TATTALINTA CHAPTER 4

TATTALINTA




CHAPTER 4





*H*ajiya kaka dake cikin d’akinta ta fito da kyar domin girma yazo mata sosai,d’akin Balqees ta shiga hannunta rik’e da casbaha tana shiga taga sai faman kokawa akeyi tsakanin Yusif da Balqees ta k’arasa gurin tana caud’a masa cikin fad’a take cewa.
“Wai kai wane irin wawan yaro ne ah?iskancin naka yakai ya kawo saika lalata ‘yar Amana ko?toh ubanka zakaci wawa kawai tashi ka barmin gida ko ranka ya b’aci.”
Tashi yayi tsaye ya matsa kusa da kaka ai kuwa ta caula mai caibin ba tare da yaji zafi ba yace mata.
“Ke daure a d’aura mana aure a cikin week d’innan idan ba haka ba kuma k’ad.”
Yayi kwafa tare da lakucewa hajiya kakan hanci ya fita, k’arasawa tayi gurin Balqees tana kallonta cikin sanyin murya tace,
“Kinga tashi kirawo min Muhammad gara ya maidake can gidan su gara can da nan maza kira min shi a wayarki.”
Balqees na kuka ta d’auki wayan ta kira Sultan,tana jin ya d’aga ta bawa hajiya kaka tace maza-maza yazo tana son ganin shi,Sultan yace tabari ayi sallan isha’i sabida ankira kaka tace mai toh. Ai kuwa ana idarwa sai gashi ya k’arasa a mashin d’inshi,yana shiga hajiya kaka ta kalleshi tace.
“Yau ba sai gobe ba zaka tafi da yarinyar nan can gidan ku sabida wannan wawan yaron na rasa uban me yake neman a gurinta.”
“Hajiya wane yaro kenan?!”
“Yusif mana, kana fita ya shigo wallahi yaron nan bashi da kunya wai idan bansa anyi musu aure ba yayi min kwafa toh kaga tunda iskancin nashi yazo nan gara ka tafi da ita kar aje ina can yazo ya cuceta.”
Shafa kanshi yayi ranshi a yana tunanin shin Yusif wane irin mutum ne,kallon hajiya kaka yayi cikin jimami yace,
“Amma hajiya ni a ganina nan gidan yafiwa baby kwanciyar hankali kinsan halin Umma sam bansan abinda yake sa k’in had’uwar jininsu ba wallahi.” 

Balqees ce ta shigo d’akin hawaye fal fuskarta ta k’arasa kusa da kaka ta zauna,ganin hawaye a fuskarta ya kuma d’aga mai hankali cikin kuka Balqees tace.
    “Kaka ki bari ni bazanje gidan su Yaya Sultan ma sabida sam Umma bata sona, anan kuma idan na zauna ina cikin hatsari hajiya kaka please ki bari a cikin satin nan na tafi ethopoeia dama ina son naje na gansu tunda na rasa Ummi ban kuma zuwa ba.”
Sultan yaji tamkar zai yi hawaye dan ba k’aramin tausayinta yaji ba,muryar kaka yaji tana cewa.
    “Nima baby ina son kije domin yayar mahaifiyar ki itama tayo mana waya cewar dan Allah a barki kije kafin ki fara makaranta,insha Allah a cikin satin nan zaki tafi share hawayenki.”
     “Nagode kaka dake da Yaya Sultan da abban shi da Adda Aisha kuna sona kuna jidani Allah ya saka muku da alkairi ina alfahari daku a cikin rayuwata.”
Rungumota hajiya kaka tayi jikinta tana shafar bayanta,tashi Sultan yayi itama Balqees tabi bayanshi ya kamo hannunta suka zauna a parlorn kaka,kallonta yayi cikin tausayawa yace.
    “Ethopoeia zaki tafi?baby nasan idan kikaje da kyar in zasu barki ki dawo nan, me yasa ba zaki bari in samu lokaci mu tafi tare muyi kwana biyu mu dawo tare ba?!”
Hawayan fuskarta ta share sannan ta riko hannunshi cikin nata tace,
    “Yaya gara na tafi idan ba haka ba ina cikin tashin hankali kayi hakuri ka barni na tafi wata kila na samu nutsuwar zuciyata.”
     “Shikenan baby zamu yi magana da Abba sai ki fara shiri nasan zanyi missing d’inki.”
Wani irin dimm taji tafara tunanin,
   “shin wane irin missing nata zai yi?inama ace irin wanda zata yi zai yi,inama ace irin son da take mishi yake mata.”
   “Tashi kije kiyi sallan isha’i sai ki kwanta kiyi bacci insha Allahu duk yadda muka yi da Abba zakiji.”
Kai kawai ta d’aga tana faman binshi da kallo har ya mik’e ya fita, yana tafiya ta koma d’akin hajiya kaka bayan tayi sallah taci abinci sai tabi lafiyar gado ta kwanta zuciyarta sai faman sake-sake take yi mata. Sultan kuwa bayan ya koma gida bedroom d’in abban shi ya wuce nan ya tarar da Abba da Umman shi,guri ya samu bayan ya gaida su ba tare da ya kalli inda Umma take zaune ba ya sanar da abban shi zancen tafiyar Balqees ethopoeia da kuma yadda Yusif ke neman b’ata mata rayuwa yana direwa Umma tace.
    “Toh Ahmad ta tafi mana ai kaga kaima kayi abubuwan dake gabanka.”
Abba yayi murmushi sannan ya kalli Umma cike da mamaki yace,
   “Zata tafi insha Allahu.”
Sannan ya maida kallonshi gurin Sultan yace,
   “Ahmad gobe idan Allah ya kaimu akwai wasu kud’i da zan samu idan har sunzo sai ayi mata viser ai dama ya cancanci taje ta gansu su ganta.”
Sultan yayi murmushi tare da yiwa abba godiya,Umma ta sakar mai harara yak’i kallonta bare ya nuna ya gani ya sanya kai ya fita yana jin dad’i dan shima yana son yaga ya cikawa baby burinta. 

Story continues below


Haka aka yi kuwa cikin kwanaki biyar aka gama komai na tafiyar Balqees ethopoeia ‘yan uwan Maman ta na can sai murna suke yi zata zo, ranar asabar ta gama shirinta Sultan da kanshi ya d’auke ya kakakaita gidan ‘yan uwa sukayi salama, gidan su Yusif shine gida na bakwai da sukaje a parlor suka tarar da mommy zaune tana duba wasu kaya na yara Sultan yayi sallama suka shiga,mommy tayi murmushi tare da fad’in.
   “Lallai Ahmad dama kana zuwa gidan mutane?!”
Sultan ya sosa cikin kunnan shi yana murmushi,sai da suka samu guri suka zauna sannan yace.
    “Mami ina nan mana ko ranar d’aurin auran su Al-eemin ai na shigo.”
Tab’e baki tayi dan tasan zai yi wahala ace anzo dashi gida kasan cewar ba zuwa yake yi ba sai idan wani abun ne ya tashi wanda ya zamar mishi zuwa dole,muryar Balqees ce ta katse shirun ta hanyar gaida Mami d’in.
    “Mami ina yini?!”
   “Lafiya lau Balqees ya jikin ki?!”
Tace “da sauki Mami zuwa nayi na muku sallama zan tafi ethopoeia.”
Da mamaki Mami ta kalleta tace,
   “Balqees kice gudun Mu zaki yi ko?toh idan kika tafi sai yaushe zaki dawo?!”
Balqees tayi murmushi dai-dai lokacin Yusif da fateema suka shigo da mamaki ya Yusif kallesu yana k’ok’arin zama kusa da Balqees yace,
   “Tab! Kice yau za’ayi mana ruwa da kankara wifey kece a gidan mu yau?!”
   “Ka gansu nan dai yanzun ma sallama suka zo yi mana.”
Mami ta fad’a tana zuba kayan da,ta gama gani cikin wata trolly Yusif ya zaro manyan idanunshi yace.
   “Sallama kuma ta meye?!”
   “Wai ethopoeia zata tafi kuma a yau d’innan ma.”
Mami ta kuma fad’a Fateema ta kali Balqees cikin turo baki tace,
   “Sister shine ba neman ‘yar rakiya?!”
    “Sorry sister naga kuna school ne shi yasa.”
Balqees ta fad’a tana kamo hannunta alamar ban hakuri yayin da Yusif ya kalleta fuskar shi cike da bak’in ciki yace mata.
    “Amma dan rashin mutunci shine zaki yi tafiya baza’a sanar dani ba?nasan hakan ma duk munafunci ne da banzo na tarar daku anan ba kenan sai dai kawai naji labarin kin tafi kenan?!”
Yusif ya fad’a yana faman wani had’e rai cikin rashin damuwa Sultan yayi murmushi be ce komai ba,ganin haka yasa shi ci gaba da masifa tamkar wani wanda ya riga ya aureta babu wanda ya kulashi hatta mami ganin yaki yin shiru yasa Sultan kallan Mami yace.
    “Mami bari mu wuce 5:30pm zasu wuce idan daddy ya dawo ace munzo.”
   “Zan sanar dashi insha Allahu.”
  “Sister sai wata rana.”
Fateema ta fad’a tana d’agawa Balqees hannu,Aisha na hangensu ta window har suka shiga mota suka bar harabar gidan ta tab’e baki tare da jan tsaki,da za’a bata bindiga ace ta harbi wani toh lashakka Sultan zata fara harbewa domin yanzu wata wutar kaunar shi ce take ruruwa cikin zuciyar ta. 

Sultan na fita ya d’auki hanyar gidan su Nadiya nan da nan Balqees ta b’ata rai cikin turo baki tace,
   “Yaya wai ina zamu..?!”
   “Gurin Nadiya.”
Ta kuma b’ata rai yayi murmushi tare da kallonta yace.
   “Ko ba zaki je kuyi sallama bane baby?ita fa zan aura me yasa bakya nuna mata kauna kinja har ta gano cewar baki santa wannan dalilin ne yasa ko zuwa dubaki batayi na lokacin da baki da lafiya.”
    “Ni cewa nayi bana sonta?kawai fa wallahi ta fiya iyayi.”
Dariya yayi sosai har yana dukan sitiyari ita kuma ta bishi da kallo cike da jin haushi wato ma dariya ta bashi dan ya maida ita wawuya,yana shan kwanar gidan yace mata.
   “Baby kinsan kuwa iyayinta ne yaja ra’ayina akan ta?wallahi komai na ta sha’awa yake bani babu abinda zatayi be bani sha’awa ba ina son Nadiya kinsan ranar Wednesday za’a kai kud’i da sa ranar auran mu?!”
    “Ranar Aure Yaya?!”
    “Insha Allahu amma fa ban sanar da kowa ba sai Abba da Umma,dan Allah baby ki dena yin abunda Nadiya zata ga kamar bakya sonta kinji baby na?!”
Shiru tayi bata kuma magana ba har sukayi parking a k’ofar get d’in,waya ya ciro ya Kara a kunne tare da cewa.
   “Gamu mun iso kizo kinsan sauri muke.”
Ajiye wayan yayi yana kallon Balqees wadda idanuwanta suka ciko da hawaye yayi saurin zaro ido yana tambayarta.
    “Mene kuma baby? Toh ko bakya son nayi auren baby? Kinsan jikina ne yake b’oye shekaruna da nasan Nadiya baxa ta aure ni ba.”
Kafin ta bashi amsa saiga Nadiya ta fito sanye da hijjab har yana jan k’asa fuskarta cike da murmushi ta k’arasa tana fad’in.
  “Oyo-yo daughter.”
  “Ina yini?!”
Ta fad’a da sauri dan kar so gano wani abun,da mamaki Nadiya ta amsa dan batayi zato ko tsammanin hakan ba daga bakin ta.
   “Lafiya lau daughter yau sai gida?Allah ya kaiku lafiya yasa ki dawo lafiya a gaida mana da kowa da kowa.”
    “Toh.”
Kawai ta fad’a sannan Nadiya ta maida kallonta wajan Sultan sai faman hararta yake yi tayi dariya tare da cewa.
   “Ya ne?!”
Sultan ya sosai kai tare da tab’e baki yace.
    “Gani nayi kamar baki san dani aka zo ba.”
Dariya ta kuma yi suka kalli juna ya kashe mata ido d’aya caraf a kan na Balqees ta d’auke kai tare da kallon agogon dake manne a fatar tsintsiyar hannunta ta kuma d’auke kai tace.
   “Ammh Yaya 4:49pm fa zan makara.”
   “Madam bari mu wuce zan dawo zuwa dare ki ajiye min abun dad’i.”
Sultan ya fad’a yana kallon Nadiya bayan ya tada motar,Balqees ta yatsina fuska gabaki d’aya ji take tamkar ta shak’e su,da kyar suka rabu kamar ta saki kuka a gurin amma ta daure ba tayi ba ta k’agara su tafi tabar k’asar ma gabaki d’aya.sosai Nadiya tayi mata fatan alkairi da fatan alkairi sannan sultan yaja motar suka tafi yana ta faman janta da hira,suna zuwa layin gidan hajiya kaka Sultan yaji an buga mai glass d’in gaban mota yayi saurin taka burki kafin yayi wani abun yaji an doka mai wani abu wanda yasa jinshi da ganinshi d’aukewa Balqees kuma aka toshe mata baki da wani kyalle wanda yasa ta sumewa a gurin gabaki d’aya, d’auke ta aka yi shi kuma aka barshi a kusa da motar suka tafi….

    *W*ani inyamuri ne mok’ocin su hajiya kaka yazo wucewa a motar shi zai wuce gidan shi yaga ba alamar motar dake gurin za’a motsa ta, horn ya din ga yi amma ba’a kauce mai ba hakan yasa shi fitowa dan yin magana sai kawai yaga Sultan kwance a k’asa k’ofar motar a bud’e jini na zuba daga kanshi inyamurin yace.
   “Heeeeyyyy nawayo.!!”
Ya fad’a da k’arfi yana zagaye gurin dai-dai lokacin Abba da Umma suka shawo kwanar gidan hajiya kaka lokqcin masu gadin mak’ota suka fara fitowa, cike da mamaki Umma tace,
    “Me Sultan yake min da mota anan gurin?!”
Gani suka yi an cicicib’eshi ana kokarin sanya shi cikin motar inyamurin, cikin tashin hankali Abba yace.
   “Toh ai ke Sultan ne ake sawa a wata motar.”
   “Innalillahi wa’inna’ilaihir rajiun.”
Cikin tashin hankali suka fito daga mota suka nufi gurin lokacin har an sanya shi a bayan motar, da Abban aka wuce zuwa asibiti ita kuma Umma ta shiga gidan hajiya kaka nan ta sanar mata da abinda suka gani hajiya kaka ba zama tasa suka bisu a baya. Su Mami, Fateema, Aisha da Yaya Yusif suna nan zaune Yusif sai masifa yake akan Balqees zata yi tafiya amma bata sanar mai ba kawai sai ga kiran daddy cewar an sace Balqees Sultan Ahmad kuma yana  kwance a asiiti. suna jin haka gabaki d’ayan su suka tafi asibitin cikin tashin hankali. har kusan sha d’ayan dare Sultan be cikin haiyacin shi sai da temakon oxygen yake samun damar yin numfashi, tashin hankali iya tashi duk family d’in suna cikin shi ga uwa uba rashin ganin Balqees sama ko k’asa an nemeta an rasa hakan ya janyo hawan jinin hajiya kaka ya tashi.
    “Wannan wane irin bala’i ne?toh waye ya sace Balqees gashi ‘yan uwan Ummi d’inta sai waya suke yi sunji shiru me zamu ce musu?!”
Abba ya fad’a hankalin shi a mugun tashe, Adda Aisha da hajiya Asma’u suka zauna wajan hajiya kaka har wajan k’arfe d’aya duk suna asibitin I.b da Al-eeman abba yace su tafi gida sabida matan su, gaba d’aya babu wanda yaso wannan hukuncin amma ba yadda zasu yi haka suka tafi harda Yusif dake ta faman sambatu wai an sace mishi mata. Ibrahim ne duk yaje ya kaisu gida kafin shima ya wuce nashi gidan.
   “Hello tana ina?!”
   “Gata nan ta dawo cikin hankalinta sai faman kuke-kuke take tana kiran wannan guy d’in.”
   “Ok gani nan zuwa tace abinci ne?!”
   “A’ah oga ai babu wani a k’asa.”
   “Toh ku bari ina zuwa zan taho mata da abinci.”
Yana kaiwa nan ya kashe wayar sannan ya nufi cikin gidan,babu kowa hakan ya bashi damar shiga cikin kitchen yayi sa’ar samun tuwon shinkafa miyar ganye ya zuba a goodflax tare da d’aukan ruwan roba ya fita. Cikin wani had’add’an guest house ya shiga bakin Shi d’auke da fito har ya k’arasa cikin d’akin da ya bada umarnin cewa a sata ciki. Shiga yayi bakin shi d’auke da sallama kamar mutumin kirki Balqees ta d’ago jajayan idanuwanta ta d’ora akan fuskar shi cikin tsananin kad’uwa da shiga tashin hankali da rud’ani tace.
   “Ya..ya yaya Yusif..!”
   “Na’am wifey, gaki ga new  ethopoeia wadda zamu rayu cikin ta daga ni sai ke.”
    “Innalillahi wa’innailaihir rajiun Yaya Yusif me kake shirin aikata min,me yasa kayi min haka kaga yadda suka yiwa Yaya Sultan kuwa?wallahi kila sun kashe shi nima na san mutuwa zanyi…”
Shhhhiii..! Ya fad’a yana d’ora yatsan shi akan lips d’in shi, juya idanuwan shi yayi yana kallonta ya d’akko bindiga yana shafarta nan da nan cikin Balqees ya kuma durar ruwa jikinta ya fara rawa ya tura mata foodflax d’in gaban yace.
   “Oya zauna kici tuwo karki sake kiyi min gardama wallahi ranki ne zai b’aci, ki d’uki leda d’aya ki cinye shi tass kafin nan da k’arfe 1:30 kinga yanzu muna 1:19am. Da sauri Balqees ta janyo flaxe d’in tana hawaye jikinta na rawa bata tab’a tunanin iskancin Yusif ya kai a same shi da bindiga ba, tana gama bud’e leda d’ayan ta fara dannawa cikinta tuwon baji ba gani kamar Allah ya aiko ta har kwarewa take yi sabida tsabar sauri shi kuma Yusif sai murmushi yake dan yasan idan ba haka yayi mata ba to haka zata kwana da yinwa. yana gurin ta gama ci da kanshi ya bud’emata ruwan ya mik’a mata hannunta na rawa ta karb’a yayi saurin had’e shi da nashi yana Mata wani irin kallo ta kawar da kai kirjinta sai bugawa yake yi gashi tuwon yayi mata sak’e-sak’e a wuyan ta.
   “Kina sona Maryam?!”
Yayi maganar a hankali dai-dai kunnanta, Balqees tayi saurin d’aga mai kai alamar eh yayi murmushi har hakuranshi suka fito sannan ya d’ago da kanta yace.
   “Wane irin so kike yi min Maryam?!”
Balqees ta kuma share hawayen ta sannan tayi k’asa da kai bakinta na rawa tace.
   “Irin wanda kake yi min Yaya Yusif!”
    “Shi kuma Sultan Ahmad fa wane iri kike yi mai naji kina cewa idan ya mutu kema mutuwa zaki yi.?!”
Ya tambaya bayan yayi micin-micin da idanuwa, kirjin Balqees ya tsananta bugawa cikinta kuwa shi kanshi Yusif yana jiyo kukan da yake yi kulululu, Yusif ya kuma had’e rai tare da kuma kara mata bindigar a keyarta yace.
    “Tambayar ki nake yi wane irin so kikewa Sultan Ahmad?!”
Baki na rawa hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta tace,
   “Broth Yusif shima irin son da yake min shi nake mai.”
  “Karya kike yi Balqees ki sanar dani gaskiya.”
  “Wallahi Yaya Yusif kaga shine ya zame min uwa uba bayan na rasa nawa iyayen, mun shaku dashi shakuwa mai d’inbin yawa amma daga shi babu wani abun.”
Ta fad’a tana kuma rushewa da kuka, Yusif ya mik’e tsaye tare da k’ara musu k’arfin iskar fankar d’akin ganin duk tayi sharkaf da gumi ya koma inda ya tashi ya zauna, kallonta yayi yaga duk ta takure jikinta sai rawa yake yace.
   “Toh sanar dani waye kwanaki kika tab’a ce min shi kike so kuma har kike sanar min cewar yana da kishin ki.!”
   “Wallahi broth wasa nake yi, bana tsayawa da kowa ba kuma na kula kowa.”
   “Toh naji yanzu ki kwanta kiyi bacci nan gidan kine, nan da kwanaki kad’an zakiji sanarwar d’aurin auran mu.”
Da sauri Balqees ta kalleshi ya d’aga mata kai alamar tabbacin abinda ya fad’a ta had’iyi wani zazzafan yawu ma d’aci, duk tana yin wannan abubuwan ne dan karya gurb’ata mata rayuwa ta maida kanta ta kwanta zuciyar ta na bugawa tsoro mai tsanani ya shigeta tunanin Sultan ya mamaye zuciyar ta ko yana wane hali yanzun oho. Rintsa idanuwa tayi kamar me bacci hakan yasa shi mik’ewa yayi murmushi wanda baxaka tab’a gane kona meye ba yasa kai ya fita, tana jin lokacin da ya murza mukuli a jikin kofar ta kuma sakin wani kukan babu wanda take tunowa sai Yaya Sultan da hajiya kaka domin tasan duk duniya sune masoyanta na hakika, tasan babu wanda zai yi tunani ga wanda ya sace ta duk cikin family d’insu tunda ita kanta sai yanzu ta ganshi tama rasa me zata kira da wannan abun _Mugunta ko So_?bata sani ba ta kasa tantancewa. 

