TANA RAINA CHAPTER 5

TANA RAINA CHAPTER 5

 
 
 
Ahankali yarinyar ta fito tana d’an kuka tare da d’ingisawa harta k’araso gunsu. D’ayan ya kalleta yace inane hanyar gidanku, tace tacan ne, yace muje mu rakaki dan muga gidan saboda wata ranama mu dawo hahahaha sukasa sa dariya sannan suka kamabinta a baya har suka iso d’an k’auyen nasu daba wani gidaje dewa bare kuma mutane sosai.
Daga nesa suka hango wata yarinya “black beauty” ta fito daga wani gida kuma ta nufosu da gudunta fiskanta d’auke da tambaya ta rungume yarinyar tana cewa “SABREEN” yana ganki haka, meya faru dake k’awata? D’aya daga cikin mutane yace wanine ya mata fyad’e shine muka samota a hanya muka rakota gida inane gidan nasu? 😳Subhanallah Sabreen fyad’e waye shi kuma a ina yake wlh Allah ya isa miki k’awata har abada bazaki tab’a yafe masaba😭 sannan tace mungode da taimakonku gacan gidansu inda na fito yanzu, se sukace to shikenanma base mun k’arasaba tunda munga gidan kuma gakinan seki k’arasa da ita sauri mukeyi suka kalli Sabreen sukace to SABREEN mungode zamu wuce👏🏻 shuru tayi batace dasu komaiba se k’awarta tace godiya me kuke mata kuma ai itace da godiya se anjumanku, yawwa se anjuma sukace da ita sannan suka wuve da sauri.
Har suka dena hangosu sannan sabreen ta juyo ta kalli k’awarta tace ke “MUNIRA” nifa basumin fyad’eba, Munira ta rud’e tace kaman yaya basu miki fyad’eba bayan gashi bakya tfy daidai kuma jikinki duk jini? Sabreen tace mamanki tana gidane, munira tace a’a taje duba mara lfy can mak’ota, sabreen tace muje to in wanke jikina da kuma zanina se in baki lbr, toh muje inji munira mamaki ne a fiskanta sosai suka wuce gidansu munira ta bata zaninta bayan ta wanke jikinta tasa ta wanke zaninma ta shanya tasha ruwa sannan suka zauna ta fara bawa munira lbr tun daga farko har k’arshe. Mamaki da tsorone a fiskan munira tace gaskya SUHAIL d’in mutumin kirkine shida ‘yan’uwansa toh ita kuwa wannan MACEN waye ita baki tambayi koda sunantaba? Sabreen ta sauke ajiyan zuciya tace ban iya ce mata komaiba saboda a gigice nake amma dai koma waye ita “TANA RAINA” bazan taba mantawa da itaba munna domin ta sadaukar da kanta domin cetona gaskya dole in sama mata masauk’i, munira tace wani irin masauk’i kuma sabreen, murmushi sabreen tayi tace masauk’i a zuciyata har abada bazan mancetaba domin “TANA RAINA”.
Munira tace wannan hakane, sukuma ‘yan iskan Allah ya had’asu da wani masifa da fitinar da zatayi sanadin mutuwars… sabreence ta rufewa munira baki da hannunta tace haba munna, aibase kince hakaba kiyi musu fatar shiryuwa mana k’ila su canja halinsu, munna tace ooh don badu miki fyad’enba shiyasa kikace hakako nasan dasu miki dakin tsine musu😄 dariya sukasa tare da tafawa, sabreen tace Allah ya kareki dan seda nazo gidanku akan ki rakani, mama tace ta aikeki shine kawai na tafi ni kad’ai, munna tace kedai dason zuwa rafi yin wanka to ai nikam daga yau na tuba sedai kiyita zuwa ke kad’ai, sabreen tayi dariya tace nima na hakura daga yau😄
Haka sukaita hiransu har zaninta ya bushe ta shirya tsab ta koma gida. Slm mamata slm kakana, wslm suka amsa se kakanta yace sabreen idan kikayi sallama d’ayama ai yayi koko, dariya tayi tare da k’arasawa kusa dashi kan taburma ta zauna tare da d’aukan k’ok’on fura da nono ta bud’e ta fara sha tana cewa nawane ko kaka, mamanta tayi dariya tace seda kika fara sha zaki tambaya, sabreen tace saboda nasan nawane ai mammina. Haka sukaita hira da mamminta da kuma kakanta, bayan isha suka wuce d’aki itada mamminta a gado d’aya suke kwanciya yayinda suke jin d’umin junansu, mammi tana son ‘yarta sabreen fiye da komai sam batason wani abu ya sameta saboda rashin mahaifinta, sabreen ta katse mamminta daga tunani da takeyi tace mammina lallai kuna kaunata sosai keda kakana inama ace babana yana raye da gatan nawa yafi haka mammina, wai mammina ciwone ya kashe mahaifina ko menene dan Allah ki gayamin dan yanzu kam aina girma koh? Mammi ta sauke ajiyar zuciya tace sabreen mahaifinki ya rasu ne sakamakon ceto wayanda ba mutaneba😭, sabreen ta tashi zaune tace mammi me kikace😳

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *