TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 3 BY MANSUR USMAN (SUFI)
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Tun daga wannan rana wadannan aljanun suke gadin gidan boka Sautul-Hidar dake kan tsaunin lauhulazwar Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa duk daya . daga cikin wadannan aljanun yana iya yakar bil’adama guda miliyan daya . Ke nan hakan ya nuna cewa aljanun zasu iya yakar duniya baki daya Tabbas a halin yanzu tunkarar gidan aljani Sautul-Hidar dai dai yake da mutum ya bude taskar ANNOBA DARI . Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo daidai nan ajawabin sa. _ _ sai idanun sarauniya lasmirat suka zazzaro kuma tsoro ya _ kamata, ta shiga damuwa ainun kamar tacewa boka Dayyubul-Barmas ta janye buKatar ta, Amma Sai ta dube sa .cikin karfin hali da Ki fadi irin nasu na sarakuna tace” ya uban bokaye shin yanzu yaushe zamu yi wannan gagarumar tafiya ta dauko TAKOBIN ° _. DAUKAKA?’ Dayyubul-Barmas ‘ya Www.bankinhausanovels.com.ng gyada kai yace’ya sarauniyar kyawawa ai komai ya na hannun ki duk lokacin da kika , shirya tafiya a shirye nake, Koda jin batu sai sarauniya lasmirat tayi godiya a gare sa” ta debo dukiya mai yawa ta basa Wannan shi ne cikekken tarihin sarauniya lasmirat.
ZAMU TASHI
*********
Koda samun wannan gagarumar nasara sai kyakkyawan saurayin ya sakarwa sarauniya lasmirat dake kwance a Kasa wani tattausar murmushi. Har saurayin ya juya da nufin da nufin ya cigaba , da tafiya a cikin kasuwar, sai yaji alamar motsin tafiya a bayan sa. Koda ya waiga sai yayi arba da ita fuskar cike da annuri ba wata ba ce face sarauniyar lasmirat, lasmirat ta dube sa tace” yakai wannan kyakkyawan saurayi ma‘abocin sadaukantaka idan baza ka damu ba ina bukatar nayi maka wadansu tambayoyi, kuma ina ~ neman wata alfarma guda daya a wajen ka, — Koda jin wannan batu sai Www.bankinhausanovels.com.ng saurayin ya yi
murmushi har fararen haKoran sa suka bayyana ya dubi lasmirat yace” . yake wannan sarauniya fadi duk abinda kike son tambaya – mi kuwa zan.baki amsar ta dai dai abinda na sani,Lasmirat ta dubi saurayin da wani irin kallo mai dauke da * alamar tambaya sannan tace . Yakai wannan ‘saurayi shin mene ne sunan ka da ma Abinda Ya Kawo ka izuwa wannan birni nawa Alfarmar da nake nema a wajen ka ina so ka biyo ni izuwa ‘. . gidan sarauta domin ina so mu _ tattaunawa wata _ muhimmiyar magana Yakai wannan jarumi kayi sani cewa kai ne jarumi na farko a rayuwa ta dana taba fafata yaki da shi har ya samu nasarar kai ni kasa
Sa’adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tambayar ta sai saurayin ya dube ta yace ” Ni dai da farko suna na yaslir ibn Hulzal na fito ne daga . wata nahiya da ake yiwa laKabi da Nashmir Game da Alfarma da kika nema a waje na kuwa bazan . amince da ita ba Sai kin yarda kuma kinyi mini alkawarin cewa zaki dunga Www.bankinhausanovels.com.ng daraja kowane dan adam, Ma’‘ana za ki dai na azabtar da mutane da zaluntarsu,-: °* . Sa’adda saurayi yaslir ibn Hulzal yazo nan a zancen sa sai sarauniya lasmirat ta zurfafa izuwa kogin tunani Sa,adda talakawa da sauran jama’‘ar kasuwar. suka ga yadda sarauniya lasmirat ta Kaskanta kanta a gaban – saurayin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi ; domin fiye da shekaru masu yawa hakan bai taba faruwa __. tunda lasmirat ta hau bisa karagar mulki Daga can sai ta dago da kanta da dubi saurayi yaslir ; tace”na amince da wannan sharadi naka yakai wannan ° jarumi, © Koda gama fadin hakan sai sarauniyar lasmirat ta yiwa wani badakare inkiya da hannu kamar badakaren yasan -abinda take nufi sai kawai ya janyo wadansu fafaren . * dawakai ya iso gaban ta ya risina ya rike mata linzamin dokin ” daya,ta kama ta hau, _ . Ta na mai yiwa yaslir nuni da ya hau bisa dayan dokin take ya kama dokin ya hau
A lokaci guda suka sakarwa dawakan linzami sauran ; tsirarun dakarun suka mara musu baya a ka cigaba da tafiya, . . Jama’a suka bisu da kallo cike da tsananin mamaki ., A can kololuwar sararin samaniya inda Allah (s,w,t) yayiwa halittu iyaka a nanne sarki Hamras ibn zulaibu ya sanya aka gina masa Kasaitacciyar fadar sa, Wacce masana suka tabbatar da cewa babu wata fada data ~ Kaita Kawatuwa da kayan alatun -jin dadin rayuwar duniya, Domin an ce sai da bakaken aljanu guda dubu shida suka shafe shekaru goma suna aikin ginin fadar dare da rana . babu sassauci,a Binciken bokaye-da matsafa ya Www.bankinhausanovels.com.ng tabbatar da cewa Sarki Hamras yakasance jinin wata Kabila da ake kira da Banu . lahzar,. Wadanda aka ‘tabbatar. dacewa sun mamaye rabin sarakunan duniya, . : . A rayuwar sarki himras fiye da abu uku, yana matukar adawar ace akwai wani sarki a duniya da ya fisa KARFIN—. MULKI, Abu na’ biyu kuma shine ya tsani ma’‘abota addinin musulunci.
Bakomai_ yasanaya hakan sai domin = mahaifinsa sarki zulaibu: ya mutu ne sakamakon kwabza yaki da wani jarumi ma, abocin addinin Musulunci, Akwai wadansu muhimman sirrikan tsafi da mahaifin sa zai sanar da shi wadanda da zarar ya sanar dashi din zai mulki duniya baki daya, Amma sai ya zamana waccan jarumin ya hallaka sa batare – da ya sanar dashi sirrikan tsafin ba, , Abu na karshe da sarki Himras ya tsana shi ne wani – gawurtaccen jarumin ma,abocin addinin Musulunci,wanda binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa shine zai kawo karshen mulkin sa a doran kasa. Lokacin da sarki Himras ya ga cewa a halin yanzu basa da abokan gaba da suka wuce ma’abota addinin Musulunci sai ya zurfafa izuwa cikin halarar tsafin sa domin ya gano ; .wata hanya zai bi ya kawar da-musulmi kuma ya mulki duniya baki daya, . Abin da bincike ya tabbatar masa shine bazai taba cika : wannan buri na sa ba face ya mallaki wata tsafaffiyar takobi mai suna TAKOBIN DAUKAKA ; ‘ Amma koda ya mallaki takobin bazai samu_ nasarar sarrafa takobin ba face ya hadiye gashin kan wadansu mutum biyu, Wadannan mutum ba wasu ba ne face” sarauniya lasmirat _da boka Dayyubul-Barmas, — Sa’adda sarki Hamras yaga gagarumin aikin dake gabansa na mallakar TAKOBIN DAUKAKA, da silin gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat sai Www.bankinhausanovels.com.ng
ya umarci wadansu gwarazan dakarun aljanun sa domin sue yanko masa gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat Bisa jagorancin aljani Huruful-labarus , Aljani Huruful-labarus yakasance GWARZON MAYAKI da masu Bincike suka tabbatar dacewa a jinsin bakaken aljanu babu mai karfin damtsen sa, Bayan Sarki Hamras ya tura Aljani Huruful-labarus sai ya shiga shiri sai da ya kwana arba’in ya na tsuma kansa da tsumin tsafi, sai ya fito ya shiga izuwa duniya domin mallakar TAKOBIN DAUKAKA. –
**********
Al’amarin saurayi yaslir da sarauniya lasmirat kuwa,
tafiyar daKika arba’in.kacal suka yi suka iso izuwa gidan sarauta . Gidan sarautar yakasance kasaitacce mai girma da fadi tamkar gari guda, gaba daya katangun ginin gidan anyi su : ne da wani irin farin gilashi , Babu wani BASARAKE .ko attajiri. dazai yi arba ‘da wannan gidan sarauta face ya Zamo cikekken dan Kauye, Tsayawa masalta tsaruwar gidan sarautar zai iya zamo wa Kauyanci sai dai abinda idanu suka gani kawai, Duk inda mutum ya Www.bankinhausanovels.com.ng duba bayi ne hade da kuyangi da barori na kai komo suna hudima Duk inda sarauniyar lasmirat da saurayi yaslir suka gufta a cikin gidan sarautar sai dai kaga jama’a na zubewa kasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa, Lokacin da aka iso wani bangare mai dauke da manyan falo guda uku hade da kewayen wanka, kayan more rayuwa sai Wadansu tsala-tsalan kuyangi na kai komo a cikin turakar, ‘Da sauri wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru hamsin ta rugo izuwa inda sarauniyar lasmirat take ta zube Kasa bisa gwiwoyin ta ta kwashi gaisuwa Bakin ta na kyarma kuma kanta a sunkuye tace “me kike da buKata ya shugaba ta? Lasmirat ta dube ta tace”’ yake zarima kiyi sani cewa bakomai nake da bukata ba face ina so wannan bako dake tare da ni a basa kulawa da dukkanin wani abu da ya . . bukata kiyi sani cewa yana da matukar muhimmanci agareni . . Koda jin wannan batu sai zarima ta sake risina wa tace ” , angama ya shugabata bin umarnin ki ai shi ne ibada ta, – ‘Tana gama fadin hakan ta mike tsaye tana Mai yiwa saurayi yaslir nuni da ya biyo bayan ta ‘. Batare da bata lokaci ba yaslir ya kama linzamin dokin sa ya sauko sannan ya rufa mata baya Amma koda ya waiga ya hada idanu da sarauniya lasmirat sai yaga tana yi masa wani mayataccen kallo mai dauke da alamar tambaya.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG