TAGWAYE
CHAPTER 20
Tashin hankali da damuwa ce sosai take bayyane a fiskokinsu yayinda suke bin gadon asibiti wanda likitoci suke turin Ma’inah suna kaita Emergency room. Jini ne sosai take fita a jikinta harma da ba’ki dukjinin ne take bulbulla har sanda aka sanya mata goran nunfashi tin suna waje (oxygen) wandake taimakamata tana nunfasawa dakyar dakyar. Zaid ne a gaba yana rike da hannayenta cikin tsananin damuwa yanakuma zubar da zafaffan hawaye tareda tinani iri iri aransa, Anisa, Aunty Rahila da Aunty Nasibah suma duk cikin damuwan suke suna kuka.
Aunty Rahila kam tunanin yedda zata fad’awa Mahaifiyar Mainah take tin tuni, k0 wa yasan halin Safeenah ba’tada sassauci ko kad’an, zata iya cewa rashin kulawa ce tai sanadiyar hakan, kuma meyesa babu wacce aka harba a gidan sai Yarta “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ iya abunda Rahila take ambatowa kenan tareda Salati.
Adedei kofar dakin aka tsai dasu duka, saida Zaid yayi iya ba’kin kokarinsa akabarsa suka shigo tare, ya’kasa barin gefenta, rike hannun damarta yai gam!!! yana hawaye ” Mainah please forgive me, I’m sorry” iya abinda ba’kinsa yake iya ambatowa kenan. Nan da nan likitoci suka fara aiki akanta cire mata bullet sukayi afarko sannan suka rufe wajen da bandeji, Saida sukayi gwaje gwaje da dama sannan suka nunawa Zaid hannu cewa ya masu masa bayani.
Dakyar akasa ya saki hannayenta yami’ke cikin sanyinjiki suka fito, Suna fita sauran jama’an gida suka taho aguje suma suna tambayan likitan abundake faruwa.
Yaja Doguwar nunfashi sannan yace’ Akira Parents dinta domin susa hannu atakarda za’a mata surgery akwai internal bleeding,jini ya taru a cikinta sosai.
“Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ suka fada alokaci d’aya. Faduwa Zaid yai, yazauna kan guiwowinsa yana kuka “This is all my fault, Mainah I should have protect you sabida tinda nafara sanyaki cikin idaniyata sanki tashigemin zuciya amma sai nabiyewa san zuciyata da girman Kai irin tawa na’kasa fadamiki. Kansa yafara bugawa akasa yanacewa” Zaid why? Meyesa katafi kabarta? meyesa baka taimaka mataba?
A wannan lokacin Zaid yafice daga cikin hankalinsa gaba daya domin yafisu duka kuka da damuwa. Securities d’insa ne suka taho, Kai tsaye suka rike shi hannu bibbiyu suka sa shi a kujera suna masa fifita.
Anan ne Aunty Rahila ta mike, jikinta na rawa yayinda tasa layin momy a wayarta tana ‘kokarin ‘kira, babu gardaman network, ‘kiran ta shiga kai tseye, amma ta’kira layin har‘a tsinke babu amsa sake gwada layin tai tana kaiwa da kawowa tanakuma Allah, Allah tadauki wayan Amma still tsinkewa tai “no answer”.
Alokacin Zaid yamike aguje babu wanda yama magana, yaja Key’n motarsa alamun gidansu Ma’inah yanufa, babu bata lokaci securities d’insa suka biyoshi abaya suma suna gud’u iya karfunsu sunabin ogan nasu abaya.
Gidan Sambo Maidugu tashi take da kida tin awaje zakaji sautin tana tashi sosai, idan kashigo kuwa ko ina Pess kake gani decorations a ko ta ina tana walkiya, Ba’ki sun cika gidan sosai ana taka rawa da nishad’in taya Maisha murnar zagayan shekara (Birthday).
‘Mommy tana nan busy da manya manyan bakinta, ta‘kumasa a shirya Mata wajen taronsu na office cikin sirri domin achan za’a Sha shagalin zagayen shekaran Ma’inah gobe da yardan Allah
Mommy tana nan busy da manya manyan ba’kinta, ta’kumasa a shirya Mata wajen taronsu na office cikin sirri domin achan za’a Sha shagalin zagayen shekaran Ma’inah gobe da yardan Allah. Doguwar ‘Bakar Riga Maisha ta sany’a masu tsananin Kyau wacce momy ta sayo musamman kimanin dubu d’ari uku. Maisha ta gayyaci abokanan ta dasu saratu, Maijidda da sauransu kowa yataho da gifts dinsa. Su Ma’isha ko yau ansha kyau, Kwalliya aka mata sosai Wanda sukayi dedei da kekkyawar fiskarta.
Momy tana matukarji da diyarta hannunta ta rike suna zagayowa cikin jama‘a tana gabatar da ita ” Yata Maisha Samba Maidugu ta taso a ‘kasar Amurka achan tai karatu kamin mudawo tacigaba har zuwa masters, ayanzu tana a aiki a confanin ZMZ Bulders as Abuja Housing Interior Decorations Manager. Ahaka momy tacigaba da introducing Maisha ga bakinta, kowa na yabon kyaun ta dakuma nitsuwarta.
Se yanzu Zaid ya iso gidan Alh Sambo Maidugu, sautin kidan da yaji yana ta’shi cikin gidan ne yaba‘sa mamaki. Kai tseye yadanna horn aka bud’e masa gate ya’karaso ciki anan wajen yai parking yayinda securities d’insa suka tsaye tin awaje. Dasauri yafito yana tafiya, kowa se kallonsa yake sunata surutai, daga Mai cewa” Laaa! ga ZMZ CEO, se mai fadan” Ga CEO Turai Mafiya ‘a Air, Kunaganin Gayen nan kunga haduwa, Kunga motarsa, Ohhh! gosh look at his Sexy eyes,. Kowa dei da abinda yake fad’i, Matan se wani shiga yanayin birgewa suke sabida yai musu magana shiko kwata kwata bai masan sunayi ba kai tseye yanufo babbar Falo anan yaga ta’ron mata suna ta’ka rawa wasunsu suna cin abinci dadei sauransu Zaid ya rasa yedda zai shigo ciki tsayawa yai anan yatabe baki yanakuma lekowa ko zaiga Maisha ko Mommy aciki.
Alokacin Maisha ta debowa momcy abinci zata kai mata a daki kenan tahango wani had’edd’en saurayi a ba’kin kofa, Saida ta gyara ldo sosai ta’kara lekowa, nan tagane Zaid Muhammad Zabir ne kamar yedda zuciyarta ta raya mata. “wow! Yasha Kyau” Abincin ta
Barar, ta zube duk ta watse a kasa, ana mata magana amma bata sauraresuba, kai tseye
tafito babu tsoro ta rungumeshi “Boss ashe ka duba text din nawa, wallahi ban taba
tunanin zaka karbi gayyata taba, duk dashike tinda akafara wannan ta’ron shigowarka
kawai nakejira, I’m so glad you came thank you so much boss you are the best.Ya ‘kasa gane abunda take nufl, baimasan yau ce ranar haihuwar suba, bare yakaiga sanin ta turomasa text tana gayyatarsa Party. Ja da baya yai yayinda yaturo d’an karamin bakinsa Yana binta da kallo cikin yanayin ko inkula yace” Ina mahaiflyarku? Ma’inah is in critical condition a asibiti za’ayi mata surgery kiyi sauri ki ‘kirata zamuje tasa hannu domun aimata aikin da gaggawa. Zaid yafada cikin nunfashi d’aya.
Share maganar dayai Maisha tai kamar bataji abinda yake fad’i ba, ta rike hannayensa tanacewa” Get in Sir, na tanadamaka kujera ta mussaman da kayan abinci duk na musamman wanda na tabbata zakaji dad’inta Sosai.
Hannunsa ya kifto kai tsaye ayayinda yake binta da kallo cikin mamaki yace” Maisha cewa nai Yar uwarki tana asibiti an harbeta …..
Bai karasa kalaman saba tai saurin katseshi” Ayau ranar haihuwartawa ma sai ka bakantamin, this is my day Zaid kadena ambaton sunan Ma’inah don darajar Annabi, wallahi wallahi Wallahi, ka fita mahimmanci a rayuwata sau dubu, Zaid you are much more important to me than Mainah a…. Bata ‘kaiga karshen maganar taba Zaid yasa hannu ransa abace ya sha’reta da mari afuska daman haushinta yakeji tun ranarda taiwa Ma‘inah rauni “watch your tongue Maisha Sambo Maidugu. Da wannan maganar yajuye yana faman tafiya tai sauri tashige gabansa, tsayawa yai chak! yana jiran abunda zata fad’a, Ba’kinta ta’soma a tasa Gam! Tarikeshi tana sunbatarsa, Dakyar Zaid yasa dikkanin karfinsa ya tureta inda tafadi a kasa shiko yajuya haushi kamar zata kasheshi yafara tafiya yayinda yacire hankerchif dinsa yana share bakinsa tareda da’nasanin zuwa gidan dayai tun a farko.
Jama’a sun taru a wajen sosai duk wannan abubuwnda agabansu tafaru, Maisha tana kwance a kasa tanabinsa da kallo har Sanda ya bacemata tafara dariya da ‘kan tace’ This is the best birthday gift ever my future husband Zaid Muhammad Zabir, Da haka tamike ko ajikinta tai Falo.
Tinda ya iso asibiti ya’kasa magana sai wani shashshare bakinsa dayake yana bata fiska, dakansa yai signing takardan aikin inda babu bata lokaci aka shigar da Mainah dakin surgery tareda likitoci da dama daga turawa, larabawa har zuwa Bakaken. Wash room Zaid yashige daman tun a hanya ya sayo brush anan ya ringa goge hakoransa yana da’nasani tareda bacin rai da sananin ba’kin ciki, yana kammalawa, yakurewa kekkyawar fuskarsa ldo a madubi anan hawaye suka fara zuba a idanuwarsa “I,m So sorry Ma’inah ki gafarceni.
Kudaden data tara a banki duk ta kwaso su, inda kai tseye ta biya Lawyarta dakuma kudin filing case a kotu, bayan wannan wayar data tsinta babu wata evidence d’in datake dashi duk dacewa Umma ta tabbatar mata cewa Ma’isha ce ta turo mutanen ta gidansu batada kwakwaran shedunda zata gaskanta hakan a gaban kotu.
Ata bangaren Ya’ran Maisha kuwa daman zuwa Maiduguri sukayi mussaman domin su
daura dukkannin shedunda zata tabbatar wa yan Sanda cewa Saminu shi yakashe Lawan
Mai gadi sukazo yi. Labari ta isosu cewa Yar Saminu ta kai ‘kara kotu kuma tanada shedu na musamman wacce zata tabbatarwa Yan Sanda cewa Mahaifinta bashida hannu wajen
‘kisan Lawan. Wannan yasa mutanen Maisha suka koma gidan Saminu inda duk suka
bincika inda wayarsu datafad’i basu ganta ba, hakan ya tabbarmusu cewa wayar ce Miemah ta tsinta Kuma ita take Shirin bayyawa agaban kotu idan Kuma ta bayyanata amasayin shedu kotu zata iya gane gaskiya sabida akwai text messages d’insu da dama cikin wayar.
Ofishin MTN suka nufa inda suka bada kudi aka chanza musu sunan wanda yai registering layin takoma sunan Saminu Maidugu sabida dazaran kotu ta binciko sunan Mai layin taga sunan Saminu babu wata bincikenda zasu d’aura akai Kai tseye za’a kaisu gidan Yari ko sunaso ko basa so. Wannan itace ta’kunsu na farko,ta biyun Kuma; Wuka mai tsananin kaifl suka samu inda suka yanka dabba da ita sabida kawaijini yatabajikin wukan. domin su ijiye wukan acikin kayansa sabida idan yan Sanda sun binciko sugano ta awajen wanda hakan ne zata tabbatar musu cewa Saminu is a real criminal.
Duk dabarun da Miemah take domin tasa mu hanyan shigowa gidansu tai bincike bata samo dama ba tinda tazo Maiduguri sai yau,yayinda polisawan dake ga’din gidan duk suka tafi, iya securities gudu biyu aka bari a kofan gidan. Miemah tai dabarunta tashige har cikin gida, ahankali take leke leke kuma atsorace tana zuwa ba’kin kofan d’akin Mahaifinta taji hayaniya nan da nan ta tsaya chak tasa kunne tana sauraronsu “Baba kai sauri man kar azo ai mana red handed, “Kai dan yayyafa jinin cikin kayannasa sosai se ka d’aura wukan cikin kayan.
Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Miemah ta’kara lekowa tana binsu da kallo cikin tsananin damuwa ta‘kai layin ‘dan Sanda wanda ta’kai karar awajensa bugu daya ya daga “Kuyi sauri kutaho gidanmu akwai wasu mutanenda sukazo kuma ga dukkan alamu sunada hannu wajen ‘kisan Lawan. Da wannan Miemah ta katseta wayarta, Aiko tana juyowa taji Sanda, an bige kanta, ihu ta rapka ayayinda takama ‘kan nata tanagudu tanakuma ihu. Wannan ihun datake yasa securities d’inda suke gadi awaje suka ‘karaso. Nan da nan yan Sandanda taiwa waya suka taho kamar daga sama, kai tseye akasasu a mota dukkaninsu babu wacce akabari direct police station aka tafi dasu, a yanzu Bibbiyu Miemah take gani, kanta na bala’in juwaya tana ciwo, ahaka har suka karaso saidei tana matukar farin cikin kamosu datayi cikin ikon Allah, kuma gobe da yardan Allah iyayenta zasu bayyana agaban kotu, wannan wahalhalun duk zasu ‘kare and they will finally be free zamu koma gida cikin kwanciyar hankali mucigaba da rayuwarmu.
A ranar dei babu wani matakinda aka d’auka akan mutanen dashike gobe da yardan Allah zasuyi zaman kotu duk hukuncin da alkali ya d’aura akansu shine dedai.
Miemah ta’kira Lawyarta a daren ya taho inda akabasu kebebben waje cikin police station din domin suyi magana a sirrance. Dariya tasaka “Attorney gobe da yardan Allah zamuyi winning case a kotu Sabida dukkanin shedunda muke bukata tana hannunmu toh ya kagani. ’
Murmusawa lawyan yai, ayayinda yabata hannu kai tsaye yanacewa” I also feel thesame way Miemah congratulations we won. Babu bata lokaci Miemah tasa hannu sukayi shaking. “Amma Miemah kin tabbata iyayenki zasu bayyana gobe? Attorney ya tambayeta kai tseye. Gyada Kai tai “Kar‘ka samu damuwa Attorney gobe da yardan Allah munyi magana da y’an Sanda Kuma na basu adireshin kauyenda sike da sassafe zasuje kauyen sutaho tare.
Tabe baki yai ‘Toh Alhmdulillahi kuma lnsha Allahu babu wata matsala, Amma sedei wani hanzari ba guduba abu guda ce zata hanamu samun nasara awannan case…. Dasauri Miemah ta katseshi “Attorney meye kake nufl duk wannan shedunda muke dasu uban meye zata hanamu samun nasara?
Gyara muryarsa yai” Karki samu damuwa Miemah Sabida ba lallai ne abun yafaru ba, wato
Idan iyayenki sun sheda lalfinda kotu take tuhumansu ma‘ana idan sun fada agaban kowa cewa su suka kashe Lawan Mai gadi idan hakan tafaru kotu bazata duba dukkanin shedun damuka tanada mataba sabida wa’inda ake tuhuma sun rigada sun karbi laifunsu Kai tseye
za’a zartar musu da hukunci. Yana gama maganarsa tai murmushi “Impossible Attorney wannan bazata taba faruwa ba I promise, iyayena basuda hannu aciki just chill out man we won…..
Ahaka tattaunawartasu takasance, karfe takwas na dare sukayi sallama dakuma akan gobe zasu hadu a kotu.
Cikin sananin farin ciki Miemah takwana a daren har zuwa wayewar gari ……
Saturday/15/March/2019
Mutane da dama sun taru cikin Kotu suna jiran polisawan dasukaje kauyen Mai Riga
domin ataho da wa’inda ake zargi wato Saminu da matarsa, sun shafa tsahon awanni babusu babu Kuma alamarsu. Anan zuciyar Miemah tafara tashi, yayinda jikinta tafara karkarwa kai tseye tinaninta yakefad’amata cewa lyayenta sun ‘kara barin kauyen Mai Riga, Nan da nan tafara hada gumi tareda damuwa mai tsanani.
“Order in the court” Judge ya buga na’uran dake gabansa ya’kara cewa “Order”. Aiko Miemah najuyowa tahango lyayenta chan sun shigo “Alhamdulillah wani sanyi zuciyarta tai tamkar kan’kara aka shafa Mata Nan da nan fuskarta ta bayyana murmushi.
Judge ya bude wata katuwar Iittafi, sannan yadaga Kai yanabinsu da kallo cikin nitsuwa yace”ina Lawyer Mai wakiltarwanda ake zargi’ zaka iya mikewa agaban kotu domin ka gabatar da kanka.
“Ya Mai girma mai sharia sunana Barrister Mustapha ni ne Kuma lawyan wanda ake tuhuma wato Saminu Maidugu da Aisha. Gyara murya judge yai ayayinda yace” Ina lawyer’n Marigayi Lawan. Bai batamusu lokaciba yami’ke ” Sunana Barrister Ahmad ni ne Lawyer’n Marigayi Lawan kuma inada tabbacin cewa hada baki Saminu yai da matarsa suka kashe Lawan sabida …….
Objection my Lord ” Barrister Mustapha yami’ke in full confidence yace’ ya mai girma mai
shari’na Bai kamata Barister Ahmad yafara bayyana alokacin gabatarwa ba my Lord wannan kuskure ne.
Yana rubutu a littaflnsa bai d’ago kai ba yace” Barrister Ahmad akiyaye, Barrister Mustapha zaka iya bayyana hujjojinka a gaban kotu ….. Bai karasa furucinsaba Saminu ya d’aga hannunsa sama ” Ya mai girma mai sha’ria inada wasu dan bayanan da zanso kotu tabani da’man bayyanata agaban jama’a. Kotu ta baka dama.
“Ya mai girma mai sha’ria tuhumar da akeyi akanmu gaskiya ce mu ne muka kashe Lawan Mai ga’ din gidanmu”. Saminu yafad’a kai tsaye ayayinda kowa yajuya yana binsa da kallo cikin tsananin mamaki. Mikewa Miemah tai wuf tasaki baki, hanci harda ido tana zuba masa ido.
IYA ABUNDA YA SAWWAKAA YAU KENAN .
NEXT CHAPTER SPOILER
“Abisa wannan kwararan hujjojin kotu ta yankewa Saminu da matarsa hukuncin daurin
rai da rai agidan yari. COURT!!!”