TATTALINTA CHAPTER 3

TATTALINTA






CHAPTER 3




*S*ai da suka huta Yusif duk ya kanainaye Balqees gabaki d’aya ta takura mata yayin da abin nashi yake bawa Sultan mamaki da haushi sabida yadda ya hanata sakat har sai da ya tafi tukunna Sultan ya kalleta,
“Baby kije kiyi wanka saiki kwanta ki huta.”
Yayi maganar cikin sanyin murya,kamar bazata tashi ba sai kuma ta mik’e a hankali har ta fara tafiya yace,
“Ammm!baby fara d’akko min phone d’ina tukunna.”
Saurin kallonshi tayi sai taga ya had’e rai ta tura baki dan tasan idan ta bashi sai yayi waya da Nadiya wadda yayi serving sunanta da am yours, ganin tana neman yi mai gaddama yasa shi mik’ewa tsaye tare da k’ara tsuke fuska yace.
“Please yanzu fa nake so.”
Kallonshi ta tsayayi ya taso ganin yayo wajanta yasa ta juya ta fara tafiya har suka shiga cikin d’akin kaka wadda fitowarta daga wanka kenan ta gansu shi sai faman had’e rai yake ta bud’e ido tare da cewa,
“Muhammad ya akayi ne naga ka b’ata rai haka?!”
“Hajiya wannan yarinyar ban san meyasa yanzu tabi ta rainani ba tun jiya ta d’auke min waya yanzu nace ta d’akko min tana neman yimin yawo da hankali.”
Yayi maganar yana lumshe idanuwa da alama bacci yake son yi,hajiya kaka ta juya wajan Balqees dake ta faman turo baki batace komai ba ta kuma kallonshi sannan tace,
“Allah ya kyauta toh,wai kuwa ka tambayeta abinda takejin tsoron kuwa Muhammad?!”
Shafa kai yayi tare da mik’a hannu ya k’arbi wayan yana cewa,
“A’a hajiya cewa nayi tayi wanka saita huta idan na dawo anjima sai na tambayeta yanzu nasan Umma nacan tana jirana.”
“Toh ai shikenan Allah ya dawo dakai lafiya Muhammadu a gaida mutanan gidan.”
      “Ok zasuji kaka sai na dawo.”
Ya fad’a tare da juyawa yabar d’akin yayin da Balqees tayi kwanciyarta a kan babban gadon kaka ta rasa gane kan Yaya Sultan sam yama maida ita sakarai ko dai itama shareshi zatayi ne amma kuma ai bazata iya ba zuciyarta dashi ta rayu dashi ta ginu tayaya zata iya bayyana mishi irin soyayyar da take mai?hakika tattalin da yake mata tun tana ‘yar kankanuwa shine ita kuma ta shagala har ta bari ya zamar mata soyayyar shi ba kuma ta shakuwa ba ta son auranshi sai dai shi ya d’auketa ne tamkar ‘yar cikin shi daya haifa.
     “Ki tashi kije ki wankan mana baby.”
     “Sai anjima zanyi kaka.”
     “A’a kiyi yanzu keda kikayi kwanan asibiti ai dole da an dawo kiyi wanka indai kuma ba kazanta kike soba.”
     “Ni dai sai anjima zanyi.”
     “Karma kiyi baby jikin waye zaiyi wari.”
Hajiya kaka ta fad’a cikin takaici nan cikin d’akin ta barta ita kuma ta koma parlor inda take zama tare da d’aukar cazbaha tana ja da haka bacci yayi gaba da ita a gurin dan dama batayi bacci ba hira suka dingayi da shi daran jiya a asibiti. 

Sultan na zuwa gida side d’in Umma ya wuce babu kowa a parlon dan dama gidan be cika mutane ba kasan cewar babu ‘yan hira bedroom d’inta ya wuce tare da bubugawa daga cikin d’akin Umma take tambayar,
      “Waye?!”
      “Umma nine Ahmad.”
      “Sultan toh ka shigo mana.”
Bud’ewa yayi ya shiga zaune ya ganta gefen gado tanata faman duba wasu kaya,gefenta ya zaune ya gaida ita sannan yace,
      “Umma Abba fa ina yaje?!”
      “Sultan kenan sabida wannan yarinyar batada lafiya yasa ka kashe wayarka sabida kar a nemeka ko?toh yayi ta kiranka be samu ba ya wuce logos yau bazai dawoba sai week d’in biki, sannan yace kasa a bugo invitation ararraba duk yadda zakayi ka tabbatar abokanshi sun samu.”
     “Umma kuma ni za’asa duk wannan aikin?wasu abokan nashi ma bansan inda suke ba kawai ni gara naje na bada sanarwar a gidajen redio duka duka nawane kud’in.”
     “Nadai gaya maka abinda yace kai kuma sai kaje kayi yadda ka tsara zakayi.”
Dafe gushin shi yayi domin wani irin bacci yakeji ganin yadda Umma ta had’e rai yasa shi mik’ewa tsaye yana cewa,
    “Yi hakuri Umma zanyi yadda yace.”
Juyawa yayi ya fita ya koma side d’inshi yana zuwa wanka yayi sannan ya haye gado ba dad’ewa wani nannauyan bacci yayi awan gaba dashi. Balqees kuwa yana fita bayan hajiya kaka itama ta fita kuka ta sanya sam yanzu batajin dadin komai gashi zuciyarta tayi mata nauyi jinta takeyi tamkar ta cirota ko zataji relief, da haka tana ta tunani har tayi bacci mai cike da mafarki wanda duk na  rayuwarta ne da Sultan harda wanda suka yi aure tayi mafarkin ta haifi yaranta kyawawa masu matukar kyau kamar baban su domin Sultan namijine da za’a iya bashi A1. 

