TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 2 BY MANSUR USMAN (SUFI)

TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 2 BY MANSUR USMAN (SUFI)

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Sau tari manyan sarakunan duniya kan kaiwa lasmirat HARIN BAZATO domin mamaye Kasar ta kuma su mallaketa a matsayin matar aure amma sai abu yaCi tira, domin duk sa‘adda aka gwabza yaki sai dai Www.bankinhausanovels.com.ng sarakunan suyi asarar dakarun yaki da dukiya mai tarin yawa bisa dole . suka janye aniyar su Lokacin da sarauniya lasmirat ta fara Kwadaituwa da son da namiji sai ta gudanar da bincike bisa halarar tsafin ta domin taga irin namijin da ya dace ta aura _ Abinda binciken ya tabbatar mata shine mijin da zata aura . Shi ne wanda yafi kowa talauci a duniya’ . . Binciken yakara tabbatar mata da cewa matsawar ta auri wani da namiji ba shi har ta tara aura ba tofa zata rasa komai nata da ta mallaka a duniya, ‘Sa’adda sarauniya lasmirat taga wannan al’amari a cikin halarar tsafin ta sai ta cika da matukar bakin ciki . marar musaltuwa ; Taya za‘ayi ace sarauniya kamar ni ace na auri wanda yafi~ kowa talauci a duniya, bayan cewa nafi kowa ne BASARAKE karfin mulki da tarin dukiya a wannan nahiya baki daya,

ZAMU TASHI 

Tabbas hakan Kaskanta daraja ta ne da Kimata a idanun sauran sarakunan duniya Kuma idan na auri talaka dukiya ta da mulki na zasu  zamo bisa KarKashin ikon sa, Lokacin da sarauniya lasmirat ta zo nan a tunanin ta sai * hankalin ta ya sake dugunzuma fiye da ko yaushe kuma ta rasa abinda ke yi mata dadi, A wannan lokaci lasmirat na zauna ne a bisa wata – : . Kasaitacciyar kujera amma sai ta mike tsaye ta shiga kai komo acikin turkarta Daga Rarshe dai lasmirat ta yanke shawarar ta ziyarci wani boka dake zaune a wani gari dake iyaka da Birnin . misra, Lokacin da sarauniya lasmirat ta isa gidan boka Dayyubul-Barmas ta kadaita dashi a cikin turakar sa . Nan take ta kwashe labarin

abinda ta gani a cikin halarar tsafin ta ta zayyanewa boka Www.bankinhausanovels.com.ng Dayyubul-Barmas tun daga . farko har Karshe, sannan ta dora da cewa , Yakai wannan boka mafi girma a halarar tsafi kayi _ sani cewa Babban burina shi ne na auri mijin da yafi kowa ~ Arziki a duniya sannan ina da burin nayi rayuwa kamar . Shekaru. dubu’ biyu domin nazamo_ nafi. dukkanin – sarakunan duniya dadewa a bisa karagar mulki, .. – Yayin da boka Dayyubul-Barmas yaji irin buKatar dake — tafe da sarauniya lasmirat sai ya jinjina al’amarin a cikin Tsawon dakika arba’in bai ce uffan ba sai daga bisani ne ya dubi lasmirat yayi gyaran murya yace” ya sarauniyar ‘ kyawawan duniya kiyi sani cewa hakika kin zomini da _ al’amari mai girman gaske Hakika bakaramar hikima kikayi ba da kika ‘bayyana bukatar a gareni domin shi ilimin tsafi. kogi ne komai nutson ka a cikin sa baza ka kwashe Abinda ke ciki ba, Kuma kinsan masu iya magana na cewa Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai hango ba, abin da – bincike ya tabbatar mini ga me da bayanin ki shi ne. . Matsawar kina son kifi kowa ne sarki dadewa abisa_ – karagar mulki kuma ki auri mijin da yafi kowanne kudi a duniya to yazama wajibi ki mallaki abubuwa guda uku domin ki samu nasarar samun ruwan: koramar matsafi _ Daryalu _ Da farko za,a nemo ruwan kogin ma’ul-hayatu, Sannan wadansu zobunan tsafi dake ajiye a kogon fatalwa a can yankin kasashen Larabawa a wani daji da -. ake yiwa laKabi da Husumul-kadar Abu na karshe shi ne kubar miftahul-daryal,  Shi dai wancan ruwa zamu yi Www.bankinhausanovels.com.ng amfani dashi ne a lokacin da _ zamu shiga wani daji Kafin mu isa inda koramar boka ‘Daryalu take ruwan zai bamu kariya ne daga wadansu musifu dake dajin, . Su kuwa wadancan zobuna zamuyi amfani da su ne a lokacin da zamu shiga gidan boka Daryalu rukuni na farko wajen sanya su a hannayen mu, Domin babu yadda za,ayi mutum ya shiga gidan face ya na dauke da wadannan zobunan sihirin, -Kubar miftahul-daryal kuwa zamu yi amfani da ita ne wajen bude gidan boka Daryalu Dazarar mun samunasarar debo ruwan koramar kinsha to shi kenan bazaki auri wanda yafi kowa talauci a duniya ba, Lokacin – da boka Dayyubul-Barmas yazo dai dai nan  azancen sa sai hankalin sarauniyar lasmirat ya dugunzuma ‘ainun. Ta dube sa cikin alamun tsantsar damuwa tace” ya Sarkin bokaye shin taya ya zan mallaki wadannan abubuwa kafin ajali ya riskeni Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuska tamkKar an aiko masa da sakon mutuwa .Sannan daga bisani kuma ya fashe da kuka. . “Al’amarin da yayi Matukar bawa. sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya daure mata kai ta dube sa ta ce” — -ya uban bokaye shin ina dalilin wannan dariya;da kuka naka? —Da jin wannan Www.bankinhausanovels.com.ng tambaya sai Dayyubul-Barmas ya share hawayen ya budi baki yace ya shugaba-ta” – abinda ya sanya ni dariya shi ne bincike ya tabbatar mini. dacewa a wannan zamani nine bokan da zan. samu daukaka fiye da kowa ne matsafi domin ya cika burin mahaifin mu.
Abinda Ya sa ni kuka kuwa shi wani bakon jarumi zai_ rushe wannan daukaka tawa ta yadda ko tarihina bata sake tunawa a duniya ba  Kuma wannan jarumi ba wani bane face namijin da zaki . aura har ki samu Haihuwa wanda yafi kowa talauci a duniya Sai dai iyakar bincike ne na kasa gano ainahin a nahiyar _ da saurayin yake, Domin jarumin yana dauke da wadansu sirrika masu basa kariya..So ; a Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai -dai nan a jawabin sa, sai hawaye suka sake zubo masa, Nan take Sarauniya lasmirat taji ta kamu da matukar tausayin sa‘Dayyubul-Barmas ya cigaba.-da cewa ya sarauniyar kyawawa kiyi sani cewa bazaki taba fin kowane sarki ‘-dadewa abisa karagar mulki ba face kin mallaki wata_ takobin da ake yi wa lakabi da TAKOBIN DAUKAKA, Asalin TAKOBIN DAUKAKA ta wani gagurtaccen mayaki ne ma’abocin addinin musulunciBayan shudewar jarumi Hilal ne wani mashahurin matsafin aljani ya sace takobin ya shiga halarar tsafi ta tsawon shekaru arba’in yana sana’‘anta takobin da sirrikan tsafi An kira takobin da suna TAKOBIN DAUKAKA ne saboda duk jarumin da ya mallake ta zai samu daukaka a duniya lokacin da aljani Sautul-Hidar ya kammala halwar sa sai -yaga wani Al amari da ya firgita sa kuma ya dimauta sa, _ Abinda ya gani shi ne bazai taba samun amfani da TAKOBIN DAUKAKA ba ajali zai riske sa, Wani jarumi wanda bai kasance kowan kowa ba shi ne zai mallaki takobin ya lalata sirrikan tsafin dake jikin ta kuma ya daukaka a duniya, . ‘ Lokacin da aljani Www.bankinhausanovels.com.ng Sautul-Hidar ya ga wannan al’amari sai ya cika da bakin cikiKawai sai aljani Sautul-Hidar ya dauki. TAKOBIN — ‘DAUKAKA ya caka a kirjinsa a saitin Kahon zuyar sa, Faruwar hakan ke da wuya sai numfashin sa ya dauke komai na jikin sa ya daina motsi ya sandare,take gangar – – jikin sa ta zagwanye ta zama: wani irin bakin ruwa mai yauki, Daga bisani sai ruwan ya rikida izuwa wadansu irin gabza –gabzan samudawan aljanu dukkanin suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da’ ban tsoro a hannayen sa‘rike da wadansu irin makaman _ yaki masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi, Koda bayyanar aljanun sai wani daga cikin su wanda da alama shi ne shugaban su ya dauki TAKOBIN DAUKAKA ‘ -ya sanya ta acikin wata akwatu ta farin gilashi ya dauki akwatin da takobin ke ciki ya shiga sanya ta acikin ‘ wadansu akwatin har guda dubu, . Sannan ka sa dakarun aljanun izuwa kowace kusurwa ta gidan domin tabbatar da cikekken tsaro ga takobin
Tun daga wannan rana wadannan aljanun suke gadin gidan boka Sautul-Hidar dake kan tsaunin lauhulazwar Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa duk daya . daga cikin wadannan aljanun yana iya yakar bil’adama guda miliyan daya . Ke nan hakan ya nuna cewa aljanun zasu iya yakar duniya baki daya Tabbas a halin yanzu tunkarar gidan aljani Sautul-Hidar dai dai yake da mutum ya bude taskar ANNOBA DARI . Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo daidai nan ajawabin sa. _ _ sai idanun sarauniya lasmirat suka zazzaro kuma tsoro ya _ kamata, ta shiga damuwa ainun kamar tacewa boka Dayyubul-Barmas ta janye buKatar ta, Amma Sai ta dube sa .cikin karfin hali da Ki fadi irin nasu na sarakuna tace” ya uban bokaye shin yanzu yaushe zamu yi wannan gagarumar tafiya ta dauko TAKOBIN ° _. DAUKAKA?’ Dayyubul-Barmas ‘ya Www.bankinhausanovels.com.ng gyada kai yace’ya sarauniyar kyawawa ai komai ya na hannun ki duk lokacin da kika , shirya tafiya a shirye nake, Koda jin batu sai sarauniya lasmirat tayi godiya a gare sa” ta debo dukiya mai yawa ta basa Wannan shi ne cikekken tarihin sarauniya lasmirat.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *