TATTALIN TA
CHAPTER 1
*A* hankali nake k’arasawa kusa dashi daga inda nake da tsaye a gefe ina kallon, matattakala shiga gurin nabi cikin wani irin taku wanda bana son ajine bare a gane d’aukar rahoto nazo yi na isa kusa da shi inda bazai hangoni ba sai dai ni na ganshi na tsaya. Kallon inda suke yake yi cikin wani salo kamar baya son a gane hakan, kallon shi nayi dan tantance kaman nin shi da tsarin shi. wankan tarwada ne dogo mai nagartaccen tsayi, ma’abocin ingarman jiki, da cikakkiyar fuska d’auke da yalwar dara-daran idanu da wadataccen dogo siririn karan hanci mai kyau, ga kuma yalwar girar idanu kwantac ce game da kwantacce mai laushi na gashi a kowan ne ga6a da take buqatar hakan.
Kallon su ya sake yi ta gefen ido ya hango yayan na shi ya zauna a kusa da ita, ita kuma sai murmushi take yi tana rufe fuska wanda da alama kunyar shi take ji, bayan ya zauna ne yayan shi ya kalle ta shima yana murmushin a hankali yake jiyo maganar su ya kasa kunne ya jiyo me zasu ce yaji yayan nashi na tambayar ta,
“Me kike yi zaune anan kinyi shiru kina tunani, ko ni kike tunawa ne?”
Saurin rufe fuska yaga tayi sai faman kakkauda kai take ta na kuma dariya kasa-kasa, yayan nashi ne ya kuma yin magana karo na biyu yana kallonta yace
“Sanar dani mana, me kike yi anan wajan ke d’aya?”
Cikin sanyin muryar ta me dad’i tace,
“Yaya hadda nake so nake na rik’e su kar gobe ayi min gwalo a islamiya, malam Jabeer yasa ayi min dariya.
*K*allon mamaki yayi mata ganin cewar wai yin hadda ne ya fito da ita resting area tsabar bawa kai wahala duk filin cikin gidan ga d’akin ta ma amma ta fito nan. Kura mata idanu yayi cike da kulawa yace mata.
“Uhm, haddar me kikeyi naji ku kin iya?”
Murmushi ta tare da k’ara rufe idanu dan ba k’aramin kunyar shi take yi ba, gashi tana ganin girman shi hakan yasa take jin kunyar shi sosai, tana susar kumatun ta tace mai a hankali.
“Cewa aka yi muje mu haddace sheka-shikan musulinci guda biyar, gobe kowa zai fad’a duk wanda be iya ba za’a mai dariya.”
Yayi murmushi tare da kallon ta yaga sai faman murza yatsunta take yi, cewa yayi mata.
“Toh naji lissafosu naji, idan kin kakare sai na tuna miki dan bana son ‘yan ajinku su yi miki dariya sai dai ayi miki kabbara.”
A nutse ba wani karab-karab ko rashin nutsuwa a tare da ita ta fara lissafomai cikin wakar da aka yi musu ta gaya mai sai dai tana yi tana yarfa hannu wajan tunanowa ta ce nafarko.
_1. Tauhidi 2. Azumi 3. Zakkah 4. Hajji 5. Sallah._
Shida yake gefe guda ba’a kasa dashi ba yayi ma tamkar besan suna yi ba amma cikin ranshi sai da yayi mata kabbara, shafar kanta yayan yayi cikin jin dad’i yace,
“Barakallahu fihi ya ukuti.”
“Kin yi kokari duk kin iya gobe dole ayi miki kauta kiyiwa wasu gwalo.
Dariya suka yi ya kama hannunta suka wuce cikin gida, shi kuwa da kallo ya bisu tare da ta6e baki ya kasa gane irin shakuwar da ke tsakanin su. A hankali shima ya mik’e yayi side d’insu yana y’in ball da duk wani abun da yagani a kan hanyar shi ta wucewa ciki kuwa harda handset d’in drive na gidan daya sa waka yana ji yana gyaran tayar mota. Da kallo kawai ya bishi cikin ranshi yayi Allah ya isa dan yasan yana sane yayi….
Washe gari bayan tayi sallar asuba dama bata komawa sabida zuwa Tahafis karfe 6:00am ba zasu dawo ba sai 10:00am, tana gama shiryawa ta fito zuwa d’akin Umma kasan cewar haka suke kiranta. K’arasawa tayi ciki har k’asa ta kai tana gai da ita amma tayi mata banza, dama tasan ba amsawa zata yi ba ta kuma mik’ewa ta bar d’akin tana jin kewar iyayenta da suna nan da ba zata yi kuka ba kuma baza’a wulakanta ta a haka ta k’arasa compound d’in gidan tana kokarin fita daga get taji an yi mata horn tare da haska fitilar motar. Cak ta tsaya tare da bin motar da kallo sakamakwan ba ta son ko wace a ciki ba, reverse yayi har ya k’araso gurinta ya tsaya ba tare da yayi magana ba, ta gane nufinshi hakan yasa ta zagaya ta shiga. Bayan ta zauna sun bar gidan ta kalle shi a tsorace ganin sai faman had’e girar sama da ta k’asa yake yasa tace.
“Yaya Zulkhalnai ina kwana?”
Wata muguwar harara ya zabga mata lokacin sun sha kwanar layin tahafis d’in kasan cewar babu nisa. Ta gane abin da yasa ta samu hararar tunda tasan baya son wannan sunan amma take fad’a mai, k’in amsawa yayi ya karasa yayi parking yak’i ce mata koma tace,
“Na gode Yaya Allah ya saka da alkairee.”
A cikin ranshi ya amsa, itakam tasan ba kulata zai yi ba hakan yasa ta bud’e kofar ta fita, tana fitowa taga wasu ‘yan ajinsu suka jera tare yana kallon su har suka shige sannan ya juya ya koma gida. A tsaye yaga Umman su ta had’e girar sama da ta k’asa tana kallon shi, yasan abin da ya sa ta yin hakan yayi parking sanan ya k’arasa inda take, kusa da kafarta ya durkusa da nufin gaishe da ita tayi saurin da katar da shi ta hanyar d’aga mai hannu tare da cewa cikin tsawa….,
“Ka rik’e gaisuwar ka ba na so, sai da ka gama aikin waccen kuyangar sannan zaka zo kace zaka gaidani ni dana haife ka..!”
Tamkar jira yake tak’i amsawa ya mik’e tsaye yana karkad’e wandon jikin shi, baki ya lasa ya kuma kallon Umman tasu yaga still shi take kallo sai yaji duk ba dad’i ya kuma duk’awa yace,
“Kiyi hakuri Umma na ki amsa gaisuwa ta dan Allah.”
“Ina kwana Umma na?”
Ya kuma fad’a yana kallon yatsun kafar ta da suka sha jan lalle da bak’i suka yi wa k’afar kyau.
Sai da ta dad’e sannan ta amsa mai a dak’ile, mik’ewa yayi tare da tsayawa a kusa da ita ba tare da yayi magana ba yana kallon wata tukunyar fulawa, kallon shi tayi tana magana cikin nuna 6acin rai akan abin da yake yi tace,
“Yanzu kai *Sultan* dab kara d’aurewa yarinya kugu nan da Tahafis sai ka d’auki mota ka kai ta?, ina lura da kai fa tun shekaran jiya da ka shigo gidan nan sai wani abubuwa kake yi mata ko zaka gaya min dalilin haka?”
Shiru yayi tare da kuma yin k’asa da kai, mamakin Umman su yake ta yadda ya lura sam ita bata kaunar *Balqees*, yarinya karama kuma marainiya da take bukatar kulawa da jin dad’i na uwa amma bata samu ba kasan cewar sun koma ga mahaliccin su, amma Umma ta kasa d’aukar d’awai niyarta bare ta jata jikin ta taji damuwar ta bare ta bata mulawa, sai kishin ta da take yi ya rasa dalilin yin haka. Muryarta ce ta katse mai tunanin da ya tafi tace.
“Shi kenan tafi, sai ka fito yin breakfast.”
“Toh, kawai yace ya wuce side d’in su, kan gado ya fad’a ya fara tunanin lokacin da yaje gidan uncle Rahim kanin mahaifin shi lokacin da zai tafi lagos yi musu sallama, yana shiga yaga aunty Rahama Matar shi tana sharya abinci a dining table, sallama yayi tana ganin shi ta fad’ad’a fara’ar ta tare da yi mai Oyo yo, a falo ya zauna ta karasa suka gaisa dan tana da matukar k’irki sosai, suna hira ne uncle Raheem ya shigo tare duk suka k’arasa gurin cin abincin ana ta hira har Balqees ta shigo da gudu ta dawo daga school da uniform masu kyau ajikin ta, Sultan yayi mamaki da yaga ta juyo ta gaidashi ba tare da ance tayi hakan ba sai yaji dad’i ya kuma rabbatar da lallai yarinyar tana samun ingantacciyar tarbiya, anan ne kuma uncle Raheem yake cewa,
“Ina son naga ina kula da mace a cikin rayuwata, budurwa, yarinya, tsuhuwa koma wace irice indai macace ina son ganin na bata kulawa nagartacciya. “Sultan ka kwautatawa mace domin abar tausayi ce, karka ce sai naka kawai a’a na kowa ma dan mace na buk’atar kulawa sosai, nidai ko a gaban idona ko bayan idona Sultan ina son ka kula min da Balqees ta samu ingantacciyar kulawa.”
Bayan ya bar gida da wata biyu yaji waya cewar Uncle Raheem da aunty Rahama sun yi accident Allah yayi musu rasuwa, daya zo gaisuwa ne ya tarar da Abban su ya d’auki ragamar Balqees sai ya tuna da hirar su da Uncle d’in nashi yace a ranshi da zuciyar shi yanzu kenan ya komai mai TATTALIN MACE?”… Anya zai iya kuwa yadda baya d’aukar raini yaje karamar yarinya ta rainashi? Toh ya zai yi bayan yasan kamar amana Uncle d’in nashi ya bashi. A hankali ya rintsa ido tare da d’aga hannu sama yana addu’ar Allah ya bashi ikon cika burin Uncle Raheem, mikewa yayi ya shiga bathroom yayi brush sannan ya dawo ya shiga cikin bargo dan yin bacci
Zaune suke a sitting room d’in gidan hajiya kaka mahaifiyar su Abban su, gaba d’aya ‘ya’ya da jikok’in ta duk sun zo ana zazzaune Uncle Jalal ya bud’e musu taro da addu’a sannan aka yi addu’ar cika shekaru biyu da rasuwar iyayan Balqees, bayan an shafa ne hajiya kaka ta kalli alhaji Abdullah mahaifin su Sultan tace,
“Ina maganar mu ta kwana?”
“Hajiya tana nan ai, yanzu sai abinda kika ce haka za’a yi.”
Zama ta gyara tana kallon jikokin nata maza su biyar tayi murmushin jin dad’i kafin ta ce.
“Ina Abduljamal?”
“Hajiya gani nan.”
Ya fad’a yana kallonta, kowa ita yake kallo yayin da Balqees ke zaune kusa da ita tana rubutu cikin wani note book. Hajiya ta kuma cewa,
“Ina Abu Ahmed?”
“Uhm…”
Kawai Sultan yace ba tare da ya bud’e baki yayi magana ba, tana jin abin da ya fad’a amma tayi kamar bataji ba ta kuma cewa,
“Yana ina ne?”
Da sauri Balqees da waheedah suka had’a baki wajan cewa,
“Ya fa amsa hajiya.”
“Ohho ai ni banji ya amsa ba kune dai kuka ci mai tuwo da miya dan haka kumin shiru shine zai amsa.”
“Ina Abu Ahmed?”
“I’m here.”
Hajiya tace,
“Yanzu naji batu.”
“Toh ina kuma ibraheem, Al’eem da Yusif?”
Duk suma suka amsa “hajiya gamu nan muma.”
Magana ta fara yi dai-dai sannan Umman su Sultan ta shigo, bayan an gaggaisa ta samu guri kusa da mijinta ta zauna Hajiya kaka ta ci gaba da magana.
“Abin da yasa nace kowa yazo ina son muyi abin da zai kara karfafa mana zumunci, ina son muyi abun da zai kara had’e mun kanku wanan kuma ba komai bane sai ta hanyar had’a aure tsakanin yaranku. Alhaji babba ya kuka gani na san dai kuma zaku bani goyan baya kamar yadda na san idan na fad’i magana bakwa k’inta?”
Tayi maganar tana kallon Abban su Sultan kasan cewar shine babba a cikin ‘ya’yan ta. Murmushin jin dad’i yayi tare da k’ara nuna goyan baya akan abin da ta fad’a, cikin nuna gamsuwa mai cike da biyayya duk ‘ya’yan na ta suka amin ta in ka d’auke jikoki mazan da suka harhad’e rai jin an ambaci auran zumunci kar suje a had’a su da wadda hankalin su be kwanta ba. Iyaye matan ma fuskar su a had’e take dan kowa sake-sake yake kar a had’a ‘ya’yan sa da wanda basa so, hajiya kaka ta ci gaba da cewa.
“Toh dama kowa na yi mishi sha’awar auran ‘yar uwar sa wanda nake fatan zaman zai d’ore, fata na guda d’aya kar wani ko wata su bani kunya a cikin duk wanda na bata/bashi. Kusani duk d’aya koke a guri na babu wanda yafi wani sai wanda yayi min abin da nake SO.”
Yaran hajiya kaka guda biyar ne uku maza biyu mata, kowane yana da ‘ya’ya, alhaji Abdullahi shine babba mai yara biyu Abduljamal (Yaya jamal) da Abu Ahmad (Sultan), sai marigayi Abdulraheem da yake da Nana hafsat (Balqees), sai Adda Aisha me yara uku, Ibraheem (heemu), Waheeda (Heeda), da Bilkisu (billy) sai Uncle Abduljalal yana da yara biyar, Yusif (sufee), Al’eem (shaheed), sai twins Aisha (A’i) Fateema (teema) sai Jamila (Nawal) sai hajiya Ma’u tana da yarinya d’aya Firdausi (feedoh).
**** **** ****
Duk sunyi shiru suna sauraran Hajiya kaka, kallon Yaya Jamal tayi tare da cewa,
“Jamal kai ne babba, dan haka na had’aka da Waheeda ganin kune manyan cikin su.”
Kallon juna suka yi tare da sakin murmushi dan dama can akwai soyayya a tsakanin su, cikin nuna amincewa jamal ya kalli hajiya kaka tare da cewa.
“Toh hajiya Allah ya had’e kanmu, ya kara girma da lafiya.”
Amin aka ce kowa yayi farin ciki dan ganin basu watsa kasa a ido ba, amma fa Umman shi ba ta so ba dan ita tana da matan da zata aurawa ‘ya’yan ta, sai dai tayi shiru da nufin ba zata yadda abawa Sultan kowa a cikin su ba dan ta hakura da had’in su jamal amma daga shi babu k’ari. Kowa yayi murna ba kamar iyayan yaran, hajiya kaka ta kuma kallan inda ibraheem yake zaune sai faman cicin magani yake, bakaramin haushin taron nan yak’e yi ba musamman idan ya tuna cewar wai zabar musu mataye ake ji yake tamkar ya make kakar tasu dan itace ummulabaisin koma, jiyayi kawai tana cewa.
“Kai kuma heemu na had’aka da jameela, kuma ina fatan zaku so junan ku da amana, ku kuma rik’e zumunci.”
Wayyo Allah zo kuga 6acin rai domin kuwa anyi rashin sa’a ba ya santa, a 6angaran Nawal kuwa murna ce fal cikin ta dan ba karamin kaunar Yaya heemu take ba, sai gashi yau Allah ya rufa mata asiri an had’asu, damuwar ta d’aya da ta ga yayi kicin-kicin alamun baya farin ciki. Hajiya kaka ce ganin yadda yayi taji duk ba dad’i sannan ta kalli iyayan taga duk sunyi shiru tace mai,
“Hemmu ko ba so a canza maka da wata ne?”
Yayi shiru ba tare da ya amsa ba, cikin jimami mahaifiyar shi (Adda Aisha) ta kalle shi tace,
“Ba uwata ka wulakanta i.b taka ka wulakantar a idanun ‘yan uwanta sakarai kawai.”
Yayi saurin kallon mahaifiyar tashi yana ware idanu jin abinda ta fad’a yace,
“Amma mama ni me nayi haka kika fad’i wannan maganar? Dan Allah ki gafar ce ni amma wallahi ni bana son fushin nan naki bala’i ne a gare ni.”
“Yanzu dai kana nufin ka amince da za6in hajiya kenan?”
Abban Sultan ya tambaye shi yana kallon shi, “eh.” Yaya heemu ya fad’a yana kara d’aure fuska sai dai ba kamar farko ba, nan da nan farin cikin Jamila ya karu jin ya ce ya amince.
“Toh kai kuma Aminullahi mai babban suna, gaka amin tacce sai ku had’a kanku da fiddausi, kuma zaman ina jinshi a jikina zamu samu karfin zumunci insha Allahu
“
“
Ba tare da ya kalli kowa ba bare a gane wani abun ya yarda ko be yadda ba ayi mai wani abun gaban yara su raina mai hankali yasa shi cewa,
“Allah yasa hajiya.”
Haka kurum ya fad’a be kara cewa komai ba, itama fiddo uwar shan kamshi karama da ita sai uban girman kai babu wanda ya gano yanayin ta hakan yasa aka yi murna suma tare da sa musu albarka, aka koma kan Yuseef wanda ke faman cizon lips yana harara harare, duk da kowa yasan dama ba kunya gare shiba hakan yasa hajiya ta ware mai mai hakurin cikin su ga kunya hajiya kaka tace.
“Kai kuma na baka Bilkisu, dama ka fi kowa san yin aure a cikin su toh gashinan nayi maka mata.”
“Uhm, wallahi ni dai bana so ahe, babu wanda ya isa yayi min auran dole dan ina da wadda nake so zan aura.”
Cewar Yuseef yana wani buga kirji yana zazzaro magana. Dama ba kunya gare shi ba, babu wanda beji ciwon abin da ya fad’a ba idan ka d’auke mahaifin shi wanda dama can shine ya shagwa6a shi, cikin nuna halin ko in kula Mahaifin shi yace.
“Ya isa toh mana, tunda kace ba ka so ai shikenan sai ka kawo wadda kuka yi maganar da ita ba shi kenan ba.”
Babu wanda be ji haushi ba hajiya kaka ta kalli Alhaji Abduljalal d’in cikin nuna 6acin rai da yadda ya goyi bayan d’an nashi akan maganar ta, sai kace be ga yadda Adda Aisha ta yiwa na ta d’an ba, da 6acin rai ta kalle shi tace.
“Maganar shi ka d’auka akan tawa?”
“A’a hajiya gani nayi ai tunda yace yana da za6i sai a hakura abashi tunda ai duk aure ne.”
Shiru tayi mai ganin shima yana nema nuna mata iyaka ta kalli Sultan duk da ranta zafi yake sai dai ba ta nuna ma ta ce mai.
“Ahmad kai kuma ga Aisha nan sai ka aure ta.”
Ba tsoro ba shakka yace,
“Kaka nima bana son kanwar shi gara a bani Balqees na raineta a hannuna amma ba zan auri Aisha ba……”
Ya kalleta tare da lumshe ido ya bud’e su tana jin mutum sai dai bata mik’e ba ta k’ara komawa ta kwanta, ajiyar zuciya yaji tana ta faman sauk’ewa, yaja d’an ja tsaki kamar ya fita sai yaji ba zai iya ba tunda amanar shi ce, ba dan karya nuna mata mahaifiyar shi tayi laifi ba da har k’asa zai duk’a wajan bata hak’uri amma sai ya daure cikin nuna kulawa dan so yake ya de na tunawa da abinda Umman tashi ta yi a cikin ranshi dan hakan da mahaifiyar shi keyi, gaban shi har fad’uwa ya ke yi idan ya tuna abinda tayi, he have to cautioned Balqees d’in da kanki kanta ta dena tuna mishi da abun dan ko babu komai at least for the mean hours, ya kuma matsawa gurin ta yana saukar da ajiyar zuciya ya zauna gefen tare da cewa.
“Am sorry sister.”
Bata ce da shi komai ba haka ma bata motsa ba daga kwancen da take yace.
“You should rest now sister please kiyi shiru kije ki wanka kizo kici abinci dan Allah.”
Kai ta dinga gir-giza mai kawai ba tare da tayi magana ba, ganin hakan tana son 6ata mai rai itama yasa shi mikewa tare da daka mata tsawa yace ta tashi, mikewa kuwa tayi da sauri tana matsar hawaye tare da ajiyar zuciya tana kallon k’asa yace,
“Fito da kayanki mu tafi.”
Idanuwa ta zaro tana kallon shi cikin ranta tana mamakin inda zai kaita, ganin fuskar shi a had’e ne yasa ta yin sauri ta d’auki mayafin after dress d’in ta ya jiya ya fita ta bishi a baya tana jan trolley d’in wadda ta dawo da ita. Mota suka shiga ta zauna ya dayar suka bar gidan, shiru dukan su babu meyin magana sai ita dake faman zubar da hawaye suna ta fiya a hankali har suka yi nisa ya samu guri yayi parking ba tare da ya kaleta ba yace.
“Kukan nan ya isa haka sister, yanzu zan kaiki inda zaki ji dad’i kiyi abinda kike so ba tare da an hantare ke ba kinji ko?”
Kai ta d’aga mai tare da sunkuyar da kai k’asa, ya kuma kallonta yana tunanin yadda zasu kwashe dasu Abba idan ya koma gida yace mata.
“Baki tambayi inda zan kaiki ba ko bakya son kiji?”
“Ina so sai dai bana son na tambaya ne sabida nasan ba zaka kaini inda za’a takura min ba.”
Motan ya tayar kawai ba tare da yayi mata magana ba ya hau titi suka tafi, gidan hajiya kaka suka shiga yayi parking suka fito ya rufe Motan suka jera yana ja mata trolley d’in. Dogon saurayi had’ad’e ita kuma ‘yar k’arama da ita dan iyakarta wajan kugunshi da temakwan hi’ll shoe d’in kafarta yasa tayi dai-dai cibin shi a haka suka shiga cikin parlon hajiya kaka wadda ke zaune tana jan carbi, tana ganin su ta fara murmushin murna tana fad’in.
“Sannunku mutanan waje daga dawowa nan kukayo salan ku cinyan tuwo na.”
“Hajiya kakus tawa, wallahi I miss you sosai.”.
Ta fad’a tana rungume kaka, shi kuwa har rintsa idanu yake idan yaga tana gudu dashi sai yaji tamkar a kafan shi yake. Kusa da hajiya kaka Balqees ta zauna shima Sultan zama yayi suka gaisa da hajiya kaka tana ta samai albarka da irin hidimar da yake yi da marainiyar Allah, anan ta kira me aikin ta aka kawo musu abinci suka zauna a k’asa suna ci tare cikin farin ciki ba kamar Balqees da take jin tamkar ita kad’ai ce a cikin duniyar. Yana kammalawa ya mik’e yana yiwa hajiya kaka sallama bayan yayi mata bayanin cewar anan zai bar Balqees shi kad’ai zai wuce anan suka yi sallama ya tafi gida.
***** ***** *****
“Daddy time yayi fa, Balqees ta dawo jiya tana gidan hajiya kaka dan haka lokacin da zan aure ta yayi.”
Kallon shi uncle jalal yayi tare da yin murmushi ya tashi zaune daga kishingid’an da yake, kallon shi yayi tare da cewa,
“Good boy! Ya kamata dai ka samu ka janyo hankalin tar ta aurreta mu samu bukatar mu ta yi.”
Yuseef ya shafa ha6ar shi tare da murmusawa yace,
“Karka damu daddy zan aurota za kuma ta soni ai ni ba kalan yardarwa bane.”
“Matsalata kawai da ita yaron nan ne Sultan, duk yabi ya kanainaye ta tamkar wani ubanta.”
“Karka damu babu ruwanka da ita, fatan mu kawai ka aureta ai ta dawo kark’ashin ka babu yadda zai yi da ita duk tattalin shi gare ta sai ka yadda ma zasu had’u.
Daddy y fad’a yana kara karfafa mai gwaiwa, da haka ya bar sitting room d’in with full confidence ya koma side nashi yana naushin iska da hannun shi.
**** ***** *****
Sultan na komawa gida side dunshi ya wuce yayi wanka sannan ya kwanta ya huta, bayan sallar isha ya fito zuwa side d’in Umman tashi ya gansu tare da Abban shi da kuma Yaya Jamal anata zancen auran su da za’ayi nan da one month. Gurin zama ya samu yana sunkuyar da kai dan ganin da yayi Umma na watsa mai wani mugun kallo, Abba ya gaidar sannan ya mik’awa Yaya Jamal hannu suka gaisa sannan yayi wa Umma sannu ba tare da ya kalleta ba, ta amsa da kyar dan tasan ya gano laifinshi.
“Sultan ashe can gurin Hajiya ka maida Balqees?”
Abba ya fad’a yana mik’awa Jamal phone d’in shi da ya nuna mai hotunan k’ofufin gidan shi da za’a sa mai. Cikin biyayya ya kuma sunkuyar da kai tare da cewa.
“Eh Abba cewa tayi can zata koma kwana biyu sai ta dawo nan.”
Abba yayi murmushin jin dad’i tare da kallon matar tashi yace,
“Toh kinji ita ta bukaci tafiya ba shi ya kar zoman ba har kina fad’an cewa shine baya son zaman ta a gidan.”
Ita dai Umma shiru tayi amma tasan shine ya zuga ta tunda ya nuna rashin jin dad’in shi lokacin da ga tayi mata fad’a, sharewa kawai tayi amma tana jin haushin wannan abun na Sultan