’alamu). Aisha tun tana qarama tayi ma kayan qwalama sabo. Kullum bata rabuwa da kayan ciye ciye irin su chocolates, biscuits, ice cream, yoghurt da sauran su. Aisha ta bala’in iya girki, kalolin abinci babu wanda bata iya ba amma kuma sai dai ta dafa ma mutane su ci. A yanzu haka shekarun ta ashirin a duniya. A dalilin makaranta da tayi a kaduna ya sa ta shaqu da Innan ta Hajara sosai har ya zamanto a can take zama. Ita da Katsina sai dai hutu. Aisha ta shaqu da dan uwan ta Zaid wanda yanzu haka yana aji biyar (ss2) a Zamani College. Idan ka ga Aisha da Zaid suna hira sai ka rantse tsaran juna ne. Abin kallon su a koda yaushe shine Cartoon, ba yadda Inna bata yi da su akan su rage kallon cartoon ba amma inaa.. abun qara gaba ma yake yi.2 Aisha ta kasance bata son yin shiga irin ta hausawa, bata qaunar atamfa da makamantan su, a kullum zaka ganta da jallabiyya ne ko kuma dogayen riguna irin wadanda ‘yan matan zamani ke yayi. Gashin kanta baya kitsuwa don haka ne ko da ta je salon an wanke sai dai a daure shi, abu daya da har yanzu da girman ta tun tana qarama bata iya ba shine daure gashin nata da hair band, a cewar ta yana zamewa ne kuma yayi yawa (tubarkallah Aisha). A kullum masu taimaka mata wurin daure gashin sune Inna da Zaid, idan ta je Katsina kuma Umma da Salma. A duk lokacin da zata fita tana nade gyale dan karami a kan ta wanda tsayi da yawan gashin ta da take dunqulewa yake sa kanta yayi girma a cikin nadin. Idan kuma jallabiya ta sanya tana nade kanta da gyalen jallabiyar. Yawanci mutane waɗanda ba su san gashin ta ba suna mata kallon qaton kai gareta yayin da wasu suke tunanin a cuce maza ne. Aisha ba ma’abociyar kwalliya ba ce. Kullum zaka ga fuskar ta fayau amma fa duk da haka kallo daya za ka mata ka san lallai first class babe ce domin sai an tona za’a samo wadda ta kai ta kyau. Aisha bata qaunar samari a rayuwar ta, a cewar ta ba don Allah suke son ta ba sai don kyan ta. Burin ta namiji ya so ta don Allah ba don kyan ta ba ko wani abu na halittan jikinta (anya kuwa Aisha?? Hakan zai yi wuya domin dai kyan ki mai jan hankali ne). Aisha a rayuwar ta tana da tsoron duhu matuqa shiyasa tunda ta yi wayau bata kwana a daki ita daya. A gidan Inna ma tare da mai aikin gidan take kwana inda tana bisa gado yayinda mai aikin tana qasa bisa katifa. Aisha tana da saurin zubar da hawaye. Abun da bai kai ya kawo ba sai yasa ta zubar da hawaye, kai hatta Zaid idan ya ga dama sai ya sa Aisha kuka shiyasa ake kiran ta shagwababa. Qawayenta amintattu a Kaduna basu wuce biyu ba, Yusra da Fiddausi. Malam Aminu mahaifin zaid wanda suke kira Baba yana zaune ne a gidan shi da ke Bissau crescent dake unguwar Malali a nan garin Kaduna, har yanzu yana lecturing ne a polytechnic inda ya samu qarin girma sosai, don yanzu haka shine head of department. Yana da motar hawa qirar Honda Henessey. Tun Aisha tana KASU ne ya koya mata mota a dalilin emergency, lokacin da Zaid ya shiga babban aji a sakandire ne ta koya mishi shima. Yanzu haka Baba ya siyo musu Honda Civic ‘yar qarama wadda da ita Aisha take kai Zaid makaranta kuma ta dauko shi sannan kuma da ita suke zuwa kasuwa da sauran su. Ita kuwa Inna da ta gaji da zama ba sana’a ne tace ma yayan ta (watau baban su Aisha) ya dinga turo mata kaya tana sayarwa tunda sana’ar sayar da kaya biya biyu tana ci a garin Kaduna. Aikuwa nan da nan kasuwa ta bude, qawayen ta