Kasa rintsawa tayi sai aikin kuka da take yi. A asibiti kuwa sai gab da asuba sannan Sultan Ahmad ya fara motsawa da kanshi ba tare da temakwan wani abun ba, hajiya Asma’u dake kusa dashi a zaune wadda itama da
alama bata samu ta rintsaba tayi saurin sake kallon hannunshi wanda ya motsa taga still ya ci gaba dayi tayi saurin tashi ta fita dan kiran Dr gadanya wanda shima a asibitin ya kwana sabida irin haka. Kwankwasa ofis d’in tayi yayi saurin fitowa hajiya Asma’u ta sanar dashi gaba d’aya suka koma d’akin da yake kwance,juya kai suka tarar yana yi Dr gadanya yayi saurin zuwa ya cire mishi na’orar oxygen d’in yana duba shi a hankali ya fara d’aga hannun shi alamar yana neman wani abun.
    “Ahmad! Ahmad!!.”
Dr gadanya ya fara kiran shi a hankali har ya samu Ahmad d’in ya fara sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai da ya dad’e yana yin haka sannan ya dena yi Dr gadanya yayi mai gwaje-gwaje sannan ya fara bud’e idanuwa a hankali har ya sauke su akan na Dr shi kuma ya sakar mai murmushi yace.
   “Sannu Ahmad.”
Sultan ya d’aga mai kai ba tare da yayi magana ba cikin harshen turanci yake tambayar shi yadda ya keji sai dai beyi magana ba sai d’aga mai kai da yake yi yana kuma bin d’akin da kallo daga gani akwai abinda yake nema, Dr gadanya ya sunkuya kusa dashi yace.
     “Wa kake nema?!”
Kamar ba zai yi magana ba can kuma bakin ya fara motsawa Dr gadanya ya kura mai ido dan gano abinda yake son cewa, a hankali yaji yana furta.
    “Baby! Baby!! Daughter.!!!”
Da sauri Dr gadanya ya fita yana fita ya tarar da ‘yan uwan nashi tsaye a bakin kofa harda hajiya kaka wadda farkawar ta kenan ya bisu da kallo gwanin ban tausayi, Nadiya ce tayi magana cikin rawar murya ta.
    “Likita ya jikin nashi?!”
    “Alhamdulillah ya farfad’o sai dai yana ta faman neman baby yana cewa daughter yana son yasan halin da take ciki sai dai a yanzu bama buk’atar a sanar dashi cewar anyi kidnapping d’inta, san samu duk wanda ya tambaya ya ce mishi tana d’akin hutu itama tana cikin asibitin har muga lokacin da nutsuwa ta saukar mishi sosai, ina fatan kun gane za kuma ku bamu had’in kai wajan ganin be samu wata matsala ba kamar yanzu da muka yi sa’a babu wata larura a tattare dashi..?!”
   “Insha Allah likita.”
Suka fad’a a tare, hajiya kaka ta kalli Dr gadanya tace.
   “Likita zamu iya ganin shi yanzu?!”
   “Yah zaku iya sai dai kar wanda ya nuna mai cewar akwai wata matsalar musamman ma akan ita wadda yake kira baby.”
Suka amsa mai sannan ya fito su kuma suka shiga kowa hankalinshi a tashe.

    
    *A* lumshe suka tarar da idon shi hajiya kaka tayi saurin rik’e mai hannu still be bud’e ba cikin alhini hajiyan tace,
   “Muhammad ko kayi bacci ne?!”
Nan ma shiru Abba ya k’arasa gurin tare da kiran sunan shi amma ya kasa bud’e idanuwan duk da cewar yana jinsu, ya jima a haka kafin ya fara bud’e idon a hankali ya tsaidasu akan Umman shi wadda ke tsaye hannuwan ta dafe a saman k’irjinta ya fara k’ok’arin tashi amma ya kasa abba yace.
    “Karka tashi Ahmad ka bari ruwan da aka sanya maka ya k’are tukunna.”
Ya d’aga mai kai alamar toh sannan ya kalli hajiya kaka sai yaga tana hawaye cikin sanyin murya dama gata sassanya ta kuma had’u da ciwo sai ta k’arayin sanyi ya kamo hannunta da ta rik’e mishi nashi yana faman lumshe ido yace.
    “Hajiya babba ina baby ne? Wai shin me nayi naji anyi sama dani? ko dai accident nayi tunda gani a asibiti, Allah yasa banjiwa baby ciwo ba, hajiya Allah yasa ni kad’ai ne naji.”
Rasa abinda zata ce mishi tayi sai hawaye, can Abba yayi magana cikin kwantar da hankali yace yace.
    “Karka damu Ahmad, Maryam tana d’akin hutu ita babu abinda ya sameta buguwa ce kawai sannan motar ce ta kwace maka.”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kuma maida idanunshi ya kulle, ya d’auki tsawan lokaci a haka sannan ya bud’e ga mamakin shi hajiya Asma’u ya gani da Nadiya sauran sun fita ya kalleta sai yaga idanuwan nan nata sunyi jawur da alama kuka tasha ya kalleta yace.
   “Nadi zonan me yasa ki yin kuka?!”
K’arasawa tayi ta d’an tsaya nesa dashi ya nuna mata bakin gado da idanunshi alamar ta zauna a gurin, sai ta girgiza mai kai a hankali alamar a’a tace mai.
   “Ya jikin?!”
Yayi shiru yana bin fuskarta da ido can yayi murmushi cikin cizon lebensa na k’asa yace.
   “Nadi gaya min abinda yake faruwa akwai abinda kike son b’oye min,kin san dai babu abinda zaki yi wanda bazan gano ba sai kawai ban san ko meye ba kamar yadda kema kike gano halin da nake ciki,so ki sanar dani abinda ke zuciyarki.”
Idanuwanta ne suka sake tsatso da ruwan hawaye amma tayi saurin mayar dasu dan bata san ya kuma gano tashin hankalin da take ciki ta sugunna a k’asa murya na rawa tace.
   “Mine ina tsoro ne karna rasaka hankalina a tashe yake da ganin yanayin ka.”
  “Ohh my Nadi…!”
Ya fad’a yana lumshe ido tayi saurin kallonshi lokacin ya bud’e idanuwan Sultan yayi murmushi sannan yace.
   “Nadi insha Allahu bazan mutu ba sai na zama mallakinki kuma sai na aurar da baby da hannunna,ki dena kuka kinji my Nadi my love my wife.”
Kuka ta kuma rushewa dashi mai had’e da murmushin yak’e tayi saurin mik’ewa tana kallonshi murya k’asa-k’asa tace.
   “Bari naje nayi sallah.”
Tayi saurin juyawa yace
   “Nadi..zo kiji.”
Ya fad’a lokacin hajiya Asma’u ta shiga toilet kirjin Nadiya ya bugawa ta d’an matsa kusa dashi ya kalleta a hankali yace.
   “Muje ki rakani naga jikin baby please.”
Nadiya ta zaro mai manyan idanuwanun ta jikin ta ya fara rawa da kyar ta fara mai magana bakinta na rawa tace.
   “Ya Sultan bari na fara lek’awa na gani ko suna bari a shiga yanzu sai nazo muje kafin su Abba su dawo daga masallaci ina zuwa.”
Tana fad’ar haka tayi waje tun yana jiranta har ya fitar da ran zai sake ganinta ya lumshe ido yana sak’a da war-warar abinda ya hanata dawowa. 

Bacci ne ya kuma d’aukar shi har su Abba suka dawo ganin yana bacci yasa suka tafi police station dan jin yadda za’a fara neman Balqees kasan cewar jiya ‘yan sandan sun fara bin cike. Wajan karfe 7:45am ya farka yana tashi yaga su I.b da Jamila Matar shi Aisha zaune sunyi jugum-jugum I.b yayi saurin k’arasawa wajan shi yace.
    “Jinin sannu.”
    “Yauwa jinin banyi sallahr asuba ba dan Allah temaka.”
   “Ok toh tashi na raka ka kayo alwala.”
K’ok’arin d’aga shi yayi Sultan yayi saurin komawa ya kwanta tare da rintsa ido yana wani huci, sai da yaji kan nashi ya dena zugi sannan yace.
   “Jinin bazan iya ba kaina kamar zai cire ga wannan bandege d’in duk ta jik’e da jini ya zanyi?!”
Ibrahim ya rik’e ha6arshi yana tunani can dai ya kalli Sultan yace.
   “Jinin gaskiya baza ka iya ba sai dai Kayi sallan daga kwance sai na yi ma alwalar ko shasshafawa ne sai ayi ma.”
    “Yauwa jinin na gode ma.”
Ya fad’a yana sauke numfashi da sauri da sauri da alama yana shan wahala amma baya son a gane ga idanuwan shi sun kumbura wanda da alama ciwon kanshi ne ya haddasa mai hakan. 

Story continues below


A kwance yayi sallar yana idarwa ya kalli I.b yace,
   “Jinin ina Nadiya?!”
Ibrahim ya kalleshi tare da komawa kusa dashi ya zauna yace.
   “Suna reception ita dasu Umma.”
   “Hmmm shine ta san ita nake jira amma tak’i shigowa ko?dan Allah jinin temaka min zaka yi wallahi hankalina yak’i kwanciya.”
    “Dame fa?!”
I.b ya tambaya yana kollanshi,Sultan ya sauke numfashi sannan yace.
   “Ina wayar ka?!”
   “Gata nan wani abu?!”
I.b ya sake tambaya yana zaro wayar daga cikin aljihunshi,karb’a sultan yayi sannan ya kalli Jamila yace.
   “Jamcy ina taki?!”
Itama ta d’akko tace,
    “Gata nan Yaya Sultan.”
Yace,
    “Yauwa good kin san me zaki min?zuwa zaki d’akin da aka kwantar da baby ki bata ni kuma zan bugo da wannan sai naji muryarta idan ba haka ba hankalina ba zai kwanta ba.”
Nan da nan suka fara kallon-kallo duk sun rasa me zasu ce mai,shigowar su hajiya kaka dasu Umma da Nadiya da Adda Aisha da hajiya Asma’u shine yasa suka sauk’e ajiyar zuciya kusan duk a tare Sultan yabi Jamila da kallo wadda ta zaro idanuwa tana rarraba su hajiya kaka tace.
   “Muhammadu ya jikin naka?!”
Sultan yace,
   “Hajiya da sauk’i, amma me yasa ba kwa san had’ani da baby kowa na tambaya sai ya fara kallona ko ciwon hauka nake yi ne,ku sanar dani ko na yi sanadiyar mutuwarta ne duk kuka kasa fad’a min…?!”
   “Idan baka yi sanadin mutuwar ta ba ai kayi sanadiyar da yasa aka sace ta ko..!”
Suka jiyo muryar Yusif dake shigowa d’akin yana fad’a fuskar nan tashi a matukar had’e ranshi a 6ace har ya shiga ciki be dena magana ba wanda yasa duk ya daskarar da mutanan wajan subida mamakin jin kalamanshi.
   “Kai wannan amma anyi d’an iskan yaro wallahi tallahi,banza wawa kawai toh ka gaya mishi kaji dad’i insha Allah kai zaka rigashi mutuwa.”
Hajiya kaka ta fad’a tana kallon Yusif sai huci ta ke yi sabida 6acin rai, Sultan kuwa gaba d’aya jin shi ne ya d’auke tunda kunnuwanshi suka jiyo mishi abinda Yusif d’in ya fad’a.
    “Ah toh karya nayi?bari kiji hajiya ni aka fi cuta wallahi sabida nine masoyinta mai shirin auranta kinga kuwa ni aka sanya cikin tashin hankali da damuwa,kuma da kike min fatan mutuwa insha Allah bazan mutu ba sai an gano min Balqees sai munyi rayuwar aure tare da ita kin goya d’anta sannan za….”
Kau..! yaji saukar mari a fuskar shi kafin ya k’arasa maganar da yake yi, a fusace shima ya d’aga hannu zai rama I.b yayi saurin rik’ewa jijiyoyin kanshi duk sun mik’e ya nuna shi da yatsa yace.
   “Karka soma yin wannan gangancin Yusif, mahaifiyarta kake gayawa magana ba zata iya jure jinsu ba,haka zalika akan idona ko a bayan sa ba zan yadda hannunka ya sauka akan fuskar mahaifiyata ba da sunan duka,wanda kai tayi maka ne da sunan gyara maka kuskuranka so ka ki yaye.” 

Wani mugun murmushi Yusif ya saki tare da fizge hannunshi daga rik’on da I.b yayi mishi,le6anshi ya ciza tare da juyawa yabar d’akin cike da jin zafin marin da Adda Aisha tayi mai tare da d’aukar alwashin sai ya wahalar dasu gabaki d’ayan su.
   “Ya subahanallah ya aka yi haka?!”
Cewar Dr gadanya bayan ya k’arasa wajan Sultan sakamakon kiranshi da Nadiya tayi,kallon shi hajiya kaka tayi tare da cewa.
    “Wan can mugun yaron ne yazo ya sanar mishi cewar ai sace Maryam aka yi,wallahi ban ta6a ganin mara mutuncin d’a ba irin Yusif tunda nake.”
   “Hasbunallahu wani’imal wakil, yanzu dai duk kufita waje bana son ganin kowa anan gurin.”
Gaba d’aya suka fita jikinsu a sanyaye yayin da hajiya kaka ke ta faman bala’i ta kalli Aisha da tayi shiru tana hawaye tace.
    “Ke Aisha ki sanar dani gaskiya kuka ce tun lokacin da su baby suka je gidan ku lokacin da suka fito Yusif na gida har sanda aka yi waya aka sanar muku yana gidan?!”
   “Wallahi hajiya duk muna tare dashi ko tashi beyi ba,hasalima masifa yake yi wai ba’a sanar mishi cewar zata tafi ethopoeia ba.”
Hajiya kaka ta sauke numfashi tare da fad’in.
    “Allah ya soshi amma wallahi banda haka ni kaina zan bada shedar cewa shine ya sace ta mugu kawai.”
Tayi maganar had’e da yin kwafa zuciyar ta na zafi su kuma su Adda Aisha sai tausarta suke suna tsoran kar hawan jininta ya sake tashi. 

Suna nan zaune a reception yayin da Dr gadanya da wasu nurses d’in ke cikin room d’in da Sultan yake sai ga ‘yan gidan su Nadiya suma sunzo a lokacin ne kuma Mamin su Yusif tazo d’auke da breakfast suka k’arasa, mahaifin Nadiya yaje suka gaisa da hajiya kaka kasan cewar shi babban likita ya sanya shi bayan sun gama gaisawa ya shiga cikin room d’in Dr gadanya na ganinshi ya tsaya tare da gaidashi cikin mamaki yace.
    “Ranka ya dad’e hala nemana kake yi ko?!”
Alhaji Nasuruddin ya kalleshi tare da k’arasawa gurin Sultan yana cewa.
    “A’a Dr nazo dubiya ne kasan yaron siriki na ne.”
Cike da mamaki Dr gadanya yace,
  “Masha Allah.”
  “Me ya faru dashi ne Dr?!”
Sultan na kwance mahaifin Nadiya yaje ya fara dubashi, nan shi kuma Dr gadanya ya sanar dashi tare da sanar mai da abinda Nadiya taje ta gaya mai ya d’ora da hakan ne ya haddasa mai bugawar zuciya.
   “Ya subhanallah.”
Mahaifin Nadiya ya fad’a sannan ya fara kokarin yin aikin shi domin ceto rayuwar sirikin nashi,sun jima a cikin room d’in kafin su fito. Da Nadiya suka fara had’a idanuwa hakan yasa mahaifinta sakin murmushi ta k’araso wajan shi ya riko hannunta suka k’arasa inda su hajiya kaka suke ganin duk sun zuba mai na mujiya yasa shi cewa.
   “Ba komai karku damu zai tashi successfully, ku dai tayi mai addu’a Allah kuma ya bayyana mana yarinyar nan.”
Duk suka had’a baki wajan cewa,
   “Amin Allah yasa.”
Sun dad’e a cikin asibitin kafin su tafi da kyar Nadiya ta bisu amma da cewa tayi ita tana nan har sai yaji sauki. Suna tafiya su kuma su Abba suka dawo duk sunyi wujiga-wujiga dasu sannan kai da kaga yana yinsu kasan babu wani sa’a sai ta Allah, anan aka sanar dasu abinda Yusif yayi,Abba dai kai kawai ya girgiza daddyn shi kuwa had’e rai yayi musamman da yaji hajiya kaka na ta faman zagin shi hakan yasa be dad’e ba a wajan ya tafi….

    
    *B*alqees kuwa ba ta samu damar rintsawa ba har garin Allah ya waye, kasan cewar akwai toilet cikin d’akin yasa ta shiga tayo alwala tare da hawa kan bedside carpet tayi sallah tana ta faman razgar kuka har ta idar. Tana nan a zaune taji ana bud’e k’ofar d’akin tayi saurin kwanciya a gurin tare da yin tamkar tana bacci sai dai ajiyar zuciya irinta wanda yayi kukan nan take ta faman saukewa,Yusif ya k’araso har inda take ya tsugunna tare da mirgino da ita Balqees tayi saurin tashi firgigita tamkar irin wadda ta farka daga nannauyan baccin nan ta kalleshi idanunta jawur ya sakar mata murmushi tare da kashe mata ido d’aya yace.
   “Wifey! Kin tashi lafiya?!”
Balqees tayi mai banza sai hawaye dake zubo mata ya d’an matsa kusa da ita tare da kamo hannunta, ta zare a hankali sai yayi murmushi yace. 

“Qees-Qees! mata ta takaina, me kike so na ci a kawo miki yanzu?!” 

Kai ta girgiza mai alamar babu komai yayi saurin sauya fuska daga fara’a zuwa had’eta yace, 

“Kallan ni nan.” 

A hankali ta d’ago ta kalleshi sai tayi saurin kawar da kai tare da cewa. 

“Yaya Yusif bana jin yinwa wallahi Allah.” 

Ya shafa kanshi tare lasar leb6ansa yana bin fuskarta da kallo,cikin kuka yaji muryarta tana cewa. 

“Yaya Yusif ka tausaya min ka rufamin asiri ka dubi maraicina ka maida ni,bani da kowa sai Allah sai ku da idan aka yi min irin wannan abun zaku yi duk yadda zaku yi wajan ganin kun sameni amma me yasa kayi min haka?!” 

Yusif yayi murmushi tare da sanya yatsun shi guda biyu ya share mata hawayan,gyara zama yayi ya kalleta sosai yace. 

“Balqees na gane baki d’auke ni kamar yadda na d’auke ki ba,ina sonki bani da buri wanda ya wuce naga na aureki amma ke sam ba haka a zuciyar ki.sannan zaki yi tafiya dan kun rainani shine ba’a sanar dani ba sai sallama nazo na tarar kuna yiwa Mami, banda haka da sai dai kawai naji kin tafi, shi yasa nima na nuna muku karfin iko na,kinga yanzu babu wanda yasan cewar ni na saceki dan idan na koma wajan su harda ni a masu nemanki Balqees, 

Yanzu ma zuwa zanyi naga ya jikin wannan sakaran da yake nunawa mutane fifiko a kanki.” 

Da sauri Balqees ta janyo hannunshi cikin zullumi da tashin hankali tana kuka tace. 

“Yaya Yusif dan Allah ka tafi dani karka barni a cikin gidan nan wallahi nayi maka alk’awarin zan aureka dan Allah.” 

Dariya yayi tare da mik’ewa tsaye bayan ya zare hannunshi ya kalleta yana girgiza kai yace. 

“Karya kike yi Balqees babu wani aurena da zaki yi inda a son ranki ne,ki bari naje na samomiki abinda zaki ci dan bana son muyi aure kina tattare da rama bana san ramammiyar mace nafi sonki a haka ‘yar kubul-kubul dake nasan ko ba’a fad’a min ba fatar jikinki zata yi dad’in ta6awa ina zuwa yanzun nan.” 

Yana fad’a yasa kai ya fita sai faman kiranshi take amma yak’i komawa,daga nan gidan su ya nufa yayi wanka ya shirya sannan ya wuce asibiti shi ne yana zuwa yaji abinda Sultan yake fad’a har ya fad’i son ranshi. 

Lokacin da ya dawo tararwa yayi ko ta6a abincin da yasa akawo mata bata yi ba,k’arasawa yayi har kan gadon da take kwance tana ta faman kuka ya kalleta ya kuma kallon soyayyan dankalin turawa da kwai da shayi yace. 

Story continues below


“Me ya hanaki yin breakfast wifey?!” 

A tsiwace ta kalleshi idanunta sunyi luhu-luh tsabar kuka cikin fitsara tace. 

“Sabida banaci! hasalima ban san da wane irin halal aka yi shi ba.Yaya Yusif ka cuce ni ka ha’ince ni indai har baka maidani gida ba wallahi bazan ta6a cin abincin da duk zaka kawo min ba.” 

Yusif ya zaro ido yana kalonta cike da mamakinta,plate d’in ya sake janyowa tare da ajiye shi a gabanta yace. 

“Tashi ki ci ina kallonki idan ba haka ba kibar ganin wai nace ina sonki wallahi tsab zan ji miki ciwo.” 

K’in tashi tayi saima gyara kwanciya da tayi tana ci gaba da kukanta,gaba d’aya ta tsane shi bata ko san ta bud’e ido ta ganshi a kusa da ita.ganin abinda tayi ne yasa shi ture plate d’in ya kwanta a gefenta tare da wulkitota ta dawo jikinshi. 

A razane ta bud’e idanuwa tana kallonshi ya sakar mata murmushi Yusif yana da kyau sosai domin babu abinda Sultan zai nuna mishi sai jan-aji da kamun kai uwa uba miskilanci tamkar Al-eemin yayan Yusif d’in.ture shi ta farayi yayi saurin rik’eta tsam a jikinshi yana shinshinar wuyanta. 

Dukan shi ta fara yi jikinta banda rawa babu abinda yake yi yayi k’ok’ari wajan matseta da kafafuwanshi hannun damar shi kuma ya matseta dashi sannan ya sanya na hagun ya janyo gashin kanta ya tsaida fuskarta saitin tashi a hankali ya furta. 

“I love you Balqees, ada ina son auranki ne dan cimma wani buri nawa amma a ‘yan kwanakin nan soyayyarki ta game min zuciyata sonki nake yi kuma auranki zanyi,yanzun ma ji nake kamar na mallakeki sha’awa ta gareki ta bijiro min amma kin san menene?!” 

Tayi shiru idanuwanta a rufe sai ruwan hawaye dake d’iga a saman fuskar shi yace mata. 

“Kice kina sona da bakin ki inji.” 

Bata yi magana ba still sai kuka take yi jikinta kuma be dena yin rawa ba a hankali yana bin fuskarta da kallo ya kai bakin shi dai-dai saman hancinta ya sakar mata pack tayi saurin d’auke numfashi tare da kuma fashewa da matsanancin kuka. 

Sake d’ago fuskarta yayi yaga sai guntsa baki take yi kirjinta banda rad’ad’i babu abinda yake yi ya fara k’ok’arin sanya bakin shi cikin nata da niyar yin kissing d’in shi kawai yaji shhhha ta kwararo mai amai a fuskarshi,lumshi idanuwa kawai yayi ba tare da ya saketa ba har tayi ta gama sai dai bata dena yinkurin yi ba amma yak’i fitowa Yusif ya janye ta daga  jikinshi ya kwanta da ita akan gadon idanshi ko gani bayayi sabida duk sun rufe da amai ta fara laluban bedsheet sannan ya goge fuskar shi. 

Mik’ewa yayi ya nufi bathroom d’in cikin d’akin ya wanke fuskar shi sannan ya fito,kusa da ita ya dawo tana kwance jikinta duk yayi laushi idanunta a lumshi ya k’arasa yana tambayar ta.
   “Wifey me yasa ki yin amai?!”
Shiru ba magana ya d’ago da ita zuwa jikinshi yana kallonta kafin ya kuma maida ita ta kwanta yace.
   “Bari ina zuwa.”
Fita yayi daga d’akin guide d’in shi ya bawa kud’i yace ya samo mishi ORS sannan ya koma ciki ya zauna a parlor yana jiran dawowar shi,ba jimawa kuwa ya dawo ya wuce kitchen ya had’o mwta sannan ya tafi kai mata cikin d’akin da take. Inda ya tafi ya barta haka ya dawo ya tarar da ita, zama yayi bakin gadon ya kira sunata cikin sanyin murya.ko kula shi bata yi ba ganin haka ya sashi d’ago ta da kyar ya rik’e ta yana kallonta yace.
   “Tashi kisha magani.”
    “Dan Allah Yaya Yusuf ka rabu dani dan Allah badan ni ba.”
Iskar bakin shi ya busar sannan ya mik’e tsaye jin tana neman yi mai kuka,fitama yayi daga d’akin be sake dawowa ba sai abinci da aka kuma kawo mata amma shima still ko kallonshi bata yi ba sallah kawai take yi itama da kya gashi oulsar tace ta tashi amma sam bata gane ba sai faman rik’e kirji take yi cikin ta kuma yana kuka. 

Nadiya kuwa suna komawa gida wanka tayi ta kuma shiryawa tazo tana yuwa Umminta sallama kan cewar zata koma asibiti dan sam hankakinta yana can baza ta iya zama ba domin zuciyarta tana gurin Sultan.Ummi ta kalleta cikin mamaki tace.
    “Nadiya sai ina kuma?!”
    “Ummi can zan koma wallahi hankali na baya cikin nutsuwa.”
Nadiya ta fad’a tana dafe gushi Ummi ta kirata ta k’arasa kusa da ita ta zauna,kallon kurulla tayi mata sannan ta kawar da kai tace.
   “Nadiya anya yaron nan Ahmad ba son kanwar shi yake yi ba kuwa?abin yayi yawa gaskiya, kuma kin san dama akwai aure a tsakanin su tunda ba wai kanwarsa bace uwa d’aya uba d’aya ba a’a cousin ne.”
Nadiya ta kalli Umminta sosai cikin damuwa tace.
    “Ummi idan ma yana sonta ya zanyi tunda nima ina sonshi?ko hakura zanyi nayi ta fama da sonshi bayan nasan shi kad’ai nake so kuma yana sona Ummi domin be ra6a nuna min cewar wai zai iya koda auranta bane.”
   “Nadiya ke yarinya ce baza ki gane abinda nake son nuna miki ba.”
   “Toh ni dai Ummi ki tayani da addu’a idan har aure na da Ahmad akwai alkairi Allah ya tabbatar min idan kuma babu Allah ya bani wanda ya fishi sona.”
    “Amin amma dai yau baza ki koma asibitin nan ba,bana son ki dinga shishige musu har su dinga ganin kina zagewa.”
Sauk’e numfashi Nadiya tayi tare da cire mayafin jikinta,tabi umarnin mahaifiyarta dan bata son duk wani abu wanda zai sa Umminta ta dinga ganin bak’in Sultan amma zuciyarta gaba d’aya tana asibit. 

Story continues below


**** 

Har tsawon kanaki uku ba labarin Balqees zuwan da Yusif yake yi ma asibitin yanzu ya dena Sultan kuwa tun ranar da yaji labarin cewar an sace Bakqees be sake furta kalmar a ba daga bakin shi ba sai dai kullum idanuwan shi da suke zubar da hawaye abinci kuwa tuni suka yi bankwana dashi dan tun ranar da abin ya faru be sake sanya komai ba sai ruwan Lipton da shima sai yaga kamar hajiya kaka zata yi kuka sannan zai sha. 
    
Yau kam da sauk’i jikinshi akan kwanakin baya sai dai har lokacin akwai bandege a kanshi sakamakon ciwon dake keyar shi,babu kowa a cikin d’akin sai shi a hankali ya sauke kafafuwan shi k’asa santala-santala ya mik’e tsaye da kyar,kofofin d’akin yabi da kalo kafin daga bisani ya hangi silifas a bakin kofar toilet yaje ya sanya duk da cewar sunyi mishi kad’an.wata kofa yabi wadda yaga ba sosai ake bin ta ba hasalima Dr gadanya ne da wasu nurses d’in yaga suna biyowa ta gurin ya bud’e a hankali ya lek’a sai ya ga shuke-shuke a gurin hakan ya tabbatar mishi da cewar boyayyar hanya ce yayi fuska kamar irin wanda lafiya ta soma samuwar nan harma irin an barshi ya d’an fara yawatawa d’in nan ya fito sai ya tsinci kanshi a harabar asibitin, lelek’awa yayi be ga wanda ta sani ba kawai ya fice bakin shi d’auke da addu’ar Allah yasa karya had’u da kowa,cikin sa’a kuwa har ya fita be ga wanda ya sani ba ya tari keke napep ya hau direct yayi mishi address din gidan hajiya kaka. 

Tsayawa yayi domin yana tunanin yadda zai yi domin bashi da ko sisin kobo wanda zai bawa mai napep d’in,kallon d’an adai-daitan yayi sannan yace mai. 

“Ina zuwa dan Allah.” 

“Toh.” 

Mai napep d’in ya fad’a yana kallon Sultan. Gidan hajiya kakan ya shiga ya kwankwasa gate d’in mai gadi yayi saurin lekowa, da sauri ya bud’e k’ofar ganin Sultan jiki na rawa ya kalleshi. 

“Rankashi dad’e sannu da zuwa ya jikin naka?!” 

“Da sauki Auwal dan Allah d’an aramin naira d’ari biyu.” 

Auwal mai gadi ya fara laluban aljihun wandon shi ya zaro yana fad’in. 

“Yalla6ai gashi d’ari biyun ta isa?!”

“Eh ta isa Auwal me napep na nan a waje d’an bashi na gode zan baka insha Allahu.” 

Juyawa Auwal yayi yana cewa, 

“A’a yalla6ai wallahi basai ka biya ni ba ma ai kaine.” 

Shi dai sultan be sake cewa komai ba haka ya wuce cikin gidan, a kulle ya tarar da kofar parlorn wadda zata sadaka da d’akunan cikin gidan ya samu guri ya zauna tare da kama kanshi wanda ke tsananin sara mai.
   
Tunani ya fara yi, shin ko su waye suka d’auke baby. Me tayi musu haka ita da ba fita take yi ba bare ace wani tayi wa rashin kunya shine yayi mata haka, Yusif! Zuciyar shi ta sanar mishi domin shine kawai yake adawa da ita, tabbas ba wani accident da yayi domin ya tuna lokacin da yaga wani ya maxgawa glass d’in gaban motar shi sanda kafin ya gama tantancewa ne ya nemi jinshi da ganinshi ya rasa. 

Cak zuciyar shi ta tsaya akan lallai Yusif ne domin shine lokacin da suka je yin sallama gidan su yake cewa. 

“An raina mai hankali da har matar shi zata yi tafiya a kasa gaya mai,toh zai yi maganin abun.” 

Tabbas Yusif ne amma ya aka yi su Abba suka kasa ganewa?da sauri ya mik’e tsaye dai-dai lokacin da yaji Auwal mai gadi yana waya yana cewa. 

“Eh Alhaji yanzun nan mai adai-daita ya sauke shi…eh Alhaji…toh..toh..insha Allahu.” 

Komawa Sultan yayi ya zauna tare da rintsa idanuwa zuciyar shi na zafi yana nan zaune Auwal mai gadi yazo gurin da alama zuwa yayi yaga yadda yake,a hankali ya kira shi ya k’arasa sultan yace. 

“Aran wayan ka Auwal, akwai credit a ciki?!” 

Auwal ya zaro Nokia d’inshi ya mik’a mai tare da cewa, 

“Eh yalla6a akwai naira 75 a ciki.” 

Kar6a yayi tare da zuba numbern Nadiya domin dama tana kanshi ya rik’eta. Tana ta ringing amma ba’a d’aga har sai da yayi mata wajan five miss call amma ba’a d’aga ba, d’an short text message ya tura mata cewar. 

_”Sultan Ahmad ne, please kizo da motan ki wajan Xoxo mall mu had’u karki sanar da kowa dan na baro hospital.”_ 

Lokacin Nadiya na kwance tana kallon hotunan da yayi musu da bikin su Jamal sarai taga kiran amma da yake number ce yasa tak’i d’agawa. Text message d’in da ta gani ne yasa ta bud’ewa ai tana ganin yace shine tayi saurin tashi, doguwar riga ta zura a saman mini wears d’in jikinta da sauri ta d’auki mukullin motar ta tayi waje.zaune taga Ummi da Yaya imran sai kaninta yazid tayi saurin saita nutsuwar ta dan kar su ga azar6a6inta tace. 

“Ummi bari naje gidan su Nabila yanzu zan dawo.” 

Ba wani gaddama kuwa Ummi tace, 

“Toh sai kin dawo ki gaida min da hajiya Aminan.” 

Da sauri ta fita tana cewa. 

“Toh Ummi zata ji.” 

A dai-dai bakin titin shiga Xoxo mall ta hange shi a tsaye, ai kuwa shine tayi mai horn ya k’arasa ya shiga. Kallonshi ta dinga yi cike da mamakin shi, shi dai be yi magana ba hasalima dafe kai yayi yana faman rintsa idanuwa…..

   _Assalamu alaikum reader’s a dinga min afuwa sannan banji dad’i ba ganin akwai kurakurai a ciki amma ba’a gyara min jin shirun ku yasa wlh ko editing banayi sai daga baya Asheatou take gaya min sannan nima jiya na zauna ina sake bin shi kawai na dinga cin karo da typing errors da kuma mistake first nace sunan Balqees Hafsat daga baya na maidashi Maryam kukayi tsit🤦🏻‍♀nasa men a matsayin man kuka yi tsit, nasa mouse a memakwan mouth nan ma shiru oh ni Dijama😪 ai shikenan…🤗_

    
    *”M*ine…!”
Nadiya ta k’ira sunan shi cikin sanyin murya tana tuk’in a hankali. D’agowa yayi yana faman lumshe ido ya kalleta idanunshi jawur tayi saurin d’auke kai dan ji tayi zuciyar ta na bugawa. Sai da ta samu guri inda babu motoci da yawa sannan tayi parking a gefen titi tana sake kallonshi tace.
   “Afuwan mine, ya aka yi ka baro cikin asibiti bayan baka warke ba?!”
Cikin sanyin murya yace,
   “Nadi ki gaya min ta yadda zan zauna a asibiti ana kula da lafiya ta bayan nayi sanadin 6atan baby. Nadi ba’a san fa a wane hali take ciki ba, tayaya ni zanji dad’i ko ayi tunanin hankalina zai kwanta harma na samu nutsuwar zuciya da ta gangar jiki?!”
Yayi shiru yana sauk’e numfashi a wahale, Nadiya ta share kwallar idanunta cikin tausa yawa ta kalleshi tace.
    “Amma dai ai be kamata ace ka fito daga asibiti ba domin kaima kana buk’atar temakon likita. mine baka da lafiya taya ya zaka samu kwarin gwaiwar nemo daughter? Dan Allah ka bari na mayar da kai asibitin nan please.”
Hak’ik’a yana da buk’atar hakan domin zuciyar shi wani iri take mai ga jiri da yake ji sai dai bazai iya bari ya kuma komawa asibiti ba alhalin be san a wane hali Balqees take ciki ba. Rik’e handle d’in k’ofar yayi da k’arfi sakamakon ji da yayi kanshi yayi wani irin nauyi tamkar zai fad’o yana faman cizon le6enshi Nadiya ta sake kallonshi tace.
   “Sannu! bari na kaika gida toh sai ka samu ka kwanta.”
Sultan Ahmad yayi saurin kad’a mata kai cikin dauriya ya kalleta yace.
   “Kaini gidan hajiya kaka sai ki koma gida.”
Kifa kanshi yayi a gaban motar cikin tsananin tausayawa Nadiya ta kalleshi,hannu ta d’aga a hankali da nufin ta6a bayan shi sai kuma tayi saurin janyewa tana furta,
   “Auzubillahi minasshai d’anurrajim.” 
A cikin zuciyarta kafin ta kunna motar taja suka bar wajan. Tafiya suke yi a hankali kai da kaga yadda ake tuk’in kasan meyin ba sauri yake yi ba, can Sultan ya d’ago ya kalleta yace.
    “Nadi akwai wanda nake zargi da d’auke baby.”
Da mamaki Nadiya ta kalleshi tana zaro idanuwa, kad’a mata kai yayi cikin tabbatarwa ya kuma jinginar da bayan shi jikin kujerar da yake zaune akai yace.         
   “Juya da motar muje gidan su Yusif,kin san gidan ai ko?!”
   “A’ah ban sani ba, amma ya akai kai kake da tabbacin cewar a gidan ne aka sace daughter bayan harda su ake faman nemanta?!”
Sultan Ahmad ya kuma rintsa idanuwa ba tare da ya bud’e su ba yace.
   “Bani da tabbas Nadi, sai dai zuciya ta tak’i dena zargin cewar Yusif ne domin nasan bashi da hankali sosai tsab zai iya sawa ayi mata haka. least word d’in shi akanta shine cewar wai yama za’ai matar shi zata yi tafiya amma ba’a sanar mai ba, wallahi sai yayi maganin abun. ki gaya min Nadi ta yaya zank’i zargin shi bayan daga gidan su gurinki muka zo a hanyar mu ta komawa gidan hajiya kaka kamar jira na ake yi na dawo kawai aka fad’o mana.”
Shiru tayi tana tunanin haka suka tafi yana nuna mata hanya, idan round about ne zai nuna mata hakama idan u turn ne a haka har suka k’arasa gidan su yusif.suna zuwa yace ta tsaya a bakin gate shi kuma ya k’arasa ciki gurin baba Auwal mai gadi ya tsaya, sai da suka gaisa sannan baba auwal ya tambaye shi jikin shi Sultan yace da sauk’i sannan Sultan ya kuma matsawa wajan shi yace.
    “Baba lawan dan Allah idan babu damuwa ina son muyi magana amma dan Allah badan niba ka gaya min iya abinda ka sani.” 
Baba Auwal mai gadi yayi murmushi tare da cewa,
   “Karka damu Ahmad insha Allahu duk abinda na sani zan sanar maka.”
Numfashi Sultan ya sauk’e sannan ya kalli baba Auwal yace.
   “Dan Allah baba tsakanin kwanaki hud’u zuwa yanzu a wane lokaci Yusif yake dawowa gidan nan?!”
Sai da baba Auwal ya kuma numfasawa sannan yace,
   “Toh Ahmad ai tun kafin wannan lokacin zan iya ce maka babu wani tsayayyan lokaci da zance ga sanda oga Yusif yake dawowa, dan bashi da wani tsayayyan lokaci wanda za’a nuna, yanzu kuwa wani lokacin ma sai ana kiran sallar asuba zaka ganshi ya dawo.”
   “Toh baba na gode bari na wuce.”
    “A’ah toh Ahmad baza ka shiga ba?ai naga uwar gidan ta dawo d’azu suna ciki.”
Baba Auwal ya fad’a, Sultan ya kad’a kai alamar ba zai shiga ba yayi wa baba mai gadi godiya sosai sannan ya juya ya bar gurin. Komawa yayi mota ya tarar Nadiya na waya da alama da Ummi take yi, sai da ta kammala sannan ta kalleshi tana kokarin yin magana ya riga tayi ta hanyar cewa.
   “Ummi taji ki shiru ko?!”
Nadiya ta girgiza kai tana murmushi kafin tace mai.
   “Tambaya na take yi wai ko nasan inda kake, nace Mata kana hospital shine tace min ai ka gudu an nemeka an rasa,shine nace mata toh zan biya ta gidan ku naga ni.”
Gyara zama Sultan yayi sannan ya kalleta itama shi d’in take kallo yace.
   “Muje ki tafi gida in yaso sai na samu napep na koma gida nima.”
   “Tab! kana tsammanin zan iya barinka a wani gurin kai kad’ai?har gida zan kaika na had’aka da Umma sannan nima na tafi namu gidan.”
Saurin bagarar da zancen tayi ganin zai yi mata gadda ma yasa tayi saurin cewa.
   “Wai da kashiga me kayo a ciki mine…?!”
Iskar bakinshi ya furzar sannan cikin damuwa yace,
   “Gurin mai gadi naje amma ban wani samu kwakkwaran abinda zai nuna min cewar lallai Yusif ne ya d’auke Balqees ba, bana son nakai zancen gurin ‘yan sanda alhalin bani da wani makari ko shedar da zata nuna cewar shine ya d’auke ta, amma yanzu ina buk’atar nazari da tunani.”
Gidan su Sultan Nadiya ta wuce be ce mata komai ba sai ma tunanin yadda zai 6ollowa alamarin yake yi, koda suka je babu kowa a gidan sultan ya kalli Nadiya itama shi take kallo yace.
   “Ina wayan ki?!”
    “Gata nan.”
Nadiya ta fad’a tare da mik’a mishi wayan,kar6a yayi ya sanya nomban Umman shi sai yaga ashe tana da ita ta sanya sweet in-law sai ya buga sannan ya kara a kunne.
   “Hello Nadiya!”
Mamaki ne ya cika mai zuciya, ke nan dama suna waya da juna amma babu wadda ta ta6a sanar mai.kauda mamakin nashi yayi gefe cikin sanyin murya Sultan yace.
   “Umma nine kuna ina ne gani a gida duk bakwa nan.”
   “Lailaha’illallahu Muhammad rasulillahi (s.a.w), yanzu daman kuna tare?!”
Sultan ya yayi shiru dan be san me zai ce ba jin shiru yasa Umma cewa.
   “Toh ga munan karku tafi ko ina duk kunja hankalin mu ya tashi.”
Lokacin da su Umma suka dawo Nadiya kawai suka tarar a mota shi kuma yana side d’in shi yana sallah, ba yadda be yi da ita ba akan suje tare amma tak’i yadda sabida tana tsoran su ke6ance su biyu alhalin duk suna son junan su komai na iya faruwa.
   “Yana ina shi kuma d’ayan?!”
Umma ta tambaya tana kallon Nadiya dake faman sosa bayan d’ankwalinta, ji tayi kunya duk ta kamata kamar ta zura da gudu sai dai ba halin yin hakan dole tasa cikin jin nauyi tace.
   “Umma yana ciki sallah yake yi.”
Ta fad’a tare da yiwa su Adda Aisha da Umma nuni da part d’inshi da yatsanta, hajiya kaka ta k’araso wajan ita da Abba ta kali Nadiya idanunta sun kankance tace.
  “Yanzu nan fisa bilillahi irin abinda kika biye mishi kuka yi kun kyauta kenan eh yi? muna cikin wani tashin hankalin bamu fita ba kun sanya Mu cikin wani tsakani da Allah kun yiwa zuciyoyin mu adalci kenan?!”
Jikin Nadiya yayi sanyi cikin girmamawa ta dinga basu hakuri gaba d’aya kasa nuna musu tayi cewar itama babu laifinta a ciki taja bakinta tayi shiru sai dai tayi ta basu hakuri  kanta a k’asa kamar ita taje ta sato shi. 

Gabaki d’ayan su suka nufi sashen nashi, suna zuwa suka tarar ya idar yana k’ok’arin fitowa Umma ta daka mai wata uwar harar dan lokacin an tada gen haske ya bayyana Sultan ya kawar da kai tamkar be gani ba tare da k’arasawa wajan hajiya kaka ya rik’o hannuta. Itama d’in ture mai hannu tayi tana zabga mai harara sai ya koma gefen Adda Aisha fuskar shi gwanin ban tausayi nan da nan hajiya kaka ta sauk’e nata fushi ta kalleshi tace.
    “Dawo nan Muhammadu ai nasan ba laifinka bane, sai dai ka karya min kudirina na cewar bazan zo gidan nan ba sai gashi yau nazo ta dalilin tashin hankalin da ka sani, zo nan kaji kaji.”
Ta fad’a tana mik’a mai hannu, sosai yaji dad’i ya k’arasa wajanta tayi saurin kamo hannunshi sai taji shi zafi zau alamun zazza6i ne a jikin nashi tace.
    “Ashe har yanzu akwai zazza6in nan a jikinka amma Muhammadu ka fito daga asibiti? Toh tashi zaka yi mu koma dan ba’a zama da larura inda ba ka rasa yadda zaka yi ba, amma kai kana da yadda zaka yi domin akwai abinda za’a biya Allah ya baka lafiya zo maza mu koma asibitin.”
    “A’ah hajiya ni bazan koma komawa asibiti ba har sai Allah ya bayya na mana baby, yanzu ku shiga cikin gida bari naje muyi sallama da Nadiya.”
Zata yi gaddama yayi saurin zare hannunshi daga cikin na ta yayi gurin Nadiya dake cikin mota a zaune. Tana ganin shi tayi saurin gyara zama tare da cewa.
   “Zan wuce gida sai Allah ya kaimu gobe.”
Sultan ya kalleta cike da kulawa yace,
   “Zaki iya komawa gidan ko nazo na rakaki?!”
   “A’ah zan iya karka damu Allah ya baka lafiya, Allah kuma ya baiyana mana daughter da rai da lafiya.”
   “Amin only one see you tomorrow bye.”
   “Ok bye.”
Da haka ta fita daga gidan shi kuma yana bin ta da kallo har tabar cikin layin. A hankali ya juya sai suka yi kicibus dasu Umma zasu koma side d’inta hajiya kaka ta kalli Abba tace.
    “Toh ni kuma sai kazo kq maida ni gida, dan Allah gobe idan kunje police station d’in ku tabbatar da kun samu kwakwaran bayani ace har yanzu babu wani motsi kullum jiya i’yau.”
Abba ya ce toh cikin girmamawa yana son mahaifiyar tashi gashi yanzu jininta ya kuma hawa sabida wannan tashin hankali, yanzu kam yasan hankalinta ba zai kwanta ba har sai randa aka ce anga Balqees shine kawai zai sa hankalinta ya kwanta.mota yaje ya bud’e mata ta shiga yayin da itama Adda Aisha tace gara ta bisu su rage mata hanya shi kuma Sultan Umma ta jashi suka shga cikin gidan sai faman rintsa idanuwa yake sabida tsananin ciwo da yake ji yana yi mai. 

*****
Balqees kuwa tana kulle damuwa tayi mata yawa duk ta rame ta sake k’ank’an cewa ciwon yinwa olsa ya kuma tsananta a gareta ta kai ta kawo ko ruwa tasha sai taji kamar zata mutu ko kuma ta amayar dashi.gaba ki d’aya ta d’agawa Yusif hankali sabida k’iris ya rage ta k’arasa lahira, domin yau sati d’aya kenan da d’akko ta amma tun tuwon da taci a daran ranar bata sake cin wani abuba sai ruwa,ta kai ta kawo yanzu sanida tsabar zafi da zugin da k’irjinta keyi sai ta sanya ruwan sanyi ko kankara a gurin sabida har wani tafasa taji yana yi mata.
    
Shigowar shi kenan d’akin da take ya tarar da ita a kwance,k’arasawa yayi inda take hannunshi d’auke da leda ya siyo mata yoghurt da tufa yaje ya ajiye a k’asan gadon tare da kallonta domin yanzu tausayi take bashi duk da taurin kan da take nuna mai ga shegen fad’in ran tsiya ya sanyaya murya cikin salon can hankali yace mata.
   “Wifey tashi kisha yoghurt bana son yau kiyi min gaddama idan ba haka ba wallahi saki gane kuranki.”
Shiru ko motsawa ba tayi ba ya kuma mai-maitawa still ko motsawa bata yi ba cikin 6acin rai ya wulk’ito da ita sai ya ganta a sassandare tamkar gawa be san lokacin daya kwallah kara ba dai-dai lokacin Sultan ya shigo d’akin domin tun washe garin ranar daya fito daga asibiti tun lokacin yake bibiyar Yusif,duk da cewar yasan tun kafin lokacin gurin zuwan shine hasalima ya maida gurin tamkar gidan shi dan daddy d’in ba zuwa yake yi ba hakan yasa shi kanshi sultan be ta6a sha’awar shiga ba sai yau da yaga kullum Yusif yana zuwa akai a kai ga zargin shi da yake yi yasa shi biyo shi a baya.
    
Tun a gate yaga mutane tamkar ‘yan daba amma hakan be sa ya d’aga hankalin shi ba sai addu’ar neman tsari ce Kawai a bakin shi da zuciyar shi, a kofar parlor ne ya kusan samun matsala domin na ukun ne ya fara mai tambayoyi Sultan cikin dakewa da yin yak’en dole ya nuna mai cewar ai tare suke shine ya kira shi sannan ya barshi ya shiga, aikuwa yana shiga idanuwan shi suka sauka akan gadon inda yaji ihun Yusif ya d’agota jikin yana faman jijiga ta amma shiru. 

A razane shima Sultan d’in yayi gurin da gudu hankalin shi a tashe yaje ya fizgeta, kwarai kuwa ita ce ya fara kiran sunanta amma ina da kyar ya iya d’agowa ya kalli Yusif jijiyoyin goshin shi duk sun firfito yayin da hakoransa suka datse na sama dana k’asa idanunshi suka kuma yin jawur ba tare da yayi magana ba ya sureta suka fita can waje inda yayi parking mutane sai kallon su suke yi don shima Yusuf biyo su yayi kai da kagan shi kasan ba’a haiyacin shi yake ba.Sultan ya sanya ta a bayan motar sannan ya koma drive seat shi kuma Yusif ya shiga bayan duk sultan be yi magana ba dan baya cikin nutsuwa, har suka isa asibitin Dr gadanya….





Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *