TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 1 BY MANSUR USMAN (SUFI)
Www.bankinhausanovels.com.ng
Saurayi ne kyakkyawa na gaban kwatance ke ta * faman tafiya a cikin Kasaitacciyar kasuwar birnin,
. Yana sanye da tufafi riga da wando wadanda aka sana’anta su da fatar damisa, hatta takalmin dake kafar sa anyisa ne da fatardamisar. — A hannun sa yana rike da wata doguwar sanda, kallo daya zaka yiwa saurayin ka fahimci cewa yakasance GWARZON MAYAKI, Www.bankinhausanovels.com.ng
Saboda da kirar karfi da suka bayyana a tare dashi, : ‘Babban abinda yakara fito da kyawun sa shine zarazaran gashin kansa daya zuba izuwa kan kafadun sa da kasumbar sa gemun sa bakaKe sidik,
Haka dai saurayin ya cigaba da tafiya a cikin kasuwar babu sassauci, – Lokacin daYA shafe tsawon rabin Sa’a yana wannan tafiya a dai dai wannan lokaci ne saraaniyar dake mulkin birnin ta fito yawon shakatawa tare da dakaru masu tsaron lafiyar mutum dubu biyar. Duk inda sarauniyar ta durfafa a kasuwar sai kaga jama’‘a sun dare sun bayarda hanya, Bakomai yasanaya hakan ba sai domin tsananin tsoron fushin sarauniya lasmirat, — Ana cikin wannan hali ne sarauniyar lasmirat ta hango wannan kyakkyawan saurayi ya tunkaro inda
take babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da fuskar sa, Al’amarin da yayi matukar bawa sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya daure mata kai, Domin shekaru masu yawa tana fitowa wannan rangadi hakan bai taba faruwa ba, Www.bankinhausanovels.com.ng
Su kuwa dakarun dake bayan ta sai zukatan su suka ‘ harzuka jikin su ya kama kyarma yana tsuma saboda
tsananin fushi, Kawai sai sarauniyar lasmirat ta daga hannun ta sama tana mai nuni da a tsayar da tafiya, Sannan ta dubi saurayin ta daka masa tsawa cikin fushi tace dashi”‘ yakai wannan saurayi me kake
takama dashi da bazaka risina agare ni ba,
Koda jin wannan tambaya daga bakin sarauniyar – * lasmirat sai saurayin ya kura mata idanu’batare da ., yace da ita uffan ba
Cikin fushi lasmirat ta sake daka masa tsawa a karo – na biyu tare da maimaita tambayar ta, Kawai sai saurayin ya saki wani tattausar murmushi
daya karawa fuskar sa kyawu sannan ya dakamata
sarauniyar lasmirat tsawa ya dube ta yace Yake wannan sarauniya mai takama da abinda bazai dawwa ma agare ta ba kiyi sani cewa bazan taba girmama ki ba, Domin a halin yanzu abinda na sani kawai shi ne bambancin dake tsakani na dake shine ke diya mace ce Ni kuma namiji, mulkin da kike takama dashi tamkar kumfar kogi ne akoda yaushe za’a iya neman sa a rasa shi, Kafin saurayin ya gama rufe bakin sa fiye da rabin dakarun sun zare makaman su yunkura izuwa kansa suna ihu da kururuwa mai firgitar wa Koda ganin hakan sai ya gyara tsayuwar sa gami da sandar dake hannun sa .yana mai jiran karasowar – dakarun Inda.ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da wadannan dabaru suka ruga izuwa kan saurayi sai _ yayi tsammanin dandazon zakoki ne suka farma barewa guda daya, saboda tsananin kwarjini daban . _‘tsoron su,.Yayin da ya rage saura baifi taku uku tsakanin su ba . sai kawai akaga saurayin ya dako tsalle daga inda – yake tsaye tamkar an harboshi daga cikin baka yana saman ya sanya sandar sa ya daki kawunan dakaru …. . mutum goma, . Take dakarun suka tsandara ihu sannan suka zube a kasa magashiyan, ~ . a Sannan ya dira bisa Kafafuwan sa a turba cikin gwaninta,. — Nan take aka kacame da azababban yaki mai matukar muni ban tsoro daban Al’ajabi. Dakarun suka wanzu suna kaiwa saurayin sara da suka cikin matukar zafin Www.bankinhausanovels.com.ng nama JURIYA DA BAJINTA,
Shi kuwa ya wanzu yana kare hare haren su cikin wani irin bakin zafin nama, kuma yana makosu da sandar sa daga kan dawakan su suna yin MUGUWAR HALLAKA, Nanfa waje ya yamutse da ihu da kururuwar mazaje, karar karafniyar Karafa ta cika dodon kunne, gawarwakin dakarun suka watsu a wajen gasu birjik kwance cikin jini. Sai da aka shafe tsawon sa,a daya ana wannan gumurzun babu sassauci, Sa’adda sarauniya lasmirat ta lura cewa saurayin ya – hallaka fiye da rabin dakarun sai ta cika da matukar mamaki, domin a tarihin masarautar tun a zamanin mahaifin ta bata taba samun wanda ya hallaka dakarun gidan sarauta mutum uku ba, Kuma zuciyar ta ta harzuka bisa ganin yadda dakarun ta keyin muguwar hallaka Duk inda saurayin ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun
na zubewa kasa cikin mawuyacin halin dake tsakanin
RAYUWA DA HALAKA, . Nan fa dakarun suka dimauce bisa ganin irin kisan da’ saurayi keyi musu, ; Amma koda kwarzane daya basu samu nasarar yi masa ba,’
Daga can nesa jama’ar kasuwar suna kallon fafatawar da ake yi wadansu ta tagogin gidajen su suke leken abinda yake faruwa, Kuma suka cika da mamaki bisa ganin yadda saurayi yazamewa dakarun sarauniyar lasmirat ANNOBA DARI wanda a tarihi hakan bai taba faruwa ba, Lokacin da sarauniyar lasmirat ta fahimci cewa idan har aka cigaba da Www.bankinhausanovels.com.ng wannan artabu a haka dukkan dakarun ta zasu rasa rayukansu sai kawai ta dakamusu tsawa suka ja da baya sannan ta dako tsalle daga kan dokokin ta tamkar an harbota daga cikin baka ta sanya Kafafuwan ta biyu ta daki saurayin a kirji da dukkanin karfin ta, , Saboda karfin dukan sai da saurayin ya yi katantanwa sau . _ uku sai ya turje aka sake yin sabon kallon kallo tsakanin ‘ lasmirat da saurayin, Lasmirat ta kasance mace mai madaidaicin jiki ba doguwa ce ba gajera ba, tana da kyakkyawar fuska mai ‘ dauke da fararen idanu dara dara tana da siririn hanci_ – . wanda akasan sa aka yanka wani dan madaidaicin baki, – wuyan yana kyawu tamkar na barewa, gashin kanta baki . ne sidik mai sheki da Kyalli,ya. zuba har izuwa Kasan . kwankwason ta, Kirjinta a cike yake kuma a tsaye Kyam bai rankwafa ba, cikin ta a shafe yake tamkar bata taba cin komai ba, daga – sama Kugunta ya tsuke daga baya baya kuma ya bude yayi tudu sosai, tana da zabga-zabgan cinyoyi, fatar jikin ta farace mai Kyalli, Wohoho Hakika duk inda kyawu yake tabbas ~ sarauniyar lasmirat ta kai, domin babu wani da namiji mai hankali da zai yi tozali da lasmirat face ya kamu da matukar kaunar ta. Yayin da aka shafe tsawon dakika talatin ana wannan kallon kallo, sai lasmirat ta zare wata zabgegiyar takobi a damtsen ta kaiwa saurayin wani wawan sara da nufin tsinke masa wuya, Cikin bakin zafin nama saurayin -ya sunkuya takobin lasmirat ta sari iska, Kawai sai suka kacame da azababban yaki suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA Www.bankinhausanovels.com.ng BAJINTA, Ana fara wannan gumurzu’ ne lasmirat ta fahimci cewa _tsananin KARFIN DAMTSEN saurayin ya nunka nata sau biyar gami da zafin nama.Sai da sa,a daya ta shude ana fafatawa batare dayan su ya samu nasarar lakutar jikin dan uwan sa ba, Bisa dole lasmirat ta sake zare wata takobin yazamana tana kai wa saurayin hari da takubba biyu, Ana Cikin wannan artabu ne Saurayin ya shammaci °lasmirat ya gabza mata wawan naushi a fuska saboda – karfin naushin sai da sarauniyar ‘lasmirat tayi sama tamkar an janye ta da kugiya,sannan ta fado Kasa a matukar . – galabai‘ce,
*********
Bayan shudewar mulkin sarki Hulbaru na birnin Misra. anyi wata gagarumar Sarauniya da ake yiwa laKabi da lasmirat bintu kazmal Lasmirat ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance kuma gagarumar basadaukiya,mace mai kamar_ maza,dadin
dadawa kuma mashahuriyar attajira ta shara ainun a fagen sanin ilimin tsafi, A gaba daya nahiyar babu kasa mai karfin tattalin arziki kamar ta ta . ; Sau tari manyan sarakunan duniya kan kaiwa lasmirat HARIN BAZATO domin mamaye Kasar ta kuma su mallaketa a matsayin matar aure amma sai abu yaCi tira, domin duk sa‘adda aka gwabza yaki sai dai Www.bankinhausanovels.com.ng sarakunan suyi asarar dakarun yaki da dukiya mai tarin yawa bisa dole . suka janye aniyar su Lokacin da sarauniya lasmirat ta fara Kwadaituwa da son da namiji sai ta gudanar da bincike bisa halarar tsafin ta domin taga irin namijin da ya dace ta aura _ Abinda binciken ya tabbatar mata shine mijin da zata aura . Shi ne wanda yafi kowa talauci a duniya’ . . Binciken yakara tabbatar mata da cewa matsawar ta auri wani da namiji ba shi har ta tara aura ba tofa zata rasa komai nata da ta mallaka a duniya, ‘Sa’adda sarauniya lasmirat taga wannan al’amari a cikin halarar tsafin ta sai ta cika da matukar bakin ciki . marar musaltuwa ; Taya za‘ayi ace sarauniya kamar ni ace na auri wanda yafi~ kowa talauci a duniya, bayan cewa nafi kowa ne BASARAKE karfin mulki da tarin dukiya a wannan nahiya baki daya,