TATTALINTA
CHAPTER 12
Sosai suka yi yawo duk inda suka je sai abokan sa sunyi mai tsiya sai dai kawai ya share su, basu koma gida ba sai bayan sallar isha’i duk sun gaji dan haka kowa d’akin sa ya shiga dan kimtsawa.
….
Sai da cikin Nadiya ya kai watanni biyar sannan suka gane cikin da take da dashi, murna a wajan sultan ba’a magana har fad’a yayi mata sabida 6oye mishi cikin da takeyi dan haka tayi mai ana humaira ma.
Shirye-shiryan bikin Nabeelah su Nadiya suke yi duk da cewar cikin ta ya tsufa amma babu inda bata zuwa, shima Yusif an sanya ranar auran su inda ya yadda zai auri bilkisu ‘yar gidan Adda Aisha, sai k’anwarsa Aisha da itama ta hakura da Sultan ganin ba samun sa zata yi ba tsakanin su da Nabeela sati d’aya.
Nadiya na kwance a d’aki tana bacci kasan cewar ta d’auki hutun haihuwa a asibiti yayin da Balqees dasu Jamila su Fiddausi dasu Aisha ke zaune a parlor sun saki teburin hira kowa na fad’ar matsalarsa Balqees ta yatsinna fuska tare da cewa.
“Ni babu abinda yake damuna irin ta rashin son ganin Yaya Sultan a shimfid’a da su nan raya sunnah, wallahi yayya waheeda duk lokacin da naga Yaya zai kusance ni wani tsanarsa nakeji tun da nazo gidan nan ban ta6ajin ina so ba, ina karanta littattafai ina son nima naji dad’in da ma’aurata ke samu amma ina! shi yasa Yaya ina kallon shi wallahi duk ranar da yake d’akin Mmn humaira har wani rawar kai yake yi, kona nuna 6acin raina sai yasan yadda yayi ya hillatar dani ya tafi, magunguna kuwa nasha su kamar hauka har na dena shama ni, ga azabar ciwo banajin uban komai.”
Da sauri Nadiya dake k’ok’arin fitowa zuwa parlor ta koma da baya tare da zama a bakin gado, duk taji abin da Balqees ke fad’a, nan da nan gumi ya fara karyo mata jikin ta ya hau rawa zuciyar ta ta fara bugawa.
Dafe kai tayi sabida jin da tayi yana juya mata, a hankali ta kwanta tare da rintsa ido, shin meyasa basu gaya mata ba daga shi har Balqees d’in, ko basu san cewa babban ciwo bane ga rayuwarsu gabaki d’aya, basu san cewar itama tana da hakk’i akan su ba na kare mata lafiyar ta…
Wannan toilet infection d’in illa ne kuma d’aukar shi ake yi, meh yasa sun san cewar ga abin da ke faruwa amma sukak’i sanar mata dan itama ta kare kanta? sunfa had’a miji suna kuma shiga toilet d’insa suyi duk abinda suka ga dama, wato su suna nemarwa kansu magani ita kuma ko oho.
Ta dad’e a kwance tana sak’a da warwara, da kyar ta mik’e ta shiga toilet tayi wanka sannan tayi sallan azahar da tajiyo ana yi, ruwan tea tasha kawai sabida tana son idan taje gidan bikin su Nabeelah taci dambu (wanda aka bawa realy mai Dambu tayo sabida gwanace wajan iyawa lol). Cikin shirinta ta fito tayi masifar yin kyau duk da cikin dake jikinta, lokacin basa parlor duk sun koma cikin d’akin Balqees d’in, a hankali ta k’arasa tare da yi musu sallama Feedo ta amsa dan ita ce kawai zaune su sallah suke yi, jin an amsa yasa ta shiga fuskarta da fara’a tace.
Story continues below

“Hajiya Fiddausi hutawa ake yi, ina boye d’in ne kika barshi..?!”
“Uhmm aunty Nadi kenan yanzu sai nayi ta yawo dashi?yana can gurin abban sa kin san basa rabuwa kamar magnet haka suke.”
Dariya Nadiya tayi jin abinda tace sai ta k’arasa bakin gado ta zauna Feedo ta kasa had’iye abinda ke wuyanta dan haka tace.
“Gaskiya aunty Nadi kinyi kyau ba k’arya.”
Murmushi Nadiya tayi tana kallon Feedo, hak’ik’a bawai yau ta fara jin wannan kalmar ba, a duk lokacin da zata shirya ta fito to insha Allah baza ta cire kwalliyar nan ba sai an samu wanda zai ce tayi kyau cikin fara’a tace.
“Na gode Fiddausi.”
Hira suka d’an fara yi har su Balqees d’in suka idar sannan tayi musu sallama ta tafi, Jamila ta kalli Balqees tana kad’a kai kafin tace.
“Gaskiya Balqees kina cikin tashin hankali amma baki gane hakan ba kin wani zauna sai kishin banza dana wofi kike yi, yanzu ke sai ki zauna a haka tare da wannan zuk’ek’iyar Matar kuma kisa ranki cewar miji sai yafi kaunarki? Bari kiji broth yana sonki yana tattalinki ne kawai dan dama da hakan ya taso yana miki, ba ta yadda za’a yi a ce kana zaune da mata d’and’asheshiya ga ilimi biyayya wayewa uwa uba tasan ta yadda zata tafiyar da mijinta da kuma wadda sai dai kici ki kwanta kin kasa gyara shimfid’ar mijinki kice wai kin fita a gurinsa k’arya ne wallahi,
Bari kiji na gaya miki yawan yiwa miji laifi ko yayane yana sa soyayya ta ragu. ki dena ganin cewar ai broth d’anuwanki ne wallahi yana sanyawa sonki ya ragu a cikin zuciyar sa, don haka idan kishiya kike da ita ta fiki nuna ladabi zuciyar mijinki za tafi kaunar ta kekuma kidawo kina cewa ai wance tayi mai asiri ta rabaki da mijinki.
Kishi, babu mutumin da zai ta6a cewa kada mace tayi kishisa, amma ana so tayi shi da hikima a kuma sauk’ak’e, wannan yana matuk’ar taimakawa ‘ya mace ta samu k’ima a gurin mijinta.
“Nana Aisha tayi kishi, kinga kenan babu yadda za’a yi ace mace kada tayi kishi, ita da kanta (Nana Aisha) ta ke cewa, bata ta6a yiwa wata mace kishin da tayiwa Nana Khadija ba, amma daga lokacin da manzon Allah (s.a.w) ya tsawatar mata sai ta d’an sassauta ta daina.
A cikin wani hadith an fad’a cewa, akwai kishin da Allah yake so, da akwai kuma wanda baya so, don haka sai ki d’auki wadda Allah yake so, kishin dake da akwai tuhuma a cikinsa, kamar Matar da koya mijinta ya k’ara lokaci akan lokacin dawowarsa gida sai ta tuhume shi dajin ina ya tsaya, amma da zaran kuma taga ya fara fad’a sai ta yi tunanin wata ce ta fad’a masa wani kalma yaji dad’i sai ita kuma ta zama tamkar hukuma a gurin mijinta, kullum cikin zarginsa kike, rashin sauk’ak’a kishi shi yake janyowa mace zuwa gurin bokaye ko matsubba wa’iya zubillah dan haka ya kamata kisan kanki ki nemawa kanki daraja Yaya Sultan gwanine wajan sauk’ak’a kanshi a kan mace burinsa yaga ana *Tattalin mace* a kuwane guri domin Umma (Adda Aisha) tana bamu labari tace shi abinda yake k’ona masa rai be wuce yaga ana wulakanta mace ba, hakan yasa lokacin da za’a fitar mana da maxaje aka had’a Yaya sufee da billy yace baya so shine abin ya bashi haushi shima yace baya son Aisha wai duk dan ya konawa Yusif d’in rai amma cewa tayi da Yaya sufee ya yadda toh ko baya son Aisha zai aureta a haka.
Ke ko soyayyar nan baki iya ba sai dai ki jira yayi miki, da ‘yan wasannin nan, an gaya miki shi baya so? Kin zauna sai wani ban zan kishi kike yi marar asali bare tushe, zuciya fa tana son mai kyautata mata dan haka ki canza taku babu abinda zata nuna miki in dai kika yi biyayya, tsawo kawai zata nuna miki shi kuma wannan halittar Allah ce karki damu..”
Yatsina fuska Balqees tayi domin bata son ma ta ina zata fara ba jiki a sanyaye tace,
“Toh ni yanzu ya zanyi? so kuke na dinga yadda ina shan wahala, tsanarsa na kuma ziyar tar zuciya ta? A da bana jin haka amma daga zuwa na school na kwaso wannan bala’in gashi yana neman hanani kwanciyar hankali.”
Story continues below

“Za’a san abin yi gaskiya dole a samo miki magani.”
Waheeda ta fad’a tana kallon Balqees cike da tausayawa. Shiryawa suka yi dan tafiya gidan hajiya kaka kasan cewar acan ake shirye-shiryen. Cikin kwanciyar hankali su Nadiya suka gama gudanar da bikinsu sai dai kemudugus Sultan yace baxa taje kai amarya Lagos ba karta je ta haihu a can. Ana gama na Nabeelah aka shiga na su yusif, anyi bidiri sosai amare da angwaye ba kamar Yusif dama ya k’aro wulak’anci gashi abin nashi akan kowa yake be rage ba.
Da Balqees aka yi komai domin ita bata rik’e shi ba duk da abinda yayi mata, bayan an gama komai da kwana uku Nadiya ta haihu ta haifi zurkud’ed’iyar budurwa masha Allah tamkar Sultan yana jariri. Murna da farin ciki a gurin su tamkar itace haihur farko da aka yi musu, komai a gidan aka yi dan cewa yayi babu inda za’a je, abin mamaki kayan jarirai akwati guda Yusif ya aikowa da Nadiya masu matukar kyau da tsada babu wanda beyi mamaki ba sannan kuma aka yi ta sanya albarka.
Ranar suna baby taci sunan hajiya kaka wato Hawwa suna kiranta da Islam, hajiya ta dinga murna tayi takwara itace harda kayan barka da kud’inta. Anyi taron suna kowa yaci yasha mai jego tayi kyau hakama Balqees iyayen ‘ya, bayan kwana biyar k’afa ta d’auke da dare bayan kowa yaje ya kwanta sai ga Sultan ya dawo d’akin Nadiya, farkawa tayi ta ganshi zaune ya kafe su da ido ta tashi zaune tana kallon shi.
“Abban humaira lafiya na ganka haka ana?!”
Kauda kai yayi gabaki d’aya ya rasa yadda zai yi da Balqees dan yanzu daya zo mata da buk’ata zata fashe mai da kuka yanzu abinda ya faru kenan yasa shi baro d’akin ba arzik’i, sake kallonsa Nadiya tayi cike da tausayawa cikin karyar da kai tace.
“Abban humaira baza ka sanar min ba? ko da yake wata kila tsakaninka da Matar ka ne amma zan so ka dinga yi mata uzuri dan baka san matsalarta ba, kayi mata a hankali karkaja tsanarka ta shiga cikin zuciyarta alhalin kai take gani taji dad’i a cikin rayuwar ta. Kad’an bata lokaci zan san yadda zanyi wajan ganin hakan bata faruwa, haka kurum sai wahalar min da miji take, zo nan zo ka gani…”
Ta fad’a tana nuna masa kan cinyar ta, Kanshe ne yake d’aurewa a duk lokacin da yaga Nadiya ta gano halin da yake ciki tamkar wata me aljannu, tasan duk wani motsin shi ba tare da ta tambayar shi ko ta takura mai da jin ba’a siba.
K’in tashi yayi ya hau girgiza mata kai tamkar wani yaro, shi yanzu ma baya jin sha’awar ganin haka yasa ta mik’ewa daga gadon ta koma wajan shi cikin hikima da dabara Nadiya tasa shi a lokacin ya kawar da buk’atarsa ba tare daya kusan ce ta ba sannan ta lalla6a shi ya koma d’akin nasa, a zaune ya tarar da Balqees tana faman kuka duk sai hankalin sa ya kuma tashi da kyar ya samu ya shawo kanta tayi shiru bayan yace mata ya dena takura mata.
…..
Bayan sati d’aya Nadiya ta fita compound, wajan Hamisu mai gyaran flowers ta k’arasa bayan sun gaisa yake tambayar ta,
“Hajiya lafiya dai ko naga kin fito da kanki?!”
“Lafiya lau Hamisu aikenka zanyi dan Allah, so nake yi dan Allah ka samo min wad’annan abubuwa a Islamic center kace a baka _saiwar zogale, saiwar gogamasu, saiwar cindaguza da jar kanwa_ dan Allah kayi sauri please ina jiran ka.”
Dubu d’aya ta bashi ya tafi ita kuma ta shiga gida, a parlor ta tarar da Balqees d’in tana zaune tana taya Sultan recording a cikin laptop shi kuma yana gefe yana cike-ciken wasu takardu, k’arasawa tayi ta zauna hira suke yi sama-sama domin aiki kawai suke yi ba kamar Balqees da ta bada himma, suna nan zaune Hamisu ya kwankwasa Nadiya ta mike ta k’ar6o ko d’ari biyar ba’a kaso mata ba ta k’ar6a ya bata cangin tace ya rik’e ta bar masa dama Hamisu yasan zata iya barmai domin macace da abin hannunta baya rufe mata ido.
Kitchen ta wuce da ledar a hannunta cikin su babu wanda ya d’ago ya kalleta ta wuce ta kunna gas cooker, tukunya ta d’akko ta zuba ruwa sannan ta zuba magungunan a ciki sannan ta sanya jar kanwar kad’an ta tafasa su, tacewa tayi sannan ta d’akko kofuna guda uku ta zuba a ciki ta d’aura akan tray ta fita zuwa parlor. Sultan ta fara kaimawa tace.
“Oga d’auki ka sha naka”
Kallon kufinan yayi ya ganshi wani irin kalla sai ya k’alleta da mamaki yace,
“My Nadi menene wannan kuma?!”
“Maganin mallaka ne, kaga idan kasha muka sha to baza ka sake yin wani auren ba mu din nan dai mune dai..”
Murmushi yayi yana mata wani irin kallo ta kashe masa ido d’aya itama tare da sake tura mai tray d’in, hannu yasa ya d’auka yana cewa.
“Toh ya zan yi dama yanzu ma kun mallakeni ina ga nasha maganin mallaka..”
Dariya tayi ta k’arasa wajan Balqees wadda domin ta duk takeyin haka tace,
“Maman humaira d’auki naki kema.”
Kallon kofin tayi sai kawai ta mayar da kai tana aiki tace.
“A’a ni dai aunty Nadi ku shanye kawai.”
Rasa me Nadiya zata ce mata tayi, bata son nuna mata cewar tasan matsalar ta dan babu kishiyar da zata so hakan. Rausayar da kai tayi sannan ta kuma mik’a mata tace.
“Ki kar6a kisha bazan ta6a yin abin da zai cutar da ku ba domin Allah baya barin mai zalinci musamman akan makoci da makusanci ungo.”
Sake kallon kofin tayi amma bata k’ar6a ba ganin haka yasa sultan kafa kai ya shanye nashi sannan ya kallesu yace.
“Baby d’auki kisha mana na yadda da Nadi fiye da yadda kike tsammani.”
Tana faman yatsina fuska ta k’ar6a, sai da taga Nadiyan ta shanye nata sannan itama tasha da kyar tana yamutsa fuska har ta shanye
Haka Nadiya ta dinga dafa magungu na tana sanya musu a tea plx, shine ya zama ruwan shan su musamman tafi bawa Balqees tun bata so har ya zama na da kanta wata rana take dafawa. Sai da suka yi sati biyu suna shanshu sannan ta kuma sawa Hamisu ya siyo mata _Makuba, hulba da sassak’an mangwaro_, suma dafa su tayi sannan ta kaiwa Balqees tace ta din ga sha tana kuma zuba mata a bahu tace ta shiga, haka take yi mata tun Balqees tana girman kai har ta dena da kanta takan tambayi Nadiyan wasu abubuwan haka shima maganin ta shashi ta shiga ciki tsawon kwana goma sha biyu, ranar da ta gama sha Nadiya ta had’a mata ‘yan shila aure d’aya tasa mu nonon rakumi da rid’i tayi farfesu d’inshi, Balqees na daga d’aki ita da Sultan da Islam ta jiyo kamshi ta fito har ta k’arasa kitchen inda rake jiyo k’amshin nan taga Nadiya tana juye farfesu cikin kula tace.
“Kai aunty Nadi ina kwance na jiyo k’amshi me ake yi mana ne?!”
Janyo ta tayi ciki tana lek’a bayan ta wai ko ya biyo ta sai ta nuna mata tace,
“Ga naki nan kiyi zaman ki anan ki cinye ki shanye roman tass karki yi magana duk abinda ya faru har sai gobe nima ga nawa dan kar mu zauna muna ci ya shigo ki gama naki idan naga kin shigo na san kin gama…”
Fita tayi da sauri ta shiga d’akin Sultan dake kwance yana aiki domin shi ba dai ka ganshi zaune yana zaman banza ba, kullum cikin rubuce-rubuce yake da danne-danne cikin laptop, tana shigowa yasan itace sabida k’amshinta na musamman ne duk inda ta shiga cikin mata dubu sai ya san cewa tana gurin.
“Zo nan my Nadi..”
Ya fad’a ba tare da ya bar abin da yake yi ba kuma be juyo ba, kan gadon ta hau tare da kwanciya akan bayansa ta zura kanta gefen wuyan sa tace.
“Gani meh zan samu..?!”
Juyowa yayi da ita ta koma kan gadon shi kuma ya dawo saman ta tare da cewa,
“Bari kiga abin da zaki samu tun da kink’i yin wanka ki fara sallah ni kuma na samu wani abun a wajan ki..”
Be bari ta yi magana ba kawai ya hau yamutsa ta yadda yaga dama ita kuma ta biye mai, sun dad’e a haka kafin su hakura kowa na yiwa d’an uwansa kalon yayane. ‘Yar hira suka fara ta6awa Sultan yana manne a jikinta, sai da yaji motsin tafiya dan kar yaji kunya yasa Nadiya mik’ewa zaune ta zauna a gefensa duk da tasan da Balqees ce baza ta d’aga shi ba, sai ga Balqees d’in ta shiga tana faman lasar le6enta ta kalli Nadiya tace.
“Wallahi aunty Nadi da kyar na gama.”
Nadiya tayi dariya tare da mik’ewa tayi waje tana cewa,
“In dai kin gama d’in ai da sauk’i haka muke so mu.”
….
Da dare bayan sun gama hira dama tun da Nadiya ta haihu Sultan ya koma gurin Balqees shi kuma sabida ganin bata son yana nemanta yasa shi denawa hakan yasa kullum yake da burin ganin Nadiya ta tsarkaka gashi kamar kwanakin nak’in yin sauri kuma jinin yaki d’aukewa.
“Gaskiya ni dai sai da safe wallahi bacci nake ji.”
“Kai Nadi tun yanzu? Dan Allah ki tsaya mud’an k’ara wani lokaci.”
“Abban humaira kasan fa halin Islam, idan ba bacci tayi ba nima banayi, yanzu kuwa tunda tayi sai naje muyi tare ko ta farka kaga nima na rage.”
“Haka ne toh sai da safe.”
Story continues below

Ya fad’a yana kashe mata ido d’aya, tafiya tayi tana yi masa dariya shi kuma ya bita da kallo har ta shiga.
“Madam muma Mu tafi namu makwancin ko?!”
Balqees ta kad’a kai sannan suka mik’e ya Kama hannun ta suka wuce bedroom, kan gado ya fad’a yayi ruf da ciki ita kuma tana tsaye tana d’aura towel sai ta bishi da kallo tana jin wani abu cikin jikin ta, juyowa yayi ya kalleta idanun sa sun kankance yana bin ta da wani shu’umin kallo yace.
“Wanka?!”
“Uhmm.”
“Toh jiki yi, kona zo na taya ki.”
“A’a zan iya.”
Tashi yayi tare da janyo ta yana kallon cikin idanun ta, sam sai taji ta kasa kallonsa illa wani abu da taji yana taso mata a game da shi, ta lumshe idanuwa, zare towel d’in yayi yana d’an tsora-tsoran kar tayi mai bori sai yaga sa6anin haka dan gani yayi ta fara sauke wani irin numfashi, ganin haka yasa shi ci gaba da shafarta cikin dabara, nan da nan kuma yaga Balqees ta shiga yana yin da tun da yake da ita be ta6a ganin ta shiga ba hasalima da kanta take mai wasu abubuwan yanzu.
Mamaki da al’ajabi suka cika zuciyae Sultan sai kawai ya fara gwada yin wanda take ma kukan, gani yayi ma kamar itama so take yi, a ranar jin Balqees yayi a wata daban itama ma kuma ya tabbatar da ta samu abinda take so sai kuma ta saki kuka mai matuk’ar ratsa zuciya yabi ya rud’e ya fara lallashin ta yana mak’ale da ita a k’irjinsa.
A hankali yaji tana riko hannun shi jikin sa duk sai yayi sanyi, yau yaji ta daban ni’ima kuwa tama yi mata yawa zai iya cewa, domin be ta6a jin ta haka irin yau ba, murya k’asa-k’asa yake sanya mata albarka tare da kalaman kauna masu zafi da be gaya mata su a baya ba, idanunta a rufe tace.
Gabaki d’aya ta d’aure mai kai da kalaman ta, shin alkairin Nadiya ya shugo cikin Balqees ne da sai yanzu ta fara ganewa, ko kuwa dai ita Balqees d’in ce ta fara gane cewar Nadiya fa bata da matsala sai dai fatan cikawa da imani kawai domin shi sai yace be ta6a ganin tayi abin asha ba! ya kwantar da ita a k’irjin sa yana shafar ta tamkar yau ya fara ta6a jikin nata yace.
“Me tayi miki?!”
Balqees tayi shiru dan ba ta san ta in da zata fara yi masa bayani ba, ta sake rungume shi tare da cewa.
“Ita ce silar da yasa kaga yau ban guje kaba Yaya wanda ina yin haka ne ba da son rai na ba, ita ce silar da tasa naji a yau nima na cika cikakkiyar mata a wajanka, na kuma tabbatar da cewar nima mutum ce Yaya kayi mata godiya karka barni wajan gode mata ni kad’ai.”
“Toh insha Allahu baby domin nine ma ya kamata nayi godiyar tunda ni aka gyara mawa, tunda gashi har na kwashi gara da tuni na kwana ina juyi.”
Shareshi tayi dan da alama sambatu yake yi, da wayo da dabara sai da sultan ya kuma yi ranar kwana sukayi cikin nisha d’i da walwala yayin da Balqees ta kuma jin soyayyarsa na sake karuwa a cikin zuciyarta tamkar goya shi. Shi kuwa jiyayi wata zazzafar kaunarta tana kuma bin jinin jikinsa da kyar suka samu yin baccin rabin awa dan suna kwanciya aka kira sallah.
Nadiya kuwa lokacin da dare ya tsala kasa rintsawa tayi sabida data rufe ido Sultan take hangowa yana making love da Balqees dan ta tabbatar ko shi be nuna yana so ba toh ita sai ta nuna dan ta tsumu sosai, da kyar da hailala a bakinta da zuciya ta samu tayi bacci tunda ba damar yin sallah.
*Some month’s ago*
Ahmad Sultan kam ya kuma samun kwanciyar hankali ta 6angarorin guda biyu dan kowacce tana iya bakin k’ok’arinta wajan ganin ta kwantar da kai a gareshi, yayin da shi kuma ya bud’e musu k’ofar zuciyarsa yana kulawa dasu sosai musamman Balqees da bata da inda zata kai kukanta sai gurinsa, ko 6ata mata yayi idan ta gama kukanta dole shi zata zo ta sanarwa abinda yake damunta sabida shine uwarta kuma shine ubanta, hajiya kaka girma ya kamata sosai tana buk’atar hutu da kwanciyar hankali hakan yasa bata iya zuwa ta gaya mata dole shi take zuwa suyi shawara su kuma lallashi juna.
Zaune yake a office d’insa yana aiki wajan k’arfe d’aya da kwata, wayarsa ya d’akko yana neman layin Balqees cikin sa’a kuwa ringing d’aya ta d’auka ta kara a kunnenta tare da mak’e murya cikin shagwa6a tace.
“Yaya na gaji wallahi 6hours muna zaune ana lecture.”
Cikin damuwa yana zaro ido tamkar tana ganinsa yace.
“What! 6hours?, wannan wane lecture ne haka?!”
A shagwa6e tace,
“Biology mana Mrs okeke..”
D’an tsaki yayi tare da cewa,
“Kin ga zo nan office d’ina muga yadda ya wujijiga minke…”
Cikin jin dad’in kulawarsa tace,
“Toh gani nan zuwa, amma ni jinake kamar ba zan iya zuwa bama, k’afafuwa na tamkar zasu cire da bayana ma.”
“Kina ina yanzun?!”
Tace, “ina depertiment d’in Mu.”
“Toh tsaya nazo na d’akkoki.”
Ta lumshe idanuwa tana jin wani shauk’i a cikin zuciyar ta, aikuwa suna tsaye da su sdy da sauran k’awayanta ba kunya yaje yace tazo, office d’in nasa suka koma ji yake tamkar ya d’auke ta a hannu ya k’arasar da ita ciki. Suna shiga kuwa ya saka key ya rufe k’ofar, k’arasawa tayi kan kujera ta zauna tare da cire zumbulelen hijjab d’inta wanda ya zame mata wajibi gurin sasu idan zata zo school, k’arasawa yayi shima ya tsuguna a gabanta ita kuma tana shafo masa kai.
“Toh ya…?!”
“Ba komai sallah zanyi sabida muna da wata lecture d’in.”
Shima hannu yasa yana shafar fuskarta murya k’asa-k’asa yace.
“Ba kya jin yinwa?!”
D’an yatsina fuska tayi tace,
“Inaji Yaya amma ba yadda zanyi dole nayi sauri idan nayi sallan na tafi.”
Yace, “Nop kiyi sallanki bari naje na samo miki wani abun kici, idan kika gama sai na rakaki babu lecturen da zai takurawa matata..”
Tashi yayi tare da yi mata peck a saman goshinta sannan ya fita tare da kulle office d’in, toilet d’in ciki ta shiga tayo alwala sannan tayi sallah, be jima ba sai gashi ya dawo ya zauna a gabanta tare da bud’ewa ya tura mata,
“Oya ci ki k’oshi ki huta sai na raka ki.”
Fried rice ce da gasassar kaza sai farfesun kifi da yake tana so da drinks masu sanyi, takura mai tayi suka ci tare duk da cewar a koshe yake taci ta koshi ta huta sannan yaje ya raka ta students sai gulmarsu suke yi ita dai Balqees ta share su bata kulasu ba.
Sosai Sultan yake kulawa da *Tattalin matansa* ba ta yadda za’a yi wani ya gane ga wadda yafi karkata akanta, hatta su kansu matan nashi ba wadda zata ce yafi son ta akan d’ayar domin duk ya toshe kafofin da zasu nuna hakan sai dai kawai a cikin zuciyarsa (ni kaina na kasa ganowa bare na sanar daku..lol).
Kusan a tare suka shigo gidan, Nadiya ta fito daga cikin mota hannunta rik’e da jakarta ga kuma Islam a hannunta da sauri Sultan daya gama parking da motar Ummansa dan yanzu shi yake amfani da ita tunda yak’i siyan tashi. K’arasawa yayi wajan Nadiya da sauri yana murmushi yayin da Balqees ma ta fito tare da rufe motar, itama k’arasawa tayj yana zuwa ya rungume su Nadiya da Islam yana cewa.
“Sannunku da dawowa, my cutie.”
Yayi maganar yana kar6ar Islam sannan ya juya cikin gida, sanu da dawowa suka yiwa juna suma sukabi bayan sa. Shekara d’aya kenan da wata biyu shekarun Islam har kuma lokacin Allah be sa Balqees ta samu koda 6arin ciki ne, abin yana damun ta sosai.
Kassan cewar Balqees ce yau a karaga yasa suna shiga tabi bayan Sultan d’aki yayin da Nadiya ma ta shiga nata, basu dad’e ba nanny d’in humaira ta dawo da ita dan haka suke yi kullum kassan cewar duk basa gida yasa Nadiya take kaita gidan Ummi idan sun dawo sai a dawo da ita, fitowa parlor Nadiya tayi bayan tayo wanka ta shirya tayi wa su humaira ma sai ta zauna dan jiran abinci. Shiru-shiru yasa ta koma d’aki dan tunda taga baya saman dining table ta san ba’a kammala ba.
Awanni biyu tsakani dama aiki Nadiya take yi a cikin d’aki sukuma yaran sunyi bacci suna farkawa suka fara kuka, kallon humaira tayi tace.
“Ke kukan nan ya isa haka jike gurin Maman ki kice ta baki abinci kici, oya sai ki kawo kuci da Islam..”
Humaira na kukan ta fita d’akin Sultan ta fara zuwa babu kowa a ciki dan haka ta kuma rushewa da kuka ta wuce d’akin Balqees. Kwance ta tarrar da ita da littafi a hannunta tana karatu tana ganinta ta mike zaune tare da kiranta tace.
“Ummina waya ta 6aki kike kuka..?!”
Cikin kukan da gwarancinta tace,
“Mamah zanci abinci inji Mommy anan.”
Yatsina fuska Balqees tayi tare da kallon humaira, hawayen ta goge mata da majina sannan ta ce.
“Jiki ce da Mommy ta baki shayi kisha mai dad’i.”
Sake komawa wajan Nadiya humaira tayi tana shaahek’a, kasa ma magana tayi da taje jin irin yadda take kuka yasa Nadiya kallonta tace.
“Toh menene kuma humaira? Ta baki abinci..?”
“Mommy zanci abinci da shayi uhmm-uhmm.”
Jin abinda ta fad’a ne yasa Nadiya ta fara yi mata fad’a a tunanin ta ko an zuba mata zafi garai ko kuma tafi son a bata a baki ita, kuma ta san Balqees ce meh yi mata komai. Tashi tayi tare da d’akko Islam suka fito zuwa parlor sai faman fad’a take yiwa humairan, abincin ta din ga nema bata gani ba sai kuma tayi shiru tare da shiga kitchen d’in tunanin ta ko humairan da ta fito bata ga Balqees d’in, Amma abin mamaki babu alamun anyi girki a kitchen d’in, fitowa tayi ta k’arasa d’akin Balqees ta ganta a kwance hannunta rik’e da waya da alama charting take yi dan sai murmushi take yi abin ta. Nadiya tayi sallama Balqees ta amsa ba tare da ta d’ago ba humairan kuma ba ta dena kukan ba Nadiya tace.
Story continues below

“Maman humaira ‘ya’yan ki kuka suke yi zasu ci abinci, na d’auka ma kin yi ina zuwa na tarar bama a d’ora ba.”
Ta k’arasa maganar tana kallon ta, abin da ya d’aurewa Nadiya kai shine ganin ko kallon ta Balqees ba tayi ba tana danna wayar ta tana d’add’aga girar ta tace.
“Eh ban d’ora ba gani nayi bamu dad’e da shigowa ba shi yasa na bari sai bayan sallan isha’i sannan na dafa ko indomie ce, sai dai nace a had’a musu tea su sha ko bata fad’a ba da taje.”
Kan Nadiya ya d’aure kawai ta tsaya tana kallon Balqees, tsayowar ta gyara sannan tace.
“Toh Maman humaira kin manta ta dena shan shayi yanzu sabida amai.”
“Toh gaskiya ni dai sai dare zan d’ora girki yanzu karatu nake yi kin san dai exam zamu fara…”
“Ikon Allah, dan Allah Maman humaira me yake faruwa ne? Idan wani abun ne be kamata ki yi shiru ba zaman tare be ce haka ba sai ki gaya min ni kuma zan baki hakuri na kuma gyara kuskure na, amma be dace ace kiyi shiru ba sai dai naga sauye-sauye a tattare dake ba.”
“Nifa babu abin da ya faru kawai dai exam zan fara gara na din ga sequzing d’in lokutana ina bawa karatuna muhimmanci.”
Nadiya ta kuma kallonta sannan jiki a sanyaye tace,
“Ban san damuwarki ba amma karki manta muna da hakki akan ki, kuma yaran nan gidan sune idan ba’a tashi an basu ba a ina zasu jesu ci? karki manta ba haka muke yin abun mu ba, duk inda mai girki taje ta dawo ita zata yi girki koda kuwa baza a ci a lokacin da ta gama ba, amma ban san uzurin ki ba Allah ya kyauta.”
Tana kaiwa nan taja hannun su humaira suka fita, kitchen ta shiga mamaki da al’ajabin abinda Balqees tayi, shin meh yake shirin faruwa a tsakanin su? Tunda take bata ta6a jin zata cuci Balqees ba koda kuwa da wasa ne sabida bata san k’arshenta ba a duniya, shin meh yasa ta fara can zawa? Ko dai an shiga tsakanin su ne? Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un, ita Nadiya ta dinga maimaitawa a haka har ta kammala dafa musu dankali suka koma parlor, zama tayi ta din ga basu zuciyar har lokacin bata dena mamakin Balqees ba, tana gamawa suka koma d’aki ita kuma humaira tace gurin Maman ta zata wato Balqees bata hana ta ba ta wuce da Islam ciki.
Koda Sultan ya dawo suka had’a duk a parlor babu meh yiwa wani magana, sam Sultan be gane ba dan babu wadda ta nuna mai wata alama, da Nadiya zata tafi d’aki sai da tayi wa kowannen su saida safe amma still Balqees bata kula ba hakan be yiwa Nadiya zafi ba ta wuce d’aki kawai tana musu fatan alkairi, bata sani ba idan ta kwanta zata farka ko kuwa ta Allah zata kasance, Allah kad’ai masani babu wani bawa da zai kwanta yace zai tashi domin rayuwar sa tana gurin mahaliccin mu.
Washe gari Nadiya na farkawa da kanta ta had’awa su humaira breakfast suka ci sannan tayi mawa Sultan sallama tayi tafiyar ta ko sanya Balqees a idanunta bata yi ba. Har tsawon kwana uku suna a haka babu me shiga harkar wani. Ranar Sunday kowa yana gida yayin da sultan yaje gida ya gaida su Umma, yana shigowa parlor yaji ana yada magana, muryar Nadiya yaji tana cewa.
“Wallahi Bilkisu kin bani mamaki, ni ba zan yi dake ba domin ke ba sa’ar yi na bace dan haka duk wani take-taken ki nayi min rashin kunya baza su d’aga min hankali ba, na rasa gane inda kika nufu, na tambaye ki idan wani abin nayi miki bisa kuskure ki sanar min amma kin k’i, abin ba akai na ya tsaya ba harda su ‘ya’yana da ba suji ba su gani ba toh abin naki ya isheni idan kuma shi Ahmad d’in ya san kina min wannan abubuwan toh zai shigo sai ya gaya min meh yasa.”
Ta6e baki Balqees tayi tana yatsina fuska gata ‘yar d’iris a gabanta amma hakan be hana ta yi mata fitsara ba,
“Nifa abin nan ya isheni nima wallahi, haka kurum toh da zaki min gorin ‘ya’ya ai kema Allah ya baki muma da be bamu ba bawai mantawa yayi damu ba, kar kuma ki manta nan gidan Yaya na ne kuma mijina dan haka ina ganin na fiki iko da gidan bana son nunkufurci abinci ne nace na dena girkawa kowa ya yi da kansa mana ah….”
Story continues below

Tsayawa kawai suka ga yayi yana bin su da kallo cikin tsananin d’aure kai, Zama yayi kawai akan kujera ba tare da yayi magana ba.
“Sannu da zuwa..”
Nadiya ta fad’a dan ko me za’a yi ta gan shi ba ta iya k’in kula shi ko yayane, banza yayi da ita dama ta san ba amsawa zai yi ba, shiru yayi kawai ganin haka yasa Balqees kud’ewa cikin d’aki ita kuma Nadiya ta samu waje ta zauna tayi shiru.
“Jiki kira min ita ta dawo..!”
Kamar bata jishi ba dan har zai kuma maimaitawa sai kuma yaga ta mik’e, fuskar ta baza ka ta6a gane a wane yana yi take ba. A k’ofar d’akin ta tsaya yana kallonta ta kawar da kai tace,
“Ki fito yana kiranki.”
Tana kaiwa nan ta juyo ta koma ta zauna. Balqees kuwa tafi minti talatin bata fito ba hakan kuma ya sake kona masa rai sai gata ta fito tana wani lasar lips taje ta zauna kusa dashi, ba tare daya kalleta ba yace.
“Tashi ki koma can inda take kema.”
“Kai Yaya ni….”
“Bana son magana biyu ki yi abin da nace.”
Tashi tayi tana faman cono baki, can nesa da Nadiya ta zauna tana faman girgiza k’afa, d’an satar kallon su yayi sannan ya mik’e tsaye ya koma kujerar tsakiya ya zauna sannan ya fara magana.
“Ban yi tunanin tun ina da rai zaku yi min haka ba, kunci amanata kun ha’inci yardar dana yi muku. Na yadda daku na baku amana ta da ta yarana amma ashe ku ba haka bane, shin ku gaya min dame na rageku? Ku sanar dani abinda nake muku har ya janyo kuke wannan abu…?”
Shuru suka yi babu wadda tayi magana, ganin haka yasa shi kallon Nadiya tunda itace babba ya bata girman ta yace.
“Nadi gaya min meke shirin faruwa a cikin gidan nan.?!”
Tace, “ka tambaye ta nima haka na gani rana d’aya lokaci d’aya, wallahi abban humairah ni dai ban san abinda nayi mata ba daga ni har su humaira.”
Wani mugun kallo ya watsawa Balqees wanda bata ta6a ganin yayi mata kwatankwacin irinsa ba, saurin kawar da kai tayi tana motsi da baki murya a kausashe yace.
“Ina sauraranki meya ke faruwa a cikin gidan nan..?”
“Ni babu komai.”
“Karya kike yi ki sanar dani meya had’a ku.”
“Ni nace ba komai..”
Ya kalleta sannan ya buga mata harara yace.
“Wani sabon salon iskancin ne kika shigo min dashi cikin gida? Baby dama ba kya kauna ta ko? yes! dole na tambaya domin da kina sona baza ki kawo min tashin hankali cikin gida ba, a rashin mutuncin naki ma harda ‘ya’ya na wad’an da nake tunanin idan babu ni babu Nadiya wata rana zaki rik’e min su da amana kamar yadda nayi miki ashe ba haka bane?
Karfa ku manta fa kwanciyar hankalin ku shine nawa, farin cikin ku shine nawa, jin dad’in ku shine nawa, walwalar ku itace tawa and baby karki manta da ace Nadiya ta bijire wajan cewar ba zan aure ki ba da na tabbata ko auran nayi ba zan samu kwanciyar hankalin ba ko auran ki ba ko da nayi to bazan samu kwanciyar hankali ba.”
“Sannan karki manta da hallaccin da Nadiya tayi miki duk da cewar har yanzu ban san abin da ya had’a kuba, amma ina son baby ki din ga bawa Nadiya respect kamar yadda kika ga ina yi mata ba wai dan wani abun ba, tayi min hallacci a rayuwar ta, bata son damuwa ta sannan tana son duk abin da duk ta san ina so hatta ke da kike kishiyar ta tana sanki kwatankwacin yadda nake sonki tun kafin ma muyi aure, idan kuka ce zaku fara yin irin wannan abubuwan wallahi..wallahi..wallahi kunji na rantse muku duk ranar da kuka sake yin irin wannan abun zaku nemini ku rasa, Allah ya bani ikon yin mata hudu sai na bar muku gidan naje can hankali na kwance kukuma still kuna matsayin matana dole dai nine naku dan ba sakin ku zanyi ba, dan haka ku kiyaye, bama naso naji ba’asi fatana ku ajiye ko meye a side…”
“Uhmm..uhmm…uhmm Allah sarki iyaye na, mutuwa mai yankan kwana, mutuwa mai yanke buri, mutuwa mai mayar da mutum maraya. Yaya yau ni kake yi ma gori kai da matar ka? Nima bani na hana kaina haihuwar ba daya bani nima dana ce ga ‘ya’yana, Yaya yau ni kake cewa wai bana sonka, dama an ce min akwai rana irin wannan da zata zo gashi na ganta da ido na. Shikenan ni yanzu bani da kowa, bani da me sharemin hawaye na, babu wanda zai lallasheni bare ya bani shawara Allah ka d’auki rayuwata nima na mutu na huta, Allah yasa na mutu yanzu ko Yaya zai samu farin ciki ya tabbatar da cewar nima ina son farin cikin sa, ya Allah ka….”
“Shut your mouth up…! Baby kina da hankali kuwa? Ni kike cewa gara ki mutu ki barni sabida na huta? An gaya miki mutuwarki ce zata sanya ni cikin farin ciki? Baby ko so kike ni d’in na mutu dan kije ki auri wani shi yasa kika tsoro min ta wannan hanyar?!”
Ya fad’a yana dafe saitin zuciyar sa a dalilin yadda yake jin tana tsananin bugawa tana yi masa zugi da rad’ad’i, ita dai Nadiya kanta na k’asa bata ce musu komai ba hankalinta duk a tashe yake, Balqees kuwa banda gurzar kuka babu abinda take yi, ji yake tamkar yaje ya rungume ta ko ya samu rad’ad’in da zuciyar take masa ya sassauta, jin kukan ta yake yi tamkar saukar ruwan guduma a cikin jikinsa amma yana son nuna mata kuskuran ta, yana son ya dai-daita gidan sa yayi musu adalci kar yaje ya cuci wata wadda zai kasan ce kuma itace mai gaskiya dan haka cikin dauriya da kai zuciya nesa ya kalli Nadiya yace……
“Kiyi hakuri kowan ne bawa dama yana da nashi kuskuren arayuwa, sannan be kama ta a ce na yi miki wani abun wanda baki ji dad’in sa ba ki yi shiru wannan ba irin zaman da manzon Allah (s.a.w) ya koyar damu bane, amma duk da ni ban san abinda nayi miki ba to ki yi hakuri, ki gafar ce ni kowa ne d’an Adam ajizi ne Allah ya baki hakuri ni dai har ga Allah na yafe miki..”
Banza da ita Balqees tayi ganin haka yasa Nadiya tashi ta koma d’akin ta ko ba komai ta fita hakkin ta, alwala tayi taje tayi sallah tare da kai kukanta gurin ubangiji akan Allah ya kawar musu da fitina, ya kawar da shaid’an d’in da yake son shiga tsakanin su.
Duk abin da yake baya kula su ko ruwa yake so da kanshi yake zuwa ya d’auka sam shima ya share su dama kuma Nadiya ce ke kula shi Balqees tunda ta shiga d’aki bata fito ba, da dare yayi ma shigewa d’aki yayi ya kulle da Nadiya taje a kulla taji sa abin ya kuma d’aga mata hankali ta hau bubuga mai tana kiransa amma fur yak’i bud’ewa. Washe gari tafiyar daban-daban aka yi kowa ya tafi inda zashi, da suka dawo Balqees ko kallon d’akin Sultan bata yi ba abin ya d’aure mai kai ganin ba ta da niyar zuwa ita ta bashi hakurin nan ma ya share su itama Nadiyan ta dena kula shi tayi ganin kamar tana takura masa.
Ganin haka ne yasa shi tashi ya shiga d’akin Nadiya, zaune ya ganta saman sallaya ta idar da sallah tana aiki a laptop d’inta. K’arasawa yayi kusa da ita ya kwanta saman cinyar ta, aikin ta ajiye ta fara shafar kansa ya lumshe idanuwa. Gaskiya Nadiya tana kaunarsa jibi duk irin wulak’ancin da yayi musu amma ta kulashi, be san me zai yi mata ba a rayuwar sa darajar ta kuma sake k’aruwa ya lumshe ido be san lokacin ma da bacci ya d’auke shi ba dama duk kwanakin baya samun baccin sabida yana fushi dasu.
‘Yar albarkar bata ko motsa ba dan karya tashi kafafuwan duk sunyi sanyi amma haka ta zauna tana mai fifita da wani file, ya dad’e yana vacci, yana farkawa ya ganta sai kallon shi takeyi ta sakar mai murmushi ya mike tare da rungumu ta jikinsa murya k’asa-k’asa yake furta mata kalmomi na ban hakuri da soyayya Nadiya sai hawaye kawai take yi dan tasan tana matuk’ar kaunar shi hakan yasa take shanye duk wani wulak’ancin da zai yi mata, uwa uba kuma tana da biyayya muryar sa a hankali yace,
“My Nadi wanka nake so please.”
Yayi maganar kamar zai yi mata kuka, kallonsa tayi sannan tace.
“Toh tashi muje na taya kayi.”
Kamar wani sakarai ya mik’e ta kama hannunsa suka shiga cikin toilet d’in ta, sai da yasa ta suka yi su biyu sannan suka fito, d’akin sa taje ta d’akko mai kaya tana fitowa suka had’u da Balqees ta wani had’e rai ita dai Nadiya ta wuce, d’aki Balqees ta koma sai kuka, wato itace tsinanniya shashasha shine ya watsar da ita, ita ce baya so ashe dan munafinci yana zuwa d’akin Nadiya suna munafintar ta, nan da nan ta sake kullatar su haushin su ya kuma kamata tasha kukanta ta godewa Allah.
Story continues below

Sai dare tukunna ya shiga d’akin Balqees shima lokacin Nadiya ta tafi asibiti, kwance ya ganta daga ita sai wani mini skirt da have vest kanta babu d’ankwali ko juyowa ba tayi ba bare ta nuna alamun taji shigowar sa. A hankali ya k’arasa bakin gadon ya zauna tare da kallonta yana mamakin ta, cikin kawar da kai shima yace.
“Baby tashi zamu yi magana dake.”
Tace, “Ni kuma? A’a kodai makuwa kayi ne Yaya..?!”
“Eh watak’ila.”
Ya bata amsa a tsaye, ta yatsina fuska tare da tashi zaune tana ci gaba da latsa wayar ta, hannunsa yasa zai kamo nata tayi saurin warce wa tare da tsuke fuska yace.
“Au bazan rik’e ki ba Baby? Haka kika za6arwa kanki rayuwar? Karki manta fa ni mijin kine, amma idan zugaki ake yi toh daga yau kin dena zuwa makarantar na kansIle ta.”
Nan da nan hankalin Balqees ya tashi domin gobe ne zasu had’u da sabuwar k’awarta da tayi mai suna Asma’u tana da aure itace amarya dan haka ta had’u da Balqees tana nuna mata yadda Nadiya keyi mata, Asma’u najin haka tace ai Nadiya zata iya kasheta a haka yanzu tana yi ne dan idan ta tashi kasheta baxa’a yi tunani ita bace shi kenan ta yadda ta d’aurawa kanta gaba da Nadiya ba taji ba bata gani ba.
“Ni dai Yaya kayi hakuri ya za’a yi sai da karatuna yayi nisa zaka ce zaka ce na dena zuwa? Kuma da yake ita waccen Matar so ce ai baka hanata ba sai ni da yake ka tsaneni baka sona yanzu.”
Kallonta kawai ya tsaya yi ba tare da yayi magana ba, sai faman murgud’a baki take yi tana juya kwayar idanunta ya ta6e baki tare da kuma janyo ta jikin sa, nan ta hau bige-bige ita wai ya saketa ya dena ta6ata amman yak’i, a hankali ya zura bakinsa cikin nata yana wasa da harshenta nan da nan tayi lukus sai ma ta fishi son abin da yake matan.
“Sai na cinye wannan bakin da bashi da kunya, abinda Nadi baxa ta ta6a yi min ba kuma bata ta6a yi min magana irin wannan da kika yi min ba, idan itace ko nine bani da gaskiya haka zata ce abban Humaira kayi hakuri..”
Nan da nan ran Balqees ya kuma 6aci dan ta tsani tayi mai abu ya wani ce da Nadi ce kaza, yatsina fuska tayi murya a shak’e tace,
“Itama ai na munafinci ne kawai.”
Da sauri ya zare ta daga jikinta cikin yana yi na damuwa Sultan yace.
“No ba da ita kike ba kawai haka zaki ce min munafiki fak’at ba sai kin tsaya kwana-kwana ba, amma ki sani Nadiya matata ce kuma dan ina sonta na auro ta sannan sanadiyar hakurinta muke tare daku cikin kwanciyar hankali kafin ki tsiro da wannan sabon iskancin.”
“Dama an ce min ta asirce ka, dama an cemin kafi sonta toh ni da baka so ka sake ni mana! Wallahi nafi k’arfin wulak’anci, dama baka sona matarka kake so sabida ita tana da kud’i kana hawa motar ta dole ka dinga goyan bayan ta.”
Wani tukuk’in takaici ya kuma sark’e Sultan kawai ya kalli Balqees yana hango yarinta da rashin kunyarta mai yawa wadda be san ma tana da ita ba sai bayan sun yi aure, ko kuma dan sun had’a gado ne kuma oho.
“Naji, ki fad’i duk abinda zaki fad’a wallahi Baby baza ki sake zuwa makarantar nan ba sai hayakin kanki ya sauka, oya mik’o min wayar ki ma sai naga yadda kika koma sannan idan naga dama na baki.”
“Ni dai gaskiya Yaya wai ya zaka min haka ne?!”
“Hmm wallahi da Nadi ce bani kawai zata yi babu gaddama babu musu..”
“Wayyo Allah na na shiga uku, wai Yaya komai zaka yi min sai ka ambato wannan ni kam na shiga uku wallahi asiri tayi maka daman an gaya min ai.”
“Ba wani asiri Baby, Nadi ko hanyar gidan malami bata sani ba bare na boka, kuma munafikin daya gaya miki tana miki asiri Allah ya tsine mai ko waye, ke kuma kamar wata yarinya ana gaya miki magana kina wani yadda da Nadi ce wallahi ba zata yadda ba…”
Ai da gudu Balqees ta mik’e ta shige cikin toilet sai ta kuma 6arkewa da wani sabon kukan, baki bud’e yake bin k’ofar da kallo, daga cikin bayin yaji tana magana.
“Wannan duk alamu ne na asiri wallahi tallahi, idan banda asiri ace mutum baya laifi kuma komai ka tashi fad’a sai ka wani sanya sunanta, wallahi asiri ne na shiga uku ni Bilkisu naga ta kaina.”
Bakin k’ofar ya k’arasa yana k’iiranta amma taki amsawa, har cikin zuciyar sa yace,
“Baby kin zama abin da kika zama dan da Nadiya ce bugun far….”
Sai ya tuna ita example da Nadiyan ne bata so, juyawa yayi ya d’auki wayar ta dake kan gado yayi ficewar sa, baya son damuwar ta hakan yasa yake tattala ta amma sam yanzu bata gani da alama 6atagarin k’awaye ta samu dan haka ya fito dan kar ranshi ya 6aci.
D’aukewa juna k’afa suka yi, sam Nadiya bata sani ba sai dai kullum idan ta dawo zata tambayi me gadi Balqees ta dawo sai yace ai bata fita bama har tsawon sati d’aya. Yau tana dawowa a parlor ta tarar da Balqees din tayi bak’i gaisawa suka yi ta wuce d’aki dan yau akin safe tayi dan haka ta dawo da wuri.
Bata dad’e da dawowa ba sai ga shi shima ya dawo, kallon bakin yayi nan suka tsugunna suna “malam ina yini?!” Dama gwanine wajan iya shariya dan haka ya share su ya kalli Balqees itama shi take kallo kawai ya shige d’akin Nadiya, Asma’u k’awarta tabi shi da kallo har ya kud’e sannan ta sauk’e wata razanannar ajiyar zuciya wadda tasa Balqees tambayar ta.
“Ke kuma meye hakan…?!”
Ba kunya ba 6oye-6oye tace,
“Wallahi Balqees mijinki first class ne, kinga da ace ke kad’ai ce dashi? Wayyo Allah gaskiya kinyi saka ci da yawa da har kika bari uwar gidan ki take shanawa, jifa ko magana beyi miki ba ya shiga gurin ta, da ace Aliyu na ne baxai wuce gurin uwar gidana ba sai yazo na rage masa zafi na rikitasa da soyayya ta yadda zan zamu nice kawai a zuciyar sa..”
“Hmmm Ma’u kenan, nan da kike ganin Yaya bashi da wannan abun, idan kuna d’aki ke kya ce ke kad’ai ce dashi sabida tsagwaran nuna k’auna da soyayya uwa uba tarairayar macr, haka yake duk d’akin daya shiga abinda yake bani haushi dashi be wuce da nayi abuba ya wani ce da Nadiya ce..ce..ce..ce mtww wallahi ina jin takaici…”
“Balqees sai kin dage wallahi da kissa da naci.”
“Insha Allahu zan yi ina ma yi ni wallahi har na gaji.”
“Hee! Ku tashi ku fita ina son sakewa a gida na.”
Suka ji maganar Sultan fuskar sa ba yabo ba fallasa, a kunya ce su Asma’u suka bar gidan yayin da ya harari Balqees sannan ya koma cikin d’akin Nadiya, ganin haka yasa Balqees kuma rushewa da kuka har da su buga k’afa yana lek’enta domin tun sanda yaji ihun ta ya lek’o. Ganin babu sarki sai Allah ne yasa Balqees fara sakkowa domin kaunar Sultan tana tsikarinta daurewa kawai take ita a dole ana yi mata rashin dai-dai.
Ana gaban nin za’a fara exam suka shirya ya barta ta koma sai dai ya rabata da duk sababbin k’awayan ta, sun dawo ita da Nadiya suna hud’ar su sai dai ba kamar da ba domin Nadiya ta d’an yi baya-baya da ita sabida ba ta son abinda zai sake had’a su rigima….
_*Bayan shekaru biyu*_
Fitowa yayi daga cikin d’akin sa, zaune ya gansu ko wacce taci uwar kwalliya kamar ta gasa ya kalle su yayi murmushi zuciyar sa fess, sam basu ganshi ba domin Nadiya na kwance da cikin ta daya bayya na d’an watanni shida amma tamkar d’an wata takwas.
“Papa kaga ni dan Allah ana min k’unshi yayi kyau?!”
Humaira ta fad’a wanda hakan yasa suka juya suna kallansa, hard’e hannunsa yayi a k’irjin sa sannan ya fara takawa a hankali zuwa cikin parlor’n. Kallon yatsun humaira yayi wadda Balqees ta gama san yawa Rani tana hura mata da iskar bakin ta dan ya bushe kar ta 6ata jikin ta, zama yayi kusa da Nadiya yana kashe mata ido murya k’asa-k’asa yace.
“Sannu uwar biyu..”
Nadiya tayi murmushi tare da cewa,
“Yauwa abban biyu sannu da fitowa.”
Murmushi yayi a wayan ce ya zura hannunsa cikin rigar Nadiya yana shafa saman cikinta, hannunsa na cikin rigar ta ya kalli Balqees yace.
“Baby kawo min lemo please mai sanyi..”
Balqees ta tashi tana cewa “toh.” Humaira ta matso kusa dashi yayi saurin zare hannunsa daga cikin riga ya kalli Nadiya yaga tana mai dariya harda rufe ido ya d’an harare ta sannan ya kalli Humaira yace…
“Angel ya aka yi?!”
“Papa kace fa ka dena cewa Mami na Baby kuma yanzu ka kuma k’iranta dashi, a school an ce baby d’an k’ararramin yarinya kenan.”
Dariyar Nadiya ce tasa shi saurin juyawa yana kallon ta jin yadda ta ke mai dariya kamar ya bata wani labarin, itama Balqees da ta k’araso dariyar take yi taje ta zuba mai exotic cikin glass cup tare da mik’a mai sai faman dariya suke yi mai shi kuma duk ya ma rasa me zai cewa humaira, da kyar Nadiya ta tsayar da dariyar tana kallon humaira tace.
“Humaira ai itama Mamin ki itama tun tana jaririya papa yake ce mata Baby, sunan ta kenan amma ke bashi zaki dinga fad’a ba kin ji ko?!”
Humaira ta kad’a kai alamar taji Nadiya ta tsuke fuska tare da cewa,
“Ba kai zaki girgiza min ba cewa zaki yi toh Mommy.”
Turo baki humaira tayi tana kallon kunshin ta ciki-ciki tace.
“Toh Mommy.”
“Aha yanzu naji batu.”
Komawa tayi wajan Balqees ta rungumeta a hankali dan karsu Nadiya suji Humaira tace.
“Mami ke da kike babata ma baki da fad’a kamar Mommyn Islam, ita fad’a gare tafa harda Islam takewa masifa nace ta gudo wajan Mami na tak’i.”
Sultan yayi saurin kallon Nadiya shima tare da yi mata gwalo ya kalli Balqees da ta rik’e ha6arta baki bud’e saitin kunnan Nadiya ya kai bakin sa tare da cewa.
“Gwara ni amma naki babba ne an ce kin feye fad’a Mommyn su islam 😜.”
Kicin-kicin Nadiya tayi ta hard’e fuska tare da mik’ewa zaune, gyara zama tayi tana kallon su Balqees na shafar kanta tana cewa.
“Toh ki dena yi mata laifin da zata dinga yi miki fad’an kinji angeli? Zaki ga ta dena yi miki itama.”
“Toh Mami, kinga kunshi na yayi muje ki wanke min sai daddy ya kaini gidan Ummi na nunawa uncle imran.”
Story continues below

Tashi Balqees tayi tare da jan hannunta suka fara tafiya, muryar Nadiya suka ji tana fad’a ashe taji da sauri Balqees ta shige da humaira cikin d’akinta tana dariya, suna shiga ban d’aki humaira tace.
“Mami kinji ta ko? Haka take yiwa Islam tayi ta kuka ita kuma sai na bata hakuri sai tayi shiru…”
“Ai laifi tayi mata shi yasa, nima idan kika yi min laifi ai zaneki ma zanyi.”
Haka humaira ta dinga bawa Balqees labari ita kuma tana bata amsa dai-dai yadda zata d’auka, acan parlor kuwa Nadiya ce ki ta salati jin abinda humaira ta fad’a, indai tayi mata fad’a toh akan yin daud’a da uniform ne ko tsalla-tsalle amma kaji wai ta fiye fad’a shi kuma ya zauna a gaban ta sai dariya yake yi jin yak’i denawa ne yasa ta mik’ewa ta toshe mai bakin sa da tafin hannun ta da ya sha jan lalle a yatsun sai ya kamo hannun nata ya juyo da ita sai gata a kan cinyar sa suka kalli juna ya kashe mata ido d’aya tare da kai bakinsa cikin nata yana kissing d’in sa a hankali.
Sai da yaji motsin za’a fito yayi saurin cirewa tare da kwanciya k’asan carpet yana sauke numfashi a hankali, ita kuma Nadiya na zaune ta bishi da kallo kamar be yi komai ba sai tayi murmushi kawai tana girgiza kai, suna fitowa ta gallarawa humaira harara ita kuma sai buya take a bayan Balqees har suka k’arasa suka zauna.
A hankali Sultan ya mik’e yana kallonsu yace su d’akko hijjabai zasu je wani guri yanzu, tashi suka yi ko wacce ta d’akko nata Balqees ta sawa humaira hula, ita kuma Nadiya suka fito da Islam wadda farkawarta kenan daga bacci. Mota suka shiga ta Daddy daya bashi 407 ash color, suna shiga Balqees da humaira da Islam duk a gidan baya yayin da Sultan ke mazaunin driver sai Nadiya a kusa da shi yaja motar suka fita.
Unguwar Nasarawa suka nufa cikin GRA, wani katafaran gida suka ga ya nufa dasu yana zuwa yayi horn mai gadi ya lek’o sannan ya wangale musu gate d’in Ahmad Sultan ya danna motar ciki. Cikin wani k’atan tampal suka nufa yayi parking sannan yace.
“Toh ku fita muje.”
Fitowa suka yi suna bin gidan da kallo, da alama sabo ne fitikil dan sai k’amshin sabin ta yake yi kuma babu alamun an tare a gidan. Kallon sa kawai suke yi shi kuma yana faman yi musu murmushi ya d’auki Islam sannan ya kallesu tare da yin gaba yana cewa.
“Ku biyo ni…”
Gida ne kantameme mai d’auke da side guda uku, na farkon suka fara shiga. Parlor ne k’aton gaske mai d’auke da Italian kujeru masu kyau da tsada sai wani k’aton enlargement wanda picx d’in su ne su uku a jiki sun sashi a tsakiya a zaune suka yi sabida Balqees duk sun fita tsawo suna dariya yayi musu salfe.
“Abban humaira what do you mean? Woww…!”
Nadiya ta tambaye sa cikin tsananin mamaki da al’ajabi da burgewa, Sultan ya k’ara sa ya zauna dashi da Islam, be yi magana ba sai murmushi kawai da yake yi. Dudduba ko’ina suka yi babu abinda ba’a zuba ba a gida komai Masha Allah sai faman santi suke yi yace musa side d’inshi ne, daga nan suka tafi sauran wad’anda suke kallon juna duk suka shiga komai iri d’aya aka zuba hatta tsarin sides d’in komai iri d’aya, gaba d’aya sun gaji sabida kowane babbane ya shigo ya gansu a parlor’n Balqees hannunsa rik’e da ledoji dan dama fita yayi ya barsu ya kalli Nadiya dake yashe a k’asan center carpet tasa humaira tayi mata tausa yace.
“Kai my Nadi keda nake so yanzu muje ki gyara can BQ sai kuma na ganki anan a yashe?!”
Murmushi tayi tana kallansa ya ajiye ledan Balqees tace,
“Haba Yaya koni a gajiye nake baxan iya ba bare ita, gsskiya a samo wasu suyi.”
“A’ah kyaleshi zan gyara amma bari na fara bawa ciki hakki sannan sai naje na yi.”
Kallon Balqees yayi tare da kashe mata ido d’aya, tsab ta gano abinda yake nufi dan haka ta ta6e baki tare tashi taje ta d’auki abinda zata ci ita da humaira.
Story continues below

Shi kuma suka ci tare da Nadiya Islam na can tana wasan ta tak’i zuwa taci, suna kammalawa suka yi mai murna tare da fatan alkairi mai d’in bin yawa daga nan d’ibar su yayi ya nufi dasu inda ya kuma basu mamaki, wato wani katafaran asibiti ne da ya tsaru ya k’eru aka kashe masa dukiya aka yi mai wani kyakyawan rubuta wato sunan asibitin _*NADIYA PRAVITE HOSPITAL*_ anata yin fenti ya danna motar ciki suka shiga. Yana yin parking kawai yaji ta rungumo shi sai kuka yayin da Balqees taja yaran suka fita tana dariya, fuskar ta ya shafo tare da d’ago ta idanunta har sunyi ja hawaye fal a cikin su ya shiga kad’a mata kai alamar ta bari tare da sanya hannu yana shafo cikinta murya k’asa-k’asa ya kai bakinsa cikin kunnanta yana cewa.
“Ya isah haka my Nadi kar kija baby na ya/ta ji haushi please bana son kukan nan kinji ko..?!”
“Why…why zaka hanani yin kuka abban humaira? Dole nayi domin kuka ne na farin ciki, jin dad’i da kuma godiya, kayi surprising d’ina dan ban ta6a zato ko tsammanin na kai ga wannan matsayin ba a gurinka, kayi hakuri abban humaira bawai gwasaleka zanyi ba amma ya dace ace wani abun kayi mana tunda bani kad’ai bace matarka kuma hakan shine adalci, idan kayi min abu ni kad’ai Allah zai tambaye ka, amma tunda kayi wannan d’in ka barshi ya zama mallakin mu mubiyu, kaga basu gama aikin ba suma wajan gate kaje kace su gyara sunan su sanya *Sultan pravite hospital* mun san namu ne mu biyu koda ita ba ta yi aiki acikin sa ba ni zanyi idan yaso kud’in da za’a samu sai mu raba wannan shine adalci wanda zaka mana…”
Kallon ta kawai yake yi, yadda take yin maganar ma tamkar rubuta mata aka yi tana karantowa tsabar yadda yaga tana magana cikin hankali da nutsuwa tare da k’ask’antar da kai da kwantar da zuciya. Hannuwan ta ya rik’o yana kallon cikin idanunta sai ta kasa had’a ido dashi tana kallon hannunsa ya ce..
“Haka ne my Nadi na gode da tunatarwar ki amma kuma ina son ki sani, Allah be hana kyautatawa wanda yake kyautatawa wani ba koda kuwa a cikin matan sa ne, kin can canci fiye da haka a gurina my Nadi na rasa me zan yi miki wanda zai sa kiji dad’i a cikin ranki kamar yadda kike sani a koda yaushe, tunda muke da ke ban ta6a ganin kin canza min koda Ado da kwalliyarki ba koda kuwa kina cikin 6acin rai ne. Da yawa mata basu kula da yadda zasu furtawa mazajen su magana amma ke kina iya yi min magana aduk yana yin da nake ciki dan haka ke d’in abar *TATTALI* nace ina sonki Nadi ina alfahari dake anan d’inki zan mutu insha Allahu.”
Yayi maganar yana d’ora kansa akan cinyar ta, cikin sauri ta toshe mai baki jikinta na rawa tana hawaye tace.
“Insha Allah zan rigaka mutuwa abban humaira kaine katangar mu idan ka fad’i wa kake tunanin zai gatange mu? Dan Allah ka dena fad’an haka..”
D’ago kansa yayi tare da had’a goshin su yace.
“Muje kiga guri.”
Fitowa suka yi lokacin su Balqees har sun yi nisa da ganin gurare, cikin wani emergency suka had’u da sauri Sultan yayi mawa Balqees alamu tayi hurging d’in Nadiya ya nuna mata hakan kamar wani bebe. Da sauri Balqees ta rungume ta tare da yi mata alasanya alkairi ta kuma taya ta murna da godiya a wajan Sultan.
Sai da suka zagaya ko ina sannan suka koma gida da nufin idan ta haihu anyi suna zasu koma sabon gida a kuma yi bikin bud’e asibitin wanda daddyn ta ya d’auki kwangilar zuba mata magunguna a ciki Yaya imran kuma yace zai sanya mata gadaje tayi murna harda kuka tana jin wani farin ciki ko yanzu ta mutu taji dad’i.
….. ……
A hankali ya mik’a mata hannunsa ta Kama, sannan a hankali ya janyo ta jikin sa ta k’ank’ame shi kamar zata koma cikin sa, sai wani faman ajiyar zuciya suke yi yana shafar saman k’irjin ta. Murmushi tayi tana k’ar6ar sakon salon nashi bata hana sa ba dan tasan yanzu ya ce mata da Nadiya ce ita kuma ta tsani wannan kwatancen dan haka tayi likimo har dai ya samu abin da yake so sannan ya rungumeta kamar wata jaririya dama gata ‘yar d’iris sai ta fara mai shagwa6a shi kuma ya rasa yadda zai yi yana ta faman lalla6a ta cikin kunnan ta yake furta mata.
_”Each time each minit each second when I look at your gorgeous face, I feel my heart melt in your love. I just can not stop thinking about you Baby I love you…love you very much…_”.
Matse shi tayi tana birgima a jikin sa tare da yi mai cakulkuli nan suka hau yi sabida kalamansa ji tayi suna mata yawo a cikin jininta, kamar kuma ana mata tafiyar tsotsa dan haka ta hau yi mai bori itama murya a sanyaye tana kallonsa da idanun ta masu d’auke dazara-zaran gashin ido yana ja mata tace..
_”I don’t have words to describe what I feel for you. I fall deeper in your love with every passing day. Every moment I spend with you, feels like a dream. I’m madly in love with you Yaya zulkallain…_”
“Woww baby na muumchh, kin san ance love is a name, sex is a game ko? Toh forgot the name and countieniou the game..”
“Hahahhah kai Yaya wallahi baka gajiya.”
“Eh bana gajiya indai akan kine baby, kema kuma gaki ‘yar k’arama amma sai na gaji ke kuma kina jin k’arfi oya zo nan yau sai na kaiki makura…”
Dariya Balqees tayi tana d’an yi mai bugan wasa, haka suka dinga wasan su cike da farin ciki, idan dai akan so ne hakika yana mutuwar son Baby haka kuma yana son Nadiya uwa uba hakurinta da kawar da kai hakan yasa ya bata wani k’aton fili a cikin zuciyar sa kuma babu me iya gano wa yafi so a cikin su dan haka yake zaune Lafiya dasu yana basu kulawa da *TATTALIN* su kamar kwai d’anye…..