Tarihin Feezy YNS ( Feezy Biography)
Cikakken sunan: Abdul Hafiz Abdullahi
Inkiya: Feezy
Kwarewa: Waka, Daukar Hoto, Mai bada Umarni
Matakin Karatu: Degree
Yan’uwa: Dj Ab, GeeBoy, lil Prince
Aure: Babu
Gari: Kaduna
Kasa: Nigeria
WANENE FEEZY
Cikakken sunansa Abdul-Hafiz Abdullahi Amma anfi saninsa da suna feezy yakasance Mai hada vidiyon Cartoon (Animator), Mai gyaran video ( video editor) Mai daukar Hoto (Photographer), Mai bada Umarni, Sannan mawaki Kuma Daya daga cikin mawakan YNS STUDIOS.
Karanta: Cikakken Tarihin Dezell (Dezell Biography)
Mafiya yawancin mawakan Yns Studios kamarsu Dj Ab, Zayn Africa dadai sauransu na amfanine da salon Rap wajen rera wakokinsu Amma shi Feezy na amfani da salon Waka na R&B Wadda Kuma za’a iya cewa yasamu gwarewa da Kuma tarun masoya a fagen.
HAIHUWARSA
An haifeshi ne a ranar shabiya ga watan satumba a shekarar alib dubu Daya da tari tara da casa’in da bakwai (1997) a jihar kaduna dake Nigeria.
KARATU
Mawakin yayi Karatunsa na primary dakuma secondary a Kaduna capital school dake malali jihar kaduna.
Bayan kammalawane feezy yasamu damar shiga makaranatar Jami’a ta Ahmadu Bello (ABU) Dake Zaria Inda yakaranci Ilimin computer.
YAN’UWA
Mawakin yakasance dan’uwa ne ga mawaka irinsu Dj Ab, lil Prince, T swags, Dakuma GeeBoy Wadda duk sunkasace Yan Yns Studios ne kamin ficewar T swags daka kungiyar.
Mahaifinsu ne yakafa musu studio nasu maisuna Yns Studios a cikin Gida domin Basu kwari gwuiwa dakuma taimaka musu wajen cika muradansu.
Karanta: Cikakken Tarihin Bash Ne Pha
Fara wakokinsa
Feezy ya farane da wakarsa maisuna Anfara Physics wakarsa sukaita tareda Geboy dakuma wiz mo daga bisani yafito a wakar Subabane wakarsa takasance hadakace ta kunkiyar Yns studios.
Jerin wakokinsa
Izuwa yanzu mawakin yayi wakoki samada talatin 30 daga ciki akwai
– Anfara Physics
– Su babane
– Yo baby
– Toy Friend
– Rainani
– lie ft Mr kebzee and sagee
– Lolo
– feelings
– I’m with you baby
– Don’t you mind
– I’m sorry
-Party
-Amana
-Spy
-One in a million
-Juyo
-Poison
Wakokin Hadaka
Siddabaru Tareda Dj Ab & lil Prince
Happy sallah Tareda Geeboy
Tsoro Tareda lil Prince & Geeboy
Amana Tareda Marshall, Kebzee & Geeboy
Dasauransu
Domin Karin bayani dangane da Tarihin Feezy YNS ( Feezy Biography) ku ziyarci YouTube channel namu a NwHausa TV.