***
Shirye-shiryen biki ake tayi tun ranar kuma Sultan be samu damar komawa gidan hajiya kaka ba har gashi ana yau dinner,gidan kaka ya shiga yana yin parking ya fito nan ya doshi cikin gidan ‘yan mata sai gaidashi suke yi suna binshi da kallo.sanye yake cikin wani d’anyen material na maza bak’i me layi-layi anyi mai d’inkin three quarter kanshi sanye da bakar hula hakama takalmin k’afarshi bak’ine sai faman shek’i da walwali yake yi ga wani sassanyan kamshi yana fita a jikinshi a haka ya ratsa ya shiga cikin parlon.
   “Broth sannu da zuwa.”
Cewar Fateema wadda ke zaune ana  yi mata kwalliya billy ma tayi mai sannu da zuwa still yauma Aisha bata kulashi ba saima yi tayi kamar bataji yadda sauran suka yi ba shima ya shareta yayi shigewar shi ciki gurin hajiya kaka.
    “Ina yini hajiya?!”
   “Lafiya lau Mohd ya kwana biyu duk kabarmu da kallon hanya.”
Murmushi tayi tare da sanya d’an yatsanshi yana sosa quarter million d’in dake kwance a fuskarshi yace mata.
    “Hajiya abubuwa ne suka min yawa shi yasa.”
    “Toh Mohd Allah dai yayi maka albarka yasa ka gama da manya lafiya.”
   “Amin hajiya na gode.”
Shiru suka yi na d’an lokaci kafin ya numfasa ya tambayi hajiya kaka,
    “Hajiya wai ina baby ne banganta ba dana shigo?!”
Hajiya tayi murmushi tace,
    “Baby na nan Mohd k’ila dai ko tana cikin d’aki suna ta shiri.”
Tsaye ya mik’e yana cewa,
    “Ok bari naje.”
Can bedroom d’inta ya shiga zaune ya hangeta a bakin gado tana d’aura takalmin daya siya mata yayi mata sallama,tana jin muryarshi tayi saurin d’agowa suka kalli juna,baki d’aya Balqees ta saki baki tana kallonshi dan ba k’aramin kyau yayi mataba cikin rashin sani ta furta.
    “Woww gaskiya ka had’u.”
Kallonta kawai yayi ganin yadda ta tsareshi da ido, tayi kyau itama cikin material d’in ankon daya siya mata anyi mata d’inkin doguwar riga bata d’ura d’an kwaliba sai mayafi d’an k’arami da ta yafa a kanta ta zagaya dashi ta wuyanta,ganin kallon yak’i karewa yasa shi cewa.
    “Ke! Meye haka?!”
Tayi saurin dawowa cikin hankalinta sannan ta waske da cewa,
    “Yaya daman kana nan?!”
     “Ganima.”
Ya fad’a ta yana ciro wayar shi daga aljihu ya matsa kusa da ita ya zauna a bakin gadon yace,
     “Tsaya muyi picture.”
Wani farin ciki marar musaktuwa ya ratsa zuciyar Balqees nan fa zuciyarta ta bafara kitsamata cewar anya Yaya Sultan shima kuwa ba sonta yakeyi ba?idan haka ne ya zataji?aikuwa da tafi kowa sa’a a dacewa a duniya gaskiya tana sonshi.matsawa tayi kusa dashi hancinta sai aika mata yake da dadd’an turaran jikinshi bata son lokacin data sanya hannu ta bayanshi ta sargafo shiba a haka yayi musu sannan yace mata,
    “Oya tashi muje kiyi min raki.”
    “Dani kuma yayi?!”
    “Eh daga can zamu wuce gurin dinner.”
Nan da nan ta hau murna sannan ta k’arasa wajan mirror turare ta fesa ta juya taga shi har yace bakin kofa da sauri tabishi suka jera,wucewa yayi ita kuma ta tsaya wajan su Fateema tace musu,
    “Mu had’u acan yanzu zanyi wa Yaya rakiya daga can zai kaini sai mu had’u daku.”
Cikin b’acin rai Aisha ta kalleta tare da cewa,
    “Amma gaskiya kin mugun raina mana wayo daga ke har shi d’in,banda wulak’anci kinsan sabida ke muka zo nan muna shiryawa shine yanzu zaki wani ce mana mu had’u acan?!”
    “Ayya wallahi sis Aisha ba…”
Aisha tayi sairin mik’ewa tare da d’agawa Balqees hannu tana cewa,
    “Ya isa karki ce min komai gobe idan kin ganni anan kiyi min wulak’anci.”
Tana kaiwa nan ta mik’e tare da kallon su Fateema tace,
     “Ku tashi Mu tafi.”
A nan tsaye suka bar Balqees duk bataji dad’i ba ta rasa gane matsalar Aisha tana lura da ita duk sanda Yaya Sultan yashigo idan tana walwala aguri to bazata karayi ba har sai yabar wajan,horn d’in da tajiyo ne yasa ta fita da sauri.tana zuwa ya nuna mata backseat ta zaro ido cikin mamaki sannan tace.
     “Yaya baya kuma?!”
      “Eh.”
Ya fad’a cikin had’e rai,cikin sanyin jiki ta bud’e ta shiga shi kuma ya rufe murfin side d’inshi yaja motar suka fita,tunda suka fita babu wanda yayi magana cikin ranta mamaki take akan dalillin da zaice ta shiga baya bayan kuma gaban babu kowa a ciki,har suka k’arasa gaban wani had’add’en get sannan yayi parking tana kallonshi ya d’auki wayar shi ya daddana sannan ya kara a kunnen shi ba jimawa taji yana cewa.
     “Muna get.”
Daga haka taga ya kashi ya mayar cikin aljihunshi,jim kad’an suna zaune kamar ance ta kalli gabanta ta hango wata tsaleliyar budurwa ta fito daga cikin gidan sanye cikin material irin na jikinta wayar ta kare jikin kunne tana magana harta k’araso wajan motar ta bud’e gaban mota ta zauna Balqees bata dena kallonta ba sai mammaki take shin wacece wannan da har Yaya Sultan ya kasa sanyata a gaba sabida ita harta ajiye wayar ta juya ta kalli Sultan sannan cikin daddad’ar murya taji tana cewa.
    “Be Maine.”
    “Am yours.”
Ya fad’a yana kashe mata ido guda d’aya,kirjin Balqees ya buga da k’arfi jikinta ya hau rawa kanta ya fara juyawa tayi saurin dafewa. 

_Afuwan pls_

    A hankali ya karkata motar ya juya,sai da suka hau kwalta yaga dai sam bata kula akwai mutum a baya ba yasa shi kallonta kad’an itama akayi sa’a shi take kallo sukayi murmushi yace,
    “Madam wai baki san muna da yawa cikin motan nan bane?!”
Murmushi Nadiya ta sake yi duk a tunaninta wasa yake mata dan haka tace,
    “Eh mana muda mala’iku ne Allah ya kaimu lafiya.”
    “A’ah ki dai duba bayan mala’ikun ma akawa ki dad’a dobaww sosai.”
Ya fad’a fuskar shi kunshe da fara’a, a hankali Nadiya ta waiga baya idanuwanta ne suka sauka akan fuskar Balqees wadda ke jin gine jikin kujera ta rufe idanunta kamar me bacci,cikin murna da farin ciki Nadiya tace,
     “Kai! Kai!! Kai!!! Lallai kuwa kace yau dai daughter aka d’akko min gaskiya ka kyauta kuma kanada kauta special.”
Zame hularshi yayi tayi baya yana murmushi ba tare da yace komai ba, cikin farin ciki Nadiya ta kuma juyawa ta kalli Balqees wadda har lokacin idanunta a rufe suke tace tare da kamo hannunta.
    “Daughter shine ba magana ko bacci kika fara?!”
Wani kolulun abune ya tokare a wuyan Balqees taji tamkar ta naushi bakinta amma ba hali sai ranta dake zafi kamar ta fita daga motar,ganin taki yin magana ne yasa Nadiya kallon Sultan tace.
    “Mine ko bazata kulani bane?!”
Yayi murmushi sannan shima ya d’an waiga bayan yaga still idanunta a rufe yake sai yayi murmushi tare da cewa,
    “Baby bazaki gaida itaba ne?!”
Ta kuma yin banza cikin d’aga murya wadda sai an kular dashi yake yinta yace.
    “Ba magana nake miki ba?!”
Sannane Balqees ta bud’e baki yana rawa idanunta rufe hawaye nasan zubar mata tace.
    “Ina wuni.”
Nadiya bata amsa ba ta kalli Sultan bayan ta tsuke fuska tace,
    “Um-um Mine akwai abinda aka yiwa yarinyar nan kafin kuzo.”
    “Me aka mata kuwa,kawai b’acin rai take dan na hanata shigowa nan front seat shine tunda muka taho take ta faman yi min shariya.”
Yafad’a cikin tabbatarwa,wani haushine ya sake dirarwa Balqees taga alamar shi sam baya gane inda ta nufa sai dai ma ya dinga baud’ewa ita kam ta shiga uku ya zatayi?muryar Nadiya taji tana ce mai.
    “Mine samu guri kayi parking ni zan koma bayan ita kuma sai ta dawo gaban kasan dai bana son b’acin ran daughter.”
Dariya yayi wadda har ta bayyana fararan kananun hakoranshi kafin yace,
   “Kinji ki da taya b’era b’ari,ita yanzu idan tajima zaki haka ai sai taji kunya bare ma ni ba tsayawa zanyi ba.”
   “Habba nawan please mana.”
   “Allah bazan tsaya ba wai ki koma baya saidai ni na barmuku motan sai ku tafi dama dan ku zani gurin kema kinsani.”
Kyaleshi Nadiya tayi ta kuma juyawa wajan Balqees tace,
    “Rabu dashi daughter zan rama miki.”
Wani tukuk’in takaici ne ya kuma rufarwa Balqees,wato ma matar nan so take ta nuna mata cewar tafita matsayi a gurin shi lallai yau taga ta kanta wannan wane irin wulak’anci ne,juyawa Nadiya tayi ganin Balqees tak’i bata had’in kai suyi magana sai ta juya suka ci gaba da hirar su yayinda hakan ya kuma konawa Balqees rai a haka har taji sun tsaya dan har lokacin idanta a rufe yake. 

Lokacin da sukaje gurin da za’ayi dinner sannan ne ma suka tarar amare da angwaye suna fitowa daga cikin motoci, guri ya samu yayi parking da sauri Balqees ta bud’e zata fita yace,
    “Wait! Ki bari sai amare sun shiga tukunna.”
Balqees ta zabga mai harara ba tare da ta bari ya kula da hakan ba,hirar su saka ci gaba dayi Nadiya na sako ta a ciki amma fur tak’i kulawa hakan yasa itama Nadiya ta denayi mata magana a ganinta koda itace tayi mata wani laifin bata canci wannan shariyar ba dan har ta fara kokwanta anya zasu shirya idan ta auri cousin d’inta.
   “Mine mushiga mana.”
    “Ok baby bud’e muje ciki.”
Ya fad’a shima yana kokarin fitowa sai da duk suka fita sannan ta bud’e itama ta fito bayan ta d’auke kai ga barin duban su, jerawa suka yi sunyi matukar yin kyau sosa kuma sunyi machines Nadiya da Sultan yayin da mutanen da ya rage a harabar gurin sai kallonsu suke yi ita kuma Balqees ta yi gaba Sultan ya kirata da d’an k’arfi kamar karta tsaya sai kuma ta juyo ba tare da ta kallesu ba har suka k’arasa inda take, hannunta ya kama ya rik’e cikin nashi sannan suka ci gaba da tafiya yayin da Balqees jikinta yayi wani yarrr jin hannunta cikin nashi mai taushi kirjinta sai bugawa yake yi suna tafiya suna hirarsu amma banda ita sai ma sake-saken zuciya da aka barta dashi.cikin hall d’in suka shiga ba karamin kyau gurin yayi ba Nadiya ta kalli amaren da angwayan cikin tsananin yabawa tace,
   “Woww gaskiya sunyi kyau Masha Allah.”
Balqees ta d’an ja tsaki kad’an duk basuji ba Sultan ya d’an matsa kad’an still hannunshi yana cikin na Balqees ya cewa Nadiya.
    “Sauran namu ko?!”
Tayi murmushi batace komai ba,duk da cewar Nadiya ‘yar gidan masu kud’i ce kuma  wayayya ce amma tana da kunya kawaici da kuma ganin mutuncin duk wani d’an Adam hakan yasa tayi saurin sace zuciyar Sultan gata kyakkyawa domin fara ce doguwa tana da manyan idanuwa da yalwar sumar kai  tare da zara-zaran gashin idanuwa dana gira uwa uba akwai fara’a domin ba dai kaga fushi ko b’acin rai a fuskarta ba,tana da diri mai matukar d’aukar hankali sai dai batada cikar kirji sosai amma tana dashi dai-dai misali Balqeeq ta kuma had’e rai so take kawai ya saki hannunta domin duk sun cika ta da takaicin su Sultan ya samar musu gurin zama basu ko gama zaman ba sai ga broth Yusif shima ya k’araso ya zauna kusa da Balqees yana kashe mata ido cikin wani salo. 

Wani kululun abu ne ya kuma tukarewa a wuyan Balqees yaukam ta shiga uku wata k’ila da b’arin hagu ta tashi daga bacci tunda yau duk haka take abunuwa babu sa’a a cikin su. Yusif ya kalleta sai wani kashe mata ido yake yi yayinda Sultan ya bisu da kallo shi abinma dariya yake neman bashi ganin yadda Yusif d’in yake yi amma ya basar cikin murya kasa-kasa yace,
   “Wifey taso muje daga ciki.”
Da sauri ta mik’e dan gara ta bishi da ta zauna a gurinsu su kashe mata zuciya,tana ture kujera baya taji an damk’i hannunta tayi saurin waigowa ido waje taga Sultan ya riketa sai ta kuma had’e fuska tana cuno baki cikin isa yake tambayarta.
    “Ina zaki kuma?!”
    “Cikin mutane.”
Ta fad’a tana kallon gefenta, Yusif shima ya had’e rai tare da sanya hannuwa cikin aljihunsa Sultan yace.
    “Nan kuma gurin su waye idan ba mutane bane?!”
    “Nifa gurin su Aisha zani nace musu idan munzo zan neme su.”
   “Toh baza kije ba anan zaki zauna.”
Kawai sai ta saki kuka dama k’iris take jira ganin haka yasa shima Yusif ya damk’o d’ayan hannun nata yace,
    “Muje wifey yadda yake da iko akanki haka nima nake dashi.”
Kuka ta saki musu sosai a gurin ganin yadda suke janta, da Sultan yaga hankalin mutane ya fara dawowa kansu gashi yawanci akwai students d’inshi a gurin yasa shi saurin sakinta hakan ya bawa Yusif damar janta suka wuce gaba yayin da ita kuma take kuka ya Samar mata guri ta zauna sannan shima ya zauna yana lallashinta.sai da ta zauna sannan taga bata kyauta ba abinda tayiwa Yaya Sultan domin tasan yana yin hakan ne dan kula da ita baya son yaga tana shiga gurin da be kamata ba amma ya zata yi ta zauna a gurin su bayan tanaji tana gani yake nunawa wata soyayya wadda kullum take burin taga yayi mata irinta amma ba irin wadda yake mata yanzu ba na ‘yan uwantaka da kuma jinta tamkar shine yayi tsugunnanta ba.
    “Sorry kinji wifey kinsan wannan guy d’in shi sai faman iko akanki bayan kuma shi ba auranki zai yi ba amma sai ya hana masoyanki zuwa gareki.”
Da sauri ta d’ago tana kallon shi jin abinda ya fad’a, girarshi ya d’aga mata sannan ya kuma matsar da kujerar shi gurin tata yana gaya mata yadda zataji dad’i a gidan shi idan sunyi aure maganar tashi duk ta gundireta a hankali ta juya side d’in da tabar su Sultan ga mamakinta basa gurin nan fa ta mik’e tsaye tana waige-waigen inda zata hangesu amma sam bata gani ba.
    “Wifey muje kiyi rawa gasu Fateema can nayi.”
    “Bana so.”
    “Sabida me?toh muje muyi tare.”
    “Broth Sufee dan Allah ka rabu dani.”
Tashi yayi tsaye ya ja hannunta tana turjewa dai-dai kunnanta ya rad’a mata.
    “Ke! Ki bari gurin su Ahmad zan kaiki.”
     “Naji amma ka sakar min hannuna.”
     “A’a ni bazan saki hannunki ba sabida fashion ne hakan da muka yi.”
Tsaki taja sabida gaba d’aya ya takura mata gefe kuma amare ne ko wacce da angonta a gefe su uku akan high table kowa cike da fara’a musamman Yaya Jamal sab’anin Yaya I.b sabida ma kar a fuskanci halin da yake ciki yasan yashi saka dark shade a fuskar shi Al’eemin kuwa wayar shima yake latsawa baya kallon kowa koda pic akajeyi kusa dashi baya barin abinda yake yi a haka kowa yake zuwa yayi hotan.
Yusif kuwa waje yaja Balqees suka fita, sai da ya bari sunje gurin duhu sannan ya rungumuta jikin shi gaba d’ayanta nan da nan jikin Balqees ya hau rawa ta bud’e baki da niyar yin ihu kawai Yusif yayi saurin toshi mata shi,kuka ta sanya tana kokarin janye jikinta shi kuma yana zura d’ayan hannun nashi saman kirjinta  jikin ta ya fara karma ziciyarta na bugawa. Dama tun sanda suka fito akan idon Sultan ne da Nadiya wad’anda ke zaune ran Sultan duk a b’ace yana cewa Nadiya lallai akwai abinda yake damun Balqees domin yau ta kular dashi ya kularwa,lokacin da suka ga Yusif ya jata sunyi wani gurin hakan yasa Nadiya takura mai akan cewar ya tashi suje suga ina zasuje da farko k’i yayi har saida yaga ranta ya d’an b’aci sannan ya tashi suka bisu,suna zuwa wani corridor kirjin Sultan ya hau bugawa yayinda Nadiya ta kurma ihu dan ma babu k’ara Sultan tayi kansu da sauri idanunshi ko gani basa yi dan tsabar shiga tashin hankali.

    *Y*ana k’arasawa gurin still Yusif na rungume da ita ko gani baya yi ya fincikota da karfi ya d’aga hannu ya yarfasu akan fuskar Balqees sannan ya hank’ad’ata tayi baya taga-taga zata fad’i Nadiya dake gurin tayi saurin rik’o,gurin ya kuma nufowa zai fincikota amma Nadiya ta hana hakan sai ya fara fad’a ta inda yake shiga batanan yake fita ba jijiyoyin kansa duk sun mik’e yana ta fad’a,
    “Dan ubanki daman abinda kike sonyayi miki kenan shine ina hanawa kika sakar min kuka? Yanzu duk irin kulawar da nake mik’i har takai ban sani ba kin zama ‘yar iska har kinyi girman da zaki mallakawa namiji jikinki? Toh wallahi kinji na rantse miki?aure zanyi miki amma bada wannan banzan ba,daman akwai wanda yaje ya tambayi Abba nine nace a’a abari sai kinyi karatu amma yanzu dole na shaida masa cewar ya turo manyansa stupid kawai.”
A gaggauce yayi saurin juyawa cikin taku uku Yusif yasha gabanshi gashi lokacin har mutane an taro a gurin Yusif ya dafa kafad’un Sultan ya kalleshi tun daga sama har k’asa sannan yace,
    “Wai shin in tambayeka Ahmad ya kuke da Balqees?shin sonta kakeyi ka kasa bayyanawa shi yasa kake irin wad’annan abubuwan na borin kunya?toh a tunanina yadda kuke da ita haka nima nake da ita har garama ni ina da burin ta zama matata mallakina dan haka ka sake taku wannan beyi maka kyau ba.”
Umman Sultan ce da Adda Aisha suka nufo gurin lokacin Sultan ya zame jikinshi daga hannun Yusif ya nufi inda yayi parking motar shi sai da ya kusa isa sannan yaji muryar Umman shi tana kiranshi,cak ya tsaya zuciyar shi na zafi amma yayi kokarin kawar da b’acin ran dake kan fuskar shi suka k’arasa inda yake Umma ta kalleshi sosai kafin tace,
    “Mekenan hakan Sultan?!”
    “Bakomai Umma.”
    “Ya zaka ce min babu komai bayan naji duk abinda yake faruwa, dama Sultan har yanzu kana nan akan bakarka na cewar zaka auri yarinyar nan?”
Ras gaban Nadiya ya buga da karfi wadda ke rungume da Balqees yayin da shi kuma yayi wani murmushi mai cike da tsantsar takaici kafin yace.
    “Umma idan munje gida mayi maganar amma banason jin kalmar wai zan auri baby domin inajin kalmar a cikin raina tamkar anayin babban sab’o domin babu aure a tsakanin Mu.”
Yana kaiwa nan ya shiga cikin mota horn yayiwa Nadiya alamar tazo su tafi,jikinta a sanyaye ta riko hannun Balqees suka nufi wajan motar,gaba ta bud’e tana kokarin sanya Balqees a wajan yayi saurin dakatar da ita cikin b’acin rai yace.
    “Kinga Nadi karki sake ki sanya min ita a cikin mota kedai ki shigo na mayar dake gida.”
    “Habba dan Allah mine ya….”
Da sauri ya dakatar da ita cikin d’aga mata hannu,ganin haka yasa ta saki hannun Balqees ta tsaya tana kallonshi yayin da Balqees d’in ta juya da gudu ta fad’a jikin Adda Aisha tare sa sakin wani kukan ita kuma Nadiya ta rankwafa tana kallon Sultan tace,
     “Nima bazan bika ba sabida tunda kayiwa daughter wannan abun toh nima zaka iya yi min kayi tafiyar ka kawai na samu mota na hau.”
A fusace ya kalleta ranshi a mugun b’ace mata cikin d’auke kai.
     “Ok zan tafi ba sai kin nuna min iyakata ba, amma a ganina tunda nine na kawoki gurin kuma ta dalilina kika zo nan d’in kamata yayi ni zan maida ke dan haka idan zaki shigo ki shigo na maidake sai ki dawo nan d’in da kanki tunda kuna da motoci a gidan naku.” 

Kallonshi tayi cikin tsananin mamaki shi kam be sake kallonta ba ganin so take ta raina mai hankali, juyawa Nadiya tayi ta tafi gurin su Balqees shi kuma ya tashi motar shi yabar gurin duk suka bishi da kallo yayin da Yusif ya kwashe da dariya sannan ya kuma matsawa inda Balqees suke tsaye.
    “Wifey na zo muje na kaiki gida.”
    “Yusif baza ta bika ba kabarta anan.”
Cewar Adda Aisha tana kallonshi fuskarta babu yabo babu fallasa, kafad’a ya d’aga tare da tura hannuwanshi cikin gefen aljihunan shi yace.
     “Kwayi kwa gama.”
Da haka ya juya cikin tafiyar shi ta ‘yan duniya su kuma suka bishi da kallo musamman ma Nadiya da take mamakin shi. Balqees kam kuka kawai take Adda Aisha ta kama hannuwanta suka koma cikin hall d’in lokacin anata cin abinci da kayan motsa baki ita kuma Nadiya tayiwa driven gidan su waya cewar yaxo ya d’auketa bayan ta sanar dashi gurin da take,samun guri tayi ta zauna zuciyarta fal mamakin Sultan domin bata tab’a ganinshi cikin wannan yanayin ba tana mamakin shi, tsayuwar mutum taji a gabanta a hankali take binshi da kallo tundaga kan takalmin kafarshi har takawo kan fuskar mamaki ya cika ta ganin Yusif ne, da sauri ta mik’e tana gyara tsayuwarta cikin tsuke fuska yayi dariya.
     “Haba ‘yan mata karde ace tsoro kikaji bayan na ganki tamkar jaruma?!”
Banza dashi tayi tana kallon get ya kuma matsawa kusa da ita har yana tab’a mayafin jikinta,a hankali ta d’an ja da baya shima ya kuma matsawa cikin b’acin rai tace,
    “Kai! Kardai abin naka kaina ya dawo?ina son ka sani ko a mafarki ka kuma yin tunanin zaka tab’ani wallahi sai kayi nadama.”
    “Tambayarki zanyi ni, wai ke wannan guy d’in yake so kokuwa anan gurin kuka had’u?!”
   “Dan Allah ka rabu dani koma dai menene babu ruwanka please.”
Juyawa tayi ta tafi shi kuma yayi saurin rik’o mayafinta tayi saurin waigowa tana zaro ido, yanzu kam tsoranshi takeji sai da bata nuna mai hakan ba amma zuciyarta bugawa kawai takeyi dan tana tsoran sharrin maza kartaje tayi wani abun yazo ya cuceta dan haka a cikin sanyin murya tace,
    “Dan Allah ka rabu dani, ni anan muka had’u dashi kuma gashi mun rabu so ka kyaleni dan Allah dan manzon Allah (s.a.w).”
     “Ayya ‘yan mata kin riga kin cuceni tunda kika had’ani da Allah da manzon sa, na kyaleki amma wallahi kinyi min idan babu damuwa kizo muje na ajiyeki a gidan ku.”
Wani kululun takaici ya kuma dirarwa Nadiya ita kam wane tsautsayin ne ya kawota gurin nan gashi har ta had’u da mahaukaci,sabar rashin ilimi wai ta cuceshi dan tace Allah da manzonsa kai mutane sai addu’a.kafin ta bashi amsa ta hango motar gidan su hakan yasa ta fisge mayafinta ta juya yayi saurin biyo ta a baya sai tak’ara sauri yace.
    “Haba mana ina zaki?!”
Lokacin motar ta tsaya a kusa dasu ta zabga mai harara tare da yin sauri ta shiga bayan motar,ganin haka yasa Yusif yin murmushi yana kallon motar har drive yaja sannan ya d’aga murya yana cewa,
    “See you baby.”
Sai da suka bar cikin gurin sannan Nadiya ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana tunanin yadda za’a karke da Balqees idan ta koma gida. Su kuwa ‘yan dinner basu suka tashi ba sai wajan 11:40pm,Adda Aisha na tare da Balqees wadda har lokacin bata dena yin kuka ba domin iya bakin ciki tana cikin shi.koda suka fito ma motar su Adda Aisha ta shiga duk da cewar Umma sai wulak’anci take mata amma tayi tsit jira kawai take a kaita gidan kaka inda Allah ya temaketa ma a gidan za’ayi iyinin biki dan haka yawancin motane can gidan zasu wuce. 

Tunda ya koma gida sallah kawai yayi sannan ya d’auki laptop d’inshi tare da komawa kan gado ya zauna,so yake yayi aiki ya manta da abinda yq faru amma sam ya kasa gabaki d’aya abun daya faru yaki gogewa daga cikin idanuwanshi da zuciyarshi,mik’ewa yayi ya d’akko wayar shi ya kasheta sannan ya kuma komawa kan gadon still ya kasa aikata komai sai kawai ya rufe ta ya juya ya kwanta, ya dad’e a kwance yana saka da warwara gaba d’aya kwakwalwarshi ta toshe baya iya tuna komai sai abinda yaga Yusif na yiwa Balqees da kuma yadda Nadiya ta watsa mai k’asa a ido ya kuma juyawa d’aya b’arin zuciyar shi na zafi a ranar Sultan be rintsaba sam yana tashi da safe wanka yayi ya wuce gurin aiki ko side d’in Umma be biya ba.
   A b’angaran Balqees kuwa bayan ankai su Adda Aisha gida tasa drive ya kawo ta gidan hajiya babba (kaka), tana shiga ta ganta zaune a parlor da mutane da alama wad’anda suka farayin parking ne ta rugu da gudu jikin kaka tare da sakin wani sabon kukan cikin tashin hankali hajiya kaka ta fara tambayarta amma shiru ba magana sai kuka.
   “Keni ki tashi ki min bayani me aka yi miki haka kike ta wannan kukan?!”
   “Oh kaji yarinya kin shigo kina kuka anyi tambayar duniyar nan kinki cewa komai.”
Gwaggo lami ta fad’a kanwar hajiya kaka,kowa sai tambayartq yake amma taki cewa komai gashi taki yin shiru kakan tace.
     “Toh d’agani tunda bazaki magana ba.”
Ai kuwa kamar jira takeyi ta mik’e tayi bedroom da gudu tana kuka, bin ta duk suka yi da kallo lokacin ‘yan dinner suka dawo nan aka sanar dasu abinda ya faru harda masu k’ari cewar wai ganinsu Yaya Sultan yayi ita da broth Yusif suna iskanci a corridor nan fa aka saki salati duk cikin masu bayanin babu wanda yake da kwakwaran sheda ko dalili amma harda masu rantewa cewar akan idansu aka yi kaka ta tashi jiki na rawa ta nufi d’akin da Balqees take.
    “Tashi dan kwal ubaki yo ai dole ki kasa magana gaya min uban meyayi miki?!”
Balqees tayi shiru tana makure jikin gado, hannu kaka ta sanya tare da janyo kafarta tana son janyota amma ta kasa sabida ba kwarin jiki.
    “Nace ki gaya min meyayi miki shine zaki cikani da kuke toh wallahi zan daddakaki a gidan nan naga me kwatarki.”
Ganin bata da niyar yin magana yasa hajiya kaka fita daga d’akin sai zuga fad’a take, a ranar Balqees bata rintsa ba haka ta kwana tana kuka har kanta yafara ciwo. Nadiya ma da tunani ta kwana sam ta rasa gane kan Sultan tun jiya take neman layin wayar shi amma akashe duk yadda zatayi wajan ganinshi bata samu ba,washi gari ma babu wanda ya sanya shi a ido har akayi komai aka gama sai ranar d’aurin aure shima ana gama d’aurawa ya gudu Yaya Hemu nata nemanshi amma sam hakan ya cutura har aka kai amare gidajan su,itama Balqees bata k’ara fitowa daga cikin d’akin ba dama tana fashin sallah dan haka bata tashi daga kan gado sai ko toilet zata shiga abinci kuwa har an dena cewa taci sabida yadda aka kawo shi haka ake zuwa a d’auke shi tak’i jin lallashin kowa duk ta fara ramewa ko wanka batayi sabida damuwa da shiga tashin hankali.

    
    *H*ar aka gama biki aka watse Balqees tana kwance a d’aki ko iya tashi bata yi sabida rashin kwarin jiki gashi tak’i bari kowa ya kula ta,yau ta kama Monday da safe Abba mahaifin su Sultan ya shigo gidan hajiya kaka, zaune ya sameta kamar kullum akan sallaya tana azkar ya k’arasa ya zauna a kusa da ita sai da ya bari ta ajiye casbahan dake hannunta sannan ya gaida ita cike da girmamawa suka yiwa juna ya gajiyar biki sannan abba ya tambaya.. 

    “Hajiya ince dai komai lafiya ko ya kuma kafar?!”
     “Lafiya lau, kamar ma batai ba Alhamdulillah taji sauk’i sai dai mun rasa gane kan yarinyar can tun abun nan daya faru bata sake fitowa daga cikin d’akinta ba nayi lallashin nayi fad’an amma duk a banza ko abinci bataci.” 

   “Hajiya wacece haka?!”
    “Ahh Maryama mana tana nan har yanzu kwance a d’aki ko iya tashi bata yi.” 

Shi kam Abba sam kasa gano zancen da hajiya kaka take yi masa yayi gashi kuma ya kasa gano wacece Maryama d’in a gidan,hakan da hajiya kaka ta gani ne yasa ta cewa. 

   “Baby fa nake nufi 
Balqees.”
    “Au toh-toh me ya faru kuma?!” 

Nan hajiya kaka ta kwashe duk abinda aka gaya mata ta sanarwa da abba ta k’arkare da cewa, 

    “Ni wallahi duk cikin zance ban d’auki ko d’aya ba sabida duk wanda zai gaya maka to sai ya ce maka wai akace kaga kuwa duk abinda akasa masa wai ai an b’ata zancen gashi ita tak’i yi min bayani sai dana fara tambayar ta kaga ta sanya min kuka kuma har yau Yusif d’in bezo gidan nan ba daga shi har Muhammad duk wanda nace a kira min sai ace basa nan toh kaji.” 

    “Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un wallahi hajiya koda wasa ban tab’a jin labarin nan ba,yanzu ina ita Balqees d’in?!” 

Hajiya kaka wadda tayi kalar jimami tace mai. 

    “Tana can d’akinta.”
Tashi abba yayi ya fita zuwa d’akin da Balqees take.kwance ya ganta tayi ruf da ciki idanunta biyu dan ba bacci take yi ba sai dai ta kafawa guri d’aya ido kamar me nazari har abba ya juyo da ita gaba d’ayanta ta wulkito tamkar gawa sabida ko motsi bata iyawa abba ya hau kiran sunan Allah hankalin shi a mugun tashe kafin ya lalubo wayar shi ya kira Yaya Jamal sam ya manta ma da cewar Jamal yana garin abuja dan acan yake aiki ana kammala d’aurin aure aka wuce da amaryar shi can,Jamal na d’agawa yace. 

   “Abba ina kwana?!”
Ba samu damar amsawa ba sabida tashin hankali abban yace,
   “Jamal zo yanzu ina gidan hajiya.”
   “Abba ni ai bana garin ko har ka manta?lafiya meya faru?!”
Kit abba ya katse kiran sabida ya tuna nan ya fara kokarin neman Sultan cikin sa’a ya d’aga tun kafin ya gaida shi abba yace. 

    “Kazo yanxun nan ina gidan hajiya karka b’atamin lokaci.” 

Yana fad’a ya ajiye wayar dan yasan indai Sultan ne zai iya fin awa uku be zoba sabida tsabar nawa da yin abubuwa slow tamkar ba Namiji ba.yana nan zaune kaka ta shigo nan suka rufa akanta yayin da a b’angaran Jamal shima hankalinshi ya tashi sai faman kiran abba yake amma be d’auka ba,basu dad’e ba sai ga Sultan ya shigo gidan d’akin kaka ya fara nufa babu kowa ya fito ya nufi d’akin Balqees kirjinshi sai bugawa yake yi dan besan musabbabin kiran nashi ba. 

A hankali ya shiga gidan bakin shi d’auke da sallama hajiya kaka ce kawai ta amsa mai sannan ya shiga ciki yaga Balqees rik’e a hannun abban shi sai faman magana yake mata a hankali amma taki yin magana, hankalin shi ne yayi matukar tashi ya k’arasa gurinta da sauri yana tambayar lafiya. 

Story continues below


    “Ahmad tashi asibiti zamu mik’ata yanzu.”
    “Toh abba amma meya sameta?!”
Ya tambaya yana shafa fuskarta amma ya mik’e tsaye cikin yanayi na damuwa yace,
    “Eh toh hajiya tace tun ranar da Yusif suka yi wannan abun shikenan ta rufe kanta a d’aki baci ba sha bare ibada,ni sai yauma nakejin zancen.” 

Kuma kallon Sultan abba yayi ganin yadda hankalin shi ya tashi yasa shi kuma cewa, 

    “Ahmad ka samu ka d’akkota muje asibiti,ka fito da ita yanzun nan.’” 

Abba na kaiwa nan ya fita lokacin Yaya jamal ya kuma kiranshi ya kara a kunne yana tafiya yana gaya mai abinda ya faru shi kuma Sultan ya kinkimi Balqees suka fita zuwa motar abba dan shi daman a lifan d’inshi yazo gidan, baya suka shiga yana rungume da ita yayinda abba ke mazaunin driver hajiya kaka kuma tana kusa da abba wato kujerar me zaman banza nan suka d’auki hanyar asibiti.Suna zuwa aka wuce da Balqees emergency room su kuma suka tsaitsaya a reception kafin wasu mintuna likitan ya fito Sultan yayi saurin karasawa yana tambaya, 

    “Doctor me yake 
damunta?!”
     “Karka damu abokina mu k’arasa cikin office sai nayi muku baya ni.” 

Duk suka bishi amma banda hajiya kaka inji likitan haka ta zauna a reception sai mita take wai sun raina mata hankali guri suka samu suka zauna kafin likitan ya kallesu yace. 

    “Ina mahaifin yarinyar yake?”
     “Gani nan.”
Kowa ya nuna kanshi abba yayi dariya shi kuma doctor d’in ya kalle su yana shirin yin magana sai abba ya rigashi ta hanyar cewa. 

    “Gashi nan likita amma mahaifinta da mahaifiyarta sun rasu so komai nata yana gurin wannan tun bayan rasuwarsu.”
Kad’a kai likitan yayi sannan yayi d’an rubutu ya d’ago yana kallonsu yace, 

    “Marar lafiyar ku tana cikin wani hali sosai abubuwa sunyi mata yawa a jikinta ga damuwa, tunani, uwa uba kuma ulcer tayi mata mugun kamu dan yanzu haka ma sai mun sanya mata robar da zata temaka mata wajan cin abinci a samu wani abun ya shiga cikinta.”
   “Innalillahi wa’inna’ilaihir rajiun wannan wane irin abune haka,yanzu likita tana cikin wane hali?!”
Abba ya fad’a yana kallonshi, Sultan kuwa dafe kai yayi cikin tsananin damuwa yama kasa cewa uffan bare ya iya kallonsu, likitan ya kalli abba sannan yace.
   “Eh toh yanzu bazamu iya cewa komai ba har sai ta tashi daga bacci domin munyi mata allurar bacci sannan an sanya mata drip yadda zata farka da kwarinta but karku damu insha Allah komai zaizo cikin sauk’i.”
   “Allah yasa doctor mun gode sosai.”
   “Ba komai alhaji Allah ya bata lafiya.”
Cewar likitan kafin su tashi gabaki d’ayan su suka baro office d’in suka dawo reception inda hajiya kaka take zaune ta rafka uban tagumi.Tana ganinsu ta kalli Abba dan tasan shine zai iya tsayawa yayi mata bayanin komai a nutse ta tambaye shi cewar.
   “Ya aka yi?me yake damunta?!”
Abba ya zauna a gefenta cikin kwantar mata da hankali yace,
    “Karki damu hajiya likita yace rashincin abinci ne kwana biyu yasa jikin yayi haka amma da ta farka insha Allah komai zai yi dai-dai karki damu.”
    “Toh ai dama duk itace ta sawa kanta damuwa banda abinta waye besan iskancin Yusif ba?ni dama can ban yadda da abinda aka ce tayi ba sai dai in shine yake son yi mata, wawan yaro kawai ja’iri dama ai ya tab’a fad’an wata banzar magana a gabana ko kunyata bejiba d’an kaniya kawai.” 

*** 

Bayan abba ya koma gida ne yasa Umma ta shirya abinci aka kai musu can asibiti duk da ta dafa ne dan Sultan amma da baxata yi ba.misalin k’arfe 12:15pm Balqees ta farka lokacin Dr gadanya yana cikin room d’in nurses yasa suka had’a mata tea aka bari ya d’an huce sannan ya sanya mata robar ana fara d’ura mata ta fara ihu tana birgima sai mammake ma’aikatan lafiyan takeyi duk ta qular dasu ganin idon Dr gadanya ne yasa suka rabu da ita har suna lallashinta amma sister Hadiza ta fisu jin zafi sabida har b’ata mata uniform aka yi da ruwan shayi dan haka tafi kowa son Dr gadanya ya fita sai tayi mata rashin mutunci. 

    “Hadiza yarinyar nan bazata tsaya ayi abun nan a tsanake ba dan haka kirawo daddyn ta a nan reception yazo muga ko xa’a samu ta tsaya.” 

Wani kululun abune ya kuma tokarewa a wuyan sister Hadiza,haka ta fito fuskar nan a murtuke ta karajin wani haushin a zuciyarta tana zuwa inda take da tabbacin ‘yan uwanta ne ta tsaya tace.
    “Akwai baban yarinyar can anan?idan yana kusa yaje ciki ana kiranshi dan yarinyar akwai kafiya.”
   “Innalillahi ta farka ne??”
Cewar hajiya kaka tana kallon sister Hadiza,shi kuwa Sultan tana gama fad’a ya mik’e ya shiga itama sister Hadiza bata kuma kula hajiya kaka ba haka ta bar wajan ta kuma ki komawa cikin sabida ta gaji gashi haushin Balqees d’in takeyi.yana shiga ya ganta sai uban kuka take yayi saurin k’arasawa gurinta yana tambayarta Dr gadanya yayi mai bayani Sultan ya fara lallashinta amma sam tak’i tsayawa ganin haka yasa shi ririk’eta tana ihu tana kuka har aka kammala bata sannan kafin a gama gyara mata fuska har ta koma wani baccin.kallonta Sultan ya tsaya yi cikin tausayi duk tabi ta rame fuskarta ta kankance bakinta ya bushi wasu kasusuwa guda biyu na kumatu sun fito ya kuma kallonta sannan ya mik’e ya fita wajan da kaka ke zaune. 

    “Hajiya wa zamu samu yayiwa baby wanka idan ta farka?wallahi duk ta b’aci kayan jikinta har jinin ya fara bushewa duk tayi bak’i.”
Yayi maganar yana yatsina fuskar shi, kaka ta numfasa kafin tace,
   “Tofa!yanzu fisabilillahi da Ummanka nada kirki ai da tazo ko ita tayi mata, ni yanzu wazan kira ince yazo yayi mata, sai dai idan nizan…”
Bata k’arasa ba sai gasu Adda Aisha dasu bilkisu sunzo hannunsu d’auke da kwando wanda yake d’auke da foodflask da kofuna a ciki, da sauri hajiya kaka tayi murmushi tare da cewa.
    “Alhamdullillahi amfanin haihuwa da yawa kenan kaga ga Aishi nan sai tazo tayi mata ai itama Maman tace.”
Kallon hanya yayi nan yaga sun k’araso shima yayi murmushi ko banza an samu me wanketa dan lokacin daya rik’eta har k’arni-k’arni yaji tanayi tamkar ta shekara batayi wanka ba.zama suka yi aka gaggaisa shi sam ya kasa cin duk abincikan da ake kawowa jiyayi ma baya sha’awar cin kowanne.har kusan la’asar sannan Balqees ta farka sai da aka kuma dura mata kunun gyad’a sannan Adda Aisha tayi mata wanka wanda daman kafin lokacin Sultan ya maida hajiya kaka gida an bashi kayanta ya taho mata dasu ana gamawa Adda Aisha ta temaka mata ta sanya kayan sannan ta kwanta har lokacin bata saki jiki ba sabida babu kwari sosai.

    
    *T*ana kwance su kuma suna gefenta sai sannu suke faman jera mata tana d’aga musu kai a haka sister Hadiza ta shigo dan bata magani,kusa da ita ta k’arasa tare da janyo magungunan ranta a had’e ta b’allo sannan ta d’akko jarkar ever ta mik’a mata maganin tare da mik’a mata ruwan ba tare da tayi magana ba. Da sauri Balqees ta d’auke kai tare da juya baya ba tare da ta k’arb’i maganin ba ran sister Hadiza ya kuma b’aci cikin bala’in da take ta faman b’oyewa tace.
    “Ke dallacan tashi ki k’arb’a kin d’auka ni baiwarki ce?!”
Sam ta manta akwai mutane a wajan sabida tsabar idanuwanta sun rufe amma fur Balqees tak’i jiyowa ta k’arb’a sabida sam bata kaunar magani, Adda Aisha ce tayi magana.
    “Habba Baqees tashi kisha magani mana kin tab’a ganin an warke ba tare da ansha magani ba? daurewa zakiyi magani dama bawai dad’i ne dashi ba.”
Cikin muryar dake shirin fashewa da kuka Balqees tace,
    “Wallahi Umman Yaya bazan iya shaba amai zanyi.”
Sister Hadiza ta mayar da maganin sannan ta rufe jarkar ruwan cikin b’acin rai, ko sake bi takanta bata yi ba tasa kai ta fita,
   “Allah ya bata ikon had’uwa da yarinyar ita kad’ai wallahi sai ta ci ubanta duk da cewar bata da lafiya amma ta fiye taurin kai da salon iskanci..”
Sister Hafiza tayi ta fad’a cikin ranta. can kuma d’aki Adda Aisha ce keta yiwa Balqees fad’a wanda duk akan ita da Yusif ne ita kuma sai faman kuka take yi dai-dai lokacin kuma Sultan ya shigo kunnan shi manne da waya har saida ya shiga ciki sannan yace.
    “Ok bari zan kiraki anjima idan na samu kaina.”
Balqees dake kwance taji wani cuss wato ma ita tana nan tana neman halaka kanta sabida shi amma shi yana can yana soyayyar shi ya zata yi? Sultan ya k’arasa kusa da gadon sannan ya zauna ya kalleta sai yaga hawaye kwance a fuskarta da sauri ya kalli Adda Aisha sai kuma ya maida kallonshi yace.
   “Baby me aka yi miki?!”
Sultan ya tambaya cikin kad’uwa dan bashi da buri da fata irin yaga ta warke ko hankalinshi zai kwanta su koma gida.Adda Aisha ce tayi murmushi kafin ta mik’e tsaye tana d’aukar towel d’in da Balqees d’in ta cire sannan tace,
    “Kasan kanwar taka wai nan fad’a nake mata akan hudd’arta da Sufee ina cewa ta fita a harkarshi shine take kuka ban sani ba ko fad’an ne bata so.”
   “Haka ne Umman Yaya,nima abinda nake tunani kenan, kinga baby kina son auran Yusif ne ko kuwa me kike nufi akan shi?!”
    “Ban sani ba!nace ban saniba.”
Balqees tayi maganar a fili ba tare da tasan hakan ya faru ba,duk zaro ido suka yi suna kallonta da mamaki fal a fuskarsu Sultan yace,
   “Tab gaskiya baby yanzu sam baki da kunya,yanzu a nan wa kike cewa baki sani ba?wallahi ki shiga hankalinki haka mukaje dake wajan Nadiya kika nuna min wasu banzan d’abi’u wanda ban sanki dasu ba,amma ban sani ba ko zugaki ake yi.”
Cikin ran Balqees tace,
    “Eh zuciyata itace take zugani ya sultan ko menene kaine silah.”
Ganin tayi shiru yasa shi tab’e baki yana k’ok’arin tashi, magungunan ya d’akko ya koma inda take yayin da Adda Aisha ta wuce toilet tana cewa,
    “Ahmad gaskiya dai ya kamata ka tambayi yarinyar nan, indai ba zugata ake yi ba toh ba shakka tana da aljanu kuma sune suke ja mata yin wannan abun.”
Wucewa tayi cikin bayin shi kuma ya zauna a gefenta ya b’allo mata maganin ya mik’a mata,
    “Oya tashi kisha magani baby.”
Kai ta girgiza mai alamar a’a yayi saurin kallonta da mamaki,mik’ewa yayi zaune ya d’aga ta sai faman kawar da kai take yi nan ya fara lallashinta ta k’arb’i maganin tana faman jujjuya shi a hannunta murya a hankali yace,
     “Toh sha mana baby.”
Kamar zata yi kuka idanunta sunyi kwal-kwal da ruwan hawaye tace,
    “Bazan iya shafa Yaya wallahi yayi babba bazai wuce a wuya na ba.”
Zaro idanuwa yayi ya kuma kallon maganin duk babu wani katoto a ciki amma take cewa baza su wuce ba,zama ya gyara tare da kallonta itama shi take kallo kafin tayi k’asa da kanta yace.
   “Yauwa baby bud’e bakin na gano inda matsalar take,idan dai har kekika sanya a baki toh bazai wuce ba amma idan ni na sanya miki sai kiga kin had’iye oya ha bud’e bakin..”
Ya fad’a yana k’ok’arin sanya mata maganin,a hankali ta bud’e shi kuma ya sanya mata tare da bata ruwa tashi, haka duk yayi mata har ta shanye su sannan ya maida ita ya kwantar yana faman jera mata sannu-sannu ita kuma ta bishi da kallo zuciyarta na faman yi mata sake-saken abunuwa da yawa. 

Story continues below


Kwanaki uku suka yi a asibiti sannan aka sallame su sister Hadiza sai hararar Balqees takeyi wadda bata son ma tana yi ba,har suka k’araci zan su a asibiti Umman Sultan bataje ba amma ‘yan uwa duk sunje hatta Mamin Yusif da daddyn shi duk sunje sab’anin ita. 

A motar Abba suka koma gida bayan sunje sun sauk’e Adda Aisha a gidan ta,direct gidan hajiya kaka suka wuce Sultan rik’e da jakar kayan Balqees suna shiga yayi saurin riko hannunta ya wuce da ita d’akin hajiya kaka ya kalleta yace,
    “Jeki wanka idan kin fito kizo ga kayan da zaki sa,akwai special abu dana shirya miki.”
Da murnarta ta shiga wankan kaka sai kallonsu take yi cike da jin dad’i shi kuma ya koma parlor yana zama sai ga Al-eemin ya shigo gidan kamar kullum shima yadda yake shiru-shiru dan har k’ara I.b yana d’an sakin jiki idan yaga Sultan amma shi sam bayayi ya k’arasa suka yi musabuha Sultan ya kalleshi yace,
    “Ina amarya ka barota a gida?!”
Murmushi kawai Al-eemin yayi ya samu guri ya zauna ba tare da ya kula maganar da Sultan d’in yayi mishi ba,shima d’in be sake yin magana ba dama zani ce ta tarar da muje duk suka yi shiru kowa da abinda yake sakawa cikin ranshi.
  Suna nan zaune shiru har tsawan wasu mintuna hajiya kaka ta fito ganin Al-eemin yasa ta k’ara fad’ad’a murmushinta tace,
    “A’a kaga ango mijin amarya yanzu kai nan har ka fara fitowa Aminu?!”
Ya kalli kaka sannan ya mayar da wayar shi cikin aljihu yace,
    “Eh ai nine mijin hajiya dan na fito ai ba laifi bane.”
    “Lallai yaron nan kudai wallahi bakuda kunya,yanzu kai duka duka yau kwana nawa dayin auran amma kana fitowa ka barta har yashe zaku kara samun shakuwa bayan baku zauna da juna ba?dama dakai da Ibrahim duk abunuwan da kukeyi yana dawowa kunnena wallahi idan kuka cucesu akan iyayanku zan rama musu.”
     “Toh ni kuma me nayi?!”
     “Oho muku wallahi duk wanda ya cuci matarshi sai Allah ya saka mata,garama idan zakayi kasan abinda zakayi yana da kwakwarar hujja ni babu ruwana auran zumunci na had’a kuma sai da na tambayi kowa idan had’in yayi mai duk abinda kukayi musu Allah yana gani.”
Balqees ce ta fito cikin wata kyakyawar doguwar riga red color da kwalliyar baki ajiki rigar tayi mata masifar kyau.k’arasawa tayi cikin parlorn Sultan ya mik’e yana murmushi ya kama hannunta,hanyar d’akinta suka yi kaka ta bisu da kallo cike da mamaki tace,
    “Au Muhammad ba zaka gayyace muba zaka wani wuce da ita?!”
Tsayawa yayi bayan ya juyo yana dariya ya kalli hajiya kaka yace,
    “Toh hajiya ku taso nayi shirune dan karkuce zan takura muku amma tunda kuna so bisimillah.”
Da kyar ta mik’e sannan ta janyo hannun Al-eemin tana cewa,
    “Taso-taso Amin kaima ka taya kanwarka murna.”
Ba yadda ya iya haka ya tashi suka bi bayansu,a hankali Sultan ya murd’a handle d’in yace ta fara shiga.wani daddad’an kamshi ne ya ziyarci hancinta tayi saurin ware idanuwa sakamakwan yadda taga an kawata d’akin an kuma sanya wata bandana wadda aka yi mata kwalliya aka sa suna _Happy birthday_ daga kasan kuma wani wuta ne mai kyalkyali yake tayi Balqees ta dinga bin d’akin da kallo cike da farin ciki kafin ta kuma sauke kwayar idanta akan birthday cake d’in wanda yasha kyau an sanya sunanta a jiki,wasu zafafan hawaye suka fara zubo mata kafin tayi saurin juyawa gurin Sultan ya sakar mata murmushi tare da yin neal dwon tayi saurin rungumeshi saka makwan idan yana tsaye baza ta iya sargafo wuyan shi ba.
   Tana makale jikinshi tana kuka wanda kukan biyu ne ya had’ar na farin ciki dana tunawar mahaifanta hakan yasa take yinshi sosai,wak’ar birthday d’in ta jiyo tana tashi a hankali daga cikin d’akin wani sanyi ya k’ara ziyartar zuciyarta musamman da taji muryar shice.kasa sakin shi tayi duk da tasan cewar hakan ba dai-dai bane musamman da takejin wani iri a jikinta amma sam zuciyar ta takasa tsawatar mata,a hankali ya janyeta daka jikinshi ya rik’o hannunta suka k’arasa wajan cake din,knife ya d’auka ya sanya mata a hannu ta rik’e ya kalli hajiya kaka dake tsaye yace,
    “Hajiya taho ki taya ta yankawa.”
Hajiya kaka tayi murmushi kawai sannan ta kalleshi tace.
    “A’ah Muhammad na bar maka ka wakilceni ku yanka Allah ya k’aro shekaru masu albarka.”
Duk suka ce Amin sannan ya kama hannunta ita kam sai faman kallonshi take fuskarta sai murmushi take hawaye na zirarowa a haka suka yanka cake d’in ya d’akko tare da sanya mata a baki ya k’arasa wajan hajiya kaka tare da cewa,
    “Hajiya ha ha bakinki.”
Dariya tayi tare da kawar da kai tace,
    “Muhammad ni meya had’ani da cin wannan abun?na yafe ni kam in ba so kake ana murnar shekaran wata sun karoba ni kuma a zauna ana kukan nawa sun k’are kuje kuci abinku banaci nidai.”
Sultan yayi dariya tare da matsawa kusa da Al-eemin ya sanya mai a baki ya d’an gutsira kad’an shima yana dariya kafin hajiya kaka ta fita tana share kwalla domin duk sanda ta tuna rasuwar iyayan Balqees sai taji wani irin yanayi tausayin Balqees kuma ya k’aru a cikin zuciyarta.tana fita Al-eemin ma yabi bayanta dan wucewa zai yi, Sultan ya juya baya cikin wata drower ya bud’e tare da d’akko wani kyakyawan agogo ya mik’e mata yace.
    “Baby ga geft d’ina wishing you long life.”
Karb’a tayi ita gaba d’aya ma ta kasa cewa komai tana bud’e wa wata takarda ta fad’o a hankali ta sunkuya ta d’auka shi kuma sai d’aukarta pics yake yi ba tare da ya bari ta shirya ba kawai duk yadda tayi sai ya d’auketa,bud’e takardar tayi taga wani kyakyawan rubutu tamkar bada hannu aka rubuta shiba sai taga birthday massage ne tafara karantawa.
_So you are officially 18 now! Happy Eighteenth Birthday._
    _For all the bills that you will pay For all the career advice you will get For all the things, you may have to do There will be no looking back from here Welcome to the club 18 my dear sister Have an awesome time here Happy 18th birthday to you my sweet daughter (baby qees)!_
Lumshe idanuwa tayi gaba d’aya ma ta rasa ya zatayi,bud’esu tayi tare da watsa su a saman fuskarshi yana zaune bakin gado dan shima ita yake kallo ba zato bare tsammani kawai yaji ta sakar mai kiss akan lips d’inshi kafin ta rungumeshi a hankali ta furta.
    “Thanks you brother for all what you did to me, I love you so…so much.”
Zare ta yayi daga jikinshi yana kallonta cike da mamakin kiss d’in da yaga tayi mishi,yana k’ok’arin yi mata magana wayar hannunshi ta fara ring ya duba sai yaga Nadiya ce bari yayi ta katse sannan ya kirata Balqees na tsaye tana d’aura agogon daya bata taji yana cewa.
     “Umm ai babu abinda zaki ce na yadda tunda kikak’i zuwa yiwa daughter murna.”
    “Ohh nak’i wayon duk wani kwana-kwanarki na gane ta k’in zuwa ne kuma zan rama.”
Har yayi ya gama soyayyar shi Balqees najin shi, kawai dai batajin abinda Nadiya ke cewa,sai da ya gama sannan ya mik’e tsaye yana gyara links din hannun rigarshi yace.
    “Baby wucewa zanyi gobe inada lecture gashi ina son in saki duba lecture notes d’in bye.”
    “Bye Yaya Zulqallain.”
Ta fad’a a hankali,fita yayi tayi saurin komawa kan gadon setin inda ya tashi ta zauna tare da dafe kanta da hannu ta fara tunanin yadda zata yakice shi daga gurbin inda ta sanyashi domin taga alamar bai san tana sonshi ba,beson son da take mishi na aure bane ba kawai yana d’aukar ta wani daban da yadda ta d’auke shi ta kuma sakin kuka tare da fad’awa gadon ta cusa kanta cikin pillow tana kuka.
    “Wifey! Wifey kukan me kikeyi kodan banzo dubiya ba?am so sorry bar kukan kinsan bana gari ne naje barno d’azun nan na dawo.”
Tunda ya shigo bata ko motsa daga inda take ba tana kwance kan gado k’asan rigar jikinta tayi mata lullub’i ya k’arasa inda take tare da sanya hannu dai-dai kugunta da nufin ya d’agota tayi saurin ture mai hannun tare da mik’ewa zaune idanunta jawur tafara zabga mai harara kamar idon zai fad’o.
    “Wow!you’re 18 today meyasa biki gaya min ba?!”
   “Sabida baka cancancin ka saniba,wai Yaya Yusif me kake so a gurina ne da duk kabi ka matsa min nida rayuwata?!”
Bakin ta kawai yake kallo yadda take motsa shi yayi saurin lasar nashi yana gyara zama yace.
    “Sabida ni zan aureki.”
    “Mtww!.”
Mik’ewa yayi tare da karasawa kusa da cake d’in ya gutsira yaci sannan ya taho da wani ya dawo gurinta.
    “Happy birthday wifey.”
Ya fad’a yana kokarin sanya mata a baki,saurin tankwab’ewa tayi cake d’in ya fad’i saman gado ya bita da kallo cikin takaici.fuskarta ya d’ago a fusace ya matse mata bakin cikin fad’a yace.
    “Ke bari kiji na gaya miki duk wani salon iskancin da zaki sai dai kiyi,duk wani kauce-kaucenki kiyi ki gama amma baki da miji sai ni! idan ba haka ba wannan yaron da kike mannewa…”
Be k’arasa yayi kwafa tare da dungure mata kai,hannu ya kai ya cire hular kanta tare da cusa yatsunshi cikin gashin yana janshi.Balqees ta rushe da kuka cikin d’aga murya ta kwalawa hajiya kaka kira da k’arfi….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *