TAGWAYE
CHAPTER 11
Likita dafatan ‘Dan uwana zai warke, Doctor kadage iya bakin kokarinka domin kaceci ran Sambo shi kadei yaragemin ba’nida kowa bayansa.
Dawannan maganar Saminu ya ‘Karaso, nunfashi yake sama sama yana waiwaigawa ko zaiga Safeenah a wajen,. Se yanzu tadawo bayan fitowa datayi karban magani gun likita. Agogon hannunta taduba yanzu ‘karfe Hudu kenan ta asuba amma babu alamun chanji tattareda mijinta tun fadowar dare yake cikin yanayin Su’ma har izuwa yanzu, likitoci se aiki suke akansa tun zuwarsu, harma suka dena suna jiran iko gun ubangiji. Alokacinda aka kawosa asibiti, Safeenah ta’kira Saminu a waya tafad’a masa halinda suke ciki daganan yabi ya ra’zana ko kad’an bai bata lokaciba nan take yai urgent flight yazo Abuja a daren.
Se yanzu likita yatashi jikinsa duk tayi sanyi ya rasa wace irin suma Alhaji yai, duk dabarunsu na likitoci yayi amma babu motsi “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ iya abunda yafurta kenan sannan ya mike yana tafiya. “Meye kake nufi Bawan Allah taya zakabarmu a duhu?” Saminu yarike hannayensa duka biyu yasake Kunnuwa, baki harma da ido yana jiran amsarda likita zai basa.
I‘m sorry munyi iya Bakin kokarinmu amma har yanzu dei babu wani chanji Sedei mujira nanda awa biyu zuwa uku, idan yatashi toh falillahil hamdu idan Kuma bai tashiba dukkanmu musulmai ne kuma munsan ma’anar Ayar “Kullu nafsin Za’iqatul Maut”. Kallonsa Saminu yake Jugumm har tseda ya kammala maganarsa yatafi sannan yafara zubar da hawaye shima yabud’e kofa yafita.
Mutuwar tseye Maisha tayi alokacinda tahango likita yafitce daga dakin Asibiti cikin
damuwa tareda Kawu_Saminu duk alokaci daya, ‘This can’t be, Innalillahi wa Inna ileihi rajiun’ kwanon abincin dake hannunta tabarar, ta‘kama Salati tana hawaye masu tsananin zafi ‘Lailaha illahu Muhammadu Rasulil Lahi (S,A,W) Daddy I‘m sorry subucewa maganar
tayi Allah ma yasan ba’nida niyar bata maka rai kawai dei gaskiya nafada, Kwata kwata Ka dena kula da Mahaifiyata nikuma Momcy itace komai arayuwata bansan naga ranta yabaci, I’m so sorry Daddy I love you so much kar’ka tafi kabarni.
Ita kadei take magana tamkar mahaukaciya mutanen asibiti se kallonta suke, Bata kula kowa ba se ‘kara murya take hawaye suna zuba babu control “Ma’inah ” Tafada ahankali sannan tashare hawayen dake fuskarta nan take tachanza ido inda ta wainasu sama tareda turo Baki gefe, tasau’karda gira “A sanadiyar ki mahaifina yashiga wannan halin, yanzu haka rai a hannun Allah, Ma’inah I will not spare you, Wallahi you must pay. Ba’a shigan gonata a kwana lafiya Ni Maisha wuta ce mai balballa wacce ruwan banza bata kashani, Koda bangon duniya Daddy ya boyeki wallahi Maisha Ra’min kurege ce takan tone ko ina a duniya. ‘
Murmusawa tayi alaman wani tunani ne yazo mata sannan ta gyara gashin ‘kanta fuskarta cikeda fara’a yayinda tafara tafiya “Dear Twin Sis zamu hadu a office gobe kuma wallahi se kin gwammace sanina dakikayi a duniya Ma’inah Sambo Maidugu.”
Tafiya take ahankali a hankali tana tunani iri” iri, se murmushi take tana waina idanu, Hangan Mahaifiyarta datayi yasa tadawo cikin hayacinta dasauri ta’karaso inda take “Momcy lafiya meye yasa kike barin Daddy shi kadei Ina kuma Zaki? Tafada cikin nunfashi daya.
Ma’isha Daddy ya farfado yi maza ki’kira likita zankoma wajensa. Momy takatseta sannan takoma daki. Bata ‘kara cewa komaiba juyowa tai kurun babu inda ta tseya se ofishin likita.
,,,,,,,,,
Bayan ta idar da Sallan asuba tareda yin naflloli, ta ‘karanta Al Qurani mai girma Sannan tamike atsorace tabude tagar dakin tana lekowa, Shiru babu kowa awaje se yan Sanda masu Bakaken ‘kaya suna yawon gadin”Gidan sekace ta shugaban ‘kasa” Ma’inah tasa ke murza ido tana ganin d’akin datake ciki, mamaki take tayi tun shigowarta wai duk wannan makaken dakin na tane ita kadei ai ko dakin Mai martaba Sarki bazai’kai haka ba.
Sallamar Aunty Rahila ce tafidda ita daga cikin doguwar duniyar tunanin da tashige, A firgice ta amsa ‘Wslm Aunty Ina kwana“ “. Zaunawa tai har ‘kasa tana gaisheta ‘Kun tashi lafiya.
Murmusawa Aunty Rahila tayi cikin Fara’a tace Lapiya Lau yata, Jiya kawu Sambo
yafadamin cewa kina aiki a comfanin ‘Dana ma’ana ZMZ Builders. Ehh haka neh, Ma’inah ta gyada kai batareda tadaga ido takalle taba. Agogo Aunty Rahila tagani wanda yanuna ‘karfe shida da rabi “Ya kamata kiyi sauri kishirya nanda minti ashirin zuwa talatin Zaid zai fito kawai sekuje tare a motarsa….
A‘a Aunty ba komai. Ma’inah tai saurin katseta ‘Ba nasan in takura masa zanje Ni kadei Kuma…
Come on baby: Aunty Rahi tarike hannayenta. Wannan hanyarce kawai zata sanya
shakuwa tsakaninku amatsayin Yaya da ‘Kanwa please don’t say No. Alryt Fine if you say so. Tai murmushin karfin hali sannan ta’kara da hadiye miyau tana tuna wulakancinda Zaid
yai mata a office. ‘
Excuse me ma’am your breakfast is ready.Ma’aikaciyar gidan ce tai sallama tashigo “My name is Qun_Shuin_in your new Maid. Matar ta durkusa gaban Ma’inah tana gaisheta da yaren Chinese wanda ko kadan bata gane abunda take nufi “Zaoshang hao”. Nihao_ma,Aunty Rahila ta amsa mata, daga Nan bata bata lokaciba, dasauri tamike
” Wo_hen_hau” Sannan tafita.
Yar China ce sabuwar mai kula dake dana kawo ta musamman daga Beijing zata ringa koyamiki yaren ahankali ahankali Zaki iya. Gyada Kai Ma’inah tai; Na’gode sosai.
Bakomai, Xiexie Aunty Rahila tafada tana murmushi bari mufara koya daga yanzu, Xiexie na nufin Thank you da yaren chaniese. Murmushin Ma’inah ta maido mata sannan tace XieXie Aunty Rahila.Shafa mata ‘kai tayi sannan tafita. Nan ne Ma’inah tai sauri tashirya cikin Pitch Colour Abaya and Veil wanda sukayi dedei ajikinta tamkar domin ita aka halicci kayan.
,,,,,,,,
Wata shegiyar dariya Maisha tai “Shege mutumina kace ‘Dan mazga shima ya shiga kungiya. Mutumin dasuke wayan ne ya amsa mata “Ahh shima dei Daman dei kawai ruwan kwalba ce Bata isheshi ba Banza hahaha huuhuhu.
“Toh ‘Dan baba nidei kawai ku tabbata kun aikatamin abunda nafada kuma ko ina kumanna hotunanta da sunanta kununawajama’a cewa ita ta aikoku domin ku dau fansa kan cin zarafin da Zaid yai mata alokacinda ya zargeta da Yar Shaye shaye Kuma Yar iska.
Ke dallah dakata wannan pa aikin pa dakika bamu akwai wahala ba kadanba sabida idan anyi mana red handed zamusha ‘kashi Kuma kamaryadda nafada miki abaya 2 million
chap muke bukata kituro Mana yanzu yanzu nan idan lokaci yayi kawai zakiga aiki da
cikawa. Murmushi Maisha tai” Dan baba kafi kowa sani Ni Ma’isha Sambo Maidugu kud’i Basu dameniba yanzu zakaji dumus Alert zasu shiga wayarka 2 million naira ka tabbata kunyi aiki da kyau.
Wannan hotonda kika turomin shine dei kadei Wanda kikace kada mu taba Koh. Shi ne, Ma‘isha ta amsa “Zaid Muhammad Zabir kenan karku tabamin shi he is my future husband Insha Allah, Idan kun aikatamin abunda na umarceku dedei na tabbata zai yiwa Ma’inah korar kare daga comfaninsa kuma aika ta prison zaiyi kaga daganan ta fita rayuwarmu babu inda zata sake haduwa dashi kawai se muyi aure dashi hankali a kwance.
Dariyar mugunta Dan baba yayi ‘Shegiya Yar Sambo inayinki wallahi, Maisha Y’ar Alhaji Sambo dakuma Alhajiya Safeenah Sambo. An ‘kara maka million daya mutumina.
Wayyo Allah kice nazama mai kudi million Uku kenan. Ehh Mana, Ma’isha ta amsa ‘Million ukun tafi karfina ne’. A’a hajiya zakiga aiki kuwa da cikawa. Anan Maisha ta katse wayar tafara tunanin yedda zata samo million Uku wajen Daddy wanda yanzu yadawo daga asibiti ko hutawa bayyiba bare yasaurari damuwarta.
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, Ahankali ahankali take tura chokali abakinta tana ci zuciyarta na bugawa, taya zata fara shiga motar Zaid “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun ya Allah ka rabani da wannan Bawan naka Zaid’ Tafad’a abayyane inda yai dedei da shigowar Zaid falon ‘Na’am ya amsa ba tareda yaga ko wacece ta ambaci sunan saba, Aiko Yana daga Ido Ma’inah kadei ce yagani afalon babu kowa, wata dan guntun tsaki yaja ‘I can’t imagine she is always thinking about me’ yafada cikin murya wacce ya tabbata bazataji abunda yake fadi ba.
Kunya kamar ‘kasa ta tone tashige rasa abun fad’a tai cikin borin kunya tace; Aunty Rahila ce ke ‘kiranka tana daki. Bai tankamataba kai tsaye yanufo dakin Aunty Rahi, inda adedei kofa sukayi Kacibus. Rungumeshi tai tanacewa ‘ Tafiya zakuyi, toh ka kulamin da kanka dakuma Yar uwarka kaji, Yarka fa?
Ta tafi school ya amsa Kai tseye sannan yai hanyan waje. Ma’inah tashi kibishi man, Ina Qun_shuin_in seki ‘kirata ta dauko miki jaka, My dear you should wait for her outside zaku tafi tare.
What? Mamy why. Ya tseya chak tamkar controlling d’insa akeyi “Mamy I don’t want to go with her, d’aga ldo yai yakalleta sama da ‘kasa ” this thing no, no way”….
Shiru Ma’inah tai tana kallonsa haushi kamar tasha’keshi tahuta. Mamy I’m sorry. Iya bunda yafad’a kenan sannan yafice. Doguwar nunfashi Aunty Rahila ta saukar inda tajuya bangaren Ma’inah tanacewa “Don’t take it the wrong way my dear babu komai kije kisameshi na tabbata Yana nan yanajiranki a waje.
,,,,,,,,,,,
Babu sallama yafado musu cikin d’aki kamar daga sama “Safeenah kibamu wuri inaso mutattauna da dan uwana. Ahankali Daddy yami’ke yayinda Safeenah tai waje kamar yedda aka umarceta. Gyara murya Sambo yai “Zan koma Maiduguri an jima kadan, zuwa nayi musamman domin kaci‘kamin alkhawarin da ka dauka na kudi naira Million biyarda dubu dari da saba’in ma’ana kudin jinyar Y’ata Miemah. Da murya irinta marasa lafiya
Daddy yace bakomai already na shirya maka kudaden kuma zanyi transfer ta account dinka, Allah kuma yabata lafiya. “
Amin’ Saminu yahada da murmushi sannan ya mike. yana fita sukayi karo da Maisha yayinda take kokarin shigowa “lsha ya kike baki ganeni bane, Kawun kine Saminu”. I don’t care “Tabugamasa harara, u don‘t even exist to me, you are so old_Fashion I mean you are Useless. Murza masa baki tai taja kofa da sallama ta’karaso ciki “Daddy yajikin naka? Alhmdulillah. Ya amsa kai tseye inda yake kokarin share hawayenda suke gangarowa a fuskarsa.
Daddy kudi nake bukata Million Uku chip! Kuma ina matukar bukatarsu yanzu yanzun nan please Daddy you never say no to me.
Sunkuyawa tai har ‘kasa tafara zubar da hawaye wanda turawa suke ‘kira Crocodile tears “Daddy ba’nida kudi a hunnuna Kuma….
Maisha will you please shake it off, Daddy yadakatar da ita “Meye zakiyi da million uku awannan karancin shekarun naki, please just get out bazaki samu ko sisi awajenaba Sedei kawai idanda abunda kike bukata zaki iya fada and I promise… Excuse me & Hannu ta daga masa cikin sananin bacin rai tace’ Daddy please you don’t have to explain, ya Isa haka ba’nason jin wata ‘karin bayani daga wajenka because it’s clear you really hate me ka tsaneni.
Kalmar ka tsaneni ta maimai ta harsau Uku sannan tami’ke tana hawaye bata ‘kara furta masa komai ba bankado kofa tai tabarmasa dakin.
‘Dakinta tawuce cikin tsananin tunanin shin “wace hanya zatabi ta’samo million uku domin ci’kawa ‘Dan baba alkawarinda tadauko masa.”
,,,,,,,,,
Ko kadan batayi tunanin ganin motarsa a tseye har zuwa wannan lokacinba, sekuma
gatanan motar tana tseye alamun ita yake jira “So Mamy really knows her son isn’t she” Wani farin ciki taji azuciyarta wacce ita kanta
batasan dalilin hakanba. Tana taku daya daya hartseda takai wajen inda tasa Hannu babu tsoro tabude kofar gaba, ai kuwa shigewa tai tamkar Uwar gida tazauna gwanin sha’awa.
Dakansa yake tuki, tana shiga ya’tada motar inda yasa kira’an sheik Sudaiz suratul Nisa’i yanabi. Shiru Ma’inah tazauna se kallonsa take a mirror tana mamakin kyaun hallitanda
Allah yabashi. Basuyi tafiya Mai nisaba yai parking adedei gefen hanya.