suna mata ciniki ba laifi musamman domin kayan da Abba yake turo mata masu kyau ne. Akwai wata rana da Baba yayi ma Aisha da Zaid alqawarin kai su Mr Biggs a dalilin Zaid yayi na daya a makaranta (abinda bai taba yi ba), a kan hanyar su ta dawowa ne tsautsayi ya gifta musu inda motar ta lalace musu a kan hanya. Baba yayi ‘yan dabarun da yake tunani amma motar ta qi tashi, gashi babu kanikawa a wurin. Baba ya kira bakaniken shi a waya amma wayar shi a kashe, ana cikin haka ne wata sabuwar mota baqa wuluk qirar toyota camry ta tsaya. Mamallakin motar ya fito cikin shiga ta alfarma. Sanye yake da farin yadi wanda daga ganin kwanciyar yadin a jikin shi ka san cewa ya ja kudi. Yayi ma Baba sallama cike da girmamawa tare da tambayan sa ko lafiya, Baba yayi mishi bayani tare da fadi mishi ‘yan dabarun da yayi. Aisha da Zaid suka gaishe shi, amsawar shi tayi daidai da saukan idanuwan shi akan fuskar Aisha. Ta lura da hakan shiyasa tayi sauri ta ja hannun Zaid suka koma mota zuciyar ta cike da tsanar irin kallon da mutumin yake yi mata. Mutumin yayi saurin dawo da hankalin shi zuwa ga Baba tare da sauke numfashi sannan ya nade hannun rigar shi ya fara gwada nashi dabarun. Mota dai bata tashi ba , da haka ne Baba ya yanke shawarar barin motar anan, suka kwashe kayan su dake cikin motar Baba ya rufe sannan suka koma motar mutumin wanda ya nemi ya mayar da su gida. Aisha dai bata so hakan ba a dalilin kallon da mutumin ya tsare ta da shi. Suna tafe a mota mutumin yana kallonta ta madubin gaba, tunda Aisha ta lura da hakan ne ta duqar da kanta tana ta latse latsen waya. Baba ne ya katse shi tare da cewa ” bawan Allah ya sunan ka?” yace “suna na Yusuf Abubakar” Baba yace “Madallah mun gode kaji, Allah ya saka” Yusuf yace babu komai Baba. Suna isa qofar gida ne Aisha tayi sauri ta bude marfin qofa ta shige get ba tare da waiwayowa ba. Zaid yayi ma Yusuf sallama ya kwashe kayan su shima ya bi bayan Aisha. Yusuf yayi ma Baba alqawarin dauko bakaniken shi sai su biyo su dauke shi a je a gyaro motar don bai kamata a bar ta a kan hanya ba. Baba yayi godiya tare da mamakin halin taimako irin na Yusuf. Nan da nan yusuf ya shiga ran Baba ya ji yana son shi. Tun daga wanann lokacin ne Yusuf ya saba da Baba, domin har gida yake zuwa yana gaishe shi, hatta Inna suna zama suyi ta hira a falo. Wadda yake zuwa domin ta dai tuni ta gano manufarshi, shi ya sa da yayi sallama take komawa daki. A dalilin nacin zuwan shi ne ta gudo Katsina don tayi sati biyu (Aisha kenan) ◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇ “Let today be the day you stop being haunted by the ghost of yesterday. Holding a grudge & harboring anger/resentment is poison to the soul. Get even with people…but not those who have hurt us, forget them, instead get even with those who have helped us” ◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇ CIGABAN LABARI Da safe bayan su Aisha sun gama breakfast, Abba ya wuce kasuwa yayinda Salma ta koma daki. Bayan Aisha ta taya mai aikin Umma sun gyara gidan tsab ne ta wuce daki don yin wanka domin zuwa wurin Mubarak. Ta taras da Salma kwance, idanuwan ta a rufe wanda ya tabbatar mata da ta koma bacci, don haka ne tayi shirin shiga wanka. Bayan ta fito ne ta zauna gaban madubi ta shafa mai a jikinta ta fesa deodorant da body spray sannan ta miqe ta nufi wadrobe ta fiddo jallabiyya baqa mai kyau. Bayan ta shirya tsab ne ta koma gaban madubi ta fesa turare sannan ta dauko hair band ta nufi falo wurin Umma domin ta taimaka mata, Umma tana ganin ta da hair band a hannu tace “bisimillah aiki ya gan mu”+ Tana dariya tace “Umma ku yi haquri zan koya sakawa da kaina kwanan nan” Umma tace “Allah ya baki iko mu huta”. Bayan Umma ta sanya mata ne ta koma daki ta janyo gyalen jallabiyar ta dawo gaban madubi ta nada shi a kanta. Nan da nan ta fito balarabiya sak, ta bala’in yin kyau dukda ba kwalliya tayi ba. Bayan ta dauki jakar ta ne ta sanya takalmi ta fito falo inda ta tarar da Umma tana ta kallon tashar african magic hausa. Ta zauna a kusa da Umma tace “Umma bari in je salon in dawo, gashi na yayi datti”. Umma tace “ai ke dama kullum gashin ki cikin datti yake” Aisha dai dariya tayi tare da miqewa tace “bari in je in dawo da wuri ma kafin a fara sophia the first” Umma tace “meye wannan?” tana dariya tace “Umma cartoon ne”. Umma ta riqe baki tayi salati sannan tace “Allah ya shirye ki”. Aisha dai ta wuce abin ta tana dariya. *************** Dakin taron (conference hall) a cike yake da manyan ma’aikatan kamfanin yayin da mamallakin kamfanin yake tsaye yana yi musu bayani akan shirye shiryen da yakamata ayi domin gabatar da Project din da ke gaban su. Wutan dakin taron a kashe take a dalilin na’urar projector da take kunne wadda da ita ne mamallakin kamfanin yake musu qarin bayani akan Project din. Aisha ta shigo kamfanin inda ta fara tsayawa wurin karbar baqi (reception) inda aka tambaye ta wanda tazo gani, bayan ta gaya musu ne aka yi bincike cikin komfuta aka gano wanda take nema da inda yake a daidai lokacin (a dalilin CCTV camera da ke kowanne lungu na kamfanin), Bayan anyi mata kwatancen inda zata gan shi ta tafi ne wadanda ke tsaye a wurin suke ta mamakin yadda aka yi hadadiyar babe irin Aisha ta zo neman cleaner. Aisha tana tafe yayin da take neman inda zata ga Mubarak, da ta kasa gano shi ne ta tsayar da wani ta tambaye shi ko ya san shi, wanda ta tambaya ne ya ce mata “ai kuwa yanzu na gan shi a sama zai kai files ofis din manaja” ta nemi kwatancen ofis din, mutumin yayi mata. Aisha ta haura sama inda aka yi mata kwatance, har ta wuce qofar dakin taron sai kuma ta dawo don ta duba ko Mubarak yana ciki. A daidai lokacin da ta bude qofar dai-dai mamallakin kamfanin yana cigaba da yin bayani akan muhimmancin Project din, Bata lura da yawan mutanen da ke zaune a dakin taron ba kawai ta afka ciki. Qamshin daddadan turaren da ya bugi hancin ta ne yasa tayi saurin tsayawa yayinda ta ga alamun mutum a gaban ta yana magana cikin harshen turancin da babu tantama idan ka ji zaka rantse bature ne yake yin shi. STORY CONTINUES BELOW  A lokacin ta ankara da projector din da ke aiki wanda ya tabbatar mata da cewa meeting ake yi. Jin mutum a bayan shi ne ya waigo da sauri yayin da ita kuma take qoqarin komawa da baya, bata ankara ba sai jin ta tayi ta tafi zata fadi, hannun ta ya riqo da sauri wanda a dai-dai lokacin ne aka kunna wutacen dakin taron. Hasken wutacen da ya gauraye dakin ne yasa tayi saurin rufe fuskan ta da dayan hanun ta. Ma’aikatan da ke zaune a dakin taron duk suka miqe tsaye suna mamakin abinda ke faruwa. Ba tare da kallon fuskar ta ba cikin fushi yace ma ma’aikatan “excuse me” ya ja hannunta suka fita daga dakin taron. Ofis dinshi ya haura da ita wanda har lokacin idanuwan ta a rufe suke saboda tsoro. Wurgin da ta ji anyi da ita ne yasa tayi saurin bude idanuwan ta. A tsorace ta kalli fuskar mutumin da ya wurga ta. “hasbunal lahu wani’imal wakeel” abinda Aisha tace a zuciyar ta kenan, bata taba ganin kyakkyawan guy irin wannan ba, gaba daya mazan da take gani a fili da cikin fina finai babu wanda ya kai kyan shi. Maganar shi ce ta dawo da ita hayyacin ta inda taji yana tambayan ta cikin fada “ke! Daga ina? Wa ya aiko ki? Me kike nema?” Hankalin Aisha a tashe tana qoqarin saita murya don bada amsa. Kafin tayi magana ya sake tambayan ta cikin fadan da ya fi na farko, nan da nan hawaye suka ciko a idanuwan ta. Ta sake qoqarin yin magana amma ta kasa. Daf da ita ya matso ran shi a bace yace “zaki amsa ni ko sai na sa an rufe mun ke a guard room?”. Anan ne hawayen da ke idanuwan ta suka fara gangarowa. Da qyar ta bude baki tace “Don Allah kayi haquri babu wanda ya aiko ni… asali ma na zo neman wani ne…” Ya katse ta tare da fadin “qarya kike”, tayi sauri tace “wa… wallahi da gaske nake”. Ya girgiza kai tare da qara murtuke fuska yace “look surareni da kyau, na riga na san irin ku. Sai ku zo da wata manufa a ran ku sai ku nuna ba haka bane a zahiri, wai tsaya ma, wa ya baki izinin shigowa dakin taron? Lafiyar ki kuwa? Idan taimako kike nema akwai charity Office meyasa baki je can ba? Meyasa kika zabi kiyi interrupting mun meeting? Kin san muhimmancin abinda nake tattaunawa da ma’aikata na? Ina mamakin daga wane gida kika fito saboda daga gani ba’a koya miki…..” Aisha ta dakatar da shi tare da fadin “malam ya isa haka, kada ka kuskura ka zage ni balle har ka sako iyaye na saboda ba matsalar ka ba ne”. Kallon ta yayi cike da mamaki da fushi. Aikuwa nan da nan ta ji ya hada ta da bango tare da fadin “ni kike daga ma murya?” Hankalin Aisha ya sake tashi, zuciyarta kuwa sai bugawa take yi. Da qyar ta qwace hannun ta wanda ya riƙe da qarfin gaske. Cikin kuka tace “an daga, me zaka yi?” Yana shirin yin magana ne tayi sauri ta ratsa ta gefen shi ta ruga a guje domin fita daga ofis din. Tayi nasarar fita yayinda ta bar shi tsaye yana mamakin yadda har ta isa ta fadi mishi magana son ranta wanda tun da ya fado duniya babu wanda ya taba yi mishi irin haka musamman ma mace da bata gaban shi. Bata natsu ba sai da ta gan ta a cikin ‘yar qurqura (keke napep), a lokacin ne ta duba hannun ta wanda yake ta mata zafi tun da ta fito daga kamfanin, hannun yayi ja a dalilin riqo da ya sha (abin ka da farar mace). A ran ta ne take fadin “ikon Allah abinda ya kai ni kamfanin nan daban abinda na tarar daban” tayi tsaki domin dai fitan ta ya zama a banza tunda bata samu tayi abinda ta je yi ba. *************** Ta shiga gida ta tarar da Umma da salma suna ta hira a falo, daga ganin fuskan Salma kasan ta riga ta fara fitar da Mubarak daga ran ta domin dai tana hira da Umma har tana dariya. Bayan sun yi mata barka da dawowa ne ta nufi hanyar dakin su har Umma na fadin “ina kuma zaki je bayan kin ce zaki kalli aljannun ki?” Aisha ta dan yi murmushi tace “Umma wallahi na dan gaji ne, anjima zan kalla” ta juya ta shige daki. Ganin haka ne Salma ta miqe ta bi bayan ta. Salma ta tarar da Aisha riqe da hannun ta yayin da take fadin “ga mutum har mutum amma kuma sai wulaqanci da ji-ji da kai” Salma ce ta katse ta tare da fadin “hajiya ke da wa kuma? Ina kika je?”. Aisha ta tabe baki tace ” Ummi Mubarak na je ci ma mutunci sai kuma reshe ya juye da mujiya ni aka ci mun mutuncin” cikin mamaki Salma tace “ban gane ba, me ya faru?”. Aisha ta janyo Salma ta zauna sannan ta bata labarin abinda ya faru daga farko har qarshe har ta nuna mata hannun ta da ya matse mata wanda yayi jajawur. Salma ta bude baki cike da mamaki ta ce “Aisha ba kya jin magana, wato sai da kika je neman Mubarak ko?, ni na haqura da shi ai na kuma bar shi da Allah. Kuma nasan dole in cire shi daga rai na in cigaba da rayuwata babu shi. Ban ji dadi ba a dalili na har an ji miki ciwo a hannu sis, i am so sorry” Salma ta janyo Aisha ta rungume ta tare da cewa “amma kuma fa kema kinyi mishi laifi, dadi na da ke baki da haquri wallahi. Kada ki qara kin ji?” Tace “toh Ummi, amma kuma wallahi Ummi ban taba ganin kyakkyawan namiji kaman shi ba, gayen ya hadu kamar aljani” Salma ta fashe da dariya tare da fadin toh ko gamo kika yi da aljanin?” Aisha ta zaro idanuwa a tsorace tace “haba Ummi ki daina bani tsoro mana” Salma cikin dariya tace “yi haquri sis, gashi kun yi fada da sai in ce qila an samo mana dream man din” Aisha ta miqe tare da bata rai tace “Allah ya tsare ni da mai zafin rai kamar shi, don kyau dai kyakyawa ne amma kuma mugu” Salma tayi dariya tace “Aisha kenan”. ************** Zaune yake a ofis dinshi yayinda ya daga kan shi sama idanuwan shi a rufe yana tunanin abinda ya faru tsakanin shi da yarinyar da ta bata mishi rai wadda bai san ko wacece ita ba. Bai Ankara ba ya ji an shafa fuskar shi daga ta baya. Idanuwan shi a rufe ya riƙe hannuwan ta tare da fadin “Anty Feena”, tayi murmushi tare da juya kujerar shi ya fuskance ta, ya bude idanuwan shi yana fadin “ya aka yi ne?” Ta kada kai ta ce “kai zan tambaya Mr Aliyu Muhammad Kankia wanda aka fi sani da babyn Ammi… what’s up??”. Yayi murmushi yace “don Allah Anty Feena ki bari.. ofis muke fa, idan ma’aikata na suka ji ki fa?” Tayi dariya tace “bani wuri in zauna, qarya na maka?” a kullum idan ta zo ofis din shi kan kujerar shi take zama. Ya miƙe da sauri ya bata wuri yayinda shi kuma ya janyo wata ya zauna yana fuskantar ta. Ta kalle shi ta ce “ya aka yi na ga kamar ranka a bace da har na shigo baka sani ba, wa ya taba mun kai?” Aliyu yace “wallahi Anty Feena wata yarinya ce mai qaton kai ta bata mun rai” Nan dai ya bata labarin abinda ya faru tsakanin shi da Aisha. Ji yayi kawai ta fashe da dariya tana fadin “yau wacce rana Babyn Ammi ya samu wadda ta mayar mishi da magana” Ran shi a bace yace “Anty feena dariya kike mun?” Tace “ba dole in maka dariya ba, ai na dade ina son in ga ranan da za’a samu macen da zata yi maka haka domin halin nan naka sai kai, ba don kai ba ne da na maka addu’a Allah ya baka irin ta a matsayin mata ko zamu samu ma ta gyara mana kai”. Yace “Allah ya kiyaye Anty Feena, macen da zan aura bata isa ta juya ni ba, infact ban ma da lokacin ta balle har in bata damar ta mun abinda taga dama.. trust me”. Nafisa ta girgiza kai tace “lallai ma Aliyu, har na tausaya ma matar ka wallahi tun ma ban gan ta ba. Muna nan dai muna sauraro a daina ruwan ido ayi a nemo mana ita”. Murmushi yayi yace “ai sai Mustapha yayi sannan zan fara tunanin yi” Zaro idanuwa tayi tace “what? Lallai Ammi must hear this, yakamata ta zane ka” suka fashe da dariya. ◇◇◇◇◇◇◇◇◇ Toh fa.. Aisha ta janyo rigima!! Aliyu has made an appearance… Interesting right???

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *