TAGWAYE CHAPTER 30

TAGWAYE






CHAPTER 30




Miemah ki gafartamana wallahi da na’san cewa kece ainihin Y’ar Uwata da tun tuni na ta’kurawa Daddy ya dawomana dake gida, sabida tunda nake rayuwa a duniya ban taba sanin yedda soyayyarY’ar uwa tajini takeba sai yau, Babu irin wulakanci da cin amanarda ban fuskanta gun Maisha ba, Kuma ina tabbatar miki cewa momy ‘kanta idan ta’san da wannan sirrin tuni tajanyoki ajiki.
Miemah tana share hawayen dake kokarin sirnanowa daga idanunta yayinda tasa murmushin karfm hali tanacewa”Babu komai haka Allah ya kaddara, ni kaina ako yaushe nakanji ajlkina tamkar akwai alaka Mai karfi dake tsakanina dake, Ma’inah wallahi tun da muka taso tare duk duniya babu wacce nafiji da ita irinki Kuma idan muna tarejinake tamkar nafi kowa sa’a a duniya…
I feel thesame way sister,. Ma‘inah ta katseta” Wataran har kuka nike, ina ma ace kece Y’ar Uwata ba Maisha ba.
Allah Sarki, Cewar Miemah inda ta rike hannayen Y’ar Uwar nata duka biyu tanacewa’ Maisha ta ta’kurawa rayuwarmu Kuma bamuda makiyin dayawuce Maisha a duk fad’in duniyar nan Sabida haka daga yau, ni dake zamu fara d’aukan fansa, dazaran muna tare Maisha bazata ‘kara ta’kurawa zuri’ar muba promise.
Dasauri Ma’inah tasa d’ayan hannunta a saman ta Miemah ” Yes Promise, Daga yau zamu
rayu cikin farin ciki da annashuwa babu wanda zai kara d’aga mana hankali, zamu farantawa iyayenmu sannan muyi rayuwa kamar yedda kowace zuria suke rayuwa cikin kwanciyar hankali, Dubun Maisha ta cika bazata Kara addabanmu ba dazaran muna tare. Haka suka rungumejuna suna dad’a farin ciki da annashuwa.
Zaune take gaban television a Babbar falon kasa inda take bin wata shirin wasan kwaikwayo mai suna Kwana_casa’in wacce ake nunawa a tashar Arewa24. Sallamar mijinta ta amsa a tsorace ta mike “Saminu lafiya? saurin meye kakeyi haka Ina Kuma zaka?. “lnji dei wa’innan munafukan basu dawoba, ke kad’ei ce agidan. Cikin sananin rud’ani
Aisha ta gyad’a kai “Ehh ni kad’ei ce, Saminu su waye kuma munafukai? Bai amsa mataba janyota yai kai tseye suka fito waje, Maisha na ganinsu ta fice daga motarta tanacewa’
Saminu don Allah kataho mutafi mutanen nan zasu dawo su sameni anan. “Sorry my dear bani minti biyu’ Cewar Saminu inda yajuya bangaren Aisha yanacewa” meye kika tsaya yi anan bazakije ki baiwa yarki hakuri ba, Ni dei ta yafemun saura ke ….. ‘
“Dakata Saminu daman sabida wannan kake wani rawanjiki haka, to kasani niba shashasha bace irinka, nina haifeta ko ita ta haifan, anki abada hakurin yi abunda zaka iya. Bata kaiga karshen furucintaba Saminu yarufeta da mari a fiska “Shashasha kawai banza, ahaka zaki kare ma’kira, algunguma. Kuka Aisha tasaka “Saminu wallahi Allah zai sa’kamin, kaje Kucigaba da aikata halinku da kai da d’iyar ka kuma kusani Allah yafl’ku
wataran sai kunyi da’nasani da yardan uban giji. Fashewa da Dariya Maisha tai achan baya, tanacewa’ Saminu wai meye take fad’i ne don Allah shareta mutati batamana lokaci zatayi da banzan maganganu. Haushi Saminu yake tamkar kare yayinda yajuye rai abace yanacewa” Kuma daga yau kin rabu da zuri’ar ki har abada, kisani dani da Maisha bazamu ‘kara dawowa nan gidan ba na sakeki saki uku, d’aya, biyu, Uku igiyar aurena dake ta’kare anan wajen. “Tafi nono fari, tafi man Saminu sai me, kafi jirgi tashi kuma kafi ruwa gudu kada ka kara dawowa so what? Bai tan’ka mataba, juyowa yai kamaryedda tafad’a yai tafiyarsa, ko ajikinsa dashi da Y’arsa suka shige mota Fuuu!!!! Suka tashi tamkar barin gari zasuyi. Anan
wajen Aisha tafa d’i sai kuka take tana istigifari “Ya Allah wace laifi na aikata a duniya, Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Allah mun tuba, Ya Allah duk inda Saminu yakai y’ar nan ta‘wa ya Allah ka baiyanota ga hukuma ta fiskanci hukuncin wannan gagarumar laifinda ta aikata maka, Ya Allah ka gafartawa wannan bawan Allah “Asad“ Allah kasa mutuwan shi yafi alkhairi agareshi. Jiki a sanyaye Miemah ta‘karaso cikin d’akin. Daddy yana tsaye achan gefe yana binta da kallo batareda ya tankamata ba. ‘
Kai tsaye Miemah ta’karaso har gadon Mommy, alokacin momy tayi zurfi cikin duniyar barci, Daddy ya gyara tsayuwarsa sosai yana binta da kallo, Yayinda tafashe da kuka “I’m sorry” tafad’a ahankali, Sannan ta rungumeta “MOMMY I LOVE YOU”.
“Zurr!!! ldanuwan Mommy suka bud’e awannan lokacin tamkar a mafarki ta‘kara bud’e kunnuwarta “Miemah did you just call me Mommy? Tafad’a cikin muryar marasa lafiya. Gyad’a kai Miemah tai tana murmushi “Kwarai I LOVE YOU MOMMY”.
“Alhamdulillah, Alhamdulillah, Ya Allah na godemaka. lya abunda Momyta iya furtawa kenan, hawaye sun hanata sakewa, wata irin kalar farin ciki ce taji ya mamayeta awannan lokacin tamkar albishirin aljanna akayimata, Ta’ke sai taji ta warke tamkar bata taba ciwo arayuwarta ba. Dasauri ta sauko daga gadon tana kokarin durkusawa a kasa domin tai godiya, Ma‘inah ce tashige d’akin aguje ta riketa gamida cewa” Mommy mun rigada mun yafemiki har abada, Kuma Ina mai tabbatar miki cewa dani da Y’ar Uwata Miemah munf’l kowa farin ciki awannan lokacin. Nan da nan momy ta maida idanunta kan Miemah domin sanin amsarta. Gyad’a Kai tayi cikin murmushi tace’ Na godewa Allah dayanunamin asalin iyayena da Y’ar Uwata Alhamdulillah. 
Nan ne sukasa Mommy a tsakiya suka rungumeta, sun dade suna manne da junansu suna zubarda hawaye, Sautin kukan Daddy daya doso kunnuwarsu ce yasa hankalinsu duk takoma kansa. Dasauri yafara share hawayen nasa yana murmushi amma haryanzu hawayen ta’kasa tsayuwa daga idanunsa ahaka ya ‘karaso inda suke, yana kokarin magana suka rungumeshi, awannan lokacin dukkaninsu kuka suke sosai ta farin ciki. 
Zaid yayita sallama amma hankalinsu duk ba’ya wajen Saida ya’karaso har inda suke tukunna sukaji abunda yake fad’a. “Assalamu Aleikum, Likita yashigo nan har ya sallamemu batareda kunsani ba, yanzu tashi zakuyi mukoma gida. Handkerchiefyacire daga aljihunsa yamikowa Mainah, inda yamatso kusa da ita yana mata magana a kunne “Baby kukan ya Isa haka Mana, share hawayen ki, ko sokike na tayaki. 
Da hannun dama ta kar6i Handkerchiefdin daga hannunsa, tafara goge hawayen nata tana 
murmushi. Aunty Nasiba ce ta gyara muryarta sannan suka dawo hayacinsu. 
“Zaid agaskiya bai kamata Ma’inah da Y’ar uwarta dakuma iyayenta sukoma wanchan gidan dazamaba, sabida Maisha shed’aniya ce kowa ya sani zata iya turo mutanenta chan gidan su halakasu duka, aganina ya‘kamata ayanzu sudawo gidanmu dazama ka’min y‘an Sanda su kamata, sabida tsaro, 
Zaid baiyi wata doguwar tunaniba, Kai tseye ya gyad’a kai” Mamy gaskiyarkl’ bai kamata sukoma wanchan gidan ba, gidanmu zasu koma sabida nan yafi tsaro ko ba hakaba Daddy? Daddy bashida wata zabi amsawa yai kurun sannan ya tambayi shawarar Matarsa itama tace‘ babu wata matsala “Babu matsala Zaid mun gode, sai dai, Iyayen Maisha suna chan na barosu a gidana, suma ina neman alfarma sudawo gidanku muzauna tare. Zaid ne ya amsa kai tseye” Ai Daddy kafi karfi kanemi alfarmata, sai dai kabani umarni babu matsala yanzu chan zamuyi gidan naku mud’auki Iyayen Maisha sannan mudawo gida mucigaba da zama amasayin Zuri’a d’aya. 
Aisha ta tattara kayanta duk ta shirya cikin jaka guda inda tayafa hijabi tafito tana kuka da takaici babu inda tasani anan garin, batada inda zataje iyayenta sun rasu, daman Saminu 
ne ke rufamata asiri shima ayanzu sun rabu ya zatayi da ruyuwarta Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’. Da wannan tunanin tajanyo Jakarta tafito, Tana fitowa tsakar gida tahango wata katuwar mota tana shigowa gidan haka ta tsaya a tsorace tana karanta dukkan ayoyinda 
tazo abakinta, Atunaninta Saminu da Maisha ne suka turo mutane sabida azo atafl da ita, 
Sai k0 taga ba hakan bane, Motartana tsayawa sai ga Y’ayanta Miemah da Ma’inah sun f‘ito aguje suka taho wajenta. Ta’ke wannan tsoron dake idanuwarta suka koma farin ciki, gashi tayi kewarsu dikansu biyu musamman ma Ma’inah. Ta rungumesu sai kuka take ta’kasa 
fad’in komai. ‘ 
“Come on sweetheart it‘s ur birthday lets celebrate my dear. Cikin tsananin hawaye Munah ta kifto hannunta “A’a zan koma wajen Daddy na”. Hajiya Turai ta’rasa dalilinda yasa Y’ar cikinta ke gudunta haka ko don sabida basu zauna tare bane shiyasa amma dei duk da haka bai kamata yariny’arta kyamaceta hakaba sabida y’arta ce kumajininta halak, malak. 
“Surprise” Maisha ta shigo da wata madaideciyar cake ahannunta “HAPPY Birthday dear Maimunah stay blessed”. Saminu ne yake biyeda ita a baya yana tapi “Happy birthday to you, happy birthday to you, Happy birthday to my Little princess happy birthday Maimunah. 
lhu Munah tasaka tanacewa’ Banasonku, Daddy na nakeso Ya Zaid d’ina nakeso, kukaini wajen Mamy da Aunty Nasiba. 
Had’iye miyau Maisha tai, a nitse tazauna kusada ita tanacewa” Baby na Ya Zaid fa ba sonki yakeba shiyasa yabaroki a makaranta Kun samo hutu amma ya’kasa zuwa yad’aukoki har sanda momy tazo tadawo dake nan, yama manta cewa yau ranar haihuwarki ce, Kidawo wajen mominki muzauna tare kinji Baby na. ‘ “A’a niba Babyn ki bace, Babyn Aunty Ma‘inah ce. Nan da nan ran Maisha ta baci, inda ta fisgo kolar rigar yariny’ar tanacewa kada ki’kara kawomin sunan Ma’inah anan ….. Bata karasa furucintaba yayinda Hajiya Turai tasa hannu babu fargaba takaimata Mari a fuska “Maisha how dare you ya kike tsawatarwa Y‘ata haka? With your dirty hands so kike ki janyomata cuta, y’ayan talakawa you are so careless daman bakuda hankali. 
Mikewa Maisha tai cikin tsananin mutuwarjiki, bacin rai da rud‘ani tanabin Matar dawata irin shegiyar kallo. Saminu yana kokarin signaling d’inta da gefen Ido domin ta maida makaman ya’kinta Amma inaa, wannan maganar da Hajiya Turai tai yamatukar batamata rai. Kuka tasaka mai kona zuci inda takecewa’ Saminu Allah ya Isa tsakanina da kai bazan taba yafemaka ba, kuma wallahi ko mutuwa zakayi bazan taba amincewa dakai amasayin Mahaifinaba banza talaka. Da wannan maganar ta ruga aguje tabarmusu falon. Saminu ya mike yana kokarin bin sahunta ayayinda Hajiya Turai ta dakatar dashi ” ina Kuma zaka? 
Muryarsa na karkaruwa yace” B bbb bi binta zzz za zanyi nnn nashawo kanta domin muzo mubaki hakuri. 
Tabe baki Hajiya Turai tai tanabinsa da kallo Sanda ya kammala bayanansa tace’ Maza ko kad’auki wannan tsiyar ta’ku kawuce da ita, Y’ata bata bu’kata irin wannan kananan Cakes kaji. 
Babu musu Saminu yakoma yad’au cake din kamaryedda ta umarcesu sannan shima yayi waJe. 
“Saminu ne yayi miki wannan cin mutuncin har yasakeki saki Uku. cewar Daddy. Cikin kuka Aisha ta amsa “Babu irin cin mutuncin da basuyinba dashi da Y’arsa, sannan yasakeni 
sukayi tafiyarsu kuma cewa yayi bazan kara ganinsu ba har abada. 
“Karyarsa Wallahi” Zaid ya katseta “ya isa ya gudu da Mai laifi irin Maisha, y’an Sanda suna nan suna nemanta Kuma da yardan Allah nan da mako guda zasu kamota sabida idon ba’a kamo Maisha ba hankalina ba’zai taba kwanciya ba wallahi. 
Zaid bai karasa furucinsaba yayinda Miemah ta mike aguje takoma d’aki tana kuka tana Kuma tuna irin soyayyar da Asad yanuna mata alokacin da yake raye, ta rasa masoyi na hakika, gani take har abada bazata ‘kara samun masoyi irin Asad ba